Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Arewa hausa novels Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239 *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 1_Nishi take iya karfinta rike da baya a tsugunne a band'akin dake a cikin d'akinta cikin zufa. Nishin da ta sake yi ne mai karfi shi yai sanadin fadowar jaririyar,da saurin taro ta cikin karfin hali daga tsugunnen. Murmushi ta saka har hakwaranta suka bayyana ganin abinda take da muradin samu ne a kullum wato 'd'iya mace'. A hankali ta ware zaninta da ke gefe tare da shinfid'e ta a gefe jin mibiya na kokarin tahowa ta jijjiga cikinta ta fito. Reza sabuwa ta sa yatsanta domin daidaito ta yanke cibin. Ita kanta tasan yau kam haihuwar tazo mata da zafi ganin ta kasa mike wa. Kofar band'akin ta tura a hankali ta fara jan jiki rike da jaririya har ta iso d'aki. Cikin cije le6e ta kwantarta tare da kok'arin kwata tashi tsaye dan taimaka wa kanta kamar kullum amma ta kasa. Kusan min 10 tana a haka har ta soma jiyo hargowar yaran. "Maman Saifu!... Maman Saifu!!. Ido ta rintse,dan bata so har yaran su kai da dawo wa tana a halin da take ba. Babban cikin ne ya ja ya tsaya tare da bin inda taja har band'aki da kallo ganin jini ya dire kan jaririyar da ta sau kuka. Da baya ya koma yana kwada kiran Abban shi, "Abba jini a d'akin Mama da jaririya,kuma... Bai jira ya karasa ba ya karasa da gudu-gudu,sauri-sauri d'akin yana fad'in "Haba Halima,ya zaki min haka bayan kinyi alkawarin bana a asibiti za ai komai. "Sam bana kaunar haihuwar gidan nan taki a kullum gudun matsa.. Shiru ya yi shima ganinta a durkushe hannu d'aya a ciki d'aya a kan babyn wacce ke kuka tana jijjigata. "Innalillahi.. Maman Saifu.. Da sauri ya karasa tare da kok'arin tallafota yaji hayaniyar yaran cikin murna Mama ta haihu zasu shigo ya tsayar su. "Maza ku je ku kira Aunty Rabi ku ce tazo yanzu. Da gudu kuwa suka fuce banda babban da ya makale ganin halin da Maman shi ke ciki. Taimaka mata ya yi ta sauya kaya tare da sanya pad ya rirrikota yana mata sannu. Juyar da kai tayi da halamar ya zasuyi da babyn? "Muje zan d'akkota. Kan su kai ga fita har yaran sun dawo tare da makociyarsu Aunty Rabi. "Dan Allah ki taimaka min da jaririyar kan na sata a mota. Kai ta kad'a tana ma Halima sannu. Maigidanta ta fad'owa tare da sanya yarinyarta babba tazo ta gyara band'akin kan suka wuce asibiti. Duk yadda zasuyi jini ya tsayawa Halima abin yaci tura. Tun mai gidan yana fad'a har ya dawo ya rissina ganin ba sauki,irin abinda a kullum yake gudu kenan. "Kai ne mai gidan Halima? Da sauri ya tashi tare da kad'a kai, "Eh ni ne, jinin ya tsaya? Kai nurse din ta girgiza tare da fad'in "Likita na neman ka aciki ne. Jiki a sanyaye ya bi bayanta har office din likita. Tsam ya yi jin bayanin likitan, "Y'ar uwata ce,wanchan karan ma jinin mu yazo d'aya, zaku iya diban nawa ba matsala. Kai likitan ya kad'a, "Ba damuwa,amma dole za'a kara auna wa,gaba ne dai ta guji haihuwar gida ita kad'ai dan gudun matsala. Kai ya kad'a. "InshaAllah doctor, wannan ma tsautsayi ne,ba kuma za'a kuma ba. Da taimakon Allah aka samu jini ya tsaya washegari da taimakon likita aka kara mata jinin ta farfado. Kan washegari har ta ware,dake ba garinsu suke ba,sai washegarin aka samu mai zuwa mata daga kano bazawarar kanwarta dake a gida. **** Kallonsu take daga shi har yaran gwanin ban sha'awa tamkar wani sa'an su in suna wasa. Sosai take jin nishad'i a duk lokacin da ta gansu a haka cikin kaunar juna da