Share this page
sake kallowa, lalle hasashenshi na dangantata da Halima bai fad'i ba,dan yasan d'aya ce tamkar da dubu koh a yara sai an tona. A hankali ya sau ajiyar zuciya tare da furta "Bravo Farida...Bravo alaiki wa Jazakillah... Hmmm. Lalle *Tuna baya shine roko*. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 47_Tsaye yake a bakin gate na makaranta ya zuba ma gate din ido. Murmushi yake ganin yadda suka sanyata a tsakiya kowa kok'ari yake ya bata labari suna dariya. Sosai ta sake fito mishi cikin uniform din wanda yasha shan tela (shape) da hijab iya kafad'a. Duk yaran sun fita haske,amma a yau gani yai ta fisu haska wa barin na in tai murmushin nan. Kai ya d'auke daga kallonta ganin sun karaso kusa. Yau da gobe kam a gareshi wai ta wuci wasa,ya yi surrender,ya kuma amshi lalle ya kamu da so a karo na biyu. Kalloshi tayi bayan sun shiga tana mishi murmushi ganin idonshi kir a kanta. Wayan cewa yai tare da kallo su Saifu yana tambayar su karatu. Murmushi tayi tare da kallon hanya kawai. Da nacin Nasir Abbanta ya ce ya yarda ai auren amma ya kasance wani term,zo ka ga murna gun Laila da Alhajinta kamar mai auren farko. "Hajiyata soyayya tayi a rayuwa,kar kiji yadda nake ji na a sama dan kulawar Baby.. Dariya Faridan ta sau, "Wollah in kince babyn nan ba karamin dariya yake ban ba.. Ina ma laifin Alhaji.. Hararar ta tayi tana tsuke fuska. "An fad'a miki mu irin ku ne? Hararar ta rama tare da fad'in "Meye damu? Kafad'a ta daga.. "Kiyi kallo yarinya,in nai gaba zaki biyo bayana ne,a soyayya ba fulako mud'in da so Hajiyata.. "Ya kirani Baby na kirashi Baby,meye aciki? Duk acikin so ne.. Tsam tayi tana tunanin zancen Laila,tabbas tayi iya kok'arinta ganin Uncle ya sota amma abin ya faskara.. Dafata Laila tayi, "Ni na saki kuka? Kallota tayi da sauri,hannu ta kai bisa kuncinta jin damshin hawaye. Murmushi tayi tare da girgiza kai "Koh kad'an, ba ke bane... Hannunta ta ruko. "Toh waye? Kuka ta sa mata ba k'ak'kautawa, dan haka tuni ta rud'e ta hau lallashi. "Ni sai dai naga ana ta so amma ni banda ni ba dole nai kuka ba,Uncle bai sona Laila.. Tsam Lailan tayi. "Wa ya fad'a miki? Believe me, yana sonki sosai. Murmushi tayi tana goge kwalla. "Fad'a kawai ki ke,amma ke kanki kin shaida baya min duk yadda Alhaji Nasir yake miki a gaban ko ma waye, a ganina shi ne so mai cike da tsantsar kulawa.. Hannun Lailan ta kamo. "A da bana damu wa Laila,amma yanzu ina damuwa in har naga irin naku salon,matuka yana burgeni, nakan ji ina ma zan samu koh rabin hakan gurin Uncle.. Kai ta girgiza, "Nasan bani da ranar samu,dan yadda yake nuna kula a su Saifu haka yake min,babu wani dan maganar soyayyar nan in a romantic way fa Laila. "Ni yadda na fuskanta kusan dani da mai dawainiya da gidanshi duk d'aya nake,sassanyan kalam nashi fa shine 'Farida,sannu da aiki.. 'Farida kin tashi lafiya? 