Share this page
na yi a raina ina faɗin, "Insha Allah na kusa aure, Yaya za su zauna da matarsa lafiya, domin rabin matsalolin zamansu a dalilina suke faruwa. Miƙewa na yi na shige bedroom ɗinmu, akwatina da ke kan wardrobe na sauko, buɗe shi na yi na fara fito da kayan da ke ciki wanda ba kayan sawa ne a jiki ba kayane masu muhimmanci na adana ciki. Wata leda wacce ke ƙasa gaba ɗaya na ɗauko, buɗe ta na yi a nutse wanda ledar ita ma cikin wata ledar take, sai da na fiddo ta gaba ɗaya sannan na kwance wadda ke ƙasa duka. Wasu takardu ne a ciki wanda sai a yanzu na gane ma'anarsu. "Wace ma'ana gare su Lilbirrah?" Yunus ya tambaye ni. Nisawa na yi ina kallon shi, "Yaya Yunus, a cikin labarina babu abinda zan ɓoye maka, a hankali za mu kawo kan ma'anar tasu." "Am sorry," ya faɗa cikin lallausar murya. Kallonsa kawai na yi sannan na kauda idona na cigaba da magana. "Takardu ne a ciki kowace a jikinta akwai rubutaccen sunana, sai dai sam na kasa gane ma'anar rubutun da ke jikinsu, sai kuma wasu kyawawan 'yan hannu (awarwaro) na zinare guda sha shida, sai sarƙa haɗe da 'yan kunne manya masu masifar kyau, dukansu na manya ne ba size ɗin hannuna ba." Shuru na yi ina tunani, "Lilbirrah waɗannan 'yan hannu da sarƙar na mallake su tun kina 'yar ƙanƙanuwa, kuma tun a lokacin na mallaka maki su halak malak, dukiyarki ce ki yi yadda kike so da ita, ko Babanki ba zai ce don me ba, domin na mallaka maki ita, ke ko ni da kaina ba ni da iko a kanta taki ce. Sai dai abinda nake so da ke, ki bari sai kin kai kimanin shekara talatin ki siyar da su ki cigaba da kasuwanci..." Motsin da na ji ya sa ni yin firgigi, Umma na gani tsaye wanda ban san lokacin da ta shigo cikin ɗakin baccin ba. Cike da mamaki ta ce, "Shalele, me za ki da wannan kayan da kika ɗauko?" Tsuru-tsuru na yi ina kallon Umma. Zama ta yi tana fuskantata, "Lilbirrah ko akwai wata shawara da kika yi a kan waɗannan kayan ne?" "Umma me ya sa ke ba za ki kasuwanci da kuɗinsu ba?" Kamar daga sama na ji ina tambayarta. Kallona ta yi a nutse, "Shalele, saboda na yi alƙawari cewa na mallaka miki su har abada ba zan yi wani abu da su ba." Nisawa na yi, "Ummanm to me ya sa kika ba ni ni kaɗai? Ga Yaya AbuƊalib ga Rumaisa." "Kin san cewa AbuƊalib ɗan mariganyiya ne ko? Rumaisa kuma daga baya ta zo, a lokacin da har na fitar da ran zan ƙara haihuwa, ke ce tawa ke na fara samu, shiyasa na mallaka miki su." Ta ƙare maganar tana murmushi. Ni ma murmushin na yi sannan na ce, "Umma yanzu zan iya sayar da ko 'yan hannun ne na hannu guda na yi kasuwanci?" "Sosai kuwa Shalelen Umma da Yayanta, amma ki faɗa min wace irin kasuwa ce za ki fara, a ina take wa ke yin ta?" Fuskata da murmushin da ya yi mata mayafi na ce, "Umma babu wata kasuwar da zan fara, da ma game da maganar da na yi maki ne jiya na kasuwar Crypto da Yaya yake so ya fara, abun yana ransa ya zauna mashi sosai, sai tunani yake ya siyar da gidansa da motarsa da sauran 'yan abubuwan da ya mallaka, ni kuma bana so ya yi hakan, idan aka samu matsala asirinsa zai tonu, wannan ko ba wanda ya