Lami amma kinga yarinyar nan mayya taki tafiya.
"Ina fa tsoron maganar Mai yankan wu....
"Rukayya! Rukayya!!..
Shiru sukai tare da kasa kunne jin kwala kiran da Malam ke wa Rukayya cikin tunzura.
Da sauri suka mike tare da lekawa.
"Fito nan tsakar gida.
Ido jajir ta fito halamun yanzu ma kuka ta d'ika.
Tsugunawa tayi kai kasa tare da fad'in
"Gani Malam...
"Munafuka rufe min baki..
Dagowa tayi,suna had'a ido ya kautar da fuska da sauri duk ya sauya kama.
Ido su Tabawa suka had'a tare da komawa d'aki suna murna jin ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba yasa suka nutsu tare da fito wa cikin marairaita.
"Haba Malam,wannan irin fad'a makota suna ji kayi hak'uri haka.
Harara ya sakar musu
"Hak'uri ya wuce wanda nake yi da ita tuntuni? Koh ba kwa gani ne?
Kai Lami tai saurin kad'a wa tare da fad'in
"Muna gani Malam,amma mey tai maka yanzu?
Kai Rukayyan ta dago dashi tare da zuba ma Lamin ido.
"Toh wai dan rashin mutunci irin nata shine ta kai karata gun Nasir wai bata san mey tai min ba duk na sauya.
Ido Tabawa ta zaro
"Kai Rukayya, toh meye ma na kaiwa kara gun kaninshi?
A tunzure ya ce
"Toh nagaji,ki tattara kawai kije sai na nemeki.
Ido ta rintse hawaye ya zubo shar, nan take ta karanto ayar yayewar mudiba.
Bazata so ta tona abinda take fuskanta ba a gidansu,amma yanzu ankai ga6ar da dole a sani.
Tashi tayi tare da kad'a kai
''Kayi hak'uri Malam,zan tafin,Allah ya huci zuciyar ka.
Tsaki ya yi tare da juyawa yana fad'in
"Na dai fad'a miki,kar kuma na dawo na sameki...
Da kallo ta bishi har ya kulle zauren.
Gudar su Lami ce ta sanya ta dawo da kallonta gare su.
Murmushi tayi musu tare da shigewa d'aki jin suna fad'in
"Y'ar gaban goshi yau sai a kara mai,a tafi tafiya ta har abada...
Ido ta sake rintsewa tare da sakar kuka.
"Allahumma ajirni fi musibati...
Ranar tayi kuka har sai da taji ba dad'i, karshe ta hau tattare abin amfaninta na waje tana kaiwa d'aki.
D'anta ta dakko wanda y'ar Lami ta mangareshi ya fad'i yana kuka.
Goyashi tayi tare da yafa mayafi ta sawa kofarta kuba ta rufe.
Har ta bar gidan su Tabawa basu bar yin dariya ba da ya6a mata habaici.
Da daddare har shago Babanta ya samo Malam Isubu kan zuwan Rukayya gida ba laifi inji ta.
A wulakance suka rabu da dattijon,dan gar da gar ya ce shi koh sunan Rukayya bai kaunar ji,dan haka yama sauwaka mata kar a dameshi.
Jiki a sanyaye ya dawo musu da bayani.
"Duk yadda akayi yaron nan ba a hankalinshi yake ba Inno, dan ba haka Isubu yake ba sam,ya sauya.
Shiru tayi tana kallon Rukayya dake hawaye.
"Kin tabbatar ba wani abu ki ka mishi ba koh Ru..
"Dan Allah Inno ya isa,koma meye yafa sauwaka mata,toh mubar tone-tone kawai.
Shiru tayi tare da bashi hak'uri.
Wannan ne silar barin Rukayya gidan Malam Isubu.
*****
Tunani yake duk da surutun da Lami take shatata mishi ba koh shan numfashi.
"In har tunani na yai dai-dai toh a watan nan Yaron nan Kabir ya shekara biyu koh Lami?
