ni da Mama, ga shi ba sana’a muke ba kamar mu yi haka Raina..." Ta ƙare maganar tana matsanancin kuka.
"Wayyo Allah na! Badiyyah to me ya sa ba ki taba fada min ba, me ya sa ba ki gaya min ba sai yau?" Na faɗa ina shirin kuka. Shuru ta yi hawaye na cigaba da sintiri daga idanuwanta. Jakata na jawo daga cikin locker din benci na fiddo kudi na ce, "Ki tashi mu je mu yi break, kin san kina cikin wannan halin amma ba ki taba fada min ba, to me ye amfanin taren mu?" Ba ta ce min komai ba muka fita wurin break. Sai da na siyo mana abinda na san zai ishe mu ni da ita sannan na muka koma class. Tun daga lokacin muka ci gaba da yin break tare da Badiyyah, wani lokaci idan zan tafi makaranta sai na tsare Yaya AbuƊalib ya linka min kuɗin break ɗina saboda mu yi ni da ita, idan ya yi min kyauta ko ya ba ni wasu kuɗi sai na raba su biyu na bawa Badiyyah rabi na yi amfani da rabi, da Umma da AbuƊalib kunnuwansu sun cika da labarin Aminci wato Badiyyatah. Kwanci tashi rana na faɗuwa dare na maye gurbinta da duhu, yanayi na canzawa daga rani zuwa damina daga damina zuwa sanyi aka wayi gari mun kammala makarantar Sakandare. Ranar da muka gama jarabawarmu ta ƙarshe da ƙyar muka rabu ni da Badiyyah, tana kuka ina kuka mun ƙanƙame juna tamkar a ce wuri ɗaya za mu tafi. Sai dai muka rabu da alƙawurran za mu riƙa ziyartar juna, za mu riƙa sada zumunci ta waya a kowane lokaci.
Ta janibin Yaya AbuDalib kuwa a cikin wannan lokacin ya samu cigaba a sana’ar dinkinsa ƙwarai da gaske duk fadin garinmu an san shagon dinkin Yayanmu wanda ya sa mashi sunana, "LILBIRRAH FASHION DESIGN." Gata da kulawa da nake samu daga gare shi sai abinda ya yi gaba, duk wani jin dadi Yaya na yi mashi. Sati biyu ciff da gama jarabawarmu kenan, na shiga ɗakin Umma na tarar da Yaya AbuƊalib suna magana, ganin alamun maganar mai muhimmanci ce ya sa na ja gefe na zauna. "Shalele barka da shigowa."
"Yayana na kaina," kun gama magana da Umma?" Na ƙare zancen tare da miƙewa na dawo kusa da shi.
"Shalele," ya fada yana kallona. "Na'am Yayan Shalele," na faɗa ina kallonshi. Wasu cards masu tsananin kyau ya miƙo mani, "Yaya wannan cards ɗin fa masu kyau haka kamar za a saka a wuya?"
"Buɗa mana ki gani."
"To Yayana," na faɗa ina zaro katin daga cikin ƙayataccen kwalin da aka adana shi.
"Please join us to the graduation and birthday party. To celebrate Lilbirrah Abdulhadi..."
"Yaya!" Na faɗa murna na neman sumar da ni.
"Yaya Party za ka yi mun?"
"Ke washa, rufe bakin kar ƙuda ya shiga." Sauri na yi na rufe bakina.
"Umma kin gani, katin nawa ne, na Party gama makaranta har da Birthday."
Umma ta ce, "Ni ma yanzu ake gwada min, yadda aka ba ki mamaki ni ma shi aka ba ni."
Wani irin daɗi nake ji kamar na yi ta tsalle, kasa jurewa na yi na miƙe na riƙe hannuwan Rumaisa muna taka rawa. Yaya AbuƊalib da ke mana dariya ya ce, "Shi ya sa ai na gwada maki da ranar partyn kawai zan zo na ce ki shirya mu tafi. Halinki na sani ya sa kar ki je ki suma."
