maganar ta na goge hawayenta.
Sai wajen ƙarfe 12 na dare Liya ta kwanta bacci ba tare da ta hau online ba.
******
Ɓangaren Yaya Alih kuwa, tun bayan da ya saka ta wuce kitchen yake ta faman karanta chat ɗinta da lily, abin na basa nishaɗi, the Lady we call Lily is soo simple buh her fake life pass her power, sometimes su kan faɗi kalan guy ɗin da suke so with some naughty talks, he can even say those girls are ƴan iska girls.
Wani voice ɗin Lily ya kunna wan da take bawa Liyana shawarar, ta ɗan ɗinga saka sexy wears, da kuma yawan yawo arround in da yake, duk abin da zai mata ta maida shi wasa, he will fall for her, idan kuma wannan hanyar bai ɓille ba sai abi ta wata hanyar.
He just smiled dan ganin wawtan ƴan matan biyu da ya gani, wai shi za'a yi seducing, yarinyar da ko shape ɗin arziki ba ta da shi, jikinta kamar na ƙwailayen shekara 14 , ita take cewa zata yi seducing ɗinsa, that girl most be in a mental health sannan ta gudo.
Tsaki yaja haɗe da faɗin ''Filthy thing.''
Kallon agogon ya yi ya na mai ganin ƙarfe 1na dare har ya wuce, hakan ya sanya sa wucewa toilet ya yi wanka haɗe da yin alwala tare da saka kayan baccinsa, sai da ya yi sallah sannan ya saka sleep mask ɗinsa ba tare da ya bi ta kan wayar ba kuma.
Arround ƙarfe 4 na asuba ya ji wayarsa ya na ringing ta shi ya yi daga barcin haɗe da ɗaga wayar dake kan bedsides ya na mai karawa a kunnensa.
Muryar Abbhi ya ji mahaifin Liyana ''Assalamu alaikum Son.''
''Wassalamu alaykum Abbhi.''
''Son sorry na tashe ku a bacci, ina daughter na take?."
''Tana nan lafiya Abbhi.''
''Okay shikenan, dama tun jiya nake ta ma ta magana a online she didn't reply, kuma i called her, almost 20 missed call she didn't respond, ko bacci na kasa yi shi ne na sanya Ilham ta bani number ka.''
Sai da ya ɗan ja tsaki ƙasa - ƙasa, sannan ya ce ''Wallahi Abbhi ta na lafiya kawai dai da yamman nan ne ba ta ji daɗin jikinta ba, shi yasa, dan har hospital muka je sai arround 10 muka dawo na dare, ta ce na gaya maka ma na ce kar a gaya dan kar a ɗaga muku hankali.''
''Ma shaa Allah, amma jikin da sauƙi ko?." ''Eh Abbhi yanzu ma bacci take da na tashe ta.''
''Just leave her ka ji, Allah ya yi albarka.''
''Amin a kwana lafiya.''
Ilham, Ammi har da Rufaidhat duk suna falon dan babu wadda ya sanya ta rintsa a cikinsu, dan different types of taught ke zuwa cikin kansa, ko ta yi hatsari ta na hospital, ko ta mutu a ɗaki ba'a sani ba.
''mtsww akan wannan ka sa muka kasa runtsa idanu, toh wallahi, Allah ya ishe min baccin da aka ƙi sani yi kuma, ƙilan ta ma club taje tayi tatil sannan ta yi dare, shi ma mijinta dake ɗan nanaye ne, ya rufa mata asiri.''
''Rufaidhat watch your tongues when it comes to my daughter, kowa yaje ya kwanta.''
Daga haka ya haura saman side ɗinsa.
Ita ma Rufy ta tashi haɗe da hararar Ammi tare da faɗin ''Babu arabi ba boko, kin ga kinje kin haifi fitina a maimakon Fatimah.''
''Ai abin sa'a ne taɓa nonon sirika, ke kici sa'a ma ki haifi ya' har ta zama fitinar.'' Ily ta faɗi hakan ta wuce nasu ɗakin dan ita ma ta san maganar akwai nauyi.
