Share this page
iya samun matsala gagaruma bayan haihuwarsa, sannan bugu da kari koyaushe ina tsoron tsohuwar bayarabiyar nan Innarsu Kulu, wadda haka nan zuciyata ta kasa amincewa da ita duk da tana kawo min ziyara da duba yanayin lafiyata a kowace safiya. "Kin yi shuru Amatullah? Da ma na yi tunanin ƙin amincewarki, hakan ya daƙile ni ga yi miki magana tuntuni, sai dai kuma tsorona a kan hali da yanayin mutanen unguwar da kike zaune ya ingiza ni har na amayar maki da zancen, don Allah Ama ki amince kin ji." Saddar da kaina na yi ƙasa saboda irin kallon da yake mini mai cike ma'anoni daban-daban da kuma nuna ƙagara na son ya ga na amince mashi. "Kin amince?" Ya faɗa a tausashe. A hankali na daga kaina, tare da yi masa nuni da hannuna na amince. "Alhamdulillah, Alhamdulillah," ya maimaita har sau uku, alamun jin dadi na amincewa ta. "Na ji dadi Ama, kuma insha Allahu rabbi na yi maki alkawarin ba za ki samu damuwa da mu ba tsawon zaman da za ki yi Insha Allah." Dan gajeran murmushi na yi, har muka isa asibitin yana yi mini surutu da ba ni labarai kala-kala. Muna isa ina tafiya da ƙyar, duk da abubuwan ƙarin jini da Yunus yake kawo mini bai sace kumburin jikina gaba daya ba, wanda Maman Yunus ta ce min ba komai, kuma da yardar Allah ba zai ba ni matsala wurin haihuwata ba. A wahale na haye matakalar bene, muna isa Yunus yana min sannu, sannun da ya kamata na samu daga Uban Abunkaunata, sai dai ya yi fatali da ni ya watsar da ni bayan ya goga mini bakin fenti da mummunan tabo a rayuwata. "Mace ce ta yi komai," wata zuciyar ta ayyana mini lokacin da muke isa ofishin Maman Yunus. Muna shiga ita ma ta dora nata sannun. Dakin da take yi mini gwaje-gwaje muka isa. A wannan karon ma ta tabbatar da komai lafiya kuma haihuwa tana gab da yardar Allah kamar yadda ta ga alamu. Bayan an gama Yunus ya dauko ni domin komawa gida. "Ama bara na siya miki dan tsire da nama mai taushi a wurin nan na san zai miki dadin ci." Ya faɗa yana yin fakin daidai wurin. Fita ya yi daga motar, bai jima ba ya dawo mini da naman wanda kamshinsa ya sa na ji yawuna na tsinkewa, karbar ledar na yi na bude nama ne ya yi jajir, ɗan ɓalla na yi na saka baki, daɗinsa ya gauraye mini bakina ga taushi da laushi kamar auduga. "Ya yi daɗi ko? Ai ina son naman gurin yana da laushi sosai." Yunus ya faɗa. Jinjina kai na yi alamun ya yi daɗi kam sosai. Buɗe wani ɗan sif da ke gefensa ya yi, a mamakina sai na ga ya fiddo waya ƙirar kamfanin apple. Tsuru na yi ina kallon wayar, “Khouhar, ga iPhonazation nan na siyo miki ki riƙa fa-fa, na san ku 'yam matan nan, sai kun rike iPhone kawai kuke ganin kun cika 'yan gayun 'yammata, a yi ta nunawa ana fa-fa... Kin ga tawa, Andoroid touching-touching kuma ta ishe ni…” Muryar da na yi kewarta na ji ta dawo mini sabuwa fil cikin ƙwaƙwalwar kaina a lokacin da ya siyo mini iPhone don ya faranta raina kuma ni ma na shiga ya yi. "Ki karba mana Ama, ni duk abinda na yi maki na yi fisabilillah kuma na san ko nan gaba ba zan yi da na sani ba." Zancen Yunus ya dawo da ni hayyacina, jinjina mashi kai kawai na yi, na karbi wayar ina jujjuya ta, sabuwar waya kirar iPhone latest version. Kafin na fara jera mashi godiya na ya ce, "Kin san wani abu, na manta da siyen SIM Card, ga yamma ta yi sosai bari sai gobe kawai idan kin koma can gida, sai na siya maki SIM din, kuma ka ki yi chargy, kodayake na ga nan gidan ma kaman ba wearing