sani." Shuru ta yi irin na mai nazari can kuma ta nisa ta ce, "Lilbirrah ke kin amince ki siyar da wannan 'yan hannun ki ba shi kuɗin ya yi kasuwar Crypto?" "Eh Umma, wallahi na amince ɗari bisa ɗari." "Shi ke nan, ki fiddo 'yan hannun guda takwas ɗin kuma ki gaggauta mayar da sauran a ma'ajiyarsu, kamar yadda kika sani bana so Rumaisa ta san da labarinsu." Jinjina kai na yi, "Umma ba za ta sani ba Insha Allah, ba zan taɓa karya maki alƙawari ba." "Yawwa Shalele, sai kuma ki kira AbuƊalib ɗin ki ce ina neman sa." "To Ummana," na faɗa zuciyata cike da farin ciki da jin daɗi. Mayar da kayan na yi kamar yadda suke sannan na ɗauki awarwaron guda takwas na adana su cikin wardrobe. Muna fita falo na dauki waya na kira Yaya na sanar da shi Umma na kiransa. Bai jima ba ya zo. Umma ta ce na tafi ɗakin Anty za su yi magana. Sam ban ji komai ba, domin kuwa na san za su yi magana mai muhimmanci da ba ta shafe ni ba. Ina shiga ɗakin Anty sabon saurayina Jamil ta kira ni muka cigaba da hira. An kai kimanin mintuna talatin sannan Umma ta kira ni Yaya na zaune yana min wani kallo tamkar lokacin ya fara ganina. Umma ta ce, "Mun yi magana da Yayanki, ya amince zai karɓi 'yan hannun amma na sa sharaɗi Shalele, duk idan aka sayi haja aka siyar za a raba ribar gida uku a baki kashi ɗaya ya ɗauki kashi uku." "Ummana, Yaya AbuƊalib ne fa, ni ba sai ya ba ni komai ba." Kaɗa kai ta yi ta ce, "Na san haka Lilbirrah amma haƙƙinki ne, dole a fitar maki da haƙƙinki." "Umma..." Hannu ta ɗaga ta dakatar da ni, "A yi abinda na ce kawai." Jinjina kai na yi, "To Ummana." Miƙewa ta yi zan je na faɗawa Babanku sannan a zo a yi rubutu sannan a je kasuwa a siyar a ba shi kuɗin. Jinjina kai kawai na yi, domin yadda Umma ke yi tamkar ba ta san Yaya ba, ya ba ni mamaki, amma ni a nawa ganina abinda na mallaka zan iya mallakawa Yayana, shi mai iko da dukiyata ne da duk abinda na mallaka. "Lilbirrah," ɗaga kai na yi na kalli Yaya yadda ya kira ni cikin wani kalar sauti. "Ba kya jin komai ki mallaka min abinda yake mallakinki ne, wannan tanadi ne da Umma ta yi maki don rayuwarki ta gaba " "Yaya to me ye ni ba zan mallaka maka ba, ka yi mun abinda ba wanda ya yi min a duniya, ko aure na yi mijina ba zai yi min kwatankwacin abinda ka yi min ba. Kuma na sani da a ce kai ne a matsayina tuni ka siyar ba tare da wata shawara ba." "Haka ne, m" ya faɗa yana fitar da wani nannauyan numfashi. "Nagode sosai, Allah ya saka maki da alkhairi." "Amin Yayana." SH 20 ABUƊALIB Miƙewa ya yi domin tafiya gida, a sanyaye yake tuƙi yana yi yana kallon hanya, zuciyarsa cike da tunanin Lilbirrah, wani irin matsayi da girma yake ji ta ƙara a zuciyarsa, irin matsayin da baya iya kwatanta shi a zuciyarsa. Karo na farko da ya ji wani abu mai ƙarfi yana fizgar zuciyarsa a kanta, lumshe idanuwa ya yi ya karya motar kan kwanar gidansa yna cigaba da tunaninta. ★★★★★ Kashegari bayan an gama rubuce-rubucen da sa hannu muka tafi kasuwa aka siyar da 'yan hannun wanda suka bayar da kudi kimanin naira miliyan ashirin da hudu kasantuwar 'yan hannun