bisa abinda ya faru.
"Ta su Farida mai sauki ne abokina in har da dubi yaran nan,na rasa wani irin zamani muke ciki wanda mata suke daura kishin su bisa yaran da ba nasu ba har su iya danne imaninsu su aikata haka.
"Wanda zai iya haka ga yaro tabbas zai iya kisan kai,duk in anyi duba da taka rayuwar a hannun *MATAN UBA*.
Murmushi ya yi dan tuna baya da irin tashi ukubar da har kullum yake ganin ba wanda yasha irinta hannun *MATAN UBA*.
"Sai dai wani hanzari ba gudu ba.
Kai ya dago yana duban shi.
"Duk tsiya taci daraja d'aya a hannunka Kabir,ka daure kayi afuwa koh ba komai yanzu nasan ta d'an d'ana kud'arta,ba dan halinta ba dan Halima dake a matsayin jinin..
Ido ya rufe tare da jingina kai a kujerar,fad'in Halima yasa duk yaji wani iri,ba dan yaso ba sai dan irin tausarshi da abokinshi da Umma sukai ta mishi yasa a saki Fatima wacce tuni aka wuce da ita asibitin gwamnati dan galabaita.
****
"Umma"...
Faridan ta kallo tare da amsawa.
"Wallahi ina tausayin yaran uncle, ban ta6a ganin muguwa irin Fatima ba sai a makaranta.
"Umma har muka taho kullum suna fad'in sun tsani step Moms nasu,har nake ganin wani iri.
Murmushi tayi tare da kad'a kai.
"Basu ji dad'in su bane Farida,dan haka har abada baza su daina tsanar *MATAN UBA* har sai randa suka dace da tagari wacce zata goge tabon y'an baya.
Tsam Faridan tayi tana tunani,duk da shekarunta bai kai ta samo musu mafita ba amma a ranta gani take da ita ce bazata ta ta6a musu mugunta ba kamar yadda Ummansu bata ware waye y'arta a tsakanin ita da Aisha.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
*ASALIN LABARIN*
11_Kabir yaro ne na biyar ga Malam Yusufa,asalin su y'an kauyen Rano ne kamin kakansu Kabir ya dawo cikin Kano yai aure.
Yara 16 ya mallaka suna rasuwa har Allah ya kawo Yusuf da Nasir suka zauna su biyu rak.
Mahaifin Kabir Malam Yusuf yana da mata uku,yayinda Nasir kaninshi yake da guda d'aya, kusan duk tare akai auren,sai dai shi Malam Yusuf koh shekara ba ai ba ya sake aure saboda iya rashin zama irin na Tabawa uwar gidanshi.
Masifa sosai ya gani lokacin da ta riski har an kai k'walla na amaryarta.
"Wallahi Isubu ka sai wa kanka bala'i da masifa a gidan nan mud'in ka kara auren nan.
"Bacin ga jaraba mey zai sa aure shekara guda kawai wai zaka kara koh haihuwa ban ba...
"Ke Malama ki fa dakata min..
"Bazan dakata ba Isubu, ba haka ka ke so ba?
Kai ta kad'a
"Toh ka samu.
Kallonta yake yana mai wani tunani cikin ranshi.
Shin ya ma akayi ya lalumo Tabawa a matsayin matar aurenshi?
Hala ya makance ne lokacin da bai gano rashin tarbiya irinta gidan su ba ya auro ta?...
"Eh kalle ni da kyau,Tabawa ce d'aya da ka sani..
Kai ya girgiza kamin ya juya da zummar fita yana fad'in
"Allah ya kyauta...
Tsakar gida ta fito tare da fad'in
"Ya kyauta maka, macuci kawai.
Kai ya kad'a tare da fita waje rai na kuna,tabbas dole ma ya jawo auren nan ayi a gama koh zai samu sukuni.
Duk yadda Tabawa takai da iya masifa amma amarya sai da ta shigo gidan Malam Isubu.
