ta yi, wasu sabbin hawayen suka zubo mata ta yi saurin gogewa. Badiyya ta ƙaraso ta zauna kan kujerar da ke kallon ta Rumaisa.
Cikin sigar rainin wayo ta ce, "Rumaisa’u sannu fa, ya gida ya su Iya?"
"Uhmmm,' kawai Rumaisa ta furta, cikin ƙyama da tsanarta ta ce, "Da ma ba wurinki na zo ba, wajen Yaya na zo, yana nan?"
"Na ce ba, na sha fada muku ku daina neman sa, saboda baya da lokacinku abubuwa ma sun masa yawa, lokacinsa nawa ne ni kaɗai. A gare ku kuma ni wakiliyarsa ce, so me ye damuwar? Rashin abinci ko? Nasan ma fi yawan matsalar talakawa ta yunwa ce." Rumaisa ba ta iya furta komai ba sai na mujiya da ta zuba mata. A wulaƙance ta ce, "Laure, Laure, Laure..." Da sauri ta ƙaraso, "A kawo mata abinci..." ta ƙarashe maganar tana kallon Rumaisa.
Muryarta na rawa ta ce, "Badiyya ke ma kin sani tun da kika san mu ba mu da yunwa, kuma har kika shiga cikin rigar arziƙinmu kina wulaƙanci ba ma nema wurin ki. Ke, ke ce dai matsiyaciya, mayunwaciya, butulu. Kuma ki sani wata rana sai kin kwashi kashinki a hannu sai kin girbi abinda kika shuka, indai rana na fitowa dare na maye gurbin haskenta da duhu."
Shuru ta yi tana mata kallon rainin wayo. "Ga abinci nan an kawo miki ki ci na san matsalarki dai duk ta yunwa ce, ita ta sa kike wannan ɗumumuwan."
Hawaye suka kara wanke fuskarta, a hankali ta ce, "Ina son in ga ɗanuwana." Harararta ta yi, "Ai fa sai ki ci gaba da yi."
Mikewa ta yi ta haye matakalar bene inda part ɗinsa yake, da sauri ta bi bayanta, "Ba inda za ki je na gaya maki."
"Wallahi sai na je tunda na tabbata ɗanuwana yana nan." Fizgo ta ta yi baya hakan ya sa ta gangaro daga kan benen, tim ta faɗa ƙasa. Dagowa ta yi jin yadda kanta da kirjinta suka bugu da ƙasa, Mikewa ta yi, daga inda Badiyya take ba ta motsa ba sai kallonta da take yadda ta dafe kanta. Juyawa ta yi ta haye benen, ba ta jima ba ta dawo, Rumaisa na tsaye inda take ta fito. "Na ga kamar kanki ya ɗan bugu, ga wannan ki sha paracetamol." Kudi ta tilla mata bandir daya na kilon Najeriya. Hannu ta sa ta dauki kudin. "Ba zan ƙi ɗauka ba saboda haƙƙinmu ne, amma Insha Allah kudin nan da kike jeho wata rana sai kin nemi daya daga cikin darinsu kin rasa, ƙarya fure take ba ta 'ya'ya."
"Yar dariya ta yi sannan ta shige part dinta har da bugo kofar da karfi don ta ji. Jinjina kai Rumaisa ta yi sannan ta juya ta nufi kofar fita. Tafiya ta cigaba da yi tana yi tana zubar da hawayen baƙin ciki, ba za ta fada ma Ummanta cewa ta karbo kudin wajen Badiyya ba, za ta yi shuru tare da fada mata wani ya taimaka mata da su.
Kai tsaye gida ta wuce, samu ta yi Umman na barci, sai Inna Uwale zaune gefe ta zuba tagumi. Ganin ta ya sa ta sauke hannun, "Nawa aka sayi zoben?"
