Share this page
Nasir.. Dariya shi dai yake tayi yana kad'a kai,dan haka kawai sai uncle din ya sa mishi ido. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 42_Wanka kawai tayi ta shiga kitchen tare da ciro markad'e ta hau abinci. Haka kawai taji tana son Nafisa dan haka koh gajiya bata bi ba ta hau girki. Hayaniyar yaran taji,wanda ke nuna sun dawo kenan daga dakko Feenah,da fara'arta ta fito dan tararta. Waya ta shigo tana yi halamun tana sauraren d'ayan bangaren. Murmushi tayi tare da ajiye jakarta tare da fad'in "Hon...I want a divorce.. Da sauri uncle ya kallota har yaran da Farida,da sauri ya warce wayar ganin zata kara magana ya harareta tare da kashe wa. D'aki ya ce su Saifu su tafi ganin tana nemar mishi kuka,dan haka sai Faridan ma ta juya duk da tana iya jiyo su daga kitchen. "Ba dan haka na baki waya ba,in kuma so ki ke muyi fad'a toh bissmillah. Kukan tasa tana fad'in "Bros banzo kasar nan dan na koma ba,na gaji da gafara sa banga kaho ba,Ummanshi ta rasu bama kasar, Abba ya rasu,kwana goma kamin nazo har an mata da yazo.. "Mey muke nema da bamu samu ba? "Koh kud'in da suke diddika mishi yake zaunarshi baya tunanin a kasarshi anfi bukatar mu? "Burina zama likita na zama,amma ba burina na bautawa masu jan kunne ba,kasata nake kishi,nan nake da burin taimako amma sanda ya murkusheni na fara bauta musu... Ido kawai Uncle yasa mata yadda take magana ba koh shan numfashi cikin masifa. Tunaninshi wai dama mata in an ta6o su basu iya fad'a bane kamar Farida koh kuma hali ne yazo d'aya? Murmushi ya yi tare da tashi ya nufi kitchen, "Bani ruwa Farida.. Juyo wa tayi duk tana jinsu,dan haka ba musu ta bashi da cup. Wala Allah in ta kora na sanyi taji sa'ida. Kofin ta mika mishi bayan ta shanye ya sake kara mata wani. A dan sace ta kallo shi tana goge fuska halamun taji kunya. "Sannu toh.. Fuska ta marairaice dan haka da sauri sakko tare da tsugunawa a gabanta tare da riko hannunta. "Ki gane Feenah ba wai ina bayan Salis bane,at least ki bashi dama ta karshe tunda ya ce zai gyara,sannan ki saurara gobe ne yai alkawarin har yara zasu taho, ina rokonki kibi a sannu ki kuma cire batun saki,ban son ji. Kai ta kad'a, "Ji yadda little Hali ke kuka a waya Feenah ba kyau fa zalunci.. Fuska ta marairaice, "Raina ya 6aci shi ne dalilin baro masa ita amma kar ka tona kasan raina kamar nai tsuntsu dan na mata yayen dole...i'm sorry.. Kunne ta kama kamar yara in sunyi laifi. Murmushi ya yi zai magana sai ga nan wani kira ya sake shigo wa. "Kar ka damu ka nutsu ka bari goben ku karaso,tana nan a guna. Feenahn ya kallo yana nunota da hannu ya tashi. Jin shiru yasa Faridan fito wa d'auke da flaks tana mata murmushi. "Aunty sannu da zuwa.. Murmushi tayi tare da kad'a kai, "Sannu Aunty Farida,ya aiki? Kai ta kad'a tana tashi da konawa dan had'a komai. Da dare bayan ta nutsu tana a d'akinta ya kwankwasa. "Dazun muna magana a mota bamu karasa ba. Kai ta kad'a tare da zama. "Yauwa,nima yana raina abin gwara da kazo. "Bros,da farko kai kuskuren dasawa yaran ka tsanar *MATAN UBA* wanda har ya zamana ta zama dabi'arsu ya kuma bi jikin su suke musu kallon duk d'aya. Kai ya kad'a yana jinta. "Na biyu baka kaunar kwa6arsu wai dan kar Farida ta sarar su in na fahimci dalili.. "A duk abu na na nan duniya bros akwai mai kyau akwai marar kyau,bazai ta6a yiwu wa ace duk MATAN UBA na