Share this page
da dukkan yadda ya santa. Ƙoƙarin fiddata daga key ya yi, sam ya mance shi, sai dai ya saka yatsanshi cikin sa a ta buɗe. Lambar Ummansa ya fara kira, sai dai switch off matar ta tabbatar masa. Kan lambar Lilbirrah ya koma, ita ma shuru ya ji ta. Hankalinsa ya tashi, duk da yana jin jikinsa kamar da zazzaɓi hakan bai hana shi tashi ya fita falon ba. Kai tsaye hanyar waje ya nufa, da sauri Badiyya ta tari gabanshi, "Kai AbuDalib, ina za ka? Zuba mata idanuwana ya yi yana kallonta kamar sabuwar halitta. Cikin ɗaga murya ta ce, "Tambayar ka nake wai ina za ka? Kodayake na lura kai ma ba ka sani ba, saboda na ga alamun haukar taka ta ida birkice ƙwaƙwalwarka, ta watsa duka saitin tunaninka, shi ya sa kake wannan surutun, kake tambayar ina wata Ummanka da wata Lilbirrah? Ina Khouhar ko?" Wani irin kallo ya watsa mata, ya matsa gab da ita, "Badiyyah kin san me kike faɗa kuwa? Ummana da Lilbirrah, Uwata da 'yaruwata kuma matata kike cewa wasu? Su kike cewa wasu?!" Ya faɗa da ƙarfin gaske. Baya ta yi tana ɗan tsorata, "To Umman taka da Lilbirrah ba wasu ne Abu..." Kafin ta kai ƙarshen zancenta ya watsa mata wani lafiyayyen mari. Dafe kuncinta ta yi hawaye na biyo idanuwanta, "Ƙarya kake wallahi, ƙarya kake AbuƊalib. Da kai da abinda ka mallaka nawa ne, kuma na kira su da ba wasu ba kuma ba kowa ba ne gunka ni kaɗai ce..!" Wani marin ya sake watsa mata ɗaya gefen fuskar, wanda ya tilasta mata haɗiye kalamanta, "Ke kike ƙarya Badiyyah..." Cikin ihu ta ce, "Na rantse da Allah kai ne maƙaryaci, ina Umman taka ina Lilbirrar suke a nan? Ba ka ga Vienna kake ba? Ka yarda da ni," ta faɗa tana sakin wani malalacin murmushi hawaye na zarya kan fuskarta. Kallon mahaukaciya yake mata, don abun nata ya fi kama da sabon hauka. "Lallai kin haukace Badiyyah." "Uhmmm! Ka je ka neme su to mu gani, Umman da Khouhar ɗin naka da kake iƙrari ka je ka neme su mu gani, in ka isa ka je inda suke." Wata mahaukaciyar dariya ta saki, "Umman da ta tsine maka da Lilbirrar da ka danƙara ma saki uku ƙwarara da jar biro su kake batu ko?" Ta ƙare maganar dariyarta na ƙaruwa. "Ke Badiyyah!" Ya faɗa a kiɗime, baya ya yi yana jin ƙafafuwansa na neman kayar da gangar jikinshi, "Umman tawa ta tsine min. Kuma ni, ni, ni saki matata Lilbirrah? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Dariya take kamar mahaukaciya. Miƙewa ya yi ya koma ɗaki kanshi na wata irin juyawa. Waya ya ɗauka ya soma kiraye-kirayen waya, sai dai ya gaza samun duk wani da yake tsammanin samu. Lallai akwai matsala gagaruma wacce ya kasa gane ainufinta da tushenta, fata ɗaya yake a ce zancen da Badiyyah ta yi mashi ƙarya take. Buɗe akwaitinshi ya yi ya fiddo tarkacen passport ɗinshi, yellow card da sauran abubuwansa na tafiya domin shirin barin garin goben ranar ba sai wani lokaci ba. Wayarsa ya buɗe ya ɗauki lokaci mai tsawo ba ya a dandalin what's app. Ɗayar wayarsa ta abokan kasuwancinsa ya duba, abubuwa ne ga su nan ya yi su ba yabo ba fallasa, sai dai shi yana aiki ba kamar