Share this page
kai. Kofar ta bud'e gaba d'aya ta yadda Farida ke iya ganin su. A yau kad'ai wani irin kyau yaga Sultanan na sake yi har bai san ya ciro waya tare da daukarta ya juya yadda suka bawa Farida baya ya kyalla musu selfie suna dariya ba shi da Sultanan. Ajiyeta ya sake tare da daukarta ita kad'ai,tuni gwalli ya motsa sai karkacewa take karawa yana mata yana dariya. Farida ya kallo wacce ke kallonsu itama baki washe,ai sai yanzu ya tuna d'akinta suke,dan haka a hankali ya ce "Oh! Farida sorry. Kai ta kad'a, duk kowa na gidan gwanin sha'awa yake a idonta ita barin Sultana. "Zamu fita,ba wani abu koh? Kai ta girgiza,kamin ta ce "Sai abu d'aya. Tsayuwa ya gyara tare da gyara farin glass dinshi. "Ok,mey fa? List din ta dakko bisa mirror tare da dan dukowa ta mika mishi da hannunta biyu. Glass ya gyara yana mai sake kallon cefenan nata,a dan sace ya kallota,hankalinta kwance take murmushi. Kamar ya ce mey zatai dasu sai dai ya basar. "Dama Uncle ni bana son abincin wajen nan ne kullum,tunda na iya sai mu siyo gobe na fara. Dariya ke kok'arin subuce mishi,har ga Allah mugun yarintar Farida yake gani,dan haka sai yake ganin kamar fad'a take amma ai tayi k'ank'anta da iya girka duk abinda ta lissafo mishi. Kok'ari ya yi ya danne tare da fad'in "Shikenan? Kai ta girgiza mishi halamun ba shikenan ba,sai dai kamin yakai ga magana ta langwa6e kai cikin shagwa6a tare da fad'in "Nima so nake naje ne fa Uncle. Tsayuwa ya gyara tare gyara glass din shi,tamkar wata Sultana in taso mishi shagwa6a haka ta dawo,dan haka da sauri ya basar tare da fad'in ''Ok... Dan tsalle tayi kad'an tare da d'aukar gyalen da ta fito dashi cikin murna. Ganin yana kallonta yasa sai ta dan nutsu tare da sauke kai tana murmushin kunya. Murmushin shima ya yi tare da fita rike da hannun Sultana dan haka da sauri ta lankaya gyalen a kafad'a ta fito dan bin bayan su. A mota suka tarar dasu Saifu duk sun shassha mur ganin Farida da gyale. Kasa hakura Saifu ya yi,dan haka da sauri ya tambayi Abban da ita zasu tafi ne? Faridan ya kallo yadda itama ta zuba mishi ido,da mamakin Saifu sai yaga Abban ya daga kai halamun eh. Kofa ya rufo da karfi yana harararta lokacin da suke kok'arin shiga gaba ita da Sultana tana murmushi. Horn ya yi aka bud'e musu gate yana kok'arin d'aura belt. Faridan ya kalla da ainashin gyale a gefen kafad'a daya kamar yadda yaga y'an mata nayi sai yai murmushi tare da dauke kai ya fita daga gidan. Da kaya niki-niki suka dawo kusan duk list din Farida harda su lunch boxes na yara da na manya da jakunkunan su harda su kitchen apron. Wani abin ma bai san amfanin da zai musu ba amma Farida ta jido su,shi dai adu'ar shi d'aya Allah kad'e mishi asara. Da kanta ta shiga kitchen tana jere kayan,na fridge ta sa,na store ma haka. Bayan sunyi sallar isha'i ita da Sultana ta cire kayanta tare da sanya sassauka suka nufi kitchen. Kaza ta gyara jin shiru basu dawo ba ta silala ta juye a roba mai murfi tare da sanyata cikin freezer.. *** Washe gari week end,wanda a ka'idar gidan suna yin bacci ne har sai randa yunwar cikin su ta taso su. Gari na waye wa ta fito tare da shiga kitchen aka d'aura apron. Fridge ta bud'e tare da ciro daskararriyar silalliyar kazarta ta jiya har tai kankara. Store ta shiga tare da dakko tukunya ta ta fara aiki. Farfesun kazar ta fara