Share this page
zai zo da sauki. Da sauri Aisha dake la6e ta koma ta corridor ta shige d'akin su. A gaban madubi ta samu Farida sai tazar kai take ta kama tashar gata cikin gidanta. Duka ta d'ad'a mata a hankali,dan haka a furgice ta kallota tana sosa gun. "Lalle wallahi an gama dake na rantse Fadila. Ido ta zaro. "Mey aka min? Zama Aishan tayi tana kad'a kai. "Tab,wallahi an cuce ki,kin san wa aka baki? Kai ta girgiza tana kallonta. Dariya ta fashe dashi tare da fara mata wakar _'Yarinya an cuce ki an had'a ki da tsoho,tsoho sa'an Abban ki shi zaki aura_'. Tsaki tayi tare da tashi, "Toh meye abin dariya? In zaki fad'a min ki fad'a min ni waye tsohon? Dariya ta sassauta tare da gyara zama. "Wallahi kin tashi a aiki,kin san wa Abba ya baki da ki ka yarda? Kai ta girgiza har ta fara tsorata. "Waye dan Allah Aisha?. "Uncle din Abuja fa.. Shiru tayi tare da kafe Aishan da ido,kan ta nufa har ta kwalara kara mai karfi tare da doka tsalle ta rungume Aishan cikin murna. "Ki ce Abuja za'a kaini? Wayyo dad'i... Baki sake Aisha take kallonta cike da mamaki. "Anya Farida kina da hankali kuwa? Koh ba kiji abinda na ce ba? Kai ta girgiza mata cikin murna. "Naji sarai,toh meye aciki? Galala take kallonta,da gaskiyar Umma,lalle Farida d'anya ce sharaf. "Uncle dan gayu ne,ga yaranshi y'an gayu masu kyau,ga garin ma na y'an gayu,ranar naji Abba na mishi murnar ya koma sabon gida irin na y'an gayu,toh meye aciki? Allah ba'a cuceni ba... "Lafiya kuwa? Abba ne a bakin kofa jin ihun Faridan. Nutsuwa tayi tare da dakko gyale ta yafa tare da bud'e mishi tana sunke kai kasa. "Lafiya Abba,kawai ban san nayi bane.. Harara Umma tayi tare juyawa d'akinta tana fad'in "Ta tsorata ni wallahi, ina band'aki na fito. "Kin girma fa Farida,dan aure za'a miki,dan Allah ki nutsu. Kai ta sunkuyar tana fad'in "Toh Abba na daina. Kai ya kad'a, "Yauwa ki kintso kizo ga Uncle din ku na Abuja ku gaisa. Kasa ta kara yi da kai wai ita kunya,yana bada baya tai saurin komawa ciki. "Uncle ne ashe Aisha dazun yazo,Abba ya ce muje mu gaisa. Kallon baki da wayo Aishan take mata tana dariyar keta. Tsam tayi,tare da sa hannu biyu ta rufe fuskarta halamun kunya. "Aisha kunya fa na fara ji,ya zamuyi? Baki ta ta6e, "Baki ma fara ba,sai kin shiga daga ciki,kizo muje dan bacci nake ji. Kai ta kad'a harda gyara gyale a mudubi, hannunta Aisha ta janyo kamin ta bar gun suka fuce. Shi kad'ai ne a parlourn ba Abba,dan haka kai a sunke suka tsuguna tare da gaishe shi a tare. Murmushi yai yana duben su,abin ma sai yaso ya bashi dariya ganin yadda suke wani sunke kai. A hankali ta dago da zummar satar kallonshi sai karaf suka had'a ido. Dan haka da sauri tai kasa da kai tare da sake janyo gyale ya rufe mata fuska tana kunshe murmushi. Kallonsu yake,har ya ma rasa mey zai ce dasu dan rashin abin fad'i. Kai ya kad'a, tare da fad'in "Aji nawa yanzu ku ke Farida? Gefen gyalenta ta rike tare da zungurar Aisha yana kallonsu,da sauri Aishan ta ce "Jss3 muke. Kai ya kad'a tare da fad'in "Good". Shiru sukai,sai dai yana kallon yadda suke dan kus-kus ta kasa duk da baya jin komai. Murmushi ya yi,ganin kamar sun takura yasa ya ce "Toh ni zan tafi,kuyi ma Abban ku magana. A tare suka mike suna fad'in toh. Yana kula da yadda suke zungurar kafad'un juna halamun musu suke,yana kallo Faridan ta dan juyo tana magana wa Aisha,ganin yana kallonsu sai ta kara sakar gyale da sauri suka kule corridor. Kai ya kad'a yana yar dariya mai sauti. Lalle ya sani da aiki a gabanshi ba kad'an ba. Dan wannan wani sabon raino zaiyi ba wai zaman aure ba in har yai la'akari da shekarunta dana Saifu ba wani nisa su ka bashi ba. Sannan har yau rainon Saifu yake da k'annenshi ta fagen yarinta. Murmushi ya yi,amma koh ba komai yarinyar tana burgishi da wannan dan rawar kan nata,yasan za ai ta buga drama a gidanshi da Farida. