take samu a gidan miji kawo a gun Umma da 'yan uwanta..
Yau ki manin shekaru 5 da wani abu ba wanda yake jin kanta in har ta cire Umman Kabir.
"Mtsww...
Tsaki Saifu ya yi tare da dauke kai,da harara sauran yaran ma suka d'auke kai daga kallonta har Uncle din kamar kullum in sun ganta a gidan in banda Farida da yau d'aya taji tausayin Fatima ganin yadda take hawaye.
Juyawa tai tare da fashewa da kuka,a kullum tsantsar tsanarta take gani gun Kabir da kuma iyalanshi,ga hararar da Umman Uzairu ke kwad'a mata.
Anan ta zube tare da fara magana cikin kuka.
"Umma duk d'an Adam ajizi ne,abu sama da shekara biyar amma kullum babu sauki duk da na nemi gafara amma anki a yafe min.
"Da wanne zanji? Da rayuwar kuncin gidan Kamal koh da tsanar dangina?
Tashi Farida tayi tare da fito wa duk suka bita da ido.
Barin wajen Umma tayi tare da zirar buta ta shige bayan gida dan haka tuni Fatiman ta sake sanya kuka abin tausayi.
Shiru tai tare da juyawa jin an dafata ta baya ido duk hawaye yai jajur.
Murmushi tai mata tare da kamota ta tashi tsaye.
"Dan Allah Farida ki basu hak'uri koh zan samu saukin wani abun,ta yuwu in Yaya Kabir da su Saifu suka hak'ura kila su Umma su gafarta min dasu Ya Uzairu..
Kuka tasa tare da rufe fuska da hijab tana cigaba da neman afuwa.
D'aya bayan d'aya suke zamewa suna bin bayan Uncle din i zuwa bangaren su Abba.
Da kallo Farida take binsu har suka fuce basu koh waiwayi Fatima ba dake rizgar kuka.
Parlourn Umma Faridan ta jata tana mai fad'in ta daina ya isa haka.
''Insha-Allah Aunty Fatima zasu yafe miki,har su Umman ma kamin mu koma,kiyi hak'uri ki bar kukan haka.
Kallon Faridan take tana murmushi hawaye na zuba.
"Na gode Farida,na gode.
Murmushi tayi tare da girgiza kai,
"Ba komai..
"Ki batta Farida,a rayuwa Fatima baki ga komai ba ma,ba mugun hali bane junin ki?
Kwafa Umman tai,
"Yanzu ki ka fara gani,sai yanzun ma na gane dalilin da yasa Allah ya hanaki haihuwa Fatima,dan ta yuwu su ma zasu iya dibar wannan rashin imanin naki da kiga girka...
Kai Farida ta girgiza da sauri tare da fad'in
"Subhanallah... A'a Umma kar kice haka dan Allah gudun kar muyi sa6o..
Hawaye Umman ta goge tare da fad'in
"Astagfurullah, amma ni na san koh Halima bazata yafi Fatima in da zata dawo..
"Zata yafe,zata yafe Umma,dan ansha fad'in min cewa mai hak'uri ce,a yanzu kuwa yafiyar ku shine nata Umma,dan Allah Umma abin nan ya wuce,matuka Aunty Fatima tai nadama..
"Na sani da duk iya muguntar Aunty Fatima bai kai digo a na abinda su Tabawa suka girka ba,na sani,Umma kema kin sani..
"Amma da wacce ta ta6a neman gafara?
Shiru Umman tayi,dan haka sai ta girgiza kai
"Nasan babu.
"Dan tunda nake a duniya ban ta6a jin marasa imanin su Tabawa ba,ban ta6a ganin su ba,ba kuma na fatan naga fuskar mugaye Umma,dan nasan munana ne zasu iya bani tsoro...
