aka yi aka aje a wurin, leƙawa ya yi inda ya ga hayaki na fitowa daga karkashin dutsen, sai daga gefenshi kwarya ce zaune dangal-gal duk da ba tarde zaune take kamar haka Allah ya halicce ta a wurin, duk da ba a kan wuta take ba a cikinta ruwa ne ke tafasa suna fitar da wani siraci. "Lahaula wala kuwwata!" Ɗayyabu yake maimatawa yana ambaton sunayen Ubangiji. Baya ya yi da hanzari yana fadin wannan ya fi karfina sai dai na fadowa Malam Babba. Baya ya yi a guje yayin da sauran yaran Malam suka firgita suka fishi gudu. Da karfi ya ji ana kiran sunanshi sam bai juya ba sai kara kaimin gudunsa da ya yi domin ya fado ma Malam Saleh abinda maganansa suka shaida. Ji ya yi kamar wani abu ya ja shi ta baya hakan ya yi daidai da faduwarsa kasa wanwar kamar wanda aka ja da igiya.
SH 10
Yunƙurawa ya yi da niyyar tashi sai dai sam hakan ya gagare shi, sunayen Allah da ayoyinsa kawai yake ta ambata cikin rikicewa da yanke ƙaunar cewa ya yi mummunan gamo a cikin gonar. Yaran Malam suka ƙara gudu don su iske Malam Saleh su sanar da shi abinda ke faruwa da Malaminsu Ɗayyabu. A rikice ɗaya daga cikinsu yake furta wallahi an tafi da Babban Yaya, ganin yadda ake jan shi kaman ana jan wasu kaya, a ruɗe ya ƙarasa wajen Malam, cikin shesshekar gudun da ya sha ya soma ba wa Malam labarin dukkan abinda idanuwanshi suka shaida mashi game da Ɗayyabu, Malam bai jira ya ƙare zancen ba ya ce, "Ta ina abun ya ja shi? A ina kuka ga dutsen?"
"Ta in ne Malam." Yaron ya faɗa yana nuna mashi hanyar. Gaba Malam ya yi ya bi hanyar ba tare da wani tsoro ko shakku ba, tunda ya tunkari wurin ya soma ganin ana siddabaru, sam bai damu ba sai ayoyin ƙona aljanu yake jawowa yana karantawa don yana da tabbacin aljanu ne suke webuwa a wurin. Tafiya yake har sai da ya isa inda dutsin yake, daidai wurin da yake hayaki da ƙwaryar da ruwa ke tafarfasa cikinta, abun ya ba shi mamaki sai dai ya basar ya fara neman inda Ɗayyabu ya maƙale. Kiran shi ya yi da ƙarfi, amma sam babu shi babu alamarshi, dube-dube Malam Saleh ke yi a zagayen wurin, kamar an jeho Ɗayyabu daga sama ya gan shi gabanshi tamkar matacce baki da hancinsa suna fitar da jini. Da sauri ya tsugunna yana, "Ɗayyabu, Ɗayyabu!" Ko kaɗan ba ya motsi sam bai san abinda duniya ke ciki ba.
Wani irin sauti ya karaɗe zagayen wurin, waige-waige Malam ke yi bai ga komai ba cikin wata irin tsawa aka ce, "Kai biladama! Me ya kawo ku nan? Saleh ka gaggauta bacewa daga wurin nan, kar ka shigo shirginmu kar ka taɓa ajiyar da aka ba mu, hakan zai zame maka haɗari!"
Wani irin dogon tsaki Malam ya ja ya yi saurin mikewa, cikin bacin rai ya nufi dutsin gadan-gadan, sam ba ya tsoro ko ɗar, ayoyin Alkur'ani mai girma kawai yake karantawa. Kai tsaye wurin ƙwaryar da ke ci da wuta ya je, sai da ya karanta ayoyin samun aminci sannan ya sa hannu ya dauki kwaryar ya watsar da ruwan da ke cikinta a ƙasa ba tare da wata fargaba ba. Wani irin ihu da wasu kalar sautika suka gauraye wurin kamar ana yaki, ihun da ya tashi lokaci daya kuma ya tsaya cik tamkar an kashe shi da wata na’ura gefe inda wutar ke ci ita ma ta mutu murus, ƙwaryar ya buga ƙasa da iya ƙarfin da Allah ya hore masa yana karanta sunan Allah. Fashewa ta yi ta koma ɓalli-ɓalli, Malam Saleh ya zuba mata ido yana kallon yadda take narkewa tana shigewa cikin ƙasa.