Lami ba tazo da mutunci ba tunda taga take taken uwar gida Tabawa,dan haka amarci kad'an aka ci Malam Isubu ya koma y'ar gidan jiya.
Kullum acikin raba fad'a ake tsakanin Tabawa da Lami,abu sai ya had'e mishi goma da ashirin.
Dan haka sai ya zabi zaman shago in da ya bud'e a kwanar gidanshi.
Bashi ba sake dawo wa sai in dare ya raba yasan kowa tana d'akinta.
***
Shekaru biyar ya jure,dan a yanzu fad'an ya dawo na yara tunda kowacce ta haihu konika yara biyu-biyu duk mata.
Karafkaf yaran ba wanda ya bar halin mahaifiyarta,dan haka su ma tun suna yara suka fara cin kai a tsakaninsu.
"Ni abinda nake gani Malam Isubu ka nema wa kanka sauki kamin masifar gidan ka ta sa ma ciwo.
Tashi ya yi daga kishingid'en da yake a kan bujukura a zauna.
"Ta ya-ya Malam Nura?
Zama shima ya gyara tare da tofar da guntun goron dake bak'inshi.
"Ina yarinyar nan da take kawo d'an b'uka shagonka ka siyar wa Ummanta?
Kai ya kad'a tare da fad'in
"Eh naji,Y'ar wajen Malam Kabiru...
Baki ya washe tare da fad'in
"Eh ita.
"Kai ya kaga tarbiyar yarinyar?
Murmushi ya yi tare da sunkuyar da kai.
"Ba laifi gidan kam akwai tarbiya,barin ma yarinyar...
Baki Malam Nura ya washe tare da fad'in
"Kawai ka nemeta,in dai har kun daidaita ina ganin zata iya zame maka waraka a gidan dan tana da hankali na yaba.
Tsam Malam Isubu ya yi yana dan murmushi, ba tun yau ba yaji yarinyar ta shiga ranshi,sai dai ganin abinda ya kawo ta kawai take shi yasa bai maida kai ba.
Shawara ya ce zaiyi,duk shi ya aminta har cikin ranshi da yarinyar.
Kan wani lokaci har magana tayi nisa tsakanin Rukayya har an kai kayan tambaya da sadaki.
****
"Alhamdulillahi dai,dan nima na haifa Tabawa balle ki min gori,yadda ki ke da biyu mata nima haka na haufesu,da ma maza ne kyayi da dalili...
"Oho dai,na fad'a miki ya'yan ki su kiyayi ya'yana koh na...
"Toh kaji,ana ta cin kan ne?..
Shiru sukai tare da juya wa jin muryar mai gidan.
Karasowa ya yi yana mai cigaba da mita.
"Ku kwantar da hankalinku, dan kunyi na kud'inku saura nawa.
Kallon-kallo suke da rashin fahimta.
"Mey kenan haka ke nufi Malam?
Ledar hannunshi ya ajiye da ba wanda ya iya amsa daga yaran har iyayen.
"Aure zan kara nan da mako hud'u masu zuwa.
Baki suka saka tare da zuba mishi ido.
"Atoh,kuma ji da wai,dan ban ma yi niyar fad'a muku ba sai ranar aure sai dan kawai hakkin ku sani.
D'akin Tabawan ya shige inda a nan yake da kwana.
Sai bayan ya wuce Lami ta kalli Tabawa tare da fad'in
"Lalle da bala'i Tabawa a gidan nan.
Shiru tai mata ita tama rasa bakin magana.
Bala'i dai bana yasha shi bibbiyu ne akan auren,dan haka sai yafi lokacin Tabawa ita kad'ai.
Takai ta kawo har abinci a gidan bai da kaso duk dan wai ya sadudu,shi kam koh a jikinshi,dan aure kam ba fashi.
By
Feenat Ja'afar
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
12_Jiya amarya ta tare,kan y'an kwanan amarya su kauce sunga abu gun su Tabawa,dan mai kid'an kwarya suka kira ta kad'a musu 'Ladi mai kid'an kwarya asha kid'a asha dad'i ari'.
