ko bakinsa ba ya zame kan kujerar.
"Yin sallah cikin lokaci yana kawo farin ciki, Joo..." Daɗe kunnuwansa ya yi jin abinda ke hargitsa ƙwaƙwalwarshi sun cika farantan kunnuwansa. Sai da ya ji guntuwar nutsuwa ta dirar mashi sannan ya sauke hannunwanshi.
Shuru ya yi, "Haka ne fa... Ban yi sallar azahar ba, ban yi ta la'asar ba, yanzu kuma ga Magrib da Isha." Tamkar ya miƙe ya yi sallarsa, sai kuma ya gyara kwanciya. "Na haɗa in yi duka idan na tashi ƙiyamul-lail." Ya faɗa tare da juyawa ya yi kwanciyarsa, bai jima ba barci ya ɗauke shi.
★
A nutse yake tuƙi, gefensa dattijuwar mace ce tana amsa waya. "Mama." Ya faɗa lokacin da ya ga ta ajiye wayar.
"Na'am, ɗan Mama ya aka yi ne?" Ta ba shi amsa tana mayar da dukkan hankalinta kansa.
"Yau na ga abinda ya dame ni ne."
"Me ka gani Yunus ɗina?"
"Ɗazu da safe na ga wata mata nan wajen Ipaja cikin masu barar nan, Mama matar fa she is pregnant and she is too young, it's not free Mama, ƙaramar yarinya kamar wannan tana bara."
Kaɗa kai ta yi cikin damuwa ta ce, "Abin da ciwo kam, ƙananan yara da mata su ne cike da tituna da kasuwanni suna bara a yanzu. It's very unfortunately."
"Mama, ni ta tsaya min a rai, yarinya ce fa, wannan na tabbata ba ta fi 25years ba, ina mijinta? Ina iyayenta? Da 'yanuwa da danginta?"
"Allah kaɗai ya sani Yunus. Allah ya sauƙe ya sa kuma ba irin masu ɗauko ma iyayensu magana ba ne, su kuma iyayen su kasa haƙuri su kore su."
"Masu ɗauko ma iyayensu magana Mama? Kamar yaya kenan?" Ya tambaya cikin al'ajabi.
Murmushi ta sakar masa, "Yunus ina nufin masu ɗaukar ciki ba ta hanyar aure ba, masu haihuwar ɗan gaba da fatiha, da yawa iyayensu ba sa jurewa sai su kore su."
Kaɗa kai ya yi cikin tsananin damuwa, "Amma ko haka ne sam bai kamata ba. Kuma..."
"Mene ne Yunus?"
"Na ga kamar tana cikin yanayin damuwa wannan, an ya lamarinta zai zama kamar haka kuwa?"
"Oho dai, ni ban sani ba." Ta faɗa tana sakin zancen.
Tuƙi ya ci gaba da yi zuciyarsa cike da tunani kala daban-daban a kan matashiyar matar da ya gani.
★
Zaune nake kan tabarmata. "Barka da yammaci abun ƙauna." Na ayyana a raina ina shafa cikina. Murmushi na saki, tamkar ya maido min amsar gaisuwar da na masa. "Abun ƙauna, ka yi mana addu'a ka san addu'ar ƙananun yara tana karɓuwa, musamman ma jariri mai ƙaunar Amminsa kamar ka. Abun ƙauna wahala ba ta da daɗi, rayuwa cikin aminci ta fi komai zama ma fi soyuwa a gun kowa."
Sauke hannun na yi na dafa shi ƙasa, hawaye suka cika kwarmin idanuwana, zuciyata cike take da fargaba da tsoron ƙarasa faɗuwar rana, domin duhun dare yana zo min tattare da masifar da take barazanar katse igiyoyin rayuwata a duk ya yin da ta sakko mini. Fatan kowane mai rai mutuwa ta zama hutu a gare shi, haka shi ne fatana a kowane taƙi da tunaninta ya zo min cikin raina, sai dai soyayyar abun ƙaunata, ya sa ina tsoron zuwanta gare ni a kowane lokaci. "Ya Allah, ka ba ni dama da ikon haifar abinda ke cikina." Na ambata cikin ƙirjina. Addu'o'i na fara jerawa cikin raina, sosai nake cikin tsoron abinda ke zo mini, wanda yake saka mani yanke ƙauna ga cigaba da rayuwa a kowane lokacin da ya zo mini.