manya ne sosai kowane dayansu an sayar da shi Naira miliyan uku. Cike da mamaki na ce ma Ummana, "Umma kenan tsakanin wancen da wannan 'yan hannun har da sarkar za su yi miliyan hamsin ko?" "Za su fi haka ma Lilbirrah 'yar Ummanta." "To Umma me zai hana a ce ba a siyar da su gaba daya ba sai mu yi kasuwanci watakil da yanzu ma mun zama masu kudi." "Uhmm, hakkinki ne Lilbirrah lokacin da za a yi hakan idan ya zo za a yi." "To amma Ummah dukiyar fa asalinta taki ce, to don me za a mallaka min ni, ni kaɗai?" Kallona ta yi da murmushi a fuskarta ta ce, "Ban san ki da yawan tambaya ba Lilbirrah, ki daina kin ji." "Ummana na daina," na fada ina kwantar da kaina kan kafadarta. Shi ko Yaya yana gaba yana driving motarsa, ko kadan bai tanka mana ba, yana dai saurarenmu. Hira muke yi mai daɗi ni da Umma har muka isa gida, da ma kuɗin account ɗin Yaya aka tura su gaba ɗayansu, yana aje mu ya juya domin tafiya gida, ita kuma Ummana ta yi masa fatan samun nasara. A ɓangarena cikin kwana biyu da haduwarmu da Jamil ya bukaci zuwa gidanmu, ban hana shi ba na fadawa Umma duk yadda muka yi da shi tun farkon haɗuwarmu. Jinjina kai ta yi ta ce, "Alhamdulillah, ina jin dai wannan za a yi da shi, tun da ga shi har an gabatar min da shi." Duƙar da kaina na yi ina murmushi. "To bari na faɗawa Babanki, idan ya ba da damar zuwan, sai ki faɗa mashi." "To Ummana," na faɗa. Tashi ta yi don ta isar ma Baba sa saƙona. Cikin sa a kuwa tana zuwa ta fada mashi ya amince, hakan ya ba ni damar ba wa Jamil izinin zuwa wurina. Ranar da ya zo mun sha hira sosai a yadda na fuskanci Jamil mutumin kirki ne sannan yana da nutsuwa sosai, hakan ya sa na ji ya kwanta min a rai. ★★★ ABUƊALIB Kai tsaye wajen Yeaster ya je domin yin maganar kasuwar Crypto, cikin nutsuwarsa yake kallon Yeaster bayan ya faɗa masa duk yadda aka yi ya samu kudin, "Ka yi nasarar sace hankali na Yeaster." Murmushi ya yi yana kallonsa sai da ya kurɓi ruwan kwakwa da ke hannunsa sannan ya ce, "AbuƊalib ba za ka yi nadama ba, ina tabbatar maka za ka yi farin ciki, kuma ba za ka same ni na cuce ka ba, babu abinda zai samu dukiyarka domin a halin yanzu exchanger ta Binance, ko Vault ma fi tsaro a duniya wanda ke akwai ɗaiɗaikunsu a shahararrun ƙasashen duniya, bai kai wannna Exchanger ɗin tsaro ba, domin akwai tarin tiriliyoyin daloli a cikinta, ba manyan masu kuɗin duniya, kai har ma sa wasu ƙasashen suna saka hannun jari domin ƙarin tattalin arziƙinsu. Saboda haka ba abinda zai samu dukiyarka ka shiga harkar trading da nutsuwa za ka yi dariya da farin ciki za ka gane alkhairi nake nufinka da shi." "Shi ke nan abokina Yeaster, Allah ya ba mu sa'a." "Amin." "Ka san Yeaster, ina jin kudin nan dukiya ma fi girman daraja a gare ni, bana jin akwai wani abu da ya fi ta ƙima a wurina." "Kai, abokina kaunarka da sister ɗin nan taka tana birge ni, da a ce wannan ba sisrer dinka ba ce uwa daya uba daya ba da na ce ka aureta, tabbas za ku yi zaman farin ciki saboda kuna kaunar juna kuna son ganin farin cikin junanku." Shuru ya yi yana kallon Yeaster da ke ta