Share this page
wa suka hau wawaso hannu baka hannu faranti suna dariya. Ita kam Sultana gaba d'aya ta kafa kai a murfin kan kace kobo duk sunyi dumu-dumu da madara. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 7_Farantin Saifu ya d'auke da guntu, tuni suka hau kewaye parlourn yana gudu suna binshi. Bud'e kofar parlourn ne yasa kowa ya yi poster. D'aya bayan d'aya take kallonsu,ta ma rasa mey zata ce,da gudu Sultana ta 6oye a bayan Farida tana raba ido. "Bala'i"... Kai Farida ta kautar tare da fad'in a hankali "Ki gani akan ki. Kan su Saifu tayo, da gudu duk suka jeru bayan Farida suna had'e rai. Tsaye tayi tana kallonsu,tabbas in batai da gaske ba sai yarinyar nan tasa yaran nan sun daina tsoronta. "Wane d'an uban ne yasa ku dakko min madara ku shanye? Hanci Farida ta fara hurowa duk suka yi shiru. "Ba magana nake muku ba? Nan ma shiru,sai tashin kukan Sultana data fara. Gyale ta tu6e tare da cin damara ta nufi gaban kayan kallo tana cirar waya. "Yau hannuna ya daina ciwo,da waya zan cid'a ku... Gudu suka sa gaba d'aya tare da nufar d'akin su Farida suka kulle suna dariya. Bugu take wai su bud'e. "Ashe bamu da wayo in ma mun bud'e. Zagi ta narkowa Farida,da sauri ta amshe tare da fad'in "Wallahi ba uwata sai dai taki... Da sauri su Amjad suka kallota, "Mun shiga uku,Aunty ki ka zaga? Mukullin ta cire tare da hararar su, "Wa ya fad'a ma uwa tafi uwa? Sai dai in na fita ta kasheni. "Ni dai Farida kinja mana masifa wallahi, yanzu haka kila gobe ma ta sake hanamu abinci. Hararta tayi. "Tama isa,kashe mu zatai kenan?. Shiru sukai jin yadda take narko ashar kan wallahi in har ta kamasu na lahira sai ya fisu jin dad'i. Hararar kofar Farida tayi,kan a hankali ta ce. ''Wannan anyi mahaukaciya wallahi,mtsww. Su dai kowa yai tsuru-tsuru banda ita da Saifu. Ranar sai a d'akin gaba d'aya suka kwana. **** Kuka take mishi ido duk hawaye tare da mishi kallon tuhuma, Tafiya yake da zummar rarrashi sai ta daga mishi hannu halamun kar ya karaso mata tana mai cigaba da kukanta mai tsuma rai. A furgice ya tashi tare da fad'in "Halima"... Ko'ina yake kallo na d'akin hotel din gabanshi na fad'uwa. Kai ya dafe da d'ukkan hannunshi biyu,tabbas mafarki yake,in kuma zai tuna wannan ne karo na uku da yai mafarkin Halima tana mishi kuka,na farko tun aurenshi da Jamila tana fad'in yaranta. Gaba d'aya sai hankalinshi ya koma gida,ya sani da kila yaran basu a lafiya. Tashi ya yi tare da nufar band'aki kawai ya dauro alwala ya tada nafila,yana mai rokon Allah yasa yaranshi suna a koshin lafiya. **** A ABUJA. Tun asubar fari ta tadasu sallah,dan in da sabo sun saba su sallah bata wuce su sabon Umma. Duk zaune suke wannan ya kalli wannan wanchan ya kalli wannan dan yunwa dake addabarsu banda Sultana dake bacci. A dan kwana biyu har sun fad'a. Har 7 na safe suna zaune,chan dai suka bige da fira Amjad na kallonsu. "Ni fa yunwa kamar ta kasheni Aunty Farida.. Kalloshi tayi tare da fad'in "Yanzu ya zamuyi toh? Nass ne ya ya