Share this page
Ta kare zancen tana ba shi peck a kunci. "Shi ke nan, Allah ya kiyaye ki gaida min da Mommy, sai kin dawo." Mikewa ta yi ta fita tana mishi bankwana. Har ta bace ma idanuwansa yana bin ta da kallo. Tafiya za su yi gobe za su bar Katsina su isa birnin Kano inda jirginsu zai tashi. Badiyyah princess Shona dinsa ta tafi gun Ummanta. "To ni fa?" Ya fada a bayyane, shuru ya yi yana tunanin da ke kulle ƙwaƙwalwar kansa. Mikewa ya yi da sassarfa ya haye steps din bene, ɗakinsa ya shige ya saka jallabiya ya fito da key din mota a hannunsa. Shi ma ficewa ya yi daga gidan, kai tsaye Yammawa ya nufa yana zuwa kan kwanar titin da za ta sada shi da Unguwar ya miƙe, sam ya kasa tinkarar gidan duk yadda ya so zuwa, da samun amsoshin da suka gagari ƙwaƙwalwarshi ya kasa. Cikin gari wuce don zuwa gun abokanshi, nan ma ji ya yi baya iya kusantarsu, tamkar wani abu na baya-baya da shi game da su, hakan ya sa ya kara ma motarshi gudu ya nufi wajen gari. Gidan zoo ya tafi, tamkar soko yake bin dabbobin daji yana kallonsu, ya jima a gidan Zoo ɗin yunwa da ta addabi cikinsa ta sa dole ya bar wurin ya nufi restaurant. Zama ya yi cikin ƙuncin rai da takurar zuciya da suka yi ma rayuwarsa dabaibaiyi, yana jin kanshi na juyi, jefi-jefi yana kallon mutane suna walwalarsu, to me ma ya sa suke dariya? Wani haushi ya taso daga ranshi, ya miƙe ba tare da ya ci abincin ba ya bar gurin. Jigum ya yi cikin mota, tamkar ya fashe da kuka, cutar ƙwaƙwalwar da ta same shi sam ba ta kyauta ba, ta raba shi da farin cikin rayuwarsa, ta salwantar da walwalarsa a haka kuma ya ji sauƙinya warke, "To me ye ke damuna?!" Ya faɗa da ƙarfi tamkar zai tarwatsa motar. Sam ba shi da amsa, hakan ya sa ya yi lamo yana jin bigawar zuciyarsa ga wata azababbar yunwa tana jijjiga 'ya'yan cikinsa. Gajiya ya yi da zaman, kai tsaye ya yi wa gidansu Badiyyah da ke unguwar Iyatanci tsinke. Kallon gidan yake kamar lokacin ya fara ganinshi, a da babban gida ne amma da likkafa ta cigaba an ɗebi wani sashi na gidan an gyara shi tsaf tamkar gidan wata sabuwar amarya. Sallama ya yi ya shiga falon Momin Badiyyah, kwance ya samu Gimbiyar tasa tana waya hankalinta kwance. Ganin shi wuri-wuri kamar an koro shi ya sa ta tashi zaune da sauri, "My lafiya na ganka kuma ko sanar da ni ba ka yi ba za ka zo." Fuskarsa da tsananin damuwa ya ce, "Wallahi ko, tun ɗazu na fito na rasa inda za ni kawai shi ne na taho nan, ban ma fito da waya ba ni Shona." "Uhmm, to hakan ya yi. Ka ci abinci dai ko My." "Na je restaurant na rasa me zan ci My, abincinki kawai nake so, girkinki." "Eyyah My, ni bana son kana zama da yunwa fa. Yanzu bara na zuba maka abincin, Alala ce na tarar Mom ta yi." "Ina ci Shona, a zuba mini," ya faɗa a ƙagare. Mikewa ta yi ta shiga kitchen ba ta jima ba ta fito da Alala da miyar kifi, sai kuma Jug dauke da soɓo mai sanyi. "Ga ya nan My ka ci don Allah," Ta ƙare zancen tana ajiye abincin a gabansa. Bismillah ya yi ya fara cin