Share this page
kar muyi haka,dan Allah kabarni naje,nai alkawarin kula da kaina ba yawo, kullum in na gida please...kaji? Haba my booo... Kai ta langwa6ar gefe rike da hannunshi kamar zata sa mishi kuka. Ajiyar zuciya ya sau tare da furzar da iska yana kallonta. "Wannan ne babban matsalar,amma dayar matsalar ma zata iya sanya wa kin san aki tafiyar. Baki ta turo tare da sanya kuka ba hawaye tana fad'in "Haba Uncle dan Allah,koh sati d'aya ne dan Allah.. Ido ya zaro.. "Sati? Kai ta kad'a da sauri "Eh sati kad'ai dan Allah. Murmushi ya yi tare da zame wa ya kwanta. "Koh ba ni ba yarana ma sanin kanki baza su iya sati baki kusa da su ba,balle azo kaina... Kuka ta fashe dashi na gasken tana buga katifa har da shura kafa ga nan ciki a gaba. Basarta ya yi,dan fa abinda bazai iya bane wannan, ta tafi ta barsu wai har sati. Kuka sosai take tun yana iya basarta har sai da zuciya ta debe shi ya jawo ta,ture shi ta fara tana mai cigaba da kukanta. Ta ma yaya za a ce a bikin Aisha ace bazata ba? A kanta aka fara haihuwa? Kyaleta ya yi ganin yadda take daddagewa tana ture shi,dan haka sai ma ta sauka tare da bud'e kofa da sauri ta fice yana kiran ta. Sauka ya yi tare da binta,dan haka da sauri ta rufe kofa,kofar ya tura tare da shiga har ranshi ya soma 6aci. Dan haka tuni ya rufe ido ya fara fad'an dan ya ce ta hak'ura shi ne har zai jawo tai ma kanta illah? Kukan ta bari tare da fad'in "Eh dan ni banga dalili ba gaba d'aya cikin biyun.. "Akaina aka fara ciki? Koh kuma da Maman su Saifu bata nan basu rayu ba?.... Baki ya saka cike da mamaki yana kallonta,sai da ta dire aya ta hau sauke numfashi. "Ni ki ke fad'i ma haka Farida? "Ni ki ke sanar ma son ranki kawai dan na ce ki tsaya? Shiru tai kanta kasa tana goge ido,tabbas zuciya ta jata har ta fad'i ba dad'i. Dan haka sai ya kad'a tare da juya wa ya fuce kawai ranshi 6ace. Burus tai mishi,a ganinta in nuna tai fushi zai batta ta tafi,ranar sai a nan ta kwana. Washegari kowa rai a dagule ya tashi har yaran su ka zo breakfast su na dan kuskus ganin yadda take dan kallon bangaren Uncle lokaci-lokaci ranta ba dad'i. Ji take kamar ta dubu shi amma ta kasa dan fa fushi take. A shirye ya fito hanunshi bisa kwalarshi yana gyara wa,bai kalleta ba ya ce "Guys,maza ku samoni mota nayi latti.. Agogo suka kalla,tabbas zai iya ci har ya gama su tafi,sai dai ganin yadda yake sauri yasa suka kwankwade shayin tare da binshi su na mata sai sun dawo. Da kallo tabi shi yadda ya nuna ba ma ai ruwanta ba a gun,kai ta d'auke cikin kunar rai da takaici taga lunch box nashi bai d'auka ba. Dauka tayi da sauri da zummar mika mishi yana kallonta yai gaba ya batta tsaye rike da ita baki sake. Baki ta ta6e tare da koma wa ciki tana masifa ita kad'ai "Wannan ai fad'an ma rashin gaskiya ne.. Zama tai a kujerar dining din tana hararar kofa. Abincin nashi ta kallo,har tea ta had'a mishi da komai,dan takaici kawai sai ta sau kuka a gun. Waya ta d'auka tana kuka tana tsara wa Umma abinda akai tun jiya har yau da hanata zuwan da ya yi. "Ban san baki da hankali ba har yanzun Farida ba sai yau... Baki ta saka tare da daina kukan. "Akan wannan maganar shi ne har zaki nemi mishi rashin kunya yana yabonki sallah? "Umma ce wa