"Aiko ba wuya," Umma ta faɗa tana dariya.
"Na ji Yaya ba komai, yanzu ma ji nake kamar na suma ɗin don daɗi cikin raina, dubi fa inda za a yi Partyn, wallahi ranar duniya za ta shaida Yayana yana so na."
"Ehh, wannan kam a faɗa da kiɗi a ƙara da busa." Yaya ya faɗa.
"Yawwah Yaya, wannan ƙawayena zan gayyato."
"Ehh amma na mutum biyar kacal zan ba ki, saboda so nake a yi partyn nan a nutse, duka friends and family mutum hamsin ne."
"Ba komai Yaya, da ma ƙawayena ba su da yawa, daga Aminci sai Humaira sai A'ishatu."
Hararar wasa ya yi mun, "Ni wannan sunan haushi yake ba ni, wai ita amincin ba ta suna ne?"
"A'a Yaya sunanta Badiyyah."
"To ki riƙa kiranta da Badiyyarta kawai, ba ki da wani amintacce idan ba ni ba, sai kuma Rumaisa idan ta girma."
"To Yaya daga yau na daina, duk abinda kake so dole haka za a yi."
"Yawwa 'yar albarka Shalelena."
"To Yaya yanzu sai na kama shiri kawai nan da kwana uku ne fa."
"Eh mana, me kike jira. Ki je a yi maki wankin kai, har dilki a yi maki, sai a yi maki wankin ƙafa da lalle. Na san inda zan kai ki duka a yi maki."
"Kai Yaya, har da dilka kaman wata amarya." Na ƙare maganar cikin sigar zolaya.
Murmushi ya yi, "Shalele, ai ni a wurina kin fi amaryar ma, don ina ga a bikina sai kin fi amaryata kyau, don zan iya kashe maki kuɗi ko nawa ne ba tare da na ji komai ba fiye da amaryata ma."
Umma ta ce, "Uhmmm. Da yake dai ko budurwa ba ka da ita, balle a je ga batun amarya. Don haka ba zan ce komai ba, amma amarya ai daban ce." Dariya muka yi mu duka.
"To Yaya ka kai ni gidansu ƙawayena na gayyato su, sai ka kai ni gidansu Aminci na kai mata gayya ta musamman."
Tsaki ya ja, “Ni Shalele kin dame ni da batun wannan kawar taki ni sunan da kike kiranta da shi ke kona min rai na ce ki riƙa kiranta da sunanta."
"Kash, Yaya wallahi na mance." Na faɗa ina daɗe bakina.
"To kar ki ƙara mancewa Shalele."
"To Yaya."
"Gobe da safe ki shirya na kai ki duka gidajen, ba zuwa za ki ki zauna ba. Kin san ban san wannan 'yan zaune-zaunen na gidan ƙawaye, ki shiga ki fito."
"To Yayana."
Umma ta ce, "Allah ya yi muku albarka ya ƙara muku haɗin kai "
"Amin Umma." Yaya ya faɗa. Bankwana ya yi mana ya miƙe ya fita. A ranar daɗi da ƙyar ya sarara mani na yi barci. Kashegari da sassafe na shirya, Yaya yana zuwa gida ya shirya ya ɗauke ni muka tafi. Gidansu Humaira muka fara zuwa, sai muka wuce gidansu A'ishatu, sannan muka wuce gidansu Badiyyah.
Ban taɓa zuwa gidansu ba, wannan shi ne karo na farko da na ziyarce ta. Sallama na yi cikin zaure, tun daga bakin ƙofa na tantance gidan na iyalai ne da yawa, domin kuwa sai ka ɗauka yaƙin basasa aka yi a cikinsa, gidan rikice yake kowa na hidimar gabanshi. Sake sallama na yi cikin tsakar gidan ina rarraba idanuwa, saboda ban ga Badiyyah ba.
Wata daga cikin 'yanmatan gidan ta ce, "Wurin wa kika zo?"
"Badiyyah," na faɗa a ɗarare.
