Share this page
Farida har ta dulmaya tunanin gata a gidanta ta share ta shiga kitchen tana yiwa mijinta girki,har haskowa take yaran su sun dawo tana musu wasa. Murmushi tayi tare y'ar murna, "Allah zanyi abu in an min aure Aisha.. Tsaki Aishan tayi tare da bud'e sabon shafin littafin HAMIDA. "Aure? Da sauri ta ce "Eh mana,koh bakya so? Baki Aishan ta ta6e tare da fad'in "Allah kiyaye,kuma zan fad'awa Umma na ce baki da aiki sai zancen aure. Da sauri ta warce littafin hannun Aishan. "Ni kuma sai na nuna mata har yanzu kina nan da karatun nan na littafin soyayya. Tsere suka fara cikin hostel din tana ta bata bazata fad'a ba tana zille mata. Hutu suka yi na Junior waec da suka zana. Cike da murna aka dawo gida harda hawayen anyi missing Umma. **** A gaban mirrorn dakinsu suke sai mangaje juna ake wajen yin kwalliya suna dariya. Dankwali Aisha ta dakko tare da fara daurawa cikin kwarewa tana murmushi. Ita kam riga da skit na english wear ta sanya masu ruwan zuma tana taje gashinta. "Gaskiya kin kwafsa Farida.. Baki ta turo tana d'aura ribbon. "Ke ni fa bazan iya rayuwar zani da d'aurin wahalar nan ba,sai dai in ki fasa zuwan dani. Kwafa Aisha tayi tana yafa gyale. "Amma wannan ai iskanci ne,ya ma za ai ga ankon aure ki wani sanya k'ananan kaya? Ribbon din ta cire da sauri tare da hullarwa a gaban mirror "Toh na fasa zuwa.. Kofa ta bud'e tare da fita waje,da sauri Aishan tabi bayanta tana kwala kiran Umma wacce tasan ita kad'ai zata sata dole. "Umma.. "Oho dai,na ce ba zani ba,dama in kaje banda cin rai mey ka ke diba a gidan auren... Fitowar Umma ne yasa tai shiru tare da turo baki. Da sauri Aisha ta ce "Yauwa Umma,ji wani wulakanci gun Farida dan Allah.. Magana take kamar zatai kuka tana kallon Faridan dake mata gwalo. "Mey tayi? Ke fa Allah ya yi ki da mita Aisha... Buga kafa Aishan ta fara cikin shagwa6a. "Toh naji,mey tayi? Nuno Faridan tayi "Ki kalla fa Umma,tsakani da Allah wai bazata sa ankon Ummahani ba da wannan yan duniyar kayan zata.. Magana Umman zata yi Faridan itama ta hau shura kafa. "Yi hak'uri muje zan d'aura miki,amma ke ce yau baki da gaskiya Farida,kuma koh ni bazan barki ki fita da wannan kayan ba. "Wayyo Umma,na tsani zani,sai da na fad'a mata taje tasa aka mana,haba,mutum yaki waye wa,ana yayin skirt mu aganmu da zani? "After all ma ni fa ban iya d'aurawa ba kin sani Umma.. Kamota Umman tayi da sigar lallashi. "Toh naji ayi hak'uri muje ni zan d'aura miki nace,a bar... Sallamar Abba ne yasa Umman tai shiru jin yana fad'in "Bissmillah".. Cikin sakewar fuska tare da nuno Farida da halamun ta rufe gashinta. Hijab din Umman ta shige gaba daya jin har an shigo. "Umman su ga bakin Abuja.. Baki Umman ta washe ita da Aisha ganin Abban Saifu dasu Saifu suna fad'in "Sannun ku da zuwa. Tuni kamshin turaren su ya bad'e parlourn. Jin sannun taki ta kare yasa Farida dan yaye hijab din ta yadda fuskarta zata baiyana. Ilahirin parlourn ido suka zuba mata ganinta cikin hijab din Umman tana kok'arin yayewa Umma na sake tura ta ciki amma saida ta fiddo fuskar. Daya bayan daya take binsu da kallo har ta sauke kallonta kan uncle din Abuja,yake ta musu kamar yadda taga suna mata kan da sauri ta sauke tare da komawa ciki tana dan tura Umman halamun su tafi d'aki Umman na yake cikin jin iskancin Farida. Kai