Ras taji gabanta ya fad'i, amma sai ta wayence tare da fad'in
"Hakane Malam,mey ya faru?
Tashi yai tare da barin cin abincin
"D'ana zan kar6o a gunta ne,nasan iyanzu kam an yaye shi,bazan iya rayuwa babu shi kusa ba..
Baki sake ta bishi da kallo har ya fuce ya bata guri.
Kwafa tayi tare da girgiza kai.
"Tabawa..
Kira ta kwalla mata, dan haka a yatsine ta amsa dan tuni an dawo gidan jiya tun fuskantar da kowa ya yi yana zagawa shi kad'ai wajen mai yankan wuka.
"Meye?.
Tsaki tayi tare da fad'in
"Malama in zaki shigo ki shigo,dan wallahi wuta bata mutu ba a gidan nan.
D'akin ta shigo dan jin ba'asi, dan haka tuni ta kora mata bayani.
"Yanzu ma nasan chan ya nufa,dan koh abinci bai gama ci ba ya tsame hannunshi.
Tsam Tabawan tayi
"Ni fa na zata tunda muka binne kwalbar nan zai manta ta har d'anta ashe ba haka abin yake ba.
Baki ta ta6e,
"Atoh,in ma zamu manta komai mu tashi tsaye toh,in ba haka ba ya kar6o yaron nan da sannu zai maido da uwar ma.
"Kin manta sun kwashe kaya ne?
"Tabawa baki san meye so ba ne.
***
"Kiyi hak'uri Rukayya kar ya tara mana mutanen unguwa kawai ki bashi yaron nan.
Sake kank'ame Kabir din tayi tana girgiza wa Inno kai cikin kuka
"Ni nasan muguntar gidan ne Inno, ina nan ma ya aka k'are bare sun san ba idona...
Kuka ta sake saka tana ita dai ko mey zaiyi bazata bayar ba.
A tunzure Babban ya shigo rai 6ace.
"Ki wuce ki kai mishi yaron nan tun kamin na sa6a miki Rukayya..
Kai ta dago cikin tsoro ganin Baban a haka,bata jin ta ta6a ganinshi haka,dan haka tuni ta mike jiki na ka'rkarwa rike da Kabir shima da ya fara kuka yana kiran Umma.
A duhu ne,amma duk da haka yana jin kukanta yai saurin dauke kai daga gareta yana huci.
Duk da a zahiri ji yake tamkar ya lallaso Rukayyanshi amma wani abu ya hana.
"Dan Allah Malam kayi hak'uri ka bar min Kabir nai alkawarin kaishi kullum shago...
"Bana so,d'ana kawai nake so.
Ba yadda ta iya,dole ta mika mishi Kabir ganin Babanta ya fito.
Kuka take Kabir nayi ganin ana nema a rabashi da Umman shi a cikin daren,kam ya riketa yana janshi yaro na rike Umman shi.
Dan haushin Rukayyan da sauri ya fincikoshi tare da had'owa da gyalenta a hannuKabir da kamar ya shid'e gun kiran
"Umma.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
15_Gaba d'aya suka bi jaririn da ya fad'o da kallo tamkar wanda aka hankad'o shi daga cikin,sai dai da halamun baya motsi.
Cike da murna Lami ta kallo Tabawa tare da nuna mata jaririn da baki halamun aikin su ya yi kyau.
"Saura mabiya Lami,dakko muciya,koh kuma muje daga nan na duba yaran nan shiru daga kiran Malam,sannu Rukayya.
Hannun Lami ta kamo sukai waje cikin murna.
Ido ta sa yaron,ganin baya motsi yasa ta kai hannu tare da dan ta6awa.
Ido ta rintse sai ga nan hawaye na malala,shikenan shima ya tafi.
Hannu ta bata tare da tafawa,cikin rad'a-rad'a ta ce
"Kai wallahi Lami ba ki da imani.
Dariya ta sa tare da itama da fad'in
"Har na kai ki?
Dariya suka kara sawa.