Da an buga sai su sa shewa tare da habaici suna kiran y'ar mai tallan d'an b'uka da fura.
Ango ne ya shigo da babbar malum-malum yana ta washe hak'ora bayan kowa ya watse.
D'akin Tabawa ya fara shiga da zummar yai mata sallama sai ya tarar da Lami ma tana d'akin.
Mamaki ya gagara barinshi har yau na yadda lokaci guda Lami da Tabawa suka dinke kamar basu bane kajin nan sarakan fad'a.
Kowacce taci daurin 'ture ka ga tsiya' a gaban koshi suna aika mishi harara.
Baki ya washe tare da fad'in
"Ashe ma kuna tare a nan..
Banza suka mishi tare da juya mishi keya kowacce.
Yau ranar farin cikinshi bazai biye musu ba balle su 6ata mishi wannan daren.
"Toh dama sai da safe nazo muku, ga nan balangon ku ga na yara.
"Mtsww aikin banza kawai..
Murmushi ya yi tare da kad'a kai.
"Koyi komai yau dan bazan biye ku ba.
"Allah bamu alkairi..
Tsaki Lami ta kara.
"An dai ji kunya wallahi Isubu, ji yadda ka ke wani 6ari tamkar sabon ango.
Baki ya washe mata tare da fad'in
"Ku dai mu kwana lafiya..
Waje ya yi ya barsu suna cizan yatsa.
"Wallahi ya ma mayarmu wasu bi ta chan Tabawa.
Kwafa Tabawan tayi tare da tashi ta bud'e balangon.
"Wato ita nasan kaza ya kai mata mu ya raina wa hankali.
Kwata Lami tayi tare da fad'in
"Toh kawo in bakya ci ni zanci.
Rai 6ace Tabawa ta kallota.
"Ke ma fa ba mutunci ya gama ratsa ki ba.
Shiru sukai jin an ta6a butar karfe.
"Yi shiru..
Shiru Tabawan tayi suna kasa kunne.
Balangon suka gama cinyewa kamin aka hau goge man ajikin kaya cikin sauri jin muryar Malam na y'ar dariya an ajiye buta.
"Muje muji,ji wata munafukar dariya da yake.
Gida ne na kasa mai d'auke da dakuna uku, d'akin Lami da Tabawa a jere sai nashi dake kallon nasu da yanzu ya dawo na amarya.
Cikin sand'a suke bin bango har suka iso kofar d'akin amarya suna kasa kunne.
Sallamar idar da sallah suka ji Malam ya yi,da sauri Lami ta zunguri Tabawa nufin ta matsa mata Tabawan tana doke hannun Lamin halamun tai shiru.
Dan tsaki Lami tayi da zummar komawa d'ayan gefen basu nufa ba suka ji Malam ya daga labule da sauri suka hau kame-kame har suna yin gware.
Kai ya kad'a tukunna ya ce
"A'a, kuyi zamanku dan kofa zan kulle na koma ciki.
Salin alin kowa tai d'akinta da borin kunya,kai ya kad'a tare da tura kauren ya kulle yana tur da wannan jahilci na su Lami.
Komai ya sauya wa Malam tun bayan aurenshi da Rukayya,dan ita mai kunya ce da kawaici, duk da tana fuskantar tsangwama gun su Lami in har ba Malam.
Ga jarabar fitsara da ashar da yaran gidan ake koya musu su mata duk tana dauke kai.
****
Bayan wata biyu da biki.
Da gudu ta fito daga d'aki rike da baki tai gefen rijiya inda suke wanke-wanke ta fara kela amai.
A razane Lami ta leko dan ganin waye mai aman.
Ido ta zaro ganin amarya Rukayya ce,tasan Malam a d'akin Tabawa ya kwana tasan asubanci yake ya fuce, dan haka da sauri ta banku d'akin ba koh sallama.