duniya halin su d'aya da su Tabawa da Jamila ba,ya kamata ka koyar da k'anka da yaran ka haka. "Farida yarinya ce,wacce bai ma dace ace tun yanzun ta iya rike ragamar k'anka da yara kamar su Saifu fa,but thank God,yarinya ce mai zuciyar manya,in har ka kyalla da kyau zaka gano son faranta wa iyalan gidan fal cikin ranta ka kula da kyau. Tabbas duk wani kuskure na Uncle a yau ta k'ak'kabe mishi tass wanda ya duba yasan yai kuskure. Parlour suka fita ta sanar wa su Saifu duk abinda za suyi in har Farida sun fito tare. D'akin Faridan ta kwankwasa ta amsa tare da bud'e mata ta shigo. Kusa da ita ta zauna tare da riko hannunta tana murmushi, "Zan ari bakin Bros da su Saifu na sake baki hak'uri, and su ma yanzu zasu baki believe me.. "Farida.. Kallota tayi ganin ta zama serious sosai dan haka sai ta nutsu. "Kamin nan ina son na baki wani tarihi,ta yu zaki fahimci wani abu daga ciki na abinda yasa zaki kara d'aura belt naki ki kuma bawa Uncle da yaranshi tabbaccin akwai MATAN UBA na kwarai a kusa. Ido ta sa mata,dan haka tun daga haihuwar Uncle ta fara bata tarihin kalubalen da ya fuskanta a hannun su Tabawa har girmanshi. Kuka take da idonta jin wai duk wannan masifar Uncle ya ganta a hannun su Lami. Dafata tayi itama tana goge hawayen tuno da rayuwar yayan nata a hannun MATAN UBA "Farida 'abin da aka gasa wai shi ya ga wuta' inji y'an iya magana,hak'uri da juriyarki ita zata sanya ki fidda wa Bros tambari da ya buga nasu Tabawa,bai da laifi in anbi ta wani bangaren,dan ance in maciji ya sare ka in kaga tsumma ma gudu ka ke. Kai ta jijjiga, "Insha-Allah zan basu mamaki,Insha-Allah daga yanzu zasu ga banbanci,dan na kara tsanar mugu tun daga jin labarin su Tabawa. Murmushi tayi tare da fad'in "Na gode Farida,nasan zaki iya,Allah zaya sanya miki hannu soon. Murmushi tayi ta kad'a kai. "Muje parlour. A zaune suka same su duk sun sanya Uncle d'in a tsakiya. "Oya,ga nan Aunty Farida ku bata hak'uri. Kallota tayi da sauri. "Aunty basu fa min komai ba.. Kai ta jijjiga "I know,amma sai sun bada. Kallosu tayi tana musu da kai halamun su bata "Kiyi hak'uri.. Cewar Amjad, kan yai shiru Nass ma ya bayar sauran Saifu dake ma Feenah yake. Y'ar hararashi tayi duk Faridan na kula,dan haka sai tai murmushi, abadan bata tunanin Saifu zai iya fad'in tai hak.. "I'm sorry Aunty Farida,daga yau baza mu sake komai ba sai yadda ki ka ce... Ido ta waro waje baki sake tana kallonshi yayin da shi kuma yake kallon Feenah halamun ya yi yadda ta ce toh. Wonder shall never end,'Aunty Farida? Ido ta karkad'a ganin Saifun ya matso tare da kama kunne yana sake fad'in sorry yana kallon Uncle dake murmushi ganin Faridan nayi. Saifun ta kamo tare da cire hannunshi daga kunnen tana dariya. Kamar gaske shima Saifun sai ya fara yana sissinke kai,dan haka sai ta dungure mishi kan da sauri ya tafi kamar zai fad'i ta riko shi suna dariya. Eh lalle ya gano inda ya gaza,ya gano ta inda ya 6ata,dan haka sai ya kallo Feenah tare da lumshe mata ido yana duk'ar da kai halamun ya gode,kan itama ta rausayar tana murmushi halamun he's welcome. Uncle din Farida ta kallo tana murmushi, bayan duk sun nutsu har yaran sun tafi d'aki dan bacci,kai ta sunkuyar ganin shima ya kallota,a yau wani lamari taji yana zarya cikin kwanyarta game da Uncle wanda ta tabbatar shi ake kira da 'Kauna' dan tausayin rayuwarshi. Yanzu waye zaice Uncle shi yaga wanchan rayuwar ta baya? Tasan yanzu sai tarihi.. Lalle ta gode Abbanta da ya bata Abban su Saifu,in har ita ce Farida Ahmad ita kwa zata shayar da uncle mamaki har sai ta matar dashi ya ta6a rayuwa a hannun su Lami. Kan ta sake dago wa still idonshi a kanta,da sauri ta sake yin kasa dashi cikin kunya tana murmushi,duk Feenah na kallonsu tana girgiza kai, lalle da wani babban aiki a gaba,ja kuwa. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 43_A kitchen suke suna had'a breakfast harda su Saifu da Aunty Feenah yau koh bacci basu koma ba daukin zasu ga yaran Feenah. Abinda su ka yi su Saifun ke miko wa Farida lunch boxes nasu tana jera wa cikin nishad'i suna tad'in su. Su kansu yaran a yau wani farin ciki suke ji a dole sun taya Farida shiga kitchen duk da taimakon Feenah. A mota ma haka,kowa ka gani yana cikin nishad'i. Dan haka Uncle tuki yake yana musu murmushi dan jin dad'in yau. Kamar kullum ya sauke su kowa ya zago yana mishi peck kamar wasu larabawa gwanin sha'awa su na fita. Juyo wa yai bayan ya gama da y'an mazan yai ma Sultana a goshi yana jan kumatunta tana dariya. Ido Faridan ta sa musu, kullum zai ma kowa amma nanda ita. Sauke Sultanan tayi tare da kallonshi kamar yai mata amma ya kasa. Ba tare da ta kawo komai na ita ta kai baki tare da mishi bisa gefen kumatun shi. Waje tai ta barshi baki sake suna mishi bye-bye ita da Sultana suna murmushi. Hannu ya daga cike da kallon Faridan,da halamun ita koh a jikinta ma kamar ba ita tayi ba har suka wuce. Tuki yake yana tunanin Farida,tabbas ta sauya,dan a da bata mishi koh da bai mata. Mudubin gaban motar ya kallo tare da ta6o kuma tun yana murmushi, kai ya kad'a, a hankali ya sau sassanyan kid'a tare da sakar ajiyar zuciya har ya isa ga office. Hmmm,Uncle something! Something!!...😜 Ita kam har Laila sai da ta zuba mata ido tana kallo ba koh kiftawa ganin yadda take murmushi ita kad'ai tana lumshe ido. Iska Lailan ta furzar tare da fari da ido ta ambaci "Ya Rabbi... Kallota Faridan tayi tana murmushi,ganin ta tsareta da ido yasa ta ce "What? "Uncle... Ido ta zaro tare da fad'in "What? Kai Lailan ta dungure mata tana hararata. "Wannan murmushin na Uncle ne for sure.. Wayence ta fara tana dan harararta. "Very funny.. Tare da bud'e littafi tana kicin-kicin da fuska. Baki Lailan ta ta6e tare da gyara zama.. "Ki ma yarda mata wallahi u r in love,cos wannan shegen murmushin '6aunar' naki ban yarda dashi ba yau. Kallota tayi tare da yin dan jim,aji ta kallo,tasan revision ake dan haka bata sa ran da zasu samu first period, dan haka da sauri taja ta waje. Hannunta duk biyu ta rike tare da marairaice mata. "Yes i'm in love Laila,buh I don't think Uncle na sona ni k'awata taimaka. Karasa wa tayi tana sauke kai kasa cikin marairaita. A dankalin gefen ajin Lailan ta zaunar su rike da hannun juna. "Anya Farida kina yin yadda Aunty ta ce kuwa? Baki ta turo gaba tana kunkuni,dan haka da sauri Laila ta hararota. Hannunta ta sake damka cikin marairaice fuska tana fad'in "Yanzu komai ki ka ce zanyi i swear Laila.. Zama Lailan ta gyara tana fari da ido cikin iyayi. A sannu ta hau mata iyayi tana zayyano mata harda irin taryar da Auntyn ta ke wa mijinta da irin sallamar da take mishi. Fuska ta yatsine da dauri tai da ita kamar taga abin amai. "Yook, dan Allah kar ki sani amai, wannan ai kazanta ce,ina