Murmushi Umman tayi,da sannu tai ta bata hak'uri Fatima na yi,tsakanin D'a da uwa sai Allah,dan haka kamin ta bar gidan Umma ta yafe.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
56_Koh da ta shiga bangaren Abba ba wanda tai ma magana har dare bayan an mayar da auren su Abba da Umma.
Sosai suke a cikin farin ciki a yau da ganin wannan rana kar ma dai Kabir yaji labari.
Bakin nan yaki rufuwa tamkar gonar audiga.
Tashi Umma tayi ta shige chan kwal d'aka jin tsiyar da Kabir ke mata wai an d'aura, yanzu ta zama amaryar Abba a karo na biyu.
Dariya yaran suke mata,dan haka sai filancin ya motsa tare da tashi ta shige chan ciki.
Tara ya shigo har yaran sun fara bacci ita kad'ai da Umma ke tad'in su jefi-jefi.
Murmushi ya yi tare da fad'in
"Muje koh?
Kai ta duk'ar tana mai kad'awa.
Fita yai yana ma Umman sai da safe.
"Umma dan Allah ki kara musu fad'a kamin nazo goben,Allah ba dad'i ne dan koh ba komai jinin su ce tunda halalin Maman su ne.
Kai Umma ta kad'a
"Ai kin san Saifu ne matsalar,in dai yaji kamar sauran ma sunji ne,chan dama ni bana son abinda ake ma yarinyar nan amma babu mai sauraro na ne.
"Sultana mai zata bini tayi bacci gobe da daru.
Murmushi Umman tai mata.
"Ai fa,
Har kofa ta rakota tana mai shi mata albarka kamin ta koma.
Kallonshi tai lokacin da ya kai hannu yana mai bud'e mata kofar yai wanka cikin k'ananan kaya kamar yadda yafi so sai kamshi yake.
Murmushi tayi tare da shiga.
Dole kullum tai ta gani yana zama yaro.
Dan ita a tashinta zata iya kirga sau nawa taga Abban su da k'ananan kaya ya sa.
Ajiyar zuciya tayi tare da jingina tana shakar sanyin a.cn mai had'e da kamshin uncle, tuni taji ta fara jin kasala kamar mai jin bacci.
Kallota yai fuska d'auke da murmushi.
"Ya akai ne Farida?
Juyo wa tai tana murmushi tare da dan girgiza kai halamun babu komai.
Kai ya kad'a tare da kallon hanya yana murmushi.
"Yau ina a farin ciki..
Kalloshi ta dan yi tare da kad'a kai.
Shima sai ya kad'a kan tare da fad'in
"Hala azumin magana ki ke?
Murmushi tai tana girgiza kai.
"Koh baki huce ba,ummm Habebtee Farida...
Kalloshi tai jin sunan har cikin ranta da mamaki.
Kallonshi take,shin da gaske ita Habebteen shi ce?
Dan kallota yai yana murmushi har hakwaranshi na bayyana.
"Koh da ja?
Kai ta k'autar tare da yin kasa dashi tana mamaki
Uncle ne kuwa?
Sake d'agowa tayi tana kallonshi,har yanzun murmushi yake mata yana kallon hanya.
Juyo wa yai harda kanne mata ido d'aya, dan haka da sauri ta d'auke kai tare da kallon d'ayan bangaren tana murmushi.
Kai ya kad'a lokacin da yake yin kwana,hannunta ya kallo tare da kai nashi ya riko d'aya tare da damke shi cikin nashi.
Ido ta rintse da sauri tare da jin buguwar zuciyarta ya karu.
"My Feery..
Ya Rabbi, ido ta sake tamke wa.
Wai dama Uncle haka yake koh dan yau yana jin farin ciki?...
Ido ta bud'e jin ya d'an matse hannun tare da fad'in
"Uhmm..
Zama ta gyara tare da fad'in
"Uhmm.
Ita ma
Kai ya kad'a lokacin da yake kok'arin yin parking a gefen tafkeken wani gu ta baya.
Kallota yai yana murmushi.
