Share this page
ya fita cikin su, ko da ta shigo ɗin ma, cacar baki Rufaidhat da Ammi suke. "Shegiyya farar karuwa, ai ke ɗin a tafin hannuna kike, uban waye bai san ba ki shigo gidanki da budurcinki ba, ko an gayamiki banda labari akai, shashasha kawai, kuma ƴar ta ki da kike ikirari da kin aurar, ina ne bata karaɗe ba hotels kala kala babu wanda bata sani b......." Rufaidhat ba ta kai ga ƙarasawa ba Liya ta sauke mata mari zafafa guda biyu tare da ranƙwashi mai rai da lafiya. "Idan kina tunanin mahaifiyyata ta na a tafin hannunki ni à ina kike tunanin zan saki, ƴar balaja'u." "Ke kuma Ammi mai na biye mata bayan kin san ƴar ƙwayace, huh." "Ke kuma Ilham mai kika tsaya yi, farar kura." Liyana ta faɗa tana ƙafe Ily da ido. "Liya Ammi ta ce nai shiru faa." Ta faɗa ta na ƙara sakin kuka. "Ina Abbhina." "Ya na ɗakinsa ciwon kai ke damunsa, since day before yesterday." "What ?! and non of you call me, ku gaya min kuma mun yi waya da shi jiya bai gaya min ba." Rufaidhat dake tsaye wajen stairs Liya ta hankaɗe tare da faɗin " Stupid hag." Da gudu ta shige corridor ɗin ɗakin Abbhi wanda yanzu ta kai four months ba ta shigo shi ba tun ranar da ta bar gidan. Ya na zaune akan Sofan bedroom ɗinsa yayi stretching ƙafarsa akan center table ya na shan lemon juice ta shigo ɗakin. "Amarya." Abbhin ya faɗa tare da buɗe hannunsa da nufin tayi hug nasa. Da gudu ta ƙaraso tare da rungumarsa nasa tana ƙarewa fuskarsa kallo. "Amma ba kai kama da mai rashin lafiya ba." "Rabu da su sun takura min da kawo ƙara ne wallahi, that's why kawai nace musu hakan na ɗan huta." "Abbihhhhh." "Naaaaam." Ya kwaikwayeta. "Buh ka sani cikin damuwa manaaaa." "It's okay dear Am sorry dear, and yanzu ina za ki je ?." "Am planning naje school akwai test yau buh na ma fasa, i wanna spend my time here with you." Ta na faɗin haka tayi kwanciyarta anan kan coach ɗin. "Ko za ki shirya muje Domino's Pizza?." "Banda kaya ai anan Abbhina." "Ina ta so daman ranar da zan zo gidanki na ba ki kayan da na siya miki amma tun da kin zo sai ki saka shi ai, ragowan kya tafi dasu." "I love you wallahi Babana." "Love you more." Daga haka ya miƙe ya buɗe tankamemen press ɗinsa tare da ɗauko wani leda mai kyau. "Na san palazzo trousers ne favorite dress ɗinki soo I picked them for you." Ya faɗa tare da zaro wasu tsala -tsalan palazzo trousers masu kyaun gaske. Daga sama har ƙasan su wani kalar beeds ne ajikin su masu walƙiya sosai daga ganin kayan za ka san kuɗi sun yi kuka . "Abbhina you're the best ever, Allah ya ƙara buɗi." Bata jira amsar sa ba ta shige toilet ɗinsa dake ƙamshi mai daɗin gaske haɗe da canza shigarta zuwa kayan da Abbhin ya siya mata. Ko da ta fito sai yabon kyaunta yake. Take taji duk wani damuwarta na ganin Sultan a gidanta ya kau. In less than ten minutes ta shirya cikin kayan da suka mata matsiyacin kyau. Already daman slippers ne aƙafarta and her bag to is the same color with her slippers. A hankali suka sauko shima Abbhi ya mayar da rigarsa na kaftan yadin nasa mai mugun kyau da tsada, sai car key ɗinsa dake hannunsa