Share this page
kule. "Wato abokina matuka ina mamakin dabi'ar Laila da Farida.. Murmushi yai yana daukan abarba. "Na mey fa? Zama ya gyara shima ya d'auka. "Yara ne,amma matuka masu hankalin manya,ga wayo,a fagen soyayya kuwa.. Ayaba ya tauna yana gyad'a kai. "Kar ma dai Lailata taji bayani,dan taci sunan nata Laila.... Dariya Uncle yai tare da girgiza mishi kai.. "Eh sosai,a lambun itatuwa ba,na san wannan. Dariya yasa yana girgiza kai "No,believe me,da gaske nake,Laila kam hmm,ba a cewa komai,amma ba karamar farar sa'a nai da tsinto ta ba cikin mata dubu.. Abarba ya gatsa yana lumshe ido dan zagi,dan haka sai uncle din ya jinjina kai yana mishi murmushi. A ganinshi shi yafi chanchanta ya ce haka,dan a yanzu gani yake mata suna suka tara,in har zai iya cire Halima,toh Farida ta sha gaban tunaninshi.. Murmushi yai yana gyad'a kai, kowa dai da nashi gwanin,dan haka abin ba'a cewa komai. Kwanika suke tattare wa har su Saifu bayan su Laila sun tafi sun gama cin abinci har takwas tayi. "La,an fara wrestling.. TV su Saifu suka kalla,dan haka tuni hankalin su yai gun suka nufi parlour tare da barin su Uncle a kitchen. A dan sace ta kalloshi tana mika mishi plate bayan ta wanke yana dauraya suka had'a ido. Kai ta d'auke tare da kallon cikin ruwan kumfar tana murmushin kunya ganin kallon da yake aiko mata. Plate din ta sake kai duk'e, murmushi yai tare da had'o wa da hannunta ya rike kam,dan haka sai ta kalloshi. Kasa ta sake yi da kanta,wannan kallon bata iya jure shi,dan ba karamin kunya yake bata ba amma shi koh a jikinshi. Kamin ta farga ya koma ta bayanta tare da sanya hannunshi duk biyu ya riko hannunta mai rike da soso suna wankewa a tare. Ido ta rufe jin numfashin shi kusan saitin kunneta. Kanshin ya d'aura bisa wuyanta tare da sakar ajiyar zuciya, a hankali kamar mai rad'a ya ce "My yori-yori.. Ido ta sake tamke wa sosai tana buguwar zuciyarta na dad'uwa da sauri da sauri. "Dady kar ya wuce ka fa.. Murmushi yai tare da dan juya jin muryar Nass ya dan daga murya dan yaji.. "Bari Nass mun kusa mu gama ku cigaba.. Ido ta dan bud'e tare da wara su kan hannunsun,a hankali ta furta "Uncle yara fa.. "Ina suke? Shiru tai tana wanke plate din da yake dirza soson hannunta a kai. Tun tana takura kanta har ta dan sau jiki a haka su ka gama tare da fita ta barshi yana d'auraye hannu ta gudu parlour inda su Saifu sai ihu suke na fad'in "1,2,3 ya cinye.. Cikin ihu gaba d'aya hankalin su yai kan wrestling. Fito wa yai yana goge hannu da karamin towel yana dan hararota kad'an tai tsakiyar su Saifu ta zauna. Murmushi ya yi tare da kad'a mata kai. Kowa yai d'aki dan bacci,daga wanka ta fito ta mirza mai kad'an da turare cikin sauri duk dan tayi ta kwanta ta zira kayan bacci. Gado ta d'ane tare da jawo bargo sai ta tuna bata kashe fitila ba,dan haka sai ta zame bargo da niyar sakkowa taji an dan kwankwasa d'akin. Ido ta waro tare kasa kunne,kamin tai kwakkwaran motsi har an turo kofar. Yawu ta had'iye tun karfi ganin Uncle rike da kofi a hannu yana kallonta ganin yadda take raba ido ya 6era a buta. Kofi ya nuno mata cikin dan kama kai "Zan samu tea please?.. Fuska ta fara marairaice wa tana kallonshi ganin ba da wasa yake ba dan haka a hankali cikin ranta ta furta "Wayyo ni Ummata... By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 