a yau ina jin kewar ɗana AbuDalib, na ji zuciyata da kwayar idanuwana tana son ganinsa, amma kuma kamar na makara saboda ina gab da kushewa, ku kira mani shi ko da a gabar numfashina na karshe ne in ganshi, na fada mashi abinda ke raina."
Rumaisa ta kama hannunta, "Umma wallahi babu abinda zai same ki, ba za ki mutu ki bar mu ba Insha Allah."
"Rumaisa, ina ji a jikina lokacin yankewar wannan wahalar da bakin cikin ya yi." Wani dan tari ya taso mata da ya sa jikin Rumaisa ya hau karkarwa. "Ya Ubangiji kar ka dauke Ummana, ya Allah kar ka dauke Ummana, Allah ka raya ta."
Inna Uwale ko hawayen kawai take yi yayin da ta kasa furta komai. Hannu Umma ta sa ta lalaubo hannun Rumaisa, "Mutuwa gaskiya ce, kuma ita ke raba kowa da masoyinsa, har jinjiri ma ta raba da uwarsa a kan me kike wannan ihun kukan?"
"Umma ni dai ba na son ki tafi ki bar ni." Wani murmushin ta yi mai ciwo, "Ki saurare ni da kyau zan ba ki wasiyya ki nutsu ki rike da kyau a ƙwaƙwalwarki."
"Na san idan AbuDalib ya samu labarin mutuwata dole zai zo wurin jana’iza da zaman gaisuwata. Idan ya zo ki shaida mashi, na yafe mashi duk abinda ya yi mini, amma na tafi da bakin cikin kazafin da suka yi wa diyata, zan yafe masa wannan laifin ne idan ya nemo ta duk inda take cikin fadin duniyar nan, ba zan yafe mashi wannan zunubin ba in har bai nemo ta ya wanke ta daga wannan zargi da sharrin."
Shuru ta yi hawaye na zubo mata tana jin dacin abinda ya faru kamar yanzu ne yake faruwa. Tari take saboda mikin da ya samu wuri cikin zuciyarta ya zauna ya motsa. Sallamar Malam Saleh cikin dakin asibitin ya sa Inna Uwale juyawa ita ko Rumaisa ta hada kai da gwiwa tana wani irin kuka mai cin rai. Umma ta ji sallamarsa sai dai ta yi shuru domin rauni ya ida lullube ta, shi ma kula da yanayin da suke ciki ya sa shi zarcewa kawai inda Umma take. Ko gaisuwa ba su yi ba ya ce, "Uwale tare muke da Baban Rumaisa." Kallon shi ta yi a dan razane, bakinta na rawa ta ce, "Baban Rumaisa kuma?"
"Ehh, idan kun ba da izini yana son ya shigo."
Umma ta kada kai, "Don Allah ku bar shi a waje ba na bukatar shi nan."
"Bilkisu ki yi hakuri ki yi afuwa domin Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, kuma lada mai yawa tana ga mai yafiya da afuwa a kan laifin da aka yi masa."
Da ƙyar ta ce, "Shi ke nan ka ce mashi ya shigo." Shigowa ya yi cikin ɗakin kallo daya za ka mashi ka tabbatar yana cikin wani yanayi marar fassaruwa, cikin nauyin harshe ya ce, "Umma ki taimake ni ki yafe mani, domin na san kuskuren da na yi maki ko a wurin Allah babban laifi ne." Shuru ta yi zuciyarta na suya, "Kin ji Umma..." Sallamar Doctor cikin ɗakin ya katse zancen da ya fara. Kasantuwar asibitin private ce kuma suna ɗakin mutane masu muhimmanci, (VIP room) hakan har ya ba su damar shiga.
Doctor ya kalli Uwale cikin nuna ɓacin rai ya ce, "Na ce a bar ta ta huta, saboda hypertension da ya tasar mata."
Inna Uwale ta ce, "Ka yi haƙuri Doctor."
"Okay, ina so zan yi aikina ku ɗan ba mu wuri."
Gaba daya suka fice yayin da Rumaisa da ke ta aikin kuka ta kasa bari, shi ma Babanta duk da kasancewar shi babban mutum shi ma kwallah yake yi.