'Farida na gode.. Murmushi tayi, "Ina jin ciwo,amma ban sanar wa da kowa ba hatta Umma,ke ma zance ne ta ratso kawai na furta.. Rungumota tayi cike da tausayin kawar tata ta fara lallashi. "It's ok.. Bayan ta nutsu ta fara fad'in "Amma fa baby yasha fad'a min Uncle na matukar sonki Farida,har yakan ce naku salon na burgeshi sau tari in yazo tad'i.. Murmushi tayi tare da girgiza kai. "Hmm,fad'a kawai ki ke,dan ranar chan na gama tabbatar wa bana gaban Uncle. "Har d'aki fa na kai mishi shekaran jaka jiya da ruwa amma Uncle yana gama sha kin san mey ya ce? Kai ta girgiza tana kallonta. Kwafa tayi tare da kad'a kai. "Wai na gode Halima.. Ido Laila ta zaro "Wace ce haka? Baki Faridan ta ta6e.. "Momyn fa su Saifu.. Dariya Laila ta sa.. "Toh meye ba ta mutu ba? Harararta tayi tana turo baki. "Eh amma ta bar mishi sonta har yanzun, ranar fa yana bacci yana ta sururunta dan so.. Dariya sosai Laila tayi, wanda har yasa ta kule,Allah bata jin tana da tsananin kishin Uncle sai ranar da ya kirata da Halima.. "I love him wollah Laila,har mafarkinshi nake,amma ki duba shi ta machacciya ma yake ba ni ba. Da kalar tausayi ta karasa tana duk'ar da kai. Kamin Laila tai magana an kwankwasa d'akin.. Uncle ne,dan haka tuni taji bata son tashi. Ido ya kura mata ganin yadda take k'auda gefe tabbas halamu ya nuna tai kuka. "Ga nan Nasir yazo.. Kai ta gyad'a kawai,dan haka cike da mamaki ya juya. Tare suka fito duk suna zaune a parlourn har Uncle. Ido ya sawa Faridan ganin taki kalloshi suna gaisawa da Nasir. "Baby nah... Kasa Laila tai da kai ganin Uncle tana murmushi. Duk ido suka sa musu daga Farida har Uncle din ganin yadda Nasir ke kashe Love a gabanshi. "Jiya d'aya amma na kasa sukuni har sai yanzun da nai arba fa,amma ke kamar ma ba kiyi missing na ba fa My sugar... Uncle Farida ta kallo ba koh kiftawa wanda ya sau baki yana kallon Nasir,tabbas yasan da biyu yake,sai dai suna had'a ido da Farida yai saurin yake mata hak'ora. Kitchen ta wuce bayan ta yake mishi nata kamar ta d'aura hannu a kai ta sau ihu.. Tashi yai yana hararar Nasir dake mishi dariyar keta yai kitchen, dan haka da sauri ya dawo kujerar kusa da Laila aka hau tad'in soyayya ba ruwan su. Ruwa take jera wa faranti ya shigo kitchen din dan haka sai tai tsam jin kamshin turarenshi. Tako wa yai tare da isa wurin da take ya tsaya tare da tayata dakko kofuna. A dan sace ta kalloshi idonshi bisa kanta. So yake ya tambayi mey ke damunta amma ya kasa. "Sannu da aiki.. Sosai ta kalloshi ido cikin ido,wannan shi ne kawai kalmar da zai fad'a mata? Kai ta d'auke cike da takaici tana kad'a mishi kai. Farantin zata d'auka sai ya rike halamun zai d'auka. Hannun nashi ta sawa ido jinsu bisa nata tare da sake kalloshi. Dan janye wa yai bayan ya kula yana fad'in "Oh! Sorry.. Kar6a yai tare da fita bishi da kallo,plates da serving spoon Laila ta shigo tare da ruk'unk'umota ta baya cikin murna. Tare suka fita su Uncle har sun isa dining suka isa dan zuba musu. Kallota ya yi, "Ku kunci ne? Kai ta kad'a halamun eh. Da sauri Nasir ya amshe. "Laila bata ci ba,dan haka ku zauna sai nafi ma ci in ina kallonta. Murmushi Faridan tayi,a zahiri ba suci ba dan ta su Saifu take su ci su tafi islamiya. Nasir zata zuba wa ya girgiza kai "A'a bani na fara zuba wa Baby da kaina ku kuci naku.. Galala Uncle ke kallonshi ganin wannan rawar kan abokin nashi yana dan kallon Farida. Dai-dai da ruwa in Laila zata dauka tuni zaiyi sauri ya mika mata cike da kulawa suna ma juna murmushin so. Kasa Farida tai da kai sai chakalar abincin take da chokali ta kasa ci. D'aki ta kule dan takaici bayan ya tafi rakasu. Kan ta farga har hawaye ya hau sintiri bisa kuncinta. Iyanzu tana da muradin taga ana gwada mata so irin na Laila,amma bata tunanin zata samu. