ta tsala wanka cikin wani material purple mai ado da milk ta dora head milk, simple make up tayi amma tayi kyau sosai sai zuba k'amshi takeyi.
Parlon k'asa ta sauki ta kunna TV, Qur'an TV ta kamo inda Shaik Sudais ke zuba kira'a tana binsa sannu a hankali idonta lumshe.
9:30...
Haiydar ya cikin shigarsa ta shadda shima purple sai walkiya take hadda hula ya murza yayi kyau sosai, saida ya kalleta daga sama har k'asa ta glass d'insa, sannan ya k'araso, bud'e idonta dake lumshe tayi karaf idonsu ya had'u, da sauri ta sauke nata sannan tace ciki ciki.
"Barka da asuba, an tashi lafia".
Yi yayi kaman baiji saida ya gama danna tab d'insa daya zame masa jiki, sannan yace "lafia ya bak'unci?"
Miskili tace cikin ranta sannan a fili tace "ga break fast can".
Still sharewa yayi yana ci gaba da sana'arsa, ita kuma ta mik'e ta haye sama.
Saida ya gama tanbad'arsa sannan ya dau dinning, yana zubo ruwan a cup yaji k'amshi ya daki hancin sa, lumshe ido yayi k'amshin kaman na Mommy, dama Haiydar bayacin abincin kowa saina Mommynsa.
Bude ciki yayi ya kwashi girki, sai wani lumshe ido yake dad'i na ratsa shi, nocking yaji anayi, sharewa yayi saida ya gama sannan ya bude kofan.
Ganin su Shamcy ne ya dashi d'an sakin fuska da yanzu yadan saba da ita gaisawa sukayi sannan suka tambayeshi ita ya gaysmusu tana sama, ya basu hanya suka wuce, shi kuma yayi part d'in Mommy don su gaisa.
Suna shiga aje basket d'inda Mommy ta basu sukayi saman dinning sannan Shamcy ta shiga kwala mata kira " Besty amarsu azo gamu munzo cin kazar..."
Da murmushi ta sauko saboda jiyo muryar Bestynta, tana saukowa tana fad'in "nayi fushi daku sai yanzu zaku shigo?" Tana binsu da hararan wasa.
Tungulawa ta kama baki tace "so kike wannan angon naki ya yayyak'emu".
'Yar samalle tace" kya fad'a dai kema, bayan ko yanzun sai bayan kun gama shanyamu sannan kuka bud'e kofan"
Warah "ki bar 'yan duniya waisu k'yank'yasansu, bayan ta gama mana kukan munfirci"
Haka suka shiga mata tsiya, sai binsu take da kallo tana murmushi, Shamcy ce mai tare mata, kafin tace.
"Wato Besty bama zaki jira mu kawo Karin ba shine kika had'a abinci ko, to Bari na koma ma Mommy da nata" mik'ewa tayi da niyyan daukan basket d'in.
Da sauri itama ta mike ta tareta "haba Besty wallahi nima ban karyaba kufa nake jira mu karya, shi kadai na had'awa".
Shewa suka dauka suna fad'in " iyye su Siddi ansan dad'in miji".
Haka suka wuni sunata zolayanta ita kuma ba baki sai binsu take da kallo, sai marece aka bada mota aka mai dasu gida ita kuma Shamcy sai gobe zata wuce Yauri gaba daya.
Su Aunty Ramlah kawai aka Bari 'yan gari suka gyagyara inda aka b'ata.
***************
Bayan ya shiga inda Mommy suka gaisa da ita da sauran bak'i, Inna sai tsokanarsa take, yana murmushi sannan ya haye saman Dady suka gaisa Su Hanan ana mak'ale dashi rashin Umar yanzu shiya maye mata gurbinsa.
Yazo kofar fita yayi kicibis da Fauziya wacce isowarta kenan, wani irin kallo sukabi juna kafin ya d'auke idonsa daga gareta yace.
"Ke da gaske kike kenan" murmushi tayi tace "indai akan ka ne, expect more than dis".
Ganin Hanan ta kuresu da ido yasa ya jata yana fad'in "ki shiga daga ciki zan fita ne"
"Yau fa zamu wuce, zaka dawo da wuri ne?" Dan ta matsu ta koma ba kanta saidai ta rage zafi ta chat.