abincin, kallonsa yake yana son tuna wani abu game da shi amma ya kasa, sai dai ya yi ɗan guntun murmushi ya ce Alala, yana zuba ma plate ɗin ido. Wani irin kallo ta watsa mashi tamkar ta yado idanuwanta. Alala tana cikin favorite din abincin Lilbirrah, tana yawan cin ta, tana yawan yin ta, ba ta wuce tayin ta idan an mata, takan saye ta ko a hanya ne saboda son da take mata, kenan tunanin Lilbirrah ne yake yi, wai tunanin nata ba zai taba barin ƙwaƙwalwarsa ba, ko dai mugun bugu za ta yi masa a ƙoƙon kansa, idan ya yi karamin hauka sai ya mance komai daga baya ya warke. Dagowa da ya yi suka hada idanu ya katse tunaninta, duk yadda ta so kakaro murmushin ƙarya da zai dishe ɓacin ran da ke daddale cikiin zuciyarta ta kasa. Cikin kulawarsa a gare ta ya ce, "My Shona me aka yi miki? Me ya faru na ga kamar ranki ya baci?" "Ba komai My Boo, gani na yi kana cin abincin nan daga gani yunwa ta kama min kai da yawa a wunin nan." Uhmm kawai ya fada, ya cigaba da cin abincin cikin nutsuwarsa ta halitta. Mommyn ta yi sallama cikin falon, ganin AbuDalib a falon ya matukar ba ta mamaki don ko a zuwan Badiyya ba ta sanar da ita zai zo ba. Bakinsa na rawa ya duka har kasa ya gaishe ta. "Mommy barka da dawowa, sannu da zuwa." "Yawwa," ta amsa mishi. "Ina wuni Mommy," ya kuma gaishe ta. "Lafiya lau, ai na je unguwa ne, ashe kana nan." "Wallahi ko Mommy yanzu na shigo." "Okay, to sannu ai yanzu ma sai tafiya ko?" "Ehh." "To Madallah ai marece ya yi." "Eh Mom," ya furta. "To bara ta shiga ta shirya sai ta zo ku tafi ko?" "To Mom," ya fada tare da mikewa ya koma kan kujera ya zauna. Tabe baki uwar ta yi, tabbas AbuDalib ya canza tamkar ba shi ba, sai yanzu ta gane abinda Badiyyah ke faman faɗa mata. Uwar daka suka shige ita da Badiyya, suna shiga murya kasa ta ce, "To na zo maki da sako fa, ya za a yi ya zo ya yi kane-kane cikin falo." "Hmm, Mom kin gani, haka fa ya koma haka nake fama da shi duk ya zama wani shashasha, yanzu idan ban ce ya tafi waje na haka zai yi zaune. Tsakani da Allah da yana yiyuwa na fi son in ga mijina dai tsaye cikakken namiji kamar yadda yake da, kin ga ay tsayayyan namiji ne amma yanzu duk ya wani susuce." "To ba haka ake so ba?" Mom ta faɗa. "Ba haka ba Mom, ni na fi son shi yadda yake da, yanzu fa ko abu na yi sai dai ki ji yana ta yi hakuri, yi hakuri Shona, yi haƙuri. Haka zai ta faɗi. Ni buƙatata ya mance da waɗancan mutanen, na cigaba da tsara mishi rayuwa da mutanen da zai yi mu'amala da su, amma ya tsaya yadda yake a da," Badiyya ta ƙare zancen cikin damuwa. "Ni ki kwantar da hankalinki duk wani abu za a gyara shi ɗaya bayan ɗaya, yanzu ki je ki lallaba shi ya fita na miki bayanin maganin nan." Fita ta yi falo ya yi zaune cikin jangwam ɗin da ya saba. "My mu tafi gidan ko?" Mikewa ya yi, "To My Shona. Mu tafi." Gaba ya yi har sun kusa ficewa daga falo ta ce ba ka yi wa Mom bankwana. "Wai na manta wallahi," hararar shi ta yi ta baya. "To mu je ka yi mata bankwana, sai