Fitowa suka yi daga waje, Inna Uwale ta nisa a sanyaye ta ce, "Malam jiya ban samu zuwa ba saboda jikin Umma da ya rikice."
"Haka ne, ina ji a jikina rikicewar jikin Umma ya tallaka ne da kiran da na yi maki. Kuma yanzu ma da Likita zai ba mu sallama da mun je an yi mata rubutu da addu’o’i ta cigaba da sha za ta warware Insha Allah."
"Malam, akwai wani abu a ƙasa ne?"
"Jinjina kai ya yi alamun eh. "Amma a nan zancen ba ya yiyuwa, ga wannan rubutun da na zo da shi a ba ta tasha yanzu. Idan aka sallame ku, za mu yi bayanin komai na fi son a yi komai a gaban Umma," ya kare zancen yana fito da rubutu daga cikin aljihunshi.
"Inna Uwale ta nisa ta ce to shi ke nan, amma jikin Umman ne…" kukan da ya taso mata ya hana ta ƙarasa zancen.
"Ba wani abu Insha Allah, kin san cuta ba mutuwa ba ce ko? Haka ciwo ba shi ke nufin ajali ya zo ba, wani lokacin ma idan ajalin ya zo ko ba ciwo tafiya ake yi. Wannan abun da ke faruwa warwara ce da samun sauki daga kunci da tsananin da aka shiga Insha Allahu."
"Allah ya sa haka Malam." Rumaisa da take jin zantukansu a kunnenta, ta daga hannunwanta sama tana kiran, "Ya Allah ka raya mani Ummana."
Malam Saleh ya ce, "Rumaisa babu abinda zai same ta Insha Allahu." Zama suka cigaba da yi jugum-jugum bayan likitan ya fito Inna Uwale da Rumaisa suka koma ciki. Kasantuwar sun samu tana barci ya sa Malam Saleh da Baban Rumaisa tafiya, tare da jaddada zancen kashe garin ranar za su koma.
SH 13
Wuraren ƙarfe bakwai na safe jirginsu ya sauka filin jirgin Malam Aminu Kano, tunda suka taho haka suke zaune kamar kurame, kowa da tunanin da ke ƙunshe cikin zuciyarsa. Kai tsaye AbuƊalib tashar mota suka nufa, takaici zuciyar Badiyyah tamkar ta yi bindiga domin ta shafe babin hawa motar haya a cikin kf ɗin rayuwarta.
Motar kwankwasiyya ya ɗauka drop kai tsaye ta kai su har birnin Dikko ɗakin kara. Fitowa Badiyyah ta yi daga motar tana yamutsa fuska, AbuƊalib bai bi ta kanta ba, sai ma abun da ya yi na in ba ki yi ba ni wuri da ya yi, da sassarfa ya tari mai achaɓa domin ya kai shi gidansa da ke Modoji. Har bakin ƙofar gidan ya kai shi, ma'aikatan gidan da suka ganshi bagatatan sun cika da mamaki sosai. Da sauri ya isa ƙofar babban falo, abu ɗaya yake so ya tabbatar wanda Badiyyah ta faɗa mashi, shi AbuƊalib ya saki matarsa Lilbirrah saki uku ƙwarara, shin da gaske ne ko kuma zafin kishi ne irin na mata ya sa ta faɗar hakan. Cikin falon ya tsaya yana kallon hanyar da sashenta yake cike da tsammanin ganinta, cikin fara'a da annushuwarta, ganin babu ita babu alamarta ya sa shi faɗin "Lilbirrah?" da ƙarfin gaske. Falon tsit yake sai sautinsa da ya karaɗe shi, ƙara kiranta ya yi da sunan da babu mai kiranta da shi sai shi kaɗai, "Khouhar," sam bai ji da alamun za a amsa ba. Gudun zuciyarsa ya ƙaru fiye da gudun da yake yi, a hanzarce ya nufi sashenta, hannu ya sa ya murɗa handle ɗin ƙofar ɗakinta, falon ya yi ƙura da har yana ganin sawayenshi a ƙasa, hakan ya ƙara tada hankalinsa sosai. "Innalillahi, kenan da gaske ne abinda Badiyya ta faɗa mani?"