fa.. "Ki rufe min baki,yana y'ancin hanaki zuwa koh baida dalili kuma dole kiyi biyayya tunda mijinki ne.. "A shirmen ki ma wa ya fad'a miki hakan zai sa ya barki? A kalla kiyi ta rarrashi a matsayin ki na matarshi kina da hanyoyi da yawa ba wai wannan rashin hankalin ba.. "Ki tabbatar baki sake sa6a mijinki ba,balle ki fad'a mishi magana da yaranshi, yasan da ba Haliman ai,dan haka ki tabbatar yana zuwa kin bashi hak'uri... Kuka sosai take,dan haka kit Umman ta kashe wayar. A ganinta akan gaskiyarta take na meye zai fita yin zuciya?. Kayan ta kwashe,duk da sosai taji ciwon yadda bai ci abinci ba ya fuce amma ba yadda ta iya zata bashi hak'uri, kuma bikin ta fasa ma zuwa. Wayarta ne tai ruri,Laila ne,kamar mey jira da sauri ta d'auka. "Mom twins ga maigida na gaishe ki.. Murmushi tai cikin sanyin murya tai magana. "Lafiya kuwa? Tabbas Laila na bata shawara wacce take bullar mata,dan haka sai ta sanarta har yadda sukai da Umma. Kwafa tai mata cikin jin haushi. "Wallahi har kin ban haushi ba kad'an ba... "Wannan ai ba abin tada jijjiyar wuya bane,cikin kissar ki zai aminci miki ba sai an kai ruwa rana ba.. "Ina mamakin da karamin abu irin wannan yake gagarar ki wataran Farida. "Abu na karshe ya zama na karshe gare ki da miji zai fad'a kina fad'a, haba Hajiyata,ba aji mu bane wannan,sannan duk tsiya kar ki sake barin d'akin mijinki wai dan ranki ya 6aci,ki danne har washegari ba'a raba shimfid'a da miji koh anyi fad'a sam ke baki ma da wayo Allah.. Ajiyar zuciya ta sau,tare da jijjiga kai, "Toh ya zanyi,wallahi ji na nake a sama ne da naji ya hana,yi hak'uri ki ban mafita.. Duk yadda zatai ta tsara mata tare da fad'in ta tabbatar kuma ya hakuran. Iska ta furzar tare da sauke waya ta kallo lunch box din,murmushi tayi tare da shiga kitchen ta juye mishi har nata tare da zirar mukullin mota tai office nasu bayan ta sake kimtsawa. Wayarshi ta kira,su na tsaka da zancen su ya gani,sai ya danna reject. Wayar ta sauke tare da mayar da gyalenta saman kai kawai ta kutsa office din tana gunguni. Tambaya tai wata Sakteria ta nuna mata office d'in. Tana ji yadda suke kallonta su na kus-kus din madam din Boss ne. Kwankwasa wa tai,daga ciki Nasir ya ce 'yes', dan haka kawai sai ta tura da sallamarta. Baki suka saka suna kallonta rike da lunch box da waya da keys a hannu. Nasir ya kallo tare da sake kallonta jin tana gaida Nasir din. Karasowa zatai ya tashi da sauri tare da fad'in su fita kawai ya rike lunch box sai wani kakkareta yake halamun kar a ganta. Mota ya bud'e suka shige da sauri ya rufe tare da kallota rai 6ace. "Mey ya sa baki ce zaki zo ba na fito koh baki ga da maza a ciki ba? Baki ta turo tare da fad'in "Ba ka ki d'auka ba,shine na shigo.. Ido ya sa mata ya ma rasa abin fad'i ganin yadda ta tsare shi da ido. Ya bud'e baki zai magana tai saurin rukunkumoshi tare da fad'in "Na tuba toh,please forgive me bazan sake ba har na jiya ma. Ajiyar zuciya yai jin yadda take mutsu-mutsu wai ya ce ya yafeta. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION(NWA). 