nan na ji zuciyata ta aminta da shi, ban yi gardama ba na juya alamun ya biyo bayana. Bai damu ba domin ya san ba lallai na aminta da shiga motarshi ba. A nutse na ci gaba da tafiya da takuna irin na masu juna biyun da suka kusa haihuwa, har muka isa daidai kofar gidan. Fitowa ya yi daga mota ya zagayo inda nake, kada kai ya yi yana jinjina yadda ya ga tsari da yanayin gidan. Ji na yi yana kiran yara da ke wasa can gefe, kayan abinci ya sa suka dinga fitowa da su, tun daga kan karamin buhun shinkafa, galon din mai taliya catton da makaroni da garin kwaki da sauran kayayyaki masu yawa. Sosai na cika da mamaki da al’ajabin abinda ya yi.
"Amatullah don't worry for this, ni zuciyata na ayyana mani akwai wani boyayyen labari a tare da ke, kuma tana ayyana mini ke mutuniyar kirki ce sai dai wata kaddara marar daɗi has separated you from your bleseed family, so ni na yi niyyah ina so don Allah ki zauna ki kula da kanki ba tare da kin kuma zuwa bara ba, ki kula da kanki kin ji." Jinjina kaina na yi hawaye na kuma wanke fuskata. Kudi ya miko ya ba ni, ban san ko nawa ba ne. "Ki karba mana komai na yi na yi don Allah ne." Nagode na fada mashi cikin yarena.
Juyawa ya yi ya shiga motarshi, har ya bace ma idanuwana ina ganinshi. Juyawa na yi na shiga cikin gidan, dukkan kayan da Yunus ya kawo mini sun shigar da su cikin dakina. Komawa na yi cikin dakin na yi godiya ga Allah tabbas dukkanin tsanani yana tare da sauki, kamar yadda Allah S. Ya ce, "Fa'inna ba'a dal usrin yusra." Duk yadda abubuwa suka yi tsananin sauƙi na biyo bayanshi ko su kasance tare.
Dirshan na zauna ina ƙara duba kayayyakin, kaya ne da yawa har da su madara da bournvita da lipton da sauran kayan tea. Sosai na ji dadi har cikin raina. Alkhairi ya same ni dole na faɗawa abokin hirata kuma abun ƙaunata.
Cikin jin daɗi na ce, "Abun kauna, ka ga taimakon Allah ya zo mana ko? Ka gani mun samu har da kayan shayi, abun kauna za mu sha dadi, kuma ba za mu mu ƙara fita bara ba, za mu huta abun ƙauna. Za ni huta har zuwa lokacin da za ka iso gare ni, lokacin da zan sa ka cikin idaniyata." Murmushi na yi na shafa ina godiya ga Allah na saukin da ya zo mana lokaci daya. *
★
Cikin shauki ya shiga office din Mamanshi, "Mama, kin san yarinyar nan ta karbi kayan kuma na ga ta ji dadi sosai."
"Ɗan Mama, dole dai ka saka yarinyar nan a ranka." Maman ta faɗa tana kallon shi.
"Mom, i have certainly yarinyar tana bukatar taimako and i believed ba irin yaran nan ne na Alaba ko Agege ba, duk da, da ka ganta ka san bahaushiya ce amma dai ko Mom..." Ya ƙare maganar yana jinjina kai kamar ɗan ƙaramin yaro.
"Uhmm to ya yi Allah ya yi maka albarka."
"Amin Mamana. Yanzu Mama, so nake na kawo ta hospital a ga lafiyarta da ta babyn." Langabar da kai Mom din ta yi. "Yunus ka sani ko matar nan na da miji, kar ka wuce iyaka fa." Shuru ya yi yana nazarin maganar Maman. "Kaɗa kai ya yi, ni dai Mom ban ga alamun haka ba. Cause when i asked her about her Baby, i just saw tears pouring from her eyes, so Mom i didn't expect tana da aure. Kawai zan kawo ta nan, na san za ta amince don a duba lafiyarta, kin ga da zaran ta zo sai ki duba ta sosai Mom. Don Allah idan lokacin haihuwarta ya kusa mommy zan dawo da ita gun ki ta haihu, ko ba haka ba?" Kallon shi take yi, "Uhmm Yunus kenan, ga ka babba haka himmm a gabana, amma kuma lissafinka har yanzu na yara ne."