mu tafi." Komawa ya yi ya ce, "Mun tafi sai anjima Mom," yana fadar haka ya yi kwana ya koma ya ce mu tafi. Kada kai kawai ta yi, sunan wata waka wai ita halittah, AbuƊalib ya zama wata halitta cikin 'yan kwanakin nan. Tafiya suka cigaba da yi sai da suka yi nisa da kofar gidan ta ce, "Kash!" Bakinsa na rawa ya ce, "Me ya faru Shona?" "Na baro hand bag dina ne My." "Ko na koma na dauko miki?' "A'ah My, karasa mota dai sai na dauko." "To," ya fada ya yi gaba ita kuma ta yi baya. Da sauri ta isa falo ta iske Mom, "Yaya dai na ga kawai kin kama kin tafi." "Uhmm. Mom, ai in ba haka na yi mashi ba, ba tafiya zai yi ba." Hannu ta sa ta bude jakarta ta fiddo wani kullin magani, "karbi wannan..." "Na me ye kuma? Game da wannan aikin da aka yi masa baya wannan ne makarinsa, hade yake da muguwar mallaka, kin ga maganin nan shi kadai ne, idan ya bace AbuDalib zai dawwama a cikin wannan matsalar, haka Boka ya tabbatar mini." Yamutsa fuska Badiyyah ta yi, "Zai dawwama fa Mom? Yanzu idan wani abu ya samu maganin nan shi ke nan AbuDalib zai dawwama a haka?" "Haka ya fada mini, kin san lamarin nasu yadda yake, su ma wani bin gardamammu ne." "Yanzu kuma ban da wannan mallakar da wata wacce ta fi ta?" "Sosai ma, ai wannan sai yadda kika yi da shi ce." "Ai ko yanzu ɗinma." "Ke dai ki amfani da shi, tunda na ce." "To Mom ya zan yi da shi?" "Yawwah. Ki tabbata daren yau kun samu kusanci ke da shi." "Tunda ya samu wannan matsalar ko kadan ba ya fuskantata da nufin wannan sai ya ce baya son ya kware ni." "Ka ji Shashashar yarinya, to ke a matsayinki na mace ba za ki iya ki jawo shi jikinki ba har ki san yadda aka yi kuka samu kusancin? Ke dai an yi sakarya wallahi." Turo baki Badiyya ta yi alamun ranta ya baci, "Kina ji na ki ji abinda zan gaya maki, wannan maganin da kun koma ki zuba mashi shi cikin ruwa ya yi wanka da rabi, rabin ke kuma ki jika ki sha sannan ki samu zummuwa ki gauraya ta da shi ki yi matsi da shi, na farko zai warke na biyu mummunar mallaka ce sai yadda kika yi da shi, duk abinda zai samu a tafiyar nan idan kika ga dama ma, za ki iya mallake kudin gaba daya, ko ya aka yi ba zai ce miki ba balle ya bi bahasi." Sakin fuska Badiyyah ta yi, "Wai da gaske Mom, kai amma na ji dadi, Boo zai samu lafiya wallahi dama ina kewar kayana, sannan kuma na samu waɗannan kuɗin kuma ai shi ke nan." "Uhmmm Badiyya ba ko kunya?" Ficewa ta yi tana dariya, har bakin get din gidan ta bi ta tana kiran ki kula fa Badiyya, ki kula sosai, kin ji abunda aka ce game da maganin. Bankwana ta sake yi da uwar sai bayan sun dawo daga Austria kuma. Da dan sauri take tafiya zuwa mota, hannu ta sa a handbag dinta ta dauko wayarta da ke ta faman tsuwwa. Ganin sunan me kiran ya sa ta buga tsaki ta mayar da wayar a jakar ta cigaba da tafiya. Zaune ta same shi a mota, ya yi zuru yana kallon hanya, kwankwasa kofar ta yi ya bude zama ta yi gefe tana na dade ko? "Eh wallahi ina ta jiranki, amma na san Mom ce ta tsaida