Share this page
tad'in uncle, dan haka da sauri ta sanya kanta cikin bargon tana leka wa. Kan ta fito dashi tare da sakar ajiyar zuciya ta furta "Thank God. A gaggauce ta mike tare da ninke bargon ta mayar inda yake ta dau farantinta ta fuce dan ma kar ya sake ritsata dan haka koh da ya dawo sai fankon d'aki babu 'yar mitsila. Murmushi ya yi yana duben wajen tare da tuno jiya,tabbas girma ya kare,dan ya gama zubewa,sannan gaskiyar Nasir da ya ce ya saki jiki yaci duniyar shi da tsinke. Kai ya kad'a,yana mai aiyana "Komai yazo karshe.. **** 10:02am ya fito yasha farar dakakkiyar shadda mai sirfani yai harda babbar riga kamar ma shine angon. Duk ido suka sa mishi har yaran wanda su ma sukai shigar shadda da zuwa d'aurin aure. Murmushi yake yayin kallonta ganin yadda ta zuba mishi ido itama tana murmushi. Ba tun yau ba ya gano duk randa yasa manyan kaya Farida naso, ya gane hakan ne ta yawan kallonshi da murmushin ta. Sosai itama tai mishi kyau,barin yadda tai baya da gashin nan sai ta dawo mishi babbar mace mai aji. Kasa tai da kai cike da kunya tana murmushi rike da serving spoon. "Wow!.. Dady kayi kyau sosai. Murmushi yai musu yana fad'in "Really? Kai suka jijjiga da sauri Nass ya ce "Kamar kaine angon... Dariya suka sa yana kallon Farida da ke dan sato kallonshi tana tayasu. "Sabhahul khair ya Dady.. Sultana ya kallo yana murmushi,kumatunta ya kamo yana fad'in "Habibtee Sultantee.. Ya ruhii,kaifa halik? Dariya tai tana fad'in "Alhamdulillah.. Peck ya bata yana fad'in "MashaAllah zan kara kud'in islamiya.. Dariya suka sake lokacin da Faridan ta dawo bangareshi domin zuba mishi tana murmushi "Ina kwana Uncle.. Kai ya daga yana sake kallonta. "Lafiya lau,ya ki ke? Kai ta kad'a mishi tana had'a mishi tea. Murmushi ya yi tare da kallo su Saifu "I'm so happy today... Da sauri suka had'a bakin fad'in "Umma zata koma gidan Grandpa right? Farida ya kallo yana murmushi jin har ta rigashi. Gira ta daga mishi tana barin wurin dauke da murmushi. Kai ya jijjiga musu baki ya ki rufuwa,ya sani da kowa zaiyi murnar wannan komen duk wanda ke yinshi. Dan haka sai yai musu albishir d'in ana gama bikin su Uncle Nasir zasu tafi Kano,dan haka da farin ciki aka gama cin abinci har suka fuce gun d'aurin aure. Da yamma tare da amarya suka dawo gidan Faridan da tsiraren kawayensu wanda suka gayyata a auren dan shirin dinner. "Oho,in zaki sha ki sha dan Allah na gaji da dure-duren nan na Aunty. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 53_Yana kallon su Saifu ya ce "Ku kai kayan mota.. Bangaren Farida ya kalla a dan sace. "Ku kar6i nata ma.. Kan ya gama har ta nufi hanyar waje janye da katuwar jaka. Uncle din suka kallo. "Dady zamu jima ne dama? Yawu ya had'iya yana mai sake kallon jakar Faridan da ta fuce. "A'a, ana gama d'aurin aure zamu dawo dan Monday zan koma office.. Kai suka kad'a tare da janyar jakar Sultana suka bi bayan Faridan. Tsam yai shi kad'ai a parlour. "Anya yarinyar nan ba wani abu take shirya wa ba kuwa? Ya sani da bata ta6a tafiya da irin katuwar trolley haka ba in zasu. "Ka ce an fasa tafiyar kawai kai kad'ai zaka. Kai ya kad'a, haka za ayi kawai. Waje ya fita,da mamakin shi har ita ake dilka dariya a cikin motar,sai dai suna had'a ido ta juya baya tare da 6ata rai tana kallon wani bangaren. Dan haka sai ya kasa fad'in sun fasa su koma