ce "Muje irin na jiya muyi break fast da kanmu. Tsam tayi,kamin ta girgiza kai, "Toh bari na leka in bata nan sai mu fito. Kai suka kad'a mata. Kamar barauniya take sand'a har kofar d'akin Fatima ta leka tana bacci,a ranta ta ce "Muguwar Allah sa tayi sallah ma. Har zata wuce taga key ajikin kofar,dan haka da sauri ta koma tare da rufeta ta waje da mukullin dan ma kar ta fito. "Ku fito na kulleta. Gaba d'aya suka duru kitchen d'in da zummar daura koma meye suka ja suka tsaya. Baki sake Farida ta ce "Kai,lalle matar nan. Bin store din suka kara yi yadda tasa mukulli ta datse shi. Kitchen din suka kalla, dan mugunta babu wani abu da zasu juya ya basu abinci su ci sai kwanika da da jerin filasai. "Yanzu Aunty Farida mey zamu ci? Kallo Amjad din tayi da har ya fara hawaye. Duk d'aki suka koma sun zuba tagumi ido ya kad'a yai ja dan yunwa. A zabure Faridan ta mike tare da fad'in "Na tuna.. Duk suka bita da kallo ganin ta nufi jakar kayan su. Kud'i ta ciro na dari bibbiyu tana wage baki. "Aisha guntun chanjin mu da Abba ya bamu kin tuna? Baki itama ta wage tare da kad'a kai. "Toh mu fita mu sai wani abu sai muci. Gaba d'aya suka wage baki tare da kad'a kai suka mike. Da kuka Sultana ta mike,dan haka sai suka sunkumeta suka bud'e gate suka fice. A gun mai shayi suka dire yana soya kwai. Dari biyar ta fitar, "A bamu biredi na duka. Da sauri Sultana ta nuna kwan da yake soyawa ta ce "Ni wannan. Kallota tayi tukunna ta kalli kud'in hannunta. Gaba d'aya dubu da dari uku ne har na biredi,mai biredin ta kalla. "Soya mana kwai wanda zai ishemu mu duka da biredin dari biyar sai muyi ta ci koh? Kai suka kad'a mata suna lashe baki cikin murna. Kowa biyu ya soya mishi tare da zuba musu a leda. "Gaba d'aya kud'inku 8,60. Bashi tayi,tare da kallonsu. "Toh da mey zamu had'a? "Tea man Aunty Farida,sai dai ba madara da siga Aunty ta kulle. Kai ta kad'a, kamin ta kalli mai shayi. "Nawa madara guda shida irin wannan? "2,10 ne. Kai ta kad'a. "Siga fa? Sai ya ce babu,tare da nuna musu kanti a gefe inda zasu samu. A kanti suka kaso sauran chanjin dan ganin bournvita da suka yi kan suka koma gida. Kitchen suka koma tare da daura ruwan zafi mai yawa,a nufinsu suyi ta sha. Brush suka yi,kan suka dawo. A baje suke kowa da kofi da an sa mishi kwai a tsakiyar biredi ga katon tea flask cike da wani ruwan na anjima, tuni suka fara kawo network har suna kwasar dariya. A zabure ta mike tare da fita,sai yanzu ta tuno da kofar Fatima da ta rufe jin bugu. Tana bud'ewa ta zuba da gudu,dan tasan in ta rikota sai ta Allah. Wajejen 11 suka leko jin karar tvn parlour. Zaune take ta hakimce tana kwasar lafiyayyen abincinta hankali kwance tana bin wakar tv. Fito wa sukai bayan Farida ta ce kar wanda yai dariya. "Chips" ne lilli6e da ga nan shayi mai kauri tana korawa. Kai ta dago tare da kallonsu har sunyi wanka abinsu suna kallonta. Murmushi tayi,ita a tsammaninta kallon za suci suke mata. "Dama kun koma,dan wallahi kunsha madarar break d'in ku