Bai tsaya wani abu ba ya fice daga ɗakin, kai tsaye gidansu da ke yammawa ya nufa domin ya samu Ummansa ya sani ita kaɗai ce za ta warware masa zare da abawa ta fitar da shi daga ruɗanin da yake ciki. Mai mashin na aje shi ya fiddo takardar Dollar da ke aljihunsa wanda da ita ya biya kuɗi tun daga Kano har zuwa kan mai mashin ɗin da ya sauke shi. Cikin mamaki mai mashin din ya ce, "Malam Dollar ce ka ba ni?"
"Je ka kawai rabonka ne." Ya faɗa yana shigewa cikin gidansu.
"Salamu Alaikum," sallamarsa ta ratsa cikin gidan. A guje matasan ƙannensa suka fito da gudu, ɗaya daga cikinsu ya rungume shi ɗayan kuma tsaye yake yana masa kallon mamaki.
Babansa Malam Abdulhadi ya fito yana masa kallon yaushe rabo, ɗayan ɗakin kuma Antinsu Rashida ita ma ta fito tana ƙare masa gani, su duka kallonsa suke kamar yau ne suka fara ganinsa. Sakinsa ƙanin nasa ya yi, "Yaya AbuƊalib..." Ya faɗa yana sakin murmushin jin daɗi, sai kuma hawaye suka ziraro daga idanuwansa.
"Yaya AbuƊalib, da ma za ka sake shigowa duniyarmu?" Shi ma kallonsu yake cikin tsananin mamaki da al'ajabin abinda suke yi. Gabansa ya faɗi lokacin da ya kalli ƙofar ɗakin Ummansa, rufe yake gam. Bakinsa na rawa ya ce, "Baba, ina Ummana, ina Lilbirrah ina Rumaisa suke? Duk suna ina Baba, na ga ba su nan kuma ba su fito ba. Baba wai me yake faruwa ne?"
Malam Abdulhadi ya ja dogon numfashi, muryarsa a disashe ya ce, "AbuƊalib, kana nufin duk ba ka san me ke faruwa ba? Kana nufin duk abinda ka aikata ba a hayyacinka kake ba?"
"Baba me na yi? Me na yi wai? Na ga Jabir yana kuka, ga Anti ma tana min wani kallo, duka kowa kallona yake kamar yau suka fara ganina? Baba me ya faru ne?"
"AbuƊalib wannan dogon zance ne."
Ƙasa ya faɗi daɓas hawaye na biyo kumatunshi, "Baba kenan da gaske na saki Lilbirrah? Kenan da gaske Ummana ta tsine min? Baba me na yi ne haka? Wane irin mummunan zunubi na aikata? Ina Umma take Baba ina Ummana?"
"Ta so mu je AbuƊalib," Malam Abdulhadi ya faɗa tare da ɗago AbuƊalib daga zaman cin doyar da ya yi.
Ɗakinsa suka shiga kafin su zauna AbuƊalib ya ce, "Baba ina Ummana?"
"Tana asibiti."
A firgice ya ɗago, "Tana asibiti Baba?"
"Tana can AbuƊalib."
"Me ya same ta to Subhanallahi."
"Ciwon zuciya ne da hawan jini mai tsanani. Baba, ni ne ma silar komai ko?"
"AbuƊalib ka nutsu, tabbas an shiga jarabawa kuma muna cikin wani yanayi mu duka. Ka nutsu domin cinye jarabawar nan..."
"Baba to wai me ke faruwa ne?"
Kaɗa kai kawai Baba ya yi ba tare da ya furta komai ba ya ce, "Tashi mu je asibitin." Miƙewa ya yi kamar ƙaramin yaro yana ta faman sharce hawaye.
Suna isa suka yi kiciɓus da Inna Uwale a bakin ƙofa, sakin plask ɗin ruwan zafin da ke hannunta ta yi ƙasa sannan ta yi saurin dafe ƙirjinta. "Baban Rumaisa, idanuwana ne ke min gizo ko da gaske AbuƊalib nake gani?"