"Zan samu rakiya?
Kasa tai da kai,duk sai taji kunya ta fara sakko mata barin wannan kallon Uncle din na kasa-kasa.
Fita sukai tare da zago wa dan nufar wajen da take ganin tsirarin mutane aksar kamar dama an tanada domin masoya ne ga nan sai tad'in soyayya ake ana aika ice cream.
Murmushi ya yi tare da dan zuwa ya zunguri kafad'arta da tashi kamar yadda yaga su na yi da Aisha in sun so gulma.
Kallonshi tayi tare da kau da kai tana murmushin kunya,Allah yau Uncle sai ka ce wani su Saifu da halamun wasa yake ji,dan haka sai ya kara mata kunya.
Tare suka fito rike da leda a hannunshi ita ya bata robar 'Fan ice' babba ta rike sai musayar murmushi ake.
Gaskiya ta yarda da hasashen Umma Uncle na sonta duk da ba kai ga furtawa ba.
Mota suka shiga,da sannu ya gyara parking din zuwa chan gefen jama'a gefen royal tree tasha kwalliyar fitilu sai walwali suke.
Kai ta duk'ar tana murmushi ganin yadda ya jingina a kujera yana kallonta.
Ajiyar zuciya ya sau tare da kar6an na hannunta ya bud'e.
"You know..
Tsam tai tana dan sauararen tad'in shi nason irin wannan lokacin da ba wani haske sai na farin wata da kyalkyali irin wannan.
Kai ta dago tare da dubanshi,Allah sakawa Abba da ya bata Uncle a matsayin miji, ta gode Allah da ya bata alfaharinta da mafarkinta.
Tana son Uncle, ta sani ba kad'an ba..
Kai ta duk'ar tana murmushi, ina ma zasu dauwama a haka tasan bazata gaji da sauraron shi ba har gari ya wanye..
"My Ferry..
Ido ta lumshe tare da saita nutsuwarta jin buguwar zuciyarta,a hankali ta juyo tare da bud'e ido bisa kanshi.
Yau kalamanta sun tsaya chak! Wanda ta rasa dalili.
Ice cream ya miko mata a chokali tare da nufar bakinta dashi.
Kai ta kautar tana murmushi tare da kad'a kai.
"Oh! common..
Juyo wa ta sake yi,dan haka bai kasa a gwiwa ba ya sake mika mata.
Bakin ta bud'e mishi kad'an,cike da so ya sa mata yana murmushi shima yana sha.
Hannu ya kai tare da kunna waka cikin baitin 'wait for me' a slow motion.
Kalloshi ta dan yi,batai tunanin Uncle najin waka balle ma ta soyayya.
Zama ya gyara tare da sake mika mata yana murmushin bin baitin cikin nutsuwa yana kallonta.
Ido ta sa mishi,ga dad'in ice cream ga dad'in wakar Uncle, ga kuma dad'in wajen da yanayin shi.
A hankali lokaci ya fara ja jama'a na watsewa sun lula a duniyar masoya.
Ringing na wayarshi ne yasa ta k'auda kai tana murmushi.
Kallonta yai lokacin da ya daga yana murmushi
"Maj'nu ina ka baro Lailan taka?
Dariya yai kad'an mai sauti yana mai nuno mata wayar dan haka tuni ta gane da Nasir yake.
Ido ya sa mata yana ma Nasir dariya ganin yadda ta matso tana fad'in
"Uncle ka ce Laila...
Kai ya kad'a ganin yadda take zumud'i.
"Toh a bamu Lailan aro Maj'nu..
Dariya suka sa tare da mika mata ganin yadda take washe baki da sauri ta ce
"Kawas..
Daga chan Lailan ta amsa da
"Hmmm,bawani kawas nai fushi..
Kai ta karkatar tare da yin kallar tausayi kamar Lailan na kallonta.
"Ayya,kiyi hak'uri tawan, tunda nazo wayanki a kashe fa..