"Eh" ya fad'a a tak'aice.
Bak'i duka sun watse bayan sun shigo sashin ta sun mata sallama da ala sanya Alkhairi, Shamcy ma da sassafe ta wuce washe gari.
Su Siddiqa hadda hawaye dak'ar suka bayan ta cikata da perfumes da kayan make up, sannan ta jaddada mata da Hutu ya k'are ta dawo kada tayi zamanta ta ansa da to kawai, Saleem ne yakaita tasha wadda zuwa yanzu sun bayyanawa juna sirrin zukatansu har Iya tsohuwa ta Sani Wanda abin ba k'aramin dad'i yayi mata ba.
Siddiqa ma tayi murna, Haiydar kuwa yace salon ya K'ara ja masa raini ne, ( Maza gadanga k'usar yak'i).
Saida Mommy tayi sati nata basu abinci sannan Siddiqa tace ta bari zataci gaba dayi da kanta, su oga D one kam sai kwasar girki akeyi amma in tana gun saiya ringa wani yamutsa fuska yana had'a rai kaman anyi masa dole wai kada ta Rena shi.
Murmushi kawai takeyi dan ita abin dariya yake bata ma, kullum sasan Momy take yini in ta gama abinda ta wuce musu dashi, Momy ta hanata kawowa amma tak'i bari dole ta saka mata ido, su Hanan kuwa an samu abinda akeso, Siddiqa biye mata takeyi dake ta saba da hayaniyar su Rufee.
Haiydar kuwa sai wutar kaunar Fauziya ke ruruwa cikin ransa kullum farashin sonta k'ara hawa yake.
Hutun su Siddiqa ya k'are, ta addabi Shamcy akan ta dawo sai cewa tayi " Besty keda ke Amarci zumudin me kika haka?"
"Basar kawai nidai ki dawo in zaki dawo, ko kin manta shima angon d'alibine?"
"Au hakane ne fa, to zan duba".
Tsaki kawai tayi ta kashe wayan ta, Shamcy kuwa sai daria take tana fad'in " kai Besty Rigima".
Haiydar ne ya shigo gidan d'auke da wata babbar Leda, suna zaune parlor itada Hanan tana duba mata assignment d'inda tayi.
Da gudu Hanan taje tana mishi oyoyo, sannan tace zata karb'i ledar yace "ba zaki iya ba matar" turo baki tayi sannan ta fce daga part d'in.
Yana kiranta tai banza murmushi yayi sannan wuce ciki mik'a ledar yayi yana tafia yana fad'in " gasunan zakiyi amfani dasu sai adaina amfani da k'anana".
Hijabai ne manya guda 10, murmushi tayi sannan ta mik'e itama, (ni kuma nace Kodai su Haiydar an fara...).
Suna isa school compound yayi parking suna fitowa students suka d'auki sowa wadanda sukasan anyi bikin, wasu kuma mamakine ya k'ashesu ganin.
_D one da fight partner nashi cikin mota d'aya_ π
βπ»
π Meryerm Abdool π
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *_HAD'UWATA DAKE_* ππ»ππππ
ππππ
( _Based on love story_ )
```Written```
```By```
π Meryerm Abdool
Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_*
( *P.M.L* )
*Wani mutum ya tabayi Manzon Allah tsira da Amincin Allah a gareshi yace, ya rasulillah mezan aikata Allah ya soni kuma mutane su soni?*
*Manzo Allah yace: ka guji duniya Allah zai soka, ka guji abin hannun mutane zasu soka.* (hakkun mubeen).
*Page* 44&45
Su Fauziya sun iso Bk cike da burin samun nasara ga k'udirinsu, sakin jiki sukayi kaman komai ya wuce sai yak'e sukewa mutane, ganin haka yasa Mummy ita sakin jiki dasu dan dama ita batada matsala, gida ya cika sai hada-hada ake dama Inna bata koma ba Aunty Salma ce ta koma saboda kara2n yara yanzu kuma ta sake dawowa.