Kwabe fuska ya yi, "Mama, yanzu wannan lissafin yara ne? I swear kika ji yadda nake ji da tsammanin da nake da shi a kanta Mom za ki tausaya mata kuma ki irin abinda nake tunanin yi."
"Shi ke nan to na ji. Idan ta amince kuma na yarda da nutsuwarta ba abinda ba zan iya yi mata ba just for you."
"Yawwa Mamana Thank you, loads of love." Ya ƙare maganar tare da ruƙo hannunta ya sumbata.
★
Yau kam da na samu cigaba ban dafa komai ba, shayi na hada da ya sha madara da bournvita mai yawa. Hannuna dafe da abun kaunata kuma abokin hira da labarina, ina sha muna hirarmu jefi-jefi na ji sallama cikin gidanmu, tamkar na so in dauki muryar mai sallamar sai dai sam ban damu ba, domin a iya sanina bayan Maman Nana da nake kai mata abinda na samu sai ko Yunus da ya taimaka mini ba ni da wani abokin hulda a Lagos da kaddarata ta kawo ni rayuwa cikinta a lokacin da ban taɓa zato ko tsammani ba.
Ji na yi an tunkaro dakina gadan-gadan. Kofar na zuba ma idanuwa domin ganin mai niyyar shigowa dakin, sosai na gane fuskarta. Matar da muka hadu ce wata rana na dawo daga ipaja har ta yi mini kyautar kuɗi naira dubu uku. To me ta zo yi wurina? Zuciyata ta jefe ni da tambaya. Fuskarta a washe tamkar gonar auduga ta ce, "Sannu, sannu baiwar Allah." Daga mata kai na yi alamun yawwa. "Na iya shigowa?" Ta tambaye ni.
Sake daga mata kan na yi. Ƙarasowa ta yi cikin ɗakin ta nemi wurin zama tana, "Allah sarki sannu kin ji, wallahi kwana biyu na ga ban ganki ba, shi ne na ce bara na zo na san yanayin jikin naku sai a hankali ne, yau kwari gobe baka." Dan murmushi na yi, na zuba mata ido yadda na ga ta kasa dauke idonta daga kan cikin jikina. Hasbunallahu wa ni’imal wakeel na ayyana a raina, sam na kasa yarda da matar da takunta tun farkon haɗuwarmu.
"Ya jikin naki da sauki ko?" Daga mata kai na yi alamun eh. "Ohh ka ga daki cike da kayan masarufi, wani bawan Allahn aka samu ya taimaka maki da su ko?" Nan ma daga mata kai na yi.
"Allah sarki, ay duk wani mai imani ya ga yanayin da kike ciki dole ya tausaya miki, Allah ya san zuciyata ni kaina ji nake da a ce ina da kudi ni wata mai tarin dukiya ce sai na miki abinda ya fi haka."
Nagode na yi mata nuni. "Sannu, sannu fa."
"Yawwah," na amsa mata da hannu.
"Na ce, amma dai kina zuwa awo ko?"
"A'ah," na bata amsa.
"Ayyah, ay ya kamata a ce ki je awo diyata, saboda kin san ba a son mai juna biyu ba ta zuwa awo. Kodayake na san ba ki san ko’ina ba cikin garin nan."
"Haka ne."
"Allah sarki. Ni ai na kai shekara 30 garin nan ba inda ban sani ba, duk Jama'ar da ke zagayen gurin nan da kin ce Innarsu Kulu, za su gwada miki ni. Kawai abin da za a yi, bari nan da kwana biyu ko uku na shirya na zo na raka ki asibiti, a yi maki awo a san halin da ɗan cikinki ke ciki."