ko?" Jinjina kai na yi, "Koma ka tafi da ita duka gobe na karba wayar na da tsada kar a kwace min." Yar dariya ya yi, "Duk wanda ya kwace ko ay sai ya ji a jikinsa Ama, don nasan zai iya taɓa lafiyarki ni ko ba zan lamunta ba." Murmushi na sakar masa. Na ce, "Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi." Har muka isa gida muna yin yar hira irin wacce muka saba, wanda da yawa Yunus yana ba ni labarai ne wasu na barkwanci wasu kuma na shi ne wanda ke cike da abubuwan ban dariya da irin gata da kulawar da yake samu gun Mamanshi, wacce takan tunatar da ni tawa rayuwar mai yanci kafin na fada halin garari. Kamar yadda ya saba har kofar gida ya ajiye ni, bankwana muka yi sannan ya juya a kan zai je ya dauki Mama su koma gida, saboda Juma'a ne lokacin tashinsu ya yi. Ina shiga gidan ba kowa sai Babansu Ayuba da ke cikin gidan, sannu ya yi min ni ma ita na mayar mashi na wuce dakina. Bude ledar naman na yi wanda a irin yadda nake cin abinci zan iya wuni biyu ban cinye shi ba, duk na san sana’ar Nama suke yi a gidan hakan bai hanani na dauko naman na kawo ma Baban Ayuba ba. "Nagode sosai, nagode kin ji." Komawa na yi ɗaki na zauna irin zaman nan na cin tuwo na fara cin naman domin na ji dadin shi sosai. Sallamar Ayuba na ji bakin ƙofa, taƙarƙarawa na isa bakin ƙofar, "Kai mun ga abun alheri mun gode sosai." "Ba komai," na yi mashi nuni. Ba tare da shawara ba na kwaso 'yan kayayyakin da na tara na amfani, kayan abinci da sauran tarkacena na ba shi. "Na me ye?" Ya tambaye ni? "Da ma gobe zan tashi, shi ya sa na ba ka kayan ina godiya da irin taimakon da ka yi mini a lokacin da nake cikin buƙatarsa, Allah ya saka da alkhairi Nagode sosai," na zayyana mashi da bebencina. Sosai Ayuba ke murna don yana sane da cigaban da na samu, ya ji daɗin samun kayan amfanin da na ba shi. Tafiya ya yi yana ta mani godiya da Allah san barka. Komawa na yi ɗaki na ƙarasa cin namana, bayan na kammala na fita waje na wanke hannuna na yi alwala na koma cikin daki. Sallolin magrib da Isha na yi a tare domin tashi na mini wahala sai na yi sallolin gaba ɗaya. Hannuna rike da wata hadaddiyar tasbih counter da Yunus ya ba ni, dayan hannuna na dago na sumbace shi sannan na dora a kan cikina. Hirarmu ta zuci da zuci na fara. "Abun Kaunata..." Wani murmushi na saki mai bayyana zallan farin cikina. "Abun kaunata, ka gani ko, duk da an tozarta mu an wulakanta mu, Allah ya yi nufin ba za ka zo duniyarmu ba a wulakance, abun kauna cikin 'yanci za ka zo kafin 'yancinka cikakke kuma na haƙiƙa ya bayyana. Ina sonka Abun kaunata. Kai ma kana son Ummanka ko?" Murmushi na yi, zuyciyata cike da amincewa Abunkaunata ya amsa mini na sauke hannuna. Kishingidawa na yi inda nake na cigaba da tasbihina, gefe ina jin Abun Ƙaunata yana ta juyi cikin duniyarsa mai cike da duhu. Gani na yi Saratu ta ɗage labulen ƙofata da ƙarfi, wanda har ya tsorata ni ya sa ni tashi zaune da ɗan razana. "Fito, fito..." Take ta maimaitawa cikin faɗa da hayaniya. Da hannu na ce mata lafiya? Me ya faru?" Tsaki ta ja ta ce, "Fito na ce, so nake ki bar gidan nan yanzu-yanzun nan, don har na samu wacce za ta zauna ma ɗakin," ta ƙare zancen tana nuna mani wata mace tiƙeƙiya da ke bayanta. Rasa me zance mata na yi, cikin kiɗima na yi mata alamun roƙo, hannu biyu ta sa tana niyyar jawo ni. Hannu na ɗaga mata alamun kar ta taɓa ni, domin bana muradin irin azabar da na sha a lokacin