"Okay, wuce ga ɗakinsu can." Ta faɗa tana nuna mini ɗakin da ke ƙarshen gidan. Tafiya na yi inda ta nuna mani, ina shiga cikin ɗakin Badiyyah ta rugonda gudu ta rungume ni. Sai da ta gama murnar ganina ta sake ni, "Rai... Raina." Dariya kawai nake, na kasa furta komai.
Zaunar da ni ta yi kan kujera, "Rai sannunki da zuwa, kin cika alƙawari tun kafin ni na cika."
"Aiko dai Badiyyah."
Mamansu ta fito daga ɗaki, "Ahhh, yau mun yi babbar baƙuwa, ina ta jin labarin Lilbirrah yau dai ga shi na saka ta a idanuwana, yarinyar kirki."
Saukowa na yi daga kan kujerar cikin ladabi da girmamawa na ce, "Mama ina wuni."
"Lafiya lau, ya Mamanku?"
"Lafiya lau suke."
"To madallah. Sannu, Badiyyah a kawo mata ruwa."
Badiyyah ta ce, "Mama ba ruwa fa."
"To, je ki ki sawo mata."
Laluba jakarta take ga alamu dai ba komai ciki. Cikin basarwa na ce, "Umma ni na gode ba sai an sawo min ba, yanzun nan zan tafi. Yayana yana waje yana jira na, kuma ya ce kar in daɗe."
Badiyyah ta yi karaf ta ce, "Kai jama'a rai, da ma ba yini za ki min ba."
Murmushi na sakar mata na ce, "Kai! Ay Yaya bai bari, sam ba ya yarda."
"Shi wannan Yayan wallahi," ta ƙare maganar kamar mai shirin kuka.
Katin gayyata na fiddo mata daga cikin jakata, "Ga shi Badiyyah. Jibi idan Allah ya kai mu, ina bikin ƙarin shekara da murnar gama makaranta."
Zaro idanuwa ta yi tana kallon katin, "Don Allah da gaske Rai. Kai! Gaskiya ina murna, Allah ya kai mu lafiya."
"Amin ya Allah, bara na tashi na tafi kar Yaya ya fara gajiya."
"To Lilbirrah Allah ya kiyaye."
"Amin," na faɗa ina miƙewa tsaye. Tare muka fito da Badiyyah har bakin zaure. Ɗan tsayawa muka yi kafin mu ƙarasa fita waje, "Badiyyah ya lamurran gidan nan ina fata an ɗan samu sauyi."
"Uhmmm, Lilbirrah har abada abubuwan gidan nan ba za su sauya ba, yadda suke haka za su cigaba da wanzuwa. Ban sani ba ko ni nan gaba ranar da na yi aure, ko ba bar gidan a gare ni su sauya. Yanzu haka yau ɗin nan, haka na sha shara da wannan tulin wanke-wanken nan, kuma wallahi Lilbirrah ko yau tun safiya har yanzu ruwa ban sha ba, kin gani sai dai su karya da 'ya'yansu mu kuma ni da Umma ko oho."
"Kai! Badiyyah ina tausaya maki sosai a kan wannan rayuwar, cire wahalar aikin nan, yunwa sam ba ta daɗi, shi ya sa gashi nan duk kin rame."
Tuni hawaye sun ciko idanuwanta, "Ki bari kawai Rai."
"Ki yi haƙuri kin ji, wata rana sai labari," na faɗa ina share mata hawaye.
Kuɗi na fiddo daga jakata dubu biyar na ba ta, "Ga shi Badiyyah ku ci wani abu, sauran jibi idan za ki taho ki hau abun hawa."
"Kai Lilbirrah, wannan kuɗin har haka."
"Ba komai Badiyyah, sam kar ki damu don na maki wani abu. Ke fa aminiyata ce wallahi da ina da dama, sai fitar da ke daga wannan halin."
"Nagode ƙawata," ta ƙare zancen tana rungume ni. Bankwana muka yi saboda kukan da take yi, na ce ta tsaya a nan ba sai mun fita waje ba.