had'awa bayan ta gama yanke albasarta bisa copping board da tafarnuwa ta watsa. A greater ta jajjaga komai gudun kar ta tashi kowa a bacci ta nan zuba,duk wasu items da take da bukata na karin dand'ano tasa tukunna ta d'aura bisa gas. Kan kace meye tuni kamshin 'Chief Faridee' ya fara bud'ad'e gidan bayan an zuba kayan kamshi. Gefe tayi da wannan, tukunna aka d'aura tea tare da binciko kayan citta dasu kanumfari da sauran kayan kamshin tea da Umma ta sanarta tasa ta watsa ta rufe dan ya dahu. Parlour ta koma tare da dakko bread wanda suka siyo jiya mai yanka-yanka ta koma kitchen tare da fara mayarshi hadadden 'Sandwich' ta jere su bisa wani dish dogo mai kyau yadda kana hango su ta ciki gwanin kyau. D'ayan wani warmer ta dakko shima mai ruwan garai ta juye farfesun kajinta aciki a hankali taje ta jere su da tea flaks,cups,plates da sauran abin bukatar kowa tukunna ta hau gyaran gida. Tsaf ta gama komai,tukunna ta koma d'aki tare watsa ruwa dan gajiya. Sultana ce ta fara tashi,dan haka sai ta mata wanka tare da mata shiri cikin kaya masu sauki suka zauna a parlour suna dan tad'in su. Amjad ne ya fito yana shasshako kamshi-kamshin abinci a parlourn yana kallon su Sultana. Murmushi tayi mishi,kamar ya mayar mata sai dai ya kautar da kai tare da neman waje ya zauna yana dube-dube. A hankali sauran ma suka fara fito wa suna muzurai na yunwa da shakar kamshin parlourn, duk suka zauna suna dan gulmarta da baki da hannu,kitchen Nass ya leka,sai gashi ya fito yana girgiza wa Saifu ksi halamun baiga komai ba,a jima kad'an ayi hamma mai tsaki nayi duk tana kallon su. Juya wa sukai jin bud'e kofar Uncle d'in da shima ya fito jin corridorn shi ya cika da kamshi iri-iri yana kalle-kalle. "Sorry guyz,yunwa koh? Kai suka fara kad'a mishi suna hamma. "Ina kwana Uncle.. Kallota ya yi tare da amsawa itama yana bata hak'uri tare da fad'in su tafi cin abinci kawai tunda an makara. Kallo uncle din tayi tare da yin murmushi. "Ai tuni ku muke jira na gama komai yana bisa table. Kallon-kallo yaran suka fara tare da kallon Abban nasu yadda ya zuba mata ido. Ganin ba mai motsi yasa ta kama hannun Sultana tare da nufar hanyar dining din ta yaye labule abincin suka baiyana. Tana yaran kowa na zungurar kowa suna kus-kus. Shikam Uncle din kallonta yake yadda take bubbude komai cikin nutsuwa,bata sake kiransu ba sai kamshi abinci da ya kira uncle dan gaskata hancinshi. Zama ya yi tare da lelleka abincin yana mata yake ganin yadda take loda mishi. Zama tayi tare da kallon yadda ya dau sandwich daya ya kai baki yana kallon yaran. Ido ya lumshe,dan haka da sauri ta waro ido ta zata koh bai mishi bane. Ido ya bud'e tare da sauke ajiyar zuciya yana kiran yaran da hannu cikin sauri halamun su taho. Kamar kwa masu jira da sauri suka mike har suna dan had'a kafad'a. Murmushi tayi tare da zuba ma kowa tana tura mishi. Tsit ka ke ji daga uban har tsagerun ya'yan an dukufa ana aika d'a'amu ba k'ak'kautawa. Wa yaga su Uncle *d'an hakkin da ka raina*😹 By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 34_Ruwa ta debo a roba kamar yadda taga Umma nayi in Abba yasa hannu a abinci tare liquid soap ta miko wa uncle tana murmushi. Hannu ya sud'e yana kad'a kai, "Bravo alaiki Farida... Baki ta washe tare tatsa mishi soap din ya wanke hannu yana kallon yaran masu kokawa da