ma daga baya na gano kuskurena, bai kamata gata da kulawar da kake ba ni ta shafi rayuwar soyayyarka ba Yaya."
Dagowa ya yi ya kalli cikin idanuwana, "Lilbirrah, cikin kadan da kike ce ana samu a cikin matan wanda ba su da wannan mugun halin cikinsu samu, yanzu na riga na gama yanke hukunci ba zan fasa ba." Shuru na yi tuni hawaye sun ciko idanuwana, "Yaya kana gani fa har an kai kudin neman aure, ana lissafin nan da kwanaki goma za a sa rana, yanzu idan ka yi haka daidai ne?"
"Bara ma ka gani, yanzun nan Badiyyah ta kira ni ta ba ni haƙuri, har da kukanta Yaya, ta yi nadama na tabbata ba za ta sake ba."
Dan karamin tsaki ya ja, wanda ke nuna maganar da na yi tamkar na yi a iska ne. "Yaya don Allah ka yi hakuri," mikewa ya yi ya fice har Ummanmu ma ya fasa gaisarwa, makarantar ma da zai kai ni duka ya fasa, goge 'yar ƙwallar da ta zubo mani na yi na miƙe na tafi makaranta.
Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba, saboda Yaya ya tsaya kai da fata ba zai auri Badiyya ba, duk da ta yi nadama sosai a kan abinda ta yi mini amma ya kafe ya ki ya sauko. Babana da Baban AbuƊalib ba su san me ake ba, sai da aka ce ya kawo goro saura kwana uku a sa rana.
A nan ake sanar ma Baba ɗanyen hukuncin da ya yanke, Baba ya ce sam bai sam wannan maganar ba, kuma ma kayan shirme kan ɗan abinda bai taka kara ya karya ba. Duka Babbaninmi caa suka yi ma Yaya, wata ranar Laraba suka hadu suka yi mishi magana, a ranar aka samu ya sauko daga kan bakanshi, shi ma sai da ya ga rayuka sun ɓaci sannan. Sai a lokacin ya amince da cigaba da soyayyarsu bayan ya yi ma Badiyyah kashedi sosai.
Na ji dadi kwarai da gaske kan sasancin da aka yi, bayan nan da sati daya a ka sa ranar auren Yayana AbuƊalib da Badiyyah, ranar murna a gare ni ba a magana, wata hudu aka sa bikin. Kuma tun a wannan lokacin ban sake fuskantar wata matsala mai kama da wannan ba a wajen Badiyya sai ma nuna min kauna da kulawa da take yi sosai wanda hakan ya faranta ran Yaya sosai, hakan ya sa ya kara kaunar Badiyyah.
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah mai girma, lokacin bikin auren Yaya da Badiyyah ya zo, wannan lokacin yana daya daga cikin lokutan farin ciki a gare ni lokacin da auren Yaya ya yi zo.
A lokacin ɗan madaidaicin gidan Yaya ya kammalu, wanda ya sha gyara tsaf daidai wa daida ga rayuwar talaka, sannan kuma ya hada ma Badiyyah lefe na ji da gani, wanda muka yo siyayyar kayan lefen ni da Ummana da Inna Uwale. Kamar yadda ta taɓa faruwa haka lokacin kai lefen ma, yadda masu kai wa suka kai shi, haka suka dawo ko ruwa ba su samu ba daga gidansu Badiyyah, hakan ya sa dangi suka fara ƙananun surutai. Sma ba mu mai da kai ba muka cigaba da hidimar bikinmu, saura kwana biyar bikin muka fara shagulgula, murna guna tamkar ni ce ake wa auren, don ko Yaya bai fi ni farin ciki ba. Kullum cikin nishadi nake a wajen kowane event da aka yi kuwa ni ce gaba-gaba. Ranar asabar ta zo aka daura auren Yayana AbuƊalib da ƙawata kuma aminiyata Badiyyah. Ranar na yi murna marar misaltuwa, misalin ƙarfe shida na yamma muka ɗauko amarya daga gidansu zuwa gidan angonta Yayana.
