Share this page
uban suna kuka. "Mu dai bama son Aunty Jamila Abba.. Tsugunawa ya yi tare da goge musu hawaye. "Nima bana sonta,yau zata tafi kunji?.. Sultana ya kar6a tare da jijjiga ta. "Yi hakuri Ummata. Hawaye Aunty Rabi ta kara goge wa, banda rashin imani a yaran nan ina abin duka,marayun Allah wanda ya dace a tausaya musu. Nawa Nass yake? Bata jin har yanzun ya kai shekara uku. Daga uban har yaran tausayi suke bata,dan haka da sauri tai hanyar waje tana goge hawaye. Bata jin a iya tashin yaran nan ta ta6a jin Halima ta duke su haka,kar kara ita batta a zan ma duka,karshe su bata hakuri ya kare. Kai ta girgiza, mutuwa bata barin wani dan wani,tasani da tuni ta bar Halima da yaranta. Kaya ya sauya musu tare da tambayar sunci abinci? Kai suka kad'a "Eh. Saifu ne ya ce "Har yanzu Mama bata dawo ba Abba,da itane bazata daki Nass ba,in ta dawo sai ta rama mana koh? Kai ya kautar tare da goge hawayenshi, "Hakane,nima bazan sake yarda a dukar min ku ba Saif,wannan ma Allah zai maganinta,muje mu tafi unguwa. Jaddada mata ya sake kan wallahi in ya dawo ya sameta tai kuka da kanta. Yana fita kuwa ta had'a y'an chanjin hannunta ta arce Kano. **** Kuka yake ma Umma da tazo yana tsara mata muguntar da Jamila take ma yaran, "Umma dan rashin imani Sultana ma bata bari ba,babban abin kuma yadda take maka wa Halima zagi alhalin tana chan a makwancinta. "Shin Umma wai duk *MATAN UBA* haka suke ne a duniya koh kuwa ni tawa jarabawarce haka?.. Ban fa manta irin azabar dana sha gun su Tabawa ba,shi yasa tun farko naki auren nan. Hawaye Umman ta goge. "Ka yi hakuri Kabiru, amma ba duka aka taru aka zama d'aya ba,ni kaga a gidan wani nake,balle na ce zan zauna da kai,kai kuma kaki rabuwa da yara balle na tafi dasu chan Kano,amma kam tabbas Jamila taban mamaki. Kuka sosai Jamila tayi jin ya ce bazai iya zama da ita ba. Rantsuwa take akan bazata kara ba shikam ya ce sam,dama chan ba sonta yake ba,haka yaranshi. Haka tana ji tana gani aka kwaso kaya da saki d'aya. Makaranta yasa Nass dan ya rinka bin su Saifu da Amjad,domin ragewa kanshi aiki,in zai tafi aiki sai ya kai Sultana gidan Aunty Rabi,da haka suke rayuwar su har ranar da Aunty Rabi suka zo tashi an ma mijinta transfer. Kuka sosai tayi ita da yaran,dan koh ba komai sun shaku sosai,toh dadinta d'aya Kano suka koma. Tun bayan tashin Aunty Rabi ya fara fuskantar matsala ta inda zai bar Sultana dadinshi d'aya anyi hutu lokacin,dan haka ya tarkatasu suka tafi Kano hutu. *** "Dole dai abinda ba'a so din Kabir shi za'a yi,hakura zakai ka kara auren koh dan kula maka da yaran. Kai ya dago cike da marairaita. "Dama jiya mun shawarta da ita Mahaifiyar marigayiya,kayi hakuri ka auri Fatima,inaga ita dake halalin Halima ce dole ta rungumi yaranta. Tsam ya yi,shawarar tayi,sai dai yana tunanin yadda zai iya zama da Fatima a shimfid'ar Halima. "Wannan ne fa kawai maslaha,hakuri kawai zaka yi. Gidan abokinshi yaje wanda kusan tare suka tashi,shine babban abokin shawarar shi in yazo