"A’ah, Allah ke tare da ni, ba sai na yi awo ba." Na faɗa.
"A’a ke kuwa 'yar nan, kamar ba ki yarda da ni ba. Ay duk ɗa na kowa ne, ni jinki nake kamar ɗiyata wacce na haifa. Ki bari dai a duba ki kar ki gardama 'yar nan kin ji, ki je ki awo a san lafiyarki a san ta ɗan cikinki."
"Shi ke nan to, Allah ya kai mu."
"Yawwa ko ke fa, bara na tafi sai jibin na zo na kai ki kin ji."
"Allah ya kai mu lafiya." Tashi ta yi ta fice har ta fita ina bin bayanta da kallo.
Kashe gari tunda safe kafin ta wuce inda take sana’arta ta siyar da abinci kamar yadda ta fada mini sai da ta biyo gidanmu muka kara gaisawa, bayan fitarta ina zaune na gama karyawa na ji karar tsayuwar mota, raina ya raya mini Yunus ne, haka nan na ji dadin zuwanshi. Kamar yadda na yi tsammani, Ayuba ya leko ya shaida mini wani Yunus yana nemana a waje. Mikewa na yi na saka yar yagwalgwal din abayata na fita.
Gaishe shi na yi, ya amsa da lafiya lau tare da jera mini sannun shi da ya saba.
"Amatullah, idan kin amince so nake yi na kai ki asibiti domin a duba lafiyarki da ta Babynki."
Kallon shi na yi, domin wani sanyin daɗi da na ji ya dira cikin raina. "Kin amince?" Jinjina kai na yi alamun eh.
"To ki shirya anjima zan zo sai na wuce da ke asibitin."
"Allah ya kaimu." Buɗe motar ya yi ya fiddo manyan ledoji ya aje gabana. Nagode da ɗawainiya, Allah ya saka da alkhairi. Bai bi ta kan godiyata ba, ya yi min bankwana ya tafi.
Cikin gidan na koma, ina shiga ɗaki na buɗe ledar, ga mamakina sai na wasu haɗaɗɗun abayas da wasu dogayen riguna na leshi da atamfa da riguna masu sauƙin nauyi, irin dai wanda za su yi wa mace mai juna biyu daɗin sakawa, sai takalma irin marasa tudu ɗinnan masu shegen kyau, sai turare da sabulun wanka, har da Shower gel ko ba a faɗa ba kasan kayan na kuɗi ne sosai.
Jigum na yi na zuba tagumi da duka hannayena biyu. "Shin me wannan bawan Allahn ke nufi? Duk da ya yi kama da mutunen kirki amma fa an ce, hali ba shi ga kama. Wannan hidima tare da ɗawainiya haka sun yi yawa." Zuciyata ta faɗa.
"Kar ki fassara shi da mutumin banza ki yi amfani da zahirinsa da kika gani, wataƙil Allah ya kawo shi ne don ya taimake ki."
Hawaye suka ziraro kan kumatuna, haka ƙaddara ta rubata mini, ya Allah ka sanya kamar yadda nake tsammani Yunus maceci ne ba macuci ba. Amin zuciyata ta amsa.
Cigaba da linke kayan na yi ina ƙara kallonsu. Sallamar da Saratu ta yi ya mai do ni hayyacina da tunane-tunanen da nake ta faman yi a raina. Fuskarta turɓune kamar magribar ɗinya ta ce mini, "Ke, kamar kin mance da warning ɗin da na yi maki ko a kan zamanki gidan nan. Kuɗin haya za ki kawo yanzun nan..."