65_Tana tutturo baki ta isa d'akin tare da tura wa. Kai ya dago yana dane-danen waya ta tsaye a gefe rike da farantin tana dan kau da kai gefe ita a dole bata son shiga d'akin. Kai ya kad'a tare da sake kallon wayar yana latsawa. "In ya huce zaki koma ki dimamo irin na jiya fa.. Kalloshi tai,dan haka sai ta ajiye gefen tare da sake tsayawa. Amma dake Uncle din namijin duniya ne da sannu yasa ta zauna. Kallota ya yi, "Daga yau ma tea din ya dawo dan kullum 10:30pm dot nake son ya iske ni tunda abin haka ne.. Fuska ta marairaice, "Uncle mey nai ni.. Kai ya d'auke yana kur6ar tea d'inshi,dan haka sai ta saita tare da sakar fuska. Tashi tai da nufin fita jin ya shareta yai saurin fad'in "Wa ya sallame ki? Kalloshi tai fuska a marairaice tana sake zama. Duk ya d'auke mata wuta, dan haka ba dan taso ba tai shiru har gyangyad'i ya fara surarta ta zame nan. A dan jima ta farka ta tashi ta zauna,in taga bai ma kallonta sai ta koma. Kai ya girgiza tare da ja mata bargo,abin nata ma abin dariya. Washegari ma haka har ta kwanta goma ya kwankwasa ta bud'e tana hammar karya da murza idanu halamun bacci take. "Shayi,koh kin manta? Wata hammar ta sake ta karya duk yana kula da ita,abin har dariya yaso bashi sai dai ya gimtse. "In kin ware ina jira.. Da kallo ta bishi tana chunno baki ganin wannan kuturin sanaben irin na Uncle. D'aki ta koma tare da zarar hijab ta d'aura bisa kayan baccin ta nufi kitchen. Mika mishi take harda wani munafukin murmushi wai duk dan ya batta tunda ta sau fuska. Murmushi yai tare da amsa yana girgiza kai,shi wai Farida zatai wa wayo. Sha yake yana dubanta jun yadda take mishi tad'in daga term din nan sai SS3. Murmushi ya yi tare da gane inda ta dosa. Dan haka sai ya fara biye mata har da su dariya. Ajiyar zuciya yai yana kallonta,kallonshi ita ma take tana murmushi, ganin abin yai yawa yasa ta dukar da kai da dan kunya,murmushi yau tare da fad'in "My yori-yori uh uh.. Sato kallonshi tayi kai duk'e tana murmushi, "Uncle wai meye ne yori-yori? Shayin ya kwankwad'e gaba d'aya jin anzo wurin yana murmushi ya ajiye kofi. "Biya na baki bayani.. Zama ta gyara tare da dunkule hannunta ta mika mishi tana murmushi. "Gashi toh.. Murmushi yai tare da kallo hannun, hannunshi ya mika mata halamun ta bashi tana kunshe dariya. Yi tai kamar ta bashi abu duk da ba komai a cikin hannun tana dariya. Tafin hannun nashi yake kallo ta biye mata yana fad'in "Uhmm,duk wannan ni kad'ai? Kai ta jijjiga tana dariya,hannun ya hau jujjuya wa kamar gaske. "Amma abin yai kyau.. Kai jijjiga "Toh a fad'a min.. Kallota yai dauke da murmushi. "Kawo kunnenki ban son kowa yaji. Matsawa tai ba tare da ta kawo komai ba ta mika kunne. Kamar mai rad'a ya fara mata magana a hankali, tsit tayi tare da nutsuwa idonta rufe tsawan lokaci. Dago wa yai yana kallonta,dan haka sai ta bud'e ido tare da kau da kai tana murmushin kunyar jin abinda ta tambaya. Tabbas da tasan wannan ce ansan da bata tambaya ba kayan kunya. ''Kin gane bayanin? Hannu tasa tare da rufe fuskarta wai ita kunya tana fad'in "Uncle.. Dariya yai tare da fad'in "Koh ke ba ita ba ce?.. Juya wa tai tare da sanya kanta jikin katifar ta rufe fuska tana murmushi. Kai ya kad'a tare da murmushi. A hankali ya fara janta da fira, tun bata iya magana har ta ware jin labarin