"Ya Ilahi, ya Ar-hamarrahimina!" Ya faɗa cikin mamaki da al'ajabi. Matsawa ya yi inda wutar ta mutu ko kadan bakinsa bai bar ambaton ayoyi da addu’o’in duk da ya san suna kare mutum daga sharrin jinnu ba, lekawa ya yi inda wutar ta mutu yana kallon yadda ta bar wani tafkeken rami. Ɗagowa ya yi saboda bai ga komai a ciki ba, juyawa ya yi don ɗaukar Ɗayyabu su koma inda suka baro, sai dai jin wani kuka-kuka yana fitowa daga saitin ramin ya sa shi ya ci birki. 'Bismillahir Rahmanir Rahim,' ya faɗa sannan ya juya cikin sanyi, leƙawa ya yi cikin ramin, wani Kwado ne ya yi lamo yana wani wahalallen kuka, duka jikinsa an tsire shi da wasu kananun ƙayoyi, sannan duk inda gaɓarsa take ta ƙafafunsa na gaba da na baya an yi musu dauri da wani abu kamar zaren saka mai tauri, Kwaɗon sai kukan wahala yake. Sai da Malam Saleh ya yi addu'o'i sannan ya sa hannu ya dauko shi, ƙuri ya yi yana karanta rubutun da ya yi arba da shi jikinshi, cikin kidima ya sake karanta abinda ke jikin nashi, da manyan baki aka rubuta LILBIRRAH. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’una," ya fada a matuƙar ruɗewa, sosai hankalinshi ya tashi. Kamar daidai lokacin ake tsira ma Kwaɗon ƙayoyin, da sauri ya ajiye shi ƙasa, fakainiyar barin duniya ya cigaba da yi, cikin ɗan lokaci ya mace. Durƙusawa ya yi kan gwiwowinsa domin fiddo duk abinda ya gani a cikin ramin, wanda yaƙini tabbatacce ya dirar mashi a kan duk abinda ke wurin ya ta'allaƙa da gudan jininshi wato AbuƊalib.
Hannu ya sa ya jawo wata kwalba hade da wani abu da ke duƙunƙune cikin leda. "Ya Ilahy," abun da ya fada kenan lokacin da ya yi ido huɗu da ɗan mitsitsin ABUDALIB yana birgima cikin kwalbar yana magowa. "Ya Allahu, ya Allahu," ya cigaba da maimaitawa. Ji ya yi durkushin ya gagari gwiwarsa hakan ya sa ya zauna dirshan kan ƙasa yana ambaton, "Ya hayyu ya kayyum," hannu ya sa ya bude kwalbar take iskar guguwa ta turniƙe wurin gaba daya, cikin mintuna kuma ta ɓace ɓatt tamkar ba a taba yin ta ba. Bayan iskan ya lafa ya sake duba kwalbar, amma babu komai cikinta ɗan mitsitsin AbuƊalib ya yi samarya tamkar ba yanzu yake cikin kwalbar ba. Sosai Malam Saleh ya firgita da ganin lamarin da kuma irin rashin tsoron Allah da aka yi cikinsa, shi kaɗai yake surutunsa, "Wannan abun mummunan sihiri ne da aka hada da aljanu munana aka yi tabbas an zuba rashin imani, zuciya ta ɓaci zuciya ta ɓaci wallahi na fuskanci haka tun farko, sai dai ban taba tunani abun ya kai haka ba, duniya ina za ki damu..." Shuru ya yi ya koma karatun addu'o'inshi, warware ledar ya soma yi, sai dai wani sauti cikin mummunan amo ya fara yawo cikin kunnuwansa, "Ni ba na yafiya Malam Saleh kuma ba na afuwa, ga abinda aka ba ni ajiyarsa ni mai tsayuwa ce, bibiya da binbinina mai dawwama ne, idan ka ga na dai na tabbas na kar ne, taɓa ni taɓa su, ka taɓa ni zan taɓa su…" Shuru Malam ya yi tare da 'yar karamar razana, "Insha Allah sai na warware ko me ye a nan ko me zai faru kuwa, wa la haula wa la kuwwata illah billah."