Daga chan Laila ta ce
"Eh na rasa wayana zan turo miki numbern ta nan yanzun yaushe zaki dawo?
Uncle ta kallo wanda ya jingina yana kallonta.
Baki ta turo tare da fad'in
"Ba rana...
Har suka gama ta bashi bai d'auke ido akanta ba.
Wayar ya kashe yana sake dubanta.
"Meye ba rana?
Baki ta chunno gaba tana dan gunguni.
Zama ya gyara tare da riko hannayenta duk biyun ya kira ta.
"Mey ki ke so nayi a wuce wurin mu koma jibi?
Shiru tayi tare da juyar da fuska gefe.
"Kina sona kuwa Farida?
A bazata tambayar tazo mata,dan haka sai ta juyo ta k'ura mishi ido kamar yadda ya yi mata.
Kai ta girgiza halamun A'a.
Ido ya zaro tare da fad'in
"Mey yasa?
Baki ta chunno gefe tare da fad'in
"Saboda baka sona ni ma..
Baki ta datse da sauri jin ta kwafsa tana dan rintse ido.
Murmushi ya yi tare da sadda kai kasa ganin lokaci yaja goma saura yasa ya tada mota.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
57_Har suka isa kofar gida kanta a gefe sai dai ta dan juyo in taji yana furzar iska tare da sauke ajiyar zuciya in ya kallota.
Kalloshi tayi tare da fad'in
"Na gode,sai da safe.
Murmushi ya yi tare da dakko ledar ya mika mata.
Hannu ta kai zata kar6a ya kautar yana murmushi, ido ta sa mishi,sai murmushi ya yi amma ya kasa ya ce Farida ina sonki,wannan ce babbar matsalarshi.
Kai ta juyar tana masifa ita kad'ai cikin zuciyarta.
"Ni ina ganin fad'in ana son mutum kamar kauyanci ne ma a fad'i Farida...
Juyo wa da tsabar jin wani abu ya tokareta mata makoshi dan haushi.
"Uhmm.
Kawai ta ce ta sake dauke kai.
"Kin san dalili?
Shiru tai,sai dai ta girgiza kai halamun a'a.
_"Cos I love you without knowing how?..when?, or from where?_..
"Dan sometimes I can’t see myself when I’m with you nakan ji wani yanayi haka nan like.. You know... Amm.. ban ma dai san ya zan ce ba ki fahimta.
Ido ta karkad'a,toh koh dai ya d'auka da Halima yake ba Farida ba? Mamaki ya hanata magana sai ido ta yadda koh kiftawa ba tai baki a sake.
Kai ya kad'a mata yana murmushi har hakoranshi na baiyana.
"Akwai wata rana da bazan manta ta ba,kila ke kin manta..
Da karin bayani take kallonshi,dan haka sai ya ce
"Na tuna miki?
Kai ta sunkuyar tana murmushi..
Dan haka sai yai ajiyar zuciya tare da jingina,
"Ranar da ki ka zo ga Abban ki kina kukan aure ki ke so kar samarin su kare kin tuna?
Gyale tasa ta kirifce fuskarta dan tuna wa suna dariya wai ita kunya.
Ajiyar zuciya ya yi tare da fad'in
"A ranar naji how I wish ni saurayi ne da na ce ni ina nan zan jira ki Farida cos idan ina tunanin a ranar na had'u da son Farida may be,domin daga wannan ranar nake tuna ki har nai ta murmushi ni kad'ai.
Tun tana iya jinshi tana murmushi fuska rufe da gyale har ta fara hawaye dan dad'i wanda ya kaita da soma shesshekar kuka kad'an kamar ana busar sarewa.
Shiru ya yi tare da daina murmushin ya matso tare da yaye gyalen wanda tasa ta rufe fuskar dashi.
"Farida..
A dan rikice ya kira ta ganin kukan gaske take yana fad'in akan maganar da yake ne bata so?