ta benz ɗinsa, hannunta acikin na Abbinta. Ilham dai ita kam abaya ce ajikinta tana lunch tana daddanna wayarta dan chatting take da Sultan da sai magana yake mata akan changes ɗin Liyana da kuma ganinta da yayi yau buh he didn't tell her a inda ya ganta. Ammi data fito da wani bowl ɗin fruit salad ce ta ce "Yallabai the lunch is ready." "Noo eatry muka nufa, yau ɗin, since babu wadda ta damu dani a cikin ku." Sidda kanta kawai Ammi ta yi sannan ta ce " Gimbiya mai ya kawo ki yau ɗin." Fuska ta yi kamar mai son yin kuka sannan ta ce "nazo naga Abbhina ne faa Ammi." "Is alright Allah ya kyauta ya kuma tsare." "Am sorry Ammi ke nazo gani faa." "Nooo da maganar farko ake amfani ai." "Nope Ammi an wuce generation ɗin fa." Kafin ta gama surutan ta har Abbhi ya wuce ya fita. Rufaidhat ce ta zauna a living room ɗin tare da faɗin "su fanko har za'a tafi kenan, har an gama barbaɗin." Cikin wani kalar ɓacin rai Liya ta ce "Naji idan ma fankon da gaske ne ba ubana ne ya maida ni ba hakan wasu kuma faaa?." Ily ta caɓe da faɗin "karuwan gidane idan an gama da iya sai adawo kansu." Wani kalar tsawa Ammi ta daka musu. Taɓe baki Liya tayi tare da faɗin " wallahi Ammi shiyasa ta rainaki, dama nice matar Abbhina da kin daɗe da fita a gidan nan tsohuwar bazawwara." Ajiye bowl ɗin Ammi ta yi tare da cire slippers ɗinta ta biyo Liyana, ai da gudu ta arce ta bar falon haɗe da ƙwalawa Abbihnta kira. Rufaidhat kuwa ta cika famm kamar zata fashe. Sannan idanunta suka kawo wani ƙwalla mai mugun zafi tana dana sanin, sanin Nabil da ƴaƴansa da tayi. Dama zamanta tayi a gidanta su cigaba da damawa da ita da Sufyan ɗinta. Da gudu ta haura sama. Koda ta shiga motar Abbih numfashi kawai take da sauri haɗe da dariya. "Wallahi Abbhi matanka ba zasu kashe ni ba, muyi sauri ka ajiye ni a gidana." Ta faɗa tare da rufe ƙofar motar. A hanya ma kawai labarai suke ta yi, a hankali ta ce " Abbih ina ma muka nufa?." "Wani sabon wurin shakatawa ne." Bata bashi amsa ba ta cigaba da jin waƙar ta da ta jona da ear plugs ɗinta sabon waƙan da Davido ya saki _Un Available _. Basu wani jima ba suka ƙaraso Hydar's palace and garden, dake a titin hanyar minjibir wurin ya mugun tafiya da tunaninta wurine dake cike da shuke shuke na ban mamaki na flowers mabanbanta tun daga gate tulip flowers ke shinfiɗe a ƙasa ga mutane nata basu ruwa. The place is damn beautiful. Kallon Abbhi ta yi tare da faɗin "i love it, promise me every friday za ka ɗinga kawo ni nan please." "Pinky promise dear." Fitowa suka yi daga motan bayan ya faka motar. Wurin ƙarshe ne wurin kyau amma gaba ɗaya wurin is artificial, komai constructing nasa aka yi. "Kaɗan kika gani idan kinje VIP ɗin za ki riƙe baki." "Abbhi dan Allah?, toh kai ya aka yi ka san nan ma bayan kana office kullum ko dai za'a wa Ammi ta uku?." ta faɗa tare da turo ɗan ƙaramin full lip ɗinta dake shafe da lipstick. " Babyn Abbhi kina da matsala, oya let's goo." Haka ta riƙe hannunsa suka wuce cikin wurin da ake biyan kuɗin. Bayan sun shigo reception ɗin ma ce musu aka yi the boss is arround, ba