Uncle din ya kad'a jin Umma na fad'in "Haba Farida.. Murmushi ya yi tare shima da fad'in "Farida"... A hankali. Da hijab ta fito ita da Aishan da Umma sai wani sinke kai suke. Cike da ladabi suka gaishe shi daga zaune su ma su Saifu suna gaida Umma. Kowa yaran kallon kowa yake yadda ya girma,sai dai ita Farida tafi mamakin girman su Saifu a shekara 4 kawai. Hannu ta daga ma su Saifun halamun 'Hi' ganin suna gulmarsu suna murmushi shi da Amjad. Ganin hakan su ma suka daga musu. Sultana take kallo ganin yadda ta zuba musu ido tana murmushi hannu a baki. Murmushi tai mata har hakoranta masu d'auke da wushirya suka baiyana. Hannu ta miko mata tare da fad'in "Sultantee" a hankali. Kabir dake kallonsu da mamakinshi yaga Sultanan ta mike zuwa gun su Faridan. Tashi sukai tare da bin Umma kitchen, su dai su Saifu da suka ganeta sai kus-kus suke yi. Bayan sun ajiye suka sake komawa kitchen, jimawa kad'an sai ga su sun fito Farida rike da hannun Umman suka nufi d'akinsu. Tamkar y'an biyu haka suka fito komai iri d'aya gyale a hulle a kafad'a, da Umma ta gyara sai Faridan ta sake sauke wa tana zunguro baki,suna ji Umma tana fad'in "Eh dai kuje tunda ta yarda tasa. Mayarda Sultana sukai tare da yi ma su Saifu sallama. "Abba sai mun dawo, Cewar Aisha. Kai ya kad'a yana zira hannu a aljihu tare da fad'in "Ku tabbatar magriba bata muku a hanya ba. Kai Aishan ta kad'a tare da kar6a hannu biyu. Shima Abban su Saifu ciro wa ya yi tare da basu, "Gashi ku kara toh. Kai suka girgiza suna kallon Abba. Abban ya kalla,sai ya ce "A'a, ba ruwana. Yana dariya,dan haka sai Aisha ta kar6a tare da fad'in sun gode. Tashi sukai gwanin ban sha'awa kansu daya,sai dai kaurin jiki da daya tafi daya. Da kallo suka bisu ganin suna dan dukan kafad'ar juna kamar yara cikin tsokana. Kai Kabir ya girgiza tare da murmushi. "Lalle kam abokina har yau su Farida basu girma ba. Kai Abban ya kad'a shima yana binsu da kallo har suka fice "Ai bana tunanin yaran nan zasu girma,barin ma dai Farida. Murmushi ya yi yana tunanin abinda ya kawo shi. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 25_Su Abdallah su Saifu su ka bi d'akin su wanda suka dawo a islamiya. Ajiyar zuciya ya sau tare da kora ruwa tukunna ya kallo Abba. "Bana 6oye maka komai abokina,koh munyi nisa ina da hanyar samun shawara kamar kullum yau ma nazo ma da ita. Zama Abban su Farida ya gyara tare da bawa abokin nashi nutsuwar shi. "Wato na raka shekara hud'u ba tare da nai sha'awar kara aure ba a rayuwata har yau din nan tun bayan rasuwar marigayiya. Kai ya kad'a mishi tare da fad'in "Hakane. "Bazan ce maka ina jin dad'in zaman haka ba,amma dai nasan ina manage in har nai la'akari da yara na 4 duk a karkashina ba mai tallafa min. "Komai na ya zama koma baya, dan latti na koye shi,dan dole sai na tabbatar kowa ya shirya kamin na sama mana abincin breakfast nima nayi na sauke su school tukunna ni na nufi office. "Ka sani da bani da sauran yadda ga mata,duk da akwai wata colleague na da take shige min amma ni anshani na warke gaskiya. "Toh yanzu kullum Sultana bata da aiki sai na ita ma tana son Momy kamar na y'an class nasu. "Takan min kuka wataran, har nake tunanin koh zan yardewa Zubii ne bisa sharad'i.. Ajiyar zuciya ya yi. "Amma kasan mey? Kai Abban su Farida ya kad'a. "Ranar