"Ni fa badan-badan ba wallahi itama mu karasata tabi jaririn kawai tunda kinga bazata lafa ba a gaba ma namiji zata sake haiho wa.
Kai ta kad'a, dan haka katuwar mociya ta dakko tare da rike hannun Lamin suka koma d'akin.
Kukanta kawai take duk da kwa irin azabar da take ji dan wahalar data sha.
Da ido tabi su ba wani guntun karfi a gareta.
"Riketa mu fito da mabiyar kar tai mata illa.
Da sauri Tabawa ta bawa Lami muciyar tare da yin baya da zummar rike ta.
"Bud'e bakin?
Kallonsu kawai take ta kasa koh motsin hanawa.
"Kinga Tabawa bud'e min bakin ki ga.
Ba musu ta dakarkare tare da wage bakin Rukayyan tun karfi Lami ta turmutsa muciyar ciki tana tura wa.
Yunkurin amai take numfashinta na sama amma Lami na sake tusawa har wani cije hakora take dan mugunta.
"Innalillahi... Lami?
Gaba d'aya suka juya tare da sakin Rukayyan ita kuma ta zare muciyar.
"Kasheta ku ke so kuyi koh mey?
Harara Lamin ta sau mata,yadda ta tsani Raliya haka ta tsani mutuwar ta.
Ledar hannunta ta mika wa yarinyar da suka zo da ita tare da cire gyalenta taci damara dashi cikin sauri ta tutsu cikin d'akin.
A hankali ta zaro mabiyar tana ta yi ma Rukayyan sannu.
Tsaki Lami taja tare da hullar da muciyar ta fita waje dan haka da sauri Tabawa tabi bayanta.
Dago Rukayyan tayi wacce sai maida numfashi take dan azaba,kai ubangiji ya rabamu da rashin imani.
Harda hawayenta dan tausayi.
"Taya zaki yarda su Lami su karbi haihuwar ki da hankalin ki?
Kuka tasa tana mai nuna mata yaron dake shinfid'e a kasa,da sauri ta juya tare da ganinshi,bacin mabiya da ta iya fidda wa ba abinda ta sani,shima an koya mata ne dan gudun haihuwar gida ba kowa.
"Ummilo..
Yarinyar da suka zo ta kwalla wa kira.
Zata shigo ta ce ta tsaya,tai gudu ta kira Marka ingozoma makociyarta.
Duk da ta fidda rai a yaron amma hakan bai hana tasa Raliya d'aura shi a zani ba daga kishingid'en ta ruko abinta.
Wajen ta fara gyara wa tana mai tir da halin mugunta.
"Yauwa Marka bissmillah..
shigo wa tayi harda y'ar jakarta mai d'auke da sabin reza da zare.
"Au,ki ce har an haihun ma Raliya?
Kai ta daga tare da fad'in
"Duba mana yaron nan Marka dan Allah.
Hannu Markan ta kai zata karbi yaron sai Rukayyan ta girgiza mata kai tare da fad'in
"Ya mutu fa Marka.
"Eh duk da haka bata dai ta duba mugani dan kamar kirjinshi na bugawa...
Kai ta kad'a tare da mika mata ba dan wai ta yarda da zancen Raliya ba.
Kai ta kawar da sauri ganin yadda Marka ta tashi tsaye ta rike kafar yaron duk biyu ta yadda kanshi na kallon kasa tana dan dukan bayanshi kad'an.
Ido ta rintse,har cikin ranta ji take kamar Marka ita take bugu, dan haka tuni ta fara kuka tana fad'in
"Marka ki bari,
"Ki bari dan Allah..
Ganin taki daina wa yasa da dan karfi ta ce
"Dan sonki da Allah Marka ki bar dukanshi haka,yafa mut..
Jin muryar kukan jaririn ciki-ciki muryarshi a dan shake ne yasa tai shiru tare da kallonsu.
Da sauri Markan ta juyo da yaron dai-dai tana dariya ita da Raliya,ganin haka yasa itama sakar ajiyar zuciya tare da kara sakar kuka.