75_Yau kam mata ansha daga,dan sai wajen goma ta sauka,muryar nan har ta dashe dan mita da karad'in a yafe mata. Dan haka tun abin na ba wa su Laila dariya har ta karya musu zuciya barin bayan ta haihun. Kuka ta sa bayan an nuna mata wai mey ta haifa koh tana a hankalinta ta rufe ido kam. Ranar lalle ta sake sara wa mata,ta sara wa iyayen da suka haifo ta duniya.. Ta kuma sara wa Halima mai haihuwa ita d'aya babu dan tayi,lalle jaruma ce ta kuma ajiye makamanta akanta. Hawaye Uncle din yake goge mata tare da jera sannu,sannu yafi a kirga idonta rufe tana jijjiga mishi kai kawai. D'akin hutu aka garata bayan an gama kimtsa ta aka kawo musu baby,zo ka ga yadda take make kafad'a tana chunno baki wai bata daukan babyn sai ta huce. Murmushi Uncle ya yi kawai tare da fad'in su kyaleta. Ba kowa daga shi sai ita bak'in nan har kunne,burinshi su Saifu su karaso da Nasir yaje d'akko wa. Babyn take satar kallo lokacin da yake nuno mata yana fad'in sun samu Sultana 2 sai k'au da kan karya take tana make kafad'a tare da k'au da kai a ganinta ita ta sanya har jarumtar k'are. Murmushi ya yi tare da juyo da babyn inda ta juyar da kan ya fara make murya da tamkar wai babyn ke mata roko da kirari a gareta na jarumar uwa. _"Dear Mom.. Forget Superman, Batman, Spiderman and all the other comic book heroes. They should make a movie about you 'Supermom'. Thanks Mom,thanks for being the hero,warrior in my life.._ _"Thank you for being so wonderful,I love you Mama.Please ki d'auke ni naji d'umin ki.._ Fuska ya marairaice mata tare da fad'in "Please.. Murmushi tayi tare da rintse ido,wani dad'i take ji yayin duk wani zugi taji yana raguwa had'i kaunar manna babynta jikinta. Hannu ta kai bisa yatsun babyn tana dan ja babyn na mutsu-mutsu,Uncle ta kallo tana murmushi sai ya lumshe mata ido had'i da shafo fuskarta. Kofa a ka bude cike da murna suka shigo. Baraden nasu ne su ma bakin nan har kunne cike da burin arbawa da baby.. Tashi yai tsaye dan basu waje tuni duk sun mamaye gadon Faridan ta matsa chan karshe kowa hannunshi bisa baby su na yabawa sosai. Ajiyar zuciya yai tuno da lokacin baya sanda Halima ta haifo Sultana. Kai ya sunkuyar yana murmushi, a'a yau ba Halima ba ce,Farida ne,rayuwa mai sauyi-sauyi.. "Dady.. Kai ya dago jin Nass ya kira shi tare da fad'in yazo wai yaga babyn na musu murmushi tasan sun zo.. Murmushi ya yi tare da matsawa ya tsugunna a gaban su nan suka lalace har kusan sha d'aya dakyar su ka hak'ura su ka tafi gida. Washegari aka sallame su sukai gida. Sai ga nan su Farida ana rokon Umma yafiya,ta sani haihuwar ta ne kad'ai ba tai ba amma ta bata ciwan kan da koh Aisha bata bata ba. Kaka har mamakin yaran da Uncle take ta yadda tun yana kawaici har ta kai ta kawo a ranar kam parlour ta koma ta barsu da yaran ganin d'aukin babyn ba na karau bane har Faridan tai bacci. Haka washegari dakyar ya lalla6a su musamman Sultana sukai makaranta, ya kuma sha mamaki da aka tashi yaje wai ba su Saifu. Da mamaki ya kira aka sanar mishi ai sun karaso. Kai ya kad'a yana murmushi, lalle yaran da gaske suke. Fur da dare baby tai ta kuka har sai da Faridan itama ta sau kukan jin da ta fara bacci mai dad'i kaka zata tayarta baby na kuka. Gyangyad'i take a zaune bisa gadon kaka na gyara ma babyn parmpers Sultana ta leko. Kai kakan ta girgiza, "Dama har yanzun ba kiyi bacci ba har sha biyu? Murmushi tai mata tare