Share this page
ta tsorata da laulayi saida Ramlah tace mata ai kowacce mace yanayin laulayinta daban sannan tadan saki ranta. Umar kam d'adi yaji da zamanta gidan Anas koba komai yafi sirri kai ga skull saboda en sa ido (irinsu zuli)yana zuwa akai-akai duk yadda yaso Haiydar yazo suje zamewa yake ya kawo wani uziri, kyalesa yayi saboda ya dauka ko dan suna skull daya ne, baiso ta ringa mishi magana a skull d'in saboda Jan girma dan yasan halin lil din. Tana zuwa skull saidai ba sosai ba saboda lectures basu kankama ba sosai,kuma data gama lec, take fita ko Shamcy ma ikacinta da ita daga hall sai can ba'a rasa ba take binta hostel, ko ita idan taje gaida Ramlah, Haiydar ma basu cika had'uwa ba koshi ita kawai ke ganin sa koya wuce da motarsa ko kuma suna yawo skull d'in. Umar kuwa kullum naci yake taje ta gaida su Mommy ita kuma tak'i saboda kunya, saida yace ai koba danshi ba taje ta gaida su tunda ko babu shi iyayenta ne, ganin ya matsa ne tace zata saka rana suje da Shamcy. Ranar Sunday sukaje gidan da Shamcy sai wani nonnok'ewa takeyi alaman kunya ko kayan rab'awa da aka aje musu kasa cin komai tayi, ga Zarah sai jansu da surutu takeyi Shamcy ce ta biye mata suke tayi, Hanan kam dad'i ya isheta Aunty ta tazo sai surutu take zuba mata tana tambayan ta su Rufee tadan biye mata saboda tanason yara ta saba da rigimarsu Rufee. Saida Mommy ta tashi ta kira masu Dady sannan ta dan sake. Tare da Dady suka sakko murmushi a fuskarsa dugawa sukayi suka gaida shi ya amsa yana tambayansu kara2 suka ansa da lafeeya qlau sannan ya koma. Mommy zama tayi kusa da Siddiqa saboda taga yadda taki sakin jikinta aiko ta wani kara takurewa, murmushi Mommy tayi tace ta saki jikin ta ai itama mamarta ce ta daina jin kunyarta ta dauketa kaman Maman ta, kai kawai ta girgiza sannan tadan sake kad'an. Bayan azhar su Umar suka shigo shida Haiydar sunje wata unguwa, da sallama suka shiga falon sai ganin su Siddiqa sukayi dake bata gayamai zuwan su ba. Zaro ido yayi ya k'arasa gabanta yace "princess! shine kinsan zakizo kika k'i gayamin" ya fad'a da muryan shagwaba. Jitayi kaman ta nutse. "Um..umm" Mommy tayi gyaran murya dan taga dan nata ya manta dasu a gurin. Kunyace ta kamashi ya mike yana sosa kansa sannan ya k'arasa kan seat ya zauna. Haiydar ji yayi kaman ya shako ya Umar saboda yanda ya wani rikicewa akan wannan abar. K'arasowa ciki yayi suka gaisa kaman ba shiba hadda sake fuska, sannan Shamcy suka gaisa da Umar. Sai bayan la'asar suka tafi bayan Mommy ta cikasu da tsaraba dakyar suka karba Umar ya saukesu gidan Ramlah har Shamcy nan ta kwana..... *2 days later* Fitowansu kenan daga lectures, tayi sallama da Shamcy zata wuce, ganinsa kawai tayi gaban ta ya wani had'e fuska alaman ba wasa, daria yaso bata amma sai ta danne. Nunata yayi da yatsa yace "wama kike Siddiqa ko meye? Koma dai ya sunanki ina mai baki warning akan ki fita hanyar Yayana or else.."ya kada mata yatsa sannan ya juya da niyyan tafia. " Hey! Mister man" yaji ta fad'a tsayawa yayi sannan ta k'araso gabansa tace "ba abinda zai rabani da masoyin rayuwata inba mutuwa kai baka isa kai komai ba, sannan da kake cewa tabarsa bani ya kamata kayi warning ba kaje kayi ma yayan