"Inaga yasha wahala ne gurin fita har gashi yasha ruwa,tabbas gwara da aka duba da munbi ta taki shikenan.
"Bari ki ga,dole na zuko ruwan nan da ya sha,Raliya bani abu kusa da abin kuskure baki.
Waje Raliya tayi tare da yin yadda Marka ta ce.
****
"Kai wannan shegiyar Raliyal wallahi Lami ta kwafsa mana,kila da tuni mun fasa kuka biyu yanzu.
Kwafa Lami tayi,
"Ki bari kawai,tunda munyi nasarar wannan ma d'an ya tafi da sauki sai musan nayi daga...
"Inyaaaaa....
"Ke yi shiru Lami kamar kukan jariri nake ji..
Tsaki tayi tare da gyara zama
"Wane jariri kuma a gidan nan?
Kai ta kad'a
"Sai dai a makota wan..
"Inyaaa...
Wani kukan suka saka ji wanda yasa Lami yin shiru tare da kasa kunne cikin zaro ido suna kallon juna.
A zabure suka mike har suna gware.
Samu sukai Marka na zuko ruwan kad'an-kad'an wanda hakan ke sa yake wage murya wajen ihun murya ta bud'e.
Chak suka tsaya tare da zubawa jaririn ido wanda ke bud'e hannuwa yana sake chanyara kuka tun karfinshi.
Duk kallonsu suke yadda suka kame,baki Raliya ta ta6e tare da sanya hannu bisa hanci tare da sakar bud'a iya karfinta.
Lami ce ta fara juyawa, tukunna Tabawa ta d'aura a bayanta.
Hannu tasa bisa ka da nufin kwalla ihu da sauri Tabawa tasa hannunta tare da damke bakin tun karfi.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
18_Kukan Kabir ne yasa su yin shiru tare da fito wa a d'akin Lami cike da al'ajabi.
"Kai shiru Kabiru, daga yau damu zaka saba..
Tabawa ce ta kalli Lami cikin hasken farin wata,da sauri Lamin ta ta6e mata tare da daga kafad'a.
"Ba dai Malam da gaske kar6o yaron nan kayi da tsohon daren nan ba?
Harara ya sau mata,
"Laifi ne dan na kar6o koh mey?
Kai ta girgiza da sauri,zatai magana Tabawa ta riga ta
"A'a ba haka take nufi ba,kawai dai sai muka ga kamar bai kamata ka amsa ba sai ka bar mata ya girma chan wajenta.
A tunzure ya ce
"Banyi ra'ayi ba toh,na dawo dashi in zaku rike min shi toh,in baza ku iya ba zan kaishi chan Rano a min rainon shi.
Da sauri Lami ta zungureta ganin zata sake magana.
"A'a Malam baza ayi haka ba muna gidan nan..
Karasawa tayi tare da mika hannu.
"Kawo shi ya zauna cikin y'an uwanshi zancen Rano bai taso ba.
Kafad'a Kabir ya make halamun bazai je ba yana cigaba da kukan shi cikin jan zuciya.
"A'a kyaleshi muga zuwa gobe,in zan fita sai na barshi da ku a hankali zai saba da kowa.
Waje ya koma dashi sai kuwa yai shiru a zatan shi gun Umman zai maidashi dan yaga sunzo layin ga gidan yana hango shi.
Shago ya bud'e mishi tare da dakko mishi biscuit mai ya'ya, hularwa ya yi tare da kara sanya kuka yana fad'in Umma har lokacin yana nan rike da gyalen tamau a hannu.
"Toh yi shiru zan kai kaji Kabir?
Ajiyar zuciya ya fara,sai a lokacin ya kula da gyalen hannunshi.
Kar6a ya yi a hankali tare da jefa shi cikin shagon yana tsuka,ganin haka yaro ya sake sakar wani kukan yana nuna mishi gyalen Umman.