Juyawa ta yi ta kalli Umman, tabbas bacci take yi. Durƙusawa ta yi wajen Inna Uwale, muryarta ƙasa-ƙasa ta ce, "Inna na je gidan Yaya ne, sai dai ƙudirina na ganinsa bai yiyu ba... Inna Uwale anya ko za mu sake ganin Yaya AbuƊalib? Anya zai sake dawowa cikin rayuwarmu?" Ta ƙare zancen hawayenta na ƙara yawa.
"Za mu sake ganin shi, kuma zai dawo gare mu, saboda ƙarya fure take ba ta 'ya'ya, ki bar ta ta sha sharafinta, wannan na ɗan lokaci ne kamar ƙiftawar ido da bismillah za ki ga komai ya warware gaskiya ta ɗauki kambunta." Numfashi mai ɗumi Rumaisata furzar. Kuɗin ta fiddo daga cikin abaya ta miƙa ma Inna Uwalen, "Dubu ɗari ne Inna, abun baƙin ciki da takaici jifa ta ta yi da su." Kaɗa kai kawai Inna Uwale kawai ta yi. "Yanzu tunda an samu waɗannan 'yan kuɗin asibiti za mu koma, a yi mata awon nan da suka ba da."
"To Inna, ni ma shi nake ta so a yi, saboda jikin Ummana ƙara nisa yake yi, kullum jinina kan akaifa yake Inna..."
"Insha Allahu ba abinda zai same ta, ai cuta ba mutuwa ba ce za ta ji sauƙi Insha Allah. Kuma zan yi duk yadda zan yi a shiga lamarin nan."
"To Inna Allah ya ba da sa a."
"Ameen." Ta faɗa.
★★★★★
Kuɗin da Yunus ya ba ni kamar yadda ya faɗa mini sunanshi suna da dama, a dunƙule naira dubu ɗari uku ne domin daurin Kilon Najeriya ne uku a haɗe. Na ɗauki kwanaki masu tsayi ban fita don bara ba, sai dai kamar yadda nake zuwa barar ina fita ina bayar da sadaka a cikin kuɗin da Yunus ya ba ni. Tun daga ranar ban sake saka shi a idona ba, domin bai sake zuwa inda nake ba, duk da na ta'allaƙa rashin ganinsa da nake yi a kan rashin zuwana Ipaja bara da safe lokutan da ya fi zuwa yana bayar da taimako. Na fi zuwa da rana bayan na gama 'yan abubuwan da nake, gami kuma da cikin jikina da ya ƙara mini nauyi.
Juyin da abun ƙaunata ya yi ya dawo hayyacina, hannu na ɗora kan cikina, zancen da muka saba daga zuciya zuwa zuciya muka fara, "Abun ƙauna... Yau ba mu gaisa ba ko? Amminka tana gaishe ka, ya ka wayi gari?" Shuru na yi ina sauraren shi, ina ji kamar yana amsa mini. "Yawwah kana lafiya ko abun ƙauna. Ni ma ina lafiya, kuma na daina shan wahala sosai, ai ka gani ko abun ƙauna."
Na daɗe zaune ina hira da halittar da na fi ƙauna a cikin duniyata, wacce ba ni da masaniya game da jinsinta, ina dai tsananin ƙaunarta sama da son da nake yi wa ruhin da ke manne da gangar jikina. Sai da na yi mai isata sannan na miƙe. Bokiti na ɗauka da kwandon wankana, wanda na samu damar siyen su bayan na samu kuɗin da Yunus ya ba ni. Ruwan da Ayuba ya tara mani na ɗiba na fita domin yin wanka.
Zaune na iske Saratu bakin toilet ɗin tana ta busar da hayaƙin taba, ɗago jajayen idanuwanta ta yi ta kalle ni, gabana ya faɗi rass na ja baya domin ban san me ta shirya ba, domin ina jinta, shi kan shi Ayuba da Mahaifinta fama suke da ita, amma sam ba ta shiga shirgina, ko gaisuwa ba ta haɗa mu. Kallona ta yi sama da ƙasa, "Wai ke a Alaba kika kwaso wannan cikin kika zo nan ki haife mana shi? Ubansa ya gudu ya bar miki shege, shi ne kika zo nan ki haife ki gudu ki bar mana ko..."