din. Maimakon haka ma sai ya shiga tare da tada mota yana duben yadda ta juyar da kai gefe. "Kwana uku kawai zamuyi,dan kowa ya zauna da shiri.. Shiru nan ma bata tanka ba,dan haka sai ya sake shan jinin jikinshi. Su na sauka Kano a gidan Umma suka yada zango har Faridan. Sosai ta sake suna ta fira kamar yadda ta saba in sunzo hutu fur taki kallon inda yake har ya fuce kama d'aki. Sai bayan magriba ya dawo duk suna tsakar gida har su Saifu ana ta labarin bikin Laila. D'aki ya shiga a zaton shi koh tana ciki. "Ka dawo? Juya wa yai jin Umma, Kai ya kad'a, "Tun dazun naje gun Abba ne. Kai ta jijjiga. "Umma ina Farida? Karasowa tai ciki, "Ai sa6ani ku kai,bata jima da fita ba kanta ke ciwo shine ta tafi nayi ta bari kazo ma ta ce za kuyi waya. Yake yai yana kad'a mata kai. Abinda bata 6a kenan tafiya ita kad'ai sai dai su kaita, ya sani da zafin na yau biyu ne harda na barin bikin Laila. "Umma bari na koma gun Abba toh duk yadda mukai dashi zan dawo kiji batu. Yana fita ya jingina da mota tare da fidda waya yana nazari,iska ya furzar tare da kad'a kai ya hau dailing numbernta. Karfi da yaji so yarinyar nan take ta sa shi cikin tension wanda a da bai cikin shi. Dan tsaki ya yi tare da cire wayar a kunne jin ba'a d'auka ba ya sake dailing. Tsam yai bayan jin ba'a dauka ba. A abu da yawa Farida zai yi wuya yaga fushinta sai wannan, ya rasa meye in ya kira ta da Halima yake kona ranta haka? 'Kishi ne' Fad'in wata zuciyar. Kai ya girgiza,yanzu kenan wannan ne ita nata salon kishin? Murmushi yai yana girgiza kai har hakoranshi suka fito. Da ma zata gane irin matsayin da ta taka a zuciyarshi ne mai shige da Halima wanda har yasa yake kasa banbanci dame ya kirata,Halima koh Farida? Ya sani da daga yanzu ta daina fushi dan ta ciro tuta. Mota ya shiga. Shi kanshi bazai ce ga ranar da kamu da son Farida ba,ya sani da tun a baya tana matukar burgishi barin yarintar ta. "Koh shine son? Zuciyarshi ya tambaya, dan haka kai ya kad'a dan yarda daga haka son ya girma. Wanda a yanzu bai jin zai iya rayuwar nisa da Farida. Dole ya sauke komai ya gurji rayuwarshi kamar yadda Nasir yasha fad'a mishi. Murmushi yai tare da tada mota ya karya kan mota inda zai sada shi ga 'yar mitsilarshi. Nasir ya kira sai dariyar keta yake mishi jin bayanin shi. "Ba fa abin mamaki bane,dan nasha fad'a maka tuni kazo wurin ka kasa kar6a ne kawai,amma 'yar mitsila ta damko wuyanka tamau. Murmushi yai yana kad'a kai. "Ni mamakina a yaushe hakan ta kasance ne Nasir,na kasa sanin rana koh lokaci. Dariya ya sa mishi harda kyakkyatawa. "A'a wannan abu na Allah,wai budurwa da jika 😹.. "Lalumo dai,ni nayi nan,a gaida 'yar mitsila. Kai ya kad'a yana dariyar shakitancin Nasir. *** "Ni abinda ban gane ba Farida wannan uwar jakar da ki ka kin kimo ta lafiya dai koh? Umman ta kallo tare da turo baki. "Ni fa na gama zaman Abuja,bazan koma ba yaji nai.. Galala Umma ke kallonta,kan ta farga Umman ta sau dariya. "Yaji? Kai ta kad'a tana kai ayaba baki. "Ba ke ki ka ce na yarda na taho ba,sauran maganar mayi a nan.. Rai Umman ta had'e "Ke bana son iya shege fa,zatona kin girma ashe har yanzun yarinta na nan bisa kanki.. Ayabar ta ajiye ta hau kukan shagwa6a. "Allah Umma da gaske nake ni fa yaji nayi,gaba daya Uncle baya sona kune baku sani ba har yau komai Halima,duk randa ta motsa mishi haka zai ta ce min wata