ban girka da kowa ba,dole kuji ajikinku yau. Waje suka samu tare da zama gaba d'aya a kujera d'aya kusa da Faridan. "Ke kuma Farida ki ke kowa? Kallota tayi a yatsine. "Bari kiji koh yaran gidan nan bana fad'a suna fad'a wallahi, ki saita nutsuwarki kamin ki bar gidan nan koh na saita ki... "Sannu uwata. Kai ta kawar. "Mey ki ka ce? Rai ta had'e tare da fad'in "Ni ba dake nake ba. Abincinta ta cigaba da ci tana fad'in "Karamar marar kunya. Haka suna kallonta dan rashin imani ta cinye tass harda dariyar mugunta tai d'aki. Kwaikwayar tafiyar Faridan take suna dirka dariya,dan mugunta yau ma tana wanka ta fuce tare da kulle kitchen gaba d'aya. Lalle Fatima akwai karfin hali. Sai bayan la'asar ta aiko dan makociyarsu da abinci flask d'aya baifi nacin mutum uku ba. Da harara tabi abincin, dan haka ba wanda ya ta6a. Yauma sai bayan magriba ta dawo duk wani abu nasu ya kare,dole abincin suka ja suna cikin ci tazo lokacin Farida sun wanko hannu dan barwa Nass da Sultana. Dariya take harda rike ciki ganin yadda sukai la'asar dan mugunta. Tsaki Farida tayi,dan tazo wuya a tsanar matar nan. "Ke,da wa kike? Cike da harara ta ce "Da ke nake. Tana murguda baki. A tunzure ta nufota,dan haka zuruf ta mike tsaye tare da kama kugu. Mari takai mata sai ta kauce. "Dole ma ki bar gidan nan gobe.. Da sauri ta amshe "Ai ba gidan ki bane ba inda zani. Chafkota tayi ta fara duka itama tana ramawa da Allah ya isanta. Cikata tayi tare da fad'in "Ni ki ke jawa Allah ya isa. Baya taja tare da fad'in "Eh,muguwa kawai azzaluma kawai,ai bari Uncle ya dawo wallahi duk sau na fad'a mishi abinda ki ka mana tun tafiyarshi... Shiru tayi ganin ta sake yin kanta tai d'akin yara da sauri ta rufe. Kai ta kad'a, kamin ta juyo kan sauran. "Uwarku ku ke kallo koh mey? Jansu Aisha tayi tana bata hakuri,sai da suka tabbatar sunzo d'aki tukunna Saifu ya ce "Mudai ba uwar mu ba sai taki,kuma an fad'a muguwa... Da sauri suka rufe duk da ba tahowa tayi ba. Uwa dai uwa ce,amma sai taji wani iri,duk da abinda ya haifota shi ya haifo tasu uwar. Tsanin mamakin abinda ya faru ranar kusan kwana tayi tana neman abinyi. Washegari Kowa kasa fito wa ya yi,musamman su,dan Farida tasha kwata fita suna had'a ido. Ga bakar yunwar data addabesu,ga kudi ya kare,ga ta tsare hanya balle su san nayi. Dan mugunta har goma taki barin parlourn, ga Sultana da Nass sai kuka suke amma ta maze. Sha d'aya tabar parlourn, dan haka da sauri Farida ta shige d'akin yara. By Feenat Ja'afar *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 8_Kuka ta tarar sunayi har Aisha,duk in ka gansu gwanin ban tausayi barin Sultana,sai ta sa hannu a baki kamar ta hakura sai ta cire taci gaba da yi. Duk wata dabara ta kare musu,dan haka har Faridan kuka suke,chan dai tai shiru. "Kuzo muje makota sai muce su bamu tunda yauma babu abinci. Kai Saifu ya kad'a "K'awar Aunty ce,wallahi itama muguwa ce,ga Abba ya hanamu yawo. Shiru tayi,sai dai ganin Sultana tayi wajen tea flaks yasa wani