Kai ta girgiza,
"Ok ni ne bakya so?
Kai nan ma ta sake girgiza wa tana kallon fuskarshi kai da ganin kukan kasan na shagwa6a ne da jin dad'i.
"Ok,ok toh mey ya sa ki kuka?
Baki ta d'aye tana ta6e bakin hawaye na zuba.
"Ba..ba..bana so fa ka daina fad'a ne uncle..
Baki bud'e ya ce
"Mey d'in ne baki so na daina fad'i?
Baki ta sake 6arewa tare da fad'in
"Kana sona uncle, ka cigaba nake so..
Tsai yai yana dubanta ganin yadda take ta6e bakin,dariya ya fashe mata dashi harda kyakkyatawa.
Kukan ta daina tare da zuba mishi ido tana kallo ganin yadda yake dariyar yana sake goge mata fuska, kan ya zata har ta sau mishi cizo dan haushi.
Hannu ya hau yarfe wa yana fad'in
"Ok,ok I'm sorry..
Jawota yai tare da mata dabaibayi.
A tare suka sau ajiyar zuciya yana mai sake jaddada mata kaunarshi kai ba kace Uncle Kabir bane.
Ba dan sun so ba suka rabe sai dan yadda dare ya shigo.
Tana shiga d'aki Aisha tana waya,da sauri ta haye gadon tare da kwalla ihu tana tsalle bisa gadon.
Da sauri Aishan ta kashe wayar tana fad'in
"Are you crazy?
Baki ta toshe da sauri tare da tare da zama ganin Abba da Umma na turereniyar shigo wa jin ihun da tayi.
"Kuna da hankali kuwa?
Da sauri ta nuna Aisha,
"Ita ce Umma..
Ido Aishan ta zaro,
"Karya take wallahi Umma ita ce..
Kai Abba ya girgiza tare da juya wa yana fad'in
"Allah ya nunan ranar da zaki girma Farida..
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
58_Washegari tun tashin su taci karo da text message nashi mai tsuma rai,dan haka koh da tai wanka sai ta samu kanta da tsaya wa kyali a gaban madubi duk da sai anjima zata fita.
"Aisha..
Galala Aishan ke kallonta,
"Nayi kyau dan Allah?
Daga sama har kasa ta kallota sai washe baki take.
Dan haka sai ta girgiza kai tare da ta6e baki.
"Ban san yaushe har ki ka bada gari ba Farida? Mey ya fad'a miki da har ya siye imaninki daga fita jiya?
Ido ta lumshe tare da fad'in
"So"...
Baki sake Aishan ke kallonta, 'So'?
Ido ta bud'e tare da jijjiga mata kai tazo ta zauna.
"Ban isa karyata son da Uncle jiya ya gwada min ba Aisha, Uncle karshe ne ban ma san na yafe ba..
Kai ta kad'a tare da fad'in
"I see..
Murmushi Faridan tai.
"Ba zaki gane ba,abu d'aya na sani ina matukar za bala'in son Uncle Aisha..
Ido ta rintse da karfi tana murmushi tare da damke hannu a kirji.
"Ya ilahii...Wollah i love him,I really love him Aisha..
Baki sake da mamaki take kallonta,dan haka jin shiru yasa ta bud'e ido.
"Oops..
Iska ta furzar tare da fari da ido tana fad'in
"Ya Allah..meye kuma?
Kai ta girgiza tana kallonta.
"Farida yaushe ki ka san so?
Baki ta chunno tare da tashi ta koma gaban mirror tana fad'in
"Uncle ya koya min..
Kai Aishan ta hau kad'awa
"Umm! I see..
***
"Mun fa zama 'yan kallo Lami.. A gidan nan tun bayan tonan asirin nan Malam ya juya mana baya,koh bangarenshi ya sanya sharad'in kar muje sai ya neme mu..
Tsaki Lamin tayi.
"Ke wannan ne ma a gaban ki?