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 29_Tun daga wannan ranar ya dage da tsantsara ginin Abbanshi da yake so a gama kamin hutun su Saifu ya kare. Da shawarar Abba yake zuwa wai fahimtar juna gun Farida,sai dai fa kullum daurewa yake amma gaba daya gidan ma wani iri yake mishi,barin ganin Umman su Faridan sai yaga kamar girma ya fad'i. Yau ma kamar koyaushe daga shi sai ita a parlour kanta kasa kamar kullum tana murmushi. Allah yaga tana son kwalliyar Uncle da turarenshi,har mamaki take in Aisha na tsokanarta akan zata auri Uncle tsoho. Kai ta dago dan sake karyata Aisha,da sauri ya fara danna waya ya bar kallonta. Sarai yasan da kallonshi take dan haka sai yaki dagowa. A ranta fad'i take "Aisha bata san kyau da tsufa ba,in za'a batta zata ce Abban su yafi Uncle tsufa Allah,dan Uncle dan gayu ne barin yanzu da ya sanya suite tamkar balarabe ya zamar mata. Ga dan sagen nan da wani hasken kyau na fulani da jin dad'i da ya k'awata fuskar. Murmushi tayi tare da dan duk'ar da kai tana murmushi, kallota ya yi a dan sace ta cikin farin glass nashi,komai irin na Farida na burgeshi,barin wannan y'ar kunyar da yanzu ta koyo takan bashi dariya in ya ke6e. Murmushi ya yi tare da kad'a kai,tare da fadin "yarinta dad'i A zuciyarshi. Kai ta sake dagowa da zummar sake kare mishi kallo sai karaf suka had'a ido,ganin yadda ya tsareta da idanu yasa da sauri ta janyo gyalenta tana rintse ido tana yarfe hannu halamun ya kama ta. Kai ya girgiza yana murmushi, gaba daya wata dabi'ar ta Farida irin ta yarintar Halima ce musamman wannan yar kunyar shakiy'ancin. Gyran murya ya yi tare da gyara zama. "In munyi tafi Abuja dake zaki cigaba da karatun ki a boarding koh day ki ke so? Kai ta dago tare da kallon wani waje halamun tunani yana kallota ta gefen gyalen. A dan sace ta kalloshi tare da fad'in "Kowanne ina so.. Kai ya kad'a,wani sa'in ba laifi ashe Faridan. Ita kam tunaninta dama ta ce 'Day', dan in ta tafi boarding wa zai na share mata gida da bawa su Sultana abinci? Kai ta girgiza halamun babu. "Bani ruwa in ba matsala... Kalloshi tayi tare da kallon ruwan,a gabanshi yake tasan hannu kawai zai mika ya dakko,sai dai ta tashi a hankali tare da tsiyaya mishi kai duk'e ta bashi. Har ya kar6a ta kasa tashi jin ya ce ta tsaya. A durkushen take kallon yadda yake dan zukar ruwan yana latsa waya,tuni har ta fara mamakin wannan sarauta ta uncle,ruwan ma sai an mishi gayu? Tana nan tsugune har ya shanye tare da bata kofin ya mike. "Hope kin fara shiri koh? Kai ta duk'ar tana girgiza kai. "Toh in kina da bukatar wani abu ki min magana dan ina son mu koma tare ne dan chuku-chukun makarantar ki. Kai ta kad'a mishi idonta a nashi,dan haka sai ya d'au mukullinshi tare da daga mata hannu halamun bye. Murmushi ta k'akalo tare da dan daga mishi nata yatsun tana yake, "Ki ce ma Umman ku na tafi toh,ga nan na bar miki wani abu