Share this page
Kabir yana ihu yana komai suka tsunduma shi. "Wayyo Kabir Lami,dan Allah ki cikani na tsamo shi... Lafiyyen mari ta dauketa dashi tare janyeta a gun gaba d'aya suka juya da zummar barin bakin rijiyar sai sukai poster. Ahmad suka gani tare Abban su Kabir sun shigo a sukwane. Kan suyi kwakkwaran motsi har shima ya karasa jin Hafsa na Kabir ne a rijiya Abba ya tsunduma kanshi cikin ba koh gargada. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 21_A kansu gaba daya aka raja'a dan cecen ransu wanda dakyar aka samu masu hakan rijiya da karafan unguwa suka fiddo su kank'ame da Kabir duk sunji ciwo. "Ban san da mey zan kira abin nan ba likita,abu daya na sani kawai ku yarda tsautsayi ne. Abban Uzairu likita ya kalla tare da kad'a kai. "Allah rufa asiri toh,amma tabbas sunyi mummunar buguwa, barin ma uban,dan shi yaron sai nake ga tamkar ma wanda aka sanya shi ciki intentionally. "Dan in ka duba gaba d'ayan shi ya tafi in banda ciwo da yaji keya, wannan kuma baida alaka da fad'awa rijiya dan direct ya shige. Ajiyar zuciya likitan ya yi tare da fad'in "Any way,a barshi a tsautsayin,amma gaba asa ido. ****** "Kiyi hak'uri Umman Kabir, mu kuma gode Allah da ya cece su. Hawaye ta goge tare da kad'a kai tana kallon gefen Abban Kabir din dasu Tabawa da sai kuka suke. Ta sani a duk rintsi dama baza'a rasa burbushin kauna ta Allah acikin kowacce rai ba,balle kuma iyaye. Bata ta6a zatan Malam zai iya sadaukar da ranshi ga d'anta d'aya tilo ba. Kai ta d'auke tare da goge hawaye... "Hafsa...Hafsa...dan Allah ki janyo ni kar ki bari su jefa ni... Gaba d'aya d'akin suka juyo tare da kallon Kabir dake ihu farkawar shi kenan ido a rufe. Kai Umman ta dago tare da kallon gefen su Lami da sukai saurin mikewa. "Na sani wallahi, na sani jefa Kabir akai da gangan dan na samu labari a bakin Ahmad... Hannu Umman Kabir tasa ta rufe ma Umman Uzairu baki tana girgiza kai. Daya bayan daya suka fara zamewa suna barin dakin ganin Kabir din ya bud'e ido. "Sannu Kabir,Allah ya kara cecen ka. Ido ya sa ma Umman Uzairu mai magana, kamin ya jiyo kan Ummanshi,suna had'a ido ya saki kuka. "Yi shiru Kabir,yi hak'uri. "Umma su Tabawa ne suka kashe ni fa... Duk kuka suka sa har shi jin maganarshi cikin shesshekar kuka. Kanshi ta shafo tana girgiza yarinyar bayanta. Umman Uzairu ce bashi amsa "Basu kashe ka ba Kabir,baka mutu ba.. "InshaAllah Allah na tare da kai. Umman yake kallo,dan haka da sauri ta kad'a mishi kai halamun haka ne. Labari ya fara basu suna kuka yana yi,wannan irin rashin imani har ina? Tsam Umma tayi, Tabbas a duniya bata da makiya sama dasu Lami,amma dole hakkinta ne ta sanya Kabir binsu da y'an uwanshi. Ta sani da wata rana sai labari,wata rana koh an ce suyi baza suyi ba. Lalle yanzu ta dau hanya bisa ga rayuwar Kabir,tana kuma rokon Allah yasa Kabir shi zai nuna wa su Lami Aya. Har aka sallame su kala Abban Kabir bai ce ba,hakan ne yasa suka gane tabbas shirin mai yankan