kulawa. Ajiyar zuciya tayi tare da dan yatsine fuska jin wani irin zafi da cikinta ya yi. Dagowa ya yi lokacin da suke ma jaririya wasa shi da yaran duk sun dirirritseshi shi kam koh a jikinshi. "Ya akai ne Maman Saifu,koh jikin ne?.. Murmushi tayi tare da gyara kwanciya cikin dauriya ta girgiza mishi kai. "A'a. Gunta karamin ya yi,wanda babban yake da shekara 6,mai binshi 4,karamin biyu. Cikin gwaranci ya ce "Maman Saifu baby na chan hannu. Yake tai mishi cikin dauriya tare da shafo fuskarshi. Al'adar su ce in sun so har yaran da Abbansu su kira ta Maman Saifu. Baban ne shima ya matso tare da fad'in "Mama Saifu yaushe zamu koma gida,ni nafi son kina min wanka da bani abinci... Murmushi tai mishi tare da miko mishi hannu tana kallon maigidan. Ido Baban ya zuba musu cikin murmushi had'i sakar mata wani dan kallo a takaice. Kai ta dauke tare da rungumo yaran bisa gadon da take a kai. "Yanzu kam Saifu ai ka girma,kannen ka uku fa,yanzu daga yau kai zaka rika bawa Amjad da Nass da baby abinci da hannunka koh? Kai ya girgiza mata cikin murmushi. "Nima na girma koh Mama? Murmushi tayi tare da jijjiga mishi kai. "Uhmmm... Gyaran murya Abban nasu ya yi duk suka kalloshi. "An mantamu fa.. Yaran ta saki tare shima da miko mishi hannu halamun yazo gareta,ba musu kuwa ya tashi rike da baby ya isa gadon yaran suka matsa shima ya tutsu cikinsu ya zauna. "Kin shagwa6a mu fa Maman Saifu, da gaske gida ba dad'i in baki a cikinshi,mun saba da tarairayarki. Murmushi tayi tare da maida hawayenta ciki. "Shi yasa nake son ko fara koyan komai da kanku,dan komai zai iya kasance wa. Ido yasa mata da halamun tambaya, kan ta kai da bashi amsa likita yazo. "Kai,kai.. Juya wa sukai gaba d'aya jin maganar doctor. Da hannu ya fara lissafa su "D'aya, biyu,uku har shida a gado d'aya? Ai sai ku bangare mana. Tashi Abban nasu ya yi yana ma likita dariya. "Bari tunda madam ta samu lafiya zamu sallameta dan naga ita ta 6ata ku da yawa. Kai tayi kasa dashi cikin murmushi jin tsiyar likita har ya gama ya fita. Kamar mai jira duk suka sake komawa saman gadon tamkar zata gudu,karan nan sai ya basu babyn shi yabi likita. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 2_Kwana uku suka sake yi aka sallame su,duk da a zahiri dauriya kawai take yi dan ta kosa da zaman asibitin. Y'an barka sun lafa zuwa dare ta tasa babynta a gaba,yayinda lokaci-lokaci tana duba agogo jin y'an gidan shiru basu dawo ba har Fatima kanwarta. Ruwan zafi ta zuba tare da d'auka tana sha koh zata samu saukin zafin ciwan da cikinta ke yi. Ido ta daga tare da kallon katon hotonsu nasu duka da tsohon cikin da suka dauka kwanan nan. Kwalla ce ta tarar mata a ido,a hankali ta kau da kai tare da fashewa da kuka tana girgiza kai. Jin dirin motar su halamun sun dawo yasa da sauri ta hau goge ido ta maye kukan da murmushi dan tarar su. Kayan da suka jido na sawarsu ranar suna suke nuna mata cikin murna ganan na baby shima da yawa. Kai ta kautar ganin yadda mai gidan ya zuba mata ido da halamun yana son karantar ta. Yasan Halima ciki da bai,yasani tana da matukar hakuri,amma yafi kuma kowa sanin wacece ita.. Dan haka ko ya ta sauya yana saurin gano ta. Sa Fatima ya had'a yaran tare da fad'in ta basu abinci suka fara make kafad'a wai su dashi zasu ci. "Toh shikenan, anji. Kanta ya dawo,tare da fad'in "Meye matsalar?. Ido tasa mishi,sai ganan wani hawayen ya sake cika. "Ok,ok,na gane,mun jima koh? Dan ta kwantar mishi da hankali ta daga kai. Murmushi ya yi tare da fad'in "Ai mana afuwa. Murmushi tayi tare da mika mishi baby da yai mata huduba da sunan Ummanshi Rukayya. Tare har ita suka ci abinci tana bawa yaran a baki da cokalinta kamar kullum,sai dai a yau takan zuba musu ido a takaice cike da sauraron labarin shagon da suka je har aka gama cin abinci. ''Ba dai anan zasu kwana ba?.. Kai ta kad'a mishi tana cigaba da shirya su,jin ta ce eh ne yasa suka hau murnar yau zasu kwana da baby. Kallonsu kawai yake yi,har ta gama shinfid'e su itama ta haye. "Ni fa? Cikin marairaita yai maganar yana mata wani kallo,sai ta nuna mishi da ido halamun yara fa na kallonsu tana kunshe dariya. "Abba zo kusa dani ga waje dayawa... Da dan gudu ya karasa tare da d'aukar filo yana fad'in "Yauwa Abban.. Kallonsu take yadda ya zamo sun saka yaran a tsakiyarsu,hakan yasa ta zuba musu ido ba koh kiftawa har uban. Kai ya dago tare da kallonta,sai ta wayence tare da k'au da kai gefe tana mishi murmushi.. Shi tau ya rasa wacce kunya take ji haka. "Mama.. Amjad ne ya kira ta. Juya wa tayi gaba d'aya garesu. "Na'am Habebee. "Yi mana tatsuniya toh... Kanshi ta shafo tana mai jinsu har bayan ranta. Cikin nutsuwa ta fara basu labari irin na littafin yara suna kallonta,da sannu har suka fara bacci d'aya bayan d'aya. Bargo taja musu lokacin da hawayen da take rike wa suka zubo mata. Tashi ya yi tare da zama yana kallon yadda take sunke kai dan kar ya gani. "Halima... "Uhmm".. "Muga" Kautar da kai tayi gefe dan jin zai mata wayo,sai dai kan ta farga har ya taso ya dawo bangarenta. Daga kwancen tai saurin rungumoshi tare da sakar kuka mai tsuma rai a hankali. Ya sani da tun dazun ya ga halamun kuka take son yi,yasan kuma ko ma meye toh babban al'amari ne,dan haka kawai sai ya dagota ya hau lallashi. "Ina tsoron ne Kabir.. Ina tsoron ranar da mutuwa zatai mana yankan kauna yarana su tagaiyyara in bani ne.. Shiru tayi hawaye na zuba sakamakon hannu da yasa ya rufe mata baki yana girgiza mata kai halamun tayi shiru. Yaran ya matsar har jaririyar,a hankali ya kwanta tare da kwantar da kanta a kafad'arshi cikin lallashi. "Sshhhh..It's ok... A hankali har ta nutsu. "Wa ya fad'a miki zamu rabu?.. Kai ya kad'a mata,kan ya cigaba. "Muna a tare InshaAllah har girmansu. Kai ta kad'a,tare da fad'in "Zanso haka,dan duniyar ce yanzun.. "Ba abinda zai faru fa,believe me. Shiru kawai tayi tana kallonshi. A hankali yana dauke hankalinta har ta fara gyangyad'i. "Rufe ni sanyi nake ji.. Murmushi ya yi, "Sanyi?.. Zafi fa ake. Kai ta kad'a mishi tare da sakar ajiyar zuciya. "Gobe fa y'an Kano zasu zo,bana sun makara har jibi suna. Murmushi tayi kawai. A hankali yana mata fira har yaji tai shiru halamun tai bacci. Tsam ya yi yana kallonta cikin tunanin kalamanta,kawai dai sai ya kawar yaja mata bargon kad'an ya rufesu har ita. Asubar farko ya farka,baccinta take,duk da baby Sultana na motsi kad'an amma bata tashi ba. Bargon ya kara ja mata tare da sauka yana gyaran sauran yaran. Sako kanshi a gidan kenan ya fara jiyo ihun kukan Sultana da sauran yaran suna fad'in Mama. Ja yai ya tsaya ganin Fatima bata ma san anayi ba d'akinta a rufe,dan haka da sauri ya karasa d'akin. Amjad da Saifu rike da jaririya ya samu suna jijjiga kafad'un Maman tasu da fad'in "Mama baby na kuka. Amma shiru ba koh motsi, da sauri ya karasa tare da tallafota ganin duk ta sake. "Halima!..Halima!!.. Girgiza ta yake iya karfinshi yana mai sa hannu a hancinta amma Halima kam ba sauran numfashi. Kukan da yai yawa ne ya fito da Fatima a d'aki tana