su Aunty Feenah zasu dawo Kano. "Yanzu nasan Little Haly ta sake girma mai kyau da ita. Kai kad'a yana murmushi. "Ki daure ki haifo muku taku mey kyaun tunda su Saifu ma naso. Ido tai mishi kir a waje. "Na haihu kenan? Kai ya jijjiga. "En,mey ki ke gudu? Kai ta sunkuyar, "Azabar haifan babyn,da ana siya sai mu siyo na huta.. Ido ya sa mata,jin yai shiru yasa ta kalloshi, dariya yasa harda kyakkyatawa,lalle har yanzun da sauran Farida. Kallonshi take tana yake baki,har ga Allah da gaske take,in dai ana siyar wa gwara a siyo ta huta da fitar da ta jikinta. Kai ya kad'a tare da tsagaita wa. "Halima da kanta take haifuwan su Saifu a gida ma ba babu mataimaki Farida.. Ido ta zaro tare da wage baki,dan haka da sauri ya jijjiga mata kai halamun yes. "Wani sa'in sai dai nazo na tarar har ta yanke cibi kamin ta kira makociyarta Aunty Rabi taimako. Kai ta jijjiga, lalle yar baiwa ce.. "Jaruma ce koh acikin mata Halima,nasan kuma yana da nasaba da hakurinta... Baki ta chunno jin yadda yake kwad'a Haliman kamar wani ita ta rage mace d'aya jaruma a duniya sai kwad'ata yake. Tuni dan halin ya motso na kishi,har kullum ta rasa mey yasa take kishin Halima koh da kuwa cikin mata ne. Kalloshi tai yadda yake murmushi yana dad'a lissafo mata wacece Halima da jarumtarta. Baki ta sake turo wa,dole ta dage dan sai tafi Halima jarumta,tuni taji tsoron haihuwar ma ya fuce akanta dan kishin yadda yake kwad'a Halima... Shiru yai tare da zuba mata ido ganin yadda take chunno mishi baki. Dan harshe ya dan cije,ashe fa ya kwafsa. Yafi kowa sanin yadda Farida ke ji in ya ambaci Halima,ya kuma rasa dalilinta na yin fushi a kullum. Murmushi ya yi tare da girgiza kai,komai na Farida daban yake,in banda haka mai ya kai ki kishi da matacciya? Baya ta juya tare da jan jiki sosai tai kan filo ta kwanta tana gunguni. Kai ya girgiza, "Farida matsala... Gadon ya haye tare da kiranta tai mishi banza. "Oh,common mana, jarumta fa na ce kawai ba komai ba kan Halima.. A tunzure ta tashi tare da fad'in "Nima zanyi fin nata,ba ita kad'ai ne jaruma ba amma tun dazun ka ke ta kod'a min ita.. Baki ta saka tare da sakar kukan 6aci. Galala yake kallonta da mamaki,kan ya farga har dariya ta subuce mishi,dan haka tuni ta sake tunzura tare da kok'arin sauka dan barin mishi d'akin ya ruko ta. "Ok,ok,toh naji,i'm sorry,shikenan? Kai ta girgiza halamun ba shikenan ba tana chunno baki kuka ba koh hawaye. "Ai ke in anzo kanki karshe ce believe me,dan sunanki jarumar mata a fagen jarumta wane Halima.. Kalloshi tai da y'ar harara jin zai zurma ta. Kafad'a ya daga da fad'in "Sosai. Har ranta kwa taji dad'i jin ya zama serious. "Sai dai fa da matsala.. Ha6a yake shafawa yana mata kallon kasa-kasa. Ido ta zaro, "Matsalar mey? Matso wa yai tare rad'a mata,kai ta d'auke tare da k'auda kai tana sinke kai,in dai zata zama jarima yanzun ai tana ga ba abinda zai gagara,dan haka cikin sauki yasha tunaninta cikin ruwan sanyi. Kallonta yake yana murmushi tai bacci, lalle ne Farida kam bata da wayo,abu kad'an zaiyi wayonta ya kare. Kai ya jijjiga tuno rigimar tata da yadda komai ya kare sai ya sake murmushi har hakoranshi na bayyana,bargo ya gyara mata kamin shima rufe ido. Tun daga ranar ya samo lagon kayarshi,yanzu zai 6atar da tunaninta daga baya ya hau dariyar keta in ta tuna yadda