Kano. "Kabi shawarar Umma kawai,ina ga wannan ne kawai mafita,dan ba wanda zai rikesu sama da y'ar uwar mahaifiyarsu. "Ka duba nawa zaman mana,kaga zaiyi wuya ka gane yaran Sumayya dana y'ar uwarta da aka min auren huce haushi da y'ar uwarta. Kai ya jinjina,dan yasan yadda abin yake,bai manta kiyayyar da yayar Sumayya ta gwada ma abokinshi ba karshe aka raba auren aka bashi kanwarta ita ta tafi ta auri wanda take so. "Ni kuwa kasan rabona da yaran nan naka na kusa shekara takwas,tun fa haihuwar Sumayya na farko. Murmushi abokin yayi. "Lalle kam yanzu sun girma sosai,suna islamiya yanzu kila ka gan.. Shiru ya yi dan jin sallama had'i da kukan Farida tsakaninta da Allah kuka take. Daga kitchen Umman ta leko dan jin kukan rabin ranta Farida. Direct wajen Abbansu ta nufa fuska rufe da dankwalin kanta da ya ware,had'i da hular da jaka da takalmi hijab a hannu. "Mey ya faru uwar bankaura? A gabanshi ta zube tana shura kafa cikin shagwa6a,tsaki Abban nasu ya d'an yi,yasan mud'in bai tambayi mey ya faru ba ta dinga wannan abin. "Toh ya isa,yi shiru,ke Aisha mey yasa Farida kuka? Dariya Aishan take harda ta keta,ganin hakan yasa ta kara jiniyar shagwa6ar tata tana mey hullawa Aisha hijab d'in hannunta. Cikin sigar lallashi ya ce "Kyaleta, fad'a min mey aka miki yayata? Ikon Allah Abban Saifu ya tsaya gani,yasan daga shi har abokinshi akan yara sam basu da zafi,halinsu d'aya shi yasa abota tazo d'aya. Kukan ta bari tare da had'iye guntun, "Abba dazun fa kace mana kana da d'aurin aure a garin nan yafi a kirga koh? Kai Abban ya kad'a mata, "Eh hakane,mey ya faru? Zama ta gyara tare da cigaba. "Abba shine,shine fa tun fa daga layin islamiyarmu Abba nake ganin taron samari da y'an mata duk sunyi kwalliya har nazo layin nan samari ne duk da matansu a tsaye.. Kai ya sake kad'a mata halamun yana ji. Cigaba tayi da fad'in "Toh Abba fisabilillahi ba dole nai kuka ba tunda mu ka ki mana aure kana kallo yadda samari suke ta karewa a garin nan suna aurensu sunkusa su kare... "Mtsww... Tsaki Abban ya yi,tare da kok'arin neman abin duka,ganin haka da sauri taja baya tana kara kukan,ita fa har ranta da gaske take,sai dai jin tayi karo da mutum yasa ta juya tare da barin kukan, haka kawai kuma suna had'a ido taji kunya ta kamata,dan haka da sauri ta mike tare da sanya gudu cikin kunya. Dariya yai sosai,sai daga bisani shima Abban abin ya fara bashi dariya yana girgiza kai. "Farida!..Farida!!.. Kai ya sake kad'awa "Farida ake fad'a maka, uwar bankaura,har kullum jinta take yarinya,in ta kwa6a ma shirme sai kaji kamar ka sa kuka. Kai Baban Saifu ya kad'a "A'a da fa gaskiyarta,kar suna kallo ai ta aure samari su su tashi a tutar babu. Dariya ya sake yi. "Toh yanzu kai in ka tsareta kila kalmar auren kawai ta sani in dai Farida ce. Kai ya jinjina "Lalle sun kam girma,mashaAllah. Ita kwa kitchen ta shige gun Umman,itama dariya ta samu tana yi lokacin da Aisha ke bata labarin. Kan Aisha tayi da zummar kai mata duka tai bayan Umma. "Kyaleta Faridee