ma laifin kumatun tunda dama yana ma su Saifu. Harara Laila ta sau mata tare da ture hannunta tana kok'arin tashi ta riko ta. "Zancen gaskiya zan iya komai banda wannan, gaskiya tsantsani nake... A tunzure Laila ta ce "Tsantsano y'ar kayan haushi kawai.. Baki Faridan ta turo, "Eh naji ke ce komai ke in kinyi aure kije kiyi tayi.. Tsaki Laila tayi tare da tashi, "Cikani toh yar nema. Tashi tayi tana mata magana ita kuma tana toshe kunne halamun bazata ji ba. **** Rike suke da little Halee mai sunan Maman su Saifu a hannu daga Faridan har su Saifun kamar su mayarta ciki. "She's pretty.. Murmushi Uncle ya yi su da Feenah da maigidanta. "Aunty Feery bani ita dan Allah,I loved babies.. Ido ta zaro tare da fad'in "Really? Kai suka kad'a har su Nass,kamin suka fara fad'in "Me too.. "Me too, "Me too. Dariya parlourn kowa yasa jin yaran da santin babies kowa na fad'in me too. Baki Halima ta yage musu cikin dariyar yara tana kallonsu ,hakan yasa Farida itama murmushi tare da fad'in "Me too.. Dariya parlourn kowa yasa jin yaran da santin babies kowa na fad'in me too. Faridan su Saifu suka kallo,yayin da ita kuma ta kallo Uncle tana murmushi. Ido ya zuba musu barin ma Faridan,kai ta dauke tare da daurawa su Saifu babyn ganin Feenah na mata tsiyar sai ta sullu6o musu. Da dare ya ce mijin Feenah ya ce tazo su tafi hotel tunda sunzo da yara ga d'akin d'aya ne amma fur Uncle yaki. "Matan su kwana d'akin Farida,sai Irfan ya kwana gun Saifu gadonshi yana da girma. Uncle din ta kallo ganin kitika-kitikan yaran Feenah, wannan ai sun cinye mata gadon in sun kwanta. Kamar Feenah ta gano tunaninta tai saurin kad'a kai. "Ai na manta akwai d'akin ka ma Bros, Hon,mu kwana tunda gobe ne zamu wuce Kano. Daga Uncle din har Faridan Feenah suka sa wa ido baki sake,murmushi mijin nata ya yi tare da koma wa d'aki shi da yaran dan su dakko kayan su zuwa d'akin Farida. Ido Feenah ta kannewa Uncle din tana dariya ta wuce tare da dago wa Farida hannu "Sabhahul khairr.. Yake ta mata har ta shige,Uncle din ta kallo ganin su kad'ai aka bari. Keya ya dan sosa tare da dauke kai. "Ba damuwa ki zo muyi sharing nawa akwai space. Juya wa ya yi ya batta nan tsaye tana jinjina kwana d'akin Uncle. Drawer ta bud'e bayan ta fito a wanka tana wa yaran Feenah yake dake kallonta. Su har yanzun mamaki suke wai wannan ita ne matar Uncle din su. Murmushi suka mata ganin ta d'aura hijab bisa kayan baccin ta dau waya tana musu sai da safe. Kai suka kad'a tare da kwanciya suna dan kus-kus. Ra6e-ra6e ta fara,anya bazata kwana parlour ba kawai? Kai ta kad'a tare da murmushi da zummar juya wa taji bud'e kofar Feenah. Yake ta mata ganin tana kallonta, "Au baki kwanta ba Faridee? Magana zatai taji takun Uncle sanye da jallabiya,corridorn ta sawa ido,dan haka ganin su tsaye yasa shima ya sa musu ido. Kitchen Feenahn tayi tana kunshe dariyarta rike da feeder a hannu. Ruwa shima ya dakko yana ma Feenahn yake,da mamakin su sai ta nemi waje cikin parlourn ta zauna tana sake fad'in sai da safe. Yake Faridan ta mata tare da wuce wa tana kallon Uncle din har ta kule corridor. Feenah ya hararo wacce ke kunshe dariya ta mike. Da kai ta nuna mishi halamun ya wuce kawai ba gardama. Kai ya girgiza yana murmushin yadda ta mayarsu kamar yaranta. A bak'in kofa ya samu Faridan wacce ganinshi yasa ta kule ciki. Iska ya furzar tare da kad'a kai, yau Feenah ta kwaso mishi aiki kawai. D'akin ya murd'a tare da bin bayan Faridan har wata fad'uwar gaba yake ji a yau. Wa yaga 'Tijara,wai dukan Miji da asubar fari.