Fara kwanta ledar ya yi daga gefe zuciyarsa na ƙara azalzalar ya ceci ɗansa da kuma 'yaruwarsa daga bakin ƙullin da ya dabaibaye su ya ruguza dukkan rayuwarsu, dole ne ko me zai faru ya warware shi ko ba gargaɗi ba, ko da an yi mashi fiye da haka, budewa ya fara yi yana jin jikinsa ya hau karkarwa, wani huci na fita ta cikin kansa. Wata irin zabura ya yi lokacin da abinda ya bayyana cikinta ya watsu wanda ya fi karfin abinda idonsa ya gane masa linkin ba linkin, dariya mai muni kuma ta gauraye wurin. Komai ya kwance ma Malam saleh Bismillah kawai yake maimaitawa. Wasu irin ƙanana-ƙanan kanu ya gani, a sifa kanum na tantabaru ne amma kuma ƙarantarsu bai fi a ce sifar wani babban ƙwaro ne ba. Bismillar ya ci gaba da yi, sosai ya cika da mamaki tamkar zai wuce da rayuwarsa domin jikin kowane kai sunan AbuDalib ne da wani daga cikin makusantansa, sunan Lilbirrah ne farko Malam Saleh ya fara arba da shi, ajiyewa ya yi ya dauki wani shi kuma sunan Ummansa ne, na gaba ya ɗauka cikin mamakin da ya jike ilahirin ruhi da gangar jikinsa ya ga sunan shi a rubuce, Malam Saleh. "Kai subhanallahi, ya Allah!" ya fada yana jijjiga kansa. Gaba ɗaya sunayen mutane ne da bai san adadinsa su ba,wasu ya san su a abokan AbuƊalib din, wasu kuma danginsa ne abinda ya shafi ƙanne da yayunsa, "Kenan a nufinsu sun raba AbuƊalib da duk na tare da shi har abada?" Sanin waye AbuƊalib ya sa ya ji wasu hawaye sun tsarga jijiyoyin ganin shi sun lulluɓe ƙwayar idonsa. Dukawa ya sake yi wani kullin ya gani, yana jawo shi kafin ya daidaita zamansa ya ga dutsin ya ɓace daga wurin tamkar ba a taba yinsa ba, wani abu mai kama da yayewar duhu ya yi afku a wurin. Ƙara addu'a Malam Saleh ya yi sannan ya sa hannu ya bude ledar wani kalar rubutu ne da bai san da irinsa ba a duniya jikin takardar da ya gani, sunan Abudalib da Lilbirrah da na Ummansa kawai ya iya ganewa sauran wani yare ne da bai san da shi a duniyarmu ba. Ya daɗe zaune a wurin cikin zallar mamaki da al’ajabi, haɗe da tsoron Allah da ya ƙara mamaye zuciyarsa. Wani marayan tari da ya shiga kunnenshi ya sa shi juyawa da ɗan sauri, Dayyabu ya gani ya farfaɗo da sauri Malam ya tashi ya ce, 'Dayyabu sannu, sannu Ɗayyabu."
"Malam, kaina ciwo yake yi," ya fada a wahalce.
"Sannu, sannu, Insha Allah zai daina..." kama shi ya yi ya mikar da shi tsaye, a sanyaye ya ce," Malam ina iya tafiya."
