Share this page
daga tsaginta ta amsa min da lafiya lau Rai. "Kina ji ko Bady kin san wani abu, Yaya ne ya ce tun ranar da ya gan ki nutsuwarki da kamun kanki ya birge shi sosai. Shi ne na ce masa ai ke ce Amincina da nake ba shi labari, shi ne ya ce na ba shi lambar wayarki za ku rika gaisawa." Murmushin da ke bayyana jin daɗinta ta yi sannan ta ce, "Ba damuwa Rai, Yayanki ai Yayana ne, Insha Allah ba damuwa zan amsa masoyiya." "To shi ke nan Badiyyatah." Godiya na yi mata sannan na kashe waya. Yaya suna fara mu'amala da Badiyyah ya shigar da zancen soyayyarsa gare ta, ita ma ba ta ja ba ta amince, domin Yayana yana da halayen ƙwarai, mutumin kirki ne, kuma kyakkyawa ne, sannan dogo ne cikakken dogo, yana da hasken fata amma ba fari ne irin tass-tass din nan ba, mutum ne mai gargasa domin gashin Nadeer da kuke ta yabawa ya same shi ne a gun Babansa AbuƊalib, haka yake yana da kwantacciyar suma, saboda shi ma babansa Malam Saleh cikakken bafulatani ne karatun allo ne ya shigo da shi birnin Katsina har Allah ya kaddara masa rayuwa a nan. Yayana yana da gira baka sidik, saboda duhunta da yawan gashin da ke kwance cikinta sai ka dauka jagira aka yi mashi haka ma girar idanuwansa mai duhu ce sannan dan-dandandan take, hakan ya sa idan ka kalle shi sai ka dauka kwalli ne ya shafa a idanuwansa yana da hanci dogo da madaidaicin baki, shi ya sa mata ma ƙaunarsa suke yi suna bin sa, amma bai taba son wata daga cikinsu ba har sai lokacin da na ƙulla alakar soyaya tsakaninsa da Badiyyah. Ta ɓangaren Ummana, ita ma ta yaba da hankalin Badiyyah hakan ya sa ta amince da zancen soyayyar wadda ta mike shantal zuwa ga aure. Tunda Yaya AbuDalib suka fara soyayya da Badiyya ta rabu da fama da irin matsalolin da suka addabi rayuwarta, saboda yadda yake hidima gare ta da yi mata dawainiya, abinci ma haka yake siyen buhun shinkafa da mai da taliya yana kai wa gidansu duk karshen wata, Yaya bai zama mai kudi ba, amma yana da zuciyar yi tsayayyen namiji ne na gaske. A janibin sana'arsa, shagonsa yana daɗa yin gaba wanda ya zama katafaren shagon da ake dinki, kaya har da zo da wanka, na kowane irin kaya mai sauƙi ko mai tsada. Irin hidimar da Yaya ya ke yi ma Badiyyah ya sa Babansu ma kanshi ya daina yi musu irin wulakancin da yake musu, ya koma mutunta su da ba su filin wuri. Shekara daya ciff suna soyayya wanda Yaya ginin gidansa da ya fara ya yi nisa sosai, yayin da mu kuma muke ta shirye-shiryen biki. Ta janibi na kuma bayan fitowar sakamakon jarabawarmu Yaya ya nema mini 'Yaradua University inda nake karantar Computer science domin shi ne burina tun tasowa ta. Wata rana ina zaune kan cinyar Ummana tana min tsifa Yaya ya shigo da manyan ledoji a hannunsa. Jibge su ya yi cikin ɗaki, sannan kuma wani almajiri ya shigo da wata ledar, su ma karɓar su ya yi ya aje inda ya ajiye na hannunsa. "Khouhar," ya faɗa yana zama kan kujera. "Na’am Joonam barka da shigowa," na fada ina mayar da hankalina kanshi. "Yawwa, Ummana ina wuni barkanku da gida," ya gaisar da Umma. "Yawwa, ɗan albarka, ya aiki ya kasuwa ya jama'a?" "Duka lafiya lau Ummana." Hira suka fara shi da Umma can ya ce, "Yau saura kwana nawa a fara azumi ne? Karaf na yi na ce, "Yau saura kwana kusan goma fa." "Yawwah, lissafina na tafiya daidai