Har tsakiyar raina na ji saukar kalamanta tamkar ta watsa mini ruwan zafi, karo na farko da na ji baƙin cikin rashin yin maganata tabbas da na sauke mata kalamai daidai da wawan zancen da ta yi mini. Kaɗa mata kai kawai na yi, alamun ba haka ba ne.
Taɓe baki ta yi, "To bara ki ji, na farko daga ƙarshen watan nan za ki fara biyan kuɗin haya domin zaman cin banzar ya isa haka. Na biyu kuma... Ki tabbata ba ki haife mana shege a gidan nan ba, na ga alamu nan da ɗan lokaci kin haihu ba wani da nisa ba, so ki koma inda kika baro ki haifi abinki, domin mu nan namu sun ishe mu."
Kallonta nake yi, baƙa ce wuluk kamar an mata fenti da kwalta, gefen kumatunta na hagu an yi mata ƙaton hetali 'bille'. Juyawa na yi na kalli gidan, bayan ƙazni da warin naman da Ayuba yake siyarwa da yake damunmu wasu lokutan, ga rashin gyara a haka take so na riƙa biyan ta kudin haya, shi ko Ayuba ɗan uwanta cikin tausayawa ya ce, "Na zauna iya lokacin da na ga dama, me ya sa ita 'yar uwata mace ba za ta tausayawa matantakata ba? Me ya sa ita ba za ta rufa min asirina ba ko da kuwa cikin jikina shege ne kamar yadda take iƙrari?"
"Kin zuba mini idanuwa kaman na mage. Ay kin ji abinda na ce ko? Idan kika ƙi yin abinda na ce za ki sha mamakina..." Miƙewa ta yi ta bar ni tsaye kamar dasasshen icce.
"Wataƙil ta ga sauyin da kika samu, domin kwana biyu ay ba ta fita tana nan tana masifa. Shi ne take son sai ta samu a jikinki," Wata zuciyar ta faɗa mini. Kada kai kawai na yi, domin tuni halayen 'yanuwana a jinsi ya daina ba ni mamaki, kuma tabbas zan yi duk abinda ta ce, har zuwa lokacin da abun ƙaunata zai diro duniya, wanda za mu samu a nutse mu nemi mafitar rayuwarmu.
Toilet ɗin na shige na yi wankana, ina fitowa na wuce ɗakina. Mai na soma shafawa, gani na yi gaba ɗaya jikina ya yi ɗan kumburi ba da yawa ba, a kintacena cikina ya shiga wata na bakwai, shuru na yi ina bitar abubuwan da ke kawo kumburi ga mai juna biyu. Numfashi na sauke, domin ban san ta ina zan je asibiti ba, yadda na saba addu'a nake Allah ya raya min abun ƙaunata ya kawo mini shi lafiya cikin wannan duniyar tamu mai cike da rikici.
Bayan na gama shiryawa kai tsaye Ipaja na nufa. Kuɗi ne dubu biyu na riƙo a hannuna domin yin sadaka kamar yadda na saba yi tun da na samu kuɗaɗen da Yunus ya ba ni.
Inda Maman Nana take zaune na nufa, duk da ba na magana, Maman Nana ta zayyana mani irin halin ƙuncin rayuwa da take ciki a lokutan da nake zuwa bara. Na tausaya mata matuƙa, hakan ya sa duk lokacin da na zo da 'yan kuɗina ita nake ba wa. Kamar koyaushe zuwa na yi na ba ta kuɗin. "Ban san sunanki ba har yau, amma yadda kike taimaka mani ni ma ba zan gajiya da yi maki addu'a ba kamar yadda kika buƙata. Allah ya ba ki mafitar rayuwarki. Hannuwa biyu na haɗa alamun yi mata godiya.