Miƙewa na yi da ƙyar na nufi wurin da na saƙe jikkata. "Dubu hamsin za ki ba da, na wata ɗaya." Ta faɗa lokacin da ta ga na fiddo jikkar. Juyawa na yi na kalle ta, kaɗa kai na yi sannan na ƙirga adadin kuɗin da ta faɗa mini na ba ta.
Karɓa ta yi ta lissafa, "Yawwah sun cika. Na ga kina mana 'yan kaye-kaye, idan iskancin za ki yi ai kya bari ki haihu amma don jaraba ba za ki hakura ba. Ga shege sai an ƙara loda wani kuma..."
Wani irin zafi maganganunta suke yi mini, ban furta mata komai ba don bana magana, amma tabbas watan wata rana sai na tabbatar mata da ɗana ba shege ba ne yana da Uba.
Tafiya ta yi tana cigaba da yin maganganun. Zama na yi na ƙarasa linke kayana sannan na fita na yi wanka, na saka ɗaya daga cikin rigunan da Yunus ya kawo mini. Kasa shafa kowane turaren da ya haɗo mini da shi na yi, da ƙyar hancina ya aminta da ƙamshin sure ɗin Nivea da Body spray na wani turare Deal. Sallah na yi, bayan na idar na ƙara shan shayi kamar yadda na sha da safe.
★
Wurin ƙarfe shida na yamma Yunus ya zo, a shirye na fita tsaf. Wani irin kallo yake yi mini, lallai sutura ita ce mutum baki ɗaya na canza tamkar ba ni ba. "Masha Allah Ama, sannu."
"Yawwah," yana yawan ce min sannu idan ya zo har ban san adadin da yake faɗa mini ba.
Buɗe ƙofar motar ya yi ya shiga sannan na zagaya ni ma na shiga bayan na zuba addu'ar neman tsari a raina. Tafiya yake yi a hankali har muka fita babban titi, ni ko na zama tamkar baƙauya duk inda muka wuce ina binsa da kallo ina ganin manyan gine-gine da ban saba ganin irinsu ba a alƙaryar da na yi rayuwata ta baya. Kwana muka yi cikin wata natsattsar unguwa, sai na ga kamar na baro ƙauye na shigo birni saboda kyawun wurin. Bakin wani ƙayataccen gini muka tsaya mai ɗauke da wani rubutu da ke haske cikin duhun magriba da ya fara yi wa gari mamaya na ga an rubuta, YUNUS SPECIAL HOSPITAL. Sake karanta rubutun na yi da kyau, "YUNUS," Juyawa na yi na kalle shi yana ta ƙoƙarin kashe mota hankali kwance. Yunus Special Hospital, to wannan Yunus ɗin da nake tare da shi ko wani ne daban na tambayi kaina? Ba ni da amsar tambayata, sai aikin kallon asibitin nake.
Sai da muka tsaya tsaff sannan muka fita, gaba ya yi ina bin bayan shi, har muka isa cikin ainufin asibitin. Masha Allah, tabbas asibitin ta ginu kuma ta haɗu, ta yi kyawu ba na iya wajen asibitin ba a cikinta ma haɗaɗɗe ne. Daidai inda za mu hau bene ya tsaya, "Amatullah za ki iya hawa steps ɗinnan kuwa?" Ya tambaye ni.
Jinjina kai na yi alamun Eh. "Okay to bi a hankali Ama," ya faɗa da tsantsar tausayinshi a kaina.
Hawan benen na cigaba da yi da ƙyar saboda jikina duk ya cunkushe saboda ɗan kumburin da ya yi. A wahalce na ida hayewa, cikin tausayina Yunus ke ta faman yi mini sannu, tamkar ya sa hannu ya haye da ni. Ina hayewa ya ce, "Jira nan ki ɗan huta, zauna a nan kin ji Ama." Ya nuna mini kujerun da aka tanada gun don hutawa. Zama na yi, gurin gwanin daɗi domin sanyin A.C ya gauraye shi.