ki." "Haka ne," ta faɗa. Bai ce komai ba ya ja mota suka fara tafiya. Ta hanyar unguwarsu suka wuce, zuciyarsa ta hau bugawa da sauri kamar yadda take yi duk idan ya zo wurin, sai dai ko iya tada zancen nan unguwarsu ne be yi ba, a dame ya juya ya kalli Badiyyah wani kallo ta yi masa hakan ya sa ya juya cigaba da tuki. Suna isa gida sun tarar Laure ta gama girki da komai, dakinsa ya nufa don yin wanka, "My Boo na zo na hada maka ruwan wanka ko?" Jinjina kai ya yi, hannu ta sa jikkarta da niyyar dauko maganin da za ta antaya masa a ruwan, sai dai wayam ita ta yi mata sallama gabanta ya fadi, "Yana ina to? Ina maganin yake?" Shi ne abinda take ta faman maimaitawa. Runtse ido ta yi ta bude tabbas maganin ya fadi, kalaman da Mom ta yi mata su suka kara tayar mata da hankali, babu wanda lalurar AbuDalib za ta fi bawa matsala kamarta, ya za ta yi kuma ina za ta sa kanta yaushe ta tara abinda take buri balle ta gudu ma ta bar shi? Ay tafiyarsu ta Vienna somin taɓi ne, yanzu aka fara da ya samu wannan matsayin... Wata zufa ta karyo mata, ba tare da shawarar komai ba ta ɗauki key din motar da ya ajiye ta fice. Kai tsaye inda ta tsaya don amsa waya ta koma, tana karyawa kan kwanar ta yi tozali da wani yaro dauke kullin maganin yana ƙoƙarin kwancewa, a guje ta nufe shi tamkar za ta tashi da shi, ba karamin tsorata ya yi ba cikin zafin nama da kokarin kauce ma motar ya yi baya, cikin rashin sa a maganin da ya riga ya kwance ya watse gaba ɗaya cikin iskar Subhana. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!" Kawai ta iya fada. Gaba ta yi don yin fakin ganin mutane sun yo mata caa ya sa ta ja motar cikin fushi ta bar gurin domin abinda take gudun ya riga ya faru. * Ɗalibai ne daya bayan daya suna biya allunansu gaban Malam Saleh, sai da suka kare tass suka koma wurin karatu sannan Malam ya gyara zaman shi. "Dayyabu, Dayyabu," ya fada murya sama. Da sauri almajirin da aka kira da Ɗayyabu ya zo. "Tun jiya nake so na tambaye ka gama saukar nan?" "Ehh Malam tun da asubar yau na kammala." "To ba ka min magana a yi sadaka." Kudi ya miƙa mashi, "Ka je maza ka ba yaro ya siyo waina ta dubu uku a yi sadaka. Zan shiga cikin gida idan an tashi a yi Tabbat yada ta tunkuɗe sihiri, idan an gama a yi salatil fatihi sha ɗaya, Dayyabu a yi na zihiri cikin satin nan nake so a hada salati miliyan daya." Cikin girmamawa irin ta Dalibi ga MalaminsaDayyabu ya ce, "To Malam," Mikewa Malam Saleh ya yi ya koma cikin gida ya bar Ɗayyabu domin ya gabatar da abinda ya ce. Shi ma Malam na shi addu’a da rokon Allah yake yi daban ban da wanda suke yi na jam'in dalibansa, da kuma na manyan dalibansa gardawa, duka suna yi a kan lamarin AbuDalib da ya zarce tunanin mai tunani. Dayyabu ya ba da aka siyo waina kamar yadda Malam ya umarce shi, sai da lokacin tashi ya yi sannan ya sa yara suka karanta, Tabbat yada kafa bakwai-bakwai kowane ya tofa a allonsa, bayan sun gama kowa ya dira kafar allonsa guda ɗaya a