Duka ta d'ad'a mata a cinya ganin ta baje sai jan minshari take ga yara a kasa duk sunyi fitsari d'aki na zarni.
A zabure ta mike rike da gun da masifar waye wannan, ganin Lami tuni ta sauya fuska da zummar magana ta rigata.
"Kin baje baki sai minshari ki ke ja ga nan amarya ta kwaso mana magana a gida.
Zani ta gyara tare da daukar dankwali cikin rashin fahimta.
"Ban gane ba fa..
"Dama tun wanchan watan na ce miki tayi tsallaken wata biyu kin ki yarda gashi nan toh.
Fuska Tabawan ta yamutse tare da tofar da yawun bakinta a bangon d'akin.
"Dan Allah ki min yaren da zan gane..
Da sauri ta katseta da fad'in
"Ciki toh gare ta..
Yafico ta tayi jin wani k'ak'arin aman suka hau leke.
Da baya Tabawa ta dawo tare da dafe kai.
"Shi kenan mun kad'e Lami in har ta haiho namiji.
Tsaki Lamin tayi tare da saurin fad'in
"Ji wani mugun baki gun Tabawa?
"Ni muje muga mey ake ciki...
Shiru sukai ganin Rukayyan zata wuce.
Hannu Tabawa ta cije kamin ta ce
"Wallahi yadda ki ka san na shako ta haka nake ji Lami.
"Ki ajiye wannan yanzu musan abinyi tun kamin ya girma.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
14_"Subhanallah Rukayya da gaske baya motsi kam..
Kai ta kawar gefe ganin yadda Inna ke jijjiga yaro amma ba halamun zai motsa.
Ido ta rintse tare da tuno da wannan ayar ta 'ALLAZINA IZA ASABATHUM MUSIBATUN QALU INNALILLAHI WA'INA ILAIHIRRAJI'UN'.
Hawaye ne ya zubo mata wanda bata ma san ya taru ba,a hankali ta cigaba da karanta Innalillahi acikin zuciyarta tana kallon Inna dake dabarar su ta tsofi.
"Inna ya rasu fa,ki daina wahala...
Kai ta dago cike da tausayin y'ar jakar tata.
Ganin zata kara karyar mata da zuciya yasa da kanta ta tashi tare da fita band'aki rike da buta jin Inna na kiran su Tabawa.
Kuka ta fara yi a band'aki, koh ba komai UWA UWA CE,koh ba sabo akwai kauna ta musamman.
Haka tana ji tana gani aka kira Malam sukai ma yaro sutura shima harda hawayenshi.
Kukan dasu Tabawa suke ne wiwi ya fara damun jama'a, dan haka ido kawai Rukayya ta zuba musu cike da wani abu a ranta.
A d'aki suka kule suna ta tuntsiririn dariya ta yadda ba mai jin su.
"Kai Tabawa kin iya shawara,da yanzu muna kwasar bakin ciki a gidan nan na ganin yaron nan..
Baki Tabawa ta rufe mata ganin inuwar wani.
"Waye nan?
Tashi Lami tayi tare da lekawa da sauri amma ba kowa.
***
"Kiyi hakuri Rukayya, nasan kinyi tawakkalli,InshaAllah ba da jimawa Allah zai sake bamu wani.
Kai ta duk'ar tana dan murmushin kunya,duk da a zahiri hawaye ke neman zubo mata.
Tashi ya yi ganin Inna na neman shigo wa.
Sannu a hankali duk sai ta fidda zargi har ta gama wanka lafiya.
Fatan ta Allah yasa mai ceto ne,Allah kuma ya basu wani nagari mai albarka.
Allah kuwa ya amsa,domin koh wata uku batai ba da gama wanka tasan tana da shigar ciki.
Rokonta daya Allah ya inganta koma mey zata haifa.
Allah cikin ikon shi sai gashi wannan karan ba tayi laulayi ba,dan haka ba wanda ya farga da cikin har ya girma.