Kai ta jijjiga.
"Har kullum baki da hankali Tabawa,wato ba ma ta auren da yai ki ke ba sai ta wani abu chan.
"Shin bakya tunanin irin daular da Kabir yake ciki a yanzu ga dawowar Rukayya?
"Shin ba zakiyi tunanin ta yadda muma zamu kwashi rabon mu ba tunda gaba daya sun sallama lamuran mu?
Tsam tayi,
"Kuma fa hakane Lami,yanzu ya zamuyi? Dan tun bayan mutuwar 'Mai yankan wuka' muka rasa na kwarai sai kud'in mu da ake ci,ga jarabar mazajen yaran nan har nakan rasa abin yi..
Shiru Lamin tayi.
"Ga dabara..
Da sauri Tabawan ta gyara zama tana washe baki.
"Muje muna kuka wajen malam din in har ya yafe toh zai iya tausar Kabir din har mu ma ya samu yana yaga mana rabon mu..
Baki ta yage duk ya 6aci da jan goro,
"Kai Lami akwai kwakwalwa,kyanta yanzu muje tunda 9 tayi ai ya tashi a bacci kamin Kabirun yazo mu kasa.
Kai ta kad'a tare da yayumar gyale suka fuce zuwa kewayen Abba mai gate wanda aka sanya katanga a tsakanin su ya zamo su suna a tsohon gida.
Kari yake a parlour
Kai ya juyar gefe jin zuciyarshi na tafasa,kai kana gani kasan kukan ba na Allah bane.
"Tabawa..
Cikin shessheka ta amsa.
"Zai fi mana kyau idan ku ka nesanta kan ku da zuwa inda nake, domin ganin ku na sake sanya min tsanar ku ne kawai..
Ido suka waro suna kallon juna.
''Haba Malam,duk tsiya fa har yanzu mu matan ka ne...
Da sauri ya juyo a masife,
"Au shine alfaharin ku?
Kai suka girgiza da sauri.
"Toh na sauwake muku auren nawa dama alfarmar makiyin naku kuke ci har ku ka kai iyanzu kuna a matsayin mata na..
"Innalillahi.. Haba Malam,daga neman gafarar?
Waje ya nuna musu tare da sake 6ata rai
"Ku 6acen da gani,sannan ya zama rana ta karshe da zan sake ganin kafafunku cikin kewayen nan dan yau Rukayya zata taro,amma in baku ji ba naga sake ganin kafar wata cikin gidana na sallama muku wanchan..
Sallamar Uncle ne yasa yai shiru ganin shi da akwati guda biyu ta Umma,tuni sukai ladab tare da sunkuyar da kai kasa harda fad'in
"Sannu Kabiru,ina kwana?
Abban ya kallo ranshi had'e
"Da wani abu ne Abba?
Kai ya girgiza tare da fad'in
"Na ce su bar min sashe sunki tashi,sannan ka zama shaida na sake su bana son kuma wata mu'amula ta gama ni dasu ta fanin zama a inuwata koh taka.
Tuni ya sake tamke fuska ya kallosu
"Toh mey ku ke jira anan?
Murya na rawa suka ce
"Hak'uri muka zo bayar wa,kuskure ne..
Murmushi ya yi tare da kad'a kai
"Ok ya yi kyau,amma zan sanar ku in har na sake ganin kafar d'ayar ku a cikin gidan nan Tabawa za kusha mamakina ne.
Ido suka waro.
"Dan Allah kai hak'uri..
Waje ya yi tare da ajiye jakar,dan haka da sauri suka koma kan Malam da ya cigaba da yagar kazarshi da Umman Uzairu ta dafo mishi tamkar ba mutane a gabanshi.
"Zaku fita ne koh na cika umarnin Kabir?
Juya wa sukai jin maganar Uzairu shima rai had'e, yadda ya tsani mutuwarshi haka ya tsani su Tabawa,dama kiris yake jira ga kwa dama ta samu.