farko da su Saifu nai latti ban dakko su ba suka dau taxi har office a lokacin Zubii ta tsayarni. "Zo ka ga yadda suke dallah mata harara wanda ba shiri nai mata sallama muka wuto gida. "Tun a mota Saifu ya fara fad'in shi ya tsaneta ba ma yason kara ganinta dani. Dariya yai, "A lokacin nai dariya,domin yadda kasan ni ne d'an Saifu Baba, haka ina ji ina gani na fatattaki Zubii duk da gargadi da nake sha a office na yawan latti na wanda nake tsoron kar ya shafi aikina. Shiru ya yi tare da sunkuyar da kai yana furzar da iskar bakinshi. Ajiyar zuciya Abba ya yi. "Matuka ina ganin kok'arin ka abokina,dole zaka samu matsala tunda ka hana kanka sukuni. Kai ya dago da zummar tambaya sai ya kad'a mishi kai halamun eh mana. "Rayuwa ba'a taru an zama d'aya ba,dole bazaka dauwama a haka ba har karshen rayuwa, in su Saifu basu bukatar uwa nasan gaba Sultana zata nema,dan mace sai mace "Ka cire shakku,ka ruki Allah ya baka mafi alkairi InshaAllah zaka ga dai-dai. Kai ya kad'a halamun ya gamsu. "Toh yanzu meye shawara? "Dan fa tuni na cire Zubii cikin tsarina dan yanzu abinda yarana suke so haka za'ayi. Jim Abba yai yana murmushi, "Eh toh,akwai shawara da ni nake gani zata bulle, amma ina son ka samu Umma kaji mey zata ce game da shawarar in yaso sauran mey sauki ne.. Zama Abban Saifun ya gyara cikin zumudi. "In har zata bulle min da yarana ina maraba da ita... Kai Abba ya kad'a, kan dalla-dalla ya fara zayyano mishi shawarar yana sauraron shi har sai da ya kai aya. Kai Kabir ya fara girgiza wa, "A dai sake wata,haba, ina ni ina... "A'a, ka tuntubi Umma na ce in tai na'am toh ka zurfafa tunani akai,dan wannan a gani na shine kawai hanya daya mafi sauki. Shiru yai yana kallon wani waje,ya sani da zai yi wuya abokinshi ya bashi shawarar da zata cuce shi,dan haka sai ya yarda a zai tuntubi Umman. ***** Shiru itama Umman tayi tana duban wani gu cikin tunani,hakan yasa ya gane batai na'am ba. Murmushi ta fara tare da dubenshi, "A gaskiya da na auna koh ni wannan shawarar tai min dari bisa dari Kabiru,sai dai fatan Allah yasa ta bulle, ya kuma sa wannan shi zaifi zama mafi alkairi ga yaran. Ajiyar zuciya ya yi,har ga Allah shi dai wannan abu bai mishi ba koh kad'an. Sai dai da mamakinshi da ya shawarci Nafisa sai ta fara dariya tana kiran great. "Wallahi bros shawara ce wannan mai kyau ka duba,a hankali a gaba zaka gane alfanunta. Sun fa sashi a tsakiya, Hafsa,Umman Uzairu,Nafisa da Umma kowa bak'inshi yazo d'aya da na abokinshi,dan haka sai yaki komawa tare da 'Istikhara' ta kwana uku,hud'u amma kullum yana jin abin a ranshi, dan haka sai ya koma ga abokinshi dan sanarshi yadda kowa ya ce da kuma Istikharan da ya yi. Murmushi Abban ya yi na jin dad'i, kamin yai magana Kabir ya katse shi. "Toh amma abokina ni fa abin ne sai nake ganin kamar... Da sauri Abban su Farida ya tsayarshi, "In har kayi na'am, toh wannan ba wani sabon abu bane koh abin assha, believe me,a gaba zaka gode Allah ka kuma gode min,dan nasan kayana. Shiru ya yi yana hasko abin,sai yaga duk wani bankwara kwai. Dan haka jiki a sanyaye ya fita,sai dai har cikin ranshi ya kasa nadamar hakan. **** "Kai,ina..A gaskiya da sake,wai an bawa mai kaza kai. Kai ta girgiza tare da d'auke kai tai kicin-kicin da fuska. "Wannan ba shawara ba ce,a gaskiya batai