"Zo Tabawa,muje daga ciki...
Binta tayi ba musu har d'aki,
"Anya zargina ba gaskiya bane kuwa?
D'aurin zani ta gyara tare da fad'in
"Na mey fa?
"Ciki man Tabawa.. Koh ke har yanzu baki da basirar gane mai ciki a ido?
"Mtsww.
Tsaki Tabawan tayi,
"Wai wane irin ciki bayan muna gidan nan koh tari bata ta6a ba balle amai?
Hararar ta tayi,
"Wallahi kina da abin haushi Tabawa,wa ya fad'a miki dole sai anyi amai ake ciki?
Baki ta ta6e tare da fad'in
"Oho.
"Amma ke baki ga yadda kullum take runduma riga da katon mayafi a tsakar gida ba?
Kai ta girgiza
"Ai kin san sanyi ne,dan haka ki bari muga ai dai dan duma ne zai baiyana.
Da wannan suka zuba ido ma Rukayya duk wani takunta,sai dai sun kasa tantancewa,dan tayi kiba ba laifi.
****
"Sannu da zuwa Malam..
Tashi tayi daga kan abinda take tana murmushi ta isa gareshi dan amsar kayan hannunshi.
Shima baki har kunne yake kallonta,a kullum yana dad'a yaba wa tarbiyar Rukayya shi yasa tafi sauyuwa cikin zuciyarshi.
"Yauwa Rukayya,sannu da gida.
Kai ta duk'ar cike da y'ar kunya.
Kwafa Lami tayi a hankali tana aika harara cikin duhu ta nufi d'akin Tabawa.
"Idan da abinda naki jinin na bud'i ido nagani toh bai wuce shegiyar nan ba Rukayya.
Baki Tabawa ta ta6e,
"Ni ai bazan iya sanya ido ina ganin wannan kinibibin ba ne shu yasa duk ran girkinta magriba take min a d'aki.
Kwafa Lamin ta sake,
"Ni ba ma wannan ba,yadda haihuwa ta tsaya mana a gidan nan yanzu ita tafi komai tsaya min a rai.
"In dai har abinda nake zargi ne wato ciki ne da yarinyar nan toh na yarda ita ta sa mana hannu haihuwa ta tsaya.
Tsam Tabawa tayi,
"Lalle Lami akwai ki da hangen nesa, ni sam ban ta6a kawo haka ba.
"Toh meye abin yi yanzu? Dan ko ni na k'agu naga na tara yara musamman maza.
Baki Lamin ta ta6e tana mata kallon tara saura kwata.
"Lami nasan abin yi,kawo kunne kiji.
Daurewa tayi tare da mika mata,a hankali fuskarta ta fara washe wa zuwa dariya.
"Kai amma Tabawa ke dai dusa ce wallahi.
Rai Tabawan ta had'e tana dubenta.
"Eh mana,in ba dusa ba ace tun da kina da wannan a hannunki ki ka bari muna shan wahala?
"Yi hak'uri baizo min ba ne.
Tsaki Lamin tayi tare da zama
"Yanzu yaushe zamu je gidan?
Tunani ta fara
"Yanzu dai bata gari,kuma ni ban san wajen ba,amma duk randa ta dawo sai muje.
Da wannan suka rufe chapter har su na fad'in in sunje mey zasu ce Mai yankan wuka ya musu.
****
A hankali ciki na girma tana cigaba da boye kayanta har yai wata 6,gaba d'aya ya gama bin jikinta,yanzu kam ba sauran 6oye,dan haka yau daga ita sai riga da zani ta fito sai dankwali a kai taci d'auri.
Da Lami ta fara ka'ro a gaban randa ta daga kai tana shan ji ka ke kwat-kwat na shigar ruwa.
Da azama ta cire mod'ar a bakinta cikin kwarewa, tuni ta hau tari tana mai kallon cikin Rukayya ba koh kiftawa.