"Inna Uwale, ke ma kina mamakin ganina kenan?" AbuƊalib ya faɗa yana kallon Inna Uwale.
Juyawa ta yi ta shige cikin asibitin, Umma barci take sai Rumaisa da ke zaune tana karatun Alƙur'ani mai girma. "Rumaisa ga yayanki AbuƊalib nan."
Zumbur ta miƙe tsaye, "Inna Uwale da gaske, ina Yaya AbuƊalib ɗin?" Kafin ta rufe baki suka shigo cikin ɗakin tare da AbuƊalib ɗin. "A she zan ga wannan ranar kusa haka?" Ta faɗa tare da yin hanzarin rungume shi.
Ɗago ta ya yi shi ma idanuwansa sun cika da hawaye, "Rumaisa don Allah me ya same ni? Me ya samu Ummana? Ina Lilbirrah kuma?"
"Uwale, Rumaisa, kamar muryar AbuƊalib nake ji..." Muryar Umma da yanayin rashin lafiya ya sa ta dishe ta ratsa cikin ɗakin. Da sauri AbuƊalib ya saki Rumaisa, gaban gadon ya yi suka ya tsugunna yana, "Ummana, ba kama ba ce. Ni ne, muryar AbuƊalib ɗinki ce."
Buɗe idanuwa Umma ta yi, domin ji take kamar mafarki ne take yi, cikin kasa gaskata ganinsa da take yi, ta ce, "Rumaisa AbuƊalib yake min gizo, yanzu na gama jin muryarsa na buɗe idanu kuma shi ɗin nake gani."
Rumaisa ta matsa gab da ita, "Umma ba mafarki ba ne, kuma ba gizo ba ne Yaya AbuƊalib ne, shi ne da kansa."
Hawaye suka biyo gefen fuskarta, ta yunƙura da ƙyar da nufin miƙewa, da sauri ya sa hannuwansa ya miƙar da ita zaune. Baya ya yi nufin yi, da sauri Umma ta riƙe hannunsa, kallonsa take, irin kallon da ke bayyana tsananin soyayya ga wanda ake mashi, kallon da ke nuna kewa da zallan kaɗaicin da aka shiga na rashin wanda ake yi ma shi. "AbuƊalib..." Ta faɗa ta kasa daina kallonsa. Shi ma ita yake kallo, cikin dusasshiyar murya ya ce, "Ummana." Sakin hannunsa ta yi ta jingina da pillown da aka saka a bayanta, juyawa ta yi gefe a dake ta ce, "Rumaisa kin faɗa masa saƙona? Kin faɗi wasiyya ta gare shi?"
Gaban Rumaisa ya buga a tare da na shi, bakinsa na rawa ya ce, "Rumaisa wa ce wasiyya Umma ta ba da a faɗa mani?"
Kallonsa take tana hangen rauni da tashin hankalin da yake ciki, sannan kuma Umma ta yi umarnin faɗa mashi wasiyyar da ta bayar a faɗa mashi, tabbas yana buƙatar tallafi yana buƙatar samun sauƙi daga goran wahalar da ya afka. Shurun da ta yi ya sa Umma faɗin, "Ki faɗa mashi, ko da rai ya yi halinsa gare ni na yafe masa duk abinda ya yi mani, amma ba zan amsa mashi maganar shi ba a yanzu, ba zan sake saka shi idanuwana ba har sai ya gano mani ɗiyata Lilbirrah a duk inda take cikin faɗin duniyar nan, idan har ina raye zan ci gaba da mu'amala da shi ne idan ya dawo da ita gare ni, ya wanke dukkan baƙin fentin da ya yi mata, ya dawo da ita cikin aminci. Wannan ita ce wasiyyata gare shi, ko da na mutu tabbatuwar yafiyata gare shi shi ne cika wannan aikin? Saboda haka ki ce masa ya fita."
"Ummana," AbuƊalib ya faɗa yana riƙe tafin hannunta. Ba ta juyo inda yake ba, cikin shaƙaƙƙar muryarta ta ce, 'Na ce ka fita, idan kuma kana son ƙarasa ni ne ka fi gaba da zama."