naka warning kace ya barni saboda shike sona and idan yaji ya barni saika gayama mai mexai gayama iyayenmu idan sun bukaci dalili" ta kaiwa nan ta tayi scrolling hand nata alaman bye fuskarta dauke da shu'umin murmushi. Dask'arewa yayi maganganunta sun sokeshi sosai musammn da tace _ba abinda zai rabata da masoyin rayuwarta_. Yace" lallai yarinya nan zanyi magananinki zakisan dawa kike zancen" yai kwafa ya wuce.... Komai aka saka mishi lokaci to zaizo ga biki sai matsowa yakeyi yayin da su Siddiqa ke shirin fara exam, zuwa yanzu Ramlah taji sauki har tana iya aikinta shiyasa Siddiqa komawa hostel saboda kara2. Gefe d'aya kuma sai shirya-shiryen biki gidanjen biyu keyi yayin couples d'in ke gudanarda soyayya cikin nutsuwa da tsabta, har lefe ankaima kowaccensu. Zuwa yanzu dole Haiydar ya hak'ura ya saka musu ido ganin ba nasara a gudirinsa, saidai har yanzu basa shiri da Siddiqa. Kai yadau zafi sai exam sukeyi kowa ya maida hankali ga kara2. Alhamdulillah sun kammala exam lafeeya yanzu sai shirin biki. _sowie naso posting tun jia charge yamin short_ love u guys ๐Ÿ˜˜ โœ๐Ÿป ๐Ÿ’„ Meryerm Abdool ๐Ÿ’„ [5/20, 6:22 PM] ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ( _Base on love story_ ) ```Written ``` ```By``` ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„ ยฎ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_* ( *P.M.L.W* ) ```Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:-``` *Bamai k'arfi bane Wanda yake d'aga mutane yana had'asu da k'asa, mai k'arfi shine wanda yake mallakar ransa yayin fushi.* nasiha ce๐Ÿ‘Œ๐Ÿป *Page* 36&37 Shirye-shirye ya kankama ba'a kama hannun yaro, tun ana saura sati biyu bikin baki suka fara isowa su Aysha 'yan Abuja har an iso da cikinta daya d'an tasa, Ramlah ta iso, dangin Mama mutanen Gulma sun fara zuwa, hadda 'yan uwan Aunty duk sun zazzo, yayin gefe daya jakadiya ta dage da gyaran Siddiqa ciki da waje. Bangaren su Dady mutanen Gwandu sun fara, dana D'akin gari 'yan uwan Mommy dake ita Fulanin can ne, harda Inna tsohuwa an k'araso Hanan kuwa na ganinta ta wani d'afe mata a jiki sai shagwaba take zuba mata, da Haiydar yaje gaisheta sai tsiya take masa tace. "Kai kuma dan kwalisa sai yaushe zakayi auren ko kananan kana ruwan ido kaman Ummaru" Smiling yayi yace" meye kuma Ummaru haka Inna abu kaman tsoho!" Kama baki tayi tace" yau naga gantalalle yaro yo me ake cewa to" Daria yayi saboda yanda tayi maganan tana kama baki yace " Umar zakice ko kice faruuk" ya fad'a yana zama kusa da ita. "To iyayye nak'i nace d'in, dalla matsa can baka iya komai ba sai iyayi da tsoron mata" Inna ta fad'a tana hararensa. Bude ido yayi yace" lalalaa! Waya fad'a miki ina tsoron mata nida ga matata nan kan cinyanki" ya fad'a yana nuna Hanan data lafe a jikin Inna kaman bata a wurin. Turo baki tayi tace "nifa na gayama kaje can ka nemi matarka ko kuma ka aure Inna tsohuwa" ta fad'a tana tsuke baki alaman da gaske take. Inna tace "ja'irar yarinya yo ai halinku d'aya keda shi na miskilanci wanda bansan inda kuka gado shi ba don Asma'u da salma ba halinsu bane" tashi tayi tana hararan inna tace "nama fasa yi dake mun shafe kawancen ta fita daga d'akin. Haiydar yace "kin dai manta ne Inna amma