Share this page
ta ji dadin dawowarka, dawowarka cikin family na tabbata tana cikin farin ciki. Nisawa ya yi, har a lokacin zuciyarsa karye take, "Rumaisa wai me ya faru ne, me ye na yi da kowa baya son faɗa mani, na san dai ko mene ne na tafka babban kuskure." "Yaya bayanin me ya same ka dogon labari ne." "Ba za ki fada min din ba," "Uhmm, yadda ka ce Yaya tabbas ka aikata babban kuskure... To ni me zance ma wai, ko ma dai mene ne wannan munafukar matar taka ita ce silar komai." "Da ma haka Baba ya ce, Wallahi sai na rabu da ita yau, yau dinnan Rumaisa." Kallon shi take kamar zararre, "Yaya ka bari ka tabbatar tukuna, don Allah kar ka kore ta yanzu ka bari gaskiyar da ita kanta ba za ta yi mata musu ba ta bayyana sannan." "Sai na rabu da ita na ce maki Rumaisa." Takawa ya yi cikin firgicin da yake ya isa bakin windown ɗakin da Umma ke kwance, zaune take suna ta labarin da bai san ko me suke fada ba ita da Inna Uwale, ji ya yi zuciyarsa ta yi kewarta sosai, idanuwansa suna kallonta kamar sun jima da yawa ba su yi tozali da ita ba. Tuno maganganun da ta yi mashi yake yi, yana jin kanshi na sarawa. Umma ta lura da ana leke ta tagar, mikewa ta yi ta zo wurin don tabbatarwa, ido biyu suka yi da Abudalib din ya kasa ɗauke idanuwansa daga kanta, "Ummana! Don Allah ki yafe mani." Baya ta koma, "Ummana ni ne AbuƊalib ɗinki fa..." Cik ta tsaya ta juyo tana kallonshi, "AbuƊalib ɗina... kai ne fa kuma na san kai ne, kai ne dai da na bawa amana ka ci, kai ne da na ba ka yarda ka ha'ince ni, ka karya alƙawarin da muka yi da kai, ka salwantar min da 'yata guda wacce nake so fiye da kowa a rayuwata. Lilbirrah, Lilbirratah ban san inda take ba, tana a raye ko a mace cikin lafiya ko akasin haka, cikin ƙoshi ko yunwa duka ban sani ba. Ta ya zan so sake haɗa ido ma da kai, fuskarka baƙi take min kamar gawayi ko kaɗan bana son ganinka, haskenka ɗaya ne wurina ka nemo min Lilbirrah." Wani abu ya haɗe cikin maƙogoransa wanda yake jin shi ya fi maɗaci ɗaci a cikin makoshinsa kalamansa na katsewa ya ce, "Umma... Na... Don... Allah..." Sai dai duk yadda ya yi namijin ƙoƙarin ida zancensa abun ya ci, ji ya yi sam ba ya da jarumtar ɗaukar kalaman da Umman furza masa masu kama da feshin wuta cikin kunnensa, dgon salati ya ja kafin ya kai aya ya faɗi ƙasa wanwar. Rumaisa ta zabga ihu, wanda ya sa Inna Uwale da ake komai kan idanuwanta ta baro dakin a hanzarce. A gaggauce suka fara ƙoƙarin ba shi taimako, sai dai masu kula da majinyata suka yi saurin kawo masu ɗauki, inda suka ɗauke shi suka nufi ɗakin bayar da taimakon gaggawa. Ita ko Umma kan gadon ta koma ta kwanta, zuciyarta na raya mata rashin daidanta cikin kalaman da ta wanke shi da su. ★★★★ IKEJA LAGOS NIGERIA Zaune nike cikin kyakkyawan dakin da aka ba ni cikin tanƙamemen gidansu Yunus, daki ne ciki da falo da toilet har biyu akwai ɗaya a bedroom sai ɗaya kafin shiga falo daga hanyar bedroom ɗin naw. Cikin sashen da aka ba ni har da kitchen da suke tare da dining