na ɗayar wayarsa ba, sannan ga tarin saƙonni da bai buɗe ba. Kanshi yake sarawa sosai, don ya rasa gane wane zaren tunani zai kama, duk abinda yake ji yake son sanin gaskiyarsa ya fi ƙarfin Badiyyah. "Ummansa ta tsine masa ya kuma saki Lilbirrah saki uku da hannuwansa," Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, yake maimaitawa. ★ Kwance yake rub da ciki, tsananin tunani yana neman tarwatsa masa kai, yadda ya ga rana haka ya ga tsayin daren, sannan bai kuma bi takan Badiyyah ba, wacce yake ji da ganinta tamkar wata halitta ta daban ba mutum ba saboda munanan kalaman da ta faɗi kan Ummansa da sanyin ransa Khouhar ɗinsa. Ta janibin Badiyyah kiran Mom ɗinta take amma ta gaza samunta, hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, duk da irin marirrikan da ta sha wurin AbuƊalib wanda har ya kumbura mata fuska, amma sam bai dame ta ba, gagarumar matsalar da ta sako kai take son a yi gaggawar magancewa, sai dai duk yadda ta so samun wayar, ba ta samu ba ɗib take. Dubarar kiran yayanta Baba Alhaji ta yi, duk ta san ba sa ga maciji, amma buƙatarta ta dole ce kuma shi kaɗai zai sada ta da Mom ɗin. Kiran wayarshi ta yi, kamar yadda ta yi tsammani tana kira ta shiga. Ɗauka ya yi muryarsa a gimtse ya ce, "Lafiya?" "Na kira wayar Mom ba ta shiga, ina so na yi magana da ita." "Ni ma na kira ban samu ba." Ya faɗa a gimtse. "To kana ina ne?" "Na yi balaguro, ki cigaba da trying har ki samu." Yana faɗar haka ya datse kiran. Sauke wayar ta yi tana sauke numfashi, jikinta a sanyaye ta kwanta kan kujerar da take kai. AbuƊalib ya fito ganinsa ya sa Badiyyah saurin miƙewa zaune, "Idan kin ga dama ki shirya, gobe za mu koma Nigeria." Gabanta ya yi wata irin faɗuwa, tabbas suka koma haka ita da AbuƊalib har abada, tarin kuɗaɗen fa? Zuciyarta ta tambaye ta. Wani huci ta fitar daga bakinta da ƙyar ta ce, "Allah ya kai mu lafiya." ★★★★★ YUNUS SPECIAL HOSPITAL Zaune nike gaban Maman Yunus jikina duk ya yi sanyi, cikin tausayawarta gare ni ta ce, "Amatallah, Insha Allah kina gab da haihuwa kin ji." Haka nan na ji hawaye sun zubo mini, jikina ya yi nauyi sosai ga wani abu da ya danƙare mani ƙasan zuciya, na kasa walwala tun ranar da Innarsu Kulu ta yi nufin sayar da ni da Abun Ƙaunata. "Sorry Ama, Insha Allah lafiya lau za ki haihu ba tare da wata matsala ba." Ban ce komai ba, sai aikin share hawaye da nake yi, "Za ki sha tea?" Ɗaga mata kai na yi alamun eh. Tashi ta yi ta jawo flask ɗin ruwan zafi, kallonta nake tana ta ƙoƙarin haɗa shayin, ji na yi Ummana ta faɗo mani a zuciyata, tabbas na yi rashinta, wani irin kewarta ta ratsa dukkan jikina, na kasa kintacen wani irin gata da kulawa zan samu daga gare ta, a lokacin da zan haifar mata jika, halittar da take son gani tun kafin zuwansa a duniya. Hawayena suka ƙara bulbowa, sorry Maman Yunus take ta ce min. Miƙo mini shayin ta yi, hannu na sa na karɓa kaɗan na sha na ji ya ginshe ni. Komawa na yi na kwanta kan gadon asibitin tare da fatan Allah ya kawo min barci mai nauyi ya yi awon