Share this page
wanda Hydar ke zaune idanunsa sun ɗan kumburo sun yi jaa. Buɗe ƙofar room ɗin aka yi wasu doctor's suka fito su uku, cire facemask ɗinsa na farkon ya yi tare da faɗin ''We are sorry to say......'' bai kai ga ƙarasawa ba Hydar ya yi saurin tashi tare da faɗin ''Ko da wasa kar ka kuskura ka faɗi kalmar da ba ta yi min ba anan.'' Ɗayan doctor ɗin ne ya ce ''Calm down Sir, give him a listening ears.'' ''Okay continue.'' Hydar ya yi maganar tare da ƙafe doctor ɗin da ido. ''Gaskiya aikin yarinyar nan yafi ƙarfinmu, because jinin da aka saka ma ta ya ƙara ƙonewa, her condition is very very critical and cutar na nunawa ma ya daɗe a jikinta a yadda x ray ya nuna.'' ya na faɗan hakan shi da sauran colleagues ɗinsa suka bar su a corridor ɗin. Tun da Ilham ta fuskanci da Liyana ake critical condition, ta zube a wajen sumammiyya. A rikice aka yo kanta Neneh da abin ya ishe ta ta sanar a platform ɗin family house na su gabaɗaya ana buƙatar taron family duk nisan ka babu uzuri, a gobe ake buƙatar kowa. Mami is Totally confused a yadda ake ta ambatar sunan Cancer tun shigowarta hospital ɗin, a hankali ta kama hannun Neneh tare da wucewa office ɗin Doctor Farouk. Bayan sun shigo nuna musu sit ya yi da alamar su zauna. A hankali Mami ta ce ''Doctor since nake ta jin kuna ambatar cancer tattare da daughter na, I hope this is a prank right?, because my daughter is pregnant, and you people are not even talking about the unborn child.'' Murmushi ya yi sosai sannan a hankali ya ce '' Maama, nothing like pregnancy a jikin yarinyar ki, akwai Mass ɗin da lulluɓe ma ta mahaifa, a yadda ruwayar wancan result ɗin ya bayar, kuma yanzu ya yi explode ya zama Cancer and every minutes jininta ƙara ƙonewa yake.'' Doctor Farouk ya gama musu bayanin tare da miƙa musu sauran test ɗin. Da sauri Neneh ta amsa tare da faɗin ''Mass ka ce ko masa, meye haɗin shi da jikata da zai shiga jikinta idan ban da zalunci fisabilillahi.'' ta yi maganar ta na jan majina....... Manage please 💎🥀 Mutuwa kan kawo canji⏩⏮️🤝 ''Ya Ubangijina ka basu daman share." Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟 Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔 *THE REGRET* PENDING AMARYA CE ✍️ JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION The Noble Writers Team. **Pending Amarya 51** What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩ Every ending is a new beginning 💎🥀 even if the heart disagrees.✅🌕🤝🦋 🤍 🫧 🤧 Not edited 🌟💔🥹 **** Da sauri Neneh ta amsa tare da faɗin ''Mass ka ce ko masa, meye haɗin shi da jikata da zai shiga jikinta idan ban da zalunci fisabilillahi.'' ta yi maganar ta na jan majina....... Murmushi ya yi sosai sannan a hankali ya ce '' Maama, nothing like pregnancy a jikin yarinyar ki, akwai Mass ɗin da lulluɓe ma ta mahaifa, a yadda ruwayar wancan result ɗin ya bayar, kuma yanzu ya yi explode ya zama Cancer and every minutes jininta ƙara ƙonewa yake.'' Doctor Farouk ya gama musu bayanin tare da miƙa musu sauran test ɗin. Da sauri Neneh ta amsa tare da faɗin ''Mass ka ce ko masa, mai haɗin shi da jikata da zai shiga jikinta