Ina zuwa na tarar Yaya AbuƊalib har ya koma cikin inuwa saboda na jima a cikin gidan. "Shalele kin daɗe sosai." Ya faɗa yana tasowa daga wurin da yake zaune.
"Yayana nan gidansu Badiyyatah ne, shi ya sa na daɗe." Guntun tsaki ya je ya ce, "Haye mu tafi."
"Toh," na faɗa na haye kan mashin.
Tun da muka tafi kan mashin labarin Badiyyah nake ba wa Yaya, ina faɗa mashi irin halin da take ciki na wahalar rayuwa da Allah ya jarabce ta. Daga eh sai a'a kawai yake ce min. Da na lura sam ba ya muradin labarin sai na muka shiga wani zancen.
Kashe gari Yaya da kansa ya kai ni wani shago da ake gyaran jiki haɗe da lalle da har da kwalliya. Tsakanin gyaran jiki da lalle da kwalliya da za a yi min dubu tis'in da biyu Yaya ya biya. Kamar na yi kuka na ce, "Yaya kuɗin sun yi yawa."
"In ji waye, a shagonki fa aka samu, shi ne za ki ce sun yi yawa." Ya faɗa sam babu abinda ya dame shi. Tafiya ya yi shago, sai da ya kintaci lokacin da suka bayar za a gama ma ni ya zo ya ɗauke ni muka koma gida.
Kashe garin ranar za a gabatar da shagalin ƙarin shekarata da gama makarantana. Tun da safe Yaya ke kai kawo tsakanin event hall da ya kama zuwa gidanmu, da misalin ƙarfe biyu bayan na gama salloli muka tafi wurin kwalliya. Tabbas ni kaina na godewa Ubangiji kuma na yabe sa lokacin da na ga kaina cikin madubi. Duk da ni baƙa ce wuluk, amma kallo ɗaya za ka yi min ka ga tsuran kyawun da Allah ya yi min. Yaya yana ganina, ba abinda yake kira sai Masha Allah. Haka muka tafi ni da shi tamkar amarya da ango saboda ankon kaya da muka yi.
Muna isa hall ɗin taron, ma fi yawancin jama'ar da muka gayyata sun zo amma Badiyyah ba ta kai ga ƙarasowa. A nan aka fara abinda ya tara mu a wurin, Party muke yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba hayaniya ko kaɗan. MC da aka gayyato ya ce, "Shin a labari kun taɓa jin inda Yaya ke ji da ƙanwarsa kamar wannan? A saboda haka wannan Yaya ya buƙaci mu saka mashi wata waƙar India ta Yaya da ƙanwa don ya sake jaddada ma ƙanwarsa irin ƙaunar da yake yi mata." Murmushi kawai nake yi, shi ko Yaya faɗar farin cikin da yake ciki ɓata lokaci ne.
Miƙewa ya yi ya fara bin waƙar da aka kunna mashi mai taken Pholo ka taaroka... Waƙa ce mai nutsuwa da kwanciyar hankali, saboda son da Yaya yake ma waƙar tuni na hardace ta na san abinda ake faɗa cikinta. Bin waƙar yake yana taku cikin nutsuwa yayin da ni kuma nake tsaye ina ɗan juyawa sashe-sashen da ya juya shi ma. Muna cikin bin waƙar na hango Badiyyah ta zo, hannu na ɗaga mata kafin mu gama abinda muke yi.
Sai da aka gama tsaf wasu na taɓi wasu na ihu, bayan mun koma mazauninmu MC ya ƙara kiran Yaya domin taya ni murna. Mice Yaya ya karɓa ya fara magana, "Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa da komai da ya nuna mana wannan lokaci, lokacin da 'yaruwata ta cika shekaru goma sha takwas a duniya kuma ta kammala karatunta na Secondry, ina taya ta murna kuma ina farin ciki sosai, farin ciki marar misali ko kwatance. Lilbirrah, kowa ya sani ita ɗin ƙanwata ce, jinina, a cikin jinin nawa Allah ya fifita sonta a cikin zuciyata fiye da sauran 'yanuwana, ina sonta ina ƙaunarta Allah ne shaida ta, ina farin ciki da farin cikinta ina baƙin ciki da baƙin cikinta, idan kana son ka ga fara'ata ka kyautata ma Lilbirrah, kuma zan iya ɓatawa da ko waye a kan Shalele.