"To shi ke nan Ɗayyabu." Juyawa Malam ya yi ya koma wajen tarkacen da ya gama gani, tattara su ya yi tas ya zuba a hularshi domin ya nunawa Umma da ta dauki zafi kamar ƙarfen da ke cikin wutar maƙera, sai kuma Uwale tare da sauran zuri'arsu. Tare da Malam da Dayyabu suka koma cikin ainufin gonar, Malam har a lokacin sunayen Allah na bakinsa, bai daina ambata ba. Su ko yaran Malam sai bin su da idanuwa suke, Malam ya tattara su gaba ɗaya suka haye mota domin komawa gida, addu’a kawai Malam yake har a lokacin ya gaza komawa ciki cikakkiyar nutsuwarshi haka mamaki ya ƙi barin zuciyarsa.
Kai tsaye suna komawa gida shagon magani aka yi da Dayyabu, ɗan gyaggyara mashi fuskarshi aka yi da ta ji rauni a dalilin buguwar da ya yi. Daga nan gida suka wuce, Malam yana shiga wanka ya yi da sallar la'asar da ta riske su suna gona. Jikinsa ya yi sanyi duk ya mutu, matarsa Sa'adatu sai tambayarsa take amma ya kasa ce mata komai, abincin da ta kawo masa ma ido ya zuba masa. Nisawa ya yi, a sanyaye ya kira wayar Rumaisa, cikin sa a ya same ta, bai ce mata komai ba sai yana neman Uwale ta zo akwai maganar da za su yi, idan da hali ta zo kafin gobe idan babu ta zo gobe da safe inda rai. Yana gama faɗar saƙon ya kashe wayar, yana cigaba da tunani da mamaki da ya ƙi barin ransa.
★★★
BADIYYAH
Zaune take cikin wani wurin shakatawa mai masifar kyau, duk kyawun wurin da kayatuwar shi amma ya kasa birge ta saboda damuwar da take daddale cikin ranta. Babu abinda ke mata ciwo a ƙwarya kamar yadda AbuDalib din ya ida koma mata cikin 'yan kwanakin da suke rayuwa a Vienna, wasu lokutan ta kasa gane kansa ta kasa fahimtarsa, ga tsabar shashashanci kamar ya rasa rabin hankalinsa ga kuma wani shuru da yake mata bayan maganar da suke jefi-jefi da ta ce ya zama kurma. Dogon tsaki ta ja wanda har ya ja hankalin wani saurayi da ke gefenta. Kallonta ya yi suka hada ido, daga mata gira ya yi, ba tare da neman izininta ba ya taso ya karaso inda take.
"Sannu beautiful Queen."
Ba ta amsa mashi ba sai wani kallo da ta watsa mashi, "Tun da kika zauna nan na ga alamun kina cikin damuwa, sannan ga alamu kina bukatar mai dauke maki kadaici, i'm sorry."
"Uhmm," kawai ta furta tana cigaba da kallonsa. "Babe ita duka duniyar nan babu abun takaici cikin ta da, duk wanda kika ga ranshi ya ɓaci to shi ya so, kuskure ne ka ta'allaƙa farin cikinka a kan wani, ke ke da kanki saboda haka ki ji daɗin rayuwarki Babe... Kina ji ko?" Jinjina masa kai ta yi, domin kuwa maganganunsa sun shige ta har sun mata tasiri.
"Ki taso kawai mu je ki huta," Plssss ya faɗa tare da sa hannu ya sa ya jawo hannunta. Cikin ingizawar shaidan ta mike ta bi bayanshi. Wani ƙayataccen wuri suka isa cikin dandamalin shakatawar wanda ba ta ma san da shi ba, lemu ya sa aka ba su su duka biyun, "Ki sha wannan zai kauda maki ƙuncin ranki, da damuwar da ke zuciyarki ina mai tabbatar maki Baby."
Karba ta yi ta ci gaba da sha, sai dai ta gama ta ji ta soma fita hayyacinta, dan dakewa ta yi can ta ce, "Ina cikin matsala Babe," ta fada tana fuskantarshi.
Kallon lebunanta da suke furta maganar yake, cikin muryarsa da ta fara canzawa ya ce, "Me ye matsalar?" Hannu ta sa ta rungume shi, dariya ya saki ya mikar da ita tsaye suka shige cikin wani daki, da ma abinda yake so kenan, don ya ga alamun sosai a kan wuta take, tana buƙatar agaji.