aikowa yasan Ardo yasan miskili ne na k'arshe" "Lah'ila'illalahu amma Kai anyi mak'aryaci yaro, Ardon nawane miskili, yana kasa amma kana binsa da sharri" ta fad'a tana tafa hannayenta. Smiling yayi yace "to meye abin taslimi hadda tafa hannu, bayan tafia yayi ya barki ni kuma nace naji na gani inaso, ni kibar tuna shi gabana kada zuciyata ta fashe" Gwalo ido tayi zatayi magana.......Umar ya shigo d'akin tace" yawwa Ummaru dan Allah zoka rabani da gantalallen yaron nan daya sakani gaba" K'arasowa yayi yana daria yace" rufeni Inna ai ba'a shiga tsakanin mata da miji wannan sirrinku" haka suka sakata gaba sai shakiyanci suke mata.... ** ** ** Saura sati d'aya biki Shamcy ta k'araso suka had'u ita da sauran k'awayen Siddiqa na cikin gari da wad'anda sukazo da wasu garuruwa irin :- Mrym warah, Mrym Dkg, Sakina mungadi, Zuly yeldu, Zuly warah, 'yar samalle, Tungulawa d.s sunyi Rabon IV da sauran shirye-shirye. Ana saura kwana hudu biki gidanjen biyu duka sun cika sun bak'e da jama'a 'yan biki. Suna zaune a k'aramin falon Aunty suna karyawa, Siddiqa juya spoon d'in take a cup ta kasa sha, Shamcy ce ta dafata tace "Besty menene na ganki wata iri yau ko duk rakin barin gidan ne kikayi" ta fad'a tana daria. Hannunta Siddiqa ta kama takai saitin zuciyanta tace "kinji yadda zuciyata ce bugawa, tun safe haka na tashi cikin wannan yanayin ji nake zuciyata namin kunci kaman na kuka nakeji" ta fad'a idonta ya cika da hawaye. "Ki ringa fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kina maimatawa zaki sauki a ranki, ki rike hawayen kada su zuba kinga da mutane a gun kada a dameki da tambaya" Shamcy ta fad'a dake gefe suke bamai jin me suke fad'a kowa na sabgarsa. Haka ringa maimaitawa har taji ranta yadanyi sanyi sannan ta tashi taje sasan jakadiya inda ake mata gyaran jiki. Bayan an gama ne tana zaune saiga kiran Umar ya shigo d'agawa tayi bayan sun gaisa yace "my wifie Allah am eager 2 see u, kusan 2 week ake kwarare fa ( dake an sakata lallai kunsan sati biyu yanzu ko'ina jakadiya ta hanata fita daga part d'insu sai nata). " bakice komai ba tawan" ya fad'a da 'yar murya. "Tome me zance my farook, kasan nima nayi missing naka amma kasan ba yadda zanyi, in mukayi hak'uri saura kadan mu kasance tare har abada". "Naji amma nikam gaskia zanxo yanzu ma tasowa zanyi saiki san yanda zakiyi". Kafin tayi magana harya hang up! Murmushi tayi tace " ya Umar ko yaushe ya koyi rigima oho!" Wanka tayi sannan tace ma jakadiya zataje sasansu gun frnd d'inta, Aunty ta gayama tace to in yazo taje dashi can falon Mubarak tace to. 30mnt later..... Ya kirata yace ya k'araso Shamcy ta fad'a ma, ita kuma sai tsiya take mata wai su tsuntsaye soyayya kwana 4 sun kasa hak'uri tace taji d'in. Suna fitowa ta tsinkayo shi ya jingina jikin motar sanye yake da wani yadi ash color harda hularsa, sai taga yayi mata haske sosai ya kuma dan fad'a kadan, ji tayi bugun k'irjinta ya tsananta, daurewa kawai takeyi, saida sukazo daf dashi sannan yasan sun k'araso. Juyuwa yayi suka hada ido murmushi suka sakarma suna mai dauke da tsantar kauna, sannan yace "wannan irin kyau haka matar, shiyasa kika hanani zuwa da shikenan bazan ganki ba koh?" Ya fad'a yana zuba mata