area, da ka fito daga dining ɗin kuma kana haye matakala falona ne, wanda babu abinda Yunus bai zuba min ba, tun daga kan kujeru, kafet har zuwa kayan kallo. kwanana biyu a asibiti jikina ya murmuje, saboda kulawa da nake samu ta musamman daga wajen Maman Yunus, AbunKaunata ma yana cikin koshin lafiya. Dattijuwar matar da Maman Yunus ta ajiye musamman don ta kula da ni da AbunKaunata mai suna Baba Abu na bawa Nadeer, domin amsa kiran Maman Yunus na wankan ruwan zafin safe. Toilet muka je ta yi mani wankanta mai azaba wanda har na saba da shi, ina fitowa na tarar Baba Abu na yi wa Nadeer dina wanka. Zama na yi gefe na shafe jikina da wani lotion mai kyau mai kamshi, cikin 'yan kwanakin gaba daya na canza ina ji na wasai cikin kwanciyar hankali. Miƙewa na yi na tafi bedroom domin saka kaya, wanda kullum sabon kaya nake sakawa, idan na yi wankan safe sabon kaya zan saka, haka ma idan na yi na yamma, Maman Yunus komai sabo ta ba siya mana ni da Abunƙaunata. Bayan na gama shiryawa tsaf na koma falon, na tarar Baba Abu tana shirya Nadeer, raina ya yi sanyi zuciyata ta sake kallon Abun kaunata na faranta mini rai, jefi-jefi idan na ga yadda Maman Yunus da Baba Abu ke hidima da ni sai ya tuna mini Ummana, ina kewar Ummana sosai da Joonam dina, sai dai ko kadan bana jin kaunar komawa gidanmu, kamar yadda na ƙudurta a raina sai da hujjah bayyanana, watakil wasu shekaru goma ko ashirin masu zuwa, wataƙil kuma ya zama ƙasa da haka ne. Ina kallon yadda ake ta shirya Nadeer Maman Yunus ta shigo tare da mai aiki, kasantuwar yau ta kasance Asabar ce ba aiki, tana gida shi ma Yunus bai fita ba yana sashen shi. Break fast ta ba mai aikin umarnin haɗa min wanda shi kanshi wani tsari daban ta sa ake haɗa min shi. Maman Yunus kenan, a lokacin da ban gani a aikace ba zan iya karyata samun mace mai kirkinta, wata zuciyar ta yi saurin ce mini Ummanki fa, tabbas Ummana mutuniyar kirki ce sosai na ba kaina amsa. Ji na yi hawaye na niyyar zubo mini, na yi saurin mayar da su. "Ama, ki mayar da hankali ki yi break mana, kin sa yaro a gaba kina ta kallonsa." Maman Yunus ta fada tana kallona. "Mama," na fada a dan kunyace. Murmushi ta yi mini ta ce, "Ama kenan, na ga wata kunya ta ma kike ko, kalli abinki ai ɗanki ne, ɗan abunka madubinka in ji hausawa." Dariya ta ba ni sosai, bayan na gama na soma karyawa. Ina yi muna hira da Maman Yunus tana ba ni labarin ita asalin 'yar garin Bauci ce, harkar chanji ta kawo mijinta Lagos. Gyara zaman ta ta yi ta ce, "Lokacin da ya fara fa bai zama haka ba, amma yanzu kin ga yadda muka zama, bari ki gama wankan ruwan zafin nan za mu je gidanmu da ke Lekki za ki sha kallo." Ɗan zaro idanuwa na yi, "Mama yanzu wancen gidan har ya fi wannan?" "Haba wannan ɗin me." Shuru na yi don gudun wuce gona da iri. Nisawa ta yi ta ce, "Na dawo nan ne saboda ya fi min kwanciyar hankali, kin ga nan muna zamanmu a nutse ni da Ɗana." Sallamarsa cikin falon ta katse hirar, "Mom, gaskiya ni ɗan halak ne na kirki. Kin