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 49_Murmushi ya yi tare da kai hannu bisa lallen yana fad'in "Oh,sorry,ya zugin? Kasa ta zamo tana murmushin kunya tare da kad'a kai halamun ya daina tana mai jawo abinci ganin lokaci yana ta sake ja. "Abinci Uncle kar ya huce.. Sakkowa ya yi yana jijjiga kai tare da zama a gabanta baki ya ki rufuwa. "Ni fa yunwar ma bana ji tun kiran Abba na farko da batun nan a karo na biyu. Kai girgiza tana mai bud'e plate din tana murmushi, "Ni zan fara fesawa Aunty Hafsa a waya kuwa gobe in Allah ya nuna. Murmushi ya yi yana mey kallon agogo. "Nasan yanzu Feenah sun tashi,bari na riga ki.. Murmushi tayi tare da debo abincin a chokali ta mika mishi bisa hannunshi halamun ya kama lokacin da yake sauraron ringing na wayar. Wayar ya nuno mata tare da nuno bak'inshi halamun ta sa mishi jin Feenah ta d'auka. A sannu take bashi a baki kamar wani yaron goye yana fesa wa Feenah labari cikin murna. Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai tana sake debo wani tare da mika mishi,bazata ce ga a yanayin da take ciki ba a yau. Abu d'aya ta sani shine tana jin wani shaukin so da kaunar Uncle ta ko'ina bisa 6argo da jinin jikinta,dan haka abincin ma a da style take bashi tamkar mai tsoron kar ya kware. Dariya ya saka jin iskancin Feenah bayan da ya bud'e baki ya amshi wata lomar yana jijjiga kai halamun ya gode. Murmushi tayi tare da sake debo wani dankwalinta na neman fita sai ta cire ta ajiye gefe tare da dagowa zata bashi ya kware. Ido ta zaro tare da saurin ajiye chokalin ta hau tsiyayo ruwa tana mishi sannu,tarin ya dan sassauta tare da bud'e baki idonshi bisa kanta tana bashi ruwan bayan ta dan kara tsayinta kad'an daga tsugune. "Uhmm..uhmm Gyaran muryar Feenah ne cikin waya yasa ya gano ya bar mutum. Baki yai saurin cire wa a kofin yana fad'in "I'm sorry.. Ita dai bata san mey suke fad'i ba taji dai kawai ya ce "Abinci ne" yana kallonta yana dariya. Famfon bayi ta wanko hannunta tare da sake zama jin har yanzun wayar bata kare ba ta fara cire nama tana ware k'ashi gefe. "Uhmm.. "Of course.. "I see.. Kawai yake fad'i a takaice yana kallon Faridan. Murmushi tayi tare da mika mishi naman bisa baki ba musu ya bud'e tare da amsa. Lumshe ido tai tana mai yin murmushin jin sautin dariyar tashi ita kad'ai ta isa ta sata a nutsuwa. Kai ta dago zata mika mishi taga yana duba wa halamun kud'i ya yanke. Ido ya zuba mata a hankali ya bud'e bakin ta sanya mishi yana dubenta. Plate din ta turo mishi halamun ya karasa tunda ya gama tana murmushi. Da sauri ya girgiza kai tare da nuna mata hannunshi halamun ba wanki. Bakin ya bud'e mata halamun ta cigaba da bashi da kanta. Murmushi tayi cikin kunya tare da yin kasa da kai tana bashi a hakan kai duk'e. Yatsun ya riko tare da kai naman baki yana kallon lallen,jin hakan yasa ta dago tana dubanshi. Baki ya kara kaiwa ya bud'e kamar zai cijeta tai saurin rintse ido tana murmushi,murmushin shima ya yi tare da zamewa ya kwantar da kanshi bisa cinyarta. Idon ta bud'e tare da sauke su bisa fuskarshi,lalle ne ba sai an sanarta yana a farin ciki ba yau,koh kuwa ya manta a inda yake. Dan haka kai ta k'auda tare da murmushin kunya jin hannunta bisa bak'inshi. Tad'i yake mata,wanda aksar na Ummanshi ne da Abban shi sai kuwa yarintarshi. Kamin su farga har lokaci ya ja ba kad'an ba wajen saurarenshi. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 48_Shirye-shiyen bikin su Laila suke,dan haka duk sun shiga busy ganin term ya kusa karewa. A gidan Uncle kam yanzu hatta yara sun fara fahimtar akwai wata a kasa. Dan rimi-rimi suna a cikin walwala da yai mistake na koh suna ne yanzu zasu kasa gane kan Faridan. Tun abin bai damun Uncle har ya fara kulewa da sabon halin Farida. Haka kawai shi ba wai da gangan bane yake danganta ta da Halima,ya rasa dalilin da yasa a yanzu komanta in tayi sai yaga kamar irin na Halima ne, a nan toh zai sa6a suna sai a samu matsala,karshe sai su Saifu zasuyi mishi sasanci. *** "Koh ni bana tunanin nayi irin d'aukin nan naki fa Laila.. Murmushi tayi tana duben lallen da ake tsantsara musu. "Ba zaki gane ba,duk da ina jin fargaba amma ina a farin cikin zama ta Baby Allah kuwa gobe. Dariya sukai,kai Faridan ta kad'a. "Ina tausaya miki Maman Nurr, kar tai miki sallama da luguden kin kwace mata Baby.. Dariya suka sake sawa harda tafawa. "Allah nima ina dan tsoron matar,dan sam bata da fara'a,dad'in ki d'aya an raba mazauni sai kashe love lafiya. Fari tai idonta tana murmushi, ''Ki bari kawai Hajiyata,har na haskoni wollah.. Kai Faridan ta girgiza tana cije le6e na mugunta. "Zaki tsara,wallahi za ki yi bayani ne muna gefe.. Harararta tayi, "Wa ya fad'a miki kowa ma irin ki ne? Kai Faridan ta dungure mata tare da fad'in "I see,muna nan ai. Sun had'e sosai,ga gyaran jiki ga lalle. Tun dazun suka je saloon wash&set tunda sun sa mai. Sai dare kusan tara ya d'akko ta a gidan Auntyn su Lailan sai cije le6e take wai farcenta zafi inda lalle ya shiga tana yarfe hannu. Parking yai chan gefe tare da kunna fitilar cikin motar yana mamakin raki irin na Farida. "Ina ne? Hannu biyun gaba d'aya ta nuno mishi tana shisshitu. Iya dubenshi shi baiga komai ba sai kyakkyawan bakin zanen da yasha jan rani. Kamar wacce aka mintsina haka ta dan zabura jin zugi tana shisshitu kamar wacce taci yaji tare da marairaice fuska tana duban hannun. Hura mata ya fara da iskar dake bakinshi yana fad'in sannu a hankali. Shiru ta danyi tare da zuba mishi ido yadda ya rirrike hannun nata yana hura su tuni sai ta kama tasha tana murmushi. D'agowa ya yi jin shiru,suna had'a ido tai saurin fad'in "Ahh,shhhh zafi.. Hurawar ya cigaba da yi sai kwa tai shiru suna duban juna cikin murmushi,a dan jima ta hau shisshitu yana fad'in sannu. Mota ya tada duk da haka hannun yana bisa fuskarshi yana dan fiffitawa. Murmushi take tare da dunbenshi cikin sassanyan kallo,sosai take jin dad'in nuna kulawar Uncle a yau. Juyo wa ya yi ya dan dubeta da sauri ta d'auke kai "Ya daina? D'ayan hannun ta bashi wanda ta hau yarfe wa dan shakiyanci tana fad'in "Wannan ma.. Murmushi ya yi mai cike da sauti yana kallon hanya tare da hura wanda ta bashi. "Gayu da wuya,but i like it dan yai kyau. Ido ta sa mishi tana murmushi, jin tai shiru yasa ya kallota cike da jin dad'i, a hankali ta janye hannun daga nashi cikin kunya tana sissinke kai tana murmushi ganin sunzo gida. Kallota ya yi shima yana murmushin, lalle yau da halamun an manta da y'ar mitsila ake tare hala? Horn yai yana mai kunna fitilar motar tare da yin baya ya jingina a kujerar kan a bud'e tana dubenta kasa-kasa. Sarai ta kula,dan haka fur taki kalloshi har aka bud'e gate sai ya kad'a kai yana murmushi. Duk daga parlour suka fito suna tutturo baki ga halamun Sultana tasha kuka. "Oh,i'm sorry Sultantee,rungumota tayi ganin ta saka