Share this page
key ɗinsa a hannunsa. Har ya ƙaraso wajen da take ba ta san da isowansa ba , ita dai kawai ba ta ma san mai yake damunta ba. Saitin fuskarta ya saita tare da kaɗa ma ta car key ɗin hannunsa, a firgice ta dawo hayyacinta tare da sakar ma sa murmushinta mai kyau. ''Je ki shirya, and don't keep me waiting.'' ya yi maganar a taƙaice tare da ficewa daga cikin falon. A hankali ta tashi tare da nufar saman stairs. Direct ɗakinta ta shige tare da sanya kimono akan shigarta, sannan ta ɗaura da wani babban mayafi wanda hakan ya bawa shigarta wani kalar kyau na wuce misali. Slippers ɗin ƙafarta ta bari ba ta canza ba sannan ta fito daga gidan ta na mai yiwa Salimah sallamah. A hankali take takowa har ta ƙaraso cikin motar na sa. Tayar da motar ya yi tare da barin cikin unguwar gaba ɗaya, shiru ne ya ratsa cikin motar, kowa na ta saƙe -saƙe a cikin zuciyarsa. A hankali ya kamo zara-zaran fingers ɗinta ya na kallon yadda suke a cike, farare tal dasu gwanin ban sha'awa. Jin lallausan palms ɗinsa a kan hannunta ne ya sanyata ɗagowa da sauri ta na mai kai dubanta kan sit ɗin nasa. ''Dubi fingers ɗinki kamar na horror movies, Sam ke a rayuwarki idan ba kiyi ƙazanta ba ma ba kya jin daɗi ne.?" Ya yi maganar da ɗan sauri tare da danna horn a dai-dai wani kantamemen building. Bayan mai gadi ya buɗe gate ɗin, wajen parking space ya nufa tare da yin parking ɗin motar, a babban parking space ɗin gidan dake jere reras da luxury rides. A hankali ya fito daga cikin motar, ita ma jiki duk ba ƙwari ta sauko tare da zagayowa wajen da yake tsaye. ''Kin san Allah kar ki min ƙauyanci dan naga ku mata da kun yi aure duk wayewarku ƙauyawa kuke komawa, You better behave yourself.'' Ya yi maganar tare da fara tafiya towards the building. Walking slowly ita ma ta bi bayansa trying to engage with her late courage. A hankali ta ƙaraso har ƙofar entrance ɗin da yake tsaye yake danna door bell. Bayan an buɗe musu ƙofar a hankali suka shiga cikin parlourn da sai tashin ƙamshi yake, wata ya'r budurwa ce zaune kan cushion ɗin falon cikin wasu pyjamas white color ƙafarta sanye da wani soft slippers na bacci, wanda da dukkan alamu daga bacci ta tashi. Ɗago idanunta ta yi da kyau ta kalli yarinyar dake zaune wanda ita ma a dai-dai lokacin ta ɗago ta kai dubanta wurin da suke tafe. Waro idanunta ta yi ganin Papi a gabanta wanda hakan ya sanyata cilli da wayar hannunta da gudu ta na mai rungume shi. Unexpectedly ya ji saukar mutum a jikinsa wadda sam bai lura da wanzuwar ta ba a falon. Shi ma Waro idanunsa ya yi da kyau tare da faɗin ''Ahh Marwa, kar ki karya ni mana.'' ya ƙarashe maganar tare da janyeta daga jikinsa. Murmushi wadda aka kira da Marwa ta yi tare da faɗin ''Papi na yi missing na ka sosai, for almost six years we didn't see each other, Kuma you're expecting me not to hug you.?'' ta ƙarashe maganar ta na murmushi mai nuna alamar zallar zumuɗi, tare da jan hannunsa ta zaunar da shi kan kujerar. Ita sam ba ta lura da Liyanar da take tsaye a kumbure kamar yeast ba, ta matsa daga wajensa tare da nufar hanyar kitchen domin kawo masa abin sha. Cikakken hips ɗinta ya bi da kallo tare da mayar da kansa gefe wanda hakan ya sanya idanunsa da na Liyana haɗuwa ta na tsaye wajen da ya barta. ''Ke azumin zama kike ne da ba za ki zauna ba.?" Ya yi maganar ya na ƙurawa kyakkyawar fuskarta ido. Ɗauke kanta ta yi tare da juyar da shi gefe wanda hakan ya yi dai-dai da isowar Amir cikin living ɗin, jikinsa sanye da wasu native dress masu kyaun gaske. Amir na mata magana hakan ya sanyata yin