😹 By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 44_A tsaye ya sameta tsakiyar d'akin tana raba ido,juya wa ya yi tare da sanya mukulli a kofar ya dan kallota. "Ki zauna man.. Yake tai mishi tana sake k'arewa d'akin kallo. Ruwa ya tsiyaya a cup yana sha tare da kallonta ta gefe ido ganin har yanzu taki zama. Tunaninta d'aya labarin da Aisha ta bata,gana y'ar yarbawa ya isa ta guji kwana d'akin Uncle.. "Farida.. Kalloshi tayi cike da tausayin kanta,toh mey ma yasa bata ce zata kwana a kasa bisa d'akinta ba?.. "Ki kwanta man.. Yake tai mishi ganin yana daukan pillow zai d'aura bisa kujerar gefen gadon mai hannu d'aya. "A'a Uncle bari ni na kwanta achan d'in.. Galala yake kallonta ganin da sauri ta rarumo pillow, "No ki kwanta a gadon yau kawai nan zai min.. Murmushi tayi a dole ita ta samo dabara, "A'a, ai ya ma kad'an 2sitter ne ba matsala zan kwanta. Kai kad'a yana kallonta da mamakin yadda take d'ari-d'ari dashi a yau. Gadon ya haye ta yadda zata samu ta shigo ta tsukukun wajen. Yake tai mishi tare da ajiye pillow ta zauna rike da waya. Akan photon su ta tsayar da idonta wani tafkeke yai kyau duk da a nesa take kalloshi. Sauka ya yi tare da isa ga fitila zai kashe ya kallota. Kwanciya tayi tare da damke ido kamar wanda yasata baccin dole. Kai girgiza tare da murmushi ya kashe fitilar. A hankali ta fara bud'e ido rike da waya a hannu duk ta takura cikin hijab d'in. Dan haske ta gani masu kyalkyalin blue da pink bisa gefen gadon cikin bed lamp. Satar kallonshi tayi taji yana adu'a tare da tofe ko'ina ya juya. Cikin sand'a ta tashi tare da cire hijab din ta ajiye gefe tana huci. Wayar ta ajiye tare da fara itama adu'ar kamar yadda ta saba ta kwanta. Juyi tayi sai lokacin ta tuno da pad din dake like a jikinta,dan haka sai ta sau ajiyar zuciya tare da yin hamdala tana murmushi. Juyo wa yai kad'an dan ganin koh tai bacci yaji shiru,idonta a kanshi,dan haka su na had'a ido tai saurin tamke nata. Murmushi ya yi tare da da yin rigin gine yana bud'e Gallery. Hotonan Sultana yake kallo wanda ya ta6a d'aukan ta a d'akin Farida. Murmushi yake tare da shafo fuskar Sultanan ganin yadda tai kyau ranar. Na gaba yake yana duba sauran,a hankali ya dawo baya kad'an tare da yin jim ya zuba wa wayar ido. Dariya suke shi da Sultanan sa6e da ita bisa kafad'arshi yai musu selfie ga chan Farida a bayan su tana musu dariya. Zooming yai yana mai sake kallota tai tsaye rike da k'ugu tamkar tasan zata shiga tai kyau. Bangaren Faridan ya kallo,idonta rufe halamun bacci na son d'aukanta. Murmushi ya yi,yarinyar tana matukar burgishi ya rasa dalili,barin ma a y'an kwana biyun nan... Ajiyar zuciya ya yi tare da ajiye wayar ya kwanta. Ido ta bud'e tare da zuba mishi ido,murmushi tayi tare da rufe idon tana gyara kwanciya,a hankali har bacci ya fara fizgarta. ~~ Hannu take nuno mishi tana murmushi halamun jinjina a karon farko tun aurenshi da Farida yau yai mafarkinta. Tako wa ya yi ganin tana kok'arin juya wa ta barshi amma tai mishi nisa,dan haka sai ya soma kiranta. "Halima!..Halima bari kiji kar ki tafi ki barni.... "Halima!.. "Halima"... Zaune ta tashi jin tamkar a mafarki ana mata rad'a. Wayarta ta lalubo tare da