Jiki a salu6e suka tashi su na mai sake bawa Malam hak'uri Uzairu ya rakasu har waje.
"Kabir ya bani damar koh baya garin nan in naji koh naga kun shigo gidan nan na sanya a d'aure mishi ku 'yan sanda..
Da sauri suka juyo har Lami na hararar shi
"Kai kuma a suwa?
Murmushi ya yi tare da kad'a kai
"Zaku gane a suwa in kun kwata sake shigo mana gida.
Gate din ya tura tare da barin su baki sake.
"Lami da gaske fa suke ba zasu bari aci arziki damu ba,ki duba kiga wannan gida ga sanyin a.c ga cima mai dad'i..
"Mtsww..
Tsaki tai mata tare da harara ta koma gida cikin konar rai.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
60_Washegari duk jikinta yai sanyi tana had'a kaya kamar kullum in sun zo zata koma.
Tashi Aisha tayi tare da isa gun akwatinta ta zuge ta dawo tare da mika wa Faridan.
Jujjuya wa tai tana kallonta da halamun tambaya ganin littafi hud'u.
"Mey zan dasu?
Zama tayi tare da murmushi.
"Ki karanta su,da ajiye wa nai sai na samu bibbiyu na baki copy d'aya akwai abubuwan da zai taimake ki sosai aciki ba wai littafi bane na soyayya.
Bankad'a su tai dan fahimtar abinda ke ciki,duk dabaru ne na zaman gidan miji harda na girki.
Murmushi tai ido cike da kwalla tare da kallo Aishan ta rungumeta tana fad'in
"Allah barmin ke 'yar uwa kwatan jikina...
Tureta tai tana harararta suna dariya
"Ke fa bakki M,kwata ce ma?
Kai ta girgiza tana goge hawaye tana dariya.
"Allah ina sonku, sai naji kamar kar na tafi..
Harara ta sau mata.
"Sai ka ce gaske.
Dariya sukai tare da tayata ta gama su na firar su cike da son juna.
Kallota ya yi lokacin da suka d'au hanya ta juya su na dariya ita da su Sultana.
Kai ya kad'a yana murmushi tare da kallo hanya.
Kalloshi ta dan yi tare da gyara zama tana mishi murmushi,a dan takaice ya kallota tare da fad'in
"Hi..
A hankali kamar bai son su Saifu su ji.
Kai ta kai kasa tana murmushi,kamin ta dago a dan sace ta kalloshi tare da daga mishi yatsunta halamun
'Hi'.
Kai ya gyad'a yana murmushi,tun yana iya jiyo hayaniyar su Saifu a hankali ita ta bingire bacci,dan haka kowa ya gyangyad'a suka bar Uncle da tuki.
Ajiyar zuciya yai tare da furzar da isa hannunshi bisa stirrn mota bayan ya kallota yadda take bacci hankali kwance fuskarta na kallo shi.
Juyi tai taji duk ta takure dan haka a hankali ta fara dan mutsu-mutsu halamun tana son space dan haka sai ya rage gudun tare da gyara mata kujerar tai baya dan ta kara jin dad'in baccin.
A gajiye suka sauka,dan haka kowa d'akinshi ya nufa dan ware gajiya.
A parlour suke suna kallo ga katon plates na fruits a tsakiya ana ci.
Waya yake da Umma yana murmushi,
"Duk kowa lafiya, ya Abba?
Ajiyar zuciya yai tare da jingina kai yana 'yar dariya mai sauti,ba sai an fad'a ba kai kasan jin iyayen nashi guri guda ke sa shi farin ciki.
Farida ya kallo wacce ke latsa waya tana murmushi halamun wata gulmar ake guntsa mata ta 2go Laila.
Murmushi yai tare da fad'in
"Za taji Umma,na gode.
Wayar ya ajiye tare da fad'in duk Umma na gaida su.