zuba zance. Murmushi kawai ya yi ya ce, "Yeaster yanzu me zan yi na gaba?" "Za ka yi register da makarantarmu da ke Kano wacce za ka ƙara gogewa a harkar, kuma na maka alƙawarin da duk iyakar iyawata zan taimaka maka abokina." "Nagode Yeaster." AbuƊalib ya fada yan ba shi hannu suka tafa. Ƙara tatttauanawa suka yi sosai a kan harkar sannan AbuDalib ya yi bankwana ya bar wurin. Tafiya yake yana driving amma zuciyarsa cike take da fal da tunanin Lilbirrah wanda abun har ya soma yi masa yawa ya fara tsikarar walwalarsa ta yau da kullum. Kwana ya yi ya nufi wajen abokinsa AbdulJalal, yana isa Abdul ya gan shi very week. Cikin kulawa ya ce, "Ya ne abokina me ke faruwa ne na ganka sai a slow." Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sai da ya nisa sannan ya ɗora idanuwansa kansa suka yi kallon ido cikin ido, a sanyaye ya buɗe baki ya ce, "AbdulJalal, ina cikin matsala." "Matsala kuma AbuƊalib ta me?" Abdul ya tambaye shi cikin tsantsar damuwa. "Abdul zuciyata ce ke neman saka ni a wata koma wacce nake da tabbacin za ta ba ni wahala, na sani da wahalar gaske na wanye da ita lafiya." "Komar me kenan AbuƊalib? Faɗa min da sauri." "Ji nake zuciyata na bugawa da so da kaunar Lilbirrah, so irin na aure wanda za mu kasance mata da miji ni da ita Abdul." Kallonsa ya yi baki sake, "AbuDalib kana sane da abinda kake fadi kuwa?" "Ina sane mana Abdul shi ya sa ma na faɗa ma, domin damuwar ita ke diddigar zuciyata a cikin yini biyu tana neman fitar da ni hayyacina. Kuma na bayyana maka ita a lokacin da ba wanda ya san da ita idan ba ni ba, na bayyana maka a matsayinka na namiji ɗan uwana wanda zai iya kintata zafi da raɗaɗin da ke raina, abokina na fada ma don ka ba ni mafita." Numfasawa Abdul ya yi, "AbuDalib ta wace fuska za ka tunkari Lilbirrah da zancen soyayyah, soyayyah irin ta aure? Bayan kai tana daukarka a matsayin Yayanta ɗanuwanta na jini, ina jin hakan zai zo mata banbarakwai AbuƊalib." "Abduljalal, Lilbirrah tamkar ɗaya ce a cikin dubu, ta ya zan yi sake matar da ake kira daya a cikin dubu ta kuɓuce daga hannuna, bayan ina da damar mallakarta, Abduljalal ka san Lilbirrah fa, ta cika kamalar da ake so kowace mace ta kasance da ita." "AbuƊalib, ni ko na san Lilbirrah, yarinyar da ta tashi a gabana tun daga yarinta har zuwa girmanta, na sani tun tasowarta yarinya ce nutsattsa, mai burin aikata alkhairi da kyautatawa, bana manta lokacin da take debo ruwan Umma da soɓonta a fridge ta kawo mana idan na je wurinka, sannan kuma abincin kowa ta samu a kitchen sai ta kawo min, tabbas ina tuna wannan halin nata na karamci. Sannan ga ta da tausayi, na sani saboda ita aka rika ba wa Aminu wannan almajirin naku abinci har zuwa yanzu da ya girma ya zama saurayi ita ta yi dalilin girmansa a hannunku. Na sani halayen kwarai irin nata kam abin so ne kuma duk wanda ya aure ta ya yi dace mai yawa, ilimi, hankali, nutsuwa, tarbiyyah sanin ya kamata kyawawan halaye duk ta haɗa Abokina, sai dai ina jin ka yi sake AbuƊalib samunta wurinka zai yi wuya." "Abdul ina sonta, ina son in aure