da abun ƙaunata yake a gudan jini na kuma maimaitawa a lokacin da nake sa ran zuwansa a kowane lokaci. Sosai gidan ya kacame da hayaniya, ko kaɗan Saratu ba ta jin ban baki balle hakuri, mutanen da suka shigo sai dai su kalle mu su wuce. Cikin hayaniyar da ake Innarsu Kulu ta shigo, hankalina tashe na yi inda take. Tambayar Saratu take, "Me ya faru?" Harara ta watsa mata, sannna ta ce, "Gidan za ta bar mana, yanzu-yanzun nan, don na gaji da zamanta haka nan." Wasu irin ƙwallah suka zubo min, shin ba na ce gobe zan bar musu gidan ma gaba ɗaya ba, ta bar ni na ƙarasa kwana ɗaya jal da ya rage mana. Juyawa na yi wurin Innarsu Kulu, "Ki ce ta taimaka min gobe zan tashi, Yunus mai Yunus Hospital zai mai da ni gidansu, ki ce ta bari sai da safe zan bar gidan..." Duk bayanin da na yi wa Innarsu Kulu shi ta yi wa Saratu, sai dai sam ba ta ji ba, sai ma gefe da ta yi ta buga tsalle ta dire ta ce sai na bar gidan babu fashi. Babansu da ke gefe duk da tsufansa ba ta sauraren shi balle ta ji me yake cewa. Tuni fuskata ta jiƙe da ruwan hawaye, sai bebenci nake na ƙarin roƙonta, amma tamkar ina yi wa dutse. Innarsu Kulu ta ce, "Tun da dai wannan abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa ke Sister (sunan da take kirana da shi) ki zo mu tafi gidana ki kwana gobe da safen sai na kai ki asibitin su Yunus ɗin shi ke nan. Ko haka bai yi ba?" Ba don raina ya so ba na ce hakan ya yi. "Yawwah to shiga ki sanyo hijabinki mu tafi." Gaba na yi na shiga ɗakin na saka Abaya na ɗaura kallabinta a kaina sannan na sa Hijab. Innarsu Kulu ta taimaka mini da ɗauko kayana da suka yi saura, ni kuma na zaro jikkata mai ɗauke da ƙananun tarkacena muka fito. Wurin Babansu Ayuba na je na sake mashi godiya. Jinjina kai ya yi tare da yi mini fatan alkhairi muka fita. Maimakon mu yi cikin unguwar sai muka nufi bakin hanyah. "Na ɗauka gidanki nan bayan mu yake?" "Eh wallahi ko, nan yake Sister sai dai kuma tunani na yi ban faɗa ma Babansu Kulu ba, kuma ɗakin shi kaɗai ne muke ciki gaba ɗaya. Shi ne zan kai ki gidan Sisterna nan gaba kaɗan yake sai ki kwana a can ɗin." Shuru na yi zuciyata ta kasa nutsuwa, cikin rashin sanin yadda zan yi na ce to shi ke nan mu je ɗin ba damuwa. Kafin mu ƙarasa titi wata mota ta yi fakin gefenmu, da wani suna na ji ya kirata, tafiya ta yi gurin mai kiran. Ban san me suka tattauna ba ta dawo tana, "Brotherna ne, gidana za shi kin gani mu je kawai ya sauke mu, mun ma samu sauƙi." Jinjina kai na yi a sanyaye, tare muka isa muka shiga cikin Motar irin ƙirar Sienna ɗin nan ta fi kama da motar jigila, mutum biyu ne a gaba sai baya ni da Innarsu Kulu, a hankali muka fice daga layin muka hau babban titi. "Yawwah Boss, mu je Ikorodu aiki ya kammala." Ta faɗa tana min kallon da na kasa fahimtarshi wanda ya sa gabana mummunar faɗuwa da ya sabbaba ma abun ƙaunata yin wani juyi tamkar zai diro duniyar a daidai wannan lokacin. SH 9 Cikin firgicin da ya dirar mani lokaci ɗaya na yi mata nuni, "Me kike nufi? Ina za ki kai ni?" "Za ki ga inda zan kai ki Sister," ta ƙare maganar tana sakar min wata shu'umar dariya. Hannunta ta miƙa wurin mutumin da ke gaban motar ta karɓi wani farin ƙyalle. Tabbas na san irin ƙyallen nikan gani a talabijin, sannan na karanta a wasu litattafai, ana sa sinadarin hodar iblis ko wani sinadarin a sa wa mutum a hanci domin a fitar da shi hayyacinsa. "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!" A