ba,tab.. Kallonta yake yana mamaki,yau wai Sumayya ke musu dashi? "Sumayya? Ido ta rufe tare da girgiza kai. "Abban su Sumayya koh gaskiya? A gaskiya da duba a lamarin nan dan kaf a gidan nan Allah bani da wata y'a da ta isa aure har za'ai min sadakar ta balle Farida,tab ka dai sake lale.. "Ni fa ba musu na tambaya ba,dan tuni na riga na bashi Aisha,in kina ganin Faridan ita ce taki kuma ta gaban goshin ki,naji tayi k'ank'anta,amma Aisha nada kaurin jiki ai... Tashi tayi tare da girgiza kai "Daga Aishan har Farida nawa ne,ban ware ba,na kuma ce basu isa aure ba wallahi, ka fa sake shawara. A tunzure ya mike,sai dai ganin ta fara hawaye yasa ya rage murya. "Nu nake iko da yarana ba wani ba,kar ki bari tun yanzu yarana su fara bijire min dan bazan... "Wayyo Allah na shiga uku... Da sauri suka juya jin ihun kukan Aisha a bakin kofar hannu bisa kai. Tsawa Abba ya doka mata,dan haka tuni ta farke da kuka iyakar iyawar ta tana fad'in ita bata so. A tunzure Abba yai yo kanta Farida da ta fito jin ihun Aishan ta kare, "Dan Allah Abba kai hak'uri.. Umma ya kalla wacce ke goge hawaye,da sauri ya nuno Aishan. "Baki da ikon hanani abinda nayi niya, wallahi na rantse kamar nayi na gama.. Waje ya fuce,da sauri Umman ta zauna akan gado da6ar hawaye na zubar mata,ganin haka da sauri Aisha ta cika Farida ta nufi gun Umma gwiwa biyu tana kuka. "Wallahi ni Umma bana son aure yanzu,dan Allah ki taimakeni ni bana so karatuna zanyi Allah.. Ido Farida take rabawa, ganin Ummanta yau na kuka,tun tashinsu bata jin ta ta6a ganin sa6ani tsakanin iyayen nasu sai yau. Hawaye ta hau goge wa Umman "Ni fa ban gane abin da ake nufi ba Umma? Auren ake wa kuka? Dama babu kyau? Cike da sauri ta ce "Rufe min baki,ku mey ku ka sani?... Shiru tayi tare da goge hawayenta ta kallo su. "Farida.. Ido ta zuba mata. "Idan ki ka sake ki ka nuna kina son auren nan wallahi ni da ke ne a gidan nan,dan naga halamun ba hankali gareki ba har gwara Aishan tasan ciwan kanta. Shiru tayi kawai tare da zuba wa Umman ido tana tunanin wani abu. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 26_Kukan Aisha ta daina jin Umman batai na'am ba ta tashi tare da zama a d'ayan gefen gadon tare da daura kanta kafad'un Umman tana jan zuciya. Hannu Umman takai fuskar Aishan. "Yi shirun ki Aisha. Kasa shiru Faridan tayi tare da fad'in "Amma Umma... Da sauri Umman ta kallota "Ki ce toh kawai Farida,in kuma kuka na ki ke so ganni bari nai tayi... Da sauri ta hau girgiza kai tana goge ma Umman fuska duk da ba komai a kai itama kamar tai kukan. "A'a nayi shiru yi hak'uri Umma. Kanta itama ta daura a d'ayan gefen kafad'ar Umman,ita dai an mata daya,ga samu ga kuma kwanan yunwa,amma tasan tunda Umma bata so toh kila akwai wani abin da babu kyau acikin aure. Abba da ya dawo yai tsaye yana kallon su tare da girgiza yana murmushi ganin dramar Umman tasu,jin sautin murmushin nashi yasa suka juya,Umma na ganin shine tai kicin-kicin kuma. A gefen su shima ya zauna yana kallonsu barin Umman da taki yarda su had'a ido. "Bari naga Umman taku in yaso naji meye matsalar. Kai suka kad'a tare da tashi ganin Abban ya sakko harda murmushi. Fita sukai sai ya kulle kofar tare da zama gefen Umman sai ta kara matsawa,bai zuciya ba ya sake matsawa yana murmushi. "Haba Summy.. Kai ta kawar jin