kasusuwa. Dariya suka sa bayan Nass yai musu wani tsurkun suna kallon Farida da ta fara kwashe plates na gaban Uncle ta nufi kitchen. Da fara'a ya kallo su duk a zatan shi abinci ne ya kwashe su. "Hala yai dad'i? Kai Nass ya kad'a lokacin da yake yagar cinyar kaza. "Not bafad'in .. Duk kallo Nass d'in sukai jin a yau har ya sauya wa Abban suna zuwa Dady cikin santi,dan haka tuni suka kece da dariya harda kyakyatawa. Dariyar su ne ya fito da ita,da mamakinta har Uncle d'in suke dariya yana kad'a harda basu hannu suka tafa. Murmushi take tare da zubawa Uncle din ido,ba karamin kyau yai mata da dariyar tashi ba,a dan zamanta na sati ta fuskanci yana da kyakkyawar alaka tsakaninshi da yaranshi dan matuka yana ji dasu tamkar tsoka daya cikin miya. Wani sa'in sai ta ga kamar ma ya maida su abokanshi cikin aminci. Ina ma zasu ra6a ta itama ta zama Family kowa ya sota kamar yadda suke son junan su. "Kar ki damu,kiyi tayin yadda Umma ta ce zasu so ki.. Murmushi tayi tare da kad'a kai jin zancen zuciyarta ta karasa garesu. Murmushi Uncle din ya dawo yi ganin Faridan,a hankali kowa ya tsagaita tashi suka ci gaba da abinda suke. Ba laifi,dan ta samu sassaucin hararar da suke mata da kallon tsana,abu d'aya ne dai har yau sun kasa kar6a shine matsayinta na 'Stepmother'.. Dan kuwa koh a gabanta d'aya ya tuna wa saura yanzu zasu fara yatsine fuska suna kiran 'No way.. Abu d'aya ta fara fuskanta shine shegen cin da su Saifu suka kowa harda na keta a kwana biyu kawai. Yanzu zata gama abinci sai ana cikin ci su riga kowa cinye wa sai su hau fad'in a kara. A d'aukin girkin take,dan haka tashi ta kara wani bai bata matsala haka zasu cinya tass. Murna take a yau lahadi gobe zata fara halartar makaranta dan Uncle ya bata uniform sun siyo school bag da duk abin bukatar ta,dan haka gobe sai bin su Saifu. Kowa yana kallo amma ita da Sultana suna kitchen sai agigin fere dankali take mai yawa tana zubawa a ruwa. Sai da safe tai musu ganin takwas har ta gota bata kwanta ba. Duk da kallo suka bita har ta kule kowa na aiyana abu cikin ranshi. Kofa aka buga mata lokacin da take kok'arin kwanciyar,tashi tayi dan jin bugun kamar na Sultana,bud'e wa tayi,ita ce kuwa rike da karamin pillown ta sanye da kayan bacci. Murmushi tayi mata tare da fad'in "Can I stay with you tonight? Waje ta bata ganin yadda take langwa6e mata kai halamun roko, da kwa dan gudunta ta shige tana murnar yau zata kwana tare da Farida. Ajiyar zuciya tayi tare da "Thank God da na iya had'a yaran baturen nan,da iyayin y'an gidan nan ya barni a baya.. Kofa ta rufe tare da juya wa tana k'akalo murmushi. Da gani ita Sultana fira tazo,ita kam daukin tashi da wuri yasa sai bacci ke fusgarta amma tana biye wa Sultanan da sai zuba take mata kamar kanya. Chan dai wajejen tara da wani abin taja bargo tare da ce ma Faridan. "Good night.. Ranar ce ta farko da suka fara had'a kwana ita Sultana,dan haka tun asuba da tashi sallah itama ta tashi tana binta. Kitchen suka wuce suna idarwa koh koma wa ba suyi ba. Da dan kwarafniyar Sultana ya ja hankalin Uncle wanda suka dawo a masallaci ya tsaya,su kam su Saifu bacci fal ido suka wuce d'aki. Yankan 'chips' ya samu suna yi suna a gaban sink suna dariya a tsaye,yayin da ta bawa Sultana kujera ta hau ta tsaya itama hannunta na cikin ruwan dankalin. Hannu ya hard'e tare da