idan banda zalunci fisabilillahi.'' ta yi maganar ta na jan majina. Kauda zancen Nenehn Mami ta yi tare da amsan result ɗin ta na ɗan dubawa a hankali, sannan ta kama hannun Neneh suka fice daga office ɗin. Ko da suka fito suna tsaitsaye cirko- cirko, Ilham ta farfaɗo, wucewa Mamin ta yi ta sami Abbhu akan maganar a fitar da Liyana ƙasar waje tun da likitocin duk sun nuna aikin ya yi ƙarfi da yawa. Bai ƙi tata ba ya sami Jiddah da Abbhi ya wassafa musu komai. A take suka yi na'am da zancen, anan take aka fara preparations ɗin tafiyar, duk wasu takardu na rashin lafiyar na ta sai da aka haɗa su as one documents. Sannan Abbhi ya bada jininsa har leda biyu aka sa ma ta saboda ta samu wanda zai ɗan riƙe ta kafin a ta fi a goben. Fashewa Ilham ta yi da kuka akan ita ma sai ta bi Liyanar, jiki ba ƙwari ta koma gida ita ma ta fara shirye-shiryen da ya dace. Su Rashanda jikinsu duk a ruɗe bayan sun dawo daga lectures, kamar su yi kuka haka suka ɗinga ji, Unaisah kam sai da ta zo da yamma duba Liyanar da ba ta iya shaida duk wanda yake kanta. ><><>><><><>> Hydar kam gwanin ban tausayi, ya rasa mai zai yi ya samu sauƙi musamman idan ya tuno ranar da ya sanyata wanke wanke kalar shirmen da ta ɗinga yi, wani kalar muryarta ya ji a cikin kunnenta ta na faɗin ''Yaya Alih please.'' wani kalar jaa idanunsa ya yi ya na ƙara hango yadda ta ɗinga rayuwa a gidan time ɗin da yake China. ''Aliyu.'' Mami ta kira sunansa a hankali tare da dafa gwiwar ƙafarsa, daman already sun riga sun shigo ɗakin da aka kwantar da Liyanar saboda sauran sun koma gida sanadiyyar dare yayi. Ɗago kansa ya yi a hankali ya na ƙafe Mamin da jajayen idanuwansa, sannan a hankali ya furta ''Maa.'' tare da sauke idanunsa ƙasa. ''Aliyu are you not a Muslim?, ba ka yarda da ƙaddara ba?, ina ilimin ka yake?, tun jiya yaushe rabon da kayi wanka ko ka ci abinci na tabbatar tun jiya, please ka cire damuwar nan a ranka, addu'a ya kamata ka yi ma ta, have you prayed.?" Bakinsa na ma sa nauyi ya ce ''Noo Maa.'' ''And you genuinely wants her to be fine?, za ka tashi ka wuce gida ka yi abin da zai fishe ka ko dai na mareka a wajen nan.'' Mami ta yi maganar idanunta a kansa. Jiki a sanyaye ya wuce parking space tare da wucewa gidansa ya na sassanar ƙamshin turarenta da bai bar motar ba. Horn ya yi wanda Salimah dake bakin gate da hankalinta yake a tashe ta yi saurin buɗe gate ɗin da wani mugun gudu ya yi parking motar ta sa tare da wucewa cikin gidan. Direct ɗakinta ta nufa inda ya tarar da shi komai tsaff, banɗakinta ya shige tare ɗaukan brush ɗin da ya tabbatar da cewa na ta ne ya yi brush da shi, tare da yin wanka da duk wani abu da take amfani da su, sannan ya ɗauro alwala ya fito daga cikin banɗakin. Manta na shafawa ya shafa ajikinsa tare da shafa roll on ɗinta har ma da turarenta sannan ya wuce ɗakinsa ya sanya jallabiyarsa maroon color haɗe da haɗa wasu kaya a cikin trolly. Sallolin da ake binsa ya gabatar tare da ƙara komawa hospital ɗin da har yanzu ta na yadda take babu wani canji. Pepe soup mai zafi Mami ta zuba ma sa, shima sai da ta masa jan ido sannan ya ci, kamar zai