kasa. Kamar yadda ya umarta kuma, sai dai suka yi salatil fatihi kafa goma sha daidaya, almajiran Malam Saleh suna da yawa sun fi karfin dubu daya domin babbar makarantar Allo ce da ta hada da yara da manya maza da mata almajirai da suka yi balaguro daga garuruwansu da kuma 'yan cikin gari masu zuwa gun Malam neman Ilimi. Sai da suka gama a kintace sun yi sama da dubu dari, bayan sun idar aka yi sadaka aka yi addu’a aka sallami kowa. SH 8 AUSTRIA Wajen ƙarfe bakwai agogon Austria jirginsu ya sauka cikin International Airport na Vienna. Vienna babban birinin Aistria gari ne matukar kyau da tsari da birgewa, wanda ya haɗa manyan wuraren shaƙatawa, gine-gine na tsara da manyan hotels da wuraren buɗe ido. Tun da suka sauka hankalin Badiyyah ya kwanta, wani daɗi da farin ciki na kaikawo cikin zuciyarta. Sai dai ta janibin AbuDalib sam zuciyarsa ba daɗi, ba ya jin wani armashi kuma ba ya jin wani abun birgewa a lamarin tafiyar, jinsa yake kawai yana raye amma sauran lamarin rayuwarsa shi kanshi bai san takamaiman ina ya dosa ba, yana jinsa a wani yanayi marar misaltuwa. Kai tsaye masaukin da aka tanadar musu suka tafi, inda aka sauke su wani kasaitaccen hotel wanda za a iya cewa ya fi kowane kyau da tsada a Vienna. Murna gun Badiyya ba a magana domin ji take duk wasu burika da muradanta sun kusa cika, domin ko a haka ma za ta iya mallakar komai na AbuDalib domin susucewar da ya yi, sannan tun a yadda aka tarbe su tun a airpot ya nuna lallai AbuƊalib ba ƙaramin matsayi ya samu a harkar trading ba. Tabbas daga zaran sun koma idan har wadannan kudaden suka shiga account dinta lallai wa'adin aurensu ya kare da AbuDalib. Wanka suka yi baki daya, da kyar ya samu ya yi sallar Magrib da Isha, abinda yake ba shi mamaki sallah ta zamar masa wani kasurgumin aiki a rayuwarsa. Shuru ya yi ya kasa tuna yaushe rabon da ya yi sallah guda biyar cikakkiya, tabbas ba zai iya tuna tun yaushe ba, domin tuni ya manta sai dai idan ya yi asuba da kyar zai yi azahar da la’asar, idan ya samu ya yi su kuma to a ranar duk dubararsa ba zai iya yin Magrib da Isha ba, abun ya dame shi kanshi kamar ya bare sai dai ya rasa ta yadda zai iya furta damuwarshi, ya rasa yadda zai yi ji yake wani abu mai nauyi tamkar dutsin Dala ne ke taushe shi ga wasu abubuwa da ya kasa tuna asalin hakikaninsu, amma zuciyarsa take son sani. Haka suka yi ta lallaba rayuwar a Vienna, kwanansu uku aka gabatar da gagarumin taron traders na duniya, manyan masu gabatar da kasuwancin ne suka haɗu, inda aka karrama AbuDalib da lambar girmamawa ta zinare a matsayin wanda ya fi kowa kasuwancin a fadin Nijeriya. Dala dubu dari biyar suka ba shi, sannan kuma suka kara mashi da wata dala dubu ɗari biyar ɗin a take ya samu dala miliyan ɗaya, kyautukan wasu ababen suke ta yi mashi ban da kuɗaɗe da haɗaɗɗaɗiyar mota da suka siya mashi wanda suka ɗora isarta.Najeriya cikin ɗan lokaci kafin ma ya koma. Farin ciki fal zuciyar Badiyyah domin ana gabatar da