wuka har yanzu yana rike da Malam. Sai dai daga wannan rana da abu ya faru Allah ya yaye wa Kabir duk wani digon tsoro nasu acikin rai. Daga ranar ya daina duk wani aikin bauta cikin gidan a ciki kuwa harda diban ruwa a rijiya. In zasu kwan dukanshi ci kanku bazai ce ba,dan tuni in da sabo yaci ya saba,zuciya har ta kekashe. In kuwa a yaran gida ne sai inda karfinshi ya kare daga kan Indo har kasa. Dan haka tanan ba karamin y'anci ya kwata ba,dan sai ya zamo gaba daya yaran na shayinshi,dan in ta fagen fad'a ne toh da duk'kan karfinshi ya ke aika musu duka. Matsalar kafa Malam ya samu,dan haka sai da dingishi yake iya tafiya. Yanzu abin ya zama sai gaba yake sake yi a harkar rayuwar gidanshi,shi ya zama matan, yayin da su Lami suka zama shi,duk abinda da suka ce akan Kabir,toh fa shi zai aikata. **** Yau da gobe sai Allah,ga nan Kabir an zana jarawar karshe ta primary cike da nasara. Gun aikin gini kuwa tuni shima ya zama kwararre,dan ba abinda zasu sa shi bazai iya ba,dan haka tuni ya zama yana samu sosai ta hanyar gini. K'ak'karfa ne,dan tun kan aje ko'ina jikinshi har ya fara murd'ewa,sam in ka ganshi ba ka ce Kabir bane dan shekara goma sha uku. "Umman Uzairu... Umma.. "Kira suke maka mata cike da murna su uku. Fito wa tayi tana amsawa rike da hannun Halima wacce ke kukan bacci. "Mun dawo,har mun rubuta.. Baki ta washe tare da fad'in "A lalle mashaAllah, ubangiji yasa an gama a sa'a. Baki suka had'a tare da fad'in "Amin "yanzun sai ta sakandere koh? Kai Kabir ya kad'a cikin farin ciki. "Eh Umma,Jss1 zamu tafi kuma. Kai ta jinjina. Halima ya kallo wacce ke mishi dariya,dan haka da sauri ya karasa tare da cire alawa yasan ita takewa ya mika mata. "Ka ganta tun dazun ta dameni da bacci,na kwantarta nan kuma ta ki. Kumatun ta yaja cikin wasa,alawa na baki ta fara bangala mishi dariya. "Yauwa,kema ki girma a saki a makaranta koh Halima? Kai ta kyad'a kamar ta gane mey yake nufi. "Ubangiji ya taimaka. Murmushi yai,kamin ya ce "Anjima zani gun Umma ma na sanarta. Murmushi tayi suka fita shi da Ahmad. "Yanzu Kabir in munci boarding ya zamuyi? Murmushi Kabir din ya yi "Ni ina son boarding Ahmad,sai dai koh na fad'a wa Abba ba kulani zai ba,ga Abban Uzairu nasan baya son boarding da muguntar wai da ake,kuma da kud'i ma dan ni da Uzairu ne,ni kuma wanda na tara ba yawa dan dashi na biya na wannan jarabawar. Kai Ahmad ya jinjina. "Sai mun had'u anjima. Gida ya shiga yana daga ma Ahmad kai halamun toh. *** "Abba takaddarmu ce ta gama primary zamu shiga secondary mun samu day,ma'ana ta jeka ka dawo. Kai Abban ya juyar mishi dashi,kawai bai son yaga Kabir na ra6arshi,wani irin haushin yaron yake ji. Jin shiru yasa ya sunkuyar da kai,bai san abinda yasa sam Abba ya tsaneshi ba. Su Tabawa dake sauraro ta janyo Lami d'aki. "Jiya a gidan Tasallah ina jin irin muguntar da danta yake fad'a ana yi a makarantar kwana,yaron duk rauni jikinshi ina ji yana cewa ta jeka ka dawo zai koma shi