"Yaruwata da yarena na Hausa, Ukhteey da yaren Larabci, Sister da yaren turanci, Didi da yaren Indiyanci, Khouhar da yaren Farisanci. Na zaɓi na kira ta Khouhar don ba kowa ya sani ba, don ya zamana sunan da ni kaɗai ne ke kiranta da shi. Khouhar ke wane suna za ki ba ni?"
"Joonam," na faɗa daga inda nake zaune.
"Ina godiya Shalele, Joonam shi ma farisanci ne yana nufin masoyi, ko na cancanci wannan sunan?" Tsirarun mutanen da ke wurin suka amsa da, "Ka cancanta AbuƊalib."
"To Nagode," ya faɗa sannan ya cigaba da magana.
"A kullum addu'a nake yi, Allah ya ba wa Khouhar miji nagari da zai kula min da ita wanda ba zai cutar da ita ba. A kullum addu'a nake yi Allah ya raya mana ita, ta rayu ta yi shekaru irin na dabino." Dariya mutanen wurin suka kwashe da ita.
"A kullum addu'a nake Allah ya ba ni ikon cigaba da kulawa da ita, fatana ko aure na yi ita ma matata ta ƙaunaci Khouhar ɗina..."
Hawaye suka zubo mani da wani kuka mai ciwo sa ya turniƙe ƙirjina, duk yadda na so jurewa na kasa hakan ya sa na fashe da kuka sosai. Yunus ya nisa ya ce, "Lilbirrah, ina jin irin abinda kike ji, tabbas dole ƙarshen labarin nan ya yi ciwo, ya aka yi kika rabu da Ummanki da wannan yayan naki da ke ƙaunarki, wanda na daɗe ban ji wani ɗan uwa da ke son 'yaruwarsa haka ba."
Ban iya cewa komai ba sai aikin kukan da nake yi. Maman Yunus ta ce, "Ni na rasa abun cewa ma, shin Lilbirrah shi wannan yayan naki shi ne Baban Nadeer, ko kuma saboda yayan naki kika saka ma Nadeer sunansa? I feel your pain Lilbirrah, ni ma ji nake kaman na yi kuka." Duka tambayoyin da suke mini ban samu fursar ba su amsa ba, sai da na sarara sosai, sannan na buɗe baki na cigaba da magana.
"A cikin labarina duka akwai amsar tambayoyin ku, ku yi haƙuri wani zafi ne ya taso min, amma yanzu zan cigaba da labarin."
SH 17
Cikin yanayin da ke nuna zuciya ta motsa Yaya AbuƊalib ya ci gaba da magana, "Khouhar ɗina ita ɗaya ce a cikin dubu, mutane da aljanu sun shaida, da tsuntsaye da tsirrai suna faɗa a cikin sautukansu, 'yaruwata Lilbirrah ɗaya ce a cikin dubu."
Juyowa ya yi ya kalle ni, "Duniya ba ta sanin dalilin fushinta, murna ko kuma damuwarta, amma ni a kallo ɗaya da na yi a cikin idanuwanta nake gane haƙiƙanin yanayinta. Farin ciki ko akasin shi, walwala ko damuwarta, burina a kowane hali, na linka farin cikin zuciyarta, idan kuma tana baƙin ciki zan yi dukkan iyawata na kawar da shi daga cikin ranta. Khouhar... A kowane hali ki zo gare ni ki faɗa mani matsalolinki na yi alƙawari da ƙarfin jikina da nauyin aljihuna zan yi maki maganinsu da taimakon Allahn da ya halicce mu ya yo mu daga itaciya ɗaya..."