"Let me come back." Ya faɗa yana tafiya da sauri. Gaba kaɗan da inda nake zaune ya tura wata ƙofa ya shiga. Ina zaune a wurin ina sauke numfashi a hankali, suka fito shi da wata dattijuwar mata. Kallo ɗaya na yi mata na fahimci mahaifiyar Yunus ce, domin kamanninsa sak irin nata ne, sai dai hasken fata da ta fi shi da zubin kyawu irin na mace.
Fuskarta cike da fara'a ta ƙaraso inda nake, "Sannu, sannu kin ji." Dattijuwar mata ta ce mini.
Yunus ya ce, "Mama she can't talk fa, but she is hearing all what you said."
"Ohh, sorry ka faɗa min fa, amma ka ga na manta shaf."
Gaishe ta na yi da bebenci, yanayinta ya nuna mini mace ce mai sauƙin kai, da halin kirki kamar Yunus. Da hannunta ta mikar da ni tsaye, taku muka cigaba da yi zuwa ɗakin da ta ce za a duba ni.
Ɗakin jinya ne mai matuƙar kyau, toilet ɗin da ke cikin ɗakin ta nuna min tare da ba ni wata 'yar ƙaramar roba ta ce na yo fitsari a ciki. Kamar yadda ta ba ni umarni haka na yo, bayan na dawo ta kira wata nurse a waya ta zo ta karɓa, a tare suka fita ita da nurse ɗin, na yi zaune cikin ɗakin ina kallon TV da ke aiki ita kaɗai. Ina zaune cikin ɗakin ina ta saƙe-saƙe da zancen zuci iri-iri ta dawo. "Yawwah Ama, yanzu za ki tashi mu je wani ɗakin, a yi miki scanning."
Murmushi na sakar mata, ina jin abun kamar almara, wai a yi mini scanning don ganin lafiyar Abun Ƙauna. Wani ɗakin muka je, muna shiga ta mai da ta rufe. Gado ne a ɗakin mai kyau tare da 'yan na'u'rori da wata talabijin da nake tunani ita ce ta scan ɗin. "Yawwah Amatullah sai a kwanta kan gadon nan don mu yi abun da ya kawo mu." Kwanciya na yi kan gadon, hannu ta sa ta kware rigar cikina sannan ta shafa mini wani abu a kan cikin. Bayan ta gama ta ɗora wani abu mai haske kaman na'ura tana yawo da shi kan cikina.
"Masha Allah, Ama kin ga Babynki yana cikin ƙoshin lafiya, kin ga yadda yake ta yawo abin sa ko?" Juya kaina na yi na ɗora idanuwana kan 'yar TVn da ke gefena. Kamar yadda Umman Yunus ta faɗa, haka na ga Abun Ƙaunata na ta yawo a makwancinshi, wani irin daɗin da ban taɓa kintacen kwatankwacinsa ba ya ratsa ni, hawaye suka fara biyo kumatuna, hawayen farin ciki da suke malala haɗe da bayyananun fararen haƙorana da na kasa rufewa.
Umman Yunus ke ƙara taya ni fara'a da murnushi, ganin yanayin farin ciki da na shiga. Bayan an gama scanning ɗin na tashi na nemi wuri na zauna. Wata nurse ta shigo ta kawo ma Umman Yunus wasu takardu ta tafi. "Amatullah, a awon da aka yi miki ya nuna cikinki na cikin wata na takwas wato yana da wata bakwai da kwanaki yanzu za ki iya haihuwa nan da sati huɗu masu zuwa, kin gani," ta ƙare zancen tana nuna mani EDD na haihuwata a jikin takarda.
Numfashi na sauke, na farin ciki da baƙin ciki. Tsuru na yi ina kallon takardar, zan iya haihuwa nan da sati huɗu?