Jin an fara kiraye-kirayen sallar Magrib ya sa na miƙe da ƙyar na yo alwala. Sallar na gabatar saboda raunin da jikina ya yi na miƙe na gabatar da sallar Isha'.
"Ko na yi kwanciyata ma kawai, wataƙil na kaucewa abinda ke kawo mani farmaki cikin daren nan." Zuciyata ta ayyana mani.
Jinjina kai na yi alamun na amince da shawarar zuciyata, ɗan mayafi na sa na kakkaɓe shimfiɗar na kwanta.
Addu'o'in kwanciya barci na yi na shafe jikina da abun ƙaunata.
SH 3
Kamar koyaushe tsira mai kama da ta allurai na fara ji tana ratsa cikin jikina, yunƙurin tashi na yi daga kwancen da nake, sai dai ji na yi kamar an danne ni da tuli-tulin yashi na kasa motsawa ko in da can, hawaye suka fara taruwa a kwarmin idanuwana, domin halin da nake shiga yana jijjigani a duk lokacin da na kasance cikinsa, ba ni da abun yi sai sunayen Ubangiji nake ta ambato a ƙasan raina.
Cikin wani sauti na ji tashin wata addu'a na ratsa kunnuwana, "Allahu ya Allahu, Rahmanu ya Rahmanu, Rahimu ya Rahimu, ya Rabbal Arbabi, wa ya Ilahal Ilahati, wa ya Malikul Malakuti Wa ya Sayyidis Sadati najjini min sharri ma ahammani." Ɗaga kaina na yi na kalli matar da ke rera addu'ar cikin muryarta da firgicin da nake ciki bai hana ni tantance daɗinta ba. Jinjina mini kai ta yi tana cigaba da maimaita addu'ar, tsura ma bakinta idanuwa na yi alamun ina son in yi, da hannu ta yi mini nuni da na yi abinda na yi niyya, mu yi addu'ar tare. Kaɗa mata kai na yi alamun ba na magana. Sam ba ta damu da abinda na nusar da ita ba, ta ƙara yi mini nuni da na bi ta mu yi addu'ar tare. Hawaye suka gangaro mini saboda azabar da nake ji tana ƙaruwa cikin jikina, ɗaga kai na yi na sake kallon matar da har a lokacin ba ta bar abinda take ba sai ma ƙara ƙaimi da take yi. Kallon bakinta nake yi da umarnin da take ba ni, cikin azama da ƙoƙari irin na mai neman mafita na yunƙura domin bin ta kamar yadda take yi mini nuni, bakina na fara motsawa cikin sa a na ji na fara kamo addu'ar, sake ƙoƙarin bin ta na yi, a hankali na ji ina maimaita abinda take faɗa, cikin 'yan daƙiƙu bakina ya kama addu'ar raɗam kamar na daɗe da saninta. Sannu-sannu na ji tsirar da ke yawo cikin jikina ta soma raguwa, nauyin da nake ji ya danne haƙarƙarina ya kau tamkar cirar ƙaya. Zufa ta fara karyo mini ta kowace hudar gashin jikina, lokaci bayan lokaci ina sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Firgigi na farka daga barcin da nake yi, zuciyata na harbawa da ɗan sauri tare da bitar addu'ar da na yi mafarkin ina yi cikin raina. Da sauri na miƙe zaune hannu na sa na fara karkaɗa fitilata da haskenta ya dishe. Numfashi nake maida wa har a lokacin, kai na haɗe da gwiwa ina bitar mafarkina. Hawaye suka gangaro mini domin a yau na tsira daga sharrin abinda ke cutar da ni a cikin dare a lokuta mabanbanta.