da kallon babyn tare da sa hannunta a baki ta koma. *** Tashinta kenan ta nufi band'aki tana hamma dan baccin dake idonta jin ana kiran assalatu. A gaban gadon ta tsaya baki sake dan kula da ba baby a gadon sai shinfid'a. "Na shiga uku... Zazzage shinfid'ar ta fara da sauri gabanta na fad'uwa ba baby ba halamunta. "Wayyo Allah,kaka..kaka.. Juyi kakan tai tare da amsawa, "Kaka baby,na shiga uku an sace min baby kaka ki taimake ni.. A zabure kakan ta mike tare da watsakewa. "Ke bana ciki da shirme.. Tashi tai ganin harda su daga zanin gado tana kiran babyn ta. "Subhanallah.. Naga karfe biyu ma mun tashi,bari na duba koh ta mirgina chan bayan gado.. Hannu ta hau yarfe wa tana kuka,da sauri tai waje tare da yin d'akin Uncle. "Wayyo Allah,naga ta kaina uncle.. A zabure ya mike jin kukanta, kasa ta zube tare da mimmike kafa hannu bisa kai tana mishi kuka dan haka da sauri ya sakko. "Lafiya? Mey ya faru? Jijjiga ta yake tana nuna mishi waje. "Baby..ban ganta ba an sace min ita.. Galala yake kallonta,jin hayaniyar Kaka yasa da sauri yai wajen tare da isa d'akin, sama da kasa babu jaririya. Waje ya nufa tare yin bak'in gate a kulle maigadi ya hau tuhuma yana mai tabbatar mishi ba wanda ya shigo koh ya fita. Parlourn ya koma gabanshi na fad'uwa ya nufi inda yake jiyo kukan Faridan kaka na bata baki. D'akin Saifu ya tura sai gashi ma ya fito jin haya niya. D'akin su Nass ya koma ya bud'e duk baccin su suke dan haka tuni ya sake rud'ewa ya soma zufa. "Toh waye zai d'au baby gida a kulle su na bacci? Tunani yake,dan haka baida mafita tunda bata gidan kawai ya doka kiran police kan su basu ga fa babyn su ba. Baba mai gadi ne yazo yana sanarshi wai baiga magen shi ba,dan yasha jin ance kuliya na cin jarirai.. Kuka Faridan ta sake kurmawa jin bayanin Baba maigadin tana fad'in ita dai kawai babynta za'a biya ta wallahi. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION(NWA). 76_Kuka sosai ta rika musu ba da ban karar gen ba da ba abinda zai hana tada kowa na gidan akan ita fa sai an fito mata 'yarta,haka kurum,yaushe ma ta dawo a nakudarta?. Dan haka ba shiri Uncle yabi shawarar maigadi na duba bayan gidan koh za a ga kuliya duk da shi sam hankalinshi bai d'au abin ba,tayaya kuliya ma zata sungumi d'an mutum? Sai dai borin Farida yasa ya d'au torchlight suka hau zaga gida. Chak ya ja ya tsaya tare da fad'in "Baba na tuna ba mu duba d'akin John ba.. Kai Baban ya kad'a, dan haka da sauri suka nufi d'akin sai ga nan kuliya kwance gefen katifar John tana bacci halamun ya manta ya rufo kofa da ita. Parlour ya koma,iyanzu kam abin ya fara bashi tsoro ba mamaki ba? Ga sabon dagun hankalin shine kukan Farida.. Waya ya ciro jin har an shiga sallah ya hau kiran Nasir wala Allah koh zai samu mafita ganin police kam shiru. Laila ce ta d'auka gabanta na fad'uwa ganin kiran, tambayarta yake Nasir ta ce ya shiga alwala lafiya? Kai ya kad'a tare da fad'in "No,ba komai.. "Yauwa gashi nan ma. Halin da suke ciki ya sanar mishi dan haka tuni ya hau salallami. "Ka tabbatar har su karkashin gado kun duba da ko'ina? Kai ya kad'a mishi tare da fad'in "Ba fa inda bamu bincika ba a gidan nan Nasir,abin yana matukar d'aure min kai.. Jim yai tare da fad'in "Toh