★
Kimanin awanninsu uku a dakin, a hankali ta bude idanuwanta, jinta jikin wani sankamemen ƙato ya sa ta yi saurin tashi zaune, juyawa ta yi gefe barci yake abinsa cikin kwanciyar hankali, baƙi ne sosai irin wanda ake ce ma baƙi wuluk, wuf ɗaya baka ce mashi mummuna amma kuma ba a saka shi layin masu kyau, kanshi ya sha wani aski mai kyau, fatar jikinsa kuma da gani ta ji hutu.
Haduwarsu ta yi saurin dawo mata cikin kawakwalwar kanta, "Kai!" Ta furta tana tafka mashi wani bugu a jiki. Bude idanuwansa ya yi da suke cike da barci, "My beautiful," ya faɗa yana shafa gefen fuskarta, bige hannun ta yi cikin ƙyanƙyami ta yi niyyar tashi tsaye sai dai ganinta haihuwar uwarta ya sa ta komawa inda ta baro da sauri. Hawaye suka gangaro daga idanuwanta, "Me na yi maka da za kai min haka?"
"Haba ke kuwa kamar ba 'yar zamani ba..." ya ƙare zancen yaja tashi zaune. "Kar ki wani damu, kin san wannan is common sam ba wani abu ba ne? Kuma me ye matsalar? Kin san ba abinda ba ki faɗa min ba, game da damuwarki?"
"Kana nufin ka ji komai game da sirrina?"
Jinjina kai ya yi yana faɗin tabbas. "Kuma ni ban ji komai ba, ma ɗauki wannan haɗuwar tamu a matsayin wata ƙaddara da za mu faranta ran junanmu, ke ba ki yi tunanin haka ba?" Shuru ta yi saboda wani tunani da ya shigo mata. "Yess, ki yi tunani, na ganki…," duƙawa ya yi ya furta mata wata magana cikin kunne. Gyara zamanta ta yi a hankali ta ce, "Ni matar aure ce, kuma kamar yadda na faɗa maka ɗin ɗazun ɗin, mijina ya samu matsala yanzu..." Rufe bakinta ya yi da tausasan hannuwansa, "Na ji komai fa, kuma bana son na sake jin komai." Jawota ya yi ya hada da jikinsa, cikin kunnenta yake fada mata wasu irin maganganu masu natsar da zuciyar mace, dago ta ya yi ya ce, "Kin amince da tarayyarmu?" Jinjina kai ta yi, "Na amince," fuskarta har da ɗan murmumushi. Shafa kanta ya yi,"Na ji daɗin yadda kika amince da wuri haka, ni sunana Nawwaz, haifaffen Kano ne ni, na zo nan jinyar Unlce dina but next week za mu koma Nigeria, saboda har na gama jinyar."
"Okay, ba damuwa, mu ma next week ɗin za mu tafi, kuma mun zo karɓar award ne..." sai da ta labarta mashi abinda ya kawo su gaba ɗaya. Musanyar waya suka yi, cikin jin daɗi Nawwaz ya sake fara romancing dinta, take ta biye mashi shi ko ko kadan bai sahirta mata ba wurin nuna mata wata kalar soyayya irin wacce ta yi kewa kuma take ƙulafuci. Sai da suka gama suka yi wanka a tare, sannan ta shirya ta koma masaukinsu sosai take jin ta cikin farin ciki da jin dadi.