tsaki,lalle daf take da ta bar gidan nan,haka kawai,yara sai shegen 6acin tsiy... "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un...Halima!!!. Jin kalmar nan ne yasa ta yin shiru tare da nufar d'akin da sauri. Daga uban har yaran kuka suke,wanda da halama yaran suna taya baban nasu ne ba wai dan sun san mey yake wa kukan ba. Da sauri ta karasa tare da fad'in "Mey ya samu Haliman Ya Kabir kuke kuka? Da sauri ya dago tare da fad'in "Lafiya fa na batta Fatima duba min ita dan Allah bata numfashi.. Kan ya karasa har ta hau jijjiga itama amma Halima shiru. A kai ta d'aura hannu tare da runtuma ihun "Wayyo yayata,wallahi ta mutu Ya Kabir. Kai ya hau girgiza mata yana mai sake girgiza Haliman hawaye na zubar mishi. "Subhanallah.. Ihun nan na lafiya kuwa a gidan nan Rabi? Kallo maigidan nata tayi tare da girgiza mishi kai. "Gaskiya kukan ya yi yawa,ka leka ka jiyo shin lafiya? Zaga wa ya yi yana sallama,jin shiru ga ihun kukan Fati da yara yasa ya karasa bakin kofar yana fad'in "Malam Kabiru lafiya kuwa? Da azama Kabir ya tashi tare da fitowa ido fal hawaye yana mishi bayani. "A'a, bari dai muje asibiti a gani,kar mu zauna a gida. Kai ya kad'a da sauri,sai yanzu ma ya tuna da wani asibiti. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 3_Ido kawai ya zuba mata a asibitin hawaye na zuba,kafad'arshi likitan ya dafa tare da fad'in "Kai hakuri,tabbas rai ya yi halinshi,a iya binciken da mukai yanzun na gano 'internal bleeding' take a hankali ta ciki har yai illah.. Kanshi ya d'aura a gawar tare da rungumota, "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un.. Ita ce kalmar da yake ta nanatawa yana hawaye. Sabo tirken wawa,koh ba aure yasan Halima jininshi ce halak-malak,wacce suka shaku tun zamanin yarintar ta. Hak'uri makocin yake bashi,kan a d'au lokaci har zancen rasuwar Halima ya iske masu tahowa suna a yau. Halima mutum ce,har da guda,dan haka kowa yaji mutuwar nan barin in anji yadda Kabir ke sururun fad'in yadda suka rabu yana hawaye. Ga kukan da Sultana take tare da yayyenta suna kiran su Maman Saifu,abin sai ya kara rikitarwa barin Saifu mai wayo. Rayuwa kenan. **** Yau kimanin sati uku kenan da rasuwar Halima,zaune yake a d'akin Haliman ya jingina kai da bango,yayin da yaran duk sukai matashi da cinyarshi Amjad da Nass suna wasa. Ido Saifu ya zuba ma Abban nasu,chan ya ce "Abba yaushe Maman zata dawo? Kai ya kautar jin zancen Saifu,ya gaji da zula mishi karyar zata dawo kullum. "Kai hakuri Saifu,ta kusa dawo wa.. Kuka yasa mishi yana fad'in shi fa Mamanshi kawai zaije. Ganin haka yasa sauran kannen ma suka hau tayashi shima yana yi. Umma dake a d'akin waje ta tashi tare da ajiye madarar da take bawa Sultana ta nufi d'akin da ita dan lallashin d'an da jikokinta. "Fisabilillahi Kabiru rayuwa zata yu a haka? "Kai ne fa zaka sa yaran nan su manta mahaifiyarsu ta yadda zasu ji basuyi maraici ba,amma a kullum sai dai ka tasa su gaba kai kuka su kuka,toh wa zai lallashi wani?.. Halima ta rasu,kasan kuma ba wai zata dawo bane... Kallonta suke har yaran,sai dai sun daina kukan sai na Sultana. "Daf nake da tafiya kuma har yaran muddin bazaka sawa ranka salama ba. Hawaye ya goge tare da girgiza kai. "Kiyi hakuri Umma,na daina. "Yauwa,koh kaifa. A sannu yau da gobe har sun ware sai abinda baza'a rasa ba har ya koma aiki. Ido jajir ya dawo ma Umma yau halamun yaci kuka yana mai mika mata takarda. "MashaAllah, Allah sanya alkairi, mashaAllah. Tashi ya yi tare da shiga d'aki, a kullum adu'ar