ta, kuma Lilbirrah ba ta da wani miji bayan ni." Murmushi ya sakar mashi, "Abokina mai sa wukaken, ban ce ba za ka aure ta ba, abun ne dai da kamar wuya. Amma ai kai namiji ne za ka iya jarabawa, za ka iya kwantanta sa'arka, ba zan dakushe ka ba Allah ya ba da sa a yasa kana da rabo." Numfashi ya sauke sannan ya ce, "Yawwah, ka ji abinda ya kamata ka faɗa min tun farko." Shuru ya yi shi kuma Abdul ya miƙe domin kula da sana'arsa inda yake siyar da baƙin mai. Shi kuma AbuƊalib ganin zaman ba mai yi masa ba ne ya sa ya mike ya nufi gida. Zaune ya iske ya Badiyya tana waya da Mamanta, ganinsa ya sa ta katse wayar a dakile ta ce, "Sannu da zuwa." "Yawwah," ya fada. Mikewa ta yi ta kawo mashi abinci, "My Luv ka dade da fita hala ka biya wajen su Umma ne?" Kallonta yake irin kallon da ya saba yi mata sarai ya fahimce ta a rayuwarta ta tsani ya ce ya je gidansu, ba don komai ba saboda ƙawarta kuma 'yaruwarsa Lilbirrah. "Ban je gida ba, wata sabgar dai ce ta tsaida ni." Ya ba ta amsa. "Okay," ta fada tana sakin fuska. "Cikin satin nan zan je Kano, wataƙil jibi ko gata." "Wurin me My Luv." "Sabon kasuwancin da zan fara, zan je domin samun horo na musamman." Shuru ta yi tabbas a laben da ta yi ta ji zancensa kaf a kan kasuwancin, tamkar ta tambaye shi a ina ya samu kudin sai kuma ta yi shuru, me ya ma damuwarta a kan ina ya same su, ai ita ribarsa ita ce tata. "Kika yi shuru," ya faɗa yana kallonta, domin gaba ɗaya ta tafi ta faɗa duniyar tunani. "Allah ya kai mu lafiya My Luv." "Amin," ya fada yana cigaba da cin abincinsa. BAYAN KWANA BIYU Tunda safe ina zaune Yaya ya shigo kamar yadda ya saba, waya nake yi da masoyina Jamil, mikewa na yi na koma bedroom na bar shi suna gaisawa da Umma. Mintuna biyu na kara sannan muka yi bankwana da shi na fito domin gaishe da Joonam. Ina fitowa na same shi zaune suna magana da Umma, a mamakina sai na ga fuskarshi ta dan canza, sai wani kallo da yake min kamar harara. "Yayana na kaina," na fada fuskata da fara'a. "Na’am," ya fada a takaice. "An tashi lafiya, ya ƙawata." "Ta tafi gidansu sai bayan na dawo." "Yanzu daga nan sai Kano?" "Eh." "To Allah ya kiyaye." "Amin." Mikewa ya yi fuskarsa a hade, "Sai na dawo." Umma ta ce, "Allah ya kiyaye Allah ya ba da sa'a." "Amin," ya faɗa lokacin har ya kai bakin ƙofa. Bin sa na yi da idanu, da hanzari na bi bayan shi, "Joonam, me ya faru ne na ga tafi haka?" Kallon harara ya yi min, "Ina shigowa kika wani tashi kika yi tafiyar ki." "Joonam, ina waya ne shi ya sa." "Ohh, yanzu har akwai mai matsayin da za ki iya watsar da ni kansa ko?" "A'a Joonam, sam ba haka ba ne." Ɗan guntun tsaki ya ja ya cigaba da tafiyarsa. Bin sa na cigaba da yi har bakin ƙofar fita, "Joonam ka yi haƙuri," na faɗa kamar mai shirin kuka. Juyowa ya yi ya kalle ni, "Ya wuce Khouhar." Hannu ya sa zai buɗe ƙofar fitar sai dai maganar da na fara ta tsayar da shi, "Yaya ka ga ni hanya za ka hau, don Allah kar ka manta idan ka tafi ka yi sadaka, sannan, nan wajen Welcome to Katsina ma ana samun almajirai a wurin don Allah Yaya ka yi sadakar kar