lokacin da na tabbatar cewa Innarsu Kulu da mutanen da take tare da su suna nufin cutar da ni ne. Tunkaro ni ta yi da ƙyalle, sai dai duk da raunin da ke tare da ni hakan bai hana ni yin ƙasa da fuskata da sauri, da duka hannayena biyu na sa na rufe fuskar. Hannunta guda tasa da ƙarfin tsiya sai ta ɓanɓare hannuwana sai dai ta kasa samun damar hakan, sosai kokowa ta kaure tsakaninmu, su ko wanda suke a gaban motar ko a jikinsu tamkar ba su san muna yi ba, wani irin karfi ya zo mini na bigi fuskarta da gwiwar hannuna, cikin azama na dunkule hannun Innarsu Kulu na ƙwace ƙyallen, kamar yadda ta yi niyyar saka mini shi a hanci hakan na samu nasarar dankara mata shi a nata hancin, baya ta yi suu ta faɗa kan kujerar motar tamkar matacciya. Juyowa na yi na fuskanci gabana ina mayar da numfashi, idonuwana sun ƙeƙashe babu alamun hawaye ko kaɗan, sai zuciyata da ke tsananin suya tamkar kosan da ke cikin kwanon mai. "Ya za ni yi? Me ye abin yi? Ina za su kai ni?" Shi ne abinda ke kai kawo a cikin ƙwaƙwalwata tare da tunanin samun mafita. Da sauri na sa hannu na fara kokarin bude murfin motar sai dai sam ba ta ko alamun motsi balle na saka ran za ta bude. Dayan ya juyo yana min kallon shashasha, cikin hausarshi mara daɗi a kunnen mai sauraro ya ce, "Madam babu inda za ka je, saboda mun biya kuɗinka da bebi naka, za ka ba mu bebi naka kafin mu kai ka inda za mu siyar da kai..." Wani irin gumi ya tsattsafo min, na daina fahimtarsa tun lokacin da ya ce, "Mun biya kuɗinka kai da Baby naka..." Abun ƙaunata, abun ƙaunar nawa suke hari, abun ƙaunar nawa ne suka karbi kudinsa da ni kaina da ke jigilarsa nake tsumayen zuwansa, da ma Innarsu Kulu bibiyar da take yi mini kenan. Dukkan illahirin jikina ya hau karkarwa, yayin da zufa ta ida wanke ni tamkar an yi mini yayyafin ruwa a kaina. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un na ƙara faɗa a zuciyata, yayin da nake fitar da numfashi mai zafi kamar daga salansar babur. "Ya Ubangijin da yake ji na a halin da babu mai ji na sai shi kaɗai, ya Allah ka kawo mini dauki ya Allah kar ka bari a cutar da ni da abun kaunata." Juyawa na yi gefe cikin tunani da neman hanyar nema wa kaina mafita, wayar Innarsu Kulu na yi arba da ita kan cinyarta, jikina na rawa na dauki wayar yayin da suke tuƙinsu hankali kwance babu abinda ya dame su da ni. Kallon wayar nake ya zan yi? Wane taimako za ta iya yi min? Wani abu ya faɗo mini, "Wannan phone ɗin numebers ne na hospital da na business dinmu, wannan kuma na family ne, amma wannan ita ce official numberna duk wanda ya kira wanda yake da dalili ne da ni, duk mai kira a wannan numbern to VIP ɗina ne..." Wata hira da muka taɓa yi da Yunus wata rana za mu je asibiti. Tunani nake ta yadda zan haɗa numbern a yadda ya zayyana ta, idan na samu to me zan faɗa masa. Vibration ɗin waya da ya gauraye motar ya sa na yi wata irin zabura, sai dai ba wayar hannuna ba ce, wayar mai tuƙin motar ne. Dagawa ya yi ya soma magana cikin harshen turanci, ji na yi yana faɗin, "Mun kusa zuwa oga, muna wurin Oshodi Markit, ta yi haka baby yana satinsa na hamsin da biyu so da mun zo cire shi kawai za a yi…" Wani yawu na haɗiye mai kama da dunƙulen dutsi, kallon matattar wayar keypad ɗin Innarsu Kulu nake yi, ina sake tariyo numbern da Yunus ya faɗa mini ta faɗo tass 07080007007 tabbas haka take, ban kira shi ba, sai text na rubuta mashi, "Yunus