A cikin kowane aure ba a rasa tsegunguma na dangi, wanda da yawa danginmu suke complain daga gidansu Badiyyah ba su kawo komai ba bayan gado da kujeru, babu kayan kicin da labulaye, babu gara da kayan dangin miji. Ummana ta yi ta kwabar bakunansu da hana su yin tsegumin, a cewar Umma da ma ba dole ba ne, sannan kuma babu laifin yarinya idan suka cigaba da tsegumin za ta ji ba daɗi a ranta.
Karamci irin na Ummana bayan kwana uku da bikin ta sa Yaya AbuDalib ya ba da dubu dari biyar muka je muka siyo kayan kitchen 'yan daidai na bukata muka saka a kitchen din Badiyyah ni ce gaba wajen jerawa, sannan kuma muka siyo labulaye aka gyara ɗakin tass.
Haka aka yi ta gungura rayuwar ana hakuri da yau da goben cikinta, na mayar da hankalina kwarai kan karatuna sannan na ki kula kowane saurayi kamar yadda na ci alwashi sai na kammala karatuna ko kuma idan ya zo saura shekara daya in gama sannan na fara kula saurayi don kar soyayya ta yi mini tasiri ta shafi karatuna.
BAYAN SHEKARA BIYU
Daidai gwargwado muna ɗan mutunci da Badiyyah duk da bai kai na lokacin farkon bikinsu ba, a lokacin abinda na lura da shi sam ba ta son ina zuwa gidansu, da na fahimci haka sai na yi nesa da zuwa gidan. Joonam ɗina zai kai ni, shi kuma babu ranar da rana za ta fito ta faɗi ba tare da ya zo gidanmu ba. Mu'amala tsakanina da shi babu abinda ya sauya, sai ma ƙara ƙaunata da yake yi da kulawa da ni da yi min duk abinda nake so, daidai gwargwado kuma ita ma Badiyyah yana sauke dukkan nauyi da hakkinta da ya rataya a kansa, ba ya taue ta da komai, amma kuma hakan bai hana ta jin ƙaiƙayi a duk wani abu da zai yi min ba, sai dai in ya yi ba ta sani ba.
A ɓangaren karatuna ya rage saura shekara daya na hada degree, hakan ya sa min tunanin fara kula samari da suke ta naci a kaina. Ina zaune ina amsa wayar wani abokin Yaya Mustafa Yaya ya shigo, bankwana na yi ma shi na kashe wayar.
Hararar wasa ya yi mini, murmushi ja yi ina gyara zamana, "Yaya yau kuma da fushi aka zo mana."
"Dole in yi fushi mana, a ce shekara ɗaya ciff wai ba ki kai mana ziyara ba, haba Khouhar ban taɓa tsammanin za ki wata ma ba ki ziyarci gidana ba."
"Kai jama'a Joonam, kamar ka sani ɗazun nan muke zance da Rumaisa za mu kawo muku ziyara ran asabar weekend kenan. Na san a ranar ba ka zuwa shago da wuri."
"Shi ke nan Allah ya kaimu."
"Amin Joonam ɗina, da ma iya wannan ne laifin?"
"Ehh mana, kina zuwa kuma kin wanke kanki."
Dariya na yi ina faɗin, "Za mu wanke shi ko tass."
"Ina Ummana?" Ya tambaye ni.
"Ummanmu tana kitchen."
"Ke kuma kina nan?"
"Yanzu ban jima da shigowa ba, na je kuma ta ce na je na huta."
"Yar Umma kenan, to shi ke nan, bara na iske ta can."
"Okay," na faɗa, yayin da shi kuma Yaya ya fice zuwa wurin Umma.
Ranar Asabar muka shirya muka tafi gidan Yaya ni da Rumaisa kamar yadda na yi alƙawari.