Ban jima ba na tashi domin komawa gida, tafiya nake yi a hankali. "Baiwar Allah... Baiwar Allah..." Na ji muryar da na tabbatar mammallakiyarta mace ce na faɗa daga bayana. Juyawa na yi domin ganinta, muna haɗa na ji gabana ya faɗi, zuciyata ta buga da ƙarfi. Da ƙyar na fizgo numfashina da na ji yana kaiwa da komawa, "Sannu baiwar Allah..." Ta faɗa mini cikin tsananin tausayi. "Ai na san ba ki magana, sannu kin ji. Wallahi kullum na zo gurin nan ina tausaya maki matuƙa." Ta ƙare zancen cikin gurɓatacciyyar hausarta da ba ta fita.
Kuɗi ta miƙa mani, "Ga wannan kin sayi wani abun kin ji." Karɓa na yi, na haɗa hannuwana biyu ina mata godiya.
"Sai an jima." Ta faɗa tare da juyawa ta yi tafiyarta. Ni ma juyawa na yi na tafi. Kuɗi ne dubu uku ta ba ni. Kai tsaye gida na koma, zaune na iske Saratu a ƙofar ɗakinsu tana waya, sam bana jin yaren da take magana da shi wanda nake tsammanin yarbanci ne. Shigewa na yi ɗaki na ɗora girki da nake yi kan murhun gawayi, bayan na ɗora na yi alwala domin gabatar da sallar azahar.
SH 5
G.R.A
MODOJI
Sallama ta yi cikin falon gidan, a guje Badiyya ta fada jikinta, tana faɗin oyoyo Mom. Sai da ta gama murnar ganinta sannan ta sake ta. A shagwaɓe ta ce, "Mom..."
"Na’am diyar Mom, duk kin bi kin ɗaga mani hankali." Turo baki ta yi, "Mom ba ki san yadda na gaji da jinyar nan ba, a ce mutum koyaushe yana barci, ko ya tashi fa kaman wanda ya sha kayan maye, a daddafe yake komai sai kuma ya koma ya cigaba da barcin, Wallahi ba ki ji yadda na gaji ba."
Murmushi Mom ta yi. "Ke ki kwantar da hankalinki, aikin ne da yawa shi ya sa aka ɗauki lokaci."
"Amma yanzu komai ya kammala ko My Mom?"
"Komai ya kammala, ke dai mu je daga ciki."
"Yawwa Mommyna." Badiyyah ta ƙare maganar da murnarta. Takawa suka yi a nutse suna mai da yadda aka yi har suka isa bedroom din ta da ke saman bene. Zama ta yi kan gado ta ce, "Mom ya ake ciki? Na fa ƙagara na ji yadda aka tsaya."
"Kwantar da hankalinki, bari ki gani." Hannu ta sa cikin haɗaɗɗiyar hand bag ɗinta ta fiddo wani magani. "Karbi wannan, yanzu da yake barcin nan kawai ki bude kwalbar ki saita daidai hancinsa, da zaran ya shaƙa zai mance da komai kuma zai tashi daidai yadda yake, wannan gane-ganen da yake yi da abubuwan da yake ji duk zai daina, haka aka tabbatar mini."
"Yawwah Mom, ki ga fa tafiyar mu bai fi saura sati daya ba amma mutum baya hayyacinsa kamar mahaukaci, wallahi Mom ba ki ji yadda na gundura ba, kuma wallahi ba na so a ce ba mu samu damar yin tafiyar nan ba, ai ni aka fasa an tafka mini babbar asara."
"An tafka maki, ko an tafka mana, ke mu je maza ki shaƙa mashi, ya mike ya warware a yi tafiyar nan." Karbar maganin ta yi ta ce, "Haka ne Mom, ba a bori da sanyin jiki, yanzun nan zan je na shaka mashi shi."
"Allah sarki, mu je in gan shi." Mikewa ta yi suka isa bedroom dinsa tare da ita, kwance yake yana baccinsa a nutse,. Badiyya ta ce, "Mom kin gan shi ko ya tashi da ya sha magungunan nan sai ya koma barcin. Kwana nawa ana abu daya, kuma abun ko sauki baya yi abun har mamaki yake ba ni ma fa. Uhmm, ba na gaya maki ba aiki da 'ya'yan Malaman zaure akwai wahala an ba su sun ci sun sha, dubi fa gumurzun da muka sha kafin a zo nan."