ka taimake ni, ga ya nan wasu za su je su yanka ni ni da abun kaunata, muna wurin Oshodi market cikin mota Sienna ja, Ama ce." Tura message din na yi zuciyata cike da fatan ya shiga. Gudu suke yi sosai, ya yin da tsorona ya linku, da sauri na kashe wayar na yi kasa sannan na tilla ta ƙarƙashin kujerar da muke. "Ya huwa ya man la huwa illah huwa..." nake ta maimatawa a zuci. Dayan da ke gefe ya juyo, wata irin dariya ya saki, "Madam," hannuwana biyu na hada wuri ɗaya alamun roƙo, dariya ya saki yana kada kai, "Madam za mu sayar da kai sassan jiki naka zai yi kudi," kallon direban ya yi yana, I swear suna sake sakin dariya. Dukkan jikina ya saki, ya yin da jikina da na abun kaunata yana ta juyi tamkar ya san abun da ke faruwa da mu. Mun wuce Oshodi market sosai, mun yi nisa da ita mun tunkari Ikoroudo kamar yadda na ji suna fada, ganin mun shiga wata hanya marar mutane ya sa wani tashin hankalin ya sauko mini, "Shi ke nan, haka Allah ya hukunta ma rayuwata, zan bar duniya a kaskance jikina da bakin fenti mai muni, abun kaunata kuma sanyin idaniyata, shi ɗaya kwallin kwal a duniya zan rasa shi, gaskiyata mai girma za ta cigaba da wanzuwa a lulluɓe ba tare da ta bayyana ba...," wani irin gunjejen kuka na yanke kauna da ke dugwigwiyar zuciyata na fashe da shi. Cikin fitar hayyaci na sa hannu na fara bubbuga kofar motar, domin neman taimako sai dai duhun dare da ya yi ma komai mayafi ya hana tsirarun masu gani shaida me nake yi, kuka nake yi sosai tamkar zan hado da makwagorona, wani haske ya dallo mu ta gabanmu wanda ya dishe ganin idanuwanmu. Ji na yi sun fara ƙoƙarin yin baya da motar da sauri, sai dai kafin mu yi nisa muka yi karo da wata motar ta bayanmu, wanda ya ida gigita mu ni da nake bayansu da su da suke sarrafa motar. Gefe suka yi da sauri, sai dai zancen da muka ji cikin mazuƙar sautikanmu ya ƙarasa firgita su da wani irin karfi tsiya suka ja motar domin su gudu, motar da ke bayanmu ta bi motarmu yayin da kafin mu isa inda daga cikin layin muka yi kicibus da motar 'yansanda. Tsaye muka yi cikk, yayin da motocin 'yansanda suka yi mana kawanya, kuka nake na fiitar hayyaci domin ganin taimakon Ubangiji da ya zo mini a lokacin da na fidda tsammani. 'Yansandan suka ba su umarnin su fito hannuwansu a sama alamun sun zama kamammu, kasa motsawa na yi saboda yadda na ji jikina dukansa ya zama tamkar an ɗaure shi da igiyoyi. Cikin hasken da ya gauraye wurin na ga an tunkaro ni da sauri, Yunus ne cikin tashin hankali, "Ama are you fine, na ce kina lafiya?" Sabon kuka na fashe da shi, yunkurawa na yi da niyyar fitowa daga motar sai dai gani na yi wani duhu ya mamaye ilahirin ganina. ★★★★★ Farfadowwa na yi na gan ni a kan gadon asibiti, da sauri na dora hannuna a kan cikina. Abun Kaunata yana nan, mu duka muna nan a raye, na ayyana a raina. Runtse idanuwa na yi abunda ya faru yana dawo min tarr cikin kwanyar kaina, wasu sabbin hawaye suka ziraro mini, na gode ma Allah da ya tseratar da ni ya kiyaye ni ya kiyaye mini abun kaunata. Har abada ba zan manta Lagos ba ba zan manta Innarsu Kulu ba, kuma ba zan gushe ba ina yi musu addu’ar Allah ya yi min sakayya da ita da sauran wanda suke da hannu a alhakin cutar da ni. "Sannu Amatullah," Juyawa na yi da ƙyar hawaye na cigaba da bin gefen fuskata, "Sannu kin ji, lallai Allah ya auna miki arziki, Allah ya dada kare ki kin ji." Jinjina kai kawai na yi, "Ya jikin naki? Ina