Ina yin sallama tun a zaure ya taso da hanzarinsa ya tare mu. Dariya nake yi sosai, "Haba, Yaya so kake tun kafin na shiga ka ja min laifi?"
Taɓe baki ya yi yana, "Ku dai mu shiga ba wani laifi, ku da ba ku zuwa daga shekara sai shekara."
"Wayyo Joonam, makaranta ce fa ta boye ni kasan aski idan ya zo gaban goshi ya fi zafi."
"Uhmm," kawai ya fada. Tare muka shiga cikin falon, Badiyyah na zaune kan kujera hakimce tana latsa waya, "Aminci bari a tuna da," na fada ina dariyar tsokana. "Uhmm ai da ƙeya ce in ji masu hikimar zance," Badiyya ta fada a dan gimtse. Zubewa muka yi kan kujera mai zaman mutum uku ni da Yaya, ita kuma Rumaisa ta yi zamanta ƙasa kan kafet da ke shimfiɗe a tsakiyar falon.
"Haba Lilbirrah haba Khouhar shekara guda daya ciff kafarki ba ta tako gidan Joonam ba."
"Yaya wai ni kam Bady ta koya maka tsegumi ne, Allah har maganar ta soma tuƙa ta, kuma fa abun nazo din ne bai taso ba, ka ga da ƙawata ma ta kira mu da na rika zuwa ganin da na ko diyata."
Kallonta na yi ina dariyar wasa, sosai ta haɗe girar sama da ƙasa, "Haihuwa ai sai Allah ya kawo Lilbirrah, tunda ba mu za mu ba kanmu ba."
"Haka ne don Allah ki yi hakuri wasa nake miki wallahi kin san ba zan faɗi haka don in muzanta ki ba."
"Okay, to ya gida ya kike ya su Umma?"
"Suna lafiya wallahi, ta ce ma a gaishe ki."
"Aiko ina amsawa."
"Ya wajen su Mama mun dade ba mu gaisa ba?" Na tambaye ta.
" Suna lafiya kalau Lilbirrah," yawwa na fada. Mikewa ta yi tana, "Bara na kawo maku ruwa to."
Mai da kallona na yi wajen Yaya. "Joonam ya gida ya aiki, na yi maka tambaya ta musamman tunda gidanka na zo."
"Ke dai kika sani."
"To Yayana har yanzu ban goge laifina ba ne?"
"Kin goge mana. Mu ba mu jima da yin break ba, amma tunda kun zo me zan girka muku?"
Rumaisa ta yi saurin cewa, "Yaya Irishi potato da soup ɗin egg and fish."
"Ke Rumaisa ki rufa mina baki, sai wani lissafi kike,".mai da kallona na yi wurin Yaya, "Ni dai Joonam bana son ka mana wani girki, idan lokaci ya yi mun yi da kanmu."
"A'a, ni zan yi muku girki da kaina, a gida ba na yi ba?"
"A nan Yaya ai gidanka ne kai za a yi wa, ko kana taya kawata ne?"
"Ina fa? Ayyuka sun mini yawa."
"To ka gani, koyaushe ba ka gajiya da goga mani bakin fenti gun matarka shi ya sa ma bana zuwa."
"Abinda za ki ce kuma kenan, ni dai zan yi abinda auta take so Irish Potato da miyar kwai da kifi."
"Allah ya ba da sa a, wannan ai ba ni na ce ba."
Murmushi ya yi yana jawo wayarsa, "Ban ba ki labari ba Khouhar, kin san harkar mining dinnan da ake yi?"
Dan daga gira na yi, "To na ji dai ana fadarsa kuma na ga irin abroad dinnan suna yinsa sosai, amma na ga bai yi yawa ba a nan."
"Ke Khouhar ba ki sani ba dai ne, amma ana yi, kuma harka ce da za a yi nan ɗin ma sosai."
"Allah ko Joonam?"
"Na ce maki zancen kike so ya yi tsayi, kin san wani Yeaster da ke zuwa shagona ina masa ɗinki?"