jingina yana kallon su. Kayan bacci ke a jikinta na riga da wando cotton fari da mitsi-mitsin flower jajaye wandon da kad'an ya wuce gwiwa yayin da hannun rigar yake mai tattara da jan zare kamar shimi harda su 'breast curve'. Dan dad'in aiki zanin da ta dauro ta cire gefe tare cire karamin gyalen ta ci damara dashi ta bar gashin haka,dan haka daga inda yake yana iya kallo tumin d'aurin da tai wa gashin da ribbon fari. Murmushi yai musu ganin Sultana na dan yarfa mata ruwan dankalin tana kautar da fuska suna dariya. Ilahirin surarta ya fara karewa kallo. Kusan da kad'an tafi Saifu tsayi da dan kaurin jiki. A zahiri surar girma ta baiyanar mata dan tuni ta fara cika mai fusgar hankali irin na cikakkun mata. Ajiyar zuciya yai tare da saurin juya wa ya bar kofar ganin tunani ya fara kaishi wani gurin dan haka sai ya barsu nan. 'French toast' da chips ta had'a musu cikin nutsuwa dan ta rage aiki jiya. Ganin kullum tea ake sha,dan haka yau sai ta dama musu tapioca na cikin garar ta ruwa-ruwa tasha madara. Da sannu kowa cikin 'lunch box' nashi ta sanya mishi 'french toast' da chips din da dan ketchup. Sai tapiocan a cikin dogon bottles din masu kama da karamin flaks na yara ta rufe su kamar jakunkuna. A gaggauce tai wa Sultana wanka ta buga d'akin su Saifu itama ta shiga kamin ta dakko goggun kayan su ta ajiye. Make-up dai-dai dai-dai ta musu ba wani jan baki sai powder kawai da wet lip komai iri guda har style na gashin su parking a tsakiyar kai. Jin hayaniyar y'an gidan halamun sun fara fitowa yasa ta kamo hannun Sultana suka fito. Sucks suke sawa a parlour,duk da kallo suka bisu ganin tana musu 'Hi'. Yake kawai suka mata kowa ya cigaba da sabgar gabanshi. Dining ta wuce tare da zuba ma kowa chips nashi a plate da 'ketchup' a gefe da kwai soyayye tare da tapioca a cup. Corridor take kallo ganin har yanzun Uncle bai fito ba,gaba d'aya ta k'agu taga an gama ta isa makaranta. Hanyar ta sawa ido jin bud'e kofarshi,turaren shi ne ya fara baiyanar dashi a gare su yana daura link na hannunshi. Matuka yai mata kyau yau a cikin dogayen kaya farare har yafi na ranar Jumma'a kasantuwarshi ma'abocin k'ananan kaya. "Sorry guys... Kai duk'e yake fad'i rike da briefcase nashi a gefen hannu. Murmushi tayi tare da kok'arin jan kujera ta zauna. "Bissmillah... Ya fad'a yana gyara d'ayan bangaren link d'in. "Good morning Dady.. Murmushi ya yi jin sunan da suka k'ak'aba mishi,hannu yakai tare da ruko kumatunta yana fad'in "Morning sweetheart.. "Ina kwana Uncle.. Kai ya dago tare da amsa wa yana kallonta. Tai shar cikin uniform din sun mata charas kamar an auna ta ba wai kallo kawai ba. ''Farida... Murmushi tayi tana zama "Na'am ina kwana. Zama yai yana dan basar da kallonta tare da amsawa ganin yadda yaran suka sa musu ido kirrr. Murmushi yai musu dan haka sai kowa ya cigaba da ci kawai. Bayan kowa ya gama ta sako hijab nasu iya dan kirji rataye da jaka sai ta nufi kitchen tare da debo lunch boxes din. Galala suke kallonta barin ma Uncle da yaji wani bankwarakwai har da shi ya tafi da nashi office koh zai ji yunwa. Dariya Nass ya saka,dan haka sauran ma sai suka fara har uncle din ganin Dady ma ya zama dan makaranta. Yake ta hau musu,amma ji take tamkar ta sa kuka dan ganin ita a dole tayi gwaninta. Kai Uncle ya kad'a, shi yasa yake ganin yarintar ta,in banda