ka mance ka san Manzon Allah S. Ya ce, "Idan za ku yi tafiya ku sayi hanyah, ma'ana ku yi sadaka kenan." Kallona kawai yake yi irin kallon da sam bai saba min irin shi ba, duk da kasancewar ina jin sa a matsayin ɗanuwana na ji wani kala a raina, ina jin cewa kallon ya yi yawa. "Joonam." "Na’am," ya fada. "Kar ka manta don Allah, ba zan mance ba ai kin fada min." "Allah ya ba da sa a da nasara, Allah ya kiyaye ku je lafiya ku dawo lafiya." "Allah ya sa Khouhar." Murmushi na yi, "Yaya za mu yi kewarka, za mu yi kewar sammakon nan naka. Muna nan muna dakon dawowarka, Allah ya bada sa a." "Amin Khouhar, ni ma zan yi kewarku sosai." "Allah sarki Yaya, ka tafi ina tsaida ka da surutuna." 'Yar fara'a ya yi bai ce komai ba ya buɗe ƙofar ya fita, leƙawa na yi domin ganin tafiyarsa, a rayuwarmu sam shi ba ma'abocin tafiye-tafiye ba ne, hakan ya sa tafiyar da zai yi na ji ta wani kala. A kan idona ya tayar da motar, hannu ya ɗaga min, "Sai ka dawo Joonam, ka kula sosai don Allah." Jinjina min kai ya yi sannan ya silala motar a nutse ya bar ƙofar gidanmu. Juyawa na yi na koma cikin gida zuciyata cike da kewarsa da tunanin tafiyarsa. BADIYYAH Kwance take kan kujera, a sanyaye ta ce "Mama." "Na’am," Maman da ke gefenta ta amsa tana ba ta hankalinta. "Wannan tafiyar da AbuDalib ya yi tafiya ce da za a kara mashi haske a kan wani sabon kasuwanci da ya zo. Mama ni fa bai fada min ba, ba ma ni da wannan matsayin, sai dai na tsinkayo su suna hirar shi da wannan munafukar 'yaruwar tasa." Nisawa ta yi ta ja dogon numfashi, "Umma na ida tsanar Lilbirrah, na tsane ta tsana mai yawa tunda na ji wai ba uwarsu daya ubansu daya ba da AbuƊalib. Wallahi Mama kullum jinina kan akaifa yake ji nake zai iya aurenta Mama, yana matukar kaunarta irin kaunar da Allah ne ke dasawa bawa ita a rai." Uwar ta karɓi zancen da, "Badiyyah tunda kika fada min ni ma hankalina bai kwanta ba don ma dai kin ce min yanzu ta samu saurayi kin ga sai zancen aure kenan." "Ni ma nutsuwata kenan Mama ba don haka ba da ban san ya za a yi ba, wallahi ko Mama." "Kar ki damu ɗiyata, ai yanzu aka zo wurin. Na fada maki in dai ina raye ba zan taba bari ki koka ba kuma a yanzu aka zo wurin mijinki zai samu dukiya yana juya kuɗi ai dole ya riƙa juye mana su." "Haka ne Mamana. Da ma ni ma tsoron da nake kenan kar ya samu ya dinga juye ma Umman nan tasa da ita 'yaruwarshi ɗin." "Yanzu dai ba kince zai fara kasuwanci ba, kasuwanci ma na manyan kudade ko jarin da ya shiga da shi ya kai miliyan talatin kika ce." "Haka yake Umma, kuma ba ma wannan ba cewa aka yi idan kasuwa ta yi kyau har kudinsa yana iya linkawa cikin 'yan watanni kaɗan." Zaro ido uwar ta yi, "Wai da gaske kike ko dai shaci fadi ne?" "Wallahi Mama da gaske ne duk abinda yake ai ina bibiyarsa shi kanshi bai san na sani ba." Nisawa ta yi, "Lallai yanzu aka fara wasan, yanzu ne lokacin da zan tashi tsaye domin nema maki 'yanci da lafiyayyar fada a wurinsa. Miliyan talatin..." Ta ƙare zancen tana jinjina lamarin. An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 14 of 14