Maimakon na koma barci miƙewa na yi ba ɗauko jikkata mai ɗauke da biro da littafi a cikinta, zama na yi na rubuta addu’ar, zuciyata cike da fatan wannan addu’ar ta zama silar yayewar kuncina, tare da maganin abinda ke damuna.
★
Kwana biyu tun da na lazimci karanta addu’ar ban sake fuskantar matsalar da nake fama da ita a cikin dare ba. Yau ta kasance ba ni da ko sisi hakan ya sa na shirya tun da safe domin isa Ipaja na barato abinda zan sa ma cikina. A hankali nake tafiya cikin nutsuwata, wata mota na ga tana tunkaro babban layin da nake tafiya a kai, kokarin ba motar hanya na yi sai dai gani na yi tana tsayawa daidai inda nake, ɗan dakatawa na yi ina bin motar da idanuwana.
Gani na yi mamallakin motar ya soma sauke gilashinta, zuba masa ido na yi zuciyata cike da tsammanin ko yana tambayar wani wuri ne duk da na kasance ba mai dogon zama ba a unguwar, wataƙil ko da taimakon da zan iya masa da yarena wanda kowa ke ji.
Kallon fuskarsa na yi, ban manta ta ba, ban mance tsayayyun idanuwansa da suka kafe ni da tuhuma kwanaki biyu rak da suka shuɗe.
Zuciyata ta buga da ƙarfi, hakan ya sa ni yin taku da sauri domin guje ma tuhumarsa irin ta waccen ranar wadda nake tsammanin ita ta kawo shi. "Hey!" Ya faɗa. Ban tsaya sauraren shi ba cikin azama na ƙara saurin tafiyata.
"Baiwar Allah...!" Na ji ya ƙara faɗa.
Ƙarar rufe ƙofar motarsa na ji alamun ya baro cikinta kenan.
"Baiwar Allah na san dai ke musulma ce , don girman Allahn da ya halicce ki ki tsaya."
Cikk, na yi ina sauraren mai zai faɗa kuma. Da sauri ya sha gabana, "Baiwar Allah, don Allah ki tsaya ina son magana da ke." Kada masa kai na yi alamun ba na iya magana.
Fuskarsa da bayyanannen tausayi ya furta, "Ya salam! Ba kya magana?" Daga kai na yi alamun eh.
"Okay. Alamu na nuna ke ba 'yar nan ba ce, domin kalarki da tsarinki bai yi kama da na wanda suke rayuwa a nan ba. Na tabbata akwai boyayyen labari a tattare da rayuwarki, kina buƙatar..."
Juyawa na yi na cigaba da tafiya, "Baiwar Allah don Allah kar ki tafi ki tsaya mu yi magana, ki tsaya don Allah na ce." Sake tsayawa na yi, da saurinsa ya dawo gabana, "Ni sunana Yunus, tun da na gan ki zuciyata ta yi amanna akwai wani abu tattare da ke, na tabbata kina bukatar taimako. Ba taimaka miki zan yi ba, na za ki taimaka ki nuna mini gidan da kike domin na yi abinda ya hau kaina." Kada kai na yi alamun ba na bukata. Wani murmushi ya saki mai nuna taurin kaina ya gundire shi. Baya ya yi ya shiga wani kutumbutsattsen shago, "Don Allah ina ne gidan wannan matar?"
Kunnuwana suka zuƙo mini tambayar da yake yi ma mai shagon. "Nan kawai nake ganinta tana wucewa..."
Iya abinda na ji mai shagon ya ba shi amsa, yayin da na fara nisa da inda suke.
Jim kaɗan har na kusa ficewa daga layin na ji ƙarar motarsa bayana. Fakin ya yi ya fito ya zo inda nake, kudi ya dauko ya miko mani masu yawa. Tabbas na ji dadin kyautar kuɗin har tsakiyar raina. Sai dai ban nuna masa a zahiri ba, na yi saurin girgiza kaina alamun ya bar shi.