Rumaisa ta yi saurin cewa, "Yaya AbuƊalib ka yi haƙuri ka fita, zan yi maka bayanin komai, ta ƙare zancenta tana hawaye.
Inna Uwale da Baban Rumaisa suka yi saurin cewa, "Umma ki taimaka ki ƙyale shi mana, ki mashi uziri."
"Baban Rumaisa idan za ya fita ku fita tare don Allah..."
Sosai AbuƊalib ke kuka, ko kaɗan ya kasa ko da motsi balle ya tashi daga gaban nata.
"Umma..." Tari ta soma yi, wanda cikin rikicewa da kaunar lafiyar Umma Rumaisa ta ce, "Yaya AbuƊalib ka fita zan maka bayani, idan Umma ta fara tarin nan siƙewa take yi."
Miƙewa ya yi da ƙyar ya fita yana jin jiri na ɗibarsa, Baban Rumaisa ya bi bayansa, dukansu zuciyoyinsu babu daɗi.
Yana fita Umma ta saka sabon kuka, tana tuna abinda ya faru. Inna Uwale ta ce, "Umma ki yi haƙuri ki yafe ma AbuƊalib, ki ga yadda ya kasance gare mu ko tunawa da mu ma baya yi, yau ga shi ya zo har inda muke, mu godewa Allah."
"Uwale, kin san wane hali Lilbirrah take ciki? Tana raye ko a mace take? Ba zan kula shi ba kamar yadda na faɗa har sai ya mai do ta gare ni."
Rumaisa ta cigaba da share hawaye, tunanin wane hali Lilbirrar ta kasance ya taso cikin ranta.
Inna Uwale ta ɗauko rubutun da Malam Saleh ya ba ta, "Umma ga shi Malam Saleh ya ce ki sha." Karɓa ta yi kasantuwar dama lokacin garin ya waye, shan shi ta yi kaman ruwa ta koma ta kwanta.
Ta janibin AbuƊalib kuwa cikin wani kalar yanayi ya ce ma Malam Abdulhadi, "Baba wai me ke faruwa? Na gaza gane komai."
"Yanzu mu tafi gun Babanka, shi zai yi mana bayanin komai." Sai da Baban Rumaisa ya kama hannunsa suka tafi zuwa gidan Malam Saleh.
★★★
BADIYYAH
Ganin sam ba ta gabanshi ya ida tada hankalinta, kai tsaye gidansu ta nufa. Tana isa ta iske gidan rufe Maman ba ta nan, sosai ta ɗimauta da rashin ganinta ga rashin jinta a waya da ba ta yi ba tun suna Vienna. Ɗayan gidansu ta shiga tana yin sallama gidan sun yi bulaƙai da ita kamar ba su ga kowa ba. Tsaki ta ja, cikin isa ta wuce ɗakin Babansu, waya yake sai da ya gama tsaf sannan ya juyo wajenta, "Baban Nana barka da safiya, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau," ya amsa a gintse.
"Baban Nana, da ma in ce ina Mom take?"
"Wa ke nan?" Ya tambaya kaman bai taɓa sanin wace Mom ɗin ba.
"Baba, Mama nake nufi."
"Ba ta sanar da ke inda take ba?'
"Eh Baba, yanzun nan na diro ƙasar fa."
"Madallah to ya yi. Sai ki je ki iske ta can Shargalle, tana can ai."
Ji ta yi cikinta ya juya, "Baba Shargalle kuma?"
"Ina can ne tushen ku ko? To tana can, sai ki same ta can.
Zaune ta yi kaman an dasa ta, ganin ba ta da niyyar tashi ya sa shi miƙewa ya baro maga ɗakin.
Miƙewa ta yi a sanyaye ta fito. "Mun huta dai da mugun iri, irin butulci da mugun abu, sai a gaida gida Umma ta gaida Assha." Muryar ɗaya daga cikin matan gidan ta dake ta, ko juyawa ba ta yi ba ta fice waje.
Ta daɗe tsaye bakin hanya nisawa ta yi, "Wallahi ko me ake yi dai yanzu ba zan koma ƙauye ba, ta ya zan koma na tashi a tutar babu kenan, ba ni ga tsuntsu ba ni ga tarko, ba zai yiyu ba. Bara na koma gidana, idan na je na nutsu sai na tafi wajen Mama, don haka can zan tafi sai dai komai zai faru ya faru. Napep ta haye ta ba shi umarnin ya kai ta gidan nata da ke Modoji.