***_______****
Ɓangaren Liya kam ji take kamar za ta mutu saboda ciwon jiki ga wani sara ma ta da kanta ke yi kamar zai cire, sallar asubar ma a daddafe ta yi shi da misalin shida na safe, sosai ta ke jin rashin samun kuzari a jikinta, barimma Kwankwason ta da take ji kamar an cire ma ta spinal cord ɗinta, da ƙyar ta samu ta yi wanka da ruwan zafi sannan ta shirya cikin wani plane abaya mara kwalliya, ko gashinta ba ta busar ba ta koma kan gadon haɗe da jan bargo domin wani kalan bacci ke fuzgarta.
Ko mintuna biyu ba ta yi ba da daddaɗen baccin da ya ɗauketa ba ta ji ana ƙwanƙwasa ma ta ƙofar ɗakinta, wani ɗan guntun tsaki ta ja haɗe da faɗin ''Waye!." Ta ɗan faɗa a tsawace, wanda ke bugun ya cigaba da ƙwanƙwasawa countinuesly ba tare da ya gaji ba, "wai Salimah wannan wani kalar karuwanci ne haka da safiyar Allah kina tashin mutum daga bacci , da wani ɗan iskan bugu."
Wani knocking aka ƙara mai shegen ƙarfin da ya fi na baya, hakan ya sata tasowa afusace haɗe da murɗa handle ɗin ƙofar da ƙarfin tsiya, saboda masifar da take cinta har rufe idanuwa take, " wai ke Salimah, wannan wani kalar iskanci ne mara license da za kina min a cikin gida dan kut....."
Ba ta ƙarasa ba idanunta suka sauka kan Hydar dake tsaye da kayan gym, hannunsa riƙe da wayarta ya na ta scrolling, " countinue what you doing, ki ƙarashe zagin." Ya yi maganar ya na ɗago manyan idanunsa haɗe da sauke ma ta su akai, sosa wuyanta haɗe da sauke idanunta aƙasa dan har ƙwalla ta fara zubar ma ta a idanunta tun kafin ya fara mazgarta.
" Welcome." Ta yi maganar a sanyaye haɗe da fara wasa da fingers ɗinta, " Your Dad wants to talk to you." Ya yi maganar tare da miƙa mata wayar.
" Allah sarki Abbhina." Ta yi maganar wani ɗan guntun ƙwalla ya ƙarasa sauko ma ta, tare da fara ƙoƙarin juyawa ta shige cikin ɗakin nata.
" Ina zaki je ?."
" Ɗakina zan shiga na yi wayar."
" Tsaya anan ki yi ki miƙo min."
Kamar ta zunduma ihu haka take ji, a nan ta tsaya sannan ta yi dailing number Abbhinata, line busy Abbhin ya danna ma ta sannan cikin second biyar aka biyo kiran.
" Hello dear."
Abbin ya faɗa a sanyaye, fashewa ta yi da kuka haɗe da faɗin " Abbhina I missed you, da kowa ma gaba ɗaya, please ka ce masa ya kawo ni yau naga fuskokin ku abeg."
Ta yi maganar ta na jan majina a kiɗime Abbhin ya ce ''Is anything wrong over there?."
Satar kallon Hydar ɗin ta yi sannan ta kalli wayar dake handsfree duk conversation ɗinsu ya na jinsu, a hankali ta ce ''Nooe just wanna say hi to you guys, ina ɗan zazzaɓin dare ƴan kwanan nan.''
''Okay well, amma kwana za ki yi, muje shan ice cream, idan ƙasar za mu bari ma duk you're okay, ni dai farin cikin ki shi ne nawa daughter, you're the only one for me, soo kar ki yi zazzaɓin da zai sa Abbhi ya ji kamar ya rasa ki okay?."
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce ''Toh Abbhina, sai na zo.''
''Okay bye dear, kar ido na ya bushe fa in ta sa rai.''