ga ina zuwa kuna sako zancena." Hararar wasa ta yi mashi, "Ah to, ni dai gaskiyata na faɗa. Ko ba haka ba ne Amatullah, Maman Baby." Murmushi na yj na sunkuyar da kaina, cikin girmamawa na ce, "Yaya Yunus ina kwana." "Ni dai ban ganshi ba," ya faɗa da sigar zolaya yana zama ƙasa wajen ƙafafun Mamanshi. "To barka da kwana Yaya Yunus." "Yawwah barka, ya My son," "Ga shi yana lafiya ranka ya daɗe," Baba Abu ta faɗa tana miƙa mashi Nadeer. Karɓar shi ya yi yana ta kallon shi yana fara'a. "Yaro yana ta ƙara kyau gwanin ban sha'awa, ni kam baya kama da ke Ama, ko Babansa ya biyo ne?" Ji na yi kamar ya ɗora min bulo, shuru na yi don tambayar ta zo mini ba shiri. Maman Yunus ta ce, "Ka ji ka ko? Rabu da shi Ama mu je hirar mu." Kaɗa kai na yi, "Ba komai Mama don ya tambaye ni kuma sam bai yi laifi ba. Da gaske ne Nadeer baya kama da ni, da babansa yake kama, irin kamar da ake cewa kamar an tsaga kara." "Ama, to mahaifinsa na da rai ko ya mutu? Me ye silar zuwanki Lagos?" Yunus ya tambaye ni, kallo ɗaya za ka yi mashi ka tabbatar ya zaƙu ya ji amsar tambayar, yayin da nake ji kamar ya mini tambayar ranar mutuwata, duk annurin da ke fuskata ya ɓace. Mama Yunus ta ce, "Kai ko me ya sa za ka tsare ta da tambayoyi haka." Murmushi mai ciwo na yi, don ban yi tsammanin wannan ranar za ta zo mini kusa-kusa ba, na ɗauka za ta ɗauki wani lokaci kafin isowarta. Ajiyar zuciya na sauke, "A'a Mama ba laifi ay don ya nemi sanin abinda ke ƙunshe a baɗinin rayuwata. Kamar yadda ka tambaye ni mahaifinsa yana da rai, sanadin zuwana Lagos kuma wata rubutacciyar ƙaddara ce marar daɗi a zahiri da baɗini irin wacce zuciya ba ta da juriyar tunawa. Ciwon 'ya mace, na 'ya mace ne. Shi ne zancen hikima da ya yi mini tasiri tun daga yarintata har zuwa lokacin da juyayyar ƙaddarata ta canza fasalin tunanina, ta karantar da ni sabon darasin da na fahimici cewa wata 'ya macen takan zamo silar zubar hawayen 'yar uwarta mace. Kamar yadda 'yaruwata mace ta zama silar zubar hawaye na, ta zama silar raba ni da farin cikina da maye gurbinsa da baƙin ciki da zullumi da tsoro, ita ce kuma silar zuwana Lagos. Ni sunana Lilbirrah. SH 15 Ni 'yar garin masu kara ce, da aka san mu da kunya kuma mun yi hannun riga da tsoro, wato Katsina birnin Dikko a can na rayu tun daga yarinta har zuwa girmana. Babana shi ne Malam Abdulhadi sai Ummatah mai suna Sa'adiyyah muna kiranta da Umma. Babana da Ummatah suna matuƙar ƙaunata, sun ba ni dukkan kulawa sun yi mini gata sun nuna mim so da ƙauna musamman Ummatah, tana so na fiye da yadda take son duka 'ya'yanta. Ni kaɗai ce wurin Ummatah sai daga bisani aka haifa min 'yaruwa mai suna Rumaisa, mun kasance mu biyu kenan a wajenta, haka Allah ya ƙaddara ma Ummanmu ba ta da yawan 'ya'ya. Ko a lokacin da ta same ni ma kowa ya fitar da rai Ummana ba za ta taɓa haihuwa ba, domin shekarunta goma da aure amma ba ta samu ƙaruwa ba, sai daga baya ta same ni. A wajen Ummana muna da babban yaya mai suna AbuƊalib, Yayana