Shagon ya rufe tare da komawa dashi gida,tuni ya kara jinyar kukan shi ganin an dawo gidan da ba na Umman ba.
Kalloshi yake yadda yake jan ajiyar zuciya cikin bacci.
Fitilar kwai ya matso da ita yana mai kare mishi kallo,kamar su d'aya dashi,sai dan abinda ba'a rasa ba na mahaifiyarshi.
A gefenshi ya kwanta,yau dai d'aya yaji d'umin yaron shi mafi sauyuwa cikin ranshi.
Washegari har yazo fita shago bai tashi a bacci ba dan rashin yin bacci da wuri jiya.
Jin ya kira Lami ne yasa ya fara motsi.
"Ni zan fita,dan Allah in ya tashi a bashi abinci shima,naga kuma ya yi fitsari.
Kai ta kad'a kamar gaske.
"Toh a dawo lafi...
"Au,kaga ma ya farka.
Kallo Kabir din yai wanda yasa musu ido daga kwancen kamar yana tuno inda yake.
Murmushi yai mishi tare da isa gurinshi ya shafa kanshi ya fuce.
Yunkurin tashi yake yana ta6e baki halamun zaiyi kuka,harara Lami ta sau mishi tare da karasa wa gareshi.
Kai ta dungure mishi tare da jan kunnenshi tun karfi da sauri ya saki wata razananniyar kara.
D'akin yaran gidan suka nufa jin kukan Kabir din kowacce baki duk koko da maikon kosai a hannu sunyi dumu-dumu.
"Kamar kai ka sakar min fitsari a katifa dan iya shege.
Tabawa ce itama ta shigo,ba imani gaba d'aya suka hau ja mishi kunne iya karfi da nuna tsana.
Shid'ewar da ya fara ne yasa suka sarara mishi tare da fitarshi tsakar gida.
Lalle da wuya na kisa da a dan kwana biyu zata kashe Kabir.
A gaban Malam kowa nannan yake dashi kamar su had'iye, yana bada baya su hau mishi mugunta daga su har yaran, karamar yarinyar Lami kad'ai ke tausaya mishi,sai dai bata da wayon da zata hana.
Sau tari yakan dawo ya riski yaron na kuka koh ajiyar zuciya ta in yaci mugunta,da yai magana sai suce sam har yau yaki ya saba dasu,kowa ya daukeshi sai kuka.
Amma fa shi in ya daukeshi zaiyi shiru ajikinshi har yai bacci.
Abinci kuwa tare za'a had'a mishi da yayyenshi gaba daya,wani sa'in kamin yai kwakkwaran loma biyu sun kwakwashe,sai dai ranar ya wuni kukan yunwa, su kuma su wuni dukanshi kan sai ya rufe musu baki yai shiru.
Kan aje ko'ina yaro duk ya rame yai baki,sam bazaka zata Kabir bane fari mai kyau da sumar kai.
Gaba daya koh bacci yake shi kad'ai zai dinga razana shi kad'ai.
****
Wasan kasa yaran suke yana kallonsu daga gefe ya zauna yai tsiru shi kad'ai tamkar maraya marar gata yai duku-duku dashi.
Tsaye take tana karewa gidan kallo,kowa yana harkarshi cikin walwala da sakin jiki cikin gata banda shi.
Sallama take shirin yi sai ta dakata ganin da jan jiki ya isa wajen yaran dake wasan kasa da zummar ai dashi.
Dagowar da Indo zatai y'ar Lami ta biyu ta ganshi a gun ta sau mishi harara tare da daka mishi
"Dalla matsa daga wajen mu shege kawai..
Mari ta kai mishi tare tureshi tun karfinta yai baya tare da fad'uwa yana kuka.
Su Lami ta kallo,sarai sun juyo sun gani,maimakon taga suyi magana sai ma dariya da suka saka tare da d'auke kai daga gare su.
Hawaye ne ya zubo mata na tsabar tausayin Kabir,a hankali ta karasa shiga ba tare da tai sallamar ba,dan a ganinta daga su har yaran ba wanda ya chan-chanci amancinta.