tashi ta haska shi ganin d'akin dulum. A zahiri ma kama sunan Haliman cikin baccin shi yana dan mutsu-mutsu kad'an da kai. Fuska ta yamutse tare da mai mata kalmar "Halima kuma? Cikin mamaki. Tabbas tasan mafarkin Maman su Saifu yake dan jiya taji Aunty Feenah ta ce little Hali takwarar Maman su Saifun ne. Uncle din ta kallo jin yai shiru yasa da sauri ta kashe wayar ta kwanta. Mike wa ya yi halamun ya farka a mafarkin tare da jan douwar ajiyar zuciya. Agogon waya ya kalla kusan ukun dare da wani abu. Kai ya girgiza tare da sauka ya shige band'aki. Tana kallonshi yadda yake jero nafila tare da kwararo adu'o'i wanda yawanci na Halima ne. Tun tana iya kirgawa har wani sabon bacci ya sureta. Washe gari tana ji yana tashinta da nufin tai sallah yana fita ta sake sabon juyi dan sam jiya bacci rabi da rabi tayi. Kallonta yake bayan ya dawo daga masallaci ba bu halamun tai sallah, dan haka tuni ya gano a halin da take. Har zai juya ya fuskanci a takure take dan haka sai ya dakko bargo tare da rufa mata ya rage karfin a.c yana dubenta. Sosai mafarkin yau ya tsaya mishi a rai,tun rasuwar Halima yakan yi mafarkin tazo mishi babu walwala barin ma lokacin auren su Fatima. Jingina yai da pillow,amma yau na daban ne,dan matuka ya gano wannan zuwan na daban ne. Murmushi ya yi yana kallon hoton sun dake manne a bango. Tabbas mutuwa mai yankan kauna ce,dan ta raba shi Halima rabuwa ta har abada. Ya sani da har kullum baida madadin Halima a duk a aurenshi. Har yanzu ita ke da mulkin birnin masarautar zuciyarshi, "Farida... Kai ya kad'a. Yasan nata ba so bane,tana burgeshi ne kawai domin aksar wasu halayenta sukanyi shige da na Halimenshi musamman ta fuskar fara'a da hak'uri,shagwa6a da yarintarsu mai ban sha'awa. Yana zaune yau koh baccin ya kasa koma wa sai tunanin Habibiyarshi yake a juma ya kallo Farida. Ya kwata ya tasheta ganin lokacin shiga kitchen nata ya yi amma sai ya bari,yasani tana da matukar kok'ari dan haka yau d'aya ya bari ta huta har sai ta motsa dan kanta dan yasan revision suke. Juyi tayi duk a zaton a gadonta take wanda take sakata ta bararraje,kallota ya yi jin a hankali tana adu'a da halamun har yanzun baccin bai saketa ba. Murmushi yai yana kallon yadda duk gashinta ya yamutse gwanin kyau ribbon yai gefe guda. A zabure ya sakko ganin zata sake wani juyin wanda daga shi sai dai tajita a tiles da sauri ya daddafe hannu yai mata k'awanya yadda ta zamo rabi a kujera jikinta rabi a hannunshi. Ido ya zuba mata,jin ta wani iri yasa da sauri ta bud'e ido sai warai a nashi. D'akin ta karewa kallo a hankali ta tuno inda take dan haka da sauri ta mirgina kan kujerar tana dubenshi. Tabbas da taci kasa ba da ban uncle ya taro ta ba. Murmushi yai mata,dan haka itama sai ta mishi tare da kallon agogo. Ido ta zaro tare da kallonshi ganin ya zauna,a zabure ta mike tana kiran "Ya Rabbi,wayyo.. Ribbon din ta gyara tare da yayimar hijab nata cikin sauri zata fita. Da kallo ya bita har ta ta sa ta fuce,dan haka sai ya bi bayanta. Kitchen ta nufa tana kukkunna wutar parlourn jin wai yau har su Saifu sun rigata tashi ga nan hayaniyar su. Ja tai tsaya da tsanin mamaki baki sake,Uncle ta kallo wanda shima ya karaso ganin ta tsaya ya kallo Feenah da ke fadin "Surprise... Murmushi tayi tana bin komai da ido, lalle yau da ta tafka lattin da bata ta6a ba har 7:10am tana bacci. Karasa