Murmushi tayi tare da kad'a kai,lalle tasan haka zata faru dan ma Tabawa bata gida.
Har ta wuce tana binta da kallo ta d'au buta ta shige bayi.
Mod'ar ta dangwarar tare da shiga d'aki jiki na karkarwa.
Tabbas ta san ciki ne da yarinyar nan amma gidahuma Tabawa ta batar su,gashi yanzu har ya girma.
Ranar har Tabawa ta dawo tana sincewa tana d'aurawa.
Hakan yake itama ga Tabawan, tana shanya ta shigo cikin ne ya fara mata barka da zuwa,dan haka tafiya take bata koh kallon gabanta idonta na kan cikin har tana neman fad'uwa dan tuntu6e da buta.
Kai ta sake kad'awa dole ne tasan irin zaman da zatai dasu Tabawa.
Tun daga wannan lokaci suka kasa zaune suka kasa tsaye,dan dabara ta kare gashi kawar Tabawa bata dawo ba balle suje neman taimako,dan haka kawai sai suka sa ido suga a haife.
****
Tun jiya take jin dan milmil tana daurewa ganin Malam na gida,sai dai yadda yana fita ciwo ya taho gadan-gadan yasa ta fara fita a hayyacinta.
Cike da cije le6e ta leko tare da kiran babbar y'ar Tabawa.
"Ladidi d'an kira min Malam dan Allah.
Gaba d'aya suka sa mata ido har yaran,take su Lami suka gano yanayinta,d'aki ta koma tana rike baya.
Yaran suka ce su fita wasan su kar wanda ya sake ya kira Malam.
Harda tafawarsu cikin murna tare da saurin bin bayanta.
A durkushe suka sameta har ta fara nishi da halamar dai haihuwar bana da sauki tazo.
"Subhanallahi..
Da sauri sukai kanta.
"Haba Rukayya, kina naguda amma ki gagara sanar mu?
Le6e ta cije tare da zame hannun Lami cikin karfin hali.
"Ku fita zan iya.
Ido Lami ta kannewa Tabawa,da sauri ta ce
"A'a baza ayi haka ba.
Shiru tayi jin d'aya ta bayanta ta rike mata hannu yayin da Lami ke kok'arin duba fitar yaro.
"Kinga har kai ya kusan fita,yi sauri kiyi ta nishi..
Bata da zabi, illa tai kok'ari taga yaron ya fita koh ta huta da azabar rikon Tabawa.
Kai Tabawa take girgiza wa Lami cikin keta ita kuma tana kanne mata ido.
A kalla goshin yaro har ya fito amma dan bakar mugunta tun karfi Lami ta sake dannashi ciki ya koma kira take
"Yauwa kara yin nishi da karfi.
A karo na biyu yaron na danno kai tana mayarshi tun karfi cikin karfin hali da rashin imani.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
16_Bakin ciki kam sun ganshi,koh suna kan ganin shi,dan fa yaro mai kuka Allah ya bawa Rukayya, dan haka in ya fara challara kuka koh bacci ka ke sai ka mike,hakan yasa a kullum suka ji kukan wata irin tsanashi ke sake shigar su.
Dan haka suka daura daga inda suka tsaya tun bayan suna da yaro yaci sunan Kabir.
Karan nan bata sakacin barin d'aki ba kowa,dan kullum Raliya na gidan koh ta turo Ummilo har ta kusa arba'in.
****
FARIN KOMAI.
Duk'e suke a gaban mai yankan wuka kawar Tabawa tana bashi bayani.
"Yanzu mey ku ke so ai da ita? Dan banga halamun za'a iya aika yaron nan lahira ba koh uwar.
Lami Tabawa ta kalla,ita kuma tana kallon mai yankan wuka.
"Allah ja zamanin ka so muke daga yau yaji bai kaunar kusantarta balle har ta kai ga an sake samun rabu,ta yaro kuma ka barmu dashi,a fara da uwar,sannan mu a dawo mana da haihuwar tata kanmu ni da Tabawa.