yi kuka. Har yanzu mamakin yadda cutar ta zo ma ta yake, daga intercourse kuma sai Cancer, anya ba sa hannu a lamarin nan kuwa. Washegari kuwa da sassafe suka wuce ta private jet ɗin Abbhu wanda direct a Germany za su sauka saboda suna da high quality cancer treatment and care. Yanayin ginin hospital ɗin kaɗai zai tabbatar ma ka da cewa ba ƙaramin hospital bane, dake Abbhu ya sanar da zuwan su hakan ya sanya suna zuwa doctor Marcus ya sa aka shigar da ita wasu machines na gwaje gwajen da ya dace ace an yi ma ta dan duk wani takardun Nigeria watsar da su suka yi a gefe aka fara sabon bincike akan Liyana. After the test results ✨😪🥹💔 Gabaɗaya test ɗin Abu ɗaya yake nunawa, amma wannan ya banbanta da sauran,dan wannan na tabbatar da cewa ba lallai ta ƙara jimawa ba a duniya duk da basu san yadda ta Allah za ta kasance ba. Ilham, Hydar, Mami, gabaɗayansu sun shiga tashin hankali mara misaltuwa, barimma Hydar da gabaɗaya ya kusa fin Liyanar shiga wani hali, shi idan ma mutuwan za ta yi ta taimaka ta yafe mi shi , da abin zai fi ma sa sauƙi a rayuwar shi. Haka rayuwar Liyana ta ci gaba a DKFZ dake a ƙasar Germany gwanin ban tausayi, sam rayuwarta a kwance take yin sa sannan Oxygen a hancinta, sai wani abu da aka sanya mata shi a hannunta wanda kamar supporting numfashinta shi ma yake. Zaune suke a cikin VIP room ɗin da yake su kaɗai, sai Liyana dake kwance samɓal a kan gadon ɗakin tamkar ba za ta yi motsi ba. Ilham na zaune kusa da Mami kanta a kan cinyar Mamin da take shafa ma ta kai haɗe da daɗaɗan kalamai wanda ke ƙara sanya zuciyarta cikin positive taughts game da rashin lafiyar yayarta. Hydar shi kam ya na zaune wajen gefen Liyana kansa a ƙasa ya na kallon wayarsa wanda dukkanin alamu sun nuna kamar hoton Liyana ne, time ɗin da take ji da kanta. Ɗago kansa ya yi daga kallon videon da ta yi shi ita da Ily a wani babban restaurant jikinta sanye da palazzo trousers fari sai wani top shi ma fari, sai wani faux fur v neck jacket shi ma fari, sai wani heels da ta saka black da jersey veil black color ya yi ma ta mugun kyau, sai wani sun shade da ta ɗaura akan black veil ɗin. Hannunta riƙe da wani ice cream a wani ice cream disposal container mai kyau. Ɗayan videon kuma a lokacin suna yara da ita da Ily da Ammi har Abbhin a Saudi Arabi, fuskarta sanye da glasses masu kyau, a ƙasan picture ɗin ta rubuta ''Family over everything ✅ 💎.'' Wasu kalar hawaye ne suka zuba a idanunsa, ya yi sauri ya share su tare da ajiye wayar ya ɗan jinginar da kansa kaɗan. Ƙarar heart monitor dake control numfashinta ne ya fara karaɗe ɗakin irin na cewa mutum na gargarar mutuwa, a firgice ya taso inda har su Mami sun danna bell ɗin kiran doctor, wani kalar ƙara ya ɗinga yi mai mugun ƙarfi, wanda hakan ya sanya doctor's mayar da su waje suka duƙufa wajen ceto rayuwarta. Ɗiff gaba ɗaya na'urar ta kawo flat line without any zigzag, ma'ana zuciyarta ya daina bugawa, wani kalar hawaye mai zafi ya zubo a kuncin Liyanar. Sannan ta ja wani dogon numfashi haɗe da wani kalar zabura daga gadon sannan ta koma da ƙarfi, da hanzari doctors ɗin suka fara danna ma ta ƙirji amma kuma Liyana is unresponsive,, Sam ba ta ba da wani alamar ta na da sauran numfashi. Doctor Samson ne ya naushi bango da hannunsa tare da furzar da wani iska daga cikin bakinsa sannan a hankali ya ce ''Guys we have lost her.........'' Manage please 💎🥀 Mutuwa kan kawo canji⏩⏮️🤝 ''Ya Ubangijina ka basu daman share." Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟 Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔 *THE REGRET* PENDING AMARYA CE ✍️ JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION The Noble Writers Team. **Pending Amarya 52** What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩ Every ending is a new beginning 💎🥀 even if the heart disagrees.✅🌕🤝🦋 🤍 🫧 🤧 Not edited 🌟💔🥹 **** Doctor Samson ne ya naushi bango da hannunsa tare da furzar da wani iska daga cikin bakinsa sannan a hankali ya ce ''Guys we have lost her.........'' Ƙara kallon gawar Liyanar dake kwance samɓal suka ƙara yi, wanda hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa mutuwa ta yi. A hankali Marcus ya zame daga cikin room ɗin tare da nufar ƙofar wajen da su Hydar ke tsaitsaye cirko- cirko, Ilham na jikin Mami yayin da shi ke tsaye a bakin ƙofar kamar wanda ke jiran sallahu. Jin ƙarar buɗe ƙofar ya sanya shi saurin shan gaban Marcus tare da tsastsare shi da manyan idanunsa, face mask ɗinsa Marcus ya cire tare da sauke wani ajiyar zuciya sannan a hankali ya ƙara kai dubansa wajen Hydar ɗin tare da faɗin ''Sorry to say, I know how you feel bro, buh we have lost your wife.'' ya na maganar ya wuce Hydar ɗin. Saurin dawo da shi baya Hydar ɗin ya yi muryarsa na breaking ya ce ''I...... Don't gerr you well, ban gane abin da kake nufi ba.'' ya yi maganar idanunsa na kawo ruwa. Shi kansa Doctor Aliyu tausayi ya ba sa, bai iya yiwa Aliyun magana ba ya zare hannunsa tare da kallon Mami da ita ma wasu kalar hawaye sun fara kawo ziyara idanunta. Ilham kuwa shock ne ya sameta ta nemi hawayenta ta rasa ga wani zafi da zuciyarta yake ma ta. Zubewa ya yi a wajen ya na girgiza kansa ya na wani kalar kuka kamar mace, tare da faɗin ''Noo, Fatimah not now, ba yanzu da zuciyata ta aminta da ke ba.'' Ya yi maganar a zauce tare da fito da wayarsa ya na dailing number Amir. Ring ɗaya kamar Amir jiransa yake ya ɗaga tare da faɗin ''Aliyu ta tashi?,'' bai kai ga yin wata magana ba Ammi ta amshi wayar daga hannunsa tare da faɗin ''Aliyu ka bawa Liyana wayar na yi ma ta magana.'' ta yi maganar itama hawaye na fita a idanunta, dake gaba ɗaya family ɗin kowa ya hallara. Kukan Ammi da na Mami da yake ji ke ƙara sanya zuciyarsa zafi, da wani kalar murya mai ɗan kauri ya ce ''Liyana is gone Ammi Matana ta mutu.'' ya na faɗin hakan ya saki wayar a wajen tare da jinginar da kanshi a bango ya ci gaba da kukansa. ><><><>><><>>< Can Nigeria kam tun bayan tafiyarsu Hydar ɗin kullum cikin sadaka ake, ba ka taɓa ganin gidan Neneh babu jama'a. Kamar yadda gidan ya saba gaba ɗaya family ɗin shuwa arabi ne a gidan,wasu na addu'a wasu na hira, har da su Abbuh da Sultan da Amir da iyayensa dukkanin su suna gidan Neneh. Ganin wayar Amir na Ring ne ya sanya