hawayen ya zubo mata. Dakkowa tayi da zummar a zuba mata shayi tsautsayi ta fad'i har flaks ya fashe sai ta sau wani kukan. "Kuzo mu fita inba haka ba wallahi kashe mu zatai da yunwa. Jiki babu karfi suka fito tare da zama a parlourn har yanzu fasasshen flaks din na hannun Sultana tana ja dakyar, yau dai iya wayyon Farida ya kare. Da sauri ta fito daga d'aki tana yake hakora, hakan yasa Nass da Amjad da Aisha da gudu sukai hanyar d'aki har suna gware. "La,ashe sun fita,amma suna dawo wa zan ma flashing in yaso sai ka kira. Kit ya kashe lokacin da yake jan jakarshi a harabar airport d'in ya isa mota. Juyo wa tayi kan su bayan ta sauke wayar tana kallon tsagerun cikin da basu motsa ba. Kan flaks din ta dire na hannun Sultana,itama duk tayi tsuru-tsuru kana ta6ata zata sau kuka. Ganin ta nufosu yasa da sauri ta cika flaks ya fad'i tare da yin gefen Farida. "Kan uba.. Tashi sukai tsaye ganin ta daga flaks din tana karkad'awa. "Ki ka fasa min flaks Sultana? Kai ta hau kad'a mata daga bayan Faridan tana kuka. "A'a ba kuka ki ke ba wannan, yanzu ne za kiyi na gasken gaske... Bayan Faridan tayi Sultanan tana kank'ame Faridan tana ihu amma sai d ta fincikota. Kunne ta murd'e mata kamin ta sau mata rankwashi sai kwa ta kara sakar kuka,bai isheta ba ta kama gefe da gefen kumatunta tana ja tun karfi tana mata kashedin in ta kara ganinta da flaks a hannu sai ta cire mata kumatu... Shiru tayi jin an hankad'a ta,tafiya tayi kamar zata fad'i ta rike kujera baki sake. Huci yake,gaba d'aya sai ya dawo mata sak babanshi in ya fito a babu wargi suna yara. "Saifu".. Cike da mamaki ta kira shi yayinda yake lallashin kanwarshi yana harararta cike da tsana. "Ni ka hankad'e?.. Banza yai mata yana huci. Da sauri Farida ta dan bugeshi tare da fad'in "Kai ka ce eh din,wallahi in ta dake ka mu had'u mu mata dukan tsiya muguwa kawai. Kallo Fatiman ya yi,yau da gobe sai Allah,dan haka nan take ya ce. "Eh an ture ki rama in kin isa. Kallonshi take,kawai sai ma abin ya bata dariya,jin dariyarta yasa su Amjad lekowa. "Wallahi yau a gidan nan zanga dan uban da zai kwace ka a hannuna... Da sauri Farida ta ce "Hmm dallah chan,Allah zai kar6eshi,kuma nima wallahi ina tsaye baki isa ki dakeshi ba bayan kin hanamu abinshi ba... Kan ta karasa tuni har tai kan Saifu marainin wayonta,marinshi take yana dukanta Farida ma ta shiga amma saida taci karfinsu ta kai Saifu kasa. Yadda kasan Allah ne ya aikota haka ta, hau ruwan cikin Saifu tana jibga ta fuska ta jiki tamkar wani babba tana maka mishi zagi da fad'in yau zatai maganinshi. Tun Farida na dukanta har taga ba ji take ba ganin hakan yasa da gudu sauran suka rufar mata Farida na fad'in su cije ta,sai dai ina,suna kawo hakori tana makewa. Yanzu kam har ta galabaitar da Saifu ya ma daina ramawa sai kokarin shid'ewa da yake jini na fita ta hancinshi amma taki daina dukan dan jin har yanzu yana fadin Allah ya isa. Tashi Farida tayi tare da nufar kitchen tunda taga baji take ta hannu sai ra