Halima ita ce Allah d'auka ka shi,gashi yau ya samu promotion amma ba Halima,a lokacin da dad'i yazo bayan wuya Halimanshi ta k'au. BAYAN WATA BIYAR. "Na fad'a maka dole kasan abinyi,koh dai ka kara aure,koh na tattare inawa-inawa na bar maka gidanka,mutum sai taurin kai,karan nan kam zan matukar baka mamaki. Kasa ya yi da kai tare da fara bata hakuri kamar kullum. "Hakuri d'aya ne shine kai aure,in ba haka ba a goben nan zan bar garin nan. "Dan Allah Umma kiyi hakuri,toh ni ina ma naga matar aure,wallahi bani da ita sai dai ki nema min na yarda. Baki ta washe tare da gyara zama. "Ko kai fa,yanzu naji batu. "Ganan Jamila y'ar wajen kanwata, nasani kaima ka sani dan kai taki aure har yanzu,a da ban goya maka baya ba dan sam bazan so kai wa Halima haka ba yarinyar kirki. "Amma yanzu tunda babu ita sai ai tuwona mai na kawai,nasan Jamila nada hankali, zata rike yaran nan tunda tana kaunarka. Shiru ya yi,amma shi kam in ta shi ne a barshi aure ba yanzu ba sai ya huce,amma tunda Umma ta ce zance ya kare,kawai sai yai na'am Kan wani lokaci zance har ya kankama, Jamila tai murna, cikin nasara akai aure amarya ta taro garin Kaduna,sati guda Umma ta tafi ganin Sultana tayi kwari. Kallon Sultana take tana maka tsaki ganin yadda take tsala kuka ta tashi bacci. "Mtsww,wace rayuwa ce wannan, mutum yai aure dan ya huta amma jarabar ya'yan nan ta hanaka hutu. Bargo ta yaye tana kara naka tsaki tare da kallon agogo. Kai ta girgiza tare da yin kwafa, "daga fita siyan alewa har kwalliyar da nayi ta tuje har yanzun bai dawo ba. Kukan da Sultana ta kara yi ne yasa a tunzure ta maka mata tsawa. "Dalla kimin shiru kema,jarababbu kawai. Shiru kuwa Sultanan tayi tare da sanya hannu a baki tana jan zuciya. Zai wuya kaji kukan Sultana,dan mai matukar hakuri ce sai in tana jin yunwa. "Mtsww. Dankwali ta figa tare da fita waje ta batta a kan gado tai kitchen. Da kallo ta bita tare da fara ta6e baki halamun kuka. Da abincin ta dawo a hannunta tare da dangwarar wa. "Daga yau abinci zaki fara ci dan bazan iya wahalar dama kunu ba kullum. Kamar wacce taji kawai sai ta kara sa kuka. Kai ta dungure mata tare da mika mata abincin da karfi da yaji yarinya tana kuka. "In banda bakar mugunta a tafi dake man a barni naci amarcina amma aka barki ban haifa ba ni da reno. Kukan da suka ji ne yasa da uban da yaran da gudu suka karaso cikin gidan,jin hayaniyarsu yasa da sauri ta finciko Sultanan ta hau rarrashi yarinya na bangarewa. "Mey ya sameta irin wannan kukan tun a titi nake jiyo wa. Wayen ce ta fara cikin rashin gaskiya. "Wai fa dole sai dai na bata abinci shine dan na hana dan akwai yaji take wannan ihun. Karbarta ya yi yana goge mata baki tare da kallon Jamilan da tuhuma. Yasan Sultana bata ra'ayin abinci, "Toh ina kununta? Tashi tayi tare da fad'in "Bari na kawo. Da harara suka bita shi da da Saifu,dan sarai ya tsani Auntyn nan tasu dan muguntar da take musu a sati kwai da tafiyar Umma. Kamar kullum yau ma ya dakko Sultana tare da yi mata shimfid'a yana had'a rai,dan tun dazun ta bashi haushi. Ido ta sa mishi,in ranta yai dubu toh ya 6aci,a kaf yaran tafi tsanar Sultana,dan akanta kullum ba ita ba miji sai lallashin ya'rshi. Wani kallo yai mata kamin yaja musu bargo dan har yanzu Sultana bata dawo normal ba kamar da. Dan haka yau da safe yana fita aiki ta hau huce wa bisa kansu da duka da tsawa. Sultana Saifu ya dakko dan sam bata da nauyi sukai gidan Aunty Rabi. Hawaye ta goge,dan duk tana jin komai tun fitar uban,tanan kam tasan yara sunyi maraicin uwa. **** Yau da gobe ya wuce wasa,da iyayinta ta tasamu kan Kabir har yake kulata, agabanshi sosai take kula da yaran har ya zamana ya saki jiki da ita akan tana kula mishi dasu fisabilillahi. Sai dai in aka ce ba idonshi mugunta ta rinka yinta kenan har sai Aunty Rabi ta zagawo tukunna. By Feenat Ja'afar. *MATAN UBA* ©Feenat Ja'afar. 2017. ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA). 4_Ita batta a duka,amma bata hanasu abinci sai randa abin ya motsa. Sai Aunty Rabi tayi kamar ta fad'a mishi sai ta bari,duk a kullum Saifu na kawo karar basa son Aunty Jamila muguwa ce. Band'akin waje ta shige kusan awa guda tana wanka,Nass dake tsaye tuni ya fara kukan kashi yake ji,ga foo amma yasan ta musu gargadi da kashin foo sai ya hau shadda,sannan basu ba shiga na d'aki. Tsoron duka yasa ya tsaya sai matsewa yake yana kuka. Tashi Saifu ya yi tare da dakko mishi foo ya ajiye mishi tare da cire mishi wando da nufin ya zauna akai. Sauri yake dan ya cire, sai dai tuni har ya fara saka a wando,amma duk da haka sai ya zauna a foo din cikin sauri. Karasa cire mishi wandon Saifu ya yi ya matsar yana kallon band'aki jin bud'e kofar Aunty Jamila. Baya ya yi ganin ta waro ido waje tare da fad'in "Kan uban chan..kashi ne haka Nasir? Da sauri Saifu ya ce "Kiyi hakuri Aunty Jamila. Buta ta ajiye tare da waiwayen neman abin duka. Tashi Nass din ya yi da sauri ya 6oye a bayan Saifu tare da sakar kuka. Takalminta na danko ta cire ta hau maka mishi yana kuka tare da rirrike Saifu kan ya cece shi. "K'auce koh kuma na had'a da kai shegu kawai. Kare Nass yake yana bata hakuri amma taki hakura,tuni ta hau jibgarsu gaba d'aya tana mai zagin uwar su, ganin su Saifu na kuka yasa Amjad d'aukar Sultana dake cinyarshi duk suka sau kuka. Hijab Aunty Rabi ta d'auka tare da saurin zaga wa. "Wallahi sai ka wanke, ni zaku had'a wa wannan kazantar?.. D'auki maza ka shiga band'aki ka zuba mishi rawa ya wanke kai ka dawo kuma ka gyara min wajen nan... "Haba Jamila,wane irin rashin imani ne wannan?.. Nawa ma Nasir yake da har zaki ce ya wanke kashi?.. Hannu ta daga mata. "Ni fa bana ciki da wannan kinibibin wallahi da munafurci,jakarsu ce ni? Wallahi bazan wanke kazantar wannan kartin yaran ba.. Hawaye Rabi ta goge, "Ni zan wanke musu toh. Baki ta ta6e tare da fad'in "Ke ki ka jiyo,amma ni dai bazan sa hannuna a kashin nan ba. Juyawa tayi gun da su Amjad suke tare da nuno su da takalmin "Kuma kumin shiru kamin nazo yanzu naci uwar... Shiru tayi tare da saurin hullar da takalmin ganin yadda Kabiru ke huci a gabanta tamkar kububuwa. "Mey ya dawo dashi iyanzu?... Kan ta karasa tunani tuni ya wanke ta da mari. Jin ihun Jamilan da faka takalmi yasa Rabi fitowa daga band'aki. "Ashe bakida mutunci?.. Muguwa azzaluma..wallahi yau sai na fanshe dukan da yarana suka sha a gunki.. Ganin takalmin bazai mishi ba ya hau jibgarta da hannu yana surutai. "Kayi hakuri Baban Saifu ka batta haka dan Allah.. "Barni da ita Aunty Rabi,ashe kema kina sane da irin muguntar da take baki ta6a fad'a min ba sai Saifu dake min complain kullum.. "Kayi hakuri bazata kara ba.. Samu tayi ta fisge tare da yin d'aki da gudu ya bita, ganin zai cimmata ta shige band'akin d'aki ta rufe. "Ki fito tun wuri ki san inda dare ya miki,dan wallahi yau sai kin barmin gida,irin haka yasa naki jinin kara aure dan bakar mugunta irinta *MATAN UBA* dana shata. Mita yake har Aunty Rabi ta gama gyara Nass ta wanke wajen duk suka rukunkume

Chapter 1 of 19