shi saurin ɗagawa saboda ganin sunan Hydar ɗin. Ya na fara magana Ammi ta amshe wayar wanda daga ƙarshe sai sumanta suka gani a ƙasa, da sauri aka ɗagata saboda su Abbhun da manyan duk sun fita kai sadaka gidan marayu. Already daman wayar a handsfree yake, hakan ya sanya su jin muryar Hydar ɗin ya na faɗin ''Ammi matana ta mutu.'' Gaba ɗaya falon aka saki salati da salallami banda Mama Fatuh da jikinta ya yi sanyi har ya fara kakkarwa. Take bowl ɗin wata melon dake hannunta ya faɗi a ƙasa tare da tarwatsewa ta na mai faɗin ''Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ni Fatuh, Liyana ce ta mutu.'' ta yi maganar muryarta na dashewa a lokaci ɗaya tare da yin wajen gidan ta fice daga gidan gabaɗaya. Kowa na wajen ya sha jinin jikinsa barin ma yadda Ammin ke zubda hawayenta, Umma Mansura ita kanta ta rasa ya zata yi. ><><>><><>><> Kamar wani abu ya mintsine shi ya yi saurin buɗe ɗakin dai-dai time ɗin da ake haɗa mortuary injection, domin kar gawar ta lalace. Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Don't you dare lay your hands on my wife, she's not dead.'' ya na faɗin hakan ya ƙaraso wajen Gawar Liyana tare da ɗaukan ta a hannu kamar baby, ta yi masa nauyi sannan kuma ta ɗan sake. Fitowa ya yi da ita daga ɗakin inda ya tarar da Mamin a corridor jikinta riƙe da Ilham, Ilham da ta kasa kuka ta na ganin Liyanar kawai ta wani irin fashewa tayi da kuka ta na ƙara ƙanƙame Mamin a jikinta. Authority ɗin hospital ɗin suka hana shi fita da gawar akan sai sun ƙara tests da wasu binciken, amma sam Hydar yaƙi yarda akan shi a basa matarsa ya fasa maganin, sai da Mami ta kusan kai masa duka sannan ya ajiye Liya a kan gadon patients aka nufi X-ray da ita. After 2 hours. Result ya fitar da komai na ta lafiya, cikin jikinta shi ma ya na nan cikin ƙoshin lafiya amma babu numfashi a tattare da ita. Abin ya mugun ɗaurewa doctors ɗin kai, amma ba su iya nunawa su Mamin result ɗin ba suka basu gawar Liyanar domin tafiya da ita gida Nigeria. A cikin jet ɗin ma hannunsa na riƙe da na ta idanunsa na fidda hawaye. After 7 hours. Direct airport jet ɗin ya sauka, wanda har su Amir da Sultan sun zo ɗaukarsu dan har ƙarfe tara na dare ya yi, hannunsa riƙe da ita aka gangaro da gadon patients zuwa wajen da yake dan har da ambulance a masu ɗaukan su. Bayan an sanyata a motar sai da yabi ganyen dake jikin motar gabaɗaya ya ciccizge sannan ya shiga bayan ambulance ɗin shi ma ya na riƙe da hannunta tare da ɗora kansa akan kan Liyanar. Hawaye na ɗiga a idanunsa zuwa kumatunta. Har suka ƙaraso cikin gidan bai san an ƙaraso ba sai da aka buɗe ambulance ɗin. Abbhi ne tsaye da jallabiyarsa shi da Jiddah da Abbhu. Abbhi idanunsa ya yi jaa, he can't even talk sai hawayen da yake zubarwa, kama gadon ma aikatan ambulance ɗin suka yi tare da yin entrance ɗin gidan Nenehn da ita. Gidan cike yake maƙil da mutane har da bloggers, ''Ƴar gidan Abbhi is dead.'' ya'n school ɗinsu da exes ɗinta gaba ɗaya duk suna jiran gawar da sai gobe da safe za'a kaita. Classy Reeda da Sandy Rash da sauransu are all crying, sun rasa ma ya zasu yi kowa sai posting