haka ina shi ina lunch box a office? Shi kam Saifu cewa ya yi ya wuce wannan level d'in ai sai dan primary koh nursery ba shi dan Jss1 ba zai shiga 2. Taji dad'i da Amjad ya kar6a ba musu,ita kam dama Sultana murna take dan kullum tana ganin kowa lunch box nashi ita sai dai in an tashi break suje shop it da su Saifu. Har a mota dariya suke,sai dai da mamakin su da zata fito dasu ta fito har mota. Sun hau hanya Uncle din ya fuskanci yake kawai take musu,dan haka a hankali ya sau karatun Qur'ani wanda yake sa yaran shiru dan dole. Har suka zo makaranta kanta na bisa hanya. Kowa ya fita har Sultana,dan haka ita karshe,duk lunch boxes din uku ta d'auka har nata tare da barin na Uncle a motar zata fita. "Farida.. Juyo wa tayi fuska a sake tare da kallonshi. "Na'am Uncle. "Kin gane ina zaki nufa koh? Kai ta kad'a tare da yin kasa da kai tana murmushi. "Zan bi su Saifu.. Kai shima ya kad'a yana dan murmushi hannunshi bisa stirrri. Fita zata sake yi ya sake fad'in "Farida.. Zama tayi tana dubenshi,dan haka sai ya ciro kud'i tare da mika mata. "Gashi in zaku shop dan su Saifu total ake min every month kan na kamin na saki ciki. Murmushi tayi tare da kad'a kai "Bana son musu.. Baki sake ta kar6a ganin yadda ya tsareta. "Na gode. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 35_Office ya wuce yana murmushin abinda Farida tayi,a kalla koh ba komai yasan da abin dariyarta yaranshi da sannu zasu sake su amsheta a matsayin uwa a gaba tunda har takan sa suyi dariya. Parking ya yi yana kok'arin fita ya hango jakar lunch box nashi da ta ajiye,kai ya girgiza tare da fita. Yasan yau in dai ya dau lunch box har office sai ya gaji da tsiya gun Nasir,dan haka kofar ya rufe. Yau dai kusan tare suka zo Nasir,bayan sun zauna yake mishi wai "Na y'ar mitsila (Feedoh daughter😘). Dariya suka sa tare da tafawa. "Yau ana makaranta an shiga SS1. Kai ya jinjina yana dariya, "Lalle ka tsinci dami fa a kale mutumina, auren yana ban sha'awa na yarinya da tsohon saurayi.. Dariya uncle din yasa yana kad'a kai "Baka da dama Nasir. Ana fira ana aiki,galibi da dabi'ar Farida ne har suka tashi break. "Coffee fa yau ba inda zai kaini,dan sosai nake jin yunwa bari nai order. Murmushi Uncle din ya yi dan tuna wa da tsarabar Farida. "Kasan mey? Kai Nasir ya kad'a, "Ranar fa Farida tasa muka jido lunch boxes har ina mamakin mey za ai dashi sai dai nai shiru. "Yau kawai mun gama break sai ga ta da lunch boxes wai ga nawa koh zanji yunwa ji kamar dan primary.. Dariyar keta ya fara mishi tukunna ya fara fad'in "Ka ga dan gatan y'ar mitsila, a tarairayi yaran ka a tarairaye ka.. Kai ya kad'a jin tsiyar Nasir. "Amma kasan mey? Kai Nasir din ya girgiza. "Y'ar mitsila fa ta bada mamaki fa... Zama ya gyara jin fara zuwa gurin. "Na mey fa? Kai ya jinjina, "Allah nake fad'a maka ta bani mamaki a ranar farko da naci girkinta har yau din nan da sabon salo na daban duk ta iya a fagen girki. Ido Alhaji Nasir ya zaro.. "A kai haba? Kai ya kad'a "Fiye da zaton ka. Cike da zolaya ya ce "Toh kar fa muje kallon kitse muke wa rogo y'ar mitsila ta san komai fa. Kai ya girgiza yana fad'in "Kai haba,bar wannan wajen.. Dariya yasa tare da fad'in "A'a toh a dakko min girkin y'ar mitsila na ta6a. Kallonshi yake da mamaki. "Wai da kana nufin na shigo da jakar lunch box? Kai ya girgiza "Ina yanzu sai