SH 14
Kamar Raƙumi da akala AbuDalib ya bi bayan Malam Abdulhadi zuwa gidan Babansa Malam Saleh, sun tarar yana zaune makarantar Allo yana fama da dalibai. Bai ji mamakin ganin AbuDalib ba kamar sauran, sai dai ya daga kai ya kalle shi, duk ya firgice ya fice hayyacinsa. Yana isa wurin Malam Saleh ya tsugunna gabansa, hawayen da yake ta faman yi suka cigaba da sauka kan dandamalin fuskarsa, murysa a dishe ya ce, "Baba… Baba na shiga uku, Baba ina cikin tashin hankali… Baba me ya same ni, me ke faruwa da ni?"
Malam Saleh bai ce masa komai ba ya miƙe tsaye ya dago AbuDAlib. Kuka ya fashe da shi sosai, "AbuDalib." Baban ya kira shi cikin taushin murya.
"Na’am Baba," ya fada yana fashewa da kuka sosan gaske. Cikin gida suka shiga kai tsaye dakin Malam Saleh suka yada zango. Zaune ya yi ya tisa AbuƊalib ɗin gabansa, kuka yake yana sauke ajiyar zuciya, sai dai ya yi mai isar shi Malam Saleh bai ce mashi komai ba haka shi ma Malam Abdulhadi baban Rumaisa duka idanuwa suka sa mashi, kowa da abinda yake tunani a ransa. Sai da ya nisa ya rage zugin da zuciyarsa ke yi sannan ya samu'yar guntuwar samu nutsuwa, Malam Saleh ya nisa ya soma magana, “AbuDalib, ka nutsu dukkan abinda ya yi farko zai yi karshe, wannan rubutacciyar kaddararka ce, haka Allah ya hukunta maka tun kafin halittarka.”
“To ni Baba me ya same ni ne?”
“AbuDalib zan so bayyana me ya same ka ɗin a abunda Allah ya nuna mini, amma na fi son sai gaban Ummanka, domin duk abin nan da ke faruwa babu wanda ya kai ta shan wahala. Kuma idan ta ga komai, watakil za ta karbi uziri har ka samu ganinta.”
Baban Rumaisa ya dago a sanyaye, “Ka ji abinda ta fada ne Malam?”
Jinjina kai ya yi, “Eh Uwale ta kira ni ta fada mani. Kar ku yi fushi ku karbi uzirin Ummah, tana cikin ƙuncin zuciya sosai, 'yarta guda aka salwantar. Sannan kamar yadda ta ce, ka yi kokari ka shiga neman Lilbirrah tana nan cikin ƙasar nan, sai dai sanin takamaiman inda take sai Allahn da ya yi ta.”
"Baba, to ni me na yi ma Lilbirrah wai da gaske ni na kore ta da kai na? Khouhar ɗina...”
“Na ce ka bar wannan maganar, na fi so a yi ta duka gaban Umma.”
“To Baba. Amma duk me ye silar wannan? Baba wallahi ni ban san na aikata duk abinda ake tuhumata na aikata, wallahi ban aikata ba Baba.”
“AbuƊalin mu musulmi ne, kyautata zato ga kowane mutum a gare mu wajibi ne, ban san wa zan dauki wannnan laifin na dora mashi ba, amma Allah zai bayyana ko waye ya yi maka wannan abun. Batun ba ka san ka aikata ba, za mu iya karɓar uziri saboda ba halinka ba ne.”
Baban Rumaisa ya yi karaf ya ce, “Malam, wallahi ni dai ba na raba daya biyu wannan abun daga matarsa ne ita da uwarta. Kuma wallahi kamar yadda ya ce, ni kaina sai daga baya na riƙa jin abinda na aikata kamar al'mara, ka duba sirrin da na ke riƙe da shi shekara da shekaru amma ban bayyana shi ba tsawon lokacin sai yanzu, wannan abun takaici har ina, shi ya sa sam bana ganin laifin Umma...”