''Kar ka ji komai my rock.''
Daga haka suka yi dariya gaba ɗaya, sannan ta katse wayar, dan har ga Allah ta ɗan ji sanyi a ranta.
Wani kalar harara ya watsa ma ta sannan ya amshi wayar da ta miƙo ma sa ''Ke ko kunya ba ki ji ba mahaifinki ya kira ki ba ki gaida shi ba kin fara koro bayani, ke ba ki yarda ba ubanki ne ƙawarki ko?."
''Amma wannan ai zagi ne.''
'' Shut up while I'm talking joor, kafin na buge miki bakin nan na ki mai kama da na jaɓa.'' daga haka ya zura wayarta a aljihunsa tare da ƙara faɗin ''I need custard, with fried plantain for my breakfast, now!." Daga haka ya barta a wajen baki sake.
Juyawa ta yi ta kalli wall clock ɗin ɗakin ta ga 6:06 na safe, by this time ai bacci take mai daɗin gaske a lokacin da take gidan Neneh, dan ko gidan Ammi ma ba kullum take barinta ta yi bacci ba.
''Which kind wahala be this one nah, ni yaushe na iya ma wani dama custard da za'a ce na dama.''
Ta yi maganar ta na goge gumin da ya keto ma ta, ganin ba ta da mai amsa mata ne ya sanyata nufar kitchen ɗin da har Salimah ta gyara shi dan jiya babu wani gyara shi da ta yi.
Store ɗin ta shige haɗe da ɗauko plantain ɗin ta fara ɓarewa a cikin bowl haɗe da yanka shi kalar yankan da ake masa, ruwan zafi ta ɗaura akan gas sai da ya ta fasa ta ɗauko garin custard ba tare da kwaɓa shi ya zama kamar gasara ba ta dama shi cikin ceramic bowl ɗin da suke haɗa fruits salad, wani kalar gudaji ya yi duk babu kyaun gani, kafin ta juyo daga dama custard ɗimma har plantain ɗin ya fara ƙonewa, da sauri ta kwashe haɗe da zuba su acikin plate, ganin custard ɗin ya yi wani iri ya sanyata zubar da shi haɗe da wanke bowl ɗin, gashi wayarta na hannunsa balle ta kira Ily, jin muryarsa kamar ya na waya ya sanyata saurin zuba custard ɗin haɗe da zuba masa ruwan sanyi sannan ta yi sauri ta dama duk da ya yi ruwa bai yi wani kaurin na muzo mu gani ba.
Wani jar ta gani jere guda biyu a waje ɗaya hannunta kawai ta kai ga na farko ba tare da ta wani duba menene a ciki ba ta juye haɗe da stiring ɗinsa ba tare da kuma ta damu da taji taste ɗinsa ba.
***_____***
Zaune yake akan kujerar dinning ya na kallon laptop ɗinsa yadda ya saba duba factory ɗinsa na China, hannunsa na dama kuwa na manne da kunnansa ya na magana a waya, yadda yake amsa wayar ne ya bata tabbacin cewa Amir ne ke ma sa magana kuma kusan ma akanta ne idan za ta iya zama judgmental, wani kalar murmushi ya saki tare da faɗin ''Amir ba na son ƙorafi, I've made it clearly to you babu inda zanje da wannan yarinyar, yadda ba ta jin magana, ta zo ta yi abin da zai sa a koro ni daga can, Amir ka riƙe advice naka please.''
Daga haka ya kashe wayar, haɗe da kulle laptop ɗin, A hankali ta tako har inda yake tare da ajiye tray ɗin akan dinning ɗin, wani banzan kallo ya wurga ma ta dan yanzu wani kalar tsanarta ya ji ya na masa yawo a kogon zuciya.
Bayan ta ajiye breakfast ɗin a hankali ya ɗauki tea spoon haɗe da shan custard ɗin, a million ya furzar haɗe ƙafeta da wani shegen kallo ''Dan ubanki uban mai ya kawo gishiri cikin wannan custard ɗin!." Ya faɗa a tsawace shiru ta yi ƙwalla na zuba a idanunta a zafafe ya ƙara faɗin ''Ba magana nake miki ba."