gaba da ni. "Salamu Alaikum." Yunus ya yi sallama bakin ƙofar ɗakin, Mamanshi ta ba shi umarnin ya jira domin na kimtsa, tashi na yi zaune na saka hijabi saboda jikina daga ni sai wata doguwar rigar bubu irin marar nauyin nan. Sai da ta ba shi damar shigowa sannan ya shigo, fuskarsa sake take ko kaɗan Yunus ba shi da ɗacin rai. Kallon Maman ya yi, "Mama, shi ne na tafi ko ki kira ni ki ji yadda aka ƙare da case ɗinnan ko?" "Ɗan Mama, ka yi haƙuri mana ka san ina fama da patient ko, kuma Ama ba ta jin daɗi sosai." Murmushi ya sakar mata, "Ba komai Mom, zolaya ce kawai, ni ki kula da Ama ya fi mun komai yanzu." Kaɗa kai ta yi tana kallon shi cikin so da ƙaunarshi. Ni ko ina gefe na yi dukum, a tausashe ya ce, "Mutanen nan sun jijjiga mana Ama, ga shi har yau ba ta cikin walwala. Sannu ya jikin naki?" Duƙar da kai na yi, 'yar gaisuwar da hannu ma ta gagare ni, sai hawaye nake kamar wacce aka yi wa duka. Mama ta ce, "Yau kam jikin ba daɗi a bar ta ta huta." "Okay, Allah ya sauƙe ya kawo Babyn nan ki samu sauƙi ki huta Ama." Mom ta ce, "Amin. To yanzu faɗa min ya aka yi da case ɗin?" "My Lovely Mom, bara na faɗa maki, kin san case ɗin nan ma yanzu gwamnati ta nemi na fitar da hannuna kuma bar musu. Saboda kin ga waɗannan da aka kama, dama ana neman su Mama, saboda ashe manyan masu safarar mata da yara ne a garin nan, sannan kuma har siyar da naman sassan jikin ɗan adam suke, ita kuma wannan Inna take ko me ye sunanta ma, tana kai musu mutanen ne, nan take silfarsu a wajen sana'arta. To tunda ta ga Ama a gidan nan ta saka ran ita ma za ta kaita, riba biyu saboda ga ta ga Baby, shi ne suka haɗa baki da 'yar gidan ko me ye sunanta ita ma." ya ƙare zancen irin na mai nazari. "Yawwa na tuna, sunanta Saratu ita ma jami'an tsaro sun kamo ta. Saboda da ita aka haɗa baki aka yi plan aka kori Ama a gidan yadda za su je su siyar da ita ɗin." Kasaƙe na yi ina sauraren labarin da ya girmi hasashena. "Allah Mama, na ji daɗi nagode wa Allah da ya kai ni rayuwar Ama, kuma ya ba ni damar ceton rayuwarta da ta bebinta kin ga na samu lada." Murmushi ta sakar masa, "Haka ne Ɗan Mamansa, Allah ya saka maka da alkhairi ka ji." "Amin, Mamana." "Yaushe za mu tafi gida to?" "Yau zan kwana gun Ama, ka je kawai." "Wayyo Mom, zan yi kewarki fa." "Kar ka damu, Ama ba lafiya dole na tsaya." "Ni ma na fi son haka ai, da kanki kina kula da ita Mom." "Zan tafi sai an jima My Mommy, Gud Night nake son cewa." Miƙewa ya yi tsaye, wanda kusan a tare suka miƙe, ni dai ina kwance daga gefe ina kallo da saurarensu, wayayyun mutane ne sosai, sam ba su da matsala. Rungume Maman ya yi bayan sake ta sannan suka fice waje, ba a jima ba ta dawo cikin ɗakin. Sannun ta da ba ta gajiya da ita ta hau yi mini, rufe idanuwana na yi ban san lokacin da barci ya sace ni ba. ★ 3:00am Kamar ana buguna na ji hakan ya sa na buɗe ƙwayar idanuwana, kallon agogo na yi ƙarfe uku daidai na dare. Gabana ya ɗan faɗi ganin ukun dare ne. Tashi na yi zaune dangal-gal, hular kaina da ta cire na ɗauko na saka, gefe kuma kan ɗayan gadon Maman Yunus ce ke barcinta a nutse. Ji na yi fitsari ya taso mini kamar na daɗe ina jinshi, miƙewa na yi na taka da ƙyar na buɗe toilet ɗin. Sai da na gama abinda nake na fito, ji na yi jikina ya fara sauyawa, kamar tsira-tsira na tasowa daga ƙarƙashin tafin ƙafata. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," na ambata ƙasan raina. Tun bayan da na samu addu'ar a mafarki ban sake fuskantar zafi da tsirar da ke galabaitar da ruhi da gangar jikina ba. Ƙoƙarin tuno addu'ar nake yi, sai dai tamkar ban taɓa saninta ba, bayan ina karantata a kowace rana, safe, rana da kuma dare. Tsirar na ji ta fara yawa a cikin ƙwarukan ƙafafuna, "La haula wala ƙuwwata illah billah," na ayyana a raina cikin yanke ƙauna da fuskantar wani sabon bala'i da na ji ya diro mini daidai lokacin. SH 12 Ji na yi azabar na cigaba da ratsa sassan jikina, yunƙurin motsa ƙafata na yi sai dai ita ma ta yi cik tamkar an kafe ta da kusa, "Tabbas babu makawa yau mutuwa zan yi." Na ayyana a raina, hawaye na silalowa daga idanuwana, jikina tamkar an zuba mini ruwa zufa ta wanke ni ko'ina, wani irin gurnani da na fara ya tayar da Maman Yunus, ganin yanayin da nake ciki ya sa ta miƙewa tsaye a rikice, "Ama me ya same ki haihuwar ce ta zo?" Ta ƙare zancen tana ƙarasowa gare ni. Yadda ta ganni ne ya sa ta ida shiga cikin tashin hankali, jikina ya sandare wuri daya sai rawa yake yi tamkar an hada mashi wutar lantarki. "Amatullah, Ama…" take ta kiran sunana tana ƙoƙarin jijjiga ni, sam ta kasa motsa ni, ni ma kuma na kasa motsawa ko kaɗan. Yunƙurawa na yi da ƙarfin tsiya jin wani abu da ya tokare mini cikin maƙoshi kamar zai tsirga maƙwagowarana, Ya Allahu, na kasa yin komai ko da a ƙasan raina ne, sai wani irin numfashi da nake fitarwa tamkar zan shiɗe. Maman Yunus ta rike ni tana kiran sunayen Allah, gaba ɗaya ta rude ta rikice ƙoƙarin tankwara jikina take yi amma ta kasa agaza mashi da komai kamar yadda ni ma na kasa sarrafa shi ko yaya, abinda ya tokare makoshina ya ƙaru take jini ya fara ɗiga daga hancina idanuwana suka yo waje kamar mai shirin barin duniya, a guje Maman Yunus ta fita don samo ɗauki, wani irin juyi cikin jikina ya yi wanda ya zo daidai da sarawar wani abu cikin ƙuguna kamar an buga mini guduma. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ta zo mini cikin zuciyata, cikin neman rayuwa irin na mai rai na sake kokarin yunkurawa a wannan karon na yi nasarar motsa ƙafata, jan ta na yi da kyar na isa jikin gadon. Maman Yunus ta shigo tare da wasu nurse guda uku, kama ni suka yi su duka hudun suna ƙoƙarin hau da ni kan gadon, sai dai abun ya gagare su azabar da ta ishe ni ta sa ni durƙushewa ƙasa kan gwiwoyina, gaba daya na fice daga hayyacina sai wani numfashi da nake yi da kyar wanda ya bawa su Maman Yunus tsammanin mutuwa na gab da tafiya da ni. Ɗaya daga cikin nurses ɗin ta ce, "Ma, wannan ya yi kama da har da wani abun daban, amma ba iya haihuwa ba ce." "Okay," Maman Yunus ta faɗa tana ida rikicewa. Ruwan