taron tana lissafin kuɗaɗen. Shi ko AbuƊalib yanayin da yake ciki shi ne cikakkiyar fassarar yaƙe, fara'a da dariya kawai yake yi, amma ba ya jin haƙiƙanin daɗi da farin ciki wanda ya sani tuni ya yi bankwana da shi tunda ya samu lalurar da ta zame mashi karfen ƙafa wacce ya rasa maganinta. Bayan kwana biyu aka gama taron, inda aka ci kwanaki bakwai na kwanakin shaƙatawar da suka ba su ya rage saura kwanaki 21 cikakken sati uku kenan su koma gida. Zaune yake cikin ƙaton falon hotel ɗin, wanda faɗin yadda ya tsaru tamkar ɓata lokaci ne. Zaune yake daga shi sai singlet da boxer, hannunsa yana karanta wani littafi, wanda yanayin da yake ciki ya sa ya zama mai shuru hakan ya saka mashi son yin kasance-karance don ya rage ƙullin damuwar da ya ɗaure zuciyarsa. Kallonshi take yi, AbuƊalib kyakkyawa ne sosai, duk da damuwar da yake ciki ta sa shi ya yi rama sai dai hutun da yake samu ya sa fatar jikinshi ta yi wani tsadadden kyau, ta ba da wata kala mai wuyar bayyanawa. Wani abu ta ji ya taso mata. A hankali ta ƙaraso inda yake, "My Man...," ta faɗa tana zama kusa da shi. "My Shona." Ya faɗa yana ajiye littafin hannunshi. Hannuwansa duka biyun ta kama tana juya da gangar jikinsa suka fuskanci juna. Cikin wani yanayi da ta tsinci kanta a ciki ta ce, "My Boo, ina kewarka, i miss you alot...," ta ƙare zancen tana shafa fatar kafaɗarsa da ke a bayyane. Ɗan baya ya yi, saboda yadda take shafa fatar jikinsa ta soma harmutsa tunaninsa. "My Shona... Stop it pl..." Kafin ya ƙarasa ta yi gaggawar haɗe bakinta da nashi. Gaba ɗaya reaction ɗin jikinsu ya canza, sun shiga wani irin yanayi marar misaltuwa wanda kewar juna da nisan da suka yi a mu'amalar ya sabbaba musu shi. Zaman ya gagare su suka faɗa kan kujerar gaba ɗaya suna romancing junansu cikin fitar hayyaci. Sosai Badiyyah ta rikice take buƙata da neman agajin kusanci na gaske, sai dai kamar yadda take faruwa a lokutan baya haka ta faru a wannan karan, ko kaɗan babu alamun AbuƊalib ɗin zai iya yi mata wani abu, jikinta na karkarwa ta miƙe daga kan jikinsa, shuru ya yi tare da faɗawa cikin dogon tunani, jikinsa ya yi liƙis tamkar an mishi duka, wani huci yake fitarwa ta hanci da bakinsa, tabbas yana cikin matsala, kuma abinda yake gudu kenan kar su taƙulo abinda zai dame su gaba ɗaya. Da ƙyar ya juyar da kanshi wurin Badiyyah, "Am sorry please..." Wani dogon tsaki ta ja ta gyara zaman rigar jikinta ta miƙe ta bar wurin da sassarfa. "Shona, My Shona," yake maimaita kiran sunanta, wanda hakan ya sa ta ƙara ƙaimin gudunta. Ɗaki ta faɗa ta banka ƙofar da ƙarfi, kalaman Mom ɗinta suna yawo cikin ƙwaƙwalwar kanta, "Yanzu haka AbuƊalib zai dawwama?" Ta faɗa a bayyana. "Ta ya ya zan cigaba da zama da mutum tamkar 'yaruwata mace? Ina ba zan iya ba, ba zan iya ba dole ne na nema ma kaina mafita." Shuru ta yi tana mai da numfashi tana sakin nannauyar ajiyar zuciya, tana ƙudira matakin da za ta ɗauka da zaran sun koma Nijeriya. ★★★★★ BAYAN SATI UKU