koh zaki nema dan abin yi. Kai ta daga,tare da fad'in "A gaida su Sultana..Na gode. Cikin sanyin murya. Murmushi ya yi tare da kad'a kai ya juya. Jiki a sanyaye ta koma ta rasa dalili. D'akin Umma ta kwankwasa jin an ce ta shigo ta shige, a bak'in gado ta sameta tana shirya wasu kaya wanda tasan duk nata ne na biki. Kud'in ta ajiye mata tana dan ta6e baki halamun kuka,dan haka sai Umman ta bar abinda take ta zuba mata ido. Tun ranar chan Umman ke fushi da ita,bata so tai aure Umma bata so ba,dan haka kasa ta zube tare da daura kanta ta sau mata kukan shagwa6a. Aikinta ta cigaba da yi ta manna mata,sai dai jin tana "Toh ni har na daina murna,ki ce wa Abba kawai a fasa auren. Murmushi tayi,tare da dagota ba koh hawaye sai matse ido take. "Za kiyi kukan gaske yarinya,ba rawar kai ba? Kwafa tai mata tare da fad'in "Bana kin aurenki, tausayinki kawai nake ji Farida.. Kafe Umman tayi da ido. "Tasayin mey toh Umma? Koh kema dan an bani tsoho ne ki ke tausaya min irin na Aisha? Kallonta kawai take,sai tai murmushi tare da kad'a kai. "Baza ki gane ba,ke dai Allah sa ya tausaya miki... Ido ta zaro cikin tsoro tare da fad'in "Wa din Umma wai Umma? Kai Umman ta girgiza. "Ba kowa su6utar baki ne kawai. Ajiyar zuciya tayi tana taya Umma aikin, kad'an-kad'an take duben y'ar tata tana murmushi, wani sa'in har mamakin rashin wayo irin na Fadila take,batta a bankaura da rawar kai amma sam ta rasa rashin wayo irin nata na yaran yau in tai la'akari da yadda duniya ta dawo. Dole zata daure ta cigaba da zamawa su Farida k'awa har sai ta koya mata dawar garin,yanzu dai tasan bazata fahimci komai ba. Murmushi tayi tare da kallonta jin yadda take tsara shirmenta na auren. **** Wata guda ya debe ana aikin bangaren Abba tare da tatsa katanga a tsakanin gidan da inda su Tabawa suke dan cike umarnin Abban. Ta bangare biyu kowa ya kid'ime da shirye-shiryen auren uncle da Farida. A yadda suka tsara ba wani taro sai d'aurin aure da tafiya da amarya kawai. A cewar Uncle shi ba abinda yake da bukata dan komai ya shirya shi cikin sabon gidanshi tamkar da mace a ciki. Abu d'aya ya ce zasu iya kara mata kayan kitchen in tana da murad'i. Kallon Farida Umman take,ganin yadda ta kama tasha,tun jiya tana fuskantar ta yadda duk tai la'asar,ga dai kayan lefe amma koh murna bata yi,fatan ba Aisha ba ce ta sanarta komai. Takan rasa ta ina ma zata fara? Koh dan irin gyaran nan da iyaye ke wa yaransu Umma ta kasa dan tausayin Farida.. Ido ta sa masu ganin sun fashe da kuka ita da Aisha suna kallonta. Da rarrafe Farida ta zo gare ta tare da kwanciya bisa cinyar Umman. "Ni fa sai yanzu na gane bani da wayo,Allah Umma bana son na barku. Kai ta girgiza mata, "Ai zaki na zuwa kar ki damu,kowa da haka ya saba. Kuka take ita dai in ta tuna kwana kad'an za'a maidata Abuja da zama. Dakyar ta rarrashe su ita da Aishan sukai shiru. ***** Kowacce tai tagumi tana tunanin rabuwa da y'ar uwarta gobe iyanzu. Duk baki suna waje in banda su,dan haka tashi Aisha tayi tare da rufo kofar da mukulli ta dawo kusa da Farida. "Kin san mey Farida? Kai ta kad'a fuska a maraice. "Kawo kunnenki kiji wani abu da dabarar yi. Kunne ta bata,tiryan-tiryan ta fara zaiyano mata abubuwa tana zaro ido gabanta na fad'uwa. Da sauri ta kallo Aishan rai had'e. "Ke uncle d'in an fad'a miki d'an iska ne wai? Harara Faridan ta sau mata, "Toh shikenan