Fauziya cikin k'awayen Zarah ta tare da ita akeyin komai amma itakam Zarah bata wani saki jiki da ita ba saboda sam batayi mata ba duk kuwa da 'yar uwarta ce, fitowa harabar gida tayi da sunan shan iska ganin ba mutane a waye inba gateman da security ba kuma suma sha'anin gaban su sukeyi, lallab'awa tayi zuwa part d'in Haiydar ta dauko kullin maganin da Uwarta ta bata barbadawa tayi hanyan shiga kaman yadda Maminta ta gayama sannan rai saurin ficewa murmushi tab fuskarta ganin burinta na mallakar Haiydar ya kusa cika.
Haiydar da dawowarsa kenan daga gurin friends d'in sa da suka dameshi da son zuwa Argungu suga Amarya haka ya d'aure sukaje, ba wanda ya fahimci yanayinda ma'auranta suke ciki face Saleem da Shamcy da yake sunan komai suna kalle da sak'on hararan da suke aunawa juna, kafin aka gama gaisawa sukaji tsarensu kudade masu yawa suka basu, sannan sukayi musu sallama da sunan sai ranar d'aurin aure in sun dawo.
Dama Haiydar irin mutanen ne masu sakaci da Addu'a wucewa kawai yayi ba tare da yayi Addu'a ba ( sihiri gaskiya ne amma kuma Addu'a garkuwar musulmi Addu'a takobin mumini mu daure mu kula rik'a Addu'a domin kare kai da samun yardar Allah, Allah yasa mudace).
Wanka yayi ya sauya kaya zuwa k'ananan kaya yayi kyau sosai dake ya kware a fannin, fita yayi zuwa part d'in Mummy domin gayamata sun dawo.
Su Zarah ne Zaune a parlor ita da k'awayenta me lalli tana zana musu, gaida shi sukayi sannan ya tambayeta Mommy ta gayamai sun fita, har juwa zai fita yaji ana fad'in "Yaya Haiydar barka da wuni" cikin wata murna wadda aka matse k'arfi da yaji wai ana yanga, juyowa yayi don ganin mai magana karaf idonsa suka had'u da Fauziya.
Samun kanshi yayi yana ansa mata harda tambyanta yaushe sukazo ina Goggo?.
K'ara narkewa tayi cikin fi'ili ta ansa masa, mamaki ne ya kama Zarah ganin wainar da ake tunawa amma bata iya furta komai, ficewa yayi kwakwalwarsa na ruwaito masa fuskarta da shigarta Wanda ada yafi tsana, amma yau yaji ta bala'in burgeshi, jiyake kaman ya koma yayi ta kallonta. _tabdijam_
***************
Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya, ayau ne aka daura Auren *Aleeyu Muktar Sadauki (Haiydar)* da *Maryam Muhammad lll (Siddiqa)* bayan saukowa daga masallacin jumu'at kan sadaki mafi sauki, sannan suka garzaya Bk aka d'aura na *Mubarak Muhammad lll* da *Fertemarh Muktar Sadauki (Zarah)*.
Waleema kawai suka gabatar inda aka gayyaci *Malam Aminu Ibrahim Daurawa* yayi lacka mai kashe jiki Wanda ba Amarya dai ba hadda sauran mutane saida zukatansu suka tsinke, ba abinda takeyi bayan kuka sanye take da Shadda fara gown akayi mata wacce tasha stone work Ja, alkebba ja, takalmi, post, har sarkar da d'an kunnen da abun hannun duka stone nasu jane, just guess readers. Lolx.
Shamcy na gefenta itama taci kwalliya sosai, su Aunty Ramla da Aysha guzame suma sun sha nasu wanka, an raba kayayyaki masu d'inbin yawa Wanda baije bane kawai bai samu ba amma kowa yasha kaya sai Sam barka, can hango member of pure moment zuwa guda sun kwashi kaya sai washe baki sukeyi musamman su o.o ban fad'i suna ba.lol
Aa Ashe hadda su Maman USSEY novella, matan kirki masu nagarta, Ameenan juna, online Hausa writers, jannart mai watch novella, kai walle abin da yawa duk sun hallara, ( hadda wadanda ban fad'a ba duk ina sonku).
Can na hango Ango Haiydar cikin taro yasha wankan fari 4rm up 2 down hadda su malun-malum sai gaisawa yake da mutane cikin sakin fuska, duk da bayason aure haka ya tsinci kansa da farinciki a ranar.