koh Aljanu ne?.. Da sauri Uncle ya ce "Aljanu kuma? Ihu Farida ta sake tare da burburwa yana tai hak'uri tana mak'e kafad'a. "Bari Nasir zan kira.. Wayan ya kashe tare da koma wa dan lallashinta har Saifu ya taso su Amjad duk sunyi chirko-chirko. Tunaninshi koh dai ya sanar dasu Umma? Kai yai saurin girgiza wa,toh mey zai ce ma? Jim kaka tai tana dan tunani, "Ni kam ka binciki wajen Sultana? A tare su ka kallota har Faridan,da azama Uncle ya mike dan tuno wa da kwana biyu tabbas baya rufeta ta baya. Kofar ya murd'a a hankali duk suka d'auru bayanshi su na leka wa tamkar sunzo sata. Kwance take a rigingine tamkar wata teddy haka ta aza babyn a kanta a rub da ciki babban yatsanta na bakinta yayin da dan karamin ta sanya wa baby,da tai motsi in taji yatsa ta hau tsotsa da haka suke baccin su daga babyn har momman. Juyo wa yai tare da kallon Farida wacce ta sau ajiyar zuciya mai karfi tana rintse ido. Kai kakan ta girgiza, ta rasa ya akai tun da hankalinta bai kawo nan ba? Lalle sha'anin y'an gidan nan sai su,dan haka su na shiga ita ta juya dan zuwa alwala. A gefen gadon Uncle din ya zauna tare da kallon wannan dabara ta Sultana ita kam baby kamar ta samu sucker sai sha take. Hannu ya kai da zummar d'auke baby sai kwa ta challa ihu,dan haka da sauri ya janye hannun yana ganin ikon Allah ganin ta sake raruma ta hau sha. Murmushi Fatidan tai tare da zama itama,jin kukan babyn yasa Sultanan fara motsi dan haka sai ya hau tashinta. Ido ta bud'e ganin yadda suke kallonsu yasa ta kallo babyn,baki ta wage tare da musu yake sai ya d'auke babyn ta tashi. Fad'a zai fara mata tai narai-narai zata sau kuka Faridan ta hau lallashi. Sanar su take babyn ke kuka shine fa ta d'akko ta ganin su Mom Farida kar ta tashe su a bacci shine ta taya su raino. Ajiyar zuciya yai tare da kad'a kai,ita kam Farida mamaki take da wayon Sultana, koh ma dai meye tasan dominta tayi. Ta sani da tun haihuwarta take sake ganin so ga iyalan gidan da babynta,dan haka koh da ya bata babyn suka fita nan ta zauna tana feeding nata Sultana na taya ta har su ka dawo a sallah. Uncle ne ya soma dariya tare da gwada ma yaran borin da Faridan ke yi dazun su na dariya,kai sai fa yanzu ta fara jin kunya. Sallamar su Laila ne yasa suka saki baki su na kallon juna,shaf ya manta bai sanar musu an ganta ba. Sosai sukai dariya lokacin da ake maida zancen yadda abin ya kasance sai tsiya suke ma Faridan. Kaka kam tana ganin wani abu wai shi fi'ili a gidan Uncle. Wanka wannan yanzu zata hau karad'in kiran Uncle din yazo kaka zata konata ya taimake ta. Haka zai zo bakin kofar band'akin yana fad'in "Kiyi hak'uri.. Umm,uhmm kaka a dan sassauta mata dan Allah.. Shiru take musu har ya gama rokanshi ya fuce sai fa tai mata. Dan haka kullum wanka da kuka ake shiga a hakan ma tai ta jan hankali ruwan na huce wa. *** Iska ta furzar ganin wannan kwalliya da taki karewa a gun Laila da Aisha. Mike wa tai su ka sake zaunarta dan haka nata ido. Sosai tai kyau ita da iyalan nata a yau kowa na yaba wa,dan haka tuni aka hau watsa selfie da y'an taron suna da babynta Leema. A kunne Nass ke rad'a mata Uncle na kira a bayan gida wai ta taho da baby,dan haka sai ta bashi babyn ta ce gata nan zuwa. Tamkar