Kai ta dago tare da kad'awa
"Muna amsawa,dazun ai munyi waya ta kira taji mun sauka..
Murmushi yai tare da kallo su Saifu da suka raja'a a kallon TV wata mata a asibiti ta haihu suna fad'in.
"Wow! She's so cute...
Tvn Farida ta kalla,koh ita jaririyar tai mata kyau.
Kallo Farida Nass ya yi yana turo baki
"Aunty Farida kin ce fa kin zama Mom namu koh?
Kai ta kad'a tana kallonsu ganin yadda ya zunguro baki.
"Toh ki je asibiti muma ki samo mana baby mai kyau muna so,Sultana ta girma...
Ido ta zuba musu jin sauran ma sun hau kad'a kai su na fad'in
"Eh kam,ki haifar mana baby mu ma..
Kallo Uncle din tayi dan jin mey zai ce tana raba ido.
Ha6a Uncle din ya hau shafawa yana kallon Faridan da wata siga yana murmushi,
"Dady ma yana so koh Dady?
Wayen cewa tare da gyara zama yana fad'in
"Eh..sosai ma Nass..ai..amma toh..
Farida ya kallo,
"Amma ita fa Momyn naku tana so?
Faridan suka kalla duk cike da son jin ta ce tana so.
Yake tai musu tare da kad'a kai tana basar da uncle
"Baby ai na da kyau..
"Toh samo mana..
Amjad ta kallo tuni har ta fara marairaice wa ganin yadda suke fad'in su kam a samo musu k'ani Sultana na fad'in K'anwa.
Uncle ta kallo,sai da ya dai daici yaran basa kallo ya kashe mata ido d'aya yana yana dariya.
Yawu ta had'iye tun karfi jin cikinta na wani irin kulululu da sauri ta d'auke kai.
Ba fa a nan gezo ke sakar ba..
Zama ta gyara tare da sake kallo Uncle din sai wani kakkane mata ido yake.
Kai ta d'auke da sauri,
"Haihuwa?
Zama ta sake gyara wa tana tunano diagram din nan cikin biology har ta soma zufa.
Su Saifu ta kallo,har musu aka fara na wai sunan da za a sawa babyn in yazo.
"Na'eem..
Kai Nass ya girgiza wa Amjad
"A'a Nawwas.
"A'a Suhaif dai..kunga Saifu da Suhaif,ya zama kamar takwara na.
Dariya suka sa har Uncle d'in in banda Farida dake yake musu hak'ora.
Kamar an mintsileta da sauri ta tashi tana fad'in
"Ina zuwa..
Ta kule d'aki.
Dariya Uncle ke ke kunshe mata tare da girgiza kai yana cije le6e,sarai ya fuskanceta da yanayin da ta shiga tun fara zancen,hakan kuwa da ta nuna ya sake tabbatar mishi da 'yar mitsila yanzu ta san dawar garin...
"Dady kai fa?
Ajiyar zuciya ya sau tare da furzar da iska,a hankali ya ce
"Farida..
Baki su ka saka tare da zuba mishi ido suka maimaita
"Farida kuma Dady?..
Kallosu yai ashe fa yai katofara,dan haka da sauri ya wayence tare da fad'in
"No.. I mean..
Kai ya dafe tare da rintse ido tare da bud'ewa yana musu murmushi.
"Sorry guys.
Sultana ya kallo tare da fad'in
"Sultanate fa? Mey ki ke so a sa ma babyn?
Baki ta yake tare da fad'in
"Sultana 2..
Gaba d'aya suka sa dariya Uncle harda janyota.
"That's my princess.. Nima baby girl nake so..
Baki mazan suka had'a gun fad'in
"Nooo Dady Boy...
Kallosu yai yana murmushi tare da tsaida su
"Ok,ok,i know boys...
Tsit tai tana jiyo su duk karad'in su daga cikin d'aki tana tunani ta inda zata fara.
Laila ta kira
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 19