Naseeha sosai Mai martaba yayi ma Siddiqa inda yake cewa " Uwata nasanki ke 'yace ta gari wacce kowanne uba zaifi farinciki da samunta to in fatan ki dore da halinki na kirki a gidanki, ke mai hakuri ce to inaso ki d'ora wani kan Wanda na sanki dashi, danshi zaman Aure gaba hakuri ke in miki na mahaukaci duniyar gaba daya zaman hakuri ne, in kika rike hakuri zakiyi alfahari da hakan nan gaba" haka yayi ta mata nasiha mai ratsa zuciya ta kuwa shige ta sosai dan ba abinda takeyi sai hawaye, daga k'arshe yayi masu fatan Alkhairi acikin zamansu.
Haka itama Mama da Aunty da sauran 'yan uwa sukayi nasu nasihan, dakyar aka banbareta jikin Aunty da Mama Wanda itama Aunty sai kukan take tayata saboda shakuwarda ke tsakaninsu.
Haka aka saka mota aka wuce da ita, tanaji tana gani, (Aure kenan! Mai raba 'ya da gidansu) bangaren Momy aka fara kaita aka danka amanarta hannunta, tarba ta mutunci suka samu daga gurinsu inda Mommy tace.
"Ai Siddiqa 'yata ce koba Aure balle da Aure, inshaa Allah zan riketa kaman Zarah ina matan Alkhairi a Aurensu" daga tayi mata 'yar nasiha sannan aka wuce da ita part d'inta.
Nan dai part d'in Haiydar nanne zasu zauna da yake dama Dady yayi tsarin ne na matar Aure da kitchen da komai, d'aki biyu a k'asa da babban parlour sai k'aramin parlor sama da d'aki biyu suma, an gyara gurin sosai inda aka k'awata falon k'asa da purple color dark and light, su kuma d'ankunan aka gyara d'aya da white and black d'aya green, sai sama d'aya na Haiydar already ya gyara abinda dayan kuma nata akayi pink, dinning na parlon k'asa yayin coffee table ke parlor sama, kitchen ma na k'asa an gyara sosai abin sai Wanda ya gani sai fatar samun zama lafia mai dorewa.
Itama Zarah an wuce da ita Argungu inda zasu zauna na sati kafin su wuce Kaduna inda Ya Mubarak ke aiki.
*10:00pm....*
Su Shamcy akayi shirin zuwa dinner wacce su Saleem suka shirya ba yadda Shamcy batayi da ita ba tace ba inda zataje k'arshe ma toilet ta shige tayi wankanta tai shirin bacci tabi lafiyar gado, dole ta kyaleta suka shirya tare da sauran k'awayenta suka wuce.
Shima Haiydar zaman shi yyi d'akin Saleem yana waya da Fuu fashion wacce yanzu wata shakuwace ta shiga tsakaninsu.
Su kadai sukayi dinner ba Ango ba Amarya zuwa 11:00 suka tashi suka mayardasu gida inda suka koma suka d'auki Ango suka rakosa, suna zuwa bakin kofa ya sallamesu yana musu gwalo, tsiya sukayi masa sannan sukace suna hanya suma.
Su shamcy bangaren Momy suka yada zango suna maimata tsaruwan dinner duk ba Ango ba Amarya, abokansa basu d'auki rashin zuwan su komai ba dan yace Amaryarsa ustaziyace bata zuwa irin guraren dama.
Yana shiga sama ya haura d'akin sa ya fara sauka yayi wanka ya kimtsa sannan ya wuce d'akinta taji shigowar sa don batada nauyin bacci amma tayi kaman mai bacci.
Saida ya k'arema d'akin kallo ba laifi ya mishi kyau sannan ya aje mata Leda kan bedside drawer sannan ya yatsina fuska yace "nasan ba bacci kikeyi ba, so gwanda ki tashi ga abinci nan kici in zaki iya, inba zaki iyaba can ta matsemiki" yana kaiwa nan ya fice daga d'akin....
_Still on buki fans, lobe yo all_ π
βπ»
π Meryerm Abdool π
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *_HAD'UWATA DAKE_* ππ»ππππ
ππππ
( _Based on love story_ )
*Written*
*By*
π ~Meryerm Abdool~ π
Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_*
( *P.M.L* )
```Bazan tab'a mantawa daku ba my mentors da bazarku nake rawa wollahπ```
ABDUL AAJ
&
MAMAN USSEY.