kenan." "Eh Yaya, ai ni kullum sai na duba calendar." "Ni yi mun shuru, ke da na ga hankalinki sam ba ya ma wurin azumin, kullum hankalinki na kan makaranta da wayar nan taki." "Joonam yana kai fa," na fada a shagwabe. "To na ji," ya ƙare maganar yana buɗe manyan ledojin da ya shigo da su. Umma ta ce, "Me muka samu?" Daga inda nake kwance na ce, "Wani abun ne Ummana?" "To ki tashi mana ki gani, don kin ga ina ji da ke shi ne kike wani sha min kamshi." Tashi na yi zaune na gyara zama, "Yaya da ma fa tashi zan yi da an ƙarasa ɗayan nan." "To in ma ba ki tashi ba, kallo zai bar ki." Wasu irin manyan lesuka da atamfofi ya fito da su, wanda suka dauki hankalina, saukowa na yi daga kan kujerar na zauna gaban kayan, "Kai! Joonam kayan nan sun yi kyau sosai na fara sakawa a lefe ne?" Kaɗa min kai ya yi yana rarraba su, "Kin ga wadannan," ya fada yana nuna mani laces ɗin, "Kin ga daya na ki ne dayan kuma na Badiyya ne." "Kai Yaya, amma na ji dadi sosai kenan anko za mu yi?" "Sosai kuwa Khouhar, tunda ni da ke ba za mu iya anko ba, ai dole matata ta yi anko da ke." "Joonam ko kunyar Umma," Dariya ya yi ya ce, "Ke, kar ki mini sharri," ya ƙare zancen yana dukar da kanshi. Umma ta ce, "AbuDalib to ita matar taka ta yarda ta yi anko da Lilbirrah ne?" "Ni ko ta yarda ko kar ta yarda Umma ra’ayi na ne, kuma kin ga kala daya ne kaɗai za su yi anko din, sauran kala hudun da ya rage kowane da kalar nashi." "Haka ne, amma duk da haka Allah ya sa kar abun ya yi mata zafi." Umma ta faɗa. Bai ce komai ba ya cigaba da buɗe ɗayar ledar, hadaddun less ne masu kyau su ma kala uku, "Wannan na Rumaisa ne idan ta dawo daga makaranta, wannan na Anty, wannan kuma zan kai wa Inna Sa'adatu." Sai kuma ya jawo dayar ledar, nan ma kala biyar ne su har an dinke su tass, "Wannan kuma naki ne Ummana." Duba kayan muke yi babu wanda za ka kalla ka ce bai yi kyau ba sai dai ka ce wannan ya dara wannan kyau, sosai nake murna, "Umma ta ce, "Allah ya yi maka albarka AbuƊalib." "Amin Umma, gobe idan Allah ya kai mu ki shirya mu je mu siyo sauran kayan da kuke buƙata, na gida da na Badiyyah." Ya faɗa yana kallona. "To Joonam, Allah ya kai mu lafiya," na fada cikin farin ciki. Cigaba suka yi da magana da Umma tana faɗa mashi kayan da zai siyo na azumi wanda Baba ya riga da ya siya wasu zai ƙarasa ne. ★ Kashe gari muka je kasuwa muka siyo dukkan kayan da muke bukata, tun daga kan kayan abinci, takalma jikka, da sauransu. Bayan kwana biyu da yo siyayyar muka shirya zuwa gidansu Badiyyah ni da Rumaisa da Inna Uwale kanwar Ummanmu muka kai kayan azumi da Yaya ya siya mata masu tarin yawa. Dakinsu Badiyyah muka yi zaune, yayin da suke bude kayan ana ta yabo ana sa alkhairi, sai dai fuskar Badiyyah ta yi gijim-gijim, a dan dame na tabo ta na ce, "Lafiya Bady?" "Zo mu je kuryar Mama," ta fada tana jawo hannuna. Shigewa muka yi kuryar dakinsu kafin su gama. Cikin kulawa na ce, "Bady, me ya faru? Me aka yi maki ba daidai ba?" "Ba komai wallahi, amma me ya sa AbuDalib bai kawo min kayan da kanshi ba? Haka kin san duk sai makwarmata sun gani, karshe sai an ba su wani abun daga ciki." Ban damu ba na ce, "To me ye Bady, ai a ci abun ka ma arziki ne." Ɗan karamin tsaki ta ja, "Ke ba za ki gane ba ne Lilbirrah." Nisawa na yi na ce "To shi