na,zo nan,ke ai naki saurayin special ne,kina a zaune zai zo har inda ki ke ya d'auke ki ku tafi gidan ku. Da sauri ta ce "Allah Umma? Kai ta kad'a mata "Da gaske. Tsalle ta sa tana murna,sai Umman ta girgiza kai. "Allah ya nunan ranar girmanki Farida. Ba musu ta ce "Amin Umma. "Toh maza kuje ku cire kaya ku nutsu ku sanya hijab ku kai ma su Abbanku da Uncle d'in Kaduna abin sha. Kai suka kad'a, da gudu kuma suka nufi d'aki dan yin yadda ta ce. "Yauwa,toh ke rike faranti da kofuna,ke kuma d'auki kunun ayar nan,ku shiga da sallama,sannan ku durkusa ku sake gaishe shi. Kai suka kad'a. Dan haka a nutse suka isa parlourn kai a kasa kamar gaske suka gaida shi,da fara'a ya amsa yana tambayar su makaranta har suka tashi. Binsu ya yi da kallo ganin suna tafe amma suna dukan kafad'ar juna sai ya kad'a kai. "Abokina kana shan drama a gidan nan. Kai ya kad'a "Sosai kuwa,mud'in Farida na gidan nan. Da wannan suka cigaba da abinda ya kawo shi. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 5_Da shawarar Abokinshi yabi ta umma,haka duk dangi sun yaba da shawarar,dan haka kawai sai aka d'aura auren da zummar in zai koma su tafi da amarya Fatima tunda dama bazawara ce kusan tare akai musu aure sai dai ita a shekara biyar auren ya mutu dan bata haihu ba shi kuma miji dama yana da matarshi, uzzura da gori ne ya kar auren ta dawo gida. *A KADUNA* "Fatima. Kai sinke ta amsa. "Dan Allah ki rike min yara da amana,ki sani tamkar nauyi Allah ya daura miki bisa kanki,ki rike min su tamkar naki.. "InshaAlla zaka sameni da rike su tamkar nawa. Murmushi ya yi tare da mata godiya. Da dare duk suna zaune suna kallo Sultana na a cinyarta tayi bacci. Kallo su Saifu tayi,sunyi kane-kane a cinyar baban nasu d'aya da remote Nass yai bacci. Tana jinjina irin sangartar da akai wa yaran,a ganinta yanzu ai sun kai minzalin barin zaman cinya. D'aya bayan d'aya yake dibansu tana taya shi duk suka kwantar da yaran a d'akinsu,ganin ya dau Sultana sun fita yasa ta bishi da kallo. D'akin ta bishi,ga nan Sultana ya shinfid'e ta shi ya shiga wanka. Kaya ta cire tare da maye gurbinsu dana bacci ta d'ane gado. Fito wa ya yi sanye da jallabiya yana goge ruwan kanshi da towel. Kallon mamaki yake mata ganin har ta kwanta ba koh wanka. Murmushi ya yi tare da zama dan shafa mai. Halima kam ta daban ce,dan haka ya kasa had'a ta da kowacce d'iya mace wajen kunya da kawaici da iya ado sassanya. "Kiyi alwala muyi sallah. Kai ta dago tare da kallonshi,ganin ya juya baya yasa ta tashi tare da shiga bayi. Sun idar amma ya kasa tashi sai lazimi yake,chan har ta gaji ta tashi tare da kwanciya. Allah yaga tun aurenshi da Jamila take haushin dama ita ya aura,ta sani Ya Kabir abin son kowacce Y'a mace ne barin ita data jima a son dama shine mijinta. Bayanshi take kallo da wani irin siga,yau Allah ya mallaka mata shi cikin ruwan sanyi. Murmushi tayi ganin ya tashi yana nad'e sallaya,binshi take da ido komai yake yinshi cikin nutsuwa da birgewa. Shi kam tunanin ta yadda