take zurmuwa. Burinta a yanzu zata iya haifar baby koh da yanzu yazo zata nuna jarumta koh dan son su Saifu da ita da suke ma Baby. **** Sun koma makaranta,dan sanabe chan karshe suka maida bencinsu su biyu ita da aminiya Laila,a cewarsu yanzu sun fice ajin yara dan haka wuce nan. A yanzu basu da burin da wuce ganin sun faranta ran mazajen nasu da iyayi irin nasu had'i da shawarwarin juna,dan haka tuni suka sake dinkewa ana baje wa su Nasir bajakolin iya yi. Su Uncle abin nema ya samu,wai matar direba ta haifi mota😜 By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 66_Zaune suke a parlour ita da yaran su na kallo,a dan jima su kalli kofa halamun dai da wanda suke jira zai zo anyi hutun makaranta sannan ba islamiya. Cike da farin ciki suka mike jin sallamar Uncle baki har kunne dan murnar zuwan bakuwar tashi. Zai wahala in baka sani ba ka ce wai tafi Uncle a shekaru,dan ita mai karamin jiki ce ga kuma wayewa da ilimi da ta samu wanda shi zai banbanta ta da sauran 'yan uwanta. "Aunty Hafsa.. Da murnar su yaran suka tare ta lokacin da ta sako kai parlourn. Da murnarta ta tare su tana mai kallon Farida da murmushi. "Sannun ku da zuwa.. Hand bag nata ta kar6a lokacin da take kok'arin since goyon dake bayanta sukai mata chaa a ka kowa na kok'arin amsar babyn. Kai ta girgiza tana murmushi ganin yadda har Uncle din sun mamaye babyn sai fad'i suke "She's so cute.. Farida na dariya. Matuka iyalan Kabir sun burgeta,duk da wannan ne haduwarta da Farida na farko sai dai a waya,amma ta gano su na da kyakkyawar mu'amula da junan su. D'akinta ta sauke ta,dan sosai ta san mahimmancin wace ce Hafsa gun Uncle a yau ganin yadda bak'inshi yaki rufuwa har kowa ya tafi su na a tare firar yaushe gamo. Ajiyar zuciya yai yana kallonta. "Har kullum ina alfahari dake sis ta yadda ki ka jajirce gun karatun ki,i'm so proud of you,ina fatan na kira ki chief Nurse watan wataran. Murmushi tai tare da gyara zama. "A kullum kai ke karan gwiwa Kabir har na zama abin da a yau na zama,na gode, Allah ya bar mana zumunci. Kai ya kad'a yana murmushi, "Amin sister,ni ne da godiya. Kai ta kad'a. "Gaskiya kai dacen mata mai tsanin son yaran ka,sannan matuka tana hankali in ka cire 'yar yarintar dake tare da ita wanda yai dai-dai da wayonta,sosai nake ganin kok'arin yadda muke zumunci a waya, a waye take batta duhun kai. Kai ya kad'a yana murmushi. D'akin Faridan ta shiga bayan sunyi sallama da Uncle din. A goye ta tarar da babyn nata Farida na dan jijjiga a hankali halamun tai bacci. Murmushi suka sakar ma juna. "Har yanzun baki kwantar ba Farida,kar fa ta saki ciwan baya. Murmushi tai tare da girgiza kai, "Ai bata da nauyi,goyon ke min dad'i ne.. Kai ta kad'a tana jinjina a gidan wa ya fi wani son yara,uncle din? Koh Farida koh su Saifu?. Tasan dai a yau 'yarta tasha kauna da d'auka. "Kullum ina cewa Uncle in mun samu dugun hutu muje Sokoto ashe zaki rigamu zuwa sai dai gaba. Kai ta kad'a tana murmushi "Yana fad'a kam,ga nan bikin Saliha ya kusa in ta gama secondary Insha-Allah,dan su ma sun kagu su zo toh karatu. Kai ta sunkuyar tana murmushi. Ganin firar Farida ke so taki tashi yasa ta ce "Kawo ta ki ga,kije ki kwanta kema. Keya ta sosa cike da kunya ta sinto babyn,ta dan jima tana sinke-sinke kamin tai mata sallama ta fita. Kai Hafsan ta