Dariya ya yi tare da kad'a kai.
"Aikin farko mai sauki ne,kai a wajena shi yafi komai sauki na juya kan miji akan mata.
Baki suka wage tare da kad'a kai na mugunta.
Tarikice ya basu tare da fad'in yadda zasuyi amfani dasu.
"Wannan dai ku tabbatar kun sanyata a kofar d'akinta, ba mu'amula ba shi da kallon d'akin ma sai dai a mafarki koh in ta sake gida.
Tafawa suka yi suna jinjina mishi cikin murna.
Yau ta Rukayya ta fara fita yawon arba'in, dan haka tana fita suka kulle gida tare da yin yadda mai yankan wuka ya umarta.
"Bakar mayya,daga yau ke da ganin miji sai dai a d'akin wasu.
Gud'a Tabawa tasa,tare da gyara wajen kamar ba ayi komai ba.
****
Jim tayi tana tunani a d'aki, ta rasa gane kan Malam,in zatai lissafi toh yau kusan watan ta guda da taga Malam ya sako kafarshi d'akinta.
Ba ma wannan ba,koh girki tayi sai dai ya ce ta kai d'akin Lami koh Tabawa koh kuma ta shinfid'e a kofar su.
A da koh Kabir ke kuka in ya shigo da azama zai isa isa ya d'auke shi koh a hannunta ne ya kar6e shi,amma yanzu sai dai ya tsaya daga nesa yana fad'in ta kula dashi man.
Koh in ya gansu a waje ya kar6eshi.
Yau da gobe sai Allah,dan haka tun baya damunta har ya fara.
Dan haka ta nemi shawarar Raliya,ita kuma ta ce ta tuntu6e shi koh laifi tai mishi.
Hakan tayi,sai dai da mamakinta sai ya ce shi ba abinda ta mishi,asalima ya nuna har kullum baida sama kamarta.
A zaure suke,ganin ta fara hawaye tuni ya hau lallashi,garin haka har ya sada ta da kafad'arshi, kamar an ce Lami leka sai kwa tai katari da hakan.
Kai ta gyad'a tare da koma wa ciki.
"Lalle mun yanka ta tashi Tabawa.
Kallota tayi tana shar6ar miyar kuka.
"Mey kuma ya faru?
Leka wa tayi sai ga nan Rukayyan ta shiga d'aki tare da kullowa rike da mayafi ta fuce.
"Innalillahi...
D'akin Lami ta koma tana doka salati,
"Wai meye Lami?
Cikin kud'ima ta ce
"Tashi ki ga,zama bai ganmu ba.
Yadda taga su Malam ta sanar wa Tabawan tare da sakon kaunar da yake isar mata.
"Kinga gashi ya ce ta fito kila ya kaita wani waje su had'e.
Kwanon abincin ta dangwarar tare da kallon Lami ba koh kiftawa.
"Mey zamuyi toh yanzu?
"Mun kad'e kawai in dai Malam ya kad'aita da jarababbiyar matar nan..
"Kinga,tashi zaki yi mu nufi gun Mai yankan wuka mu kora mishi bayani..
Hannu ta hau lashewa tana kad'a kai da kallon yaransu wanda suka zuba musu ido.
"Ya zamuyi da yara?
Tsaki Lami tayi,
"Ni in zaki fito ki fito,da a ina muke barin su?
Sunje suka kora mishi bayani, dariya ya yi tare da gyad'a kai.
"Ai nayi mamakin ku da banji kunce ai musu farraku ba,ta yadda koh kallonta kar ya kaunata,ai in zaka sha giya toh kasha ta dubu.
Kai Lami ta kad'a
"Ayi ta zama mujiya a idonshi.
Wani kallo ya musu tare da mika hannu
"Nafi son na rika fa jin dumus saboda dad'in aiki.
Guntun kud'in gadon Tabawa suka bashi,
"Dan Allah ai mana mai zafi Mai yankan wuka.