zai iya kebanta da kanwar Halima yake shi yasa yake ta sininki. Satar kallonta yake,ganin haka yasa ta rufe ido kamar mai yin bacci. A dirare ta zauna a gefen gadon tamkar ma shine amaryar. Ganin zaman bazai yu ba sai ya gyara filo tare da jingina yana dan leken ta. Gaba d'aya data rufe ido sai ta juye mishi Haliman. Da sauri ya d'auke kai tare da janyo Sultana ya d'aura bisa hannunshi yai mata filo tare da tofeta da adu'a. Tsam tayi tana kallon wani ikon Allah,karamin tsaki tayi tare da juya baya tana gunguni ciki-ciki,yaji, koh bai jiba sai Allah,shi dai tuni ya tsunduma a baccinshi. Warai ta tashi,da halamun wannan tafi Jamila Bariki,ita tai ma yaran wanka,ta basu abinci gwanin sha'awa har suka tafi makaranta. Tun yaran basa sake wa da ita da baban nasu har suka ware in banda Saifu,da sannu duk ta siyesu da halaiyar da koh a da bata da ita. Yanzu kam ya aminta yaranshi sun samu madadin karamar uwa,shi kam Saifu har yanzu bai sake da ita ba,dama kuma tun zamanin mamansu ma baya shiri da Fatima. Sau tari baban yakan sauya mishi harce da turanci in tana wajen dan yasan bata jin turanci ita islamiya tayi tun a jss3 ta rufe zuwa,dan haka da yaga yana kama kai ya tambaye shi mey ya faru,kullum amsar d'aya ce "Nothing.. A haka har aka shafe shekara. Samun promotion nashi a baya ya kawo bud'i sosai a rayuwarshi,aciki harda daga wa daga Kaduna zuwa Abuja. Abu na farko da ya fara shine sauya musu makarantar yaran masu kud'i, dan yana ga koh kobon shi zata kare toh fa zai bawa yaranshi ilimi mai kyau. *** Shekara d'aya ta shud'e lafiya ba tare da wani abu ba,wanda shi yai dai-dai da shekara su biyu da aure, abu d'aya ne da ya fara fuskanta shine sam yaran basa ra6ar Fatima har Sultana,in dai yana nan koh kiranta tayi yanzu zata fara kuka. In ya tambaye su kuma yanzu zasu fara raba ido babu mai fad'in dalili. A boye-a boye ashe take sau musu dan hali,ita ba duka,a'a, mintsini da jan kumatu su Jan kunne sune aikinta. Sannu a hankali sai ya fara ganin wani sabon sauyi,mud'in suna d'aki tare da Fatima toh kowanne yaro zai nemi waje yai ladab babu mai ra6arshi har Sultana. Dan kam zasu riketa dan ma kar taje suna yi suna kallon gefen Fatima. Ranar suna zaune a parlour sai zuba take mishi ya kanya, shi kam d'aya bayan d'aya yake karewa yaran kallo,akan Amjad ya dire kallonshi. "Kai Amjad,zo nan.. Da mamakin shi sai yaga ya kalli gefen da Fatima take yana sissinke kai. "Amjad baka ji Abba na kira ba... Da sauri yaron ya tashi jiki na 6ari yai gun Abban. Baki sake yake kallon yaron, duk sun fara zama wasu dolaye mud'in a gaban Fatima ne. Kallon Fatiman ya yi,da sauri ta sau mishi murmushi. "Mey ya samu kumatunka naga ya kumbura? Cikin sauri ya girgiza kai tare da fad'in "Ba komai. Kai ya girgiza. "A'a Abbana,fad'a min mey ya kumbura ma shi? Saifu ya kalla,shi kuma ya kalli gun Fatima,yana kallo ya kad'a mishi kai halamun ya ce ba komai. Shiru kawai ya yi,amma tabbas yasan da wata a kasa,yana fatan ba zargin da yake bane. Dan