JINJINA GAREKU MEMBER GIDAN KWARAI IRIN ABARKA, KU KAM HALIN KU DABAN NE, KAMAN YADDA KUMA KUKE NA DABAN A GARENI MEMBERS OF PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S, NA GAISHEKU, ALL ILY π
*Page* 48&49
Junawa juna baya sukayi kowa ya kama hanyar Dept, nasu sun d'an yi nisa da juna sai suka juyo same time, karaf idanunsu suka had'u a tare suka sakawarwa juna murmushi mai kayartawa.
Ihu students sukayi suna shewa saboda abin ya burgesu, ihun ne ya dawo dasu, juyawa sukayi suna mamakin wannan murmushi da basusan ma'anarsa ba, (ni kuma nace na love oo).
Menat dake gefe tazo wucewa taji ana ihu, tsayawa tayi tana kallonsu baki sake sannan tace da wata dake gurin tsaye "me wadannan suke yi haka?" Cewa tayi.
"Baki san meke faruba halan? Ai aure sukayi shine suke b'arar da love mu kuma muna ganin sha'awa"
Tabe baki tayi tace "Ayya" amma cikin ranta sai tsinewa D one take tana cewa "Tsinanne dama sonta yake yi, amma yasa nayi mata wancen abu? Shege dan iska daga yau na daina kaunarka a raina wallah, itama shegiyar sumi-sumi kam ta Allah" ta buga tsaki tana wucewa (ni kuma nace kin samu aikinyi).
Ba wani lec, ne da yawa tayi ba dake ba'ayi resuming gaba d'aya ba, ga Shamcy tak'i ta dawo tayi nacin harta yi fushi da ita.
Bakin titi ta isa harta tari me napep zata wuce, sai kuma taga rashin dacewar hakan, wayanta ta ciro ta kirasa saida ya tsince.
Siririn tsaki taja zata shiga saiga kiransa ya shigo, d'agawa tayi jin yayi shiru tasan kuma ba maganan zaiyi ba yasa tace.
"Na k'are lec, nawa zan wuce gida"
Saida yayi yangarda ya saba sannan yace "wazai kaiki?"
"Napep zan hau mana, gashi har na taresa".
"What!! Salon a renani kenan! To jirani yanzu zanzo nayi dropping naki" ya katse wayar.
Tsaki taja tace "ko meye nashi a ciki, wai a renani! Son girma sai kace dawo mtsss".
Ba me napep hakuri tayi tare da bashi 200 ya wuce, minti kadan ya iso, shiga kawai tayi har ya kaita ba Wanda ya cewa d'aya uffan, fita tayi tare da cewa " thanks" cikin makoshi.
Ya jita amma yayi banza, motar kawai yaja ya fice ya koma skull, saboda research da yake na project d'insa.
B'angaren Mommy ta wuce direct, tana shiga Hanan da dawowanta kenan daga skull ta taso tana mata oyoyo, d'aga ta tayi tana tambayan ta skull sannan ta k'arasa ciki suka gaida da Mommy inda ta tambaye ta skull ta ansa da "Alhmdllh".
Tace " ina son d'in?"
"Yanzu ya ajeni ya koma ne".
"Ayyo" da murmushi a fuskanta, alaman taji dad'in hakan, saboda dama ta gayamai shi zai rinka kaita da maidata muddin yana gari ya ansa da to.
Nan ta zauna suna d'an tab'a hira da Mommy sai da taji kiran sallah sannan taja hannun Hanan ta wuce part d'inta.
****************
"Dota wai kuke ciki ne da wannan miskilin yaron ana samun progress dai ko?"
Gyara zama Fuu fashion tayi tace "sosai kuwa Mami, yanzu yayi laushi sosai sai abinda nace, har cewa yayi fa zaije ya gayawa Dady ayi magana don ya matsu wai soyayyata na rikitarda shi" ta k'arasa fad'a tana tuntsirewa da daria.
Itama Mami dariyar take hadda shewa tace "shegen yaro waya gayama masa gombe gabas take, aini na yadda da aikin malam dama yace sannu- sannu abin zai rika shigarsa".