a mana dariya. Tashi Alhaji Nasir din ya yi. "Toh kawo ni na dakko,muke shigo da order ma,meye ne aciki? Kai anya nima bazan dau wata y'ar chukul din ba nima ta mayarni yaro... Dariya suka sa,lalle Alhaji Nasir akwai shakiyi, haka ya bashi mukulli yaje mota ya kinkimo jakar lunch box har office nasu. "Bissmillahi.. Bud'e wa ya fara d'aya bayan d'aya yana kallonshi. Dariya yasa ganin abin ciki,sai dai yai mishi kyau a ido dan haka sai ya dau French toast ya gutsura yana kok'arin zuba tapioca. "Kai,lalle ne,a kalla tai ma maganin yunwa. Murmushi ya yi yana kur6ar coffee shi dai. "Toh shi wannan breadin da mey tayi shi? Allah ya min dad'i.. Kallonshi ya yi lokacin da yake jujjuya french toast din hannunshi. "Breadi koma? Kai ya kad'a mishi dan bak'inshi ya cika da tauna. Tashi ya yi tare da zuwa ga table d'in Alhaji Nasir din yana leka abin. "Ka d'au d'aya kaji yai dad'i fa.. D'auka ya yi yaci d'aya, a hankali ya janyo kujera ya zauna cin mey duka,iya dariya Nasir yasha ta,lalle y'ar mitsila ta iya kiwo. **** Ita kam kamin ta samu su Saifu har sun shige cikin taron y'an assembly, dan haka itama sai tabi sahu tana karantar tsari da yanayin makarantar ta masu hannu da shuni,kowa ka gani kwas dashi dan gayu. Iya dubenta bata ga su Saifu ba sai Sultana da tai mata bye-bye ta tafi class. Dan haka a matsayinta na sabuwar zuwa sai ta tsaya inda-indar in da zata dosa. Juya wa tayi sai ga nan wata kusan za suyi sa'anin juna da ita tana takun y'an gayu da iyayi. Da dan fara'rta ta tare ta da tambayar ina zata dosa musamman da kayan hannunta. Kallon banza ta mata tana yatsina tare da wuce wa ba koh magana. Juya wa tayi tana kallon yadda take tafiya kamar bazata taka kasa ba. Harara ta doka mata tare da fad'in "Ji ka'fa kamar ta agwagi dalla... Chak yarinyar taja ta tsaya tare da juyo wa. Kai Faridan ta d'auke tare da had'e rai ganin tana taho wa. Daga sama har kasa ta karewa Faridan kallo tabbas bata da makusa ta fuskar shigarta da tsayuwarta. Kallota tayi ganin yadda take kare mata kallo tana taunar cingam sai ta dauke kai. Murmushi yarinyar taga tayi da mamakin ta,kan ta farga ta miko mata hannu tare da fad'in "Friends?... A takaice ta kalleta, kyakkyawa ce daga gani y'ar masu kud'i ce, sai dai ita sam batai mata ba balle har tai kawance da ita... Kai ta d'auke tare da kin kulata,tasan Umma tasha fad'a musu shasha ce mai taunar chewing gum a titi koh karuwa,dan haka bata ga abin kawance anan ba. "Allah kiyaye nai kawance da mai cin chewing gum a titi.. Dariya yarinyar tasa tare da cire chewing gum din ta hular tare da fad'in "Ok,fine,kiyi ta tsayuwa na fasa nuna wa.. Juya tayi,ganin da gaske tafiya zatai ga duk an watse yasa ta tsayarta. "Toh rakani dan Allah.. Juyo wa tayi tana murmushi kamin ta kar6i wani kayan suka tafi,duk sai taji bata kyauta ba da ta ce mata mai kafar agwagwa dan haka a hankali ta ce mata "Sorry.. Kallota tayi da halamun mai saukin kai ce ba yadda tai tsammani ba sai dai ta shafeta a rawar kai. Murmushi tai mata tare da fad'in "It's ok.. Ajin da zata ta tambayeta,da mamakinta sai taji ajinsu d'aya ma ashe. Kamin zuwa break duk ta gama karantar halin wacce ta kira kanta da Laila,dan haka sai ta yarda suka kulla kawance dan daga gani zatai saukin lamura. Ita kwa Laila kawai Farida mata tayi dan tana son mutum marar daukan