murmushi suka gaisa sannan ya yi mata insisting zama kusa da Aliyun sannan ta zauna. Tafe ta ke hannunta riƙe da wani serving tray mai kyaun gaske, ɗauke da kayan sha da na motsa baki. Sannan a hankali ta ajiye tray ɗin tare da kallon Liyana dake kusa da Papi da idon mamaki. ''Who's she Aliyu.?" Marwa ta tambayi Hydar idanunta a kan na Liyana da jin tambayar da ta ke ma Hydar ɗin ya sanyata ɗago da kanta ta kalli Marwa ɗin. HYDAR dake ta daddanna wayarsa ne ya ɗago tare da kallon Marwa kafin ya yi magana har Amir ya riga shi da faɗin ''Don't you dare create any problem, kina dai jina ko.?" Ya yi maganar tare da dailing wayar Umminsu ya na mai sanar ma ta Aliyyu da matarsa sun iso. Babu jimawa Ummi ta ƙaraso falon cikin wani simple Egyptian abaya. Sosai Ummin ta yi farincikin ganin Liyanar da Hydar. Ba su fi mintuna talatin ba Hydar ke sanar ma Ummi zasu tafi, sosai ta haɗa ma Liyana turaruka da wasu kayan sha'anin mu na mata. Marwa dai ta kasa magana dan ita a tunaninta wajenta ma Hydar ɗin ya zo. Bai ƙara kallon Marwar ba ya wuce shi da Liyanar da taƙi Sam ta haɗa ido da kowa na wajen. Suna shiga cikin motarsa ta haɗe kanta da gwiwa ta fara wani kalar kukan da ba ta san dalilinsa ba. Har cikin ƙwaƙwalwarsa yake jin kukan na ta wanda hakan ya sanya shi samun gefen titi ya yi parking ɗin motar. ''Fatima what's wrong.?" Ya yi maganar ya na ɗan kallonta, ganin ba ta ba shi amsa ba ya sanya shi ɗan kai hannunsa da niyar taɓa ta. Da sauri ta ɗago tare da buge hannunsa tare da faɗin ''Don't touch me.'' sannan ta jinginar da kanta wajen sit belt ta ci gaba da kukanta. Ganin sanyin da yake ƙoƙarin fara ma ta ba son sanya raini a tsakaninsu ne ''ya sanya shi juyo da kanta a fusace ya na mai kallon cikin idanunta. Ƙoƙarin cire hannunsa take a jikinta amma ta kasa, hakan ya sanyata sadaƙarwa tare da ƙafesa da manyan idanunta. Haɗe bakinsa ya yi da nata ya bata wani light kiss tare da mayar da ita baya kaɗan, kana ya ce ''Tell me what's going on, why are you frowning, kin san fushi ba ya miki kyau, you look like gorilla, idan kika yi kuka kuma, kama kike da ostrich, sai wuyan ki ya yi dogo.'' ya yi maganar yana gesturing da hannunsa. Ƙara fashewa ta yi da kuka sannan ta ce ''After the cin mutumci of that hug har da zagina kake, a gabana yarinyar nan ta rungumeka and you're even enjoying the hug, ''Ahhh Marwa kar ki karya ni'', haba Yaya Aliih wannan ba girmanka bane sam sam.'' ta ƙarashe maganar tare da ɗaukan tissue ta na goge hawayenta. ''Ahh okay, sakar miki fuskan da na yi har ya kai da za ki ɗinga ga ya min magana son ranki kenan, ya yi kyau.'' ya na faɗin hakan ya yiwa motarsa key tare da barin wajen. Bai ma ta magana ba ita ma ba ta masa ba har yaje ya yi shopping ɗinsa ma ba ta fito daga cikin motar ba, a cewarta kar ta ga abin da ya fi ƙarfinta a wannan karon. Sai da yamma sannan suka dawo gidan shi ma ko abincin da aka jera a dinning ba ta ci ba ta wuce saman ɗakinta duk da yunwar da yake nuƙurƙusanta. Ya na kwance a ɗakinsa ya na kallon duk wasu moves ɗinta. Seeing her naked body always turns him on, kamar magnet haka ya yi ta jan ƙafa har ya ƙaraso cikin ɗakin nata. Tsaye take a gaban madubi jikinta ɗaure da towel light color, ta na shafe jikinta da tsadaddan manta. Jin an fisge towel ɗin jikinta ne ya sanyata ɗagowa a razane tare da kallon yadda yake binta da wani kalar mayen kallo. A fusace ta fisge towel din na ta daga hannunsa haɗe da dalla ma sa harara sannan ta yi hanyar restroom ɗinta. Saurin fizgota ya yi ta faɗo jikinsa, sannan a hankali ya fara