Wani motsi ya yi tare da juyawa, cikin ƙaraji ya furta, "Ummaaah! Lilbirrah!" Badiyya ta ruƙunƙume uwar, sake maimaita sunayen ya yi guda biyu. Badiyya ta saki Mom tana wiƙi-wiƙi da idanuwana tana kallonta. "Ke Badiyyah da ma haka yake wannan abun?" Mom ta fada a firgice. Kada kai ta yi, "Bai taba haka ba Mom, hasali ma yana dan tuna abubuwa amma bai taba ambatar sunayen su ba." Dukar da kanta ta yi kasa, "Innalillahi, Mom kwalbar ta fashe." Ta ƙare maganar a firgice. Zaro ido Mom ta yi, "Ɗauki abun ki shafa a hancinshi, dauki ki shafa mashi na ce. Kin san nawa na biya kafin a yi mini wannan aikin dubu dari biyu da hamsin na bayar, haba Badiyya ya za ki saki kwalbar?"
"Mom wallahi tsoro ya ba ni, ban san ma ya faɗi ba." Dukawa ta yi ta dauko kwalbar, abinda ke ciki mai kamar mai ya zube, sai dai ɗan abunda ba a rasa ba. Matsawa ta yi inda ya koma barcinshi bai san suna yi ba, hannu ta sa ta lakaci maganin da ke ciki a hankali ta goga mashi a hancin. Juyawa ya yi tamkar yana sane da me aka shafa mashi, ya ƙara buɗe ƙofofin hancinsa ya shaƙa.
"Yawwah aiki ya yi dama haka Boka Rigijim ya ce zai yi." "Wai Allah Alhmadulillah, ai Mom hankalina har ya tashi, a ce ya tashi da wadannan mutanen a bakinsa ai kashinmu ya bushe kuma.
"Ɗan buhun uba, yanzu kai da su Ummah kuma sai lahira kwa haɗu." Badiyya ta faɗa. Dariya suka yi gaba daya.
"Yawwah, komai ya kammala bara na tafi."
"Yanzu Mom komai lafiya?"
"Na ce maki garau zai tashi, ai mu dama mun san daga inda abun yake, saboda haka an ƙaras." Dariya ta kuma yi, ta ce to Mom Allah ya kiyaye, sai kin ji ni zancen tafiyarmu. Tare suka fita suna kara tattauna abubuwan da suke son cimmawa a gidan AbuƊalib.
★
ABUƊALIB
Wuraren ƙarfe biyar na yamma ya tashi, hannu ya sa ya dafe kanshi da ya yi mashi nauyi, muryarsa a shake ya ce, "Shona… My Shona." Da sauri ta karaso cikin falon. "My Boo, ta fada tana zama gabanshi."
"Wanka nake so na yi." Ya faɗa yana kallonta.
"Okay Bubuna bara na hada maka ruwan, ya karfin jikin naka, da sauki ko My boo, sannu ka ji," ta fada tana shafa fuskarshi.
"Na ji sauki sosai, ji nake kamar an cire min kaya, sam bana jin komai cikin kaina."
"Wayyoo dadi, Alhmdlillah. My Boo ya sami lafiya, haka nake ta son ji." Shafa fuskarshi ta yi, Haka nake ta son na ji ka faɗa, Allah ya kara maka lafiya My King," bai amsa ba ya zuba mata idanu yana kallonta. Sumbatar gefen kumatunshi ta yi, sannan ta mike ta shiga toilet dinshi, ruwa masu dumi ta hada mashi cikin kayataccen jacuzzinshi, foitowa ta yi ta kalle shi tana murmushi.
"My Boo, na hada maka ruwan." Okay. Mikewa ya yi ya buɗe wardrobe yabdauko rigar wanka. Rage kayan jikinshi ya yi sannan ya shige toilet din. Wanka ya yi zuciyarsa tana ta sake-sake da tunane-tunanen da ya rasa madafarsu.