dan wahalar ta kwana. Tsam Lami tayi "Toh mey ki ke so ayi? Gyara zama tayi "Yauwa,mey zai hana mu sanya baki a aika wanchan gawa taki ramin a lallasa mana shi achan? Dariya suka sa harda tafawa. "Eh lalle yau Tabawa kin kawo shawara. Bakin kofar Hafsa ta bari da sauri jin zasu fito. Baki har kunne suka isa wajen Malam,Kabir yana ganin su yasan za'a mishi wata tsiyar. Dan haka tashi ya yi jiki ba kwari zai bar wajen yaji sunce "A zauna man Kabir.. Baki sake yake kallon su,sai ya kallo Hafsa dake girgiza mishi kai halamun yace bai yarda ba. Yadda suke murmushin shi yasa yasan da mugunta suka zo. "Amm Malam. Kallosu ya yi yana amsa wa. "Mey zai hana ka kai Kabir din makarantar kwana tunda naga yana da son karatun zamanin. Cike da mamaki Abba da Kabir din suke kallonsu. "Eh wallahi Malam a kaishi,mun goyi baya... "Kabir.. Da dan hankali Hafsa ta kira shi,ganin yadda take girgiza kai yasa Lami ta mako mata harara. Sai yai murmushi tare da zama,tsam ya karanci abinda suke nufi,dan haka jin Abba ya yarda sai ya musu godiya. Hararar shi Hafsa tayi bayan ta biyo shi waje sai yai mata murmushi "Kai baka san tarko aka d'ana maka ina ta cewa kace baka yarda ba amma sai da ka amince. Murmushi ya yi tare da kad'a mata kai "Kar ki damu Hafsa,ba abinda zai faru,nima ina son boarding,kawai dai ki dage kema ki fara karatu koh primary 2 a saki tunda kin iya abinda nake koya miki. Kai girgiza, "gaskiya nai girma yanzu da makaranta,shekarata 15 fa Kabir. Rai ya had'e "Wa ya fad'a miki? Akwai wanda suka fiki Allah kar ki biyewa su Indo kiyi ta yawon tallar nan Hafsa. Kai ta kad'a mishi, "Toh zan fad'awa Abba,koh Abban su Uzairu. Da taimakon Abban su Ahmad su Kabir suka samu gurbi a makarantar kwana ta boy's and girl's,shi kam Uzairu fur ya ce sai Day,da wannan abotar Ahmad da Kabir ta kara kulluwa. Sai ga su Tabawa harda tara mishi kanzo su a dole wuya zata kashe Kabiru a boarding. Da murmushi kawai yake bin su,dan duk ya gano shirin su a kanshi. "Umma gobe zamu tafi ki min adu'a. Murmushi Umman tayi "Adu'a kullum ina kan yi maka Kabir,ubangiji yasa aje a sa'a, amma ni sam ba dan ka nace ba bana kaunar makarantar kwana dan yadda ake fad'in muguntar su. Dariya ya yi bawa Nafisa abinci ta dan cije shi tana dariya. Hannu ya yarfe yana mai kallonta. "Tafiya zanyi naga wanda zaki na cizo kullum in ya zo. Dariya tayi. "Ina zaka Yaya? Kallon su Umman take,tun yanzu zaka gano kaunar juna ta y'an uwan taka a tare da yaran musamman Nafisa da Kabir. "Makaranta zan tafi Nafi, sai na jima zan dawo. Kuka take neman yi ya hau lallashi,ita ta wa zai na kawo mata alewa take. Da zai tafi Umman ta dakko mishi abinda ta mishi. "Gashi Kabir,ubangiji yasa a fara a sa'a,ka kula da amana kawai da karatun ka. Kai ya kad'a yana duben abin, "Kai Umma na gode, kamar kinsan bani da kayan y'an gayu su cabin da peak,sabulu ma duk bakud'in nawa ya tafi a littafai da jaka da sabin kaya. "Dan ma wannan karan Abba yai min uniform har biyu da akwati.. Murmushi tayi tana kad'a kai "Allah ya cigaba da ganar shi,a kullum kai ta sa shi a adu'a kar kaga laifinshi. Kai ya kad'a "InshaAllah Umma,bari na biya gidan Inno kar na amsa quarry dan I know her. Murmushi Umma tayi,tana jin dad'i taji Kabir na d'an yaren turawan nan. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 22_Da dad'i ba dad'i haka Kabir da Ahmad suke daurewa har suka ci karfin karatun su. Ganin ba abinda ya ragu jikin Kabir sai ma waye wa da kara kyau da yake shi yasa suka sanya Abba cire hannu a karatun Kabir,ba musu ya daina cin kwandalarshi,yanzu kam kud'i ba matsala ba ce sai dan abinda ba'a rasa ba,dan a kanshi Ummanshi ta fara dinki. Da duk karfinta take neman kud'i dan cika burin d'anta na yin karatu mai zurfi. Sosai harkar gini take kai mishi har ya samu ya tallafawa Abbanshi da yanzu kasuwar bata kai mishi,sai dai har ya bashi abinda zai bashi bazai ce mishi kanzil ba. Da ya kaiwa Umma kukan shi magana d'aya ce "Kai hak'uri, watarana sai labari... Har ga Allah ya gaji da zuwan watarana d'in nan da har yanzu bata zo ba. Sun gama secondary cikin nasara da kyaututtuka na yabo ga Kabir masu tarin yawa. Kowa yai murna dan har gida makota suke zuwa ganin kyauta da a unguwa ya zama zakaran kwajin dafi. A ranar su Tabawa sunyi da na sanin aika Kabir boarding, a ganin su banda nasara ba wata wahala da yaci achan,tai ma Tabawa Allah wadai da wannan shawara gashi ya zama d'a tamkar da dubu. Shekarunshi goma sha tara,dogo ne mey kirar karfafa, a yanzu kamaninshi sunfi fito wa na sak da Abba. Fari da sumar kai kawai ya lakato na Umma dake da jinsi na fulani. Zai wuya ka ce bai kai 25 ba a lokacin dan sam bai d'aukar wargi,dan gayu ne mai ci da guminshi har ya tallafa. In dai zai samu,toh burinshi ya wadata ran mutum uku, Ummanshi, gidan su Uzairu ,sai kuwa Abanshi in ka had'a Hafsa,sauran kam tun Umma nayi har ta hakura ta zuba ido,dan in ba ta dalilin Abba ba yadda ya tsani *MATAN UBA* ba mai cin kwandalarshi. **** "Kiyi magana cikin na uban waye... Baki ta turo tana guna-guni,Kabir da ya shigo yai tsaye jin zancen cikin Indon. Shiru sukai tare da zuba mishi ido. Tamkar kabewar dake kan kabari ne shi a yanzu a idonsu wai bakin cikin mai taushe. Handsome, matashin yaro mai ci da kuruciyar shi. Kallonshi kad'ai a garesu babbar aya ce dake sa suyi shiru. Dan haka baki kowa yaja ya tsuke har ya shige inda nan ne d'akin shi na Ummanshi na da. Tsam ya yi cike da mamaki,a ganinshi wannan ai ba abin tada hankali bane dan Indo ta kara ciki. Shi shaida ne yadda samari har a cikin zaure yasha kicibis dasu suna lalume Indo. Sannan in bazai manta ba yasha jin an kama Indo da wani a rufar kasuwa ba so d'aya ba ba biyu ba... Sam ya rasa dalilin da ya kasa jin tausayin Indo a cikin ranshi sai tsanar su. A kullum in ya rintse ido yakan tuna hankad'a shi rijiya da tayi ne tana dariya. Hmm,abin da aka gasa kam wai shi ya ga wuta. Ajiyar zuciya ya