massaging jikinta. ''Ni ka daina taɓa ni, just go away, go and make your stupid love to her.'' Liyana ta yi maganar a hasale tare da ƙoƙarin fizge jikinta daga nasa wasu hawaye na zubo ma ta. ''Sorry i can explain.'' Hydar ɗin ya faɗa tare da stretching hannayensa a kan kafaɗarta ya na kallon cikin idanunta. ''Explain what?, the hug?, or that stupid Marwa.'' ta yi maganar ta na nuni da hannunta kamar Marwa na wajen. Wani kalar numfashi ya furzar wanda a take idanunsa suka yi wani kalar jaa, sosai ta tsorata da ganin yanayinsa yadda yake wani kalar huci kamar mayunwacin zaki, sannan a hankali ya soma magana '' Can you just give me a chance to talk, I can explain na faɗa miki, Marwa......... Marwa is the girl that I intended to marry few years back, na sota a lokacin, amma ta watsa min ƙasa a ido, ta zaɓi wani a maimakon ni, kuma har yanzu ina jin sonta a raina, amma ki yarda dani sam ban yi tunanin za ta yi hugging na wa ba, i didn't even see her, why am I even telling you this bayan ba yarda za ki yi ba.'' ya ƙarashe maganar ya na ƙoƙarin zama a cushion ɗin ɗakin. ''Karka zauna min a ɗaki, tun da Marwa ce wadda kake so sai ka nufi wajenta, thank God da ban ma yi accepting ɗin stupid friendship ɗinka ba.'' ta yi maganar hawaye na ɗan zuba daga idanunta. ''My Lord, ke nake so yanzu ba ita ba just understand....... Jiya banda data Wallahi kuyi haƙuri 🥹😂 Manage please 💎🥀 I'm missing something precious 💎😭 ''Ya Ubangijina ka basu daman share." Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟 Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔 *THE REGRET* *PENDING AMARYA CE *🫧💕🥰 *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*🥰💕✌️🗣️ *Page 55* Respect that lady that wants nothing from you but your loyalty and real love 💕👌🏼🫧❤️ Respect her bro 😎 🥰👌🏼😔 Note edited ✍🏻✍🏻✍🏻 ><><<><><><> My Lord, ke nake so yanzu ba ita ba just understand.” Ya yi maganar ba tare da ya san ya faďe ta ba. Jin maganar da ya faďa ne ya sanya ta ďagowa da sauri, Wanda hakan ya sanya shi saurin ďago da wani zancen daban tare da tashi daga zaunen da yake ya na mai tallab’o hab’arta tare da faďin “Liyana , idan kika natsu za ki fahimci duk abin da nake son fahimtar dake, for my pass life I make some mistakes that ni kaina idan na tuna su I feel like dying…’’ bai kai ga ķarasa maganar ba ta yi sauri ta cab’e haďe da faďin “ You make love with her right?, daman na san za’a rina, you cheated on me tun kafin ka sanni.” Ta ķarashe maganar tana mai zama a kan edge ďin gadon, hawaye na silala a kan fuskarta. “ Noo wallahi Liyana is not what you’re thinking.” Ya yi maganar tare da ķara janyota jikinsa. “ Let go of me, ni wallahi ka daina tab’a ni tun da Marwa kake so, sai ka je ka aureta daman akwai parts da dama a gidan sai ka ajiyeta.’’ Ta ķarashe maganar ta na gyara zaman towel ďinta. “ Liyana ki gane mana, wallahi she’s just a friend.” Ya yi maganar trying to get her lips on his lips. “ Incredible, first ka ce min she’s the girl da kake son aura, amma yanzu you’re telling me she’s just a friend, are you okay?.” Ta yi maganar a hasale. “ Are you insulting me?, ko kin fara shaye shaye ne?, tun da har Ina lallab’a ki kin ķi ganewa sai mu zuba dake, spoiled brat, oya hau kan gadon nan kafin na kwashe ki da maruka a wajen nan.” Ya ķarasa maganar a zafafe. Fashewa ta yi da kuka sosai sannan a hankali ta ce “ Daman na san ba sona kake ba, since from day one a haďuwar mu ba sona kake ba, Allah ka zama gatana a gidan Aliyu, daga wannan sai wancan , ni na gaji.” Ta yi maganar ta na mai goge