pictures ɗinta yake Ya'r gidan Abbhi ta rasu, Liyana bae is dead. Ko ina a yanzu ya amsa mutuwar Liyana. A falo aka shinfiɗeta bayan kulle ƙofar ɗakin iya love ones ɗinta ne a falon, a hankali Abbhi ya rarrafo idanunsa na zubda hawaye tare da faɗin ''Ya'r Abbhinta why?, mai sa za ki tafi ki bar Abbhinki,? Where are the promises?, First fruit wake up na san you're pranking me.'' Abbhin ya yi maganar tare da riƙo hannunta ya na karawa a hancinsa. ''Yaya dan Allah kayi haƙuri ka daina kukan nan.'' Umma Mansura ta faɗa hawaye na sauka daga idanunta itama tare da ɗan jan Abbhin daga kusa da gawar Liyanar. Neneh kam sai gwale ido take ta kasa kuka sannan ta kasa dariya, duk ilaihirn falon na cike da ya'n uwanta amma banda Mama Fatuh da Rufaidhat, dan har Yusrah kuka take na rashin Liyanar. Hydar na can gefe Amir na rungume da shi, yayin da Sultan ke shafa bayansa shi ma duk ransa babu daɗi. Ɗaki ɗaya aka ware ma Liyanar inda za'a ajiye gawan na ta a kwana da shi, da Neneh da Umma Mansura sai Ilham da Unaisah su kaɗai aka ware da zasu kwana da ita. Ganin duk mutanen falon na ta preparations na binne Liyar da safiyar ranar ya sanya shi barin wajen su Amir tare da nufar ɗakin gawar na ta. Auduga na toshe da hancinta da kunnenta ya iso wajen da take wanda Ilham ce ke kusa da ita, matsa ma sa Ilham ɗin ta yi tare da komawa bayan su da kaɗan. Mami ce ta fara yi ma sa alamar ya fita da hannu ganin kukan da yake amma ya yi mata biris tare da ɗauke kansa. ''Hey sweet heart, duk ranar da na mutu, don't cry dan Allah,secondly idan ina da aure a lokacin after 40 days ki auri mijina, thirdly, kin san dai suratul mulk is my favorite surah, and Sheik ya ce ya na sanya sassauci ga mamaci, try to read that surah for me, to cut it short I will miss you guys.'' Liyana ta ƙarashe maganar tare da yin ƙwai da chewing gum ɗin bakinta. ''Yaya da wani talk, TOH yanzu mai ya kawo zancan mutuwa?, ko santin chewing gum ɗinne har haka.?" Ilham ta faɗa ta na ƙarasa saka hular baccinta. ''Ke wasiya nake ba ki, sannan ki kula da yarana abeg.'' ta yi maganar ta na ɗaga video call ɗin Sultan. ''Toh ni ki daina min kalar wannan wasiyar ba na so.'' daga haka Ily ta yi kwanciyyarta akan gadonta hawaye na zubo ma ta. Firgigit ta dawo daga tunanin jin an dafa ta amma still muryar Liyanar take ji ta na faɗin ''Ily I'm stuck in this pot, please hurry up, ILY save me, kar ki barsu su kai ni ƙasa lokacina ya kusa.'' A zabure Ily ta tashi tare da ɗauko Al- K'ur'ani mai girma cikin muryarta mai daɗi ta fara karanta Suratul mulk....... Manage please 💎🥀 Mutuwa kan kawo canji⏩⏮️🤝 ''Ya Ubangijina ka basu daman share." Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟 Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔 *THE REGRET* PENDING AMARYA CE ✍️ JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION The Noble Writers Team. **Pending Amarya 52 countinuation.** What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩ Every ending is a new beginning 💎🥀 even if the heart disagrees.