Kwance ta iske AbuDalib yana ta aikin barci, kallon shi ta yi ta saki ɗan siririn tsaki, domin kallonshi ma takaici yake ba ta, wayarshi da ke kan bedside lokcker ta dauka, kokarin bude key ta yi sai dai kuma ya sha banban da wanda ta sani kafin ta fita. Kamar ta fasa ihu, tsayin kwanaki sha hudu tana biƙin tura kudin daga asusun AbuDalib zuwa nata asusun abun ya gagara, sai ma wani kara son kudin masifa da ya yi bayan ya ida susucewa, ga taurin kai kamar ba shi ba, a da irin raƙumi da akalar da ya zamar mata da tuni ta tura kudaɗen, sai dai duk ya sauya ya zama kamar wani tababbe, kowane dare ya yi gari ya waye da kalar da zai tashi da ita. Wayarta ta dauka ta kira Mom saboda ya ki taunuwa ya ki haduwa gareta, ya kuma ki tura mata kudadenta, dole a gaggauta ɗaukar mataki, sai dai daga gefe matar ta sanar mata wayar ba ta tafiya. Wani tsakin ta kuma ja ta jefar da wayar gefe, yadda ta samu wannan Man din ya mata daidai a soyayya, haɗuwarsu a sa'o'i ƙalilan ya gama mata komai, dole ta same shi ya zame mata mallaki, da ta watsar da AbuƊalib sai ta rungume shi ta yi aure cikin kwanciyar hankali. Ajiye wayar ta yi ta koma ta zauna, "Abun dai gashi nan," ta fada a bayyane, "Shi ya zama wawa gaya nan ba aikin fari ba na baki ba hira ba labari, yo me zan ma da mutum haka? Tunda an ce ya koma haka kuma zai dawwama a hakan wallahi ba zan zauna da kai ba." Wayar ta dauka ta sa yatsansa ta fara kokarin saka thumb print sai dai kamar ta sa dutse wayar ko motsi ba ta yi ba. "Don Ubanka bara na fito maka a mutum, tashi ka tura mini kudi miliyan dari AbuDalib." Sam ko motsi bai yi ba, kara girgiza filon da kansa yake kai ta yi, "AbuDalib. AbuDalib."
Wata dunƙulewa da ya yi ya sa ta yin baya tana kalloshi, dunkulewa yake kamar wanda ciwon ciki ya turnike, zuba mai ido ta yi idan mutuwa ma za ka yi, "Allahumma sauki, abinda ka bari ni kadai zan ci in cinye." Kofa ta nufa tana "Bara na fice kada na yi mugun ji da mugun gani ma..." ihun da ya yi ya sa ta tsayawa cik, juyawa ta yi a dan tsorace tana kallonshi, zaro ido ta yi ganin ya mike ya sandare kamar icce, da sari kuma ya sake dunkulewa cigaba ya yi da magowa yana kiran hasbunallahu wa niimal wakilu, maimatawa yake ba adadi yana dunkulewa yana mikewa, wata juyawa ya yi ya fado daga kan gadon, ƙasa ya faɗa tim. Zabura ya koma yi kamar ana tsittsira mashi allurai, magowar da yake ta ƙaru, yi yake tamkar wanda ciwon cikin ya yi ma mummunar kamu sai dai abun ya fi karfin haka, gaba daya Badiyyah abun ya girmi kwakwalwarta kallonshi take a tsorace, "AbuDalib," ta fada dan karfi ganin jini ya biyo ta hancinshi, "Wace irin mutuwa ce wannan?" Shuru ya yi kamar ba shi ke bige-bigen ba.
"Abu Ɗalib," ta ƙara faɗa ƙasa-ƙasa wani irin tashi ya yi zaune, sai dai ko idanuwansa bai buɗe ba, "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un," yake maimaitawa da ƙarfin masifa.
"Kai AbuƊalib!" Shuru ya yi jikinsa ya hau wata irin jijjiga, a slow yake faɗin, "La haula wa la ƙuwwata illah billah." Ƙura mashi idanuwana ta yi, don ta ga wani abun ne daban da wanda take tsammani. Buɗe idanuwansa ya yi yana kallonta, hawaye suke kwararowa daga cikinsu, kamar an mishi duka. Rufe idanun ya yi ya koma ya kwanta ƙasa kan shimfiɗaɗɗen kafet ɗin ɗakin.
"AbuƊalib..." Ta sake kiran shi, zuciyarta na ɗaɗarniyar kar mugun ganin ne da ta guda ta yi. "Abu Ɗalib," ta sake faɗa. Da wani irin ƙarfi ya amsa yana kiran "LILBIRRAH!"