yi tare da fad'in "Allah ya kyauta. "Kabir"... Kofa aka kwankwasa. Amsawa ya yi tare da tashi ya bud'e mata jin muryar Hafsa. Murmushi yai mata tare da bata waje ta shigo. Murmushi ita ma tayi tare da zama. "Ya akayi sisto? Murmushi ta sake yi tare da girgiza kai,jin tayi shiru yasa ya zauna kusa da ita yasan da magana. "Uhmm. "Aure nake son yi nai nisa da gidan nan da bakin cikin cikin shi Kabir,bazai yu na zauna barikin gidan nan tabi ta kaina ba Allah... Kuka tasa tana mai tir da halin y'an uwanta. "It's Ok.. Lallashinta ya fara. "Yunus dama ya matsa ya turo ina ki,dan ina tunanin karatuna dana fara. Kai ya kad'a "Banki taki ba,amma zanso ki tuntu6i Yunus akan cigaban karatun ki,Jss2 ki ke. "Koh ni a kullum burina kiyi nisa da dabi'ar y'an matan gidan nan, ki bi Allah ki rike mutuncinki,auren Allah sa shi yafi alkairi, amma zanso ki idda makaranta koh kina gidan miji. Kai ta kad'a. "Zan tuntu6e shi,koh kuma kasa baki naga yana yaba mutuncinka a gidan nan. Kai ya kad'a. "InshaAllah zanyi kok'ari. Taje kai ya yi yana fesa turare. "Yanzu sai ina? Murmushi ya yi tare da fad'in "Gidan Umma zani,tukunna zan biya naga budurwa ta Halima. Dariya suka sa suna kok'arin fita, "Wannan had'in Allah sa ya tabbata. D'aki ya datse yana fad'in "Amin sisto. "Bye.. Hannu ta daga mishi tare da fad'in "Ok,bye.. Yana fita kusan gidan gaba daya suka d'au tsaki. "Tusa kai ba kwarjini, wallahi kinji asara marar kishin y'an gidan nan. Kallo su tayi tare da Indo mai magana. ''Ji da abinda ke a gaban ki,dan asara ke ki ka ganta... Shiru tayi ganin ta zaburo zata nufe ta. "Wallahi kar ki kuskura ki shafan kazamin jikin nan da yaga maza turum... "Ki kiyayeni Hafsa wallahi. Tsaki Hafsan tayi tare da jan mayafinta ta fuce, "Asara kawai,yawun bacci. Kwafa Indo ta kuma yi tare da koma wa, In da sabo ta saba da yadda Hafsa ke wanke su musamman in sun dawo a bariki. In dai zasu kawo toh ta ciki mai sauki ne,yanzu za'a hararrameka in ka fad'i waye uban a hau lalarsa daga baya su murtsike cikin. **** "Nan A.B.U nake hari Umma InshaAllah. Kai ta kad'a "Allahu ya taimaka Kabir,ga dan uwanka(Uzairu) ya ce shi ba rana wai sana'a zai fara. Kai ya kad'a "Hakan ma yana da kyau,a hankali zaiyi ne. Tsakar gida ya kalla ganin Fatima a zaune. "Yau banga budurwar ba Halima. Murmushi tayi tare da fad'in zaka ganta bada jimawa ba.. Sallamarta ne yasa suka dubi waje gaba d'aya. Daga yanayinta zaka gane ranta a dagule yake,sai dai tana yin arba da Kabir ta sau fuska tare da sunkuyar da kai tana murmushi. "Uhmm,budurwata kinyi kyau fa. Hannu tasa ta rufe fuska bakin nan yasha kan ta kile. Dariya Umma tai musu tana kad'a kai jin tsokanar Kabir din. "Toh ni kam Umma haka za ai auren kullum ana kunshe min ido. D'akin su ta nufa tana dariya,ita har ga Allah da gaske kunyar Kabir take. Gidan Umma ya nufa duk da yana d'ari-d'arin zuwa,dan tun girmanshi suke y'ar tsama da mijin Umman. Wai komai na Umma a Kabir yake karewa,maimakon