ya kira sunan dake sata dariya. "Toh naji amini afuwa a fad'a min meye matsalar. Kamar wata su Farida haka take turo mishi baki kadan-kadan irin na shagwababbu. "Ina jin Summy.. Murmushi kuwa tayi kamar yadda yai dan shi. "Ni dubawa nake so kayi yaran nan ba abinda suka sani game da aure ne barin ma Farida kar taji labari. "Koh fa 15 ba wacce acikin su ta kai ka duba wannan lamarin. Kabli da Ba'adi ta fara kawo mishi yai shiru tare da zuba mata ido yana murmushi sai da ta kai aya ta dire tukunna ta hau kunkuni. "Kuma ma..kuma ma fa... Cike da murmushi ya ce "Kuma mey? Shiru tayi tana murza yatsunta. "Shekarunki nawa aka miki aure ne ni na ma manta dan tuna min.. Inda-inda ta fara mishi na kan ta dakarkare ta ce ''Sha takwas. "Saboda Allah fa Summy? Kai ta kawar dan sarai tasan ta zuluka. Hannunta ya kamo tare da rike su kam ya had'a suka zama (15). "Shekarun ki goma sha biyar aka kawo min ke gidan nan da wasu watannin,ki ka haihu a shekara daya da rabi. Shiru tayi dan tasan haka zancen yake,dan haka yaci gaba. "Nana Aisha(R.A) tana y'ar shekara (6) aka aura mata ma'aiki (S.A.W),sannan ta tare a shekarunta (9) a gidanshi... Magana zatai ya girgiza mata kai. "Ina kai ki tukunna. Shiru tayi tare da sauraron shi. "Har yau bana jin a kauye an daina wannan al'adar ta aurar da yara da sun fara sanin kansu daga shekara 10,11,12,har zuwa sama. "Naji zaki ce min ne y'an da dana yanzu ba d'aya bane,amma kiyi duba a birni nan ana aurar da yara wanda basu kai shekara 15 ba Allah nasha gani Sumayya. "Ki min alfarma kar ki tsorata yaran nan,aure bai kashe ki ba,ba rage ki da komai ba. "Kinfi su sanin waye Kabir, ya rayuwarshi ta kasance har zuwa yau din nan.. ''Zan so a abinda na yarda dashi jinina ya nuna wa Kabir da ban-banci,zanso ki barni nai amfani da damar ganin yaran shi dasu Aisha sun saba in yaso in sunje su dauke ta kamar kawa ta inda ba matsala. "Na yarda dake Sumayya,hakan yasa na yarda da yarana kaf ciki babu mai iya kwata halin su Tabawa koh Fatima. "InshaAllah bazanji kunya ba,na yarda dasu zasu iya. Ajiyar zuciya tayi,dan haka sai ya cigaba da kwarin gwiwar shi. "Ki taimakeni ki tayani wannan jihadin, ina so su gane akwai banbanci daga yaran har Kabir,dan Allah ki min alkawarin wannan. Kai ta girgiza, "Ka bani zuwa gobe zan duba lamarin. Murmushi ya yi tare da kad'a mata kai. "Koh nan da sati ne na baki. Kai ya dungure mata. "Ashe a gunki yaran nan suka koyi daru ban sani ba. Kai ta sunkuyar tana dariyar kunya. **** Washegari ma duk sukuku suka tashi. Duk sunyi tsumu akan gado kowacce na tunani. Chan dai Farida ta ce "A gaskiya kin luza wallahi Aisha. Harara tai mata tare da gyara kwanciya. "Ni nasan mey ranar chan na karanto a littafi ai Farida,ina da wayona Allah bazan yarda ai min wannan abin ba da kankanta ta. "Ba ma wannan ba,haka kawai sai a min aure ba soyayya ba komai ban san miji sai ka ce auren da... Katseta Farida tayi a dan tsorace jin bayanin Aisha. "Meye toh a auren dan Allah fad'a min abin tsoro ne? "Zaki tsara ke ba iyayi ba? Kwafa tayi "Allah yasa Abba yai miki toh. Kai ta girgiza da sauri. "A'a wallahi nima ba amin ba tunda abin tsoro ne, ji muguwa. Duka ta kaiwa Aishan tana turo baki "Uhmmm Gyaran murya Umma tayi ganin kofar su a bud'e tare da kwankwasawa. Tashi sukai ganin Umman