raini. Sultana ta hango da halamun nemanta take,dan haka da sauri ta karasa tare da taryarta. Inda zata samu su Saifu ta kaisu ita da Laila,dan haka har cikin abokanshi taje tare da mika mishi nashi ta kauce. "Wace ce Saif? Yana hura hanci ya ce "Wai ita Step-mom namu ne..wai fa... Dariya abokan suka sa tare da sake kallo Farida. "Kai amma an cuci Step-moms,kalleta fa na fita tsayi kuma ma y'ar secondary... Kwafa Saifu ya yi dan jin anzo wajen. Koh shi ya masifar raina girman Farida a matsayin step-moms,balle kuma in ya tuna akidarsu ta tsanar duk wata wacce ta amsa sunan step moms barin ma ace tasu,dan su fa ansha su ne sun warke. "Wow,French toast Saif.. Kallo su ya yi yadda suka fara hakar abinda ta kawo yana ta6e baki. "Amma kun more zaku ci dad'i a gidan ku.. Kallosu ya yi yadda suke ci suna fad'in yau ba zuwa shop,yaje kawai. **** Sai ya zamo daga wannan lokacin daga Uncle din har yaran kowa baijin kunyar daukar lunch box barin ma Saifu da yanzu a dalilin zuwa da lunch box yanzu abokanshi sun mayarta kayan wata karya kowa ka ganshi da ita a rataye,tanan dai Faridee ansau✔ Uncle kam yanzu har ya saba ya dau briefcase da lunch box a hannu ya shiga office har wani alfahari yake. A nan za'a had'u in snacks ta zubo ai taci ana mishi tsiyar y'ar mitsila,dan haka yakan ce ta kara yawan abin akwai maciya a office. Zama da Laila kowa yasa ta fara koyan wasu abubuwa na daga dabi'ar ta aciki kuwa harda wannan gwalangwazon da yanga karfi da yaji. Ga kullum da snacks din da zata koya gunta dan duk su masu burin girke-girke ne,dan haka zani ce ta tadda muje. A class suke wanda kusan watan ta guda kenan da fara zuwa makaranta. Zaune suke sunyi tagumi jiran teachern Biology ya dawo har sun gaji period nashi ya kusa fita bai dawo ba. Duk tagumi suka zuba Laila na bankad'a text book na Biology ita da wata y'ar yarbawa suna duba abubuwan ciki duk da ba nasu bane ita ta taho kawai dashi. Farida ta zungura da sauri tana nuna mata abu a jiki suna kallon y'ar yarbawa. "Ga baby acikin womb Farida wai... Diagram din ta zuba wa ido tare da gyara zama. "Toh anan yanzu ta ina zai kutso wannan katon kan nashi? Dariya y'ar yarbawa tayi,kamin ta kai hannunta kan layin "Ta nan man. Harararta sukai,dan haka tuni ta fara basu bayani suna waro ido. Farida Lailan ta kallo,wacce tuni har ta fara gyara mazaunin hijab nata tana had'iyar yawu jin bayani daga bakin y'ar yarbawa dalla-dalla. Kan ka ce mey tuni har ta tsure ta fara zufa,kallo kawai katon kan yaron take amma ace wai ta jikinta zai hudo ya fito. "Mun shiga uku Farida. Kallo su y'ar yarbawa tayi ganin yadda sukai tsuru-tsuru suna kallon juna tare da fad'in "I see,da kun zata aman baby ake koh mey? A tunzure Laila ta ce "Kinga Malama tafi,tafi dalla, gaba daya kin tsorata mu da wani bayanin ki na karya da gaskiya,dau littafin ki. Baki ta ta6e tare da bar musu wajen suna jimami. "Farida.. Tsuru tai mata kamar 6ere a buta. "Ni har ma na fara tsoron nai aure wallahi Farida. Da sauri ta ce "Nima fa.. Shiru tayi,dan shaf ta manta bata fa fad'a wa Laila Uncle ba dadynta bane kamar yadda ta ce mata su Saifu k'annenta ne. Hannunta ta kamo tare da fita waje suna leka wa. "In fad'a miki gaskiya? Kai Lailan ta kad'a, sai ta duba gefe da gefe tukunna a hankali ta ce "An fa min aure ni... Baki sake take

Chapter 9 of 19