AbuƊalib bayan Ummana babu wani mutum da ke ƙaunata kamar shi. Shi ya kasance ɗan ƙanwar Umma ne, tana haihuwar shi ta rasu ko fuskarshi ba ta gani ba, Yaya AbuƊalib bai san mahaifiyarsa ba sai dai a hoto, kuma tun daga ranar da aka haife shi mahaifiyarsa ta rasu Ummana ita ta ɗauke shi, ta shayar da shi ta raine shi har ya girma, sai bayan ya girma ma sannan ya san cewa Umma ba ita ta haife shi ba. Rayuwa muke yi cikin jin daɗi da farin ciki, duk da kasancewar mu ba mu su ƙarfi ba ne, amma rayuwa muke wadata, saboda Baba bakaniken mota ne, yana da gareji babba na gyaran motoci. Baba yana da ɗayar matarsa wacce muke kira Anty. Ita tana da yara biyar, cikin hukuncin Allah su duka maza ne, Yaya Abbas shi kaɗai ne Yayana, sai sauran Ali, Yusuf, Kamal, Mustafa duka ƙannena, kasancewarmu tsakiyarsu ya sa gatan mu ya ƙaru ni da Rumaisa. ★ "Jaƙiri..." "Sarkin Gombe..." "Ya aiko ni..." "A takarda..." "A rubuce..." "Bature..." "Ya iya ƙira, ya ƙero jirgi ya ƙero mashin..." "Wayyo Ummana..." Yaya AbuƊalib ya faɗa lokacin da ya ji saukar tasbaha bisa gadon bayanshi muna tsaka da wasan jaƙiri. Harara Umma ta dallah mashi, "Kai dai kam an yi ƙaton banza. Kana namiji, maimaikon a ce hula ta ja kallabi, a'a kallabi ne ya ja hula, ina amfani." Dariya na kwashe da ita har da ƙyaƙyatawa, idanuwana kan Yaya AbuƊalib yana sosa baya. "Ke ma za ki tashi ku tafi Islamiya ko sai na haɗa da ke..." "A'ah Umma bana son bulala." Na faɗa ina miƙewa tsaye. Kallona Yaya ya yi, "Sai na rama dariyar nan da kika yi min, tunda Umma ba ta dukanki ai ana dukan ki a Islamiya, can za a rama min." "Yayah, kai da ba ka bari a dake ni ma, ta ya za ka rama dariyar to?" "Za ki gani kuwa." Ya faɗa fuskarshi da alamun ɗan fushi. Harara Umma ta watsa mashi, "Kai ni yi mani shuru, me za a gani, ana dukan yarinya kana yi kamar za ka tashi sama. Hala ka ɗauka ban sani ba, rannan har gida aka kawo min gulmar an ce ana dukan Lilbirrah Islamiya kana ƙoƙarin hanawa har tashi kake yi sama, kamar mai aljanu." Dariya muka yi baki ɗaya har da Yaya Umma ta ce, "Ka gani ko? Har ka mance." "Na ji a bar ni a mai aljanun, in dai a kan ƙanwaliliya ne to ni mai aljanu ne." Umma ta ce, "Na ji to Yaya mai ƙanwa, sai ku mai da hankali ku tafi kar ku makara." Haka muke da Yaya AbuƊalib sam baya son abinda zai taɓa lafiyar jikina, ko a gida ko a makaranta duk wanda ya taɓa ni to ya san Yaya AbuƊalib zai tare mini, hatta Malaman Islamiyarmu idan za su dake ni sai ya ce a yi mishi bulalata, wanda suka ƙi suka nace sai sun doke ni sai Yaya ya yi kamar mai aljanu ya hana dukan. Haka muke rayuwarmu ta makaranta, muna idar da Sallar asuba sai mu tafi makarantar allo ta Baban AbuƊalib, da mun dawo kuma za mu shirya a gaggauce mu tafi makarantar boko inda nike firamare aji biyar, Yaya AbuƊalib yana aji na uku. Makarantar kuɗi ce ta masu ƙaramin ƙarfi, saboda daga aji uku ƙaramar sakandare ta ƙare da zaran mutum ya gama sai dai ya tafi wata makarantar ya ƙarasa babbar