Kai ya kad'a,tare da dakko wata gwalba mai dauke da wani bakin turare mey kamshi mara dad'i.
"In har kullum zaku na sanya mishi wannan a kayanshi na yau yafi na gobe yawa,toh haka a hankali kinta zai rika hau hawa har a wayi gari bai kaunar ganinta.
"Sannan daga zarar turaren ya kare toh komai zai iya faruwa,koh dai ya saketa,koh kuma in ya cigaba da ganinta abin ya shafi kowa,aciki kuwa harda ku..
Ido suka zaro.
"Kamar ya mai yankan wuka?
Murmushi ya yi tare da dauke kai.
"Toh meye amfanin zamanta bayan matsala ce? Kawai daga nan ta kara gaba kar ya shafe mu.
"A'a Tabawa,
Kallo Mai yankan wuka tayi.
"Meye mafita in har ya kare bata fita? Nasan kasan wata hanya koh sauya tsari sai ayi.
Kafad'a ya daga,
"Ni dai na gama bayani,in kuma har na sauya toh ba lalle ku samu abinda ku ke so ba,dabara ta rage taku ta yadda zata fita kan turare ya kare,a kuma adana kwalbar ta hanyar binneta,in har kunyi wannan.
Da hannu ya nuna musu halamun komai ya kare.
Ido Tabawa ta hau zarowa tana kallon Lami
"Toh in kuma ba'a adana kwalbar ba mey zai far...
"Malamai ku tashi ku ban waje wasu na jira.
Hannu Lami ta yafito ta halamun ta tashi kawai su wuce.
Da harara ya bisu,
"Bai dame ku bane in har ba'a adana ta ba..
Juyo wa Tabawa tayi jin abinda ya ce.
By
Feenat Ja'afar.
*MATAN UBA*
©Feenat Ja'afar.
2017.
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA).
17_Tsafi dai wai gaskiyar mai shi,sannan asiri ya wuce wasa,a hankali Rukayya ta fara ganin sauyi mai gaba daya gun Malam,in har ta fuskance shi kamar ganinta ne ma baya kaunar yi a gidan.
Yaronta yai wata shida,rarrafenshi a ko'ina acikin gidan,tun daga wannan lokaci ya fara fuskantar cin zali wajen y'an uwanshi da iyayen su.
Amma abinka da yaro gobe ma zai rarrafo ya sake zuwa gare su,sai dai in taji kukanshi ta dakko abinta ta goya kawai.
***
"Raliya abin nan ba fa na karau bane,wallahi kullum Malam kara tsanar ganina yake a gidanshi, ga tsangwama da habaici da nake kwasa gun matanshi, ga bakar azaba da ina ji ina gani ake gasawa yaron nan..
Kuka ta fashe dashi tare da girgiza kai
"Wallahi nayi iya bawa Malam hak'uri ya ma fad'a min mey na mishi yaki Raliya.
Dafata tayi cike da tausayawa.
"Tabbas nasan kina hak'uri Umman Kabir,amma ki kara akan na da,InshaAllah in na koma zan sanar da Abban su Uzairu in yaso ya tuntu6e shi muji koh wani abun ne...
Shiru tayi tare da dan tunani.
"Amma anya Umman Kabir abin nan baiyi kama da aikin asiri ba?
Dagowa tayi tare da zuba mata jajayen idonta,
"Ni nasan su Lami zasu iya komai koh dan yadda Malam ke nuna miki so..
Katseta tayi ta hanyar girgiza kai.
"Ban kawo wannan ba Umman Uzairu, nafi kawo laifi na mishi tunda bai kin Kabir.
"Ni dai kawai ki sanar da Abban Uzairun tunda kila ya fad'a mishi laifin.
Kai ta kad'a tana mai kallon yadda duk tabi ta rame duk akan Malam.
***
"Turaren nan fa baifi a kwakkafeshi ba a yau da gobe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 19