ba wannan bane karo na farko ba,ya ta6a ganin bayan kunnen Sultana ma a kwarzane,sannan cinyar Saifu tayi ja. "Gobe yaran abokina zasu zo hutu su biyu daga Kano,gashi a goben nake son tafiya Jos work shop,toh zan jira su zo sai na tafi jibi in Allah ya kaimu. Kai ta girgiza, "Allah ya nuna mana. Yaran ya kalla,da mamakin shi sai yaga duk suna neman kuka. Hannu ya mika musu,duk sai suka kasa tahowa in banda Saifu,dan haka da kanshi ya tashi tare da daukan Sultana. "Kuzo muje naji mey ke damun sojoji na. Hannunsu ya kama,duk da yana kula da yadda Nass da Amjad ke kallon gun Fatima. "Common boys.. Chakulkuli ya fara musu,a hankali suka fara warewa suna dirka dariya,take sai suka manta da hudubar Fatiman suka bishi d'aki. Kwafa tayi bayan ta gama bin bayansu da harara. "A hankali zan saita ku wannan rawar kan naku da 6aci duk sai kun daina. **** "Ku shigo man ku ka tsaya a bakin kofa. Juya wa yaran sukai tare da kallon bakin kofa jin muryar Abban. "Saifu,kuzo ga yayyenku nan su Farida, Tashi sukai da nufin isa gun shi Fatima ta fito a d'aki duk sai suka tsaya banda banda Saifu da ya karasa. "Kuzo man. Yake ta fara da fad'in "A,har sun iso? Kai ya kad'a mata yana kallon yaran,abin har ya daina bashi mamaki ya dawo bashi tsoro. Ta yaya in sunga Fatima zasuna haka? "Ku karaso. Katseshi tayi,dan haka sai ya kauce su Farida suka shigo. Duk iyayin Farida da Aishan da murnar zuwa Abujan duk sai suka yi sanyi. Akalla yanzu za suyi shekara 10,zuwa tara,dan duk sun shiga Js1. "Ku zauna yanzu zan dawo,ku kuzo muje kan suci abinci Amjad. Da sauri har sun rigashi fita a parlourn, yana ji Fatima tana cewa Sultana "Kema tafiya zakiyi kawas?. Mota ya bud'e musu,yau kam dole yaji dalili gun yaran. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 6_Yara kam fur kowa yaki magana,sai Saifu ke kwata magana sai Amjad yai saurin girgiza mishi kai. Kai ya kad'a, koma meye yasan gaskiya zatai halinta wataran. Washegari da kuka suka rabu,duk ya sake damka amanar yaran a hannun Fatima,zai iya cewa wannan ne karo na farko da zaiyi tafiya ba tare dasu ba. Bayan fitarshi ta juyo da kamar gaske a gaban Abbansu tana lallashi, yana bata baya ta maka musu tsawa. ''Ku wuce mu shiga ciki ya'yan mai. Kai Farida ta dago tare da kallonta,sai harara take maka musu jiki na 6ari suka wuce banda Saifu da bai daina kukan ba. Bayan su suka bi,kowa ya zauna ya nutsu yana maida kuka. Kan Saifu ta dawo cikin zare ido, "Kai ba zaka rufen baki uban d'an taurin kai? Juyawa mata baya ya yi yana cigaba da kukanshi,a razane ta juyo tare da nufo gunshi,kamin ya yi kwakkwaran motsi ta damki kumatunshi tun karfi ta hau murdewa tana kuma marin bakinshi da d'ayan hannun. "Rufe min baki,shegun yara sarakan y'an 6acin tsiya... Aisha Farida ta zungura da kafad'arta cikin rad'a "Wannan muguwa ce wallahi Aisha... Zungurarta tayi da halamun tai shiru,harar inda Fatima take tayi,ganin yadda Saifu yake kuka take Jan kumatunshi da mari wai sai ya yi shiru. "Mtsww"... Tsaki