Shuru na yi irin na mai nazari, "Gaskiya na kasa tuna shi Yaya."
"Ina wani ɗan ƙasar Sin wanda ya zo a bikinmu har yana kula ki, kina cewa ba kya son farar fata."
Dariya na yi ina faɗin, "Joonam ka ce mini Yass abokinka kawai zan fi ganewa."
"To shi, in faɗa maki shi babban ɗan Crypto Currency ne, shi yake koya min harkar trading ɗinnan, tun bana ganewa yanzu na fahimta, wallahi Khouhar da zan samu jari na zuba a harkar nan, to nan da shekara biyu zuwa uku za ki ga na zama hamshaƙin mai kudi, kawai sai dai ki ji sunana a manyan masu kudin kasar nan ba ma garin nan ba."
Dariya na kwashe da ita, "Yaya kenan 'yan shafe-shafen za ka rika yi ko me? Kuma na ga masu yi fa ba su sa komai."
"A’ah ba ki gane ba ne, masu shafe-shafen dai idan sun tara wannan coins din za su sayar sai na rika saye, nima idan na siya ni ma sai in siyar a market din crypto."
"Okay na gane Joonam, za ka siya sai ka siyar, to da ka ce jari kenan kudi ake bukata."
"Kuɗi da yawa ma Khouhar akalla a ce kadan ina da dala dubu ashirin kasuwar."
"Ahhh, lallai kudin da yawa, ai za su kai aƙalla miliyan ashirin ko Joonam."
"Ehh mana, sun kai haka, ko a ce ba su ida ƙarasawa ba."
"Joonam ya za a yi kenan? Na ji ni ma kasuwar ta zauna min a raina."
"Gaskiya kudi kawai nake so idan na samu wannan kudin sai kasuwa, yarinya kar ki ce me ye muna Makkah? Ke har China zan kai ki mafarkinki na zama software engineer na mayar da shi gaskiya."
"Kai!" Na fada baki bude.
"Tunani nake yi na siyar da gidan nan, da 'yan abubuwan da na mallaka na ga nawa zan samu sauran Allah ko bashi ne zan ci na cigaba."
Shuru na yi saboda wani tunani da ya zo mini. "A’ah Yaya ba za a yi haka ba, harkar da ba ka san ya take ba sai ka rabu da kadarorinka saboda ita, ba za a yi haka ba Yaya, Umma ma ba za ta bari ba."
"Shi ke nan da ma ke ce abokiyar shawarar, tunda ba ki yarda ba shi kenan."
Duk labarin da muke zubawa Badiyyah ba ta dawo daga kichin ba, na shaƙi iska zan cigaba da magana ta shigo. Gaba ɗaya ɗan sauran annurin da ke fuskarta ya ƙarasa dishewa, "Uhmm na ji ana ta zuba hira tsakanin Yaya da kanwarsa, na ji har da su zancen China."
"Ke dai Bady rabu da Yaya kawai." Zama ta yi tana mana hararar kasan ido, duk da shi Yaya bai ganta ba amma ni na lura da ita.
"To ita Lilbirrah haka za ta yi ta zama ba aure, ko bayan auren mijin kamar sakarai zai bari kawai ta tafi China karatu shi ya nan zaune kamar sakarai."
"To aure dai zuwa yake idan lokacinsa ya yi, sannan kuma idan na samu halin ko bayan auren ne sai ta tafi mijin ba zai hana ba, ai ba mai tsawo za ta yi ba tunda masters ne."
"Ni tunda nake ban taba ganin wa da kanwa irin kai da ita ba, da a ce ana aure wa da kanwarsa shakikai ai da na ce me zai hana kawai ka aure ta sai in ga ta karshen soyayyah."
"Ai ko yanzu ma zan iya aurenta ko ba ki sani ba ne?"
Kallon Yaya na yi sam ban taba zaton zai mayar mata da amsar haka ba. Kallon shi ta yi a fusace, "Lallai so ya kai karshen rufe maka ido, da har kake tunanin take iyakokin Ubangiji?"