"Kar ki damu, Inshallah za ki haihu lafiya." Umman Yunus ta faɗa ganin kogin tunanin da na afka. Wasu magunguna kuma wata nurse ta kawo, tana ba ta ta miƙo mini su, "Amatullah, jikinki ya nuna akwai ƙarancin jini a tare da ke, saboda haka ki dage da cin kifi, nama, da ganyayyaki musamman alayyahu." Jinjina kai na yi. Wasu shawarwari ta ƙara ba ni, sannan daga ƙarshe ta ce, nan da sati ɗaya Yunus zai dawo da ni a ƙara duba ni.
Waje muka fita, kiciɓus muka yi da Yunus, kallon Maman ya yi, "Mom, you keep me waiting, kin shiga kuma kin daɗe, ina fata komai dai lafiya ko."
"Lafiya lau ɗan Mama. Ba wata matsala a tare da Amatullah, sai ɗan ƙarancin jini shi ma ba sosai ba."
"Yawwah, to Alhmdlillah."
"Tare za mu wuce ko Ɗan Mama? Da ma ka tsaida ni dai na biya na duba Amatullah."
Murmushi ya saki yana faɗin, "Haka ne Mamana. Thank you."
Tare muka fita suna ta hira gwanin ban sha'awa irin ta Uwa da Ɗa. Tunanin Ummana ya faɗo mini, da yadda muka yi rayuwarmu mai cike da shaƙuwa da ƙaunar juna, da kuma ƙarshen tarihin rayuwarmu da muke ciki yanzu. Ko Yaya Ummana take? Numfashi na sauke, domin tun idaniyata na zubar da hawaye a kan irin wannan tunanin, har ta bushe ta ƙeƙashe. Kuma ba zan taɓa komawa cikin zuri'ar da muka yi hannun riga da su ba a yanzu, har sai na samu tudun dafawa, ranar da zan koma riƙe da hannun Abun Ƙaunata, ranar da zan shelantawa duniya halascin ɗana tare da hujjojina bayyanannu.
Umman Yunus ta ce, "Bi a hankali ki shiga mota." Motar na shiga wacce na zauna baya, Umman Yunus kuma suka shiga gaba suna cigaba da hirarsu.
Har ƙofar gidanmu suka kai ni, lokacin da muka isa ƙarfe takwas na dare ta ɗan gota. Bankwana suka yi mini sosai, tamkar ni ɗin 'yaruwarsu ce, ga alamu dai Umman Yunus tana ƙaunar ɗan nata sosai.
Shigewa na yi cikin gida, ƙofar ɗaki na samu Saratu wani kallo take mini, ban kulata ba na yi shigewa ta ɗaki.
Kashe gari tun da safe zuwan Innarsu Kulu ya tayar da ni daga barci. Yadda ta saba rakaɗi da surutu haka ta shigo, "Wallahi kina raina, na ce bara na biyo na ga ya kika tashi."
Tsuru na yi mata, kai matar ta faye alamun mutane marasa gaskiya. "Ya ƙarfin jiki ya kika tashi?"
"Lafiya, ina kwana an tashi lafiya?"
"Lafiya lau."
"Cewa na yi, kawai ki shirya mu je awon."
Miƙewa na yi na ɗauko takardun awon da aka yi mini asibitin su Yunus, karantawa take tana yi har da tishi, gana ɗaya sai na ga launin fuskarta ya canza.
Sakin fuska ta yi, "Tooo, ai ko na gani. Kenan bawan Allahn nan da yake taimaka maki ya kai ki Yunus Hospital? Lallai kam. Ai asibiti ce mai kyau da tsada a garin nan, sun san aikinsu sosai. Shi ke nan, ai kin ga sun hutar da ni, illah iyaka na riƙa leƙowa ina duba ki, tun da na ga haihuwar ta kusa, na shigo na karɓi Ɗan Baba ko 'Yar Baba. Allah dai ya raba lafiya."