shiga neman madoki. Allah ya bawa Nass sa'a ya kamo fatar bayanta da hakori tare da sau mishi chafka iya karfinshi yana kuka. Da halama taji zafi,dan haka sai ta sau Saifu ta juya tare da mangare Nass iya karfinta a fuska,da sauri ya cikata tare zubewa ya dafe inda ta make. Bai isheta ba shima tabi kanshi da duka tana fad'in ''Ni ka ciza? "Yau sai na zubar ma da hako... Shiru tayi jin saukar wani zazzafan duka a goshinta,kan ta dago taga waye an kara kwad'a mata muciya, tuni dan azaba ta daga Nass tare da juyawa da zummar chafkar mai d'ukan suka ji ansa salati da karfin tsiya. Gaba d'aya suka juya har Sultana da Amjad da Aisha dake jijjiga Saifu ya tashi suna kuka. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 9_Jakar dake rike a hannunshi ya hullar cikin sauri tare da fara tattare hannun rigarshi jikinshi har wani 6ari yake tare da juyawa ya dannawa kofar sakata. Take ya sauya kama tamkar ba uncle din Abuja ba. Da sauri Farida ta hular da muciyar dake hannunta tare da matsawa ganin itama Fatiman na matsawa lokacin da Abban su Saifu yake kusanto su a sukwane. Neman guduwa take jiki na 6ari,sai dai taku uku kwakkwara ya fard'o ta. Kamar yadda ta haye kan yaran tana jibga shima haka yai mata tare da dage wa iya karfinshi yana mari da kai mata naushi a duk inda ya samu. Duka yai mata na fitar hankali yadda yasan bazata iya koh motsi ba kamin ya kyaleta ya rarrafa ga Saifu da baya motsi. "Saifullah, Jijjigashi yake hawaye na digar mishi amma ba koh motsi ajikin yaro. "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un...Saifu. Farida ya kallo da sauran yaran,da sauri ya ajiye Saifun ya karasa gun Nass dake yunkurin amai daga kwance ya kasa ya dago shi shima baki fashe. "Farida... Jiki na 6ari ta ce "Na..na.. na'am. "Yi sauri ki dakko min Nass,Aisha ki dakko sauran ki ku fito ku sameni a mota. Da sauri sukai yadda ya ce shi kuma ya kinkimi Saifu. Har zai tada mota yai saurin komawa tare da cire mukulli ya kulle Fatiman dake a kwance cikin jin jiki. Kallon yaran yake yadda aka dukufa kansu barin ma Saifu da ake neman cechar ranshi. Da sauri ya fuce tare da yin kwana yadda ba mai kallonshi kawai ya sau kuka. Irin azabar da yasha a hannun *MATAN UBA* bai manta ta ba dai-dai da second. Kai ya duk'ar hawaye na zuba yana adu'ar Allah ya ceci yaran. "Abba... Fuska ya guge kamin ya dago tare da k'akalo mata murmushi na dole jin muryar Sultana ta dafa shi. Ganin Amjad na tahowa yasa ya rike hannunta tare da cewa su tafi. Anyi nasara Saifu ya kawo wuta,har sun mishi dressing na ciwon da yaji shi da Nass ana musu karin ruwa. Waya ya ciro tare da kiran d'aya daga y'an office nasu. "Ina son ka aika min y'an sanda majiya karfi mata gidan da nake,ka had'o da maza biyu dan Allah masu zafi... "Subhanallah, lafiya Kabir?.. Kai ya kad'a kamar yana kallonshi, "In zan samu kamin yadda nace zan ma bayani daga baya,kamin nan dan Allah ka kawo su asibiti suga wani abu. Wayar ya kashe bayan ya fad'a mishi asibitin