Dagoshi tayi tana mai kad'e mishi jiki tana bashi hak'uri.
Da harara suka bita har ta fuce dashi sa6e akafad'a.
''Munafuka kawai.
Baki Lami ta ta6e,
"Ke ta isheki kallo ma,ni fa na fara gajiya da bautawa d'an nan Tabawa,a kullum ta duniya ji nake ina kara tsanar yaron wallahi.
"Ki bari kawai Lami,wuya ma kad'ai ta ishe shi karasa wa a gidan nan,dan wallahi baki fini tsanar yaron ba.
Ranar a gidan Raliya ya wuni tai mishi wanka,a ranar yaci mai kyau,sai ga Kabir ya ware suna wasa da Uzairu d'anta.
Dan haka da Ummilo yarinyar makotansu ta mayarshi da kuka suka rabe, dan yasan ya dawo gidan azaba.
****
"Ya ki ka tarar shi da ki ka je Umman Uzairu?
Murmushi ta k'akalo tare da fad'in
"Lafiya lau,a nan ma ya yini.
Shiru tayi tare da sauke ajiyar zuciya.
"Ya rame koh?
Da sauri Raliya ta girgiza kai.
"Ba wata rama da ya yi fa Umman Kabir,ki kwantar da hankalin ki.
Murmushi tayi hawaye har ya taru a idonta.
"Ba gaskiya bane wannan Umman Uzairu, kina so ne kawai ki kwantar min da hankali, amma a yadda nake mafarkin yaron kullum nasan ba kalau yake ba,ina ji ajikina.
Shiru Raliyan tayi,tasan kawai ta fad'a ne,amma ba wanda zai ce Kabir yana lafiya koh da kuwa makotansu Tabawa ne,sai dai kowa na tsoron su ba mai ta6a yi musu fad'an basu kyautawa Kabir.
Dan haka sai ta dafata tare da fad'in
"Kiyi ta sa shi cikin adu'ar ki Umman Kabir,InshaAllah ina ji a jikina a gaba Kabir zai zama wani ni,a yanzu dai dole kiji,ki kuma ki ji, ki gani ki kau da kai.
"Ki sa a ranki wuya bata ta6a kisa,InshaAllah Allah zai kare miki shi a duk inda yake.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
20_Washegari tun asuba ya tashi dan himma,gaba d'aya ya gama cika ruwan gidan yai shara tukunna ya shiga ya watsa ruwa ba koh sabulu.
Kallonshi Abban yake yadda yake tattare gidan cikin sauri kamar kullum.
Suna had'a ido ya dauke kai,har kasa ya tsuguna tare da mishi ina kwana,kai kawai ya kad'a tare da fita da sauri.
Duk da har akasan ranshi ji yake tamkar ya ce yaje ya kwanta kamar kowa ya huta,sai dai bai isa ba.
Kok'arin fita yake sai ganan Tabawa da sauri ta fito har tana tuntu6e
"Wato kamanta dukan da kasha jiya koh?
Kasa yai da kai.
Kubar kofar zauren tasa tare da kullewa,
"Yau zanga karyar taurin kai.
Binta yai da kallo ido fal hawaye,samu yai ya zauna dan ya rasa na yi,ga sai karar mota da babura yake ji wanda shi ke nuna mishi lokacin makaranta ya yi.
Yau dan mugunta dan ma kar ya fita ba yaron da ya fito siyan kosai duk dan kar yaje makaranta.
Tashi ya yi ganin turmi,duk da katangar kasar bata da tsayi sosai amma shi nashi tsayin bazai kai ba.
Dan haka turmin yasa tare da danewa ya haura ta katangar.
Ba karamin ciwo yaji ba a gwiwa, amma dake abinda rai ke so ne shi koh ajikinshi haka ya tafi gidan su Uzairu yana dingishi.
Har kullum Umman Uzairu na mamakin son makaranta irinta Kabir.