in baki yarda ba wallahi haka na karanta. Jim tayi,da sauri ta fara kad'a kai. "Gaskiya ban yarda ba,wannan ai iskanci ne ma. "Mtsww.. Tsaki Aisha tayi tare da harararta. "Wa ya fad'a miki iskancin ne? Toh wallahi zakiyi bayani. "Ba aure ba? Kwafa tayi tare da kad'a kai "Zaki ce Aisha ta fad'a miki... Ido ta fara warewa yana raina fata, "Dama haka ne auren? Baki Aisha ta ta6e "In banda Umma da ta hanani ai da tuni na fad'a miki. "Kai,ina,uncle bazai haka ba Allah Aisha, tab...da kwa nai mishi ihu wallahi.. "Mtsww.. Wani tsakin Aisha ta kara, "In zaki nutsu ki ma nutsu wallahi. Gaba daya ta tsorata ta,dan haka tuni ta fara neman hanyar bullewa. Murmushi take mata jin abinda take karanta mata wanda a ganin su shi zai bullar musu. Hannu ta bata tare da tafawa suna dariyar keta. "Ba mai miki wayo in kinyi haka Allah. Kus-kus dinsu suke su kad'ai ba mai jin kansu, duk da a zahiri Faridan na jin dan fad'uwar gaba in ta tuna da bayanin Aisha. Da wannan suka kwanta zuwa gobe d'aurin aure. *** Washe gari *RANAR D'AURIN AUREN UNCLE da FARIDA* Kusan wannan auren ya kusa da farkon shi dan ya tara jama'a. Y'an aikinsu na Abuja da Kaduna kusan duk sun halarta harda Aunty Rabi. Yai farin cikin auren,in yai la'akari da yadda karan nan Abbanshi ya sanya albarka ya kuma tako har kofar gidan su Farida. Dan haka baki har kusan kunne yake washe shi,haka ya dinga bi yana nuna wa y'an aikinshi Abbanshi suna gaisawa. Matsala daya ya fara fuskanta ita ce ta tuburewar su Saifu tun jin zai yi aure a yau,yai lallashin abanza amma Saifu da Nass sai kuka suke,yasan zasu ware in har suka ga wace ce amaryar,dan haka sai ya kyalesu ba tare da ya sanar su ba. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 27_Murmushi Abban ya yi jin shawarar Umman,kai ya kad'a. "Banki taki ba Umman su,amma ni ina da tawa shawarar in har kin aminta. Kai ta gyad'a "Ki kira min yaran nan tukunna. Ba musu ta tashi tare da kwankwasa d'akin su Farida,ciki ta shige tare da zama. Kallonsu take d'aya bayan d'aya kamar yadda su ka sa mata ido. "Aure ba abin ki bane,dan baida wani aibu acikin shi Aisha.. Kallo Umman Aishan tayi, tuni har idonta ya fara kawo ruwa. "In karatu ne ana iya yi a gidan miji, sannan ga dimbin lada dake cikin shi ga na biyayya ga iyaye. "Ki ma Allah Aisha kar ki bani kunya a gaban Abban ku komai ya ce kiyi na'am... Bata jira mey zata ce ba ta ce su biyo ta. Kai sunkuye tana hawaye Abban ya kallo ta, "Aisha wannan ya nuna min bazaki iya sharen hawayena ba tun yanzun da nake so ki share koh? Kai ta girgiza tare da fad'in "A'a. "Toh meye matsalar? Umma ta kalla hawaye na zubar mata. "Ni zaki kalla kar ki kiji komai ki fad'i matsalarki. Kai ta sunkuyar tare da fad'in "Kai hak'uri Abba,wallahi bana son aure yanzu Farida ke so,dan Allah Abba kar amini dole. Kuka ta fashe dashi sosai,dan haka sai Abban yai tsam. "A'a, ni fa ba muyi da kai zaka tsaya tambayar ra'ayi ba Abban su,kowacce ka isa da ita,itama Aishan fad'a kawai take. Kai Abban ya girgiza. "A'a Sumayya, a bi a hankali. Farida ya kallo da take harar Aisha,ita tun a d'aki jin Umma ta ce ba komai a aure take Allah-Allah Aisha ta amince. "Farida.. Abban ta kallo tare da amsawa. "Kin shirya amsar tayina na aure yanzu?.. Kai ta kad'a da sauri duk da tana kallon yadda Umma ke girgiza mata kai halamun ta ce a'a. "Umma yanzu fa ki ka ce 'Aure