Kada kai Malam Saleh ya yi, “A’ah ba za mu ce haka ba, ba za mu ce matarsa ko wata uwarta ba, ko mene ne gaskiya za ta yi halinta, duk abinda kuka yi ko kuka ji kuma duka gaskiyar nan dai ƙwara ɗaya za ta yi halinta.”
Shi ko AbuDalib sauraren su kawai yake, zuciyarsa tunani take kala-kala wanda rabinsa yana wajen Khouhar ɗinsa.
"Baba, to ya za a yi har Umma ta zo mu ji abinda ke faruwa, ta yi fushi da ni sosai, kuma ko zan tafi neman Lilbirrah sai Ummana ta yafe mini."
"Idan ta ji sauki za a sallame ta a asibitin, to da zaran sun sallame ta ɗin sai a yi komai a gama."
"Amma Malam, ni na san Umma ba za ta yafe mana ba har ta koma gidana ba."
"Za ta koma Malam Abdulhadi, kai dai a yi hakuri a bi komai a hankali."
AbuDalib ya dago kansa da ke duƙe cikin sauri, "Baba kenan Ummana ba ta gidan ma, to tana ina?"
"Tsawon watanni bakwai kenan ba ta nan."
Malam Saleh ya ce, "Wni gida suka koma ita da Rumaisa nan wajen tudun 'yan lihidda."
"Umman nawa, a gidan haya?" AbuDalib ya faɗa cikin takaici.
"Ka nutsu ka daina zantukan nan komai zai wuce. Kar ka sa ma kanka hawan jini mana da ƙananun shekarunka."
"To Baba." Sun tattauna sosai kafin daga bisani Malam Andulhadi ya miƙe ya tafi gida shi kuma Malam Saleh ya tafi wajen ɗalibai. Zamewa AbuƊalib ya yi ya kwanta ƙasa cikin ɗakin. Sai yamma ya farka daga barcin da ya yi nasarar sace shi, salloli ya yi saurin bayarwa saboda lokaci ya yi nisa. Bayan ya gama sallolin Malam Saleh ya shigo ɗakin, "Sannu ka tashi ko, ina ta ƙoƙarin tashinka ka yi Sallah amma ko motsi baka yi."
Murmushin yaƙe kawai ya yi, "Ka ɗauki abincin gaya nan ka ci ka ji ko."
Kallon shi ya yi, "Baba Wallahi ni ko yunwa bana ji, na manta rabon da na zauna ma ko abinci na ci."
"To ka ci wannan ko yaya ne, tuwo ne zai maka sauƙin ci."
"Naƙoshi Baba." Malam Saleh bai kuma ce mashi komai ba ya ƙyale shi.
"Yanzu tun da ka ɗan huta, ka je gida ka huta, ka ga daga saukarka airpot ba ka huta ba, ka je ka yi wanka ka canza kayan jikinka."
Mikewa ya yi a sanyaye ya fice, yana fita maimakon ya tafi gidansa sai ya wuce asibitin da Ummansa take. A waje ya samu Rumaisa, saukin da Umman ta ji ya sa ta ɗan sakewa har ta fito wajen ɗakin. Tana ganinsa ta mike ta zo inda yake, "Yaya..." ta fada tana kallonsa.
"Rumaisa, ya jikin Ummana, zuwa na yi in sake ganinta."
"Da sauki sosai, tana shan rubutun nan da Baba ya kawo mata ta ce mana sai ta ji kaman an zare mata kaya a jikinta, ta ji sauki sosai."
"Ni so nake in ganta Rumaisa."
"Yaya AbuDalib, Umma tana kewarka sosai, amma kuma…" ta dan yi shuru.
"Amma kuma me Rumaisa?"
"Halin da zuciyarta ke ciki na rashin sanin inda Yaya Lilbirrah take da kuma irin kazafi da bakin fentin da aka yi mata shi ne ya hana ta karɓarka, kuma Yaya duk da akwai lauje cikin naɗi, Umma gani take kai ne ka yi komai."
"Rumaisa a faɗa mani me na yi?"
"Yaya... Ni dai kawai kar ka damu Umma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 14