"Ai kuwa yayi gaskia don kuwa yanzu har abin ya shigesa sosai baya iya minti goma bai kiraba, a chat kuwa abin ba'a magana har da cewa zaizo Skk na hanashi"
"Ai bakiga komai ba ma saboda malam nanan nata yi maki wasu Addu'o'in, kuma gara da kika hanashi zuwa saboda banaso iyayensa suyi zargin wani Abu har sai ya gayamusu da kansa".
Haka dai Uwar da 'yar sukayita tattauna suna shewa da daria kaman wasu k'awaye kafin ta fita yawon gantalinta ( Allah ya shirya, ya karemu da mugun gani da mugun ji Ameen).
" hello besty, kiyi magana mana besty, Fushin har yanzu? To maida wuk'ar ina hanya fa!"
Sai lokacin tayi magana "da gaske kike besty? Pls kada ki sakamin rai".
" Allah da gaske nake gashi har na kusa isowa".
Turo baki tayi kaman tana ganinta tace "kai besty shine kika k'i gayamin sai da kika iso".
"Sowie besty, ai kece tun dazu inata kiranki kika k'i d'agawa waike fushi kike nan".
Daria tayi tace " kece ai kin iya zama mutum rai, amma dai nan zaki sauka ko?"
Kama baki tayi kaman ta ganta " wah! Rufani ki sayani so kike oga D one ya cinyeni, hostel zan sauka indai nayi arrange d'in gurin zan shigo zuwa anjima".
Tab'e baki tayi "mezai miki kedai bazaki zo dai bane, in kin k'araso ki gayamin nazo na tayaki gyara gurin".
" kanki d'aya kuwa besty taya zakizo ki taya ni gyara, ko Ya Haiydar d'inne zai kawoki?"
"Wane Haiydar kuma, ai yana cikin skull d'in".
" to nidai ki zauna banaso, inna shigo zanzo da kaina danagan naga ko an sama mana Baby"
"Hehehe! Aa ba Baby ba k'ozo dai aka samu 'yar air"
Dariya Shamcy tayi sannan ta tsinke wayar.
Tashi Siddiqa tayi ta shiga kitchen dan had'awa Bestynta delicious.
*40:00pm*
Shamcy ta iso gidan saida taje part d'in mommy suka gaisa sannan ta isa inda Bestynta da murna suka rungume juna cike da farinciki, sannan ta jata zuwa cikin parlor suka zube, nan da nan ta cika mata table da better.
Tare sukaci sannan aka bude shafin hira, Shamcy tace "besty naga kinyi wani fresh lallai wannan babyn namu yazo da sauki".
Harara ta balla mata sannan tace " zakiga baby kuwa, kita jiran zuwan sa kinji".
"Aiko zan zura ido kaman mujiya"
Daria kawai ta sannan ta kauce maganar da tambayan mutan gida, daga nan sukaci gaba da hira.
Tare da Saleem suka shigo gidan dake Shamcy ta gayamasa taje gidan haka suka had'u aka dasa sabuwar hira amma banda Haiydar da sai yaga dama yake saka bakinsa.
Sai bayan isha sannan Shamcy suka wuce, ita da Saleem ya sauketa hostel sannan ya wuce gida.
Haka couples d'in sukaci gaba da zaman doya da manja amma basa bari kowa ya gane musamman idan suka had'u parts d'in Momy kilawa suke nunawa juna, amma dake babba babba ne saida Mommy ta fahimci wani abu amma ta saka musu ido taga iya gudun ruwansu.
Yanzu kam kara2 ya kan kama haka zai kawota kullum ya mayarda ita kuma, wani sa'in ma jiran sa takeyi hostel har ya gama su ko gida tare.
*A months later...*
Haiydar ne duge gaban Dady dake balbalesa da fad'a, yace.
"Bana gayamaka ka fita hanyar yarinyan ba, amma dake kunnenka bana ji bane shine kaje ka gayawa su kawu ko, toka kyauta amma ka Sani ni ba ruwana a cikin wannan zancen".
Momy dake zaune gefe tana jinsu bata ce komai ba, ita kanta Sam batason zancen da ya kawo musu, saidai bazata fad'a ba, saboda kara kada Alhaji yaga taci fuskanshi saboda ai 'yar k'anwarsa ce, cewa tayi.