roba ta ɗauko ta kwarara cikin cup, addu’a ta fara tofawa cikin tana gamawa ta tsiyaya su cikin bakina, ji na yi azabar ta karu kuguna ya ci gaba da sarawa wanda nake ji har cikin gadon bayana da dukkan ilahirin jikina, yanayin yadda nake yi ya sa Maman Yunus fadin, "Haihuwa ce ta zo yanzu, haihuwa ce Ummi," ta ƙare maganar tana neman ɗaukin nurse Ummi. Sosai lamarin ya koma mini nakuda gadan-gadan, Maman Yunus tare da nurse din suka cigaba da shirin tarbar haihuwa, tabbas nau’ikan azaba kala-kala ne amma ban taba jin kwatankwacin wanda nake ji ba daidai wannan lokacin. Na kai kimanin awa uku cikin gumurzu, wadda nake ji a raina na hakura da komai na rayuwa na haƙura da duk wasu burikana, roƙo nake yi Allah ya dauki raina ko na samu na huta. Abun da ke tokare da makoshina ya sake tasowa, hannun da ke dafe da kuguna na yi gaggawar dagowa na rike wuyana, Maman Yunus kuka take da idanuwanta domin ba ta taba ganin wata mai haihuwa a irin halin da nake ciki ba, a daidai lokacin kuma na ji kuguna da wasu ƙasusuwana da na kasa tantance na wane bagire ne sun motsa lokaci daya, tsananin radadin ya wuce duk wani sanina, tamkar an cire min wani abu na ji a makoshin hakan ya ba ni damar furta, "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un," da tsananin ƙarfi, a daidai lokacin kuma na ji abun kaunata ya ratso jikina da taimakon Maman Yunus ya ƙarasa dirowa a cikin duniyarmu, duniyar ruɗani da rikici. Wani irin nannauyan numfashi na sauke, haɗe da ajiyar zuciya, na yi baya luuu kafin na iya ba wa kaina taimako na ga wani duhu mamaye ganina. ★ BAYAN WASU AWANNI A hankali na fara bude idanuwana, biji-biji na fara gani ga tsananin nauyi da suka yi mini, sake rufe su na yi zirr na ji saukar hawaye, hannuna na yi ƙoƙarin ɗagowa shi ma jinsa na yi ya yi mini nauyi, ware idanuwan na yi sosai a kanshi, ganinsa na yi sakale da zaren karin ruwa, ɗayan hannun na ɗora kan cikina, jinsa silib ya sa ni zabura sai dai cikin matuƙar gudu irin na ƙwaƙwalwa abinda ya faru da ni ya soma dawo mini, "Abunƙaunata," na faɗa da sauri tare da yunkurawa da nufin tashi zaune, daidai lokacin Maman Yunus ta shigo, da saurinta ta karaso ta mikar da ni zaune. "Sannu Amatallah, sannu." Jinjina kai na yi, da hannu na yi mata nuni ina abun kaunata? Da rai ma kuwa ya zo ko ba rai? Mace ce ko namiji?" Murmushin da Maman Yunus ta yi min ya ba ni tabbacin da ransa ya zo. "Nutsu Amatallah, Abunƙauna da ransa ya zo, kuma namiji ne, kyakkyawan yaro kaman balarabe..." ta ƙare zancen tana ƙara gyara mini zamana. "Alhamdulillahi," na ɗaga hannunwana sama ina yi wa Allah godiya. Juyawa ta yi baya da ni kadan, gani na yi ta juyo da jariri cikin wani hadadden farin showel mai matukar kyau, fiddo shi ta yi daga cikin shawul din ta juyo mini da fuskarshi, "Kin ganshi ko Amatullah," "Na ganshi," na faɗa hawaye na sakkowa daga idanuwana, hannuwa na bude da nufin karbarshi, sai dai Maman Yunus ta wuce hannuwan ta dora mini shi kan ƙirjina, zuciyata ta hau bugawa da sauri wani