Muryarta na shaking ta ce ''Dan Allah ka yi haƙuri wallahi ban iya ba Salimah ce ke yin komai ba ni ba.'' ta ƙarashe maganar idanunta na zubdar da hawaye.
''Salimah!.'' Salimah ce ta fito jikinta na ɓari dan tun tuni ta na jikin ƙofa saboda wani kalar tausayin Liya da take ji, so take ta faki idonsa ta shiga kitchen ɗin amma ta kasa saboda ya na zaune a falon.( TOH Salimah mun ji uzurinki koma gefe 🥱😵💫).
Kallon Salimah ya yi sannan ya cillo ma ta dubu goman da yake aljihunsa tare da faɗin ''Ki koma gidan Neneh za ta cigaba da aikace-aikacen gidan nan, ko kuma shirya kayan ki kawai zan sauke ki.''
''Toh yaya.'' Salimah ta faɗa haɗe da wucewa cikin ɗakin domin kwashe kayanta.
Wayarsa ya ɗauko tare da kiran mutane kusan huɗu, cikin ƙanƙanin lokaci wani dattijo da samari uku suka ƙaraso cikin falon, ''Alhaji barka da safiya.'' suka haɗa baki wurin faɗa.
Kallon ko wannensu ya yi sannan ya ce ''Barka dai Baba, daman ina son na sallame ku ne na ƴan watanni amma akowani wata za'a saka muku kuɗin aikin ku, za ku iya tafiya.''
''Toh mun gode Alhaji Allah ya ƙara buɗi, ɗan shuwa jikan shuwa.''
Bayan sun fita juyowa ya yi ya ga har a lokacin kuka take ''From today babu baccin banza a cikin gidan nan, girki, buɗe gate, bawa flowers ruwa, wanki, guga, komai ke za ki yi, tun da aure kika zo yi ba hutu ba, am I clear?."
Bai jira amsar ta ba ya yi ma ta pointing kan kujerar dinning ɗin a sanyaye ta zaune sannan ya turo ma ta tray ɗin abincin tare da faɗin ''Cinye abincin nan, tun da ba akuya aka kawo miki ba da za ki kawo min kalar wannan abincin.''
A hankali take cin abincin ba tare da ta ɗago ta kalli fuskar shi ba, cokalin custard ɗin da take sha ne ya faɗi aƙasan tiles wanda hakan ya sa ya ba ta wani kalar dirty slap, wanda sai da jinta ya ɗauke na wucen gadi.
A daddafe ta gama cin abincin da ya tilasta ma ta, sannan ta shige banɗaki ta yi wanka haɗe da shiryawa cikin wani abaya, shiru shiru ta ji har kusan ƙarfe shida na yamma ba taji ya ce ta fito ta tafi gidan Ammin ba , sannan kuma bai ba ta wayarta ba.
***________****
Tsaye ta ke a jikin ƙarfen balcony ɗin dake compound jikinta sanye yake da abaya ɗin jikinta tun na ɗazu, tun ƙarfe sha biyu ya fita daga gidan domin kai Salimah gidan Neneh, har yanzu bai dawo ba, horn ɗin da taji ne ya sanya ta firgita, dan wani kalar tsoronsa da tsoron gidan ne suka ɗirar ma ta arai, ita kaɗai ƙwal kamar mayya.
Da ɗan sauri taje ta buɗe ƙofar ta kusa mintuna uku ta na buɗe shi saboda nauyinsa da yawa yake, da mugun gudu ya shigo cikin gidan, goge gumin da ya zubo ma ta tayi haɗe da kulle gate ɗin da ƙyar sannan ta fuskanci ƙofar shiga falon dan shi ya jima da shiga cikin gidan.