Taɓi aka hau yi, yayin da hawaye suka fara sintiri daga idanuwana, cikin kulawa ta musamman Yaya AbuƊalib ya ce, "Khouhar ki daina kuka ba zan iya yafe ma kaina ba, matsawar na zama silar zubar hawayenki."
Hannuwa na sa ina share hawayen sai dai na kasa tsayar da su, "Ba za ki daina ba, to bara in cigaba da marin kaina na san za ki daina." Hannu ya sa ya ɗan mari kansa, "AbuƊalib baka jin magana ko ka sa ka Shalele kuka..." Dariya ta kama ni sosai, "Yawwa ko ke fa, sam kuka ba ya maki kyau Khouhar." Ya ƙare zancen yana murmushi.
Mayar da abun magana ya yi wajen MC, ya dawo gefena ya zauna, duƙawa na yi wajen shi, "Joonam Allah ya taimake ni ba ka da budurwa, da yau ta ta zuba mini mari kan wannan abun da ka yi."
"Khouhar idan matata tana so mu zauna lafiya, kawai ta ƙaunace ki, idan ta so ki to ni ta biya ni," ya ƙare zancen yana murmushi.
"Joonam ina ƙaunarka, ina godiya ga Allah da ya ba ni ɗanuwa mai ji da ni mai ƙaunata irin ka." Bai ce komai ba sai wani kallo da shi kaɗai ya san fassarar shi.
MC ya ce, "Mun gama sauraren waɗannan daɗaɗan kalamai masu kama da baitukan waƙa da Yaya ya shiryawa ƙanwarsa, saboda haka muna kira ga duk wanda ya kawo ma Lilbirrah kyautar Birthday ya kawo mata, za a yi hotuna daga nan za a nannaɗe tabarmar wannan taro sai Allah ya kai mu wani lokaci."
Kasantuwar duk wanda aka gayyato 'yanuwa da dangina ne haka suka riƙa kawo min kyautuka ɗaya bayan ɗaya, Badiyyah ta zo inda muke, cikin girmamawa ta gaishe da Yaya, ba yabo ba fallasa ya amsa mata. Muryarta ƙasa ta ce, "Ni dai ban zo maki da komai ba Raina," Yaya AbuƊalib ya juyo ya mata wata harara da ni kaɗai na gan shi, "Ina maki fatan alkhairi, da addu'ar tsawon rayuwa raina."
"Nagode sosai Bady, Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen," ta faɗa sannan ta koma mazauninta. Sai da kowa ya gama bayar da kyautukanshi sannan MC ya ce, "To kowa ya kimtsa, za mu ga wace iriyar kyauta ce Yayan nan mai ji da ƙanwarsa ya tanada mata, Babban Yaya muna jira mu gani daga gare ka." Miƙewa Yaya AbuƊalib ya yi, sannan ya yi wa babban abokinsa Abduljalal inkiya da ya miƙo masa ajiyar da ya ba shi.
Tashi ya yi ya fita bai jima ba ya zo da wata leda, ni kam na zuba idanuwana don ban san me Yaya ya tanada min ba a matsayin kyautar ƙarin shekarata, ledar Yaya ya buɗe, "Da farko dai na siya ma Shalele waya, domin ta jima tana son waya amma da na ce sai ta gama makaranta ko gardama ba ta yi mun ba, saboda haka Shalele ga wayarki."
Taɓi na hau yi ina murna kamar yadda na ga saura na yi, "Sai kuma wannan turare ne domin na san Khouhar akwai tsabta ga son ƙamshi, saboda haka na yi mata kyautar turare, wannan kuma kuɗi ne dubu ɗari ta je ta sha choculates duk da na san ita ɗin ba ma'abociyar shan su ba ce."