ba abin ki bane,dan baida wani aibu acikin' koh? Banza Umman ta mata,dan haka sai ta dawo kan Abba dake mata murmushin jin dad'i. "Ni Abba ka min Allah ina so in dai za'a bani kayan d'aki da komai zan zauna,meye aciki? Ina so Allah.. Kai ya kad'a yana kallon Umma da sai harara take mako wa Farida, "Toh Alhamdulillah, na gode Farida,zan miki komai kar kiji komai har kayan kitchen. Aisha ta riko tare da fad'in "Wayyo dad'i" Cikin murna. "Na gode Abba,wayyo Allah Aisha. Hawaye Aishan ta goge tana kallon Umma da kamar ta rufesu da duka gaba daya dan haushi,sai ta marairaice mata. "Abba yaushe za'a daura toh? Gaba d'aya ido suka sa mata har Umman,ita kam koh ajikinta Abba ta zubawa ido jiran amsa,basu nufa ba suka ji Abba ya kece da dariyar jin tambayar Farida,dan haka da sauri Umma ta ce "Tashi ki bar wajen nan marar hankali kawai.. Tashi sukai har da dan tsallen murnar Farida,ita kam Aisha dariyar mugunta ta fara mata. "Lalle muguwar d'anya ce ke wallahi Farida. A gado suka zauna tana lissafin abin yi. "Naji dai wallahi nafi ki wayo yarinya. Dariya Aisha tayi. "Wai,wallahi har na hasko ki a gidan miji, zai debi abu. Zama ta gyara. "Bama wannan ba,tukunna kinsan wa za'a aura miki da ki ka amince? Baki ta ta6e "Oho,ni dai aure kawai. Kai Aishan ta kad'a. "Za kiyi bayani, sai kinje zaki gane abinda nake gudu wallahi.. "Za muyi anko kuwa Aisha? Harara ta sau mata. "Au baki ma jin abinda nake fad'a kenan? Kallonta tayi, "Mey ki ka ce? Banji ba ina lissafi. *** "Ka kara lale Abban su,ka duba abinda Farida take shi kad'ai ya isa nuna ma ba abinda ta sani sai hauka wallahi.. Karasa wa tayi tana goge hawaye. Murmushi yake yana duben Umman. "Bana jin munyi haka dake Sumayya,dan haka kar ki maida min hannun agogo baya. Tayi takaici tai komai amma agun Abba aure kamar anyi an gama. Dan haka sai ta sa musu ido har Faridan taga iya gudun rawarsu. **** Kwance yake a rigingine bisa gado ya zubawa fankar dake kad'awa a sama ido. Tabbas tarin arziki da yake samu a yanzu baiyi ba mud'in ya kyale mahaifinshi a gidan kasa na shekara da shekaru. Juyi ya yi jin hawaye ya taru bisa idonshi. Sai yaushe ne zai ga soyayya mahaifi a gareshi? Sai yaushe? Har yau d'in anan ba abinda ya sauya zani daga abinda yake fuskanta,ya sani da a iya kuriciyarshi bai ta6a sa6a ma mahaifinshi ba,ina ma ya ra6e shi bare ya sa6a? Kai ya girgiza, amma har yau d'innan baya yarda ya kalleshi balle ya mishi maganar arziki. Tamkar an tsikareshi sai ya mike tare da goge hawayen ya nufi band'aki tare da gyara fuskarshi ya rufo d'akin hotel d'in. Tun ba yau ba ya sai kangon makotan Abbanshi,a kullum yakan kwata rushe gidan yai na zamani amma Abban bai nuna ya aminta koh a'a. "Bissmillah.. Gidan ya shago da masu ruguje gini,ba kowa a gidan sai halamun kofar su lami a rufe. "Daga nan d'akin nake so a fara zuwa katangar kangon nan tunda a had'e suke. Kai suka kad'a mishi tare da fita dan bawa wanda yake cikin motar umarni ya fara aiki. Kan kace meye tuni d'akin dake a matsayin na Umma na da yai flat tamkar ba ata6a yi ba. Kamin yamma hatta kasar motar ta kwashe ta matsar chan gefen kangon. Kallon gidan yake,ba karamin fili yai ba da aka had'e da makotan. Juya wa zaiyi sai dai yaja ya tsaya ganin kwalba an tono ta har ta dan fashe, dan haka a hankali yasa leda tare da karasa tono ta,sosai ya kad'u ganin kasanta da wata