Tsaye ta tadda shi ya na haska falon da wayar hannunsa ''Ni kike jira na kunna miki inverter ko ba ki san aikin ki ba?."
Ya yi maganar ya na ɗan takowa wajen da take, ''Dan girman salatin Annabi kar ka dake ni.'' ta yi maganar ta na ɗan ja da baya zuwa wajen stairs, wani kalar tsantsi ne ya kwasheta kanta ya buge da benen farko wanda hakan ya sanyata sakin wani kalar razananniyyar ƙara........
*Durrah Hydar.*✍️
"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."
*THE REGRET.*
Pending Amarya ce ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION.
THE NOBLE WRITER'S TEAM 💎
*** Pending Amarya 39***
Tsaye ta tadda shi ya na haska falon da wayar hannunsa ''Ni kike jira na kunna miki inverter ko ba ki san aikin ki ba?."
Ya yi maganar ya na ɗan takowa wajen da take, ''Dan girman salatin Annabi kar ka dake ni.'' ta yi maganar ta na ɗan ja da baya zuwa wajen stairs, wani kalar sulɓi ne ya kwasheta kanta ya buge da benen farko wanda hakan ya sanyata sakin wani kalar razananniyyar ƙara....
Takowa ya yi har wajen da take a yashe, tare da zuba hannayensa cikin aljihu, a hankali ya tsugunna a wajen tare da faɗin ''I don't care about kin faɗi ko kin ji ciwo, all I know is that sai kin canza change over, and right now not later.'' ya ƙarashe maganar haɗe da hankaɗe ta da ƙafafunsa ya na mai ball da ita.
Wani wahallalen kuka ta saki haɗe da dafe kanta tare da yunƙurawa ta tashi domin zuwa backyard ta kunna solar.
A daddafe ta kunna solar sannan ta dawo cikin falon, inda Allah ya ceceta ma kanta kumburi kaɗai ya yi ba ta ji ciwo sosai ba, direct kitchen ta nufa tare da ɗora tukunya dan har ga Allah ba ta san mai za ta dafa ba, kashe gas ɗin ta yi tunawa da conflakes da ta yi.
Komai na conflakes ɗin da za'a iya amfani da shi wurin shan shi ta zuba a resin tray, haɗe da jera shi akan dinning table ɗin.
Wanda ta jiƙa ma kasa sha ta yi dan ba ta wani jin yunwa.
Hydar kam ya na shiga ɗakinsa ruwa kawai ya watsa tare da jona phones ɗinsa a charge, sallolinsa ma acikin ɗakin ya yi su dan a lokacin har an fara kiran sallahr isha.
Wayarsa ce ta fara ringing wanda hakan ya sa shi sakin wani ɗan gajeren tsaki dan ya tabbatar ƙila Abbhi ne, dan wayar Liyanar na hannunsa har yanzu, tun ɗazu Abbhin yake kiran wayar daga ƙarshe ya kasheta gaba ɗaya.
Ko da ya ɗauko wayar nasa ma Amir ne ke kiransa hakan ya sa shi ɗaga wayar a hankali, tare da faɗin ''Assalamu alaikum, Amir what's wrong ka yi min booking ɗin?.''
''Wassalamu alaykum, Man an ɗan samu matsala babu jirgin da zai je China direct.''
''Fucked up, yanzu sai yaushe?, ɗaga meeting ɗin zan yi kenan?."
''I think soo Man, ka ɗaga meeting ɗin, wannan ACn da ka turo min ita ake son ka ƙera a companyn ka?."
Sai da Hydar ya ɗan ja numfashi sannan ya ce ''Yeah, na ma rasa wani suna zan saka mi shi.''
Dariya Amir ya yi sannan ya ce ''Toh ka saka sunan matarka ma na .'' ya yi maganar ya na gimtse dariyarsa.
A take muryarsa ta canza cikin wani kalar salon rashin mutumci kalar na Hydar ya ce ''Soo ka na son Ac ɗin ya ƙi samun karɓuwa ko ajanye offer ɗin Almost 70 billion dollars, kar ka sa raina ya ɓace da daren nan please.'' daga haka ya kashe wayarsa tare da jan duvet ya na mai kwanciyarsa.