girgiza tana murmushi tare da sauya wa babynta pampers. D'akin ta tura tare da shiga tana leken shi. Harara ya dan sau mata lokacin da yake gyara labule ganin iska na kad'owa na hadiri. Marairaice wa tai tare dan karasa wa tana ajiye farantin shayi. "Mey nai kuma my boo nah?.. Sake harararta yai kamin ya janyo window. "Wato kin samu Hafsa ni kin manta ni koh? Na zata achan zaki kwana.. Murmushi tai tare da cire hijab da zanin da ta d'aura a kai. "Toh bari na koma,dama firar bata kare ba ita ta koroni.. Zani ta dau tana chunno baki kamar gaske ta juya zata koma ya chafko ta yana fad'in "Ba ki isa ba kuma wannan,in an shigo min ba'a fita kin sani.. Baki ta sake chunno mishi tana gunguni ya hau mata chakulkuli kad'an tuni ta ware tana dariya ta zille zuwa katifa ya biyo ta. Ajiyar zuciya yai tare da yin filo da kaffafunta. "Sosai nai farin cikin zuwan Hafsa a yau,dan rabon da tazo nan tun lokacin Fatima,matuka ina sonta da burin kyautata mata iyakar iyawa na Farida.. Kai ta kad'a tana murmushi sai ya cigaba. "Hafsa kad'ai ke kaunata a lokacin da sauran 'yan uwana ke burin sun kuntata mini.. "Hafsa kad'ai ke iya sharing na kwanon abincinta dani Farida a lokacin da bani da rabo acikin abincin gidan mu.. "Hafsa ce kad'ai za'a dakeni,a tsangwameni a cikin yayuna ina kuka tazo tana lallalashina itama tana kuka tare da fad'in "Kabir kai hak'uri,bani da karfi da na rama maka.. A yayin da sauran 'yan uwan nawa ke murna da dariya in har sunga kukana.. "Wallahi Farida Hafsa ce kad'ai a wanchan lokacin zata iya fad'awa wuta ta tsamoni dan so in har su Tabawa sun hullani dan so.. Ido ya rintse yana tuno wata rana achan baya,ranar da bazai iya goge wa cikin rayuwarshi ba. Ranar da yake ihu yake komai tare da roko na Allah da annabi amma babu mai jinshi,maimakon haka ma dariya suke suna mai turereniyar hankad'a shi cikin rijiya in banda Hafsa dake ihun taimakonshi ba hali. Hawaye ne ya zubo mishi ido rufe,da sauri tasa hannu tare da taro su itama tana hawayen. Ido ya bud'e, sai ta hau kad'a mishi kai. "A yanzu hawayenka masu matukar tsada ne Uncle balle har ka zubar min su kan wasu chan wanda basu chanchanta ba su Tabawa. Murmushi yai mata tare shima da kai hannu yana goge mata nata. "Basu nake ma kuka ba my yori yori. Kai girgiza "Kaunar Hafsa gareni ce ta sani kuka,na san koh yanzu ina da 'yar uwa shakikiyata mai kaunata a bangaren Abba da muke da jini.. Kai ta kad'a mishi tana murmushi. "Ka d'auka toh d'aya ce tamkar da dubu,dama da wani taron na yuyu gwara d'aya kwakkwara Uncle. "And na san watan watarana su Tabawa zasu iya kwaso kafa su iso gare ka,toh ina so daga yau ka barmin komai a hannuna,ka manta da ka ta6a rayuwa da wasu chan wai su su Tabawa. "Yanzu kana da Umma,Abba,su Saifu,Aunty Hafsa dasu Aunty Feenah masu kaunarka.. "Bayan haka kana da Farida,koh ni kad'ai na isa na maye maka gurbin su Indo da ka rasa believe me. "Cos you're my heart,my soul,my world,my Jannah,my treasure.. Murmushi tai tare da jaddada mishi "You're my everything.. Murmushi yai tare da janyo fuskanta ya had'a tare da nashi yana sauke ajiyar zuciya, in da Farida a kusa yasan ba shi babu shiga cikin bakin ciki zata wanke zuciyarshi ne tass. Ya gode Allah da ya bashi Farida madadin Halima,domin in ana neman *Mar'atus saliha* a garshi zai daga hannun Farida sama ya nuna,domin ga ta a gareshi. By Feenat Ja'afar. Ai min afuwa jiya na ce zan turo shiru,na fita ne anyi rashi ma Auntyn mu, thanks. Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Arewa hausa novels Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239 *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 67_Kwanan Hafsa shida ta tada ballin gobe zata tafi dan kwana uku tazo musu sun hanata tafiya,wasa-wasa sai da tai kwana takwas kamin ya batta ta tafi yana mata tsiyar koh Yunus ya motso kambun sa? Murmushi kawai ta musu amma ba wai dan ta gaji da zaman gidan ba,yara take tunani da ta baro ga zata Kano. Ba karamar tsaraba suka jido mata ita da yaranta, barin Farida kayan baby na mata sai jida take ma babyn Hafsan su kayan wasa. Ido ne kawai nata,dan so kam ta ganshi gun Kabir da iyalanshi,bata jin koh Fatima dake a jininta tai mata rabin karar da Farida tai mata,dan haka cike da kaunarta ta baro gidan da sake son d'an uwan nata Kabir. *** "Tashin hankali, wannan ai koh Makkah ki ka je sai haka irin wannan tsarabar Hafsa,lalle duniya tana gidan Kabiru.. Kai ta kad'a kanta na bisa waya tana latsawa, sai dai jin abinda Tabawa da Indo suka fad'i yasa ta dago kai da sauri baki sake tana kallonsu. "Ku ma za kuje ina? Harararta Lami tayi tare da fadin "Abuja gidan Kabir,koh ba komai ai wannan ma nashi ne kuma jininshi ne.. Baki Indo ta yage tana kad'a kai "Kwarai kuwa,dama wallahi dama kawai nake nema na rokeshi kud'in jari dan ni kwarjini yake min.. Murmushi Hafsa tai na takaici.. "Baza ku ta6a sauya wa ba daga inda nasan ku,a kullum ku duniya ku ke hange ba wai lahira da mugun abinda kuka shuka ba.. "Ban tunanin har yanzun baku saduda ba,wato ku ba ma ta neman gafarar abinda ku ka mishi ku ke ba sai ta abin duniya? Le6e ta cije "Na gode Allah da ya wareni cikin ku sannan ya banbanta ni da dabi'ar ku wallahi, ba da ban Kabir yai mun tuni ba da sai na ce wallahi ina da na sanin kasantuwa ta acikin ku... Mari Lami ta dauketa dashi tana huci. "Wawiya kawai,toh bari kiji duk lalacewa ta baki isa sauyani daga uwarki ba,da wanda zai ce bai son duniya? Koh ke ba kwadayin bane ya kai ki mu za kiyi wa bakin cikin zuwa?.. Hawaye ke zubo mata dafe da wajen marin,sai da ta kai aya kamin ta tashi ta sa6a yarinyarta ta hau tattare kayanta dan takaici. Gidan su Abba ta koma jin duk sun chako mata da fad'in "Eh ki kwashe yar bakin ciki,wanda zamu samo sai yafi wannan, ki zuba ido. Kamar kullum in tazo Kano da kukan bakin cikin y'an gidan su take koma wa sokoto, amma yau dake Umma na gida dama takan je mata ita da Kabir tun da sun saba anan ta gama hutun ta ta koma. Sunfi sati su na neman address na Kabir a Abuja sun rasa wanda zasu tuntu6a,su Indo kad'ai ke shiga sashin su Abba a dalilin zuwan Umma,toh ba fuska balle su tambaya, ga kacha-kacha sukai da Hafsa sunyi imani bazata basu ba. "Ga dabara.. Tabawa suka kallo gaba d'ayan su. "Ke Fatsima tunda kina da waya ki kira Hafsa a zuwan bata hak'uri sannan ki ce munji munyi nadama ta baki adireshin zamu mu bashi hak'uri, in ta kama ki kawo har kukan karya zanyi mata nasan ita akwai wayo. Shewa suka sa harda tafawa har yaran. "Tinkiya ta na siyar jiya dan nasan in munje zan maida har kud'in rago, na fad'a wa Murtala sati biyu zamuyi koh wata dan haka dama bai bani