ango shima ya sha farar shadda ta manyan kaya bakin nan har kusan kunne yana daukansu da yaran. Murmushi take tana gyara ma baby showel ya sake daukanta a hoto,a ganinshi bata ta6a mishi wai kyau ba irin na yau daga nan ya kira su Aunty Feenah da su Hafsa. Suna kam ya kayatar matuka. Watan su d'aya suka nufi Kano dan samun hutun su Saifu daga nan ta karasa wankanta chan. Wannan farin zuwanta Kaduna gun Momynta ba tare da Aisha ba sai Sultana,sosai zaka fahimci da rashin sabo a tsakanin su,dan daga murmushi sai y'ar fira jefi-jefi. Abu d'aya da ya bata mamaki bai wuce sakewar fuskar mijin momyn nata ba wannan karan,dan ita da gani take kamar ma bai son tazo gidan shi. Shi kam ganinta nasa yaji haushin da fa yanzun ya'rshi ce da Abbanta bai mishi fashin mata ba karon farko. Uwa uwa ce,dan haka a dan sati sosai ta ja 'yarta ta rage wani filakon,ganin hakan har da mata kukan ita tun aurenta bata ta6a zuwan mata ba. Murmushi tai tare da fad'in zata zo ne watan wataran. Cike da tsaraba Uncle ya dakko su suka dawo Kano daga nan Umma ta dasa a inda ta tsaya na gyaran d'iyar tata. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION(NWA). 77_A mota suke bayan sun dawo a gidan Aunty Rabi sun kai mata yini da Aunty Feenah. Sai d'an kallota yake yana shafo ha6a da murmushi. Kai ta sunkuyar dan wani abin har kunya ma yake bata a yau. Sosai ita kanta tasan ta tsatso kyau da gyaran jikin Maman Juwairiya,ga nan kitso yiri-yiri da bai saba gani ba Umma ta sanya dole an yaryara mata shi harda na gaba,ga nan kunshi sak dai sai ta dawo kamar ba Momyn su Saifun ba. Parking ya yi su Saifu sukai gaba da baby yayin da ya jingina yana sakar ajiyar zuciya. "A gaskiya ki fa shirya,ni in son samu ne gobe ma mu wuce.. Kai ta langwa6e tare da marairaice mishi fuska kamar zatai kuwa. "Kai My Boo,wata uku na zata zanyi kamin na koma ni fa nai missing su Umma fa. Harara ya sau mata tare da fad'in "Kwanan ki nawa da barin gidan ki? Marairaice wa ta sake tare da fad'in "Wata na fa kachal.. Murmushi ya yi tare da fad'in "Itakillah Mom Saifu fa,wata amma kina neman kari? Baby Leema 2month take fa.. Baki ta dan turo kad'an tana gunguni ya matso tare da gwara mata goshin shi ta rike gun tana 6are baki. Bakin shima ya 6are tare da tayata,dan haka sai suka fara dariya. Wani waje ya kallo,a hankali fara'r dake fuskarshi ta fara raguwa tare da jan jiki ya koma set nashi ya zauna. Juya wa tai dan ganin mey ya gano? Su Tabawa ne tsaye ita da Lami su na nuno motar su halamun basu dai san su na ciki ba dan glass din mai duhu ne na ciki kawai ke iya hango na waje. Murmushi tayi tare da girgiza kai,a kullum ta duniya Allah sake kaskantasu yake ta sani da hakkin mutum babban abu ne mud'in bai yafe ba. Uncle ta kallo tare da kai hannunta ta riko nashi,ta sani da duk da su Tabawa basu a gabanshi amma tabbas in dai zai gansu toh fa zasu tuna mishi baya ne mey sa shi a 6acin rai. Ajiyar zuciya ta sake saki,ta gode Allah da bai sa ta ari halin su Tabawa na *MATAN UBA* ta lakawa ruhinta ba. Uncle din ta kalla,mutum har mutum mai matukar kamala da suffar kwarjini,ga kud'i ga lafiya da tsabar kyawun kama da jin dad'i da Allah a yanzi yai mishi baiwar su. Su Tabawa ya kalla