Jin shiru bai fito bane ya sanyata shigiɗa akan kujerar parlourn tare da duƙunƙune jikinta wuri ɗaya, dan har a lokacin ba ta san asuba ta yi ba. Cikin shirinsa na masallaci ya kalleta kan kujera takure waje ɗaya ta na baccinta hankali kwance, direct kitchen ya wuce haɗe da buɗe fridge tare da ɗaukan goran ruwa mai sanyi, da sauri ya ɓalle bottle ɗin haɗe da juye ma ta shi gaba ɗaya a fuska wani kalar wahallalen ajiyar zuciya ta sauke, haɗe da tashi a zabure ta na mitsitsika ido.
Da ga haka ya fice i zuwa masallacin, ta shi ta yi haɗe da nufar stairs ta na mai nufar ɗakinta.
Sai da ta yi wanka haɗe da brush sannan ta yi sallar jikinta duk agajiye.
Hijabyn jikinta ta zare tare da saukowa ta na mai nufar kitchen ɗin, chips kawai ta soya da ƙwai sannan ta ɗaura coffee a coffee mixer, tare da ɗaukan flask ta tari ruwan zafi a dispenser.
Ƙarar shigowarsa ta ji wanda hakan ya tabbatar ma ta da ya dawo daga masjid, hakan ya sanya ta ɗan gyara kitchen ɗin dan ta san zai shigo ɗaukan coffee.
Kayan da ta jera a tray ta ɗauko tare da nufar dinning room ɗin ta na kallon cikin tray ɗin da ta ga wani ƙwaro na yawo aciki, karo ta ci da shi da yake kallon waya wanda alamu sun nuna kallon wasu abubuwan yake masu muhimmanci acikin wayar.
Abincin dake cikin tray ɗin ne gaba ɗaya suka zube ajikinsa wayarsa dake hannunsa kuma ya yi flat a ƙasa.
''Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun, am dead, wallahi tallahi billahillaxi la ila ha illahuwar - rahmanu i didn't do it intentionally, ka ji rantsuwar Musulunci kenan.''
Ta yi maganar hawaye na zuba a idanunta. ''Thank God kin san kuɗin wayar da kika fasa right?.'' gyaɗa kanta ta yi sannan a hankali ta ce ''Is 4 million plus.''
Murmusawa ya yi tare da faɗin ''Smart girl, oya miƙo min wayata before I turn your face to blue black.'' ya yi maganar a tsawace.
Durƙusawa ta yi da niyyar ɗaukan wayar wanda hakan ya sata jin saukan wani kafirin duka a bayanta.
Runtse idanunta ta yi tare da ƙarasa ɗaukan wayar tare da miƙo ma sa idanunta na zubda hawaye.
Sai da Aliyu ya sa ta gyara gidan ga ba ɗaya tsaf sannan ta huta, still kuma he didn't gave her, her phone, duk hakan ya sata shiga wani hali.
***_____***
Da sassafe kamar yadda ta ɗan saba a kwanakin nan ta tashi tare da yin iya abin da za ta iya, glass cleaner da mooper da kuma towel a hannunta ta nufi kan dinning domin goge area ɗin .
She was surprised to see her phone akan dinning table and also shocked at the same time, ''Ahh wannan halittan ya manta wayar yau anan kenan, ɗan ƙwal uba.'' ta iddasa maganar haɗe da ajiye tarkacen dake hannunta ta na mai ɗaukan wayar, screen ɗin wayar a kunne yake picture ɗinta da Ammi da Ilham da kuma Abbhi ne agaban wayar,wanda da alama dai hoton last year eid ne.
Kallon wayar ta yi haɗe da faɗin ''One big family." Ƙwalla na ɗan zubo mata.