taja tare da juyawa d'akin da aka sauke su rai 6ace,ji take tamkar taje ta shigar ma Saifu. Cika Saifu tayi tare da juyo wa jin tsakin,da kallo ta buta har ta shige d'aki ta rufo kan ta dawo kan Saifu. "Bazan lamunci wannan ta6arar ba wallahi, dakaku zanyi tunda Abban naku ya kauce. Kai ta dungure mishi tare da juyawa tana makawa su Amjad harara da sukai tsuru-tsuru. "Sauran ku,yau na sake naji muryar wani wallahi sai mutum yaji jiki. Kasa sukai da kai,tana shiga d'aki da gudu sukai wajen Yayan nasu tare da rungumoshi cikin lallashi suna hawaye. Hannu Sultana ta kai fuskarshi tana goge mishi hawaye tare da girgiza mishi kai yayinda hannu d'ayan ke bakinta tana tsota. D'akin su Farida suka nufa,duk da ido suka bisu Faridan harda guntun hawayenta. "Allah ya isanka,azzaluma kawai. Kallonta suke jin yadda take zafin Fatima. "Ni fa Aisha tun jiya naji na tsani matar.. Hannu ta sa tara da rufe bakin Faridan "Ba ruwana Allah,ki rufa mana asiri. Gun yaran suka je tare da lallashin Saifu, "Dama haka take muku? Kai Amjad ya daga. Tuni suka fara basu labarin Fatima Farida harda hawaye. "Toh mey yasa baku fad'i ma Abbanku ba? Shiru suka yi suna kallon-kallo. Kan wani lokaci har sun ware dasu Farida. Yunwa ce ta fito dasu,guntun abincin safe suka ci tare da fita tsakar gida yin ball. Farida kad'ai take yi,da hannu take wa Saifu wai ya shigo suyi. D'aki ya koma tare da sako takalmin ball ya fito sai wage baki yake. Ganin haka yasa Amjad ma dakko nasu ya mika wa Nass sai dillika dariya suke Farida kawai ke ci,dan haka aka raba gida team nata daban na Saifu daban,da taci d'aya shima zai dage yaci. Yau d'aya sun zage suna wasa cikin kwanciyar hankali dasu Farida. Sama-sama take jiyo ihu cikin baccinta,dan haka tuni baccin ya fara mata kaura bata ma da lokacin tashi balle ta d'aura abinci har 12 saura. "Meye haka kuma? Juyawa sukai jin muryar Fatima cikin tsawa,da sauri Nass ya hullar da ball din dake hannunshi jiki na 6ari. "Hakuri Aunty. Hararar su Farida tayi tare da jan tsaki ta juya,itama tana hura hanci ta bita da harara. Anyi ball ciki ya rarake,tuni kowa ya fara russuna. "Ni fa yunwa nake ji wallahi Aisha. Hamma Saifu ya yi. "Me too" "Me too" Nass ma ya ce "Me too". Dan tsaki tayi,tare da kallon agogo. "In a gida ne ai tuni mun jima da cin abinci,wannan ai mugunta ne. Tsaki ta kara yi tare da kallon Sultana wacce ta zuba mata ido hannu a baki tana tsotsa. "Kema kina jin yunwa koh Sultana? Kai ta kad'a Saifu ta kallo. "Je ka ce ma Auntyn ku muna jin yunwa. Da kamar mai jin tsoro,chan dai ya nufi d'akin yana kwankwasawa sai yaji ta kofar ta bud'e,Farida ya kallo,da kai ta mishi halamun ya shiga kawai,kai ya kad'a kamin ya tutsu. Su da suke a parlour ma sai sa sukai saukar marin, dan haka rike da kunci ya fito yana hawaye. "Anki a baku d'in, yunwar ta kashe ku. Rai Farida ta had'e jin ta fito tana sababi. "Ai dama guntun na safe na ajiye a matsayin na rana,tunda kun cinye au kunci rabanku sai kuma na dare.. Da sauri Farida