zasu iya shiga VIP ɗin ba, indai kuma suna don shiga sai dai 500k each person. A haka ta matsawa Abbhinata sai da ya biya suka shiga wurin da idan ka gansa zaka manta Nigeria ne. Kana ganin yanayin wurin ka san all the way from out side aka masa wannan aikin. Dan wani kalan rafi aka yi a wurin sannan aka zuba yashin sahara, da duk idan kaga wurin za kayi tunanin ocean ne sai dai ocean is big and wider than what she's seeing right now. Komai na wurin looks classy ga bishiyoyin kwakwa da suke a wurin just saboda passion. She was like woow, wayarta ta ɗauko ta fara sakin reels in less than a minute ta samu like fiye da 1million because ta riga da ta tafi viral in everything akan social media sai dai fa ita bata facebook da tiktok. Ko ina yayi kyau ga wasu boats dake ta yawo kan ruwan because sai da akayi ramin almost 20 kilometer sannan aka yi constructing rafin. Ga wasu kujeru a wurin na shakatawa, turawa ɗaiɗaiku ne a wurin saboda is a VIP place sannan aNƙara zuƙa masa kuɗi duba da boss na nan. Ɓangaren Mr. Ali namu kuwa tun safen da ya kira Amir bayan ya ɗaga suka yi magana ya kira Sultan domin ya duba masa abubuwan dan yana da buƙatar fresh air. Bayan Sultan ɗin ma yazo jogana sa yayi da laptop ɗinsa suka fara meeting ɗin daya kamata da CEO ɗin Adafar Ventures Adam Ayan Muhammad Ali Alkhaizaran. Combat ne ajikinsa sai wani white designer polo shirt sai ya saka Gucci slippers masu kyau haɗe da ɗaukan key ɗinsa suka wuce a motarsa. Wurin shakatawar sa ya nufa domin ya samu bacci, dan baccin hotel da ban yake da na gida dan da akwai hotel a wurin shakatawar nasa. Arround 10 O'clock ya ƙarasa cikin ƙantamemen luxury Joint ɗin nasa wanda daga gani kasan an narka wasu mahaukatan kuɗi a wurin gina shi. Direct lift ya bi ya shiga dan idan yace ta ƙofofi zai bi QR code zasu masa wahalan snapping ga thumbprint ma zai ba shi wahala. Danna bell ɗin da zai sada shi da réception ya yi. Wanda a take suka kawo masa breakfast ɗinsa. A ɗakin ma Amir cika mi shi kunne ya yi da surutai berekete babu kai da ƙafa, da dabara ya sa shi yaje wurin rafin domin ya shiga boat ya za ga wurare, ya yi race da polo with so many games dai arround 2 O clock zai sauko, dake Amir ɗan sharholiyya ne babu ruwan shi dan shi he's an extrovert kowa ba shi ne. A take ya amince ya bar ɗakin nasa. Bayan fitar Amir ɗinma wani bacci mai mugun daɗi ya wuce da shi, wanda kuma babu wani ɓata time ya basa haɗin kai. Liyana kam daman tun da suka zo da ta ga one hour ne ya cisu zuwa nan tace masa after four zasu koma gida. Arround one thirty ta fara jin yunwa ga Abbhi ya na can gefen rafin ya na amsa waya da business partners dan sabon engine na atamfa yake son siya. Ga shi babu wani waiter dake wurin balle ta kira a kawo mata strawberry smoothie ta sha. A hankali ta tashi daga kan kujerar dake wurin tare da fara tafiya a hankali towards Abbhi at the same time pressing her phone in a comfortable way. Bigewa tayi da mutum ta yi baya kamar zata faɗi sannan ta dawo ta tsaya da ƙafafunta. Sai da ya ƙarewa jikinta kallo, sannan ya