tare da kallon yaran da suke kallonshi,ita kam Farida da Aisha jin zancen y'an sanda har sun fara raba ido suna kallon juna. Amjad ne ya riko hannunshi tare da fad'in "Ka ce su kama Aunty Abba su sata a cell har abinci itama su hanata Abba. Kai ya kad'a mishi tare da kallonsu d'aya bayan d'aya, gaba d'aya a kwana uku duk sun fad'a har su Faridan. "Kunci abinci kuwa ma yau? Da sauri Sultana ta girgiza kai halamun a'a. Le6e ya cije tare da girgiza kai,har in yabar Fatima a haka yasan bazai huce takaici ba,dole a nina ta yadda ta azabta yaranshi. "Kuyi hakuri Farida,bari na kai ku kuci abinci,ina zuwa naga su Saifu... Kuka ta sa,tare da girgiza kai, "Mu dai gida zamu tafi, a kaimu Kano gun su Umman mu. Da kallo ya bita, sai ya hau kad'a mata kai. "InshaAllah,kuyi hakuri zan kai ku da kaina. Ba'a jima ba sai gasu sun iso. Y'an sanda 4 biyu mata biyu maza tare da abokinshi,matane wasu kitika-kitika tamkar dangin samudawa a dire da ganin su kasan ba wasa. D'akin su Saifu ya kaisu. "Ku fara duba ga wannan kamin mu wuce ga inda zamu.. "Innalillahi, Kabir accident sukai ne?.. Subhanallah. Kai ya kad'a yana murmushin takaici. "Ku biyoni kawai. D'an sanda d'aya suka bari tare nurse a gun su Saifu. Kofar ya bud'e tare da fad'in su shiga. Bin bango suka samu tana yi cike da cije le6e fuska a kumbure. "Officers ina so a tafi da ita ai mata duk hukuncin da ya dace ga wanda yai yunkurin kisa ta hanyar duka,ina si ku lakad'a min ita sai inda karfinku ya kare wallahi koh nawa ne zan biya. Kasa ta koma tare da sanya kuka tana bashi hakuri. "Subhanallah, a'a Kabir,kar ayi haka,a dai yi sasanto matarka fa?.. Ido ya sa mishi,kamin ya kad'a kai. "Kaji mey nace kuwa Nasir? Yarana ita tai musu duk wannan aika-aikan ciwon ba wani hatsari,dan haka bani da guntun alaka da ita aure na saki. Bayanin yadda ya sameta akan su Saifu yai wa y'an sandan, tun kan aje ko'ina tuni matan suka fara sakar mata mari "Wuce da kafafunki.. "Dan Allah Ya Kabir ka yi hakuri kar su tafi dani,wallahi kasheni zasuyi... "Mey ku ke jira da ita officers? In ta kama a kashe ki wallahi zai fi min dad'i Fatima.. Nayi imani da Halima na raye irin hukuncin da zata sa a miki kenan dan irinki annoba ce a gari.. Juyawa ya yi tana kiranshi cikin kuka. Kai Nasir din ya sunkuyar,ganin ya fuce hakan yasa shima yabi bayanshi jiki a sanyaye,hakan yasa da fatattaka suka tsamota a gidan tare da hullata motarsu. Da kallo yaran suka bi motar har suka bar ganinsu. Gun cin abinci ya kaisu,a hankali suka fara zamewa suna d'aura kai bisa table din kan a kawo abinci. Cike da tausayawa yake kallonsu ganin yadda sun ma kasa cin abincin sai Aisha dake chaka a hankali. "Ummata bud'e bak'i in baki abinci kinji? Kai Sultanan ta girgiza mishi tare da lafewa a jikinshi baki a hannu. Ajiyar zuciya ya yi,duk ci irin na Sultana amma yau ba kanta. Su Farida ya kallo, "Kuyi hakuri Farida kuci kar yunwa tai muku illa. Kai ta duk'ar tare da zubawa abincin ido wanda yasha kaji,sam na abinda