ta kula mishi da yaranshi. Duk murna suke na ganin shi musamman Nafisa ta zama y'an mata y'ar gayu. *** Da taimakon Umma da kud'in gini ya bi Ahmad suka samu kurbi a jami'a inda ya zabi bangaren zane koh dan gini wanda zanensu shine burinshi yayin da Ahmad ya zabi bangaren kasuwanci. Anyi auren Hafsa inda aka kaita Zamfara. Bayan wuya kam sai dad'i,gashi yanzu har sun kammala. Aminin Abban su ne ya bashi yarinyarshi Ahmad ya aura,kamin su gama akai rikicin auren kan matar bata sonshi, da dad'i ba dad'i har ta samu ciki,da wannan aure ya mutu ta auri mai sonta,haushin wannan yasa sirikin Ahmad din ya fanshe wa Ahmad da kanwarta Sumayya Umman su Farida. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 23_"In har zakuji ta tawa toh da kun daina wahalar da kan ku a wannan yaron yanzu kuyi ta yaran nan su samu mazan aure Tabawa,kullum sake dakko muku magana suke amma ku ta abu daya ku ke kullum ba nasara.. Lami ta kallo jin bayanin Tasallah,kuma fa da gaskiyar ta,dan duk wata kadarar su a Kabir ta kare na ya ta6e yaro sai gaba yake. "Nima ina jin bakin cikin abin nan fa Lami,mu rabu da yaron nan kawai Mai yankan wuka ya hau aikin su Indo yaje chan ya karata. Da wannan suka ajiye makamen su akan Kabir na asiri,tunda sun san yanzu kam Kabir sai kallo daga nesa. **** Kai ya taje,shi kad'ai kawai ya tashi da wani farin ciki tun mafarkin Halima da ya yi tana mishi y'ar kunyar nan. Ya sani da a da kam da gaske wasa yake,amma yanzu tabbas yasan yai nisa cikin son Halimatu,dan haka yau wankan nata ne. Gidan ya shiga tana a tsakar gida ta daga madubi tana ta kallon gefe da gefen fuskarta cikin fari irin na masu iya yi. Kallonta yake,matuka abin ya fara bashi dariya,ganin yadda ta dage tana tsatso kyanta a madubi. "Oh ni Raliya,yanzu Halima har yau kwalliyar nan bata kare ba? Madubin ta ajiye tana ma Umman "Nayi kyau? Kai ta girgiza,tare da niyar juya wa ta kula da Kabir a bakin kofa. Magana take shirin yai mata halamun tai shiru zai shigo,Halima ta kalla wacce ta cigaba kyalinta,sai ta girgiza kai tare da yin ciki. Waka ta dan fara rera wa tana dan rufe ido kamar wai tana jin kunya. _'Kalaman juyan baya_ _'da kayi su sai naji kunya'_ _'Akan kwa bana sanya ka hu_... Shiru tayi tare da waro ido ganin yadda ya hard'e hannu yana mata murmushi, juya wa tayi da sauri tare da rintse ido cikin kunya,tabbas tasan ya jima a nan wajen. Tashi tayi tana gyara gyalenta cikin satar kallonshi,ganin yana takowa yasa tai saurin sadda kai kasa tana murmushi tare da fad'in "Ya Kabir.. Shiru ya yi bai amsa ba,dan haka sai ta dago a hankali. Madubin ya dauka yana dan gwada yadda tayi cikin tsokana. Kau da kai tayi tana dan dariyar kunya,akanta kam shi zai komai in Halima zatai murmushin kunyar nan. "Nayi kyau? Gyale tasa ta rufe fuskarta wai ita a dole kunya. Kai Umma ta kad'a da ta fito, "Na rasa ina zata tafi awa a zaune kyali,ashe saurayin ne zai zo zance. Kai ya girgiza,lokaci ya yi da za'a