"Take iyakokin Ubangiji kamar ya?"
"Na auren ƙanwarka mana da kuka fito ciki ɗaya."
Mayar da abun na yi wasa, "Kai ku kenan muka hadu wuri daya dole sai kun yi fada a kaina."
"Rabu da ita na ga tana min wata fassara ne, ki bari na fada mata ta ji kuma ta sani ni ke ba ciki daya muka fito ba iyayenmu ne suka fito ciki daya, akwai halastaccen aure tsakaninmu." Mai da kallonsa ya yi wurin ta, "Idan gatsen da kika yi ya zo da bakin mala’iku ke ce za ki fi kowa tashin hankali na sani."
Kallon Yaya take yi kamar za ta hadiye shi, "Wai da gaske Lilbirrah ba Umma ce Babarsa ba?"
Jinjina mata kai na yi, "Haka ne amma wallahi ba soyayyar aure tsakaninmu, kin ji ma na rantse miki da Allah, ni ina matsayin kanwarsa ne haka shi kuma yana matsayin Yayana ne, kuma ko mutane a haka suke daukarmu ba mu fadar cewa ba Uwa daya uba daya muke ba, don a hakan muke jin kanmu."
Hararata ya yi, "Ni ki min shuru kina ta mata wata rantsuwa, idan aurenkin na yi ai ban aikata haram ba, babu laifi a shari'ar kowane littafi."
"Yaya a bar wannan maganar mu je zancen mu na Crypto, idan ba ya yiyuwa kuma mu mike mu koma gida."
"Lilbirrah kenan, ki kyale shi ya fada mani duk abinda yake so...," kafin ta kai aya na yi hanzarin mikewa, "Sai ku cigaba da musayar yawunku ni kun ga tafiyata, Rumaisa taso mu tafi gida, yaya sai wani lokacin kuma." Na ƙare zancen muna tunkarar ƙofa ni da Rumaisa.
"Khouhar ki dawo mana," Yaya ya faɗa.
"Allah ni mun tafi, mun karasa maganar a gida, yini kuma na fasa ziyara dai ga ta na kawo sai wani lokacin kuma."
Hannu ya sa cikin aljihu ya fiddo kuɗi ya miko min, "Gashi tunda ba za ku tsaya ba na shirya mu tafi tare, kun hau keke napep."
"To mun gode Yaya sai ka zo," na fada sannan muka fice daga gidan.
Muna fita muka tsaya jiran Napep, wata danƙareriyar mota ƙirar Marcedes ta yi fakin gabanmu kaɗan, juyawa na yi na kalli Rumaisa, ita ma ni take kallo domin ga alamu mai motar domin mu ya tsaya.
Leƙowa ya yi ta windown motar yana magana, ganin haka ya sa muka ɗebi hanya ni da Rumaisa muka cigaba da tafiya har mu yi gam da katar da Napep. Horn ɗin da muka ji bayanmu ya dakatar da mu, mai motar ne ya sake cin taren mu. A wannan karon fitowa ya yi tsagwayam daga motar bayan ya yi fakin, "Haba baiwar Allah, tun can nake maki sallama amma kamar ba 'yaruwata musulma ba kin ƙi amsawa."
Ɗaga kai na yi na kalle sa, "Masha Allah, barakallah," ya faɗa yana kallona, irin kallon da ke bayyana soyayyah a zahiri.
"Assalamu Alaiki,"
"Wa alaika salam," na faɗa can cikin maƙoshi.
"Daga ganin yanayinki ba za ki shiga mota na rage maki hanya ba, amma don Allah ba don halina ba a taimaka a faɗa min suna, numbern waya, da kuma unguwar da ake zaune, ba zan ɓoye maki ba ni dai na gani kuma ina so."
"Rumaisa ke taho mu tafi," na faɗa ina jan hannunta domin mu bar wajen.