ta amshe "Dare kuma Aunty? Harara ta maka mata kan ta ce "Eh har dare,koh da magana? Baki Faridan ta ta6e tare da kau da kai gefe. Kofarta ta turo tare da jan tsaki. "Kaima naka iya ja mata Allah ya isa ne, amma ace duk girman nan naka ka tsaya kuka,toh wa zai tarewa kannenka fad'a? Shiru ya yi kamar mai nazarin zancen. "Ni ba ma wannan ba,mey zamu Ci yanzu? Dube ta fara,akan Corn flakes ta dire,da sauri ta tashi tare da nufar kan dining din ta dakko da madara da sugar. "Abu mai sauki,musha corn flakes kawai. Kofuna ta d'akko kowa ta zuba mishi,da wannan suka samu suka cike wani gurbin,sai daren kuwa ta basu indomie. Washegari. Har sha d'aya bata fito ba ga Sultana acici ta fara kukan yunwa tun corn flakes da suka kora dazun. Kallo Saifu tayi,sai ta tuna da marin da ya sha jiya,dan haka da kanta ta tashi tare da nufin taso ta. "Ke Farida wallahi fa ba ruwanmu. Harara tai mata kan ta tura kofar d'akin Fatiman. Bacci take hankali kwance, dan haka sai ta kai hannu kan filon tare da fara bubbugawa. "Aunty!.. Aunty!!!. "Mtsww".. Tsaki tayi,tuni Faridan ta had'e rai, duk da tana karamar amma ta tsani tsaki. "Ke.. Kallota tayi rai had'e "Mey ki ja zo yi min har d'aki? Kai ta kautar dan jin warin bakinta na yawun bacci da sauri. "Abinci Sultana zata ci naga shiru ba'a daura ba ne shine nazo tada ki. Tsaki ta sake yi tare da juya mata baya wanda da sauri Farida ta kai hannunta hanci halamun toshe wa. "Kinji Aunty... A zabure ta mike tare da yarfo mata zagi. Ciki-ciki ta ce "Allahumma yahdiki. Da ido ta tsareta "Mey ki ka ce? Kai ta k'autar hannu bisa hanci. "Ni ba abinda nace. "Toh wa ki ke rufewa hanci? Baya taja tare da sauke hannun. "Kefa dama tun jiya naga take-taken baki da kunya,toh bazan d'aura ba,wanda yaji yunwa ya fita ya daura... Kwanciyarta ya sake yi hakan yasa Farida ta6e baki tare da fita. "Yau fa ake yinta,nifa badan ina tsoron Umma ba da wallahi na sau rashin m. Gunta Sultana tayi tare da fad'in abinci. Baya ta bata tare da goyata, ''Zaki sha corn flaks? Kai ta girgiza mata tare da fad'in "Abinci. Aisha ta kallo, "Ba mun iya dafa shinkafa da miya ba? Kai ta kad'amata "Toh muje in da miya mu dafa,dan ko ni yunwa nake ji. "Um-um Farida,ni fa ba ruwana,wannan matar in ta zaune ki wallahi babu mai kwatarki. Baki ta ta6e tare da kallo Saifu. "Zo ka nunan inda kayan miya yake,ina ruwana da ita,mai warin bakin kawai. Kitchen ta nufa,cikin sa'a kuwa akwai guntuwar miya a tukunya ta jiya da taiwa cikinta su ta basu indomie. Rishi ta girgiza, cike yake da kalanzir,wannan bata matsala dan ta iya kunna wa. "Ina ashana? Da sauri Saifu ya kawo mata, "Yauwa. "Dakko tukunya babba. Nan ma da sauri ya shiga store tare da kinkimo katuwa irin ta cin gidan su. "Yauwa.. Saura ruwa, da gishiri,in ya tafasa sai a wanke shinkafa a zuba,ai na iya. Aisha ce ta leko,ganin tilin shinkafar da Faridan ta debo zata wanke. "Ke Farida,Allah wacce Umma take auna mana bata kai wannan ba,bari ki gani. Ragewa tayi,tare da rage ruwan, "Eh