Halima da nai magana ya hau fad'in shi ba haka ya ce min ba. Ido Umman ta sa mata yadda mitar ta ta kare a kan Halima,in ta fuskance 'yar tata ba ma rashin halartar bikin yafi kona ranta ba kamar wannan. Murmushi tai tare da kad'a kai, lalle kowa da nashi salon kishin,dan haka hannunta ta riko tana murmushi. "Toh naji bai kyauta ba.. "Amma Farida ina ke ina kishi da wacce bata ma duniyar? Baki ta zunguro tana kunkuni. "Toh naji,in fad'a miki wani abu? Kai ta kad'a har yanzun baki a d'ane. "Uncle yana sonki hakan yasa yake danganta ki da Halima saboda ita ce kawai yafi so.. Baki ta saka tana kallon Umman. "Koh ya ta6a kiranki da sunan Fatima koh Jamila? Kai ta girgiza da sauri tana kallon Umman. "Yauwa,toh ki gane kina da matsayi gareshi irin na Halima a yanzun shi yasa yake kasa banbance ku. "In kuwa kinga mutum na kishin ka toh ki tabbatar yana matukar sonki shi yasa bai son wani ya ra6eki koh da kuwa ta kallo ne,dan haka ki d'auka so ne yasa yai miki haka a gun dinner. Tsam tai tana tunanin maganar Umman har Aisha tazo suka kule d'aki Umma na karanta mata dabarun zaman gidan miji. "Toh ta ya Aisha zan tabbatar yana sona kamar yadda Umma ta ce? Zama Aishan ta gyara tana bata darasi. "Ga hanyoyi da yawa da zaki gane mutum na sonki,kin ki kar6a ne tun da,da tuni an wuce wurin... Shiru sukai lokacin da wayar Faridan ta hau kara lokacin da Uncle ya kira. Aisha ta kallo tana nuna mata wayar,kai ta girgiza halamun kar ta dauka. Dan haka sai ta ajiye Aishan na fad'in "In dai yana sonki zai sake kira,in baki d'auka ba zai damu.. Dan haka har yai 2 missed call taki d'auka tana murgudawa wayar baki kamar Uncle din ne. "Toh daga nan fa Aisha mey zanyi? Murmushi Aishan tayi,tuni fi'ili ya tashi ta hau zayyana mata abinda zasuyi koh Uncle yazo biko. Da wannan ta tashi tai wanka tare da da sauya kaya. *** "Bissmillah man... Maganar Abba suka jiyo a parlour lokacin su na d'akin Umma,da sauri suka leko da kai cikin sand'a. Baya sukai da sauri Faridan na zaro ido had'i da dafe kirji. "Uncle?.. Kai Aisha ta jijjiga tana dariya,cikin rad'a ta ce "Ba na fad'a miki ba.. Leka wa suka sake yi,da sauri suka komar da kai ganin uncle din na dan satar kallon corridorn kamar mey son ganin wani abu. "Muje..muje. D'akinsu suka shige da sauri tare da rufo kofa. A gaban mirror Aisha ta tsayarta ta hau gyarata har dasu powder. "Toh meye hakan kuma? Harara Aishan ta sau mata lokacin da ta tuje dankwalin kan nata. "Ki sa ido,koh a haka zaki je koh powder babu in an ce Uncle yazo? Galala take kallonta, dan haka bata bi ta kanta ba ta cigaba da gyarata kamar wata 'yarta a gaban mirror. Zama sukai da sauri jin an kwankwasa d'akin. Abba ne,dan haka tashi Aisha tai tare da bud'e wa. Da dan gudu Faridan ta nufe shi dan murnar ganinshi yana mata murmushi. "Ki je ga chan mai gidan ki a parlour zai tafi,ki taho da abin sha. Kai ta kad'a mishi tana duk'ar da kai wai ita kunya har ya kauce. Aisha ta kallo,da sauri ta doka tsalle har da bawa Aishan hannu su ka tafa. Shi da Abba ne a parlourn, dan haka a nutse su ka shigo kai a kasa rike da faranti da abin sha da Umma ta jera musu. Ido ya sa mata tukunna ya d'auke kai yana ma Abba yake. Gaishe shi Aisha tayi yana tambayarta makaranta lokacin da Faridan ke tsiyaya mishi ruwa a kofi. Duk sai ya ji yau ya bala'in takura a gidan abokin nashi