Sai daya gama sannan ya fito, zama ya yi kan kujerar gaban mirror. Lotion din shi ya dauko ya fara shafawa, da sauri ta isa wajen shi ta karɓa, "My king ciwon nan naka ya tayar min da hankali." Dan gajeran murmushi ya yi mata, "Ni ma ya ya daga mini hankali My, amma yanzu ji nake na yi garau don ma ciwon kai da nake ji kadan-kadan. Amma kar ki damu fa, i'm feel okay."
"Na ji dadi My, ka warke, yanzu bara na je na hada maka Dining, ka zo ka ci abinci, ina kallon fuskarkan nan mai kyau tana mun murmushi."
Jinjina kai kawai ya yi yana mayar mata da martanin murmushi, tana fita kai tsaye bedroom dinta ta nufa. Waya ta dauka ta kira Mom din, cikin murna ta ce mata "Mom, albishirinki, yadda kika faɗa hakan ta kasance ya tashi tangarangam, kamar ba abunda ya same shi."
"Me na faɗa maki, ai aikin mutumin nan ƙarshe ne, sai ki mai da hankali kuɗin aiki har da la'ada za ki wawuro mana."
"Mom ke ma kin san ba ki da matsala." Badiyya ta faɗa suna dariya.
Tana ajiye wayar ta fice zuwa dining area, a nutse ya fito ya zauna kan ɗaya daga kujerun dining ɗin. "My Boo, har ka fito? Ka ga ban haɗa abincin ba ko, ina fitowa na ji ina son zuwa toilet."
"Toilet kuma, Shona za mu ci abincin?"
"Sorry My. Kawai na yi no.1 ne fa."
"Okay. Haɗa min abincin ina jin yunwa sosai."
"Okay. Let me do it quickly. Ba za ka jira ba." Kitchen ta shige ta fara harhaɗa kayan tana ajiyewa. Bayan ta gama tsaf ta fara zuzzuba mashi, ci yake a hankali. Jefi-jefi take jifar shi da hira, amsawa yake yi kamar baya son magana har ya gama cin abincin gaba ɗaya.
★★★★★
Tun bayan komawar su asibiti jikin Umma ya dan yi sauki, har tana iya cin abinci sannan tana iya zama da zuwa toilet. Rumaisa ta kalle ta cikin tausayawa, tabbas Ummah ta hadu da jarabawa da kaddarar rayuwa, wacce ko a mafarki ba ta taɓa tunano ta ba.
Abu kamar wasa har an kwashi tsayin watanni shida ciff ba tare da sun kara saka Yayansu AbuDalib a idanuwansu ba, haka sunan 'yaruwarsu Lilbirrah ya zama tarihi daga zuri'arsu, wannan abun takaici ne da baƙin cikinsa ya wuce a kwatanta.
Ummah ta fito daga daki ta nufi toiet a hankali. Kallon Inna Uwale Rumaisa ta yi, cikin sanyin murya ta ce, "Inna ranar nan kika ce za a shiga cikin lamarin nan na Yaya Abudalib, Umma kowa ya yi shuru ya rabu da mu, tamkar ba wanda ya san abinda ya faru, haka za a zuba idanuwa Badiyyah su cigaba da juya Yaya su kaɗai?" Numfashi Inna Uwale ta sauke a hankali ta ce, "Ban mance ba Rumaisa, abun yana raina kamar kuɗin haya, kuma tabbas zan ɗauki mataki ba za mu zauna bisa hukuncin Umma ba, don ba mu san abinda su Badiyya za su yi a gaba ba. Alhamdulillah jikin Umma ya yi sauki, don haka da yamman nan zan shirya in fita idan na fita zan je can Yammawa wurin Malam Saleh, idan an gama abinda ake yi, an ɗauki mataki Umma ta san komai."
"Shi ke nan Inna Uwale, amma idan Umma ta sani yanzu akwi matsala."