irin sanyin dadi da babu kwatankwacin ya ratsa lungu da sakon zuciyata ya cigaba da zagaye sassan jikina, hannu na sa na dafe shi, "Abun kaunata…" na fada hawayen jin dadi na cigaba da sintiri daga idona. Maman Yunus ta duko ta sumbace ni ta sumbaci abun kaunata, hawaye ne ita ma cike fal da idanuwanta, cikin raunanniyar murya ta ce, "Abinda nake so ta in ji kenan, jiya na ji kin yi magana na kasa tantancewa ina tunani ko gizo kunnena ya yi mini ashe da gaske ne, Alhamdulillah." Jinjina kai na yi na kasa tsaida hawayena, "Ni ma na ji tamkar hakan Mama," dago abun kaunata na yi daga kan ƙirjina, kallonsa nake yi cikin shaukin soyayah, cikin shaukin so da kaunar da ban taba yi wa wata halitta makamancinta ba, na zuba mashi idanuwa ko ƙyaftawa bana yi, barci yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, gashi linkib a kansa ya yin da wani ya yi mashi kwalliya a goshinsa, hancinsa da bakinsa daidai wa daida, tabbas duk wanda ya san AbuDalib kallo ɗaya zai yi masa ya gane gudan jininsa ne, cikin muryata da ba ta gama fita ba na ce, "AbuDalib," sannan na sumbaci goshinsa da fuskarsa. Maman Yunus ta ce, "Amatullah sannu kin ji, kin sha wahala sosai." Murmushi na sakar mata, domin ji nake duk wata wahala da ƙuncin zuciyata ya yaye. "Amma Alhamdulillah, tunda ke da Abunƙaunarki kuna cikin koshin lafiya. Yanzu kafin ki ci wani abu shi ma ki ba shi na shi abincin saboda tun ɗazun ba abinda aka ba shi, ga shi yanzu kimanin karfe huɗu na yamma. "Toh Mama," na furta ban yi gardama ba. Hannu ta sa cire ƙarin ruwa da ke sarƙafe da hannuna, kasantuwar rigar da na bude idanuwa na ganta jikina babban wuya gare ta Maman Yunus ta gyara zaman Abun kaunata jikina, sannan ta ba ni umarnin na fiddo Mamanshi na ba shi, kiciniyar yadda zan yi na fara, hannunta ta sa ta fiddo sannan ta ce, "Ki yi bismillah ki sa ma shi bakinshi." Bismillah na yi kamar yadda ta ba ni umarni, zukar maman ya yi kamar ya saba da shi, wanda sai da na ji har cikin kaina. Alhamdulillah Rabbil alamin, na fada, ga abun kaunata a gabana ga maganata da na mance yadda ake yin ta ta dawo. "Allah nagode maka, Allah nagode maka," na fada cikin muryata mai cike da jimami da kuma farin ciki. Sai da Maman Yunus ta kintaci ya koshi ta karbe shi ta ajiye shi kan gadon da duk su ne suka dauki dawainiyar siyo shi. Maman Yunus ta ce, yanzu sai ki shirya a je a yi wanka, ko kuma za ki sha tea. Jikina ya yi wani kala hakan ya sa na fara zaɓar wankan. Mikewa na yi cinyoyina na ta rawa, abun ya zo in ji mai haihuwar fari ni ma abun ya zo kenan. Saboda rashin karfin jikina Maman Yunus ta kama ni har toilet muka je, kamar yadda Uwa ke kula da 'yarta a wannan lokaci da ta shiga wata sabuwar chapter ta rayuwarta haka Maman Yunus ta wanke ni tass da ruwan zafi wanda aka kare wankan da koke-koke na har da ihu. Fitowa na yi na nemi wuri na zauna, kayan shafa tun daga kan mai powder, turaruka da kayan sawa Maman Yunus ta kawo mini, tabbas ba abinda zan ci gaba da yi wa Allah sai godiya domin shi