Sosai nake samun kulawa daga wajen Yunus da mahaifiyarsa Mama, kamar yadda na ji yana kiranta, cikin satika ukun zuwanmu asibiti biyu, muna zuwa a kowane sati, sosai nake jin dadi zuciyata cike da amincewa Allah ne ya kawo min daukinsa da taimakonsa kamar yadda yake yi wa bayinsa ta inda suke zato da ta inda ba su zato ba su tsammani. Kamar yadda muke duk sati yau ta kama za mu koma asibiti karo na uku, shirye na fito na samu Yunus kofar gida, hannu nasa na bude kofar mota na shiga, juyawa na yi don rufe ƙofar, ganin Saratu na yi tsaye bakin kofar gidansutana kallon motar, tamkar ta karaso wurina bakinta da abin fada. Yunus ya ja motar ya tafi, har muka fice daga layin tana tsaye tana kallon motarmu. Kada kai na yi domin a cikin kwanakin gaba daya ta ida rikicewa, kullum kuma cikin son rigima da ni da yin sabon tsiri a cikin zamana na gidan wanda ya sa har na fara jin gundura a zaman. Sai dai Baban Ayuba da shi kansa Ayuban suna kyautata mini, da tausaya mini a game da hali da yanayin da nake ciki. "Amatullah," sabon sunana da Yunus ya kira ya katse mini tunanina. Juyawa na yi na zuba mishi idanuwa, kamar yadda na saba yi ga duk wanda ya kira ni ko ya yi mini magana. Muryarsa a tausashe ya ce, "Ya karfin jikin naki?" "Da sauki, Alhamdulillahi." Na fada mashi. "Masha Allah, ya Baby yana lafiya ko?" Jinjina kai na yi alamun, Eh. Murmushi ya sakar mini yana sannu Ama. Nisawa ya yi a hankali cikin nutsuwarsa ya ce, "Amatullah ina son yin wata magana da ke, sai dai ina Shakkun shin za ki amince ko zan samu akasin haka, duk da dai na san yanzu kin fahimce ni kin gane ko ni waye, ga shi har ma kina mu’amala da mahaifiyata, kin ga asibitinmu, kuma na san duk da ba ki mu’amala da mutane da yawa ba za ki rasa jin feedback a game da mu ba." Jinjina kai na yi alamun eh, sannan na dora da, "Kuma ban ji wata magana marar kyau a game da ku ba, ni ma kaina zan iya shaida wannan." "Haka ne. Ama, a halin yanzu kina cikin hadari, ina nufin a yanzu kina bukatar kulawa fiye da ta kowane lokaci, saboda a yanzu haihuwa za ta iya zo miki a kowane lokaci. Don haka na yi ma Mama magana a kan ina son ki koma gidanmu ko na ƙanƙanin lokaci ne. Duk da ba ki sanar da ni ko ke wacece ba, i agreed 100% ke bahaushiya ce." Ɗan murmushi ya yi, "Ni ma da kike gani na, da Mama da Babana dukansu Hausawa ne, Babana yana zaune a Lekki amma ni da Mamana muna zaune a G.R.A Ikeja, daga ni sai Mamana da ma’aikatanmu muke zaune a gidan, Amatullah a can ko kaɗan ba za ki samu takura ba, kuma ina mai tabbatar maki za ki samu cikakkiyar kulawa. Idan kin amince sai a gyara inda za ki zauna gobe weekend sai na zo na dauke ki ki koma a can, amma fa sai kin amince." Magana yake yana kallon hanya, ni kuma na yi kasake ina saurarenshi, zuciyata na matsanancin gudu tsakanin amincewa da rashinta. Saratu koyaushe cikin laluben hanyar da za ta wulakanta ni take haka zalika tana aibata ni da aibata abinda ke cikina, za a

Chapter 5 of 14