ajiye zancen wasa,amma bari ya fara ta Ummanshi yaji. "Dama gun Umma zani,tunda bata wajen zuwa ni kam Umma ki ara min ita ta rakani,amma ta sanya nikabi tunda kwalliyar tawa ce.. "Umma nima zani.. Kallo shi sukai Khalifa da ya shigo dan autan su Halima. Dariya Umman tayi "A ba ruwana, kunfi kusa,a gaida min Umman da kyau,amma Halifa da kai hak'uri.. "A'a Umma,yazo muje dashi karin dan rakiya. Duk sabon su da juna a yau sai kallo sai murmushi, tamkar wasu masoyan nan masu kunyar juna. "Matar... Kai ta kawar jin sunan da yake kiranta tun yarinta tana murmushi. "Uhmm. Kai ya kad'a. "Ni fa na shirya,koh yau a daura mana aure.. Dariya ta dan sa,a zatan ta har yanzun wasan ne.. Sai dai jin har a gaban Umma yana fad'in shi fa tare zasu koma Kaduna in zai fara aiki yasa ta hau kunya. Ya Kabir a kullum shine mafarkinta,shine burinta tun zamanin yarinta. Zata iya cewa daga tausayin rayuwarshi ya rikid'e ya koma 'so' sannu a hankali. A kullum burinta ta aure shi koh dan share mishi hawayen da su Tabawa suka dasa mishi. Tana fatan tai silar dai daituwar lamarinshi shi da Abba. Abu kamar wasa a hankali magana ta zama babba,kowa yai na'am da had'in, duk a lokacin ba wata babba bace daga ita har Fatima, amma aka sanya su lalle sai Kaduna. Rayuwar aure suke mai cike da so da tattalin juna. Halima mai matukar hak'uri ce da k'au da kai,hakan yasa zai wuya ka ga sun sa6a,kullum cikin farin ciki yake har takan mantashi rayuwar gidan su Tabawa har suka samu Saifu. A wannan lokacin ne Abban su Farida aka aikashi Jigawa,silar rabuwar shi da Abokin shi Kabir sai daga baya ya dawo Kano. ***** "Sai fa kana yi kana manta baya kamin zaka iya daure wa kai musu wani abin Abban Saifu. Murmushi ya yi tare da kwantar da Saifu. "In na ce zan iya manta abin da kwasa a gidan nan Halima ba mai yuwa bane. "Naga rayuwa duk da nasan kin riski wani abin wani kuma sai labari. "Maman Saifu har yau ina neman wanda yasha irin azabar da na gani gun *MATAN UBA* amma banga ba. "Dani da Abba har yau dinnan sai kallo daga nesa,tun tashi na ban san tararrayar mahaifi ba sai tsana karara. Da yai ta tuno wa Haliman na hawaye wani abin ma sai yau taji,a ranar ta kara tsorata ga sha'anin *MATAN UBA*.. Tamkar karamin yaro haka yake mata kuka yana tuna mata da baida kamar su Lami a sahun makiya. Nata hawayen ta shanye tare da janyoshi gareta. "Abban Saifu gashi yanzu sai labari,ka yafe musu tunda a kalla suna ganin Aya akan su Indo. Murmushi ya yi tare da girgiza kai. "Zan yafe musu duk randa suka tabbatar min da zasuyi abu daya,wanda na tabbatar baza su iya ba,sai dai su dauwama da zunubi. Kai ta kad'a, kamin a hankali ta janye maganar suka dawo wata. "Ni na fa matsu da auren nan na Nafisa yazo mu tafi. Murmushi ya yi. "Toh ku auren da ba amarya ma ina zaiyi dad'i. Dariya tayi tare da kad'a kai. "Yaki hak'uri a gama biki su tafi ba,ni fa sam bana son American nan yaya gani nake kamar mutum in ya zauna zai dau al'adar su. Kai