sanya kukan tana fad'in sai jiranta take bata dawo ba ta d'auka ta 6ata ne.. Dariya suka sa har uncle din "Allah Aunty Farida na dad'i kin fa jima ga kukan Sultana. Kallo Saifun tayi tana sake basu hak'uri. "Ban san zamu jima ba haka nima duk fa na gaji nai kewar ku yau kawai. Da kallo ya bisu ganin sunbi bayanta tana sa6e da Sultana a baya ba ma wanda yake ta tashi wato Farida da ce tasu yanzun. Kai ya kad'a yana murmushi, jin dad'in yaranshi tabbas nashi ne,dan haka yake kara jin Faridan a chan kasan ranshi a kullum barin ma dai yau. Bayan su ya bi,a parlour ya tarar su Sultana na shafa gashin da yasha wanki sai kyalli yake tana fad'in yai kyau suna mata dariya. Sosai kam yai kyau gashi ya kara tsayi sai walwali yake anyi baya dashi. "Mu fa yunwa muke ji mun kasa ci tun dazun muna jiran ki. Ido ta waro, "Haba Saifu,kuma in ban dawo ba fa koh bana nan ba fa kyau jira... Ido suka sa mata har uncle din "Ina zaki? Ganin yadda suka zira mata ido yasa tai saurin gyara zancen. "No ina nufin in nai tafiya fa. Kai su ka kad'a, "Ai tare muke tafiya ma. Yake tayi tana jijjiga kai halamun haka ne. Tashi Uncle din ya yi jin ana mishi waya ya ciro a aljihu. 'Uzairu'. Daga wa yai tare da sallama suka gaisa,sanarshi yai ya kira Abba shi zai tafi gida ne za suyi magana. Tashi yai yana mai kiran Abban yana musu halamun su ci kamin ya dawo. Shiru Uncle din bai dawo ba har yaran suka tashi ta kai Sultana ta kwanta bai zo yaci abinci ba. Har zata wuce itama d'aki sai ta kasa,haka kawai ta raya mata ta kai mishi in yaso ta duba koh lafiya. Kwankwasa wa tai,jin ya ce yes yasa ta dan tura a hankali rike da faranti mai d'auke da plate da ruwa da cup. A hankali ta ajiye tare da kok'arin fita ganin yana waya sai yai mata da hannu halamun ta tsaya. "Umma.. Shiru yaji,dan haka sai ya sake karyar da murya. "Amincewar ki kawai muke bid'a Umma wannan karan dan Allah ki cika min burin nan.. Shiru ya yi tare da daina fara'r da yake jin kukan Umman, dan haka da sauri ya fara bata hak'uri. "Umma ban san zai 6ata miki ba dan Allah kar ki min haka zamu hak'ura har Abban,amma ki daina kuka.. "Na amince ne Kabir, wannan ne ya sani kuka ba komai ba,ubangiji yasa ai damu.. Zirif ya mike cike da farin ciki ya toshe baki,kamin ya farga har hawaye ya zubar mishi. Adu'ar da yake kwararowa Umman ne yasa Farida gano akan mey ake wayar dan haka tuni itama ta doka tsalle ta dire tare da isa ga inda yake cikin murna. Wayar ya sauke,kamin Faridan ta ankara cilak ya dagata sama yana sanarta Ummanshi ta yarda zata koma wa Abbanshi. Kai ta gyad'a mishi tana sanarshi ta fahimta suna dariya cike farin ciki. Sauketa ya yi tare da ruko hannunta ya zaunarta bakin gado shima ya zauna. "Na fi kowa farin ciki a yau Farida da naga wannan ranar da su Umma zasu sake zama a inuwa guda,ina a farin ciki. Kai ta gyad'a mishi itama bakinta yaki rufuwa. "Nima Uncle nai farin ciki sosai,tun ranar da Aunty Feenah ta bani tarihin rayuwar ka da tasu Umma nake da burin naga sun koma tunda mijinta ya rasu,nasan Abba zai sake sonka a yau su Tabawa sai su mutu. Ido ya sa mata yana murmushin jin dad'i, kamin ta farga har rungumota dan murna suna dariya,tuni aka ture batun kunya murna ta mirtsiketa. Sosai ya yake murnar dan haka ba rukon wasa yai mata ba,a tare suka sau ajiyar zuciya suna dariya. Chan ta dago tare da tuna mey take tana sinke kai tare da satar kallonshi. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 51_Jarkar Farida ta daga tana lekawa, "Ke kamar na jiyan nan Allah akwai dad'i kamar shayin larabawa. Dariya Laila tayi, "Eh shine,kiyi ta sha toh dan har mun fito ta biyo mu dashi wai ya zama ruwan sha na koh sassaken 6aure koh mey ne?. Kai Faridan ta daga abinta sai kwakwand'a take kamin ta sauke "In ma sassaken darbejiya ne akwai dad'i chakwai.. Harararta Lailan tayi, "Ji ta agun,bakin naki ne chakwai din ai ni dai ba ruwana.. *** 7:50pm Uncle ne tare da angwaye sau hud'u suka shigo jin har ya shirya su amare na kule a d'akin Farida. Nasir bakin nan har kunne sai dariyar keta yake wa Kabir lokacin da suke zama. Waya ya dakko tare da danna kiranta yana murmushi yaji an bud'e kofar d'akin Faridan. Ido ya sawa kofar jin taku kwas-kwas ana fad'in "Hello... Murmushi ya yi tare da fad'in "Hi sweetheart... Wayar ya kashe jin dariyarta, Sultana ce sanye ita da yar Auntyn Laila da farin gown na yara tana jan kasa. Tashi yai tare da ware hannu ganin ta taho da gudu ya dagata suna dariya ya dire. Matuka sunyi kyau da make-up sosai sun kwaskwareta su na bayan amarya gashin nan yasha gyara. "Ina Auntyn ku?.. D'aki ta nuna mishi tana rad'a mishi wai su ma sunyi wai kyau. "Really? Kai ta daga mishi. Sautin murmushin su da kamshin amare ya fara ziyartar angwayen da karar takalma cikin takun 'yan gayu kwas-kwas. Dan haka duk ido suka sanya ma kofar barin ma kar ango da Uncle suji labari. Karasa mike wa ya yi a ranshi yana kiran "Tsarki ya tabbata ga shugaban halitta... Murmushi tayi tare da dan sunkuyar da kai. Mike wa Nasir yai tare da fad'in "Charkwai mad'agwai.. Dariya suka sa da abokan ango dana amarya banda Farida da Uncle da suka lula duniyar musayar kallo da digar da murmushin so Faridan na dan saukar da kai. Sanye amaren suke da net brown mai flower bakake da ratsin green kadan na zaiba head ma baki yasha nad'in Turai 'yar adu'a da stones brown. A yau koh ke baka ce a cikin su kin saje da farare dan make up sai walwali suke. Ita ta dafo amarya wacce tai wankan green itama bakin nan yaki rufuwa. Da kafad'a Nasir ya zungureshi,a wayance ya dauke kai yana murmushi tare fara mirza hannun Sultana. A dan sace ya sake kallota ganin zasu ratsa su wuce ta kusanshi. Kalloshi tayi,matuka yai mata kyau shima dan ya sake sabuwar shiga da wannan farin tabaron gadon wanda a ganinta shine sirrin kyaun Uncle ta ido. Kai ta duk'ar tana murmushi tare da fad'in ma su Sultana "Common.. Common.. Common.. A hankali,da dan gudunsu kwa suka nufe su Sultana na rike hannunta. Ajiyar zuciya ya sau,tamkar ya janyo baya ace yau ne auren su,dan shi a ganinshi ta ninka kowacce kyau dan ita kad'ai yai tozali da ita ya makance bai tantance sauran ba. Binsu sukai a baya har yanzun yana dan kallota ya basar har suka isa ga waje. "Ku sako min amaryata nan da driver d'aya ba kari kafata kafarta. Nasir suka kallo jin shakiyancin shi suna dariya. Dasu Sultana da ita kad'ai suka rage,dan haka a dan sace ta kalloshi lokacin da yake bud'ewa su Sultana baya suna shiga. Juyo wa yai ya kallota,yau d'aya yaji wani kishi na sanya gyale a gefen kafad'a kamar yadda ta saba. Bud'e mata gaba ya yi,kamar wani sirikinta yau sai wani sissinke masa kai take da munafukin murmushin nan nata. Rufe wa ya yi a hankali suna kallon juna. Zaga wa yai ya shiga ganin har sauran sun tada sun wuce. Juyawa tayi tana ma su Sultana magana akan yadda zasuyi kamar yadda suka tsara. Kai suka gyad'a mata,dan haka sai ta juyo tare da fad'in "Good.. Kallota ya d'an yi ganin tana gyara zaman gyalen da warwaron hannunta. Iska ya furzar yana karya kan mota kamar ya ce lullu6e ko'ina koh a fasa zuwa. Ya sani da ana zuwa kan kowa bisa matarshi zai dawo dan ganinshi wai tafi ta kowa.