ďan ķwallan da ya zo ma ta. Saurin jawota ya yi jikinsa tare da rungumeta sannan a hankali ya fara sakar mata kiss a goshi sannan salon labarin ya sauya. Washe garin ranar ma da mugun kwaďayin abaćha ta tashi. Ko da ta farka ba ta gansa ba cikin ďakin jiki ba ķwari ta nufi toilet tare da yin duk abin da ya dace sannan ta fara harraman sallah. Bayan ta idar da sallar ma direct kitchen ta nufa tare da kamawa Salimah aikin da ya dace sannan ta koma samanta shirya cikin wani silky gown da ya mannewa shape ďin jikinta. A hankali take saukowa daga saman stairs ďin hannunta ďaya na dafe da ķasan cikinta ya yin da ďayan hannun ke riķe da mariķin benen. A dai-dai lokacin kuma Hydar ya buďe ķofar parlourn hannunsa riķe da bottle water da hanky ya na goge gumin jikinsa. Kallon second biyar ta ma sa sannan ta ďauke kanta ta cigaba da taunan chewing gum ďinta, sannan ta tako a hankali ta zauna a kan three sitter tare da ďaura ķafafunta a saman center table. Da kallon mamaki kawai ya bita da shi tare da fara ķoķarin wucewa domin ya shirya, dan daga yau zai fara shirye - shiryen su na tafiya china. Har ya wuceta ya jiyo siririyar muryarta a kunnensa na faďin “Yaya Alih dan miķo min Apple.” Ta yi maganar ta na ďan shafa cikinta. Bai tanka ma ta ba ya wuce har zuwa inda take ya ďauki basket ďin apple ďin gabaďaya ya miķa ma ta. Har ya tafi ta kuma kiransa, ķanķance idanunsa ya yi tare da miķo ma ta remote ďin da za ta iya stretching hannunta ta ďauka, sannan ya ďauka ya miķa ma ta. Daga haka ya wuce stairs da ďan sauri ba tare da ya ķara ko kallon inda take ba. Ko da ya ķarasa ďakinsa ma banďaki ya shiga direct tare da yin wanka. Zaune take a yadda ya barta hannunta riķe da plate ďin abinci, ďayan hannunta na kan cikinta ta na shafa shi kamar jikin kyanwa. Ķarasowa ya yi cikin shigarsa na wani sky blue ďin _Senate wears_ hannunsa na sanye cikin aljihun wandonsa, sai ķafafunsa dake sanye da wasu takalma masu kyau da tsada black color, kansa kam na sanye da hula black kalar na yoruba people ďin nan. Kallonsa ta kai garesa ta ga yadda shigarsa ya masa wani kalar mugun kyau, ga wani haska shi da kayan suka yi. Take taji wani kalar wutan kishinsa na wuruwa a cikin zuciyarta. Bai bi ta kanta ba ya wuce dinning ya na mai zama, coffee kawai ya sha mai madara sannan ya ďauki car key ďinsa. “Ina za ka je.?” Ya tsinci muryarta a cikin kunnensa. A fusace ya juyo tare da faďin “ Wallahi daraja ďaya kike ci a gidan nan you better behave yourself, just because ina ďan ďaga miki ķafa kar ki saki ki ďauko hanyar raina ni, c’mon wuce ki ďauko himar ďinki ki same ni a cikin a mota.” Ya ķarasa maganar tare da ficewa daga cikin gidan. Sai da ta saki wani tsaki sannan ta wuce ďakinta tare da ďaura wani zunbulelen hijab a kan kayan jikinta. Sai da ta bawa Salimah sallahun lunch ďin da za a yi sannan ta bar living room ďin.” Tsaye yake jingine da motarsa ķirar Lexus hannunsa riķe da wayarsa Wanda alamu sun nuna chatting yake. Bai ji alamun tahowarta ba sai Jin ķwace masa waya da a ka yi. Da sauri ya ďago kansa tare da kai dubansa wajen da take tsaye, ta na kallon screen ďin wayar ta na kuma kallon inda yake tsaye. Ji take kamar ta buga wayar da ķasa ko za ta ji sanyin abin da take gani a ciki. Kamar wata mai asthma haka numfashinta ya yi ta mata barazanar ďaukewa, ganin hakan ne ya sanya Hydar saurin tallab’ota amma ta ķwace jikinta daga cikin nasa hawaye na ķoķarin fita daga idanunta. Miķa ma sa wayarsa ta yi tare da shigewa cikin motar tare da mayar da kujerarta baya ta na mai ďan