"Amin." Kawai na yi mata nuni a taƙaice. Surutu take ta yi kala-kala, daga ƙarshe ta tashi ta tafi. Taɓe baki na yi, koma dai me ye aniyarki ta biki na ayyana a raina na koma barcina. Domin tsarina sai sha ɗaya zan tashi, bayan na shirya na je gun Maman Nana na kai mata kuɗi sannan in shaida mata ta aiko su Nana su ɗaukar mata abincin da na ɗibar musu.
SH 7
ABUƊALIB
Kwana uku cif suka rage tafiyarsu zuwa Vienna, ba ƙaramin dadi Badiyyah take ji ba da AbuƊalib ya warware tass hakan ya sa za su samu damar tafiyar, sai dai abu ɗaya ya dame ta, wanda kuma ta mayar da shi ba abun damuwar ba, gaba ɗaya ya ƙarasa sauyawa, yana wani bin ta kamar bawa da Ubangida. Watsar da tunanin abin ta yi gaba ɗaya, ta cigaba da shirya komai na tafiyarsu, wacce take buri da ƙulafucin a yi kawai don kuɗaɗen da za ta mallaka.
Yana zaune babban falon gidan ta fito cikin gayunta ya zuba ma matakalar benen da ke kallonsa ido. Mai da idanuwanta ta yi inda yake kallo, take ta kyabe fuska da baki, wannan jarabar duniya, wai ko AbuƊalib zai manta da Lilbirrah har abada? Zai manta ta yadda nake so kuwa? Kallon me yake ma sashenta? Dan karamin tsaki ta ja ta ida ƙarasawa inda yake, sake fuskarta ta yi kamar ba ita ce ta gama haɗeta ba.
Zama ta yi kusa da shi turarenta ya bugi hancinshi, idanuwanta ta saka cikin nashi, "My Boo, me kake kallo ne na ga ka zuba ma kafar bene idanuwa?"
"Ba komai My shona. Me kika gani ne?"
"My ka san dai bana son abinda zai dame ka ko? Idan na ga kana damuwa kai kaɗai sai hankalina ya tashi na ga kamar har yanzu ciwon ka bai warke ba." Ta kare maganar hawaye na ciko idanuwanta.
Hankalinshi tashe ya ce, "Am so sorry Shona, don Allah kar ki yi kuka ki bata kwalliyanki. Am sorry please ba abinda yake damuna na warke sosai."
Shararo hawayen ta yi a shagwaɓe ta ce, "Ni dai ka fada mini gaskiya, ka fada mini gaskiya My Boo please." Rungumeta ya yi tsam jikinsa, "Na fada maki Shona ba komai ba abinda ya dame ni kuma, amma kin san akwai abubuwan da dole su saka ni tunani ko? Kin sani My Shona, wani lokacin ji nake kamar ina kwarar ki..." Dariya ta so kamata sai dai ta kara lafewa jikinsa, "Ni ba ka kwarata, ba ka min komai, and I luv you AbuDalib game da matsalarmu a zamanmu kar ka damu, kuma na sha faɗa maka ka daina damuwa zan zauna da kai ko da za ka dawwama a haka." Ajiyar zuciya ya sauke, "Shi kenan to, na daina Shona, yanzu ki tashi ki tafi gun Mommy ki mata bankwana, kar ta ce na hana ki zuwa please, hankalinta zai tashi."
"Ni dai in har ba ka jin dadi ba inda za ni."
"A’ah My shona ki tafi please."
Dagowa ta yi fuskarta duk ta hade da hawaye. "Ka tabbata ba abinda ke damunka My Boo."
"Ba komai wallahi, kin ji na rantse."
Share hawayen ta yi, "Shi ke nan na yarda My."
Mikewa ya yi da hanzari ya dauko tissue da ke kan table na tsakiyar falon ya goge mata fuskarta."Na san ba a rasa kayanku na mata ko, bara na shafa maki powder." Ya faɗa yana buɗe jikkarta.
Murmushi ta yi, "Bar shi My, na tabbata a haka na fi kyau saboda hannunkan nan mai albarka ya gyara mini fuskata."
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 14