kalli fuskarta dake sanye da farin glasses. Ganin wanda ke tsaye gabanta ya mugun ɗaga mata hankali, amma sosai ta dake haɗe da murguɗa bakinta tare da faɗin "kai kullum duk inda zan je sai ka bi ni are you for real?." Ta faɗa tare da ƙara murkuɗa masa bakin. Shanyayyun idanunsa dake nuna alamun basu daɗe da tashi a barci ba ya zuba mata su sosai wanda hakan ya sa cikin ta ya yi wani mugun kaɗawa............" "Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need." Allah ya haɗa mu ranar monday mu fara Posting steadily.😪 *THE REGRET* (Dana sani). ~PENDING AMARYA CE~ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪 The Noble Writters 🦚 Dedication is Our Strong 🤝 _ Pending Amarya 29_ Ganin wanda ke tsaye gabanta ya mugun ɗaga mata hankali, amma sosai ta dake haɗe da murguɗa bakinta tare da faɗin "kai kullum duk inda zan je sai ka bi ni ? are you for real?." Ta faɗa tare da ƙara murkuɗa masa bakin. Shanyayyun idanunsa dake nuna alamun basu daɗe da tashi a barci ba ya zuba mata su sosai wanda hakan ya sa cikin ta ya yi wani mugun kaɗawa............" A hankali ya buɗe bakinsa ya ce "I will be the one asking you this spoiled brat, duk inda naje kina sane da ni da rayuwata, kina yawan satar kallona, this should be the last time da zan ganki arround me, if not." Bai ƙarasa ba kawai ya yi ƙwafa. "Ƙarasa karta kashe ka." " I don't have time ga wa'yannan kalan matan, for the last time don't you dare show your face again, get lost!." Sakin baki ta yi dalala har ya ɓacewa ganinta bata sani ba, ga baƙin cikin ɓakar maganar da ya sakar mata, wai wa'yannan matan?. Karuwa fa kenan yake nufi. "Kam balasti." Ta faɗa a fili kafin tayi wani harraman binsa har Abbhi ya iso inda take. "Abbhi yunwa." "Da ƙwandala ake cin abinci fa anan." "Abbhi manaaa, Allah yunwa nake ji ba wasa nake ba." " Sorry babyn Abbhi." daga haka yaja hannunta suka ƙarasa wajen wurin order abinci kafin suka fara ci. Sai da ta shiga ruwa suka yi yawo sosai, sai ƙarfe goma sannan ta nufo hanyar gidanta dan sai da Abbhi ya ajiyeta a gidansu ta ɗauko kayan da Abbhin ya siya mata da motarta, shima Ammi kamar ta kasheta da faɗa. Da wani mugun speed take sharara gudu a saman titin da babu kowa sosai sai manyan motoci haka tayi ta overtaking mutane. Wani kalar birki taci sanadiyyar karon da suka yi da wani mota ƙirar Lexus LC 500. Wani kalar matsiyacin duka ta kaiwa sitiyarin motar tare da daka wata uwar tsaki ta fito daga cikin motar ta. Babu mutane sosai a unguwar, a hankali ta duba motarta tare da leƙa wanda suka ci karo. Yana zaune ahakimce ya na ma waya. Ganin hakan ne ya sanya ta komawa cikin motarta da niyar tada motarta ta ƙara gaba. Still motar a buɗe ta barta dan sai ta gama tada mota sannan take kulle ƙofar ita haka tsarin ta yake. "Kamar saukar aradu taji muryar mutum a kunnenta unexpectedly wanda saboda hakan ya sanya ta firgita a take dan Liyana akwai tsoro. "Can't you say sorry?." Dake babu wani haske a motar yasa bata ga fuskar ba buh the voice sounds familiar amma wannan ya na da sanyi not wanda ta saba jin sa