ke ranta duk kuwa da kaunarta da dajjaja. "Amjad kai fa? Kai ya dago tare shima girgiza wa. "Tea Abba zansha ni. Kai ya kad'a tare da aikawa a kawo kofi hud'u harsu Farida da farfesu. "Tashi Ummana kisha tea kinji?.. Hannu yakai bisa kanta da sauri jin zafi k'au. "Subhanallah, Sultana. Kallonshi tayi ido lumshe. Da sauri ya dakko kofin tare da fiffitawa ya fara bata sha uku ta fara amai. Kan ya yi kwakkwaran motsi Farida ma data dau shayin ta fara. "Ya ilahi... Gaba d'aya rikice wa ya yi ganin Faridan na kuka ita da Sultana,ba yadda ya iya dole su ma asibitin ya mika su dan yadda zazzabi ya rufe Farida da Sultanan. **** Reras yake kallonsu an jere mishi su a gado hud'u kowa da drip,kukan ma ya kasa zuwa mishi,lalle yasan ba karamin azaba suka sha gun Fatima ba. Tashi ya yi tare da fita waje yana danna waya. "Abba ina zaka tafi? Juyo wa ya yi tare da kallon Amjad, "Ba inda zani Amjad waya zan ma Umma jirani yanzun. Chan bayan bishiya ya nufa tare da jingina yanajin yadda wayar ke ringing. "Assalamu Alaikum... Shiru ya yi,sai da ta sake kamin ya ce "Umma... Kuka yasa mata kamar wani yaro,dan haka tuni ta rude ta fara tambayar lafiya? "Umma Fatima y'ar uwar su Tabawa ce,itama tabi sahun su duk sun kassarani Umma.. "Subhanallah Kabiru,mey tai maka? "Umma Fatima itama bata da imani,wallahi yanzu dai ki yarda dani duk *MATAN UBA* mugaye ne,kiris ya rage ta kashe min su Saifu Allah ya kawo ni... "Kayi hak'uri Kabiru ka bar kuka,InshaAllah ina bisa hanya zuwa gobe kar ka mata komai... "A'a Umma,ba sai kinzo ba,dan tuni nai mata hukunci dai-dai da laifinta,Umma na had'ata da hukuma... "Kai,kai Kabiru,bai kai haka ba,yanzu kai hak'uri a sunto ta InshaAllah muna kan hanya.. Kai hak'uri. Hawaye ya goge tare da fad'in sai ta zo. D'akin ya koma tare da jan kujera ya zauna yana kallonsu. Ilahirin fuskar Saifu da Nass duk a kumbure. Kai ya kautar jin hawaye ya taho mishi. Gefen Farida ya dawo,bacci take fuska duk tayi fayau sai dogon hanci. Yanzu mey zai ce da abokinshi in wani abu ya samu ya'rshi? Kai ya girgiza tare da shafa kan Sultana. By Feenat Ja'afar *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 10_"Abba".... Dagowa ya yi da sauri jin muryar Nass,da sauri ya tashi tare da isa gareshi. "Sannu Nasir, ina ke maka ciwo?... "Abba ina Saifu? Aunty zata kashe shi fa. Hawaye ne ya cika mishi ido,da sauri ya kawar da ido tare shanye su. "Juya ga nan Saifu yana bacci.. Kai ya juyar inda ya nuna mishi dan gaskatawa. "Ina ke maka ciwo? Juyowa ya yi tare da kafe Abban da ido. "Abba ina Aunty Fatima? Murmushi ya yi tare da shafo kanshi. "Tana chan an kulleta a cell,daga yau ta bar mana gida gaba d'aya.. Da mamakinshi sai yaga ya fara murmushin murna. Gun Farida ya juya sai yaga ta zuba musu ido halamun itama ta tashi. "Kin tashi Farida? Kai ta kad'a tare da goge hawaye. "Sannu,ina ke miki ciwo? Kai ta girgiza halamun babu. Nurse ya kira ta cire ma Faridan ruwa ya kare har ta zauna. Ko'ina take dubawa ba Aisha