kuma siriki barin ganin Faridan. Murmushi yake lokacin Abba na tayashi murnar su Umma. Tashi tai tare da dan duk'awa rike ruwa a hannu zata bashi,kalloshi tai ta gyalen yana iya kallo gashin da aka gyara a gefe. Yake yai mata tare da mika hannu zai kar6a,a hankali kamar mai yin rad'a ta ce "Ni fa bazan koma ba. Ido ya sa mata, a hankali ya bar murmushin baki sake ya marairaice fuska. Ruwan ta sa mishi a hannunshi tare da juyo tana wa Abba murmushi shima ta bashi kamar ba ita ba. Yake yai wa Abba ganin sun tashi yana mai kai ruwa baki,a san sace ya kallosu zasu shige Aisha na dan mangarar kafad'ar Faridan itama tana ramawa kamar yadda suk saba tun yarinta. Ruwan ya ajiye tare da kallo Abba yana jijjiga mishi kai ba wai dan ya gane mey yake nufi ba. Wannan shine ga koshi,ga kwanan yunwa 😜. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 54_"Kashe wayar da sauri dan koh ya kira yaji a kashe kinga mun kara mishi tension.. Marairaice wa Faridan tai tana langwa6e kai "Uncle ne fa,Allah har naji tausayin yadda yai dazun. "Mtsww... Tsaki Aishan tayi tare da warce wayar ta kashe tana harararta. "Baki shirya kwatar y'ancin bane ina ga 'yar dad'i Uncle.. Kai ta girgiza da sauri. "Ni fa tausayi kawai na ce miki nake ji kar ki min fassara. Hakan kwa akai,koh da ya tashi tafiya duk da Abba ya ce a kira suyi sallama ya ce a'a zai kira kawai dare ya yi. Har ya gama komai ya kwanta yana tunanin gashin kumar Farida. Wayar ya sake gwada wa har lokacin a kashe,ba yadda ya iya dan haka a hakan ya kwana da abin cikin ranshi. Washegari ma a kashe,dan haka tun tara ya isa gidan Umma achan suka karya ya jira duk suka shirya. "Dady kaimu gidan su Aunty Farida.. Sultana ya kallo yana murmushi,kamar mai jira da sauri ya kad'a mata kai. "Ok,muje toh. A mota Saifu ya ce "Ta huce Dady? Juyo wa yai kad'an yana tuki ya kalloshi tare da kad'a kai. "Ku tayani lallashi ta ce baza fa ta bimu mu koma ba,just imaging. Ido suka zaro "Ina d'in Dady? Ajiyar zuciya ya sau tare da furzar da iska. "Gidan mu.. Dariya suka fara kunshe wa,dan haka da sauri ya juyo yana dan duban su tare da koma wa yana kallon hanya tare da fad'in "Ya Rabbi...Please Guys,be serious..please. Kai suka kad'a mishi. Su na isa ya kallo su,yake suka mishi,sai yai ajiyar zuciya, yana fatan in taga su Saifu a wuce wurin su wuce jibi gida. A waje ya tsaya su kuma shige dan ai mishi iso. Abba ne ya fito da halamun fita zaiyi. "Kullum tamkar bako ka ke,koh zanyi wa kowa iyaka da gidana banda kai abokina. Murmushi Uncle din ya yi lokacin da suke shiga. Daga su Saifu har Faridan ba wanda ya gani,dan haka sai ya fara ware ido. Magana Abban yai ma Umma tare da cewa uncle zai je baya ya dawo,Umma ta tafi fad'o ma Faridan ta shirya zasu fita inji Uncle. Yaran ne suka fito sai ware ido yake yagan su tare. Da ido yai musu halamun ta huce? Kai Saifu ya girgiza yana marairaice fuska halamun bata huce ba. Iska ya furzar, toh mey take so ya mata? Kusa dashi Saifu ya dawo ya zauna. "Dady ga shawara.. Zama Uncle din ya gyara yana kallonshi. "Idan budurwata ta 6ata rai abu uku nake ta huce har tai dariya.. Kai Amjad ya hau kad'a mishi yana fad'in "No.. Amma sai Saifun ya hararoshi halamun mey a ciki? Hannu Amjad yasa tare da dafe kai jin Saifu ya tuni asiri. Ido Uncle din ya zaro da sauri. "Saifu? Budurwa fa? Dan matsawa Saifun ya