kenan." "Kina ji na ko?" "Ina jin ki Bady, wai ke ko Anty ba za ki rika ce min ba, ni fa yanzu matar yayanki ce ba wai kawarki ba." Dagowa na yi domin abun nata ya soma ba ni mamaki, "Yanzu kenan mun daina kawance saboda za ki auri Yayana?" Na tambaye ta. "Eh mana, yanzu na zama Antynki, kuma kawarki," ta kare zancen tana mayar da abun wasa. "Na ji, yanzu fada min abinda za ki fada min ga shi can su Inna Uwale za su tafi." "Ba komai, kawai ki je za mu yi waya." "Okay," na fada sannan na fice daga dakin. Yadda muka je gidansu Badiyyah haka muka koma gida, ko naira biyar ba su ba mu ba da sunan tukwici. Ba mu mayar da hankali ba kan abun mun bar shi a gajiyawa da kasawa ta dan adam. Bayan azumin ya kama mun yi mun gama, ana cikin shagalin bukukuwan Sallah Yaya ya ce, les ɗin da ya yi mana kala ɗaya, za mu saka mu raka shi gidan abokansa ni da Badiyyah da wasu cikin danginmu su ganta. Tsaff na shirya cikin kayan ba tare da wani tunani ba, ni da Yaya muka iske Badiyyah domin a motar abokinsa za mu tafi. Muna zaune a mota muna labari Badiyya ta fito, fuskarta sake take sai dai muna hada ido fuskar ta sauya tamkar na aika mata da sakon mutuwa. "Matar Yaya, wani ya mare ki ba ki rama ba?" Na fada da sigar tsokana. Gefe ta kalla ba tare da ta samu fursar amsa min ba, Yaya AbuDalib ya fito yana faɗin, "Gimbiyar... Wa ya taɓa mani ke?" Bata amsa ba sai huci da take faman yi. "Shi ke nan tunda ba za a amsa min ba, ki shiga mota na san kya faɗa min." Muryarta da alamun bacin rai ya gama cika ta ta ce, "To a ina zan zauna?" Fitowa na yi daga motar da sauri, "Badiyyah ga wurinki mana, ka gani Yaya shi ya sa tun a gida na ce zan zauna a baya ka ki ga shi nan an batawa Antyna rai." Ba ta ce komai ba sai faman kallon gefe da take yi. Yaya ya ce, "To ki shiga mana tunda ta ba ki wuri." Shiga ta yi tana kallona, da yadda kayan suka karɓe ni, duk da ina baka kirin na fi Badiyya kyau nesa ba kusa ba, yayin da muka banbanta a dirin jiki saboda ita tana da tsayi ba sosai ba yayin da ni kuma nake da cikakken tsawo da madaidaicin jiki. Badiyya ta ce, "Ashe da muka yi ankon kayan har da dinki ma?" Yaya ya juya ya kalle ta, "To laifi ne Badiyyah, ɗinkin nan ni da kaina na zauna na yi shi, ban bawa kowa ya yi muku ba, ko bai yi ba?" "Uhmm!" Kawai ta ce ta juya ta kalli gefen titi. Har muka isa kamar kurame ba wanda ya tanka ma wani, ni ko na mayar da hankalina kan waya ina bincike kan karatuna da ƙara naƙaltar na'ura mai ƙwaƙwalwa. Gidan abokin Yaya AbdulJalal muka fara zuwa, a cikin abokansa shi ne shakikin amininsa tuni na dade da sanin matarsa wacce da mu aka yi hidimar aurenta, muna isa yadda Badiyyah ta ga mun san juna abin ya bata mata rai sosai. Sauran gidajen muka je, ma fi yawa sun san ni, cikin murna suke karɓarmu, amma dalilin yanayin ɓacin rai da Badiyya take nunawa ya sa suka fi mayar da hankali kaina. Gidan wani abokin Yaya muka je karshe, muna fitowa Joonam ya ce, "Daga nan sai gida kuma." Jakata na buɗe na fiddo kuɗin da aka ba ta, "Ga shi Badiyyah," na ƙare zancen ina miƙa mata. Karɓa ta yi tana ta kumburi ta buɗe jaka ta zuba su. Ɗan ƙaramin tsaki ya ja, "Ki ƙirga mana ki ga nawa ne, sai ki ɗauki rabi ki bata rabi." Tamkar ya watsa mata wuta haka ta yi, cikin zafin rai ta fiddo duka kuɗin