Gyara mishi ciwon tayi tare da bashi uniform yasa ta zuba musu abinci suka ci harda zuba musu na tara.
Da suka dawo sai wai wayen masu gini yake yi yadda suke jidar kasa suna mikawa na sama yana laftawa.
"Kabir,
Juyo wa ya yi jin muryar Ahmad
"Mu tafi man ka tsaya.
Wuce wa sukai amma tunanin masu gini yana a kasan ranshi.
Kasa shiga gidan ya yi bayan yaje ya sauya kayanshi a gidan Umman Uzairu, haka kawai ta raya mishi yaje wajen masu gini.
Kallon yadda suke,dan haka sai ya karasa wajen mai bada umarnin.
"Nima zan iya...
Wai wayo wa ya yi,sai dai ganin Kabir da bai ma fi shekara 7 ba sai abin ya bashi dariya.
"Haba yaro, wane kai wannan aikin sai dai kai wasa dai...
Shiru ya yi ganin Kabir din ya wuce tare da daukar kwa6a66iyar kasar da aka fara zubawa ya daga yana nishi ya daura a kai shi kad'ai.
Gaba d'aya baki suka saka suna kallon yaron,lalle sa kai wai yafi bauta ciwo.
Dan haka mutumin baida bakin hana Kabir,sai dai yasa ana zuba mishi rabi yana mikawa.
Ganin washegari gari ma ya dawo shi da Ahmad, sai ya ce a'a sai yaga Babansu tukunna.
Dan haka ba musu ya kaishi gun Abba,bai samu matsala ba,dan take ya ce ai jikinshi ne.
A kwana biyar har ya saba kullum sai yazo dan Ahmad fur babanshi ya hana shi,yau aka gama gini dan haka sai kirgo kud'i y'an sile-sile ya bashi.
"Ga kud'in aikin ka Kabiru,ka burgeni sosai,ina matukar son yaro mai zuciya.
Kallon kud'in yake yana washe baki,
"Na gode,in za'a sake ma zan zo har inda ka ce ka ke.
Da gudu ya nufi gidan Umman Uzairu yana murna yau an bashi kud'in aiki.
Kallonshi take cike da mamaki,lalle wani abu sai Kabir,
"Umma ki ajiye min har na tara dashi zan dinga siyan littafi na siya mana gida na siyawa Umma ma.
Fara'arta ce ta yawaita, har ba tasan hawaye ya tarar mata ba.
"Allah yasa Kabir,Allah ya amsa.
Murmushi ya yi tare da kallon Uzairu da ya shigo.
"Ka ga ka ki zuwa gashi har an bani kud'in aiki.
Da sauri Uzairu ya ce
"Wai Umma?
Nuna mishi tayi tana musu dariya.
"Ai Umma Uzairu rago ne bazai iya ba wai.
Kai Uzairu ya kad'a
"Tab,naje kaina ya lo6a,kai dai kaje kai tayi ni bazan iya b...
Shiru ya yi jin sallamar Umman Kabir.
Da sauri Kabir din ya juya tare da isa wajenta da gudu.
Hawaye ya fara kamar kullum in ya ganta,yau ba labarin gidan su Tabawa sai labarin aikin da ya yi aka bashi kud'i.
"Umma nuna wa Ummata ta gani.
Ajiyar zuciya ta saka,lalle bata isa dakushe Kabir ba,sai dai a ganinta yai kankanta da aikin gini.
"Toh Kabir Allah yasa kafi haka.
Baki washe,sai Uzairu ya ce
"Amin zaka ce.
Kai ya kad'a tare da fad'in
"Amin toh Umma.
Tsarabar da ta kawo ta basu,cikin murna harda kayan sallah da littafi da pencil harda jakar makaranta ta buhu shi da Uzairu.
"Na gode Umman Uzairu, ubangiji ya baki lada,ina farin ciki idan nazo gidan nan naga Kabir a farin ciki.
"A kullum bani da adu'a sai ta Allahu l ya taimake shi da sauran yaran musulmai.