ci balle sutura dole ya barni zuwa cin arziki yaki,karshe wai na zabi daya. Shewa suka sake yi suna dariya "Toh ke mey ki ka ce? Baki ta ta6e "Wannan kaddararran auren wallahi kud'i yafi min shi,tuni ma na ce na zabi tafiya Birnin tarayya Habuja.. Dariya suka sa suna fad'in tai musu dai dai,harda mai fad'in itama in dai ta samo dayawa sakin nata mijin zatai ta kama gida. Haka kwa akai duka kira Hafsa,duk da bata yarda dasu ba amma jin yadda suke rantsuwa da Allah yasa ta yarda sun gane gaskiya,karshe harda sake musu nasiha zata kashe waya suka sake makale murya akan ta basu address na Kabir koh su Indo su wakilta su nemo musu gafara. "A'a Tabawa,bai kamata daga dawo wata su na su diba su je ba.. Da dad'in baki sai da ta bayar tana mai fatan Allah sa da gaske su Tabawa sun shiryun. Kwana biyu da haka kuwa sukai shiri su biyar dan wai masu kud'i basa son yuya balle ya'ya, dan haka suyi hak'uri sauran duk abinda suka samo tare za'a raba. Da wannan aka nufi Abuja koh su Umma ba wanda ya sani. **** Waya yake mata yana tuki tana y'ar dariya mai sauti tare da fad'in "Me too.. Shiru tai tana saurarenshi tare da barin abinda take tana fad'in "Ok Sugar... Wayar ta cire a kunne tare da kaiwa baki ta bata dogon kiss tana mishi dariya. Kai ya kad'a tare da fad'in "Yauwa,sai na iso.. Wayar ta ajiye bayan sunyi sallama ta cigaba da juye abinci a flaks tana murmushi yaran zo dan cire kayan Jumma'a wai za su wasa jiki a backyard. Dariya suke ma su Saifu dake nuna kumatun Nass wai yafi kowa kiba tana kad'a musu kai suka fuce. Koh ita kanta Uncle fad'i yake wai shi kam ya iya kiwo, sai sake cika mishi ido take da kyau. Murmushi tai dan tuno Boo din nata,tasani duk inda yake toh yana gaf da dawo wa gare su dan 5 tayi.. Windown kitchen din ta leka ta inda take jiyo hayaniyar su Saifu. Murmushi tayi tuno da lokacin baya suna ball tare,kai ta kad'a, yaushe zatai tunanin zata zama Mom nasu Saifu a lokacin, murmushi tayi tare da sakar ajiyar zuciya ta ambaci "My boo. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 68_Sallama akai,dan haka sai ta rufe tare da fita jin muryar John na fad'in ta leko wai gidan suke nema wasu daga Kano. Gyale ta dakko tare da fita tsakar gida kowacce da kullin kayanta. Da fara'a ta ce su shigo jin sun ce dangin su Kabir ne daga Kano ta zata koh yan Rano ne. Kalle-kalle suka fara suna zungurar juna jin sanyin a.c da kuma kyaun parlourn. "Humm,Aljanar duniya,ji wannan alatu ni Tabawa... Zungurarta Lami tai halamun tai shiru kar aji ganin Faridan ta nufi kitchen kashe gas. "Ji matar tashi,wannan ai ya haifeta ashe da gaske? Hannu Lami ta kai bakinta halamun suyi shiru man. Da fara'a ta sake fito wa d'auke da faranti da kofuna da abin sha,tuni suka hau yage baki.. "Ya ku ka zauna a kasa? Ku hau kujera please.. Baki suka sake wangale wa kamin duk suka d'ane bisa kujera,duk da yarinya ce Faridan amma ba karamin kwarjini tai musu ba dan ta gaji da gayu ta ko'ina, dan haka tuni suka sake raina kansu. Zama tai suka gaisa,tuni suka hau bata labarin irin wahalar da suka sha gun neman gidan kaf kud'in su ya kare. Yake tai musu tare da tashi ta koma kitchen, haka kawai taji basu wani kwanta mata na sosai duk Sonta da dangin Kabir. Abinci ta zubo a plate yaji naman kaji da akai wa Pepper chicken

Chapter 16 of 19