ta watso min, "AbuƊalib da ma ka taho da ƙanwarka ne don ka wulaƙanta ni ka nuna min iyakata, ka ce na shirya za ka kai ni gun family ɗinka da abokanka amma sai ka tane da tahowa da ita, abun takaici ga anko iri ɗaya, idan an je ma ita ka fi nunawa saboda ka nuna musu ta fi ni muhimmanci wurinka, a karshe ma kudin da aka bayar saboda ni su ma sai an raba to ta ɗauka ni naira ba na buƙata ciki." Tamkar ruwa ya ci ni na yi shuru a bayan motar, yadda ta watsa mini kuɗin na kasa ko taɓa su. Cikin tsananin ɓacin rai Yaya ya ce, "An zo wurin, da ma ai tun da muka fito na ga walwalarki ta kau saboda kin ganta, na ji duk abinda kika faɗi ba ni da buƙatar sharhi, kuɗi kuma kan ki kika yi ma wa don na san kina da buƙatarsu fiye da ita." "Uhmm, ka yi min gori sai me?" Da sauri na ce, "Don Allah ku yi haƙuri, duk laifina ne, sam ban kyauta ba da na biyo ku. Badiyyah ki yi haƙuri wallahi Yaya shi ne ya ce na shirya na raka ku, din ya san ba za ki ji daɗi ke kaɗai ba." Dogon tsakin da ta ja ya tabbatar min da ba ta ma san ina yi ba. Shuru na yi, tuni zuciyata ta kariya, haka suka cigaba da musayar yawu ita da Yaya yana faɗa tana faɗa, a karshe dai baram-baram muka rabu. Sosai ran Yaya ya baci, a fusace ya ajiye ta a ƙofar gidansu. Yana yana ta ba ni haƙuri, ni kuwa zuciyata ta zo maƙoshi, kuka kawai nake son yi, muna isa na fita daga motar na shige cikin gida, tun daga bakin ƙofa na fashe da kuma Umma tana ta tambayar lafiya. Duk yadda muka yi da Badiyyah na fada mata cikin kuma, domin ko a tsammani ban taɓa tunanin Badiyyah za ta yi min haka ba. Cikin jinjina lamarin ta ce, "Ikon Allah ita kuma haka take? To me ye damuwar don AbuDalib ya hada ku ya je da ku unguwa tare? A tunanina ai bayan auren ke ce za ki mata ido ciki family din." Umma na magana Yaya ya shigo a fusace, "Khouhar ki yi hakuri ki daina kukan nan, ki yi hakuri ki daina zubar da hawaye na ce. Ki kwantar da hankalinki wallahi daga yau na rabu da waccen yarinyar, ta je ta auri wani wanda ba shi da ƙanwa ko wanda za ta juya shi yadda take so, amma ni ba za ta sa na yi abinda ban yi niyya ba, ta je Allah ya haɗa kowa da rabonsa." Da sauri na dago daga jikin Umma, "A'ah Yaya kar ka yi haka don Allah, na san bacin rai ne da zafin kishi kuma dama Badiyya tana da kishi tun muna makaranta in tana son abu ba ta son a rabe shi, ko ni ma sai da na rabu da dukkan ƙawayena sai ita sannan ta samu natsuwa." "Nagode ma Allah da ba ki iya ƙarya ba, kin ga tun yanzu ta nuna za ta iya raba ni da 'yanuwana saboda kar na raɓi kowa. Ba ta isa ba wallahi, ta je ta auri wani amma ni na gama da lamarinta babu ni babu ita." "Yaya don Allah..." A fusace ya buɗe ƙofa ya fice faga gidan, faɗawa na yi jikin Umma na saki sabon kuka domin sam bana so a ce abinda na haɗa kuma na zama silar rabuwar shi. Umma ta shafa kaina ta ce, "Ki bar kuka komai zai daidaita su duka ɓacin rai ne ya jawo musu hakan, amma da sun sauko za ki ga komai ya koma yadda yake." "Toh Ummana," na faɗa ina goge hawaye na. Ɗaki muka shige ni da Umma, yayin da na rage kayan jikina na faɗa toilet na yi wanka. Ina fitowa kasantuwar magrib ta kawo jiki, alwala na yi na zauna na fara karatun Alkur'ani mai girma, a hankali na ji zuciyata na sanyi, na yi kimanin wanda ya kai izif ɗaya aka