tare da yin shiru. Zama tayi tare da musu murmushi. "Yau ba wanda naga ya fito tun bayan gama breakfast dinku lafiya duk gidan shiru? Kai kasa Aisha tayi,yayin da Farida ta girgiza kai "Lafiya Umma. Kai ta kad'a tare da gyara zama. "Tambaya nake son muku kowa ta bani tata amsar. Kai suka kad'a tare da bata nutsuwarsu. "Aisha.. Cikin sanyi ta amsa. "Ina so ki fad'a min mey ki ka fuskanta a game da aure? Kai ta duk'ar da sauri gabanta na fad'uwa,hakan ya nuna wa Umma ta san takan abin ita. "Ina jinki. Ido suka sa mata ita da Farida,sai ta hau in ina tana susar keya. "Ni fa..Umm..nima ban sani ba. Murmushi Umman tayi,da sauri Farida ta zungureta. "Allah Umma karya take ta sani.. Rai Aisha ta had'a "A ina na sani. K'yaleta tayi tare da kallon Umman. "Ni na sani na fad'a miki? Dasauri Umman ta kad'a mata kai halamun ta fad'a. Zama ta gyara ta fara lissafi, "A islamiya malamin mu ya ce 'aure sunnar Annabi ce,ya ce duk wanda yai aure ya haihu da yawa ranar gobe kiyama annabi zaiyi alfahari da zuri'arshi dan ta kara yawan al'ummar shi. Kai Umma ta kad'a tana murmushi dan jin anzo wurin. "Ina ji. Da sauri ta cigaba "Yauwa,daga nan sai taru a daura aure da mijin ai party koh walima daga nan sai a kai amarya gidanta. Kai Umma ta sake jijjiga mata halamun tana ji,ita kwa tsakaninta da Allah ta dage tare da ci gaba. "Yauwa,sai tai ta aiki tana biyayya inji malamin mu duk macen da bata biyayya a wuta za'a sata hakane koh Umma? Cike da kaguwa Umman ta kad'a kai sai ta cigaba. "Daga nan sai ta haihu,tai ta haihuwa har ta daina in yaran sun girma.. Tsayarta Umman tayi, "Toh ya zata samu cikin tukunna? I mean a in btw auren da haihuwar Kai Aisha tai kasa dashi halamun wai kunyar Umma take ji. Ita kam ido ta zubawa wani waje halamun tunani,chan da sauri ta ce "Na tuna Umma.. "Bayan anyi auren tana shara,dafa abinci,da sauran su. "Toh daga nan fa? Cewar Umma, Kallon Umman take da halamun tambaya. "A'a sai ta samu ciki man Umma ta haihu ai na fad'a, Kai Umma ta kad'a halamun gamsuwa. "Na ji,shine na ce taya zata samu cikin? Cikin cire shakku ta ce "Idan mijinta yana bata abinci man tana koshi kullum sai cikin yai katoto kamar haka..hakan nan Nuna musu take halamun girman cikin da nata cikin. Hannu duk biyu Umma tasa tare da dafe goshinta cikin takaici tana kiran "Ya Ilahiii... "Mtsww.. Tsaki Aisha tayi tare da harararta. Gaba d'aya kallonsu tayi ganin Umma kamar ta sau kuka tare da dagawa Aisha kafad'unta halamar tambayar mey tayi? Ita iyakar gaskiya ta fad'i ba ragi, dan haka sai ta ce "Umma mey nayi? Koh ba haka bane? Dagowa Umman tayi tare da daga mata kai halamun haka ne. Kallon Aisha tayi cikin farin cikin ta fad'i dai-dai. "Dalla ba gashi ba na fad'i dai dai,da har da min tsaki dan ke kin kasa. Baki ta murgud'a tana kallon Umma da ke kok'arin tashi jiki a sanyaye ta fice. Lalle zata kwari yaran nan in har tai la'akari da rashin yardar Aisha wacce tasan komai, gefe d'aya ga Farida mai son auren amma ba abinda ta sani sai iyayi. Amma mamakinta da abin haushi ma bai wuce na malamin islamiya ba. A ganinta wannan bayanin su yafi chanchanta su sanar da kamar dai Farida ma'anar aure ace ta sani ba wai manufofi ba. Zama tayi tare da sakar ajiyar zuciya. Tabbas Aisha tasan komai,dan tasha kamata da karatun littafi,tasan koh a chan zata iya fuskantar wani abu fakacin Farida uwar y'an shirme ita dai batta a shakiyanci da iyayi. Dan haka dole wacce tasan takan aure ita za aiwa. Kai ta jijjiga cike da zancen zuci. "Aisha yafi chan-chanta kam,tunda Abban nasu ya dage. Da wannan ta rufe in Abban yazo su yanke shawara kawai a bawa Uncle Kabir Aisha. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 28_Gidan su Uzairu suka je jin yana kukan rabashi da Rukayya da sukai har tai aure ta hayayyafa a wani waje. A hankali irin ukubar da Kabir yaci yake sauraro har izuwa randa Allah yafi karfin su Tabawa ya tsaya da kafafunshi. "Lalle ka ga rayuwa Kabir,ka ga ukuba,ka ga jarabta iri-iri a duniyar nan. "Na gode Allah da ya rayaka har ka zama wani daban cikin yarana kamar yadda naso tun farko. "Duk hukuncin da zaka d'auka akan su Tabawa bazai gamsar dani ba mud'in ban gansu a kurkuku ba Kabiru. Kai ya girgiza mishi. "Kayi hak'uri Abba,wannan ba komai bane in har kaji dayan laifin,na sani ga duk DAN ADAM(sis Ruffy) bai isa tsallake KADDARA shi ba,a yanzu bana ganin su Tabawa a gabana sai ku kad'ai. "Dole na gode Allah da ya nufa duk wani sihirinsu ya warware komai. Kai ya kad'a, "Na sani,amma matuka su Tabawa sun cuce ni ba kad'an ba. "Allah ka bi ma kowa hakkin shi kawai. Kai suka kad'a tare da fad'in "Amin. "Bana bukatar na koma kusa dasu sam,a barni a nan kawai. Murmushi Kabir ya yi,yau farin cikin har yaso yai mishi yawa. Dan haka yana fita ya nufi gun masu gini dan gobe su je su fara foundation na ginin. A yau d'aya farin cikin shi ya dawo sabo fil. Dan haka daga nan gida suka dawo gun Umma. "Umma da gaske. Kam ya rungume Umman yana mata hawayen dad'i. Dagoshi tayi itama idonta fal hawaye. "Alhamdulillah, mu gode Allahn da baya bacci Kabir,na gode Allah da yasa yau komai ya kare. Kai ya jijjiga mata yana washe baki. "Insha-Allah a gobe nake so a fara zuba katangar da zata raba gidan Abba da nasu Tabawa a fara gini. Kai ta girgiza mishi. "Ba za ai haka ba Kabir. Murmushi ya yi. "Wannan ne babban adalcin da zan iya musu Umma,dan ba dan mu ba da tuni gidan ma sun bari. **** Baki har kunne da daddare ya isa gidan abokinshi,ya ma kasa barin gari ya waye. "Alhamdulillah toh,sosai nai maka murna,ubangiji yasa karshen wahalar kenan abokina. Cike da farin ciki ya ce "Amin abokina. Sun jima tare tukunna suka dawo batun aure. Jim ya yi yana murmushi kai a kasa. "Farida"... Kai Abba ya kad'a. "Eh Insha-Allah, Farida ce matar. Kai ya jijjiga. "Amma ta yarda koh? Ta yarda da auren tsoho? Murmushi Abba ya yi tare da kad'a kai. "Farida bata da matsala,asalima murna take bisa za'a mata aure,abu daya na sani sai kayi hak'uri dan Farida yarinya ce koh auren bata sani ba. "Abu d'aya nake fata shine ta rayu a gidan ka ta yadda zata gama wayonta a cikin iyalinka wanda tanan komai zai fara. Kai Kabir ya kad'a. "A gaskiya samun aboki irin ka tun yarinta zai matukar wuya. "Duk rintsi,duk tsanani,duk dad'i kana tare dani. "Na gode da wannan kyauta,na gode da wannan karamci. Kai ya kad'a. "Kar kaji komai,a yanzu dai mun zama daya,abu daya na sani yanzu na girma maka,dan siriki nake remember. Hannu ya bashi tare da tafawa suna dariya. "Lalle aboki ka ban aiki,yanzu ta yadda zan fara da su Saifu nake tunani. Kai ya kad'a, ''Insha-Allah komai

Chapter 7 of 19