a fusace. A hankali ta fito daga cikin motar wanda hakan ya ɗan sa shi ya ɗan ja baya. A nitse ta fara magana " You will be the one to kace min sorry ai, saboda kana waya kana tuƙi which is not allowed." Ta faɗa tare da fara ƙoƙarin komawa cikin motarta. "Wayarsa daya mayar gaban aljihunsa tun lokacin da ya gama waya ne ya fara kawo flash alamun kira. Wanda hakan ya hasko masa fuskar wadda take cikin motar. Sai da ya ɗan ja baya kaɗan sannan ya ce " at this time daman sai mata Irinku ke shawagi a titi." "Whaaaat! How dare you?." Ta faɗa tare da cire glasses ɗin ta. "Don't you dare ki yi min magana son ranki." A hankali tayi shiru tare da mayar da hankalinta kan gaban motarta tana kallon titin da babu kowa, sannan a hankali ta ƙara faɗin " ja gefe zan kulle motana." Tsaye yayi bai motsa ba awurin. "What's all this wai, ko kaine ka siya min motar?!." Ta faɗa a hasale. Ja yayi da baya yana ƙare mata kallo da kyau wani kalar matsiyacin kallo ta masa duk da duhun haɗe da tsaki sannan ta tayar da motar ta wuce. Tun bayan da suka rabu da ita a joint ɗinsa sai da suka yi yawo sosai da Amir sannan ya kamo hanyarsa na dawowa gida domin ya huta, still a hanyarsa sai da ya haɗu da wannan shaiɗaniyyar yarinyar. Har yanzu mamakin kalar iyayen da suka yi raising ɗinta yake. Gaskiya sun yi sakaci da yawa. To eleven ace ƴar ki bata dawo ba kuma ba zaki iya neman inda taje ba. Dubi yadda take ta'amali da tsofaffi duk sugar daddies that girl is a fitina to society gaskiya. Sai tsaki yake ta jaa, dan Hydar na da mita sosai. Murza motarsa ya yi ya cigaba da tafiya har ya ƙaraso gidan. Liyana kam ranta fess she didn't even care about rashin ɗan idon data masa duk da bai bata fuskar hakan ba. Bayan ta dawo ɗinma sai da taci abinci ta yi wanka ta sauko parlour cikin shigarta na pyjamas wandon ya tsaya mata a dai-dai gwiwa. Rigar ta lafe luf - luf a jikinta. Duk da uban daren da ake tsalawa sai da ta kunna waƙa a TV haɗe da ƙure volume. Ga home theater da sai amsa kiɗan suke. Koda ya dawo cikin gidan ma tun a parking lot yake jin kiɗa na tashi na ban mamaki. Shigowarsa keda wuya ya tarar da ita tana tweking kamar wadda take a club. Waƙar Ayra Starr Bloody Samaritan ce ke tashi a living room ɗin. With all her body take girgiza ko ina na jikinta ko ina ta na malƙwayashi haɗe da lanƙwasa shi dai-dai da salon kiɗan. Baki sake ya tsaya kallon wadda yafi tunanin cewa ita ce matar tasa sannan a hankali ya ƙaraso living room ɗin haɗe da ɗaukan remote ɗin Tvn ya na mai kashe tvn. A tunaninta ko Saleemah ce hakan ya sa ta juyowa a fusace wanda hakan ya yi sanadiyar haɗa idanunsu a daidai inda ya duƙa zai maida remote ɗin mazauninsa......." "Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need." *THE REGRET* (Dana sani). ~PENDING AMARYA CE~ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi._ With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words. *THE NOBLE WRITTERS TEAM.