Ajiye su ya yi a gabana, "Gasu nan Malam, ko ki riƙe su ko ki bar su, a nan duk ɗaya. Ni ba zan fasa abinda na yi niyyah ba." Yana faɗar haka ya juya ya tafi alamun ya fusata. Tsaye na yi sororo ina kallon kuɗin, a kowace rana ina neman taimakon Ubangiji, safe, rana, dare da kowane marece. "Fiii!" Ƙarar iskar wucewar motarshi ya katse min tunanina.
Bin motar na yi da ido, na duƙa a sanyaye na ɗauki kuɗin. Maimakon na tafi bara, baya na yi na koma gida, domin Allah ya hutar da ni.
★ ★
★
Kwana uku curr da dawowarsa daga Kano, amma sam ba ya jin dadin rayuwarsa, haka nan yake jinsa cikin yanayi na ƙunci da baƙin ciki, ga maganganun da kunnuwansa ke jiyo masa suna neman su zarar da shi.
Cikin sanyi ya fito daga ɗakin baccinsa a shirye, kicibus suka yi da ita a bakin ƙofa.
"My boo," ta fada tana kamo hannunsa. Sororo ya yi yana kallonta, "Ni bana son ina ganinka cikin damuwar nan, za ka samu lafiya fa, mun yi magana da Doctor ɗin, yanzu haka yana can yana jiran mu."
Kallonta yake yi kamar sabuwar halittah, ba tare da ya furta komai ba. "Mu je asibitin ka ji My Bubuna."
Shiga gaba ta yi ya bi bayanta, a nutse suke tafiya har suka isa inda ma'ajiyar motoci take. Ba don ya so ba ya shiga motar don yi tuƙi zuwa asibitin, har suka isa asibitin ta masu saukin hankali bai tanka mata ba. Wuri ya samu ya yi fakin, kai tsaye wurin likitan mai suna, Doctor Bashar suka isa.
Masauki likitan ya ba su suka zauna, cikin mutuntawa da girmama juna suka gaisa. Kallon AbuƊalib ya yi, sai da ya gama ƙare masa kallo tsaf, sannan ya fara masa wasu tambayoyi. Cikin muryarsa da ba ta cika kaifi ba ya ce, "Doctor, ni dai ba abinda ya same ni, amma wasu lokutan sai in rika jin wasu maganganu, idan na ji su kuma sai in ji suna ta min yawo a cikin kwakwalwa kamar na taba saninsu, sannan kuma wasu lokutan ina jin kaman na san wasu mutane amma kuma na gaza sanin su waye. Sai kuma ina ji kamar na aikata wani laifi, zuciyata ta yi ta ayyana mini idan na mutu daidai wannan lokacin wuta za a sanya ni. Doctor na ruɗe na rikice, cikin kwanakin da ba su na mako ba, ina nema na haukace..."
Jinjina kai Doctor ya yi. "Okay, amma ba abinda ya faru da rayuwarka?" Badiyyah da ke gefensa ta yi karaf ta ce, "Ba abinda ya faru da rayuwarsa Doctor, lafiya lau yake, a kwanakin nan abun ya same shi."
Jinjina kai Likita Bashar ya yi, sannan ya yi wasu 'yan rubuce-rubuce ya mika ma Badiyya takardar.
"Ki je nan clinic dinmu ki siyo wadannan magungunan."
"Okay Doctor," ta fada. Jikinta na rawa ta fita waje. Tsayawa ta yi tana kallon takardar, sam ba ta fahimci komai ba game da magungunan da aka rubuta. Ɗan gajeran tsaki ta ja sannan ta jawo wayarta. Juyawa ta yi gefe-gefenta ta tabbar ba kowa a wurin sannan ta danna kira. Cikin 'yan sakanni aka ɗauki wayar, "Mom, akwai matsala fa. Kamar yadda na fada maki, AbuDalib ya zama wani soko-soko haka, kansa kamar yana nema ya kwance, sai kokarin tuno wadannan mutanen yake yi. A tsorace nake, kar ya koma hayyacinsa mu shiga uku, domin duka damarmakin da muka samu za su ruguje."