na tuna,in ta tsotse sai a kara har sai an ta6a in ta fara fashewa,wallahi na tuna. Risho suka kure,dan haka tuni ruwa ya tafasa,ana watsa shinkafa ana matsawa gefe dan yadda ruwan ke tafasa. Da taimakon Aisha dai shinkafa ta had'u kasa duk ruwa,haka suka yad'e aka watsa a faranti tare da juye miya gaba d'aya da nama suka dawo parlour. Sai murna suke har yaran yau kam sun shiga kitchen da kansu sunyi girki. Hankali kwance yau suka saki jiki da su Farida sai da sukai nak duk an 6ata parlour da watsin shinkafa ta fito jin hayaniyar tai yawa. "Kanbu... Duk suka juya jin muryarta, "Meye hakan? Parlourn take nuna musu kowa yai shiru. "Wa ce gwanar girkin? Shiru ba amsa,cike da tsawa ta sake tambaya "Aunty ke fa ki ka ce wanda yake jin yunwa ya shiga ya d'aura, shine gaba d'ayan mu muka shiga dan duk yunwar muke ji.. "Toh naji rasai,kinfi y'ar gida koh? Kai ta dauke tana girgiza kai. Kitchen ta nufa,sai gata rike da tukunyar miya a hannu ba komai cikinta. Duk ido suka sa mata yadda ta sa musu. "Kun san Allah tunda har ku ka shanye miyar nan gaba d'aya toh wallahi kunci rabonku har na dare. Ido Farida ta waro,kan ta kai kallonta ga agogo, "Har dare kuma? Karfe d'aya fa Aunty. Tsaki tayi tare da juya wa kitchen din,tsintsiya ta dakko. "Ku tabbatar kuma kan na dawo a d'aki kun share min wajen nan tass wallahi, in ba haka ba jikin kowa zai fad'a mishi. Wannan ba wani abu bane gin su Saifu,dan haka da sauri Amjad ya d'au tsintsiya ya hau shara Nass ya yi kitchen. Da yamma tai wankanta ta tafi makota,ganin lalle da gaske take basu da abinci yasa dole corn flakes suka d'akko dan sha. Binsu tayi da kallo ganin yadda duk suka zuba mata ido,gaba d'aya corn flakes din bai fi Sultana tasha ba ya kare. Duk haka suka hakura suka barma Sultana dan har ta fara kukan yunwa. Sallar magriba suka yi,gaba d'aya sun kafawa TV ido ciki na kiran Chiroma,a jima kad'an Farida ta kalli agogo tayi tsaki. Gwangwanin madara Nass ya dakko,kan ya wuce d'akin su duk suka bishi ido. "Kai,wallahi Aisha har Abujan nan ta isheni, tunda muke mu Umman mu bata ta6a barin mu da yunwa ba. Kallonta Saifu ya yi. "Ai dan ba step mom naku bace,muma da Maman mu tana nan bazata hanamu ba. Kallon sukai gaba d'aya da tausaya. Amjad ne ya amshe,tare da fad'in "I hate step moms,dan mugaye ne I swear Farida. Aisha Faridan ta kalla,tana shirin basu amsa Nass ya fito rike da school bag d'inshi da gudu. "Na tuna,akwai sauran biscuit namu da Abba ya sai mana guda 3. Kar6a Faridan tayi,kamin cikin harara ta ce "Da ka san da wannka barmu da yunwa? Toh debo mana kofuna. Manya ne biscuit d'in, dan haka dasu sukai maganin yunwar daren ranar tare da fashaka da madara sai da sukai nak suka kora da ruwa. A faranti suka juye sauran madarar,duk Farida suke kallo cikin readyn wawaso suna dariya amma tayi sama da ita. "Ku tsaya a deba ma Sultana sai ayi wawar. Kai suka kad'a, dan haka a murfin madarar ta bata kan ta ce musu "Ready? Da karfe suka ce "Yessss. Tana ajiye

Chapter 2 of 19