* _Dedication is Our Strong_ _ Pending Amarya 30_ A tunaninta ko Saleemah ce hakan ya sa ta juyowa a fusace wanda hakan ya yi sanadiyar haɗa idanunsu a daidai inda ya duƙa zai maida remote ɗin mazauninsa......." Da wani kalar speed ta ja baya sannan ta ƙara matsowa sosai haɗe da murza idanunta ko gizo suke gane ma ta, da ta ga dai da gaske idanun na ta ba su mata ƙarya ba hakan yasa ta daddage ta runtuma wani uban ihu wanda duk wani na kusa da ita idan ya ji zai ji shi ne har dodon kunnensa. ''Salimah! Salimah! Na yi gamo da aljani, innalillahi wa inna ilaihir rajiun!." Jikinta sai rawa yake dan ganinsa da ta yi ya yi mugun ɗaga mata hankali. Ƙwalama Salimah kira take amma babu alamun zata fito ma, kuma mutumin sai ƙara dosota yake, itama ta na matsawa baya. A hankali ta tafi tare da zurawa a guje zata haura saman stairs teddy slippers ɗinta ya faɗar da ita a ƙasa. A hankali ta ƙara yunƙurawa ta tashi daga ƙasan haɗe da tsayawa ta na ƙare masa kallo. Salimah dake kwance ta na waya da boyfriend ɗinta ce ta fito a kiɗime jin kiran da Liyanar ke kwaɗa mata, "Aunty Liyana what's wrong?." Idonta ne ya sauka akan Hydar dake tsaye ya ƙafe Liyanar da eyes ɗinsa. ''Laa Ya Hydar sannu da zuwa.'' ''Yawwa!, Sannu!, who's she!?." Ya amsa gaisuwar nata haɗe da jefo mata tambaya akan Liyanar da itama ta ƙuresa da firgitattun idanunta. Sai da ta tsaya yi musu kallon mamaki sannan a hankali kuma ta ce ''Matar ka ce mana Yaya.'' ''You can go.'' ''Toh Yaya.'' A hankali ya fara ta ko ƙafafunsa zuwa inda take tsaye a fusace ta ce ''Kar ka matso kusa dani ko da wasa!.'' Bai kula ta ba ya cigaba da matsowa kusa da ita. ''Don't you dare come closer, you dog!." Jikinsa har wani kalar huci yake, idanunsa na canza kala dan ya sha faɗa ya tsani mace mara tarbiyya da kuma mara kunya a rayuwarsa. Da sassarfa ya ƙaraso wurin da take haɗe da ɗauke ta da wanni kalar gigitattcen mari sannan a hankali ya ce ''wannan na ranar da kika faɗar min da waya ne, kin tuna ranar?, nasan ba za ki tuna ba.'' wani marin ya ƙara mata wannan karon sai da ta ga stars kalar na duniyar mars (😂😅). '' Wannan na ranar da kika bige min mota ne.'' sannan ya ƙara mata wasu twins ɗin mari making four ''wannan na marin da kika min ne saboda lack of tarbiyya da iyayenki suka ba ki.'' Hannu ya ɗaga zai ƙara sakar mata wani marin wanda bai kai ga marin ba ta bangaje hannun nasa tare da hawan kan stairs da gudu cikin shashsheƙar kuka ta fara magana ''Ai ba jaka aka kawo maka ba da tun safiyar Allah kake marina mugu kawai, lack of tarbiyya kuma wannan kai za'a kira da shi, banza kawai mai dukan mata lusari!.'' Da gudu ya biyo ta zai dake ta wanda hakan ya saka ta arce a guje. Ko da ta shiga ɗakinta ma faɗawa ta yi akan gadonta ta fashe da wani sabon kuka, a haka har bacci ya kwasheta. Ɓangaren HYDAR kam marin da ya mata ma a ganinsa bai huce ba, dan laifukan ta sun fi yadda ya lissafo, ga yawo da samari da aurensa akanta, ai wannan ma sam - sam ba matar aure bace, ya sha ganinta a joints kala - kala, musamman da ya ke gina joint ɗin shi da yake duba kalar wa'yanda ake da su anan kano ɗin. Ƙwafa ya yi tare da faɗin ''kaɗan kika gani, zaman gidan nan ma sai ya gagare