Numfashi uwar ta ja, "Ai kin san hada abu dama da 'ya'yan malaman zaure akwai wahala, amma ki rabu da shi, kar ki damu ko kadan, komai zai daidaita."
"To Mom, amma fa dole sai an yi gaggawa."
"Na ce kar ki damu. Kina ji na, yanzu ki siyo maganin in sha zai yi ki ba shi ya sha, in ci zai yi ma dai haka, ke ko ma dai me zai yi ki masa. Zan warware matsalar nan da kwana biyu."
"Okay Mom. Amma na ce, Baba Alhaji na nan?"
"Yana nan."
"To ya same mu nan asibitin, don kin san magungunan sakatiri (Psychiatry) barci suke sa wa, kar ya yi barci kuma kin san ban kware a tuki ba na rasa yadda zan da shi.
"Bari gaya nan zuwa, yanzu nan zai taho," kashe wayar ta yi gaggauce ta isa clinic din.
Takardar ta mika, take suka ba ta wasu allurai tare da magunguna. Komawa ta yi cikin ofishin likitan. Iske shi ta yi ya kwantar da kansa bisa teburin da ke gaban likita. Wani kallo ya yi mata wanda ya sa cikinta juyawa, a ɗan razane ta ce, "My Boo… lafiya dai." Rufe ido ya yi ya bude, "Lafiya lau."
Doctor ya karɓi zancen, "Ba wani abu za ku samu lafiya. Yanzu sai ku mike na muku allura ko."
Tsaye ya tashi Doctor ya yi masa allura. Kafin ya zare tsinken alluran daga jikinsa barci mai kama da na tsafi ya dauke sh, a take ya faɗa jikin Doctor din gijib. Gyara shi likita ya yi ya kwantar da shi kan kujera. "Amma Doctor ya zan yi da shi?" "Ba komai, ki kira wani yayansa ko kaninsa ya zo ya taimaka maki a tafi da shi gida."
Bata rai ta yi don sam ba ta son jin zancen da ya shafi 'yanuwan AbuƊalib. "Okay, Doctor kamar na sani dama, yanzu za a zo sai mu tafi da shi ɗin."
"Ba damuwa to." Wasu magungunan ya ba su ya ce ga su nan ta tafi da su tare da lokacin da za ya rika shan su. Kudi ta zaro daga jakarta ta miƙa masa, tana maimaita mun gode sosai Doctor. Ba a fi tsayin mintuna sha biyar ba yayanta da suke kira da Baba Alhaji ya karaso. Har inda AbuDalib yake kwance suka isa, da taimakon Doctor suka ɗauke shi suka kai shi har cikin mota. Fuskarsa a daure ya ce, "Me ya same shi ne?"
"Ba ya da lafiya Baba Alhaji."
Tabe baki ya yi ya zagaya mazaunin direba ya kunna motar suka tafi. Tuki yake fuskarsa a daure, "Badiyya." Ya kira sunanta. "Na'am," ta furta tana mayar da hankalinta kansa.
"Kin ga rayuwar nan duk abinda ka shuka shi za ka girba, idan alkhairi ka shuka to alkhairi za ka girba haka idan ka shuka sharri shi ma sharrin za ka girba. Wani lokaci mutane suna yin abu kamar su ne suka halitta kansu alhali kuma duka bayi ne da suke da ubangida, yana sane da komai yana kallon komai, kuma ya sanya sharuɗa da dokoki."
"Uhmmm. Baba Alhaji to ni me ya sa kake mini duk wannan maganganun?"
"Kin san dalili mana." Shuru ya yi lokacin da suka isa get din tamfatsesen gidan. Ba kowa gidan sai jefi-jefin masu aiki, kama shi suka yi suka kai shi har zuwa bedroom dinsa, barci yake tamkar matacce. Jawo kofar dakin ta yi ta rufe, Wani kallo Baba Alhaji watsa mata sannan ya buga tsaki.