fara sallar Magriba. Miƙewa na yi na gabatar da sallar, ina gamawa na yi azkar, sannan na yi sallar Isha. Daga inda nake zaune barci ya yi nasarar sace ni, lokacin da na farka dare ya fara yi hakan ya sa na miƙe na cire kayan sallar na haye gado na kwanta. A ranar ko abinci ban iya ci ba saboda damuwar da ta lullube zuciyata yadda Badiyyah da Joonam ɗina suka samu matsala a dalilina. SH 18 Ta janibin Badiyyah kuwa, tana komawa gida ta kwashe duk abinda ya faru tsakanin ta da Lilbirran da AbuƊalib ta faɗawa Mamanta. Shuru Maman ta yi, "Ke ko Badiyyah ina ganinki da wayo ashe sakarya ce." Cikin fushi da ƙunad zuciya ta ce, "Haba Mama, haba Mama, ba ki ji yadda zuciyata ke zafi a kan ƙanwar nan tasa ba, Mama har ji nake na tsani Lilbirrah, na tsane ta, saboda ta yi Ka-ka-gida cikin zuciyar mutumin da nake mafarkin zai zama mijina, Mama ko rabin son da yake mata baya min, ta ya ba zan ji haushinta ba, na tabbata a yadda yake kaunarta da ba kanwarsa ba ce har aurenta sai ya yi haba Mama," ta ƙare maganar tana shirin kuka. "Haba mana ɗiyata, duk abinda kike fadi na san shi kuma ina ganinsa ina tsammaninsa, kuma duk abinda kike ji nima ina jin kwatankwacinsa. Amma kuma wannan hanyar da kika bi ai ba mai ɓullewa ba ce, fushin da kika yi sai ya sa ki biyu babu. Shi ko wannan AbuDalib din tamkar lu'ulu'u ne a cikin ruwa sai kin tona kin tona kin sannan ki samu. Ina nufin sai kin yi tuna, tuna mai tsanani sannan ki samu kamar shi a cikin maza, saboda haka ko da wasa ka da ki kuskura ki asarar shi." "To Mama, wannan abun zai iya sa wa na yi asarar shi?" "Ka ji ki, shiyasa na ce sam ba ki da wayo. Ba ke kika ba ni labari a taron ƙarin shekararta da kike je yana faɗar ko matarsa idan ba ta sonta zai iya rabuwa da ita?" "Haka ne Mama, amma ni na ɗauka sha-ci-faɗin zance ne ya yi a gun." "Kayyasa! To da gaske yake, ke ce dai sam ba ki da tunani. Zai iya rabuwa da ke saboda ita, yanzu haka ma kar ki ɗebe tsammanin ya yanke hukuncin haka." "Don Allah ki bar wannan maganar Mama." "Ba zan bar ta ba saboda bana son ki rasa shi, don kika rasa shi ba ke kaɗai ba har ni kin yi wa asara. Abinda nake so ki sani, ba haka za ki yi ba." Shuru ta yi irin na mai nazari, "To Mama ya zan yi?" Nisawa uwar ta yi, "Abinda za ki yi shi ne ki bi shi ta ruwan sanyi yadda za ki mallaki zuciyarsa ki bi shi a hankali har ki mamaye ƙoƙon ransa, wani faɗan ba gaba da gaba ake yin shi ba, sai an bi ta yaƙin sunƙuru." "Mama ai ina bin sa a hankali, kuma ina nuna masa ƙauna da kulawa." "Ba haka nake nufi ba, za ki mallaki zuciyarsa ta hanyar ƙanwar tasa, ki nuna kina sonta kina ƙaunarta, kar ki yarda ki ƙara nuna mata abu mai kama da wanda kika nuna mata yau ɗinnan, idan kika yi haka har ya yarda da ke, sai mu nemi hanyar da za mu yi maganin ta, don ba zan zauna kina auren miji wata baƙar ƙanwarsa ita ce a zuciyarsa, ba laifi ya so ta, amma kar son ya wuce na yau da kullum na al'ada." "Mama to ya zan yi maganinta, kina gani akwai wata ziga ko zancen iska da zai sa AbuDalib ya juya ma Lilbirrah baya?" "A’a ta ya zai juya mata baya, da kamar wuya wannan, ke dai ki abinda na ce za ki ga yadda za a yi maganin nata." "Shi ke nan Mama." Badiyyah ta faɗa. "Yawwa, wannan matakin da kika dauka kar ki zato ko tsammanin biyo ki za ya yi, wallahi zai iya kyale ki har abada duk da ba zan lamunci hakan ba." "To Mama yanzu ya zan yi don Allah? Kar fa a ce ya kyale ni din, don na kira wayarsa kin gani bai dauka ba bai kuma biyo kiran ba." "Kara kira mu gani, da ya ɗauka sai ki ba shi haƙiri." "To Mama, bara na sake kira mu gani." Hannunta har rawa yake wajen kiran AbuDalib, sai dai kiransa take amma ko kadan bai dauka ba, kuma babu alamar zai ɗauka. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, a ɗan firgice ta ce, "Mama kin gani bai ɗauka ba fa." "Ba shi rata daga yau zuwa gobe mu gani," Maman ta faɗa tana shaƙar iska. Har aka kwana aka yini aka sake kwana AbuƊalib bai dauki wayar Badiyyah ba, sannan duk irin tarin messages na ban hakuri da take yi masa bai amsa ba. Wani murmushi Maman Badiyyar ta yi, dafa Badiyyah ta yi wacce ta zuba tagumi hawaye na bin fuskarta, 'Ki kwantar da hankalinki dole ne sai kin auri AbuƊalib tunda har Allah ya kawo shi to fa ya zo hannu. Yanzu kafin na fara ɗaukar mataki, kira wayar Lilbirrar, kin san shashasha ce, kina yin kalar tausayi za ta karɓe ki." "Shi ke nan bara na tura mata saƙon ban haƙuri, na san da ta gani za ta kira." ★★★ Ina zaune da safe ina shirin tafiya makaranta na ji ƙarar shigowar saƙon karta kwana cikin wayata, a ta shigo wayata. "Lilbirrah, na sani har abada ba zan samu mutum mai ƙaunata kamar ki ba, wacce babu alaƙa ko ta jini amma ya nuna min soyayya irinki. Shekaran jiya na tafka miki babban kuskure ki taimaka ki yafe mini tabbas ban kyauta ba, amma na gane kuskurena ki yafe min Lilbirrata, ki yafe ma amincinki." Na karanta saƙon ya kai sau uku, kafin na yi reply kiran wayar Badiyyah ya shigo. Ɗagawa na yi cikin damuwa kafin na ce wani abu na ji ta ce, "Lilbirrahta!" Kafin ta yi wata magana ta fashe da kuka, wani irin tausayinta ya kama ni, cikin muryar kuka ta fara magana, "Lilbirrah don Allah ki yi hakuri, kan abinda ya faru wallahi sharrin shaidan ne, na yi nadama kuma ba zan sake aikata hakan ba, don Allah ki yi haƙuri..." Hakan da ta fada ya sa na ji zuciyata ta karaya har ni ma ina shirin yin kuka, "Badiyyah wallahi babu komai ya wuce, ni dama ban riƙe ki a zuciyata ba, na san ba halinki ba ne kawai zafin soyayyah ne da kishi irin namu na mata." "Da ma na san za ki fahimce ni, ki yafe min ina ƙara roƙonki." "Wallahi na yafe miki, Allah ya yafe mana gaba ɗaya." "Nagode Lilbirrah, don Allah ki ba wa Joonam ɗinki haƙuri, tunda wannan abun ya faru ko wayata ba ya ɗauka." "Insha Allah Badiyyah da ya zo zan faɗa masa duk yadda muka yi." Bankwana muka yi da Badiyyah tana ta ƙara ba ni haƙuri. Sati daya da faruwar lamarin amma sam bai canza ba. badiyyah da kanta ta kira ni da kanta ta ba ni hakuri, na fadawa Yaya amma sam bai yarda ba. Ina sauke wayar daga kunnena Yaya ya shigo ɗakin, da saurina na gaishe shi, "Yaya AbuDalib barka da safiya." Sai da ya zo gab da ni ya ce, "Khouhar barkanmu juna, ya kika tashi?" "Lafiya klau Joonam Alhamdulillahi." "Masha Allah," ya faɗa a gimtse. "Amm, don Allah Yaya, ka janye kalaman da ka fada na ka fasa auren Badiyyah, kar ka ɗauki abinda ya faru wani abu, wallahi bacin rai ne kuma yadda muke mu mata kowace mace ma za ta iya yin haka, daidaiku ne a cikinmu za su amince da abinda ka yi din Yaya, ni

Chapter 12 of 14