Murmushi tayi.
"Yi wa kaine ai Umman Kabir,kema kina ta fama da kan ki ya kamata ki hakura da fita haka tunda kin kusa haihuwa.
Kai ta kad'a
"Kamar kin san akan zuwa gun Kabir yau ma sai da muka kai ruwa rana da Malam,na rasa mey Kabir ya tsare mishi fur yaki jinin na ce zani gunshi.
Murmushi Raliya tayi.
"Ki bishi a hankali kin san maza kila yadda ki ke zata ba haka bane.
Kai ta girgiza,
"Kishi kawai yake da Kabir nake gani.
Baki tai ta bata har dai ta gamsu ta bar maganar.
****
Yau Jumma'a,su Kabir har an shiga primary 3, da wuri aka taso su dan ganin jiya nad'ar da yaci ta tsayawa a gun masu gini yasa yau ya wuto gida yana cire kayanshi.
Shigarshi ke da wuya duk suna tsakar gida har yaran.
Indo ke gaban rijiya tana diban ruwa,yayin da Hafsa ke wanke-wanken kayanta.
''Yauwa,zo ka karasa min dan wahala.
Kallota ya yi,sai dai ya karasa tare da kar6ar gugar hannun nata.
"Kabiru wai makarantar da dad'i ne?
Hafsa ya kallo ganin ita ce sai ya saki jiki.
"Eh,ni kinga yanzu har ajina uku Allah Hafsa ki shiga.
Kai ta kad'a tana mishi murmushi.
"Ni da ban iya komai ba Kabir.
Ruwa ya zuba yana kok'arin bata amsa yaji Lami na duka mata tsawa.
Shiru tayi rai a jagule, sai dai tsugunawar da zaiyi yaji an kwada mishi abu a gadan baya.
Dagowa ya yi dan azaba yaga Indo na kok'arin kwad'a mishi ice
"Ni zan saka abu ka tsaya yin fira?
Kai ya kad'a tare da kok'arin kaucewa ya manta da bayanshi rijiya ce.
Taga-taga yai zai fad'a da sauri ya dafa Indo,tuni gabanshi ya fara fad'uwa ganin bai fad'a ba.
"Lalle ma yaron nan?
"Toh mey ki ke jira dashi da ya rike ki?
Kallo Lamin suka yi,da ka ta nuna mata halamun ta hankad'a shi,batai wata-wata ba kuwa iya karfinta ta hankad'a shi.
Kai ya buga tare da sakar ihu da karfi ya kank'ame gugar da Allah yasa a kulle take.
Ahmad da yazo nemashi yaga abinda ake neman yi wa abokinshi sai ya juya da gudu shagon Abban su Kabir din.
Hafsa yake kira ganin yadda kafafunshi ke cikin rijiya hannunshi rike da igiyar guga,ga nan inda ya bige har ya fara jini.
Da gudu ta rike gugar ta waje tana kiranshi.
Daga yaran har iyayen dariya suke mishi har wacce ta hankad'a din.
Ganin Hafsa na kok'arin ciro shi yasa su Tabawa suka taso tare da kok'arin kunce igiyar suna ihu shi da Hafsa akan kar su hullashi.
Dukan hannunta Lami take tana fad'in
"Idan baki cika ba wallahi zan hulla ku tare.
Kai take girgiza musu
"Wallahi Lami mutuwa zaiyi, ku taimake shi kar ku kunce.
Guga taki kuntuwa dan haka da sauri Tabawa ta dakko wuka,tuni makota suka lelleko ta katanga masu iya bada hak'uri suna yi amma iya karfin su suke yanka igiyar suna dariyar mugunta.
"Da wannan basirar tazo mana ai da tuni ka manta da fad'a shege mai taurin rai...
"Hafsa...Hafsa dan Allah,dan Allah ki janyo ni...
Bata da cikiken karfin janyoshi,dan tamau Lami ta riketa tana ji tana gani suka sau igiyar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 19