ki.'' Daga haka ya shige toilet domin watsa ruwa sannan ya sanya kayan baccinsa tare da kwanciyarsa, sai da ya ɗan duba laptop sannan ya gyara kwanciyarsa bacci mai daɗi ya kwashesa. Washegarin ranar ma Liyana ko da wasa ba ta fito ba rayuwarta kawai take a sama Salimah na kawo mata abin da take so. Shi HYDAR ma ko ta kanta bai bi ba, duk da ya ga abinci jere kan dinning buh he prepared ya ci na siyarwa because shi yanzu komai na gidan ya fice masa a kai, ga tsanar yarinyar na ƙara fizgarsa. Fitarsa ke da wuya a gidan wayarsa ta fara ringing ko da ya duba ma Abbuh ne ke kiransa a wayar ajiyar zuciya ya sauke sannan a hankali ya ɗaga. ''Assalamu alaikum Abbuh.'' ''Wassalam, har ka fita ne?." ''Eh Abbuh.'' ''Kana ina toh yanzun?." ''Ina hanyar zuwa gida ne." ''Gidanka?." ''A'a Abbuh gidanmu, naka kai da Mami toh.'' ''Yayi maka kyau, ka zo ka sameni a office yanzun nan.'' ''Wanne a ciki?." ''Na takalma.'' ''Toh sai na iso Abbuh.'' "Okay, alright.'' Ajiye wayar ya yi haɗe da fuzgar da iska a bakin sa sannan ya juyar da kan motar tasa zuwa can office ɗin. Liyana sai da taji fitar motarsa sannan ta fito falon fuskarta duk shatin mari dan har lokacin shatin na nan. ''Munafuki.'' shine kalmar da ta faɗa haɗe da zama akan kujerar dinning ɗin ta fara cin abincin da ta ganshi a jere a kan dinning ɗin. Salimah ce ta fito daga cikin ɗakinta fuskarta da dan damuwa tazo wurin Liyanar ''Aunty Liyana, kin tashi lafiya?.'' ajiye spoon ɗin hannunta ta yi tare da faɗin ''lafiyar ce ta saka kika ganni da shatin mari à fuskata algunguma!.'' ta ƙara jan tsaki haɗe da kwaikwayon Salimahn. ''Laa Yaa Hydar sannu da zuwa baka sani ba matarka ce ai.'' ta ƙarashe maganar da tsaki tare da faɗin ''Rubbish.'' Sannan ta cigaba da cin abincin ta . Har Salimah ta fara kwashe warmers ɗin Liyana ta ƙara faɗin ''Shi ko menene sunan da kika kira ma, ko a ina kuka haɗa dangi har ya zama yayan naki oho.'' ''Aunty Liyana dan Allah ni kiyi haƙuri, ki barni haka.'' ''Ni kauce min a hanya, mtsww laa ya hydar.'' Ta faɗa sannan ta ƙarasa up stairs da gudu. Miss call ɗin Lily ta gani hakan ya saka ta bi wayar. Ring biyu ta ɗaga a hankali suka fara magana because test ɗin jiya shine jigon exam ɗinsu na first semester a level 400. ''Lily yaushe za ki zo?." ''Bae i think next week zan zo buh kinsan ni wallahi am not good a zuwa gidan friends unless idan zamu haɗu a Hydar's palace and garden.'' ''Ai sai dai kar mu haɗu wallahi.'' Haka suka cigaba da hira har ƙarfe biyu sannan ta yi sallah. Bayan ta idar ma fitowa dinning room ta yi domin cin abincin rana. ''Aunty Liyana kin fasa zuwa Saloon ɗin ne?." ''Kin saka an yi min damaging fuskar zan fita a hakan?." Parking ɗin mota Liyana taji a compound wanda a take ta saki spoon ɗin hannunta haɗe da arcewa da mugun gudu. Salimah kawai da idanu ta bita. ''Assalamu alaikum jama'a.'' Muryar Neneh ta daki kunnen Liyana da saura ƙiris ta ƙarasa buɗe ɗakinta. Juyowa ta kuma yi a million ta fara saukowa da gudu jikinta daman tun mini skirt ɗin yau da safe ne ba ta yi wani wankan

Chapter 13 of 31