ya girgiza mata, "Toh ya za ayi,kinsan Nafisa kuwa yadda take ji da wannan mijin dan zasu zauna a America? Dariya suka sa tare da girgiza kai "Nafisa gidan fafu,chan karyar zata karu. Dariya sukai yana kad'a kai. Har cikin ranshi yasan zaiyi missing Nafisa y'ar kanwarshi tsoka d'aya cikin miya. Bayan sun dawo a bikin Nafisa ya jona masters nashi Zaria. Sau biyu su Tabawa na kwata zuwa ana katari baya gari,dan haka sai yadda sukai da Halima haka zata cika su da sha tara ta arziki amma babu gwaninta,daga karshe har gida yaje yai musu kashedi kar ya kara ganin kafarsu a garin Kaduna. A hankali yai ta samun bud'i da dad'i babu dad'i suna zaune da Halimenshi da yaran su,har kawo lokacin da mutuwa tai musu yankan kauna. Yaso ya jiyarda Halima dad'i dan a ganinshi tare sukaci zamanin wuya,ga nan dad'i yazo babu ita. **** *WAIWAYE*... "Abba wai Aunty Fatima ta dawo? Saifu ya kallo tare da cire farin glass din idonshi. Kai ya kad'a mishi, "You know.. Ba wai ita zaku duba ba,ku duba Maman Saifu sai mu mata afuwa. Shiru sukai suna duben shi. "Amma Abba bazata dawo ba koh? Murmushi yai tare da saurin kad'a kai "Ta tafi har abada,yanzu ni ne Mama,ni ne Abba.. Fuska suka washe harda dariya dan murna banda Saifu. Kallo Saifun ya yi ganin yadda ya zuba TV ido,tvn ya kalla,sauran ma duk sun maida hankali gun film din 'Cinderella' Rai Saifu ya had'a tare da fad'in "I seriously hate them.. Da sauri Nass ya ce "Step-Moms ba? Kalli Cinderella.. Dan tsaki ya yi yana kara volume. Jiki a sanyaye ya kalle su,da gaske kuma suke,dan a haka ji suke kamar su shiga suje su mak'ure step mom na Cinderella. Amjad ya kallo jin ya ce shima "Me too.. Jingina ya yi tare da kallon su,tabbas sai ya yi da gaske,dan karara yake ganin kin *MATAN UBA* a idon yaran shi sama dashi kanshi. In har ka cire Sultana da shan hannu ke a gabanta tana musu dariya. Tun daga ranar suka zama y'an lele,abinda suke so shi za ayi,mace kuwa koh ta office suka ga tana yage wa Abban su baki yanzu zasu hau hararar ta suna Abban yazo su tafi. Ya sani da koh dan lafiyar yaranshi zai hak'ure da rayuwar aure,dan gaba daya ya tsorata da lamarin auren duk da jiki da jini sai a hankali. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 24_"Wayyo dad'i, dama ni ce wallahi Ummahani. Harar ta tayi. "Dallah,dan baki san meye auren bane,dan wallahi ni dai karatu nake so... Hawaye Umma Hanin ta goge,ita kam sai fad'i take dama ita ce. "Ke baki da wayo,da ni ce? Kai ta kad'a "Tuni na yarda. Lissafi ta fara mata. "In fa za'a miki aure ke y'ar gata ce. "Kinga gadon ki ma ke dai za'a siya miki,a siya miki kayan kitchen, TV,kujeru,ga kayan lefe duk ke kad'ai, kije kiyi ta abinci kina share gidanki ki fesa turare.. Tsaki Ummahanin tayi jin yadda Farida ke kara bata haushi,sauran kam marasa wayo y'an uwanta sai fad'in "Eh man,ai bata da wayo,koh ni ce yarda zanyi Allah. Tashi tayi ta bar musu wajen ganin baza su gane ba. Ita kam

Chapter 6 of 19