"Baba Alhaji wai duk me ya faru kake ta min wannan abun?"
"Badiyyah, kina bata min rai da wannan tambayar. Ni dai ina fada maki, abinda ka yi kamar jifar mashi ne, kai ka jefa amma ba ka san kan wa zai sauka ba duk iya yaƙininka, ko ya samu wanda ka sai ta, ko kuma ya samu wani wanda ba ka tsammani. Wannan ne abun tunanin ina zai fada. Na barki lafiya sai anjima." Bin shi ta yi da wata muguwar harara tamkar za ta yado idanuwanta. Dogon tsaki ta ja, a hankali ta ce, "Allah ya raka taki gona, wani jaye-jayen masifa. Ni kam na samu abun harina tunda har na kafa daula."
Wani tsakin ta ja ta baro sashen shi, ta yi sashenta na kasa.
____________________
★
Kwance take kan gado wanda ko shimfida babu, hannunta sakale da igiyar karin ruwa, numfashi take mayarwa tamkar yana neman ya gagareta.
"Umma, don Allah ki taimaka ki bari na je gidan Yaya ya taimaka mana da kudin magani, kar mu rasa ki Ummanmu, don Allah."
Kada kai ta yi, da kyar ta ambaci sunanta, "Rumaisa… watakil ke kina da ɗanuwa amma ni ba ni da wani ɗa, idan kuma kika je gidan AbuDalib ki sani kin je ba da yawuna ba, ba zan taɓa yafe maki ba." Hawaye masu dumi da suka gangaro mata ta share, "Umma don Allah ki gafarce ni ki taimaka don Allah..." Ta ƙare zancen muryarta na rawa.
"Idan kin gaji da zama inda nake, ki tashi ki tafi wurin ma ci amanar Babanki, ki cigaba da zama da shi. Ni dama gabar da nake ina kaunar mutuwa ne sama da rayuwa."
Dafe kanta ta yi ta hadiye yawun da ya yi mata tsaye a makoshi kamar dutse. Cikin muryar kuka ta ce, "Shi ke nan Umma, ni ina tare da ke, ba zan taba tafiya ko’ina in bar ki ba, kuma ina nan ko mutuwa za ki yi mu mutu tare."
Rufe ido wacce ake kira da Umma ta yi, wasu 'yan kudi ta mika mata, "Ga shi ki hau abun hawa ki dauki wannan zoben nawa, ki je kasuwa ki sayar da shi."
"Shi ke nan Umma, idan na tafi kuma wa zai zauna nan?"
"Ki kira min Uwale ta zauna nan kafin ki dawo." Jinjina kai ta yi da sauri ta kira Uwale, cikin mintoci kadan ta kira Innarta Uwale ta iso. Fuskarta cike da hawaye ta durkusa gefenta, "Babbar yaya… Jikinki nisa yake yi, haka za ki zauna cikin wannan halin? Don Allah ki bari a shiga lamarin nan."
"Uwale… ba kiran ki na yi ki min wannan maganar ba. Ki kula da ni kafin ta je kasuwa ta dawo. Shi ma don kar na cika ba kowa a kusa da ni wanda zai maimaita mani kalmar shahada idan mutuwata ta zo."
SH 4
RUMAISA
Abaya kawai ta saka ta fita, Keke Napep ta hau zuwa kasuwar central market, tana isa ta ƙarasa layin masu siyar da gold, ciro zoben ta yi daga aljihun rigarta, tsayawa ta yi bakin shagon tana kallon zoben, shi kaɗai ya yi masu saura a abinda suka mallaka, idan suka siyar ba su da wani abun ƙaddara da za su cigaba da fuskantar rayuwarsu. Wani abu mai tauri ta hadiye cikin makoshinta, take hawaye masu ɗumi suka tsiyayo daga idanuwanta. Da sauri ta juya ta bar ƙofar shagon, da sassarfa ta fita bakin hanya inda za ta samu Napep, 'yan kuɗin da suka rage mata ta duba, "Ɗari uku," ta furta tana fitar da wani huci. Ba ta karaya ba ta tsayar da mai Napep ta ce ya kai ta Modoji, cikin sa a ya amince zai kai ta da kuɗin da suka yi mata saura.