yi yana sosa keya tare da kad'a kai halamun eh. "Oh no.. Ido Uncle ya k'ank'ance tare da fad'in "How old r you?.. Yake Saifun ya yi yana kallonshi kamar ka ce kule yace chass. "I'm 14.. Baya Uncle din ya yi yana rufe ido tare da dafe kai ya furta "Saifu... Matso wa Saifun ya yi yana dariya tare da dafa hannun Uncle din "Common Dady, I'm only trying to help you out,amma shikenan ba ruwana. Ido ya sa mishi,dan haka da sai abin ma ya bashi dariya. Wai Saifu da budurwa? Ya ilahi. Sosai yai dariya,yasan yaranshi tamkar abokai suke gunshi,wannan ba wani abu bane dan Saifu bai boye ba,amma shi dariyarshi kamar Saifu mey zai iya fad'i ma budurwa? Fatanshi Allah ya tsare mishi su,dan yanzun ne yake da kalubalai tunda har sun fara sanin wannan. Magana yake shirin yi sai ga nan su Faridan sun fito,zama ya gyara yana kallon fuskar Faridan. Gaisuwa kawai ya samu,duk da ba karamin kyau yai mata ba dan da farko har ido ta zira mishi Aisha ta zungureta kamin ta saita kai tana chunno mishi baki. "Muje koh?. A dirare ta kalloshi kamar gaske tare da tashi ta fad'awa Umma. Tare suka fito Uncle din yai mata sallama suka fita. Yau Uncle harda bud'e mata kofa ma'ana ta shiga,yake tai mishi sai ta bud'e baya ta shige sai Nass ne ya shiga. Tuki yake in banda dariyar su ba abinda ka ke ji da ya tsomo baki sai ta gimtse fuska. Iska ya furzar yana yana girgiza kai,shi gani yai ma kamar yaran suna a bayan Faridan,dan ba mai sako shi cikin firar har suka isa gidan Abba. Duk sun fuce sai ita ta rage bayan ta fidda Sultana. "Farida.. Juyo wa tai a dirare tare da sa mishi ido. "Subutar baki ne fa.. Marairaice mata ya yi tare da karkata kai "I'm sorry... Yake tai mishi tare da saurin gimtse wa ta fuce. "Farida..Farida. Koh waiwayo wa batai ba ta isa ga yaran suka shige gidan Abba. Iska ya furzar, yarinya karama tana wasa zuciyarshi? Kwafa ya yi,yasan abin yi. Motar ya kashe tare da shiga gidan ranshi duk ba dad'i. Sai dai ganin su cikin walwala tare da su Abba yasa ya sake jin Abban sai sanya wa iyalanshi albarka yake ganan Farida kanta kasa tana murmushi tare da fad'in "Amin Abba. Bangaren Umman su Uzairu suka nufa ita da su Saifu. Murmushi Abban yai yana mai kad'a kai "Kayi dace Kabiru,iyalin ka yarinya ce,amma tana da hankali sosai musamman in naga kusancinta da yaranka nasan akwai kyakkyawar mu'amula a tsakanin su,Allah yai albarka. Murmushi ya yi yana kallon bayan su su Faridan dake tsakiyar su Saifu suna magana kasa-kasa tare da kallo Uncle din halamun dashi suke. "Amin Abba,ya k'afa? Kai ya jijjiga, "Alhamdulillah, maganin da ka aiko yana min dad'i in na shafa,Allah kara bud'i. Murmushi Uncle din ya yi yana kad'a kai "Amin Abba. Shiru sukai kamin daga bisani ya ce "Ni fa Abba yau da daddare nake so in son samu ne a mayar da auren nan gobe Umma ta tare hankali sai yafi kwanciya. Murmushi Abban yai yana gyad'a kai, "Mey Umman naka ta yanke? In ta aminta duk yadda kai dai-dai ne Kabiru.. Baki ya wage yana murmushi. "Itama haka ta ce Abba,naji dad'i bari Abban Uzairu yazo a tsara komai kawai. Da murna ya nufi bangaren su Umman Uzairu. Bayan sun gaisa baki yaki rufuwa yake sanarta abinda suka yanke. Murmushi tayi tare da kad'a kai. "Allah yaso Kabir,ubangiji ya nuna mana,naji dad'in wannan lamari tun kwanaki a gun Abban ku. Su Farida ya kallo wanda suke murnar jin da abinda