ba Amjad. "Ina Aisha uncle? Kallota ya yi ganin tana neman kuka. "Sun tafi da Amjad gidan Uncle Nasir, kar ki damu da safe zasu dawo. Kai ta sunkuyar tana goge hawaye. Chan ta sake fad'in "Zanyi sallah.. Kallota ya yi da mamaki,sai ya kad'a kai. "Sister dan Allah a taimaka mana da abin sallah da hijab. Kallonta yake yadda take rama sallolin dake a kanta har ta idar,lalle ne abokinshi yai ma yaran tarbiya ba kad'an ba. Dakyar ya zuba mata abinci tare da tilasta mata taci. Shi kam Saifu sai chan dare ya farka da kuka yana kiran Abba. Attendance d'in dake kula dasu ne ta farka kamin Abban nashi ya farka. "Ga ni nan Abba nah,sannu. Dakyar yake iya bud'e idon dan duk sun kumbura dan duka. **** Washegari 11 na safe a Abuja tai ma su Umma dan asubanci sukai ta kasa nutsuwa. Sanarta asibitin da suke ya yi,lokaci kad'an sai gasu sun iso tare da yayan Fatima da Umman Fatiman wato kakarsu su Saifu. Ba karamin al'ajabi sukai ba da ganin su Saifu a wannan hali,hakan yasa Umman su Fatiman kuka da yin tir da halin Fatima. "Wannan shi ya dace da ita Kabir wallahi ka min dai-dai. "Ko ni ne a matsayinka wallahi sai in da karfina ya kare kan wacce tai ma yarana haka... "Haba Uzairu,ka yayyafawa wutar ruwa man ba wai ka kara hurata ba,Fatima jinin ku ce koh dan haka ai mata hak'uri.. Da sauri yayan Fatiman ya katse Umman. "Wallahi Umma in Kabir yai hak'uri toh tabbata an maka Fatima kotu ta yadda zata amshi hukunci dai-dai da laifinta,kila ta hakan sauran y'an baya masu hali irin nata su hankalta in sunga ana daukar mataki... Dagowa Ummansu Fatiman tayi tana kad'a kai. "Wallahi Umman Kabir ina bayan Kabir d'ari bisa d'ari, a yau nai nadamar zaman Fatima a zuri'ata,ni dai bani ta gado ba a wannan mugun halin da rashin imani,na sani da in da marigayiya Halima ma ce bazata ta6a wannan mugun halin ba... "A'a Ummansu Uzairu,hannunka baya ta6a ru6ewa ka cire ka yadda,kuskure duk muna yi,ni dai in anbi ta tawa a sinto Fatima Kabir... "Kiyi adalci Umman Kabiru,ki d'auka baki da alaka da Fatima kuma ta aikata hakan a jikokin ki wallahi nasan sai inda karfinki ya kare. "Dan haka yadda Fatima ta manta alakar dake tsakanin yaran nan da mahaifiyarsu wallahi nima na manta ta,kuma ina rokon Allah ya bi ma yaran nan hakkinsu da ta ci. Kai ya Uzairu ya kad'a "Amin Umma,kema Umman Kabir ki manta wata alaka kawai Fatima ta karbi hukunci,na tabbatar a gaba zai zame mata izina da y'an baya. Shi dai Kabir yai shiru yana jin su,dan sam bai tunanin iyayen Fatima zasu mara mishi baya ba. Kwana biyu suna jinyar Saifu da Nass,tuni Farida da Sultana aka sallamesu sai dai rikicin gida da take musu kullum. Dan haka ana sallamar su a ranar suka tattare da yaran suka nufi Kano ba wanda yabi takan Fatima. ***** A Kano kowa tir yake da halin Fatima na wannan irin rashin imani da ta girka, sai dai wasu suna fad'in bai dace a barota a hannun y'an sanda ba zasu iya lahanta ta. Har gida ya kai su Farida yana mai bawa abokinshi hak'uri a

Chapter 3 of 19