"Rumaisa ƙanwata tsaya mana," ya faɗa har yana jan abayarta. Sakinta na yi na cigaba da tafiya, sai da na yi ɗan nisa da inda suke tsaye sannan na tsaya. Gani na yi suna magana da Rumaisa, ni ko sai aika mata nake da saƙon harara. Ina tsaye ina dakon jiranta ta ƙaraso.
"Yaya Lilbirrah mutumin yana da kirki," ta faɗa lokacin da ta zo gab da ni. Kamar in kwaɗa mata mari, "Yanzu a cikin abinda bai fi five minutes ba har kin gano yana da kirki." Ɗaga min kai ta yi, "Kin ga ma na ba shi lambar wayarki, na faɗa mashi sunanki, ya ce in faɗa maki sunan shi Jameel..."
Dogon tsaki haɗe da kyakkyawar harara da na yi mata ya sa ta tsuke bakinta. Daidai lokacin Napep ta zo ina ganinta ba kowa ciki na shige, a fusace na ce, "Idan kin ga dama sai ki shigo mu tafi idan kuma kina da sauran abin cewa sai ki zauna a nan." Shigowa ta yi tana kallona, faɗa mashi inda za mu je na yi, har muka isa gida tamkar kurame ba wanda ya ce ma ɗanuwansa wani abu.
SH 19
Ina zaune da dare na ji wayata na kuwwar neman agaji, ɗago kai na yi na kalli wayar, ganin lambar da ke yawo kan madubin wayar ba suna hakan ya sa na bar ta ta cigaba da kuwwarta har ta gama. Sake kira aka yi a karo ba biyu, shi ma har ta yi ta ƙare ban dauka ba. Jin ƙarar shigowar saƙon kar-ta-kwana da na ji ya sa na ja ɗan gajeran tsaki sannan na sa hannu na ɗauki wayar, "Please pick My call Dear." Karanta saƙon na yi har da maimaici, kafin na ƙarasa yanke hukunci wani kiran ya sake shigowa, har ta kusa yankewa wata zuciyar ta ba ni shawarar in ɗauka.
A sanyaye na kanga wayar a kunne, wata doguwar ajiyar zuciya na ji ya sauke cikin kunnuwana, "Da ba ki ɗauki wayar nan ba na tabbata da yau na kwana a asibiti." Ɗan gajeran murmushi na yi, "Kwana a asibiti kuma?"
"Ehh mana, saboda ruhin da ke ɗauke da gangar jikin yana cikin matsala kin san dole mamallakiyarsa ta fi shi shiga matsala don tafi shi rauni."
"Haka ne," na faɗa a gajarce.
"To ya kike ya kika je gida?"
"Lafiya lau."
"Ya su Mamana da Babana?"
"Duka lafiya suke."
"Na ji daɗin haka My Queen." Shuru na yi daga haka ina sauraren shi.
"Lilbirrah." Ya kira ni cikin wani sauti mai nauyi.
"Na'am," na amsa ina sauraren abinda zai faɗa min, "Zan faɗa maki gaskiyar abinda ke raina, tun lokacin da kika tunkaro ni a kallo ɗaya da na yi maki na rasa tunani da dukkan nutsuwata, kuma a take na yanke hukuncin na ga matar aurena, ina fata mafarkin da nake ya zama gaskiya."
Murmushi na yi, "Lallai kam wannan shi ake kira daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi,"
"Ni ba zaƙi kaɗai miyar ta yi ba, tsokokin nama na riƙa gani cikinta."
Dariya ya ba ni sosai, "Kai na ji daɗi sosai, ni Jameel yau sai na yi wa kaina kyauta domin na sa sarauniyata dariya."
"Uhmm, gaskiya kana da abun barkwanci Malam Jameel, amma abinda zan faɗa maka ni matar aure ce."
"Kalar ki bata yi kama da ta masu ƙarya ba, saboda haka a fitar kalamanki kaɗai na gaza yarda, duk da dama kanwarmu Rumaisa ta faɗa mani Lilbirrata ba matar aure ba ce."