laya nannad'e cikin fata. Jujjuya ta ya fara,in banda wari ba abinda take tai bakikkirin da ita. Juya wa yai da zummar fita sai ya tsaya tare da gyara farin glass idonshi ganin wata bakar kwalba na yalki da laya a gefenta. Kamar kar ya duba,sai dai ya kasa daurewa tare isa wajen ya fiddo da handkerchief a aljihunshi tare da rufe hannunshi ya bankad'o su. Kai ya kawar tare da yin bissmillah ya dakko layar da kwalbar sai wari take yana jujjuyawa yana yamutsa fuska. Tamkar an jeho su haka suka shigo gidan ganin manyan motoci a kofa. Suna yin ar'ba suka fara inda-inda,sai dai idon su na kaiwa kan kayan da motar ta tono suka hau raba ido. Ido ya zuba musu,gaba daya a yanzu koh a y'an aiki bai tunanin zai iya d'aukar su Tabawa dan munin kamanin su agunshi. A yanzu tsantsanin kallonsu ma yake dan yadda duk suka zama wasu zararru in sun ganshi,dan haka da sauri ya d'auke kai tare da fita da kwalbar daga gidan. Ba wacce ta iya magana sai da ya fuce,dan haka da sauri Tabawa ta d'aura hannu bisa kai tare da runtuma ihu. "Shikenan asiri ya tunu,wallahi Lami kwalbar nan ce da layar da mai yankan wuka ya ce mu sata tare da kwalbar ta aikinshi yau ya tono ta. Kasa magana Lami tayi tana zufa,tasan yau kam karya ta kare,kila in Malam yazo ya dankara musu saki tunda ba makawa sai an fasa kwalbar nan.. "Yanzu meye abinyi Tabawa? Kai ta girgiza "Mu bishi muga inda zai hullar sai mu dawo mu binne. Fita sukai da sauri,sai dai ba Kabir sai kurar motarshi. Gidan Umma ya nufa a inda nan ne su Saifu suke mata hutu. Kallon ikon Allah suke lokacin da k'anin Nafisa ya kunce layar. Baya su Saifu sukai da sauri dan ganin kai kamar na miciji da korayen ido duk ya bushe cikin layar. "Ban fa yarda da abin nan ba Umma,kamar yadda naga ganin abin su Lami sun kasa sukuni. Ajiyar zuciya Umman tayi,tare da fad'in "Allah kyauta. "Amin. Kai Aliyu ya dago. "Yanzu ya za ayi dasu Ya Kabir? Umma ya kallo,sai ta ce ya fita ya sa musu kalanzir gaba daya bayan ya fasa kwalbar. "Abba meye wai? Nass ya kallo tare da kad'a mishi kai. "Ba komai Nass. Saifu ya kallo, "Je ku shirya mu fita in da abinda kuke so ga Sultana naga ta shirya. Tashi sukai tare nufar d'akin Umma. "Yau na yanken shawarar tunkarar Abba Umma a wannan karan koh zan san laifin da nai mishi dan nasan yau da matsala dan na rushe wani bangare na gidan... Shiru ya yi jin karar wayarshi, duba wa ya yi,Abban Uzairu ne,dan haka sai ya d'auka dan yasan yanzu ba jimawa suka rabu. "Kabiru kana ina? Cike da mamaki ya kalli Umma dan koh sallama Abban Uzairu bai mishi ba. "Ina gidan Umma Abba,lafiya? Cike da dauki ya ce "Kazo gida yanzu inda hali kaga wani abu. Wayar ya ajiye yana kallon Umma. "Kai Umma ba lafiya ba,duk yadda akai nasan Abba ne yaje gida yaga abinda nasa ayi. Shiru sukai, "Kaje dai kaji koh lafiya, Allah rufa asiri. Tashi ya yi ganin su Saifu. "Ku jirani na dawo koh? Kai suka girgiza "Muje dai Abba mun shirya. Jama'a suka samu a gidan makil ga nan ihun Abba yana fad'in sai sun fito mishi da Kabir. Karasawa sukai ciki,da sannu ya fara fitar da jama'a yan kallo yana kutso wa ciki. "Abba.. Chak ya tsaya da bugun kofar d'akin da su Lami suka kulle ya bari,a hankali ya juyo tare zuba wa Kabir din ido wanda ke hawaye. Abban su Uzairu Abban ya kallo da halamun tambaya, da sauri ya daga mishi kai. "Yaya shine Kabirun ka.. Baki sake ya sake kallon