Bakin tamfatsetsen gidan Yayanta aka sauke ta, tsaye ta yi tana kallonsa, katon gida ne da ya ji gini na tsara, ko ba a fada ba kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar mamallakinsa ya tara manyan kuɗaɗe.
"Idan kuma kika je gidan AbuƊalib, ki sani kin je ba da yawuna ba, ba zan taɓa yafe miki ba..." Wasu kalaman Ummanta suka soma yawo cikin ƙwaƙwalwarta. Hawayen da suka zubo mata ta sharce, "Rayuwar Ummana na cikin haɗari, sannan kuma ga rashin amincewarta a kan zuwana nan... Wannan shi ne gaba kura baya sayaki..." Hawaye suka sake wanke fuskarta. "Ya Allah ka sa ni ba da son raina na ƙi bin umarnin mahaifiyata ba, ina son ceton rayuwarta ne, Allah ka yafe mini." Tafiya ta yi ta isa daidai ƙofar, kwankwasa wa ta yi sannan ta tsaya tana dakon jiran a buɗe mata.
Mai gadi ya leƙo, kallonta ya yi sama da ƙasa sannan ya ce, "Hajiya barka da zuwa." Ba ta amsa mishi ba saboda ba ta cikin yanayin da za ta amsa mishi.
"Ammm Hajiya Rumaisa, Hajiya ta ce kar a bari ki shiga gidan nan..." Ya faɗa cike da jin nauyin kalaman da furta mata. Wani kallo ta watsa mashi, "Salahu, ni kake faɗawa wannan zancen? To, da ni da Hajiya wa ya fi matsayi a cikin gidan nan, ina iya dawwama a cikinsa ita kuma wata rana za ta iya yin waje ta bar shi, kuma wallahi sai na shiga cikin gidan nan." "Hajiya na sani, amma ki yi hakuri, cewa ta yi idan na bari kuka shigo bakin aikina..." Cikin bacin ran da ke nuƙurƙusarta ta hankada shi har ya fadi ƙasa, da gudu ta shige ciki, harabar gidan babba ce kafin ta isa wurin da zai sada ta da ƙofar shiga falon tafiyar da 'yar tazara. Hakan ya sa har Salahu mai gadi ya iya cimma ta. Muryarsa a rikice, yake maimaita, "Hajiya don Allah kar ki mini silar aikina..." Sam ba ta sauraren shi sai ma ƙara ƙaimi da ta yi don isa bakin ƙofar.
BADIYYAH
Ta tagar bene ta hango su, ɗan guntun murmushi ta saki sannan ta mike ta bude kofa ta leƙo, cikin isa da kasaita ta ce, "Kai Salahu bar ta ta shigo." Tsayawa ya yi, ita ma cikk ta tsaya daga kai ta yi ta kalle ta, ta ɗora hannuwanta kan bagalar benen ta yi kyau sosai ta ƙara kiba da haske tamkar wata matar Gwamna. Wasu kwalla suka zubo mata, ɗan adam kenan ka yi ma shi rana ya yi maka dare, har abada ba za ta taba mance Badiyyah ba a cikin kundin tarihin rayuwarta. "Lafiya kika zuba min ido?" Ɗan firgigi ta yi, a hanzarce ta sa ƙafa ta cigaba da tafiya. Badiyya juyawa ta yi ta koma cikin dakin, ita ma cigaba da tafiya ta yi ta shiga cikin falon gidan.
Ƙarema falon kallo take ya zame mata sabo kamar yau ta fara ganinsa, cike da yake da kayan alatu tamkar falon wani basarake. Kallon sashen "Yaruwarta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 14