"A surutunta har ta faɗi haka? To shi ke nan, na ji ba ni da aure amma gaskiya ina da tsayayye."
"An sa muku rana?"
"A'a an kusa dai..."
"Alhamdulillah, na ji na kuma yarda, kenan a yanzu da ni da shi duk muna takara ne, saboda haka ina so a ba ni dama ni ma na shigo cikin fagen yaƙin neman zaɓe, a bar ni a fafata da ni ko a primary election na faɗi, na dai gwada sa a ta."
"Shi ke nan toh, ban cika son jayayya ba, saboda haka Allah ya ba mai rabo sa'a."
Wani ɗan ƙaramin ihu ya buga, "Alhamdulillah, Allah ya ba mai rabo sa a."
"Amin," na faɗa. Hira muka cigaba da yi sama-sama, a wayar da muka yi na lura da Jamil mutum ne mai saurin sabo, domin yadda yake magana da ni tamkar mun yi shekaru da sanin juna.
Kashe gari da safe Yaya ya shigo, kasantuwar muna hutun ƙarshen mako ne ina gida. Bayan sun gama gaisawa da Baba sannan ya shigo ɗaki ya gaisar da Ummana. Miƙewa ta yi ta fita daga ɗakin jin Baba na kiranta daga can cikin ɗakinsa, Ummana na Yaya ya ce, "Khouhar."
"Na'am Joonam, ya aka tashi, ya aka baro min ƙawata."
"Ki yi shuru don Allah kar ki kuma ɓata min rai."
"Me ya faru kuma Joonam?'
"Ba buƙata sai kin sani, kawai rabu da ƙawarkin can, sam ba ta da hali wallahi, a kanta yanzu ina jin tsoron mutane masu shuru-shuru."
"Yayana, me ya faru?"
"Na ce ki rabu da zancenta, mu yi magana mai amfani. Kin san wani abu bayan tafiyarki sai da Ankit ya sake kirana a kan harkar nan, Joonam gaba ɗaya hankalina ya karkata kan abun nan."
"Ka san ko Yaya, ina dawowa gidan nan sai da na faɗawa Umma, ta ce haka ba zai yiyu ba ka siyar da kadarorinka ka faɗa harkar 'trading'. Amma akwai abinda na yi tunani idan har Umma ta amince to haka za a yi."
"Me za ki yi Khouhar?"
"Ba zan faɗa maka ba Joonam, sai na yi sannan."
"A'a fa Shalele, kar ki je ki ɗauko min magana."
"Idan na ɗauko ta ma Yayana ga shi a gabana zai biya."
Murmushi ya yi ya ce, "Haka yake Khouhar, rigima ko zan siyar da kaina ne domin tseratar da ke zan siyar."
"Kai Yaya, shi ya sa kullum kuke faɗa da Badiyyah a kaina, dole ta nuna kishinta."
Dogon tsaki ya ja, "Don Allah idan muna tattaunarwarmu ki daina sako min Badiyyah, ki bar mu can mu cigaba da fafatawa, da ba don an ce aure ɗan hakuri ba ne ta ya zan cigaba da zama da Badiyya ma." Ya ƙare maganar ransa ɓace.
"Shi ke nan na daina Joonam, amma don Allah hakurin da ake a ƙara wani a kai, duka mata haka muke."
"To ke meyasa ba ki abinda take yi?' ya ƙare zancen yana yi min kallon harara.
"Yayana, ni ma zan yi sai na yi aure ina kishin mijina sannan."
"Mtseww," ya ja wani tsakin. Miƙewa ya yi a saluɓe yana, "Ni kin ga tafiyata, idan kun yi magana da Umman kin neme ni."
"Sai an jima Joonam a gaida min ƙawata." Sam bai bi takaina ba sai komawa da ya yi wurin su Umma ya yi musu bankwana.
Murmushi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 14