SH 11
Gaba ɗaya idanuwanta suka yo waje, "LILBIRRAH kuma?" Ta tambayi kanta cikin mamaki, "AbuDalib!" Ta kira shi da ƙarfi. "Na’am," Badiyya ya amsa cikin muryar galabaita, tashi ya yi zaune yana share hawayen da ke tarara daga idanuwansa, hannunshi ya kalla ya ga jini, "Ya Salam, Badiyya me ya same ni? Ina Lilbirrah? Kai ya Allahna, ina Ummanah? Badiyya su nake son gani, wani abu nake ji game da su, suna ina? Wurin su zan tafi..."
Yana fadar maganar ya mike tsaye yayin da Badiyyah ta daskare kamar wani gunki. Buɗe ƙofar ɗakin barcin ya yi ya fita, tozali da falon da ya yi ya dakatar da shi, ji ya yi ƙwaƙwalwarshi ta ƙara hautsinewa, "Ina ne nan?" Runtse idanuwansa ya yi yana son tuno abinda ya faru. Ƙasa ya faɗi daɓas yana dafe kansa da ke juyawa. Da karfi ya kira sunan Badiyyah, a zabure ta iske shi tana raba idanuwa kamar an kai akuya mahauta. "Ke ina ne nan? Ina nake? Ina Lilbirrahta? Khouhar dina tana ina? Na ce tana ina?" Ya ƙare maganar yana daka mata tsawa.
Bakinta kawai ke motsawa, amma sam ba ya jin me take furtawa, miƙewa ya yi sam bai damu da tsamin da jikinsa ke yi, toilet ya shiga don ya yi wanka ya je gun Khouhar ɗinsa, tsaye ya yi yana kallon kansa jikin madubin ban ɗakin, fuskarshi ya shafa da ya ga ta yi rama sosai, sannan ya yi wani haske kamar ba shi ba, ga jini a hancinsa ga hawaye sharkaf a fuskarsa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una! Wai me ya same ni ne?" Wasu hawayen da ya rasa takamaiman dalilin zubowarsu suka sake yo ambaliya, duƙawa ya yi wanke fuskar tass, "Babu wanda zai faɗa mani gaskiyar abinda ya same ni sai Ummana da Khouhar ɗina na san ba za su min ƙarya ba, ba zan yi wankan ba ma, idan na je wurin Umma na yi, na san Lilbirrah ma tana can." Shi kaɗai ke surutunsa, sai da ya gyara fuskarshi sosai sannan ya fice. Badiyyah na tsaye bakin kofa tana dakon fitowarshi, tsananin mamaki ya hana ta komai, so take ya fito ta tabbatar da gaskiyar lamarin da take tsammani. Wuce ta ya yi ya nufi wurin wardrobe, ba komai cikinta sai tarkacen kayan da ya sa ya cire, sai kuma akwatinsa daga gefe, "Ya salam." Ya faɗa, "Ke wai ina ne nan? Na ce maki ina ne nan? Kaina juyawa yake na rasa gane inda nake."
Matsawa ta yi gab da shi cikin salon yaudara ta ce, "My Boo, ka manta wai muna Austria, ka mance mun zo Vienna..." labari ta soma ba shi, a tsawace ya ce, "Ke dakata! Dakata na ce!" Faɗawa ya yi kan gadon ya runtse idanuwansa, jefi-jefin abubuwan da suka faru suke faɗo mashi game da zuwan shi Vienna shi da Badiyyah, taron karrama shi da sauransu, "To me ya sa ban zo da Lilbirrah ba? Ya aka yi na zo da Badiyyah na baro Lilbirrahta? Ai da ita ya kamata na zo, duk wata nasarata Khouhar ce ƙashin bayanta... Ya aka yi to..." Ya ƙare zancen zucinsa yana kallon Badiyyah.
"Ka tuna ko My Boo," wani kallo ya mata, "Dan Allah ki ƙyale ni in huta, ki fita kawai ina son in huta." Tsaki ta ja ta miƙe ta fice daga ɗakin. Runtse ido ya yi, yana jin wani irin abu, zuciyarsa ta yi nauyi ya rasa mene ne abin yi. Wayarshi ya jawo, duk ta canza, tun daga kan tsarinta,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 14