''Uban mai kike da wayar hannunki?." Wani kalar bugawa da zuciyarta ta yi sai da ta tsorata, wani tsawa da ya daka ma ta sai da wayar hannunta ta faɗi aƙasa.
''Hasbunallahu wa ni'imal wakil, my phone, innalillahi wa inna ilaihir rajiun.'' ta iddasa maganar ta na fashewa da kuka.
''Idan ba ki rufe min baki ba za ki gane shayi ruwa ne.''
Da sauri ta yi shiru haɗe da cigaba da goge dinning ɗin ta na kallon wayarta dake yashe a ƙasa.
Sai da ta gama gyara gidan duk da bai wani gyaru ba, sai arround 3 i clock sannan ta ci abinci shi ma abincin bai ma ta wani daɗi ba, noodles ne sai hollandia strawberry da ta haɗa da shi.
***_____***
Sosai ya canza turarensa ya mai da shi shumuk luxury scent ba Valentino da Baccarat ko Georgia armani ba, dan sosai shumukh ya take su wajen tsada, mazubin sa ma abin kallo ne.
Shi da Amir ne suka je shopping sai da suka biya ta gidansu Liyana da Neneh har gidan Mami da kullum take cigiyar Liyana.
Bayan sun fito daga gidan Mami ma sai da ya biya restaurant ya yi take away ɗin fried rice and chicken sannan ya sauke Amir shi kuma ya zaryo gidansa.
Ta na daga cikin falo a zaune ta ji an yi horn, da gudu ta tashi haɗe da saka slippers ɗinta tare da buɗe masa huge gate ɗin.
Bayan ya yi parking motar na sa a wajen flowers ya tsaya ya na ƙare musu kallo, da ƙyar ta ƙarasa rufe gate ɗin da ƙirjinta ke amsa nauyinsa sannan ta wuce shi da niyar shiga cikin gidan.
''Ke dan ubanki come back here.'' dawowa ta yi baya a hankali haɗe da faɗin ''Gani.''
Sai da ya mata kallon some seconds sannan ya ce ''Uban wa kika barwa watering flowers ɗin gidan nan, abi na me you dey wait make i remind you tun da agidan ubanki ba ki saba ba?."
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi ƙwalla na ziraro ma ta cikin sassanyar muryarta mai haɗe da kuka ta ce '' I'm sorry.''
Da ga haka ta nufi backyard domin ɗauko abin da za ta yi watering flowers ɗin.....
Manage please b yawa🤗
*THE REGRET.*
Pending Amarya ce ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION.
THE NOBLE WRITER'S TEAM 💎
*** Pending Amarya 40***
''Ke dan ubanki come back here.'' dawowa ta yi baya a hankali haɗe da faɗin ''Gani.''
Sai da ya mata kallon some seconds sannan ya ce ''Uban wa kika barwa watering flowers ɗin gidan nan, abi na me you dey wait make i remind you tun da agidan ubanki ba ki saba ba?."
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi ƙwalla na ziraro ma ta cikin sassanyar muryarta mai haɗe da kuka ta ce '' I'm sorry.''
Da ga haka ta nufi backyard domin ɗauko abin da za ta yi watering flowers ɗin.....
Da ga haka ta nufi backyard domin ɗauko abin da za ta yi watering flowers ɗin.
Direct ɗakin shi ya nufa ya na mai shirya turarukkansa akan standing mirror ɗin.
** After 3 weeks**
Zaune take akan kujera ta na kallon TV ɗin ɗakin amma sam hankalinta ba ya kan kallon da take, yau sati uku kenan da fashewar wayarta da har yau bai ba ta ba, ga rashin chatting da Abbhinta da su Rashidat da ke ta ɗawainiyya da ita.
Tunanin kalar halin da Abbhi zai shiga idan ya kira ya ji wayarta a kashe ta ɗinga yi, duk ta rasa abin da ke ma ta daɗi, yaushe rabonta da ta ci abinci mai nauyi yau kusan wata biyu kenan tun barin Salimah daga gidan nan.
Cikin takunsa na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 31