"Ki kwantar da hankalinki ba wanda zai sani, ba kuma abinda zai faru."
Jin takun Umma ya sa suka yi shuru suka daina zancen da suke yi. Wuce su ta yi ta koma kan gado ta kwanta, kallon Inna Uwale suka yi da Rumaisa, shuru ta yi alamun ba ta ji zancen da suke ba.
★
Inna Uwale tana fita kai tsaye Yammawa ta yi ma tsinke. A kofar gida ta samu Malam Saleh, kasantuwar yana cikin daliabai gaisawa kawai suka yi ta wuce cikin gida.
Inna Uwale suna cikin gaisawa da Sa'adatu matar Malam Saleh ya shigo. Cikin girmama juna suka sake gaisawa.
A hankali ta ce, "Malam na zo ne kan maganar AbuƊalib, duk kun yi shiru tamkar AbuƊalib ba jininmu ba ne, kun zuba ida kun bar waccen yarinyar ita da mahaifiyarta suna cin karensu babu babbaka."
Ɗan gajeran murmushi ya yi irin nasu na manya, "Uwale, kin faɗi jini ga Uba da ya haifi ɗansa da kansa? AbuƊalib fa ɗana ne, ɗan da na haifa. Kamar yadda bana mance karatun da ke kaina, sau ɗaya ba na mancewa da AbuƊalib. Kamar yadda kika ce, na bar su ne su ci karensu babu babbaka, na bar su kuma na ga iya gudun ruwansu. Amma na lura ba su san me suke yi ba, kuma ba su san kawaici da kauda kai ba. Saboda haka sun yi nasu, muma za mu yi namu."
SH 6
LAGOS NIGERIA
Karfe sha daya na safe na fito domin tafiya Ipaja, a hankali nake takuna, gangarowar wata mota ya sani ɗan dakatawa, duk da ban iya ganin mammallakin motar ba, amma zuciyata na ayyana mini macecina ne. A hankali motar ta rage gudunta lokacin da ta ƙaraso inda nake, sauke gilashin motarshi ya yi kamar yadda na yi tsammani kuwa shi ne. Cikin muryarsa mai dan kauri ya ce, "Amatullah," ɗan murmushi na yi jin sunan da ya kira ni da shi. "
"Ama," ya sake fada yana kallon cikin idanuwana, da sauri na sauke kaina ƙasa, gaishe shi na yi cikin yarena na bebenci.
"Lafiya lau," ya fada. Ya kike? Ya kika tashi?"
"Lafiya," na amsa mashi da yaren da nake yi.
"Ya Baby? Shi ma yana lafiya ko?" Kallonsa na yi ƙwaƙwalwar kaina na tsere cikin dogon tunani, karo na farko da irin kalmar ta shiga cikin kunnuwana, ni ce uwa da Uban abun ƙaunata, wani bai taɓa jingina kanshi da shi ba balle ya tambayi kwana da tashin shi, ba wanda ya taba damuwa da shi, ba wanda ya taba tambayata game da shi ni, ni kaɗai nake kulawa da wannan a kan shi. Take na ji idanuwana sun kawo ƙwallan, hannu na dora kan cikin lumshe idanuwana na yi hawayen na ƙara malalowa.
"Sorry," da ya fada ta dawo da ni daga duniyar tunanina. hawayen da suka kwararo daga idaniyata. Kallona ya yi cikin tausayi yana kara maimaita sorry. Jinjina kai na yi alamun ba komai.
"Ban san sunanki ba, sai dai na kira ki da baiwar Allah shi ya sa kika ji na kiraki da Amatullah, kuma haka zan cigaba da kiranki har zuwa lokacin da kika yarda kika aminta da ni kika fada mini sunanki ko da rubuce a takarda ne." Bance da shi komai ba, sai aikin saurarenshi da nake yi.
"Kwana biyu ba na nan na raka Babana America wata seminar, shi ya sa kika kwana biyu ban leko ki ba. Kuma idan ba damuwa Amatallah mu je ki kai ni gidan da kike don Allah." Haka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 14