lokacin Indo ta fito,kai ta girgiza, tabbas the difference is clear,lalle ne duk wanda ya ce d'an wani bazai kyau ba toh fa lalle nashi ne bazai kyau. Hannunshi ta sake rintse wa cikin nata tana jijjiga kai. Ina ma *MATAN UBA* zasu gane abinda ta gano na game da sirrin rike da ta gano da tai imani daga yau an daina samun mugayen *MATAN UBA*. Domin ta duba,aksar duk wanda hakan ta same shi kamar Kabir d'inta Allah yakan daga darajarsu ya martaba su sama da kima, ya kuma kaskantar da irin su Tabawa da d'iyan su. Har kullum tana mamaki idan har aka ce *MATAN UBA* na cin zalin yaran kishiyoyinsu takan dasa ayar tambaya Shin *kishi* ne koh mey? Murmushi tayi tare da girgiza kai, "Ba kishi bane,in har kishi ne matuka tana kishin Uncle ta yadda bata bukatar wata mace ta ra6ar mata abinta. Abu d'aya ta bari wanda shine take ganin dalili su ne abu uku= *Hassada* *Mugunta* da kuma *Rashin imani*. Tana ganin wannan ita ce cutar da ke damun zukatan *MATAN UBA* irin su Lami.. Murmushi tai har hakoranta suka baiyana gareshi,cike da nutsuwa ta fara mishi kirarin da tasan in ta fad'i yakan dara koh da bai yi shiri ba. "Gaba dai gaba dai Uncle na Farida Dadyn Saif da Amjad, Nass,Sultanat da Leema,wallahi kai makiyanka nisa nisa na har abada.. "Allah ja min zamanin ka,lalle ne kam mai laya kiyayi mai zamani, mai zamani kiyayi mai Allah,ka rugasu dan ka rike Allah..wai Aradu maganin shagalalle.. Dariya yasa sosai jin wannan kirari tamkar wata marokiya a gaban sarki,take yaji kuncin ya yaye,tuni maye gurbin da farin ciki. Kai ya girgiza tare da fad'in "Farida.. Kai ta karyar kasa tana murmushi tare da fad'in "Yes your Highness.. Murmushi ya yi tare jinta lungu da sako na zuciyarshi. Allah yai mishi baiwa, da Ni'imar ababe da yawa,ya gode,ba kuma zai gaji da gode sarki Allah na da ya sanya rawarshi har tai kyau haka. Zaga wa tayi tare da bud'e mishi mota tana mai sake kaskantar da kai a gareshi tamkar wata driver, tuni kuwa ya fara jinshi bisa sama. Motar ya kulle suka jero zasu wuce su Lami da suka sau baki gun kallon su. Kasa suka zube da sauri ganin wani dan banzan kwarjini da yai musu har basu san sun furta ina wuni ba baki na ka'rkarwa. Gefe yai da kai,sai Farida ke kallo su tare da rausayar da kai halamun ya amsa. Da kallo su ka bisu har su ka shige gidan su Umma su na tad'in su cike da kwanciyar hankali tamkar ba mahalukai su ka wuce ba a gun. Jiki a salu6e su ka tashi tare da shiga gida,sun sani basu isa tambayar gafara ba,dan a kullum sharad'i d'aya ke taka musu burki, sun sani da baza su iya zuwa ga hukuma ba su ce su din masu laifi ne ba. A ganin su da kunyar duniya gwara ta kiyama,dan haka sun yarda su zauna a haka duk tabbas wataran hakan zai iya kumbura zukatansu,dan fa ga koshi ne,ga kuma kwanan yunwa. *Karshe* Lalle ne kam dama ai wata Shari'ar sai a lahira. Ina rokon Allah ya yafe min d'ukkan kurakuran da nai a wannan labarin nawa na *MATAN UBA* Ina rokon Allah da ya isar min da sakona inda nake da bukatar ya isa dan *MATAN UBA* su fahimci ina na dosa. Nafisa Bashir Tanko,(Feenat Ja'afar) ke muku fatan Alkairi. Ubangiji ya gyara zukatan mu da aikata khairan. An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Chapter 18 of 19