wa tayi cike da jin dad'i tana fad'in "Kai Aunty amma na kin taimake mu,gaba d'aya na sha'afa da bacci yau...ina kwana. Murmushi tayi tare da amsa wa tana dago wa Uncle yatsu dake musu murmushi. "Yanzu kije yau na hutarki har lunch kuje ku dawo. Murmushi ya yi tare da juya wa dan shiga wanka. Kwarai taji dad'i, duk da taki yarda amma ganin Feenahn taki bata yasa ta zari tsintsiya tare da fita parlour. Jim tayi,yau dai d'aya ya kamata ta gyara d'akin Uncle dan koh ba komai chan ta kwana,dan haka sai ta nufi chan ta hau gyara jin yana a band'aki. Fita take kok'arin yi ta tsaya tare da kurawa hoton ido,tsaye suke shi da Maman su Saifu yaran na zaune kan kujera da tsohon cikin Sultana. Juna suke kallo cike da so da kauna suna murmushi rike da hannun juna. Kai ta dauke daga hoton,haka kawai taji tana dan kishin Maman su Saifu dan tasan ita kad'ai ta mallaki son Uncle abinta har ta koma gashi har a bacci yana ta sururunta. Waje tayi dan isa ga d'akin Sultana,da mamakinta yaran Feenah shima sun hutarta wankan Sultanan har tasa uniform. Cike da marmarin zaman su tare da iyalan Feenah suka rabu dan isa ga Kano,dan haka sai aka d'aura daga inda aka tsaya in har ka d'auke jituwar su dasu Saifu da ta kara karfi,ta Uncle kuwa iyakarta da d'akinshi gyara shine kawai cigaba. *** Sunyi hutu,wanda daga shi zasu shiga SS2,duk da mai tsayi ne amma Uncle kad'ai yaje duba mahaifan nashi ganin Aisha ta kawo musu ziyara yau. "Yanzu ya zamuyi Saifu? Ga nan John bai dawo ba balle yai mana refilling ga yau uncle zai dawo miya kawai gareni.. Tunani suke na gas da ya kame gashi ba kero ba hot plate dan ba wuta,mai gadi ya je gida ya dawo. Yaran ta kallo,tasan iyanzu yaci duk su fara jin yunwa barin su Saifu acici. Fuska ta washe tare fad'in "Idea.. Tashi tayi duk suka bita da kallo har ta isa gun dining. Gwangwanin madara ta girgiza tana murmushi da kallon su Saifu dan tuna wa da wani lokaci chan baya zamanin Fatima. Cornflakes ta zuba wa kowa tare da jerawa a faranti ta bawa kowa nashi. Dariya suke dan tuno musu da baya gashi Aisha a gurin. Guntun dake ciki ta juye a plate tare da dawo wa cikin yaran tana kunshe dariya,a hankali suka fara tariyo baya suna gyara zama. "Ku tsaya a deba ma Sultana sai ayi wawar.. Kai Sultana ta girgiza tana dariya,dan haka sai ta ce "Ready? Kallon juna suke suna dariya ganin a hankali tana tuna musu da rayuwar da sukai da ita chan baya dan haka da karfi suka ce "Yessss. Kai ya sako cikin gidan har zai bud'e parlourn ya bari yaje ga window in da yaga labile a dage yana lekensu sanda ta ce ready. Tana kwa ajiye plate din aka hau wawaso hannu baka hannu bisa faranti suna kyalkyala dariya. Dariya shima ya fara ciki-ciki yana kallon Faridan yadda suka zama basu maraba da yaran wajen wawaso. Tsayuwa ya gyara ganin Sultana ta d'auke farantin tana gudu tana lasar guntun sauran sun d'aura a bayanta ta zille musu su na dariya. Farida ya kallo,wacce tsuguna tare da dafe baya tana maida numfashi cikin murmushi. Ido ya zuba mata, tabbas wannan shine mafarkin Halima a kullum tun tana raye, yaranta kawayenta. Yau ga nan Farida ta maye gurbin in da ta tsaya. Dariya take harda rike ciki tana nuno gefen su Sultana,dan haka sai ya kallo gun,Nass ke jan plate Sultana na ja,kan ya farga ta kai hakori zata sa cizo yai sauri ya cika shine suke dariya. Faridan ya

Chapter 11 of 19