kishingiďa. Fashewa ta kuma yi da kuka tare da juyar da fuskarta ta na kallon window ďin b’angarenta. Ko da ya shigo ma sai da ya ďan saci kallonta sannan ya fara tuķin motar. Sun ďan yi nisa da fara tafiyar sannan yaji saukar muryarta kamar saukar aradu. “Explain it Aliyu.” Ta faďa tare da karkato da jikinta ta na kallonsa. Bai ma ta magana ba ya cigaba da tuķinsa. Cikin wani kalar murya ta ķara faďin “ Aliyu explain what I just saw, ko na kashe abin da yake cikina tun da ka na da wani .” Ta ķarashe maganar ta na shafa cikinta hawaye na ďiga daga idanunta. Saurin take birki ya yi tare da parker motar a lokaci ďaya ya na mai juyowa tare da fuskantar Liyanar. “Please Liya zan miki bayani idan kika ba ni dama stop this childdish okay!.” Ya yi maganar tare da dafa hannunta. D’ago jajayen idanunta ta yi tare da sauke su akan kyakkyawar fuskarsa. Wani kalar ajiyar zuciya ya sauke tare da matso da kansa ya sakar ma ta wani kalar kiss a goshi sannan a hankali ya ja baya tare da fara faďin. “ Amir is my favorite Cousin, he has one sister which is Marwa, Maman Amir da Mami are sisters, and Abbha and Abbhu are also brothers from the same mom and dad. A gidansu Amir na yi kusan rabin rayuwata, hakan ya saka ni sabawa da Marwa sosai. Na so Marwa sosai ba wai soyayyar yan uwantaka ba, soyayya na aure, dan har feelings namu bamu iya b’oyewa musamman da muka fara zama teenagers. Marwa is 28 years old a yanzu, na girmeta da shekaru 5, lokacin da na gama secondary school da zan tafi China a lokacin ita kuma ta na ss one a lokacin ne muka fara sexing each other. That’s the first time that I noticed what women really feels like. Ko da naje Beijing bayan na yi one year itama tayi waec and neco ta ce dole sai an dawo da university ďinta a can Beijing. Shi kuma daman Amir Germany is his best country dan nan ya saka a first choice ďinsa. Bayan dawowan Marwa babu abin da muka maida hankali a kai sai kasancewa da junanmu. Ina level 300 a time ďin ta na level one ta samu ciki bamu lura da cikin ba sam har sai da ya bayyana. A lokacin mun shiga tashin hankali sosai mara misaltuwa. And we have no option sai dai ta haifeshi. Bayan ta haifi yarinyar da kwana ďaya yarinyar ta mutu that was 2011 . Na barta ta huta for good three months sannan muka cigaba daga inda muka tsaya. Ko da nayi final year ďina ban dawo gida ba na cigaba da masters. 2015 ne muka dawo gida gaba ďaya then muka faďawa iyayenmu muna son juna har aka fara shirye shiryen aure a tsakaninmu. Still mukan haďu da Marwa a hotel ko wani ďan ķaramin gida da Abbhu ya siya min, we always made love there. Bayan results dinmu ya fito ma I suggest na dubo mata, a lokacin aure na da ita saura one week. Ko da na dawo ban nemi naje gida ba sai gidana da yake a nasarawa. Ko da na Isa gidan Marwa na tare da wani namiji wannan shine dalilin da yasa na fasa aurenta. Ita kuma ta koma North Korea ta cigaba da karatunta, Amma dan Allah Liyana I’m very sorry I don’t know that akwai ranar da zan faďawa wani all this, yanzu hoton jaririyar ta turo min wai we have to remake our little angel again.” Ya ķarashe maganar hawaye na zuba a idanunsa. “Innalillahi wa inna ilaihir raji‘un, Hydar you’re once stucked into Haram relationships and calling me yar iska all this years, ni yanzu ya’ya’na kar wani ya zo ya musu abin da ubansu ya yiwa ya’ya’n wasu.” Ta yi maganar hawaye na zuba a idanunta. Janyota jikinsa ya yi ya na shafa bayanta tare da faďin “ Babu abin da zai faru da su please, don’t say those words again kin ji , kowa ya na da mistake a rayuwa nawa