sakandare ɗinsa. Da mun dawo daga makarantar boko kuma za mu tafi makarantar Islamiya da ƙarfe huɗu, idan mun dawo sai mu je Islamiyar dare, sosai Baba da Umma suka yi tsayuwa irinta daka kanmu a kan karatun sanin addininmu da na zamaninmu. Lokacin da AbuƊalib ya gama ƙaramar sakandare, lokacin ni kuma na gama firamare ɗina. Cikin kayan makarantar Pilot ya shigo a can zai ƙarasa karatunsa, ni kuma ina makarantarmu inda zan yi ƙaramar sakandare, Yaya ya zaɓi 'Pilot ne saboda tana kusa da makarantarmu, idan ya ajiye ni makarantar sai ya wuce ta su makarantar haka ya tsara mana. Cikin sababbin kayan makaranta na fito ina ya ƙwambo na zama 'yar babbar makaranta, kallona ya yi sama da ƙasa sai da ya gama ƙare mani gani ya ce, "Lilbirrah." "Na'am Yaya AbuƊalib," na amsa mashi. "Kayan sakandaren nan sam ba su karɓe ki ba, kin ganki abunka da baƙar fata sai kika yi kamar bokanya." Ƙuri na yi mashi da idanuwana, "Lilbirrah kika zuba min waɗannan idanuwan naki." "To cewa ka yi na yi muni." Na ƙare maganar cikin shagwaɓa. "Ke wasa nake maki, ai ke ma kin san kyau kika yi." Murmushi na yi daidai lokacin Umma ta ƙaraso sai da ta dafa kaina sannan ta ce, "Lilbirrah tah, ki yi bismillah idan za ki shiga ajin nan kin ji, yanzu kin shiga babbar makaranta, ki mai da hankali sosai na san kina mai da hankali to ƙi ƙara mai da hankali. Kuma na ji Yayanki na faɗin wai ba ki yi kyau ba, kin yi kyau sosai ma, tamkar wata zaiba." Daɗi na ji ya sauka cikin raina, saboda yabon da Ummana ta yi mini. Yaya AbuƊalib ya ce, "Ba wani kyau, ina kyan yake. Kuma ni ma na faɗa mata, ba ruwanta da kowa ta nutsu kafin ko irin ƙawayen nan ta yi." "To kin ji abinda Yaya ya faɗa ko ƙanwar Yayanta." Jinjina kai na yi, "Na ji Ummana." "Yawwah, to ku tafi Allah ya kiyaye." "Amin Umma." Ficewa muka yi daga tsakar gida muka shiga farfajiyar gareji inda sabon Keken Yaya AbuƊalib ke jiranmu. A nutse muka tafi makaranta, sai da ya ajiye ni sannan ya wuce tasu makarantar. Haka muka cigaba da rayuwarmu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, inda Yaya AbuƊalib ya fara sana'ar ɗinki, a cewar shi yana matuƙar son sana'ar hannu, duk da jan hankalinsa da Baba ya yi ta yi na ya riƙa zama gareji amma sam ya ƙi, ya cigaba da sana'ar ɗinkinsa. Lokacin da na yi jarabawar gama ƙaramar sakandare lokacin Yaya AbuƊalib ya gama babbar sakandare, farin ciki gare mu ba a magana, domin ji nake tamkar ni ce na gama. Yaya AbuƊalib ya zama matashin saurayi mai kimanin shekaru ashirin da biyu. A lokacin ni kuma ina da shekaru sha biyar, shekarun girma sun kama ni na yi tsayi sosai na ƙara kyau, baƙar fatata ta ƙara kwanciya idan ka ganni za ka ɗauka cewa, ni ɗin 'yar masu ƙumbar susa ne saboda yadda Yaya AbuƊalib ya tsare mini komai na buƙatar rayuwata da sana'ar da yake yi, shaƙuwarmu kuma ta ƙara ƙaruwa, duk wanda ya san Yaya to ya sanni haka wanda duk ya san ni to tabbas ya san Yaya AbuƊalib. Sana'ar ɗinki ta karɓi Yaya, yana samun ɗinkuna sosai, duk