fata babu inda yake miki ciwo." "Babu Mama, jikina da sauki sosai," na yi mata nuni. Tashi na yi zaune, saboda fitsari da na ji ya kulle marata, a hankali na taka na shiga bayin cikin dakin. A daddafe na fito yayin da na ji jikina ya kara nauyi, ƙasan cikina ya ƙara ƙullewa, har na gama abinda nake a bayin na fito na kasa tsaida hawayena. Maman Yunus ta kara yi mani sannu. Shayi ta hada mai kauri ta miko mini, tana ta yi mani maganganu na lallashi masu taushi da sanyaya zuciya, tare da sake jaddada mani ba abinda ya same ni kuma ya samu abunƙaunata. Sam na kasa tsaida hawayen, abubuwa marasa adadi da tunane-tunane sun cika kwanyata, kadan na sha tea din na koma na kwanta. Yunus ya shigo, na yi gaggawar rufe idona na yi lamo kamar ina barci. Daga gefena na ji yana, "Mama ya jikin Ama, ta tashi da karfi ko?" "Da sauƙi sai dai akwai tarin damuwa tare da ita." Tattaunawa suka cigaba da yi ina kwance ina saurarensu barci ya yi awon gaba da ni. ★ Gaba daya daliban Malam Saleh sun hadu a kofar gida, Dayyabu da suke kira da Babban Yaya ya karaso da mota J5, kafin ya ce wani abu daliban sun fara ruguguwar hawa kan motar. Malam Saleh da ke gefe ya ce, "A bi a hankali yaran Malam kuma kar a yi abinda bai kamata ba idan an je gona, kun ji ko?" Bara ma in fada muku ina nan zuwa yanzu zan biyo bayanku. Cikin jin dadi yaran suka tafi, domin ransu sake yake a duk lokacin da za a gona ranar ba a karatu. Kai tsaye suka nufi gonar da ke yammacin garin Katsina, suna isa suka hau aikin gona na barbaje taki kafin saukar ruwan shufka. Lokacin da Malam Saleh ya zo har sun ci karfin aikin, bayan sun gama suka ci abinci da hura da Malam ya je da su. Dayyabu ya karaso wurinshi cikin girmamawa ya ce, "Malam gida za a tafi?" Shuru ya yi yana nazari. Dan nisawa ya yi ya ce, "Mu je a cirema Gonar can ta gabas sabra an dade ba a yi mata shufka ba ita ma sai a kawo taki, yanayin da ake ciki bana dole duka gonaki zan yi noma." Cike da mamaki Dayyabu ya ce, "To Malam." Zuwa ya yi ya ja motar suka haye suka yi gonar wadda ke da nisa da wadda suke. Suna isa yaran suka hau aiki, ɗaya daga cikinsu ya ɗan yi nesa da su dan yin fitsari wani abu ya gani kamar hayaki na tashi a gaba kaɗan da inda yake, kura ma wurin ido ya yi sai kuma ya ga wuta ta taso ta nufo shi gadan-gadan, a guje ya bar wurin yana ihun wuta, yaran malam wuta. Duka yaran gudu suke yi, yayin da Dayyabu ya hango su sun nufo shi a guje, cikin faɗa ya ce, "Kai, lafiya? Me ya faru?" A rikice yaran suka ce, "Wuta muka ga tana ci babban yaya." "A ina," ya tambaye su da mamaki. "A can," suka haɗa baki wurin faɗa. Cikin al'ajabi Ɗayyabu ya ce, "Wuta a wurin nan, to wuta cikin dajin nan ai sai dai wutar daji ko? Amma bari mu gani." Ya ƙare zancen yana tafiya don ya tabbatar da abin da suke fada. Tunkarar wurin ya yi, sai dai ji ya yi wani irin tsoro ya dirar mashi hade da tashin hankali. Wani abu ya hade kutt cikin makoshi wanda bai san dalilin zuwan shi ba, a hankali ya fara karanta ayatul kursiyyu a bayyane da duk ayoyin neman tsari da suka fado bakinshi. Ji ya yi kamar an daka mashi tsawa ana kiran sunanshi cikin wani irin mummunan amo, "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!" Ya fada ba tare da ya yi baya ba, Bismillah ya yi cike da kwarin gwiwa ya cigaba da tunkarar wurin yaran Malam na bin bayanshi. Wani katon dutsi ya gani wanda ga alamu ɗauko shi

Chapter 6 of 14