mistake ďin kenan and I’m still REGRETTING.” Sannan ya janyeta a jikinsa tare da tayar da motar suka nufi gidan Neneh dan har ķarfe shabiyu na rana ya yi. Jiki a sanyaye ya yi horn a gaban gate ďin gidan Nenehn, da ďan sauri gate man ya zo ya buďe ya na musu waving ďin hannu at same time kuma ya na miķa gaisuwarsa zuwa ga Aliyun. Aliyu just nodded his head countinue to search for inda zai parker ride ďinsa. Bayan ya parker motar ma jikinsu a sanyaye ya riķo hannunta suka ķarasa shigowa gidan Nenehn. A zaune take kamar yadda ta saba zama ta na hira da yan aikin gidanta, idanunta sanye da eyeglasses cikin shigarta na lifaya butter color da ya mata kyau sosai. Ķarasa shigowa suka yi bakinsu ďauke da sallama ko da Neneh ta ďago ta ga way’anda ke tafe sai da zuciyarta ta yi wani irin faďuwa sannan ta dake ta cigaba da magana da Fadila sannan a hankali ta ďan kallo su Liyanan tare da faďin “Baķin lahira maso gabas an iso kenan.” Ta faďa tare da cire eye glasses ďinta ta na mai dallawa Hydar harara. Shi kam bai wani kulata ba ya ďa rage tsayinsa tare da gaisheta. “ Wallahi da wannan ya’r iskar gaisuwar mai sifirin da barina ka yi a hakan ba ka gaishe ni ba, Aa toh dan da safe ake kalar wannan gaisuwar.” Neneh ta faďi hakan tare da ďan saci kallon Liyana. Tsaki Hydar ya ja tare da zama a kusa da Nenehn ya na kallon Liyana da ta kasa ďago idanunta ta kalli ko wannensu. Ganin ta yi hanyar ďakinta na gidan Nenehn ne ya sanya sa ďago kansa tare da ďan kallon Nenehn. “ Nifa yarinyar nan yanzu tsoro take bani, ooh ni Ajiddeh.” Ta ķarashe maganar ta na ďan kakkab’e rigarta. “ Neneh daman abin da ya kawo mu yau ďin ranar litinin zamu bar ķasar soo a saka mu a addua dan Allah.” Ya yi maganar ya na ďan wasa da mayafin Nenehn. “Idan ka yi wani abin kamar mai hankali, toh Allah ya tsare bara na zuba maka wani pepe soup ďin Abaji da nayi.” Ta yi maganar tare da fara ķoķarin tashi. “Nooo Neneh bar shi yanzu haka muna kan hanya ne zamu je gidan Mami Sannan mu biya gidan Ammi.” Ya yi maganar ya na mai kallon diamond wristwatch ďin dake hannunsa. Sannan ya ķara da faďin “ Neneh ki ce ta same ni a waje.” “ Kai malam shiga ka tafi da ita, haka kawai na yi ta zabura cikin dare , wallahi ko bacci take kinkimarta ka tafi da ita, hanyar lafiya a bita da shekara.” Ta yi maganar ta na mai pointing ķofar ďakin Liyanar. Cikin takunsa na isa ya ķaraso har cikin ďakinta tare da kullo ķofar. Zaune take a kan gadon ta jinginar da bayanta a fuskar gadon hannunta na rungume da pillow. Ķarasa shigowa ya yi a hankali tare da ķarasowa inda take zaune ya na mai tallab’o fuskarta. “What’s it for ?, mai sa kike saka kanki a damuwa bayan kin san mai ciki baya shiga kalar yanayin da kike ķoķarin tursasawa kanki shigarsa?.” Ya yi maganar ya na mai shafa kanta. “ Yaya Aliih .” Ta faďa a sanyaye. “ Naam.” “Did you love me.?” Ta yi maganar ta na kallon fuskarsa. Shiru ya yi yana kokwanton amsar da zai ba ta sannan a hankali ta ķara faďin “Is a Noo right, Marwa kake so, since she’s the best ta na baka kanta a duk lokacin da kaso right.?” Ta ķarasa hawaye na fita a idanunta. “Listen Liyana, ina son ki tun da har na kawo yanzu ina tare dake har affairs ya shiga tsakaninmu, just know one thing, son ki yanzu na fara kuma babu ranar dainawa, idan ki na tunanin bana ma sonki toh ki sauke wannan IOS version ďinnan a ķwaķwalwarki Okay, soo are we good to go.” Ya ķarashe maganar tare da ďage girarsa ďaya. Gyaďa kanta ta yi sannan kuma a hankali ta maida himar ďinta ta kamo hannunsa suka fito daga

Chapter 25 of 31