abinda ya samu kuma sai ya kawo ma Umma, wani lokacin kuɗinsa ma sai ta ɗiba ta ba shi, idan ta yi mashi magana, zancensa ɗaya ne saboda mu yake neman kuɗi. Hankalinku kwance yake, har muka shiga aji biyu na sakandare. Kowace safiya Yaya ke kai mu makaranta, idan ya ajiye Rumaisa sai ya wuce da ni, muna tafiya muna labarinmu, babu wani da zai same ni ban sanar da Yaya ba, haka duk abinda ya same shi zai sanar da ni. A dalilin yaya ko wata babbar ƙawa ba ni da ita, domin Yaya shi ne abokin nawa, kuma babban aminina. A cikin wannan gaɓar ne Allah ya haɗa ni da ƙawa wacce na ɗauka aminiya a makarantarmu muna aji na biyu. ★★★★ G.G.S.S Zaune muke cikin aji an gama break Malami bai kai ga shigowa ba, kowa sabgar gabanshi yake ni kuma kamar koyaushe ina zaune tare da abokan zamana ina ba su labarin Yayana ya ce zai siya min waya idan muka shiga aji uku. Sallamar Malam Bashir cikin ajin ita ta sa muka yi tsit kamar ba wani mahaluƙi cikin ajin. Bayansa wata yarinya ce da ba za ta wuce sa'armu ba, zubinta yarinya ce mai matsakaicin tsawo ba ka kiranta doguwa haka sam ba gajera ba ce, fara ce sosai a halittar fuskarta kuma tana da komai tsaka-tsakiya, tun daga kan hanci da baki da idanuwana. Gyaran muryar da Malam Bashir ya yi ya dawo da ni hayyacina daga kallon da nake yi mata. "Ga abokiyar karatu an kawo muku, ya ma sunanki kika ce?" Ya ƙare zancen yana juyawa wajenta. "Badiyyah Salisu," ta faɗa cikin sanyin muryarta mai laushi. Duƙawa na yi wajen Humaira Shamsu ƙasa-ƙasa na ce, "Da gani saliha ce, mu uku ne sit ɗin mu mu yi mata wuri." Duƙawa ta yi wajen Aishatu Kallah ta raɗa mata abinda na faɗa mata, take su duka suka yarda. Malam Bashir ya ce, "Ga ta nan ita ma abokiyar karatunku ce, ku zauna lafiya da ita." Duka ɗaliban suka ɗauka, "To Malam." "Yawwah, je ki zauna." Malam ya faɗa. Tahowa ta yi sumumu irin na baƙo a sabon wuri, tana zuwa kan sit ɗinmu wanda shi ne na biyu na yi karaf na ce, "Zo ki zauna nan, kin ga sauran duk su huɗu ne nan kuma mu uku ne." Murmushi ta yi fuskarta na bayyana daɗin da zuciyarta ta ji. Matsa mata muka yi ra zauna, duk da ta kasa sakin jikinta da mu jefi-jefi muna sako ta cikin hirarmu. Kwana biyu muka yi tare da Badiyyah ta fara sakewa da mu, inda da ni da abokan zamana muka dage kwafar mata dukkan rubutun da aka yi na zangon karatun da muke ciki. Sannan bayan mun gama aikin kwafar mata muka fara aikin koya mata karatun da ya wuce ta, a cewar mu kar a zo jarabawa ta kasa ba da amsa. Sosai Badiyyah ta ji daɗin zama tare da mu ta kuma ji daɗin yadda muke mata hidima. Muna haka na ji ta fara kirana da wani suna, "Aminci," ko kuma ta kira ni da, "Rai." Duk yadda ta kira ni haka ni ma nake kiranta sai muka zaɓi suna ɗaiɗaya, tana kira na da, "Rai," ko "Raina," ni kuma ina kiran ta da, "Aminci, ko "Amintacciyata." Sosai muka shaƙu, muka ƙulla ƙawance na gaske, duk wanda yake cikin ajinmu ya san ni Ran Badiyyah ce, ita kuma Amintacciyata ce. Badiyyah ta shiga jikina sosai, ko