✅🌕🤝🦋 🤍 🫧 🤧 Not edited 🌟💔🥹 **** Firgigit ta dawo daga tunanin jin an dafa ta amma still muryar Liyanar take ji ta na faɗin ''Ily I'm stuck in this pot, please hurry up, ILY save me, kar ki barsu su kai ni ƙasa lokacina ya kusa.'' A zabure Ily ta tashi tare da ɗauko Al- K'ur'ani mai girma cikin muryarta mai daɗi ta fara karanta Suratul mulk....... ><><><><><>><<> Tun fitar Mama Fatuh ba ta zame ko ina ba sai ɗan ɗishe, gidan Malam Barbushe, sosai ta firgita ainun da abin da ke faruwa da Liyana, idanunta sun yi jaa kamar zasu firfito saboda firgici, number Rufaidhat take ta dailing wanda MTN suke ta nuna ma ta network busy. ''Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ni Fatuh mai na aikata hakan, Ni sam ban so a kashe ki ba Liyana, ban taɓa tsammanin hakan za ta faru ba, duk tsubbu na ban taɓa kisa ba, sannan na rasa wa zan kashe sai ya'r ƙanwata, Noooo ba zai yiwu ba.'' ta ƙarashe maganar tare da dukan stiring motar ta ƙirar 206 hawaye na zuba a idanunta a daidai lokacin da ta shawo kwanar gidan Malam Barbushe. Parker motarta ta yi wanda tun a bakin ƙofar gidan ta fara cin karo da motar Rufaidhat, kutsa kanta ta yi cikin shagon dake ƙofar wani gida, inda candles ke kunne berekete sai turarukan aljanu da babu adadi ke jere reras a kan wani ɗan tebur, sai tulu ƙananu dake ɗaure da jan ƙellaye suma da ɗan yawan su, face wani guda ɗaya dake ware akan wani abu mai kama da mangal amma babu wuta a ƙarƙashin sa. Wani ɗanyan ƙwai ne a hannun Malam Barbushe jikin ƙwan sanye da wani ƙyalle sai wani ɗan rami dake kusa da shi wanda alamu sun nuna kamar ƙwan yake ƙoƙarin sakawa aciki. Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Daga zarar na saka wannan ƙwan a cikin wannan ramin, Fatima ba zata ƙara rayuwa ba sai dai na bayan mutuwa, kin tabbatar a aikata tun da na ɗauko ruhinta daga tulun nan.'' Malamin dake sanye da wani shegen kwalli ya yi maganar ya na kafa Rufaidhat da ido. ''Malam ni kayi abin da ya dace akan yarinyar nan, bayan komai ya lafa zan dawo a naɗe min ita ma ƙanwarta, ita kuma mahaifiyyarta abin da aka saba za'a ci gaba, dan yanzu ita ce da gidan, amma ni a yanzu idan akwai gaba da mutuwa toh a shirye nake ka aika min Liyana tun da ita ma wadda ta fara kawo shawarar ita ma ta ce ko mai ya dace ayi ta bani wuƙa da nama, kai ma kuma bayan kuɗi akwai ɗayan ihsanin.'' ta ƙarashe maganar tare da kanne ido da kuma lashe leɓenta duk a lokaci ɗaya. ''Ba ki isa ba shegiyya algunguma ya'ta za ki kashe, Malam kar ka saki ka kashe Fatima, saboda babu wani laifi da ta yi, ni ban san kashe ta zata yi ba.'' ta yi maganar tare da fashewa da kuka tana mai durƙushewa a wajen. Kallon mamaki Malam Barbushe ya tsaya yiwa Mama Fatuhn sannan kuma a hankali ya ce ''Idan za ki iya bawa aljanu kanki su kwana dake na sati ɗaya, a shirye nake da na fasa abin da nake shirin aikatawa.'' Malam Barbushe ya faɗa tare da ƙafe Mama Fatuh da ido. Cikin sauri ta ce ita ta yarda ko da wata ɗaya zasu yi da ita, ita dai ba zata so a kashe wani ba, da ace kurciyya ne ta saba yiwa ya'ya'n mijinta. ''Toh haka ake so, ku ci gaba da tsula tsiyarku mutuwa ba yanzu ba ya'ya'n sheɗan'' haka ya yi ta yiwa mata kirari

Chapter 23 of 31