ya hada ni da Yunus da Mamansa suka tallafi rayuwata. Shiryawa na yi tsaf cikin doguwar rigar atamfa, sannan Maman Yunus ta haɗa mini hadadden shayi mai kauri da zafi tare da wata gasashhiyar kaza, sam na kasa ci da yawa, amma ta tsare ni sai da ta tabbatar cikina babu kwarin yunwa a cikinsa sannan ta bar ni na huta. Fita ta yi za ta duba marasa lafiyarta, hakan ya ba ni damar zuwa wurin abunkaunata, barci yake cikin kwanciyar hankali ɗauko shi na yi na koma mazaunina, juya shi ina sake yi masa kallon ƙwaƙwaf, ba shi da wata tawaya jikinsa ciff yake sannan yana da cikakken kuzari da koshin lafiya. A shake na ce, "Abun kaunata, barka da zuwa zuciyata, abun ƙauna ga ka ga Amminka, Allah ya kare min kai, Allah ya raya min kai, Allah ya ba ka rayuwa mai albarka, ina sonka abun kaunata." Hawayen tausayinmu ni da shi suka ziraro min. A daidai lokacin na ji ƙwanƙwasa kofa, cikin dakakkiyar muryarsa ya ce, "Mu shigo." Mayafi na sa na lulluɓe jikina, sannan na ce ku shigo. Yunus ne fuskarsa cike da annuri da murmushi, tamkar shi ne Uba ga Abunƙaunata, tamkar shi ne aka yi wa haihuwar. Cikin girmama shi na ce, "Ina wuni." Kaɗa kai ya yi, "Ama, Masha Allah Ama kin dawo magana." Jinjina kai na yi, miƙa mashi Abunƙauna na yi, karɓar shi ya yi cikin bayyanan nan jin daɗinsa, "Ama na ga abunƙauna, na ma riga ki ganinsa." Murmushi na yi ina duƙar da kaina, saboda kallon da Yunus ke yi mini tamkar ranar ya fara ganina. "Mun yi ta barka Amatullah, abun ƙauna ya zo duniya lafiya. Ban tambayi izininki ba ɗazu na zo wajen 7:00am kina ta barci, na yi masa ta'aniƙi na yi masa addu'o'i Allah ya raya mana shi." "Duk abinda ka yi masa daidai ne, kai ai Uba ne a gare shi." "Nagode," ya faɗa yana sakar mini murmushin da ya kasa barin fuskarshi. "Ya kamata a yi masa huɗuba, wane suna za a saka mashi?" A sanyaye na ce, "A saka mashi AbuƊalib." Sunan da na faɗa ya sa hawaye zubowa daga idanuwana. "Okay, amma waye AbuƊalib ba za a saka mashi Muhammad ba?" "A saka mashi AbuƊalib Yaya Yunus, amma za a riƙa kiransa da Nadir." "Shi ke nan Ama." Ɗago Abunƙaunata ya yi, ya saita bakinsa kan kunnuwansa ya fara rera mashi kiran sallah, sai da ya gama masa huɗubar sannan ya mayar da shi kan gadonsa. "Bara na je Ama, ki kwanta ki huta, kin sha wahala sosai." "Nagode muku, Allah ya saka da alkhairi." Kaɗa kai kawai ya yi, ya miƙe ya fice daga ɗakin. Miƙewa na yi na koma kan gadon na kwanta, kasantuwar akwai tarin gajiyar wahalar da na sha ban jima ba ina ta tunane-tunane kan rayuwata barci ya yi awon gaba da ni. ★★★ Inna Uwale ce tsaye kan Umma, Rumaisa ta yi kuka har ta gode ma Allah ganin Umma cikin yanayin da ba ta taba ganinta ba, duk da sun yi gaggawar zuwa asibiti, amma likita sai cewa ya yi ba su ga komai ba jikinta, hatta zargin da suke na cutar kansar mahaifa da ta same ta ba su ga komai ba, hakan ya sa za su iya cewa ma babu wani abu da ke damunta hawan jininta da damuwa ta sabbaba mata shi. Bude idanuwa ta yi da kyar ta kalli Uwale. "Uwale,

Chapter 8 of 14