kaɗan ba ta bari wata ƙawar ta raɓe ni, sauran ma da muke ɗan ƙawancen da su, abokan zamana Humaira da A'ishatu sun saka mana idanu, suna jinjina ƙawancen da muke yi, amma kuma... Wani irin takaici ya taso mini wanda ya hana ni ƙarasa maganar. Yunus ya kalli fuskata da zallan ɓacin rai ya bayyana a kanta, "Amma kuma me Ama? Wai Lilbirrah a yanzu. Amma kuma me? Me ya haɗa ku?" Nisawa na yi, na miƙe na ɗauko ruwa kan table na sha don rage zafin raɗaɗin da ya taso min, sai da na sha ruwan sannan na cigaba da magana. Ba abinda ya haɗa mu a lokacin sai dai.. SH 16 Mun cigaba da ƙawance ni da Badiyyah, shaƙuwar da muka yi ya sa na fuskanci akwai matsalolin da ke damun rayuwarta, wasu lokutan ba ta zuwa da kuɗin break, wasu lokutan kuma sai ta yi shuru duk da dama ba ma'abociyar yawan magana ba ce, tana da shuru-shuru she is so calm and innocent. Kamar yadda takan yi, zaune take ta yi jugum kallo daya za ka yi mata ka gane tana cikin damuwa. Zama na yi kusa da ita, amma ba ta ma san na zauna ba, ganin haka ya sa na sa hannu na ɗan doke ta ina faɗin, “Aminci,” zabura ta yi. "Na’am Rai.” “Aminci me ya same ki? Me ke damunki ne haka plsss.?" Na ƙare maganar cikin bayyana kulawata gare ta. Hawaye suka ziraro mata, "Rai… Raina… ina cikin damuwa ina shan wahala sosai a rayuwar nan." "Wace irin wahala Aminci?” "Rai… Ban taɓa faɗa maki ba, gidanmu, gidan da Mamana ke aure sam ba na jin daɗin rayuwa cikinsa, wahalar da ni suke yi sosai, na soma gundura ji nake da ma ban kasance cikinsu ba." "To Amintacciyata, ba nan ne gidanku ba?" Kada min kai ta yi, "A’a ba gidanmu ba ne, ni Babana ya rasu shekara ɗaya kenan, to bayan Mamana ta gama takaba shi ne wannan ya aure ta abokinsa ne. Mu ba ma a garin nan muke ba, muna zaune a garin Shargalle ne, cikin ƙaramar hukumar Dutsi, auren Mamana ne kawai ya kawo mu nan da zama, amma danginmu da dukkan 'yanuwanmu da kowa duka suna can. Da Mamana ta yi aure shi ne ta taho da ni nan, amma zaman gidan ba daɗi Rai, kullum sai na yi kuka ina ma Babana yana nan..." Ji na yi zuciyata ta karaya, cikin tausayawa na ce, "Eyyah! Allah sarki, Allah ya jikansa da rahama." "Ameen," ta fada cikin juyayi da kewar babanta. "To nan din ba sa son ki ne? Ko wani abun suke maki?" Murmushin yaƙe da ya fi kuka ciwo ta yi, "Raina, inda Mama ta yi auren nan matansa uku ita ce ta hudu, duka cikin gida guda muke ga tarin ‘ya’ya manya da ƙanana, amma duk yawan "ya'yan nan duk safiya sai ni na yi shara na yi wanke-wankensu, kar ki ga tarin kwanoni Lilbirrah, tamkar na gidan biki. Sannan kuma abinci ma ba kullum muke samu ba, idan kuma ya samo kadan sai dai ya ba 'ya'yansa kadai amma ni, ni ɗaya ƙwallin ƙwal na za su ba ni filet guda na ci ba Lilbirrah sau tari sai dai na kwana da yunwa, haka zan tashi da ita ranar da ya gama ya ba ni kuɗin break idan bai ga dama ba haka zan taho da yunwa Lilbirrah kuma ba kuɗin siyen abinci. Yanzu haka yau kwanan mu biyu ba mu saka wani abu a cikinmu ba

Chapter 10 of 14