Kabirun dake murmushi yana mai gode Allah da ya nuna mishi wannan rana. A hankali suka fara isa ga juna bakin Abba na ka'rkarwar kiran Kabiru har suka had'e. Daga sama har kasa yake kallon Kabir din shima yana hawaye. "Kabiru na ne yanzu haka? Hannun Abban ya riko yana jijjiga mishi kai, "Sannu Kabiru,Allah ya raya min kai duk rintsi. "Azatona ka mutu dan tun hullaka rijiya na daina ganin ka na kuma kasa komai a kai,kai hak'uri Kabiru,ba laifina bane... Kuka yaAbban yanai. Juyawa ya yi tare da nuna wa Abba su Saifu yana murmushi halamun nashi ne. "Ikon Allah. Hannu ya mikawa su Saifu,dan haka da sauri suka karasa ganin Abban su a jikin shi,sun sani da kullum in sunzo Kano bai musu magana sai kallo da ido. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 33_Tana d'aki lokacin da suka dawo,tun daga bud'e kofar su suka fara kallon parlourn yadda yake diddika kamshi a gyare tsaf-tsaf kamar kullum. D'aki kowa ya nufa a gajiye har Uncle din,sai Sultana da ta nufi d'akin Faridan ganin bata ganta ba. "Anya wannan gyaran d'akin na john ne kuwa Nass? Kallonshi Nass din ya yi shima yana mamakin yadda aka dame musu gado ba irin yadda john ya saba ba. Kafad'a ya daga halamun shima bai sani ba. Duk mamaki suke har Saifun,sai dai shi sai ya bari a ya sake iyawa ne kawai,dan haka ba wanda ya kawo Farida ce tayi. Fito wa tayi jin muryar uncle din tai mishi sannu da zuwa kamin ta wuce da Sultana d'akinta. Kamar kullum kowa ya d'au abincin shi ya nufi dining dan ci. Jin shiru sai dariyar Sultana daga d'akinta yasa Uncle din sanya Nass ya mika wa Farida nata ya kira Sultana. Tashi yai ba dan yaso ba ya d'auka tare da kwankwasa kofa yana kallon Abban,dan ka'idarsu ce dole a baka izinin shiga kan ka fad'a. Farida ce ta bud'e, ganin ita ce yasa kawai ya mika mata tare da kawar da kai yana kiran Sultana ta fito. Kar6a tayi tana mishi murmushi kamar yadda Umma ta ce,shi kam ganin Sultana ta taho yasa ya bar kofar yana chunno baki. Chokali Uncle din ya ajiye bayan gama kallon su din ya dafe kai da duk hannu biyu. Ya sani tun ranar da suka fita ya ja musu kunne suka daina maganar Farida,duk da yaji dad'in ba wanda ya sake tada zancen mey yasa ya aurota amma yana kula sun fita a sabgarta ma gaba d'aya sai kallon tsana da harara. Kai ya dago jin Nass na kiran Sultana ba iyaka dan haka sai ya kallota. Kafad'a ta make musu rike da abincinta a hannu halamun d'aki zata bi Farida su ci. Ajiyar zuciya ya saki tare da girgiza kai. "Bari taje... Jin haka yasa da sauri ta kara mai zuwa ga Farida tana murna. Yau a d'akin Sultana tai wanka bayan ta ma Sultanan nata. Ganin ba wasu kayan kyali sai farar powder kawai,dan haka sai tajata suka koma d'akinta. A nan ta tsantsara Sultana tare da sanya mata kayanta riga iya gwiwa blue mai flower pink dan lokacin fitar su ya yi na yamma. Riga da skirt itama ta sanya na attamfa pink da ratsin blue,sai zamo sunyi kusan anko da Sultanan. Dankunne kawai tasa blue mai kamar barima tare da daura dankwali. Ta mudubi take wa Sultanan dariya ganin yadda take kallon yadda take mirza jan baki,dan haka sai ta juyo tare da shafa mata suna dariya. Kofa aka kwankwasa,da sauri Sultana taje ta bud'e. Uncle ne cikin kanan kaya sai ka ce dan saurayi sai kamshi yake. "Wow...my princess,ke ce kuwa? Dariya take mishi jin ya fara kod'a kwalliyarta tana gyad'a

Chapter 8 of 19