Daɗi ne ya jagoranci ƙafafuwana zuwa wurin Yaya, "Joonam nagode, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen Khouhar ɗina." Ji na yi tamkar ba wanda ya yi min wata kyauta sai Yaya AbuƊalib sosai ya faranta min rai, bayan na gama murna aka hau yin hotuna bayan an gama sannan aka sallami kowa. Haka muka koma gida zuciyata fess tamkar an biya mani hajji, wanda a raina ko shakku bana yi duk ranar da Yayana ya zama hamshaƙin mai kuɗi ina cikin wanda zai fara biya ma Hajji. Komai na kwashe na faɗawa Ummana, ita ko koɗan ba ta damu ba sai murna da farin ciki da take yi. Kuɗin na ba ta ta yi duk abinda za ta yi da su, ni Yayana ya sallame ni da waya da turaren da ya siya min.
Lambobin 'yan ajinmu da muka gama makaranta wanda na kwafa a littafi na cigaba da juyar su a waya, cikin ɗan lokaci muka cigaba da zumunci da juna ciki ko har da aminiyata Badiyyah.
Tunda na mallaki waya, kusan kullum Badiyyah tana kan faɗa mini halin da suke ciki a gidansu, ni kan taimaka musu da abinda nake da shi wani lokacin har abinci sai in aika mata da shi, sosai nake jin tausayinsu da tunanin ta wace hanya zan sama musu mafita. Tun da ta gane gidanmu kuma tana yawan zuwa, amma ba su taba hadewa da Yaya AbuDalib ba, saboda idan ya fita da safe sai dare yake dawowa daga shagonsa.
Ina zaune ina aikin da na saba na latse-latsen waya Yaya AbuDalib ya shigo, "Khouhar," ya fada yana zama kan kujerar da ke kallona. "Joonam," na amsa cikin yanayin damuwa.
"Me ya faru ne Khouhar?" Ya tambaye ni cikin kulawa.
"Yaya wallahi ko, kawar nan tawa ce Badiyyah, Allah Yaya tana cikin wani hali wallahi kuwa, tana shan wahala sosai a gidansu ga yunwa, ga wuya tana shan gun kishiyoyin mamanta, Yaya tausayinta nake ji sosai."
Kada kai ya yi, "To Allah ya ba ta mafita." Tashi na yi tsagwayam daga inda yake na koma kusa da shi, ƙasa- ƙasa na ce, "Joonam, wani tunani ne na yi, ka gani da ma Umma tana so ka yi aure ba, Baba ma yana maganar ya ce har ka kusa zama tuzuru, amma kullum sai ka ce ba ka ma da lokacin neman budurwa."
"Uhmmm, ina jin ki," ya fada yana ba ni dukkan hankalinsa.
"To Yaya na zaɓa maka budurwa, kawai ka auri kawata Badiyyah, yarinyar kirki ce ga ta kyakkyawa, sannan tana da ilimin addini da na boko, kuma tana da kokari a school ka ga 'ya'yan da za ta haifa mana za su yi kokari. Sannan Yaya ba ruwanta shuru-shuru ma gare ta, tana da tarbiyya sosai…"
Tun da na fara maganar bai ce komai ba har na kai karshe. "Khouhar, kin sani duk abinda kika fada min zan yarda da shi, kuma idan har ke da kanki kin yaba da hankali da nutsuwar kawar taki ni ma zan iya amincewa, saboda tunaninmu daya da ni da ke, kuma na san in har kin amince tabbas kin ga inganci."
"Yaya wallahi ni na yaba da ita dari bisa dari."
"Shi ke nan to, amma fa ni ko kare mata gani ban yi ba."
"Ahhh, Yaya ba ka lura ba ne ranan Birthday dina, bara ka ganta," na kare zancen ina kokarin nuna masa hotunan mu na taron birthday da ke a wayata. Kallonta yake yi a nutse, yanayin yadda yake kallonta na tabbatar da da shi ma ya yaba. "Shi ke nan, yanzu sai ki kokari ki gabatar mata da ni, ki ce za mu riƙa gaisawa daga nan zan jarabata in gani idan ta dace da tsarina."
"Da gaske Yaya, kai amma na ji dadi sasai." Murna na yi ta tamkar ni ce aka ce za a aura, sosai na ji dadin yadda Yaya ya amince da ita farat daya. Kasantuwar Umma ba ta nan yana fita na daga waya na kira Badiyyah,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 14