" Alhaji kayi hakuri kabarshi yayi tunda ya nace gashi kuma har kawu ya shigo cikin zancen, kada hakan ya kawo sab'ani tsakaninka da 'yan uwanka".
Dady yace " haba Mommyn Zarah, duka yaushe yayi Aure dazai jajibo wani yanzu karamin yaro dashi yaushe zai iya rike mata biyu fisabilillah"
"Allah ya huci zuciyarka, kayi hak'uri ka kara duba lamarin, kuma tunda yace yana so ai zai iya ne"
"To shikenan naji, amma matarka tasan da zancen ta kuma amince?"
Kai ya girgiza alaman eh.
"Maman Zarah k'aramin ita a waya yanzu naji daga bakinta" Dady ya fad'a.
Jin kalaman Dady yasa k'irjinsa bugawa nan tace zufa ya karyo masa.
Kiranta Momy tayi minti kad'an ta shigo sanye da hijab har k'asa, gaidasu dady tayi, sannan ta samu k'asan carpet ta zauna kaman yadda taga Haiydar yayi.
Dady yace "yawwa 'yata dama tanbayanki zanyi, da saninki da amincewarki mijinki yace zai k'ara Aure?"
Tashin hankali Wanda ba'a sa mishi rana, wani zupa ne ya karya mata k'irjinta sai bugawa yace duk da bata sonsa amma abin yazo mata a bazata, saurin tattaro nutsuwarta tayi don kada su fahinta tace.
"Eh Dady na Sani kuma da Amince wata".
Wani irin sauke heart Haiydar yayi.
_tofah_ π€
Battery lowπ kuyi manage da wannan , ily β€ fans.
βπ»
πMeryerm Abdool π
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *_HAD'UWATA DAKE_* ππ»ππππ
ππππ
( _Based on love story_ )
*Written*
*By*
π```Meryerm Abdool``` π
Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
( *P.M.L* )
K'AWAYEN ARZIKI, MASU SAKANI FARINCIKI A KULLUM KUNA RAINA.
*Zee Yabour(Neighbor), Ubaida Gwandu, sa'adatu(Nuwaira), Rukie, Qwllytah, Besty, My Shamcy, Aunty Azland, Salma pinky(Momma), Aunty khady, Suhana(Duduwa), Ayshat garkuwa, Momyn sultan, Momyn ihsan, Seemaluv, Rufaida, Hapsy baby, Mrs, Fawwaz, Maman Amima (MSB), Zarah Adamy, Ummin yusrah, Lalata(sadnaf), Zarah surbajo, Fareedat, Mashkura, Ummihaneefa, Ummi hambali, Dija waziri, Jannart, Ummi Garkuwa.*
Kaiππ€ wallah kunada yawa har ma da wadanda ban ambato ba wallahi duka ina sonku ππ.
*Page* 50&51
" 'yata kin tabbatar ba wata matsala kuma kin amince ba tursasa ki yayi ba?" cewar Dady.
"Eh Dady Nina amince ba matsala"
"Allah yayi miki Albarka ya baki zuria ta gari masu sanyin hali irin naki"
"Ameen" Momy ta fad'a, itama tace "ameen" cikin mak'oshi, sannan Dady ya juya zuwa ga Haiydar yace.
"Kayi Sa'a ta aminci saidai da Sharadi, kada ka yadda ka walak'anta min 'ya akan zakayi Aure ko bayan kayi Auren, idan naji haka zanyi mummunan sab'a maka, sannan Abu na biyu da nakeso ka sani shine ka tanadi inda zaka aje matarka sannan aure sai bayan ka dawo daga service dai2 an k'are gina company ninka ka fara aiki sannan za'ayi, ka jini ko?"
Still kanshi na k'asa yace "eh Dady naji na kuma gode, zan kuma kiyaye inshaa Allahu, Allah ya k'ara girma da nisan kwana".
" Ameen" Dady yace sannan yace zaku iya tafia, ya mik'e ya haye sama.
Mommy tace "yata zonan" tashi tayi taje dai2 kafafunta ta zauna.
Zai fita tace Momy tace "Son kaji dai abinda ya fad'a ko, to wallahi ka kiyaye idan kuwa ka sab'a to ka sani nima zanyi mummunan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 16