😜 By Feenat Ja'afar. In anjini chilu, gobe ina da islamiya da walima sai jibi.. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). _😍😘Ga masoya labarin *MATAN UBA* I would thank you from the bottom of my heart..❤ but for you, my heart has no bottom😜_... _Amma fa a gareni ni abadan babu kamar *KIYAYYA* duk da *SAKEENA* na fara daga nan sai *DAN YAU*._ _Yayin da a gare ku wasu suke fad'in *BARIKI IYAWA* yafi su, wasu su na fad'in a'a *A BAKIN AURENKI* dai._ _Wa'azi ne gare ku kishiyoyi,zan so ku rike a Ranku *BA KISHYA BA CE* 'yar uwa ce in har mun rike wannan kalmar ta *KADDARA CE* daga Allah koh da kuwa Kaddarar ta zama *JUYA* ce mudin *RABO IN YA RANTSE*_ sai ta zauna...📋✍🏼. Jumma'@ Mabrook.. Love you all😍. 50_Sannu a hankali bacci ya dan fara fusgarta tana gyangyad'i dan yau ba karamin gajiya tai ba ga aikin gida ga yawon gyaran jiki. Murmushi yai tare da dan tashi a hankali daga kafafun nata ya dakko pillow. A bisa lallausan center carpet din da suke ke kai ya ajiye pillown tare da kwantarta kamar wata babyn da ake lalla6awa dan kar ya tashi ya lullu6a mata bargo. Ajiyar zuciya ta saki tare da gyara kwanciya. K'afa ya tankwashe tare da zama kamar mai d'aukan karatu yana mai kare mata kallon. Murmushi ya yi,a hankali ya mika hannu tare da gyara gashin da ya zubo mata garin gyaran kwanciyar ya mayar baya. Ya dan jima a haka yana kallonta,ya sani da in zai kwana bazai gajiya da kallon Farida ba wanda yake ganinta a baccin ta kara k'awatuwa mishi. Murmushi ya sake,a hankali ya furta "Sleeping beauty".. Agogo ya kalla,ba dan yaso ba ya shiga bayan gida dan watsa ruwa shima dan ya kwanta dan gobe yasan akwai jigilar d'aurin auren su Laila. Cikin nutsuwa yake shirya wa, a hankali ya kan kallota,na jijjiga kai ya yi,na murmushi ya yi har ya gama. Maimakon ya hau gado ya kwanta sai kawai ya samu kanshi da komawa ga Faridan ya matsar da faranti,a hankali ya sanya kanshi bisa matashin da take yana jan bargo dan kar ta tashi. Ido ya sa mata jin yadda har numfashi suke had'awa dan kusanci. Murmushi yau tare da kai hannu saitin bakinta ya zagaye su y'an chukul dasu,daga karshe sai 6àrawo bacci ya sace shi kan ya farga a hakan. Kiran sallah ne ya tada shi ba dan baccin ya ishe shi ba ya bud'e ido bisa fuskarta bak'inshi dauke da adu'ar tashi a bacci. Murmushi ya yi tare da tashi jin zai makara ya gyara mata bargo. Su Saifu ya taso a gaggauce jin an tada ikama. Ita kam juyi ta ta sake da halamun bacci yanzu ta fara taji ana sallama a wani gun na sallah. Tsam tayi ido rufe duk da ta kawo wuta abubuwa suna dawo mata na jiya daki-daki. Ido ta bud'e ta bud'e da sauri tare da tashi tana karewa d'akin kallo,tabbas anan ta kwana. Gado ta kalla,bata ga halamun an kwana kai ba dan komai yana nan bisa inda yake ga kuma bargo tare da ita. Gefenta ta kalla,kenan Uncle nan ya kwana? Tunani take mey ya faru kamin tai bacci,abu d'aya ta iya tuna wa

Chapter 12 of 19