yazo,ido ya sa mata yana murmushi ganin yadda take juya hannunta cikin magarya ta kasa sha. Alfarmar komen su Umma yasa ta mayar mishi kanta duk'e. Tashi Umman tayi dan kawo musu ruwa su Saifu ta kira suka bita amsar magarya wai su bar ma Faridan wanchan. Matsowa yai kusa da ita yana dan kallo waje yana murmushi. "Ba koh tayi. Kai ta dago tare da turo baki ta janye kwanon ganin zai tsoma hannu. Fuska ya marairaice, "Wai dama baki hak'ura ba har yanzun? Kai tai saurin girgiza wa tare da fad'in "Eh,ba zan koma ba ni ka matsa kar Umma ta shigo. Ido ya sa mata ganin yadda take k'au da kai halamun baza ma ta kalleshi ba. "Amma na ce kiyi hak'uri fa Farida,kina da rigima fa.. Kalloshi tai da sauri, "Koh? Kai ya girgiza, "A'a, ba wannan ba,yanzu fad'a min meye matsalar sai na gyara? Kai ta girgiza halamun bazai iya ba koh ta fad'a. Da mamaki ya kallota. "Mey yasa toh? Ido cikin ido ta dubeshi,ba zato ya ji ta ce "Saboda ba ka sona... Baki ya saka yana kallonta da mamaki. Jin ta kwafsa yasa da sauri ta gyara. "I mean baka damu dani ba,amma ban ce ni dole a soni ba fa... Murmushi ya yi yana kallonta,sai yanzun ya gano bakin zaren. Matsawa ya sake yi kamar mai neman shige mata,dan haka da sauri ta ja baya rike da kwanon magarya tana sake chunno baki. Kwanan yai saurin riko wa yana kallonta ganin yadda take kautar da fuska gefe. Juyo wa tai tare da kallonshi,kam ta sake riko kwanon da hannu biyu yana ja tana ja kamar wasu yara yana murmushi. Da karfi taja har tana ciccije wa dan haka sai ya taho tare da sakar magarya ta zube a tsakar ledar. A tare suke bin magaryar da kallo wacce ke tsere bisa ledar d'aki. Kalloshi tai,dan haka sai ya daga mata kafad'a yana ta6e baki halamun ba ruwan shi. Fuska ta hau shagwa6e wa kamin ya farga har ta sa mishi kukan karya tana nuna magaryarta. Ido ya zaro yana mai kai hannu bakinta halamun tai shiru yana kallon waje halamun kar aji. Da sauri ya fara tattaro mata yana zuba wa a kwanon tare da fad'in ''Shhh,i'm sorry,bari na kwashe Cikin rad'a. Kukan ta tsaida tana kunshe dariya tare da mishi gwalo,jin ta daina yasa ya dago,da sauri ta sake d'aye baki tana nuna sauran magaryar tare da fad'in "Ummma... A hankali cikin rad'a ya ce "Farida,I said i'm sorry... Yana kallon kofa jin wannan karan mai sauti tayi. Da sauri ya hau tattare wa yayin da ita kuma take kunshe dariya ganin yadda ya dukufa cintse magarya da ya juyo zata sake sakar kukan shagwa6a tana nuna magarya tare da kiran Umma. "Lafiya kuwa? Kai suka daga da sauri ganin Umma dasu Nass a bakin kofa kowa rike da kofi da magarya aciki. Faridan ya kallo da dan harara kad'an ganin tana kallon Umman Uzairu. "Umma magaryata fa ya zubar min. Uncle su Umman suka kalla yadda yake tsincewa yana dan harararta halamun ta tara mishi jama'a. Murmushi Umman tayi tare da girgiza kai ta juya ta bar wajen,a ranta sai jinjina wa Uncle yake,wato auren yarinya sai ya sa ka dawo yaro. Kai ta kad'a tana dariya tuno yadda ya dukufa tsina, lalle aiki ya samu manya. Sosai take son Farida,dan fa abinda 'yarta ta kasa gashi ita tana yi aciki kuwa harda kula da su Saifu. Juya wa tai tare da sake kallo bakin kofar jin dariyar su Saifu suna kallon cikin d'akin, kai ta girgiza itama tana yin tata kasa-kasa cike da jin dad'i, fatan ta Allah yasa farin cikin iyalin Kabir ya d'aure. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 55_Gaba d'aya ya tattara tare da mika mata daga ita har yaran yana dan hararar su tare da kunshe tasa dariyar yana zama. Faridan ya kallo wacce ke dariya, kai ya kad'a,koh ba komai yaji dad'i da a dalilinshi take dariyar. D'ukawa Sultana tayi tare da juye tata magaryar a ta Farida tana dariya ta zauna. D'aya bayan d'aya suka zo suna juyewa tare da zama suna dariya. Circle suka had'a,dan haka sai ta turo kwanon tsakiya dan kowa ya iya samu ya sha. Murmushi ya yi tare da kai hannu zai d'auka ta dan janye tana murmushi. Kai ya langwa6e mata,dan haka sai ta dawo dashi kowa ya fara sha suna tara kwallo a gefe cikin kofi. "Dady ka shuka mana bishiyar magarya a gidan mu muna ci kullum akwai sweet.. Dariya suka sa ma Nass har Uncle din Farida yana kad'a kai. "Toh Abbana,kar kaji komai,amma kamin nan koh taro min shi kar ya wuce zazzau.. Hularshi ya cire tare da bawa Amjad ya tare bayan Nass da ita suna dariya. Faridan ya kallo lokacin da take sanya wa Sultana a baki tana shirin cizonta cikin wasa tai saurin janye hannun tana yarfe wa. Murmushi ya yi tare da kallon hannun yana mai jin wani abu na tsirga mishi bisa jini da bargonshi. Farida tabbas farin ciki ce a cikin gidanshi Allah ya bashi kyauta dalilin wuya da yaci da yaranshi a baya. Tabbas lokaci ya yi da ya dace ya cike sauran gurbin da ya rage bai cike ba. A dan sace ya kallota cikin wani yana yi,tai mishi kyau sosai cikin attamfa mai riga da skirt tasha d'aurin turai 'yar adu'a pink dan haka sai ta haska mashi ita tamkar Zahra kusa da wata. Kai ya kad'a tare da sake sanya hannu dai-dai ta kawo nata har hannun nasu na karo da na juna. Yatsan ya riko yana kallonta cikin wani yana yi. Da sauri ta kallo su Saifu duk hankalin su baya kansu sai daga kai duke suna cilla magaryar tana fad'awa bakin su Sultana na musu dariya. Kiciniyar kwace wa ta fara ya rike yatsun kam kamar zai cire su. Kan farga har ta tsuguna tare da kaiwa hannun nashi hakori tuni ya cika da sauri yana yarfe wa. Yake tai mishi tare da 'yar harara tana sanya magaryar a baki. Kai ya jijjiga yana kallonta tare da kai wajen da ta cija bakinshi yana dariyar zai kamata ne. Fari tai da ido tare da lumlumshe mishi ido tana murmushi. Magarya ya hullo mata guda d'aya dan haka da sauri ta bud'e ido tare da ware su kanshi. Su Saifu ta kallo tare da daga mishi gira,da sauri ya daga mata kafad'a halamun ba shi bane. Kai saukar yana kok'arin diba ta hullo mishi itama d'aya. Dago wa yai tare da shima daga mata gira,dan haka da sauri ta daga kafad'a itama halamun ba ita ba ce. Tsaye tayi tana musu murmushi ta window bayan taga komai,kila da yanzu ita ce tare da iyalan nan masu matukar ban sha'awa ba dan zuciya data rinjayeta ba. Hannu ta kai tare da goge hawayenta,ta nufi cikin d'akin da sallama. Tuni tamkar anyi ruwa an d'auke haka kowa ya gimtse fuska suna ganinta har Uncle din. Kasa tai da kai,tuni taji ta sake muzanta,kunya ta rufeta,ta sani da taci amanar 'yan uwan taka tsakaninta da Kabir tun ma kamin a tsallako 'yan uwantakar da koh a musulunci babu kamarta. 'Uwa d'aya, uba d'aya ya wuce wasa,amma tai fachali da wannan ta muzgunawa yaran 'yar uwarta halaliya. Hawaye ta goge tare da sake kallo su. Da mey ta karu yanzun? Ribar mey taci bayan wannan? Kai ta girgiza dan tasan babu,sai ma tsangwama da

Chapter 13 of 19