ido. Itama zuba mishi ido tayi tana kallonsa cikin ido abin bata tab'a yi ba, k'irjinta kuwa sai bugawa yake fat!fat!!. Shamcy ce tai gyaran muryan ganin sun shige wata duniya, sauke numfashi Siddiqa tayi sannan ta rufe idonta da tafin hannu alaman taji kunya, shi kuma murmushi yayi sannan ya juya gun shamcy yace" bestynmu ashe tare kuke" itama murmushi tayi tace "ina kuwa zaka Sani ya Umar besty ta rikita ka". " wlh kuwa ashe kema kinga mena gani, nikam wai me kuke matane haka ta sanja". "Aa wannan sirrine ya Umar" shamcy ta fad'a daria sukayi gaba daya sannan suka k'arasa falon, Shamcy kuma ta shige cikin gida. Sambatu ya shiga yi mata kaman wani zararre, ita kam sai mamaki take wai Ya Umar ne kuwa? gaba daya ya canja mata, itama saita biye masa. Da zai wuce ya kalleta yace " i am going 2 missing u my wifie" kallonsa tayi tace "kai ya Umar 4 days fah kaman gobe ne". Murmushi yayi sannan " yace bazaki gane me nakeji bane, well ni zan tafi sai munyi waya"bata iya furta komai ba sai binsa da ido da tayi. Har ya ja motar sai kuma yayi reverse ya dawo dai2 inda take tsaye yace "kada kiyi kuka kinji" ji tayi hawaye na shirin fito mata da sauri ta maidasu murya can ciki tace. "I am going 2 missing u too" scrolling hannunsa yayi alaman bye, sannan ya ja car d'insa. Tsaye tayi tana kallonsa harya fita harabar gidan sannan ta koma ciki. Tafe yake yana driving sannu a hankali, k'ira'ar Majeed Hakeem na tashi cikin suratul- kiyamat, yana dan murmushi jefi-jefi. Ya kawo dai-dai Ambursa gurin ramin nan na bayan gari, sai ga wata babbar mota ji kake kuuuu ta hankad'a shi cikin ramin, shima ya bishi kowa ya fad'a nashi bangaren. Innalillahi wa'innah ilaihirraji'un kawai mutane ke fad'a da suka taru gurin domin ceto yarukan su,dai2 sojojin da ke bakin hanya suka k'araso gurin aka samu aka ciro su, shikam driver babbar motar nan take ya rasu yayin shi kuma Umar sai bleeding yake ta hanci da baki numfashi na fita sama-sama, ambulance aka kawo aka daukesu zuwa F.m.c direct A&E aka wuce dashi yayin da wancen driver aka wuce dashi mutuware. Ta hanyar id card d'insa aka ganeshi koshi waye, kai tsaye aka kira Alh,Muktar aka fad'a masa abinda ke faruwa, Mommy ya samu cikin mutane ya kirata yace da dakko galenta sannan suka fita. Haiydar sukaci karo dashi zai fita sai Dady yace ya kaisu F.m.c, momy sai tambayan shi tace meya faru saboda ganin yadda ya rud'e itama tuni hankalin ta ya tashi, shima Haiydar jin an ambaci asibiti tuni ya shiga rud'u dama haka ya tashi yau Sam baya jin dad'i, Dady shiru kawai yayi mata dole itama ta kama bakinta. Suna isa asibitin direct A&E, sanin matsayin Alh,Muktar yasa aka barsu suka shiga, idonsu ne ya sauka kam Umar da har yanzu bleeding yake yanxu jinin hada tsare2 yace fita. Da sauri Mommy ta k'arasa bakin gadon idon taf kwalla ganin halin da d'inta ya shiga cikin kankanin lokaci. Haiydar ma tuni idanuwansa suka kad'a ganin tilon yayansa kuma abokinsa da basu Dade da rabuwa ba ya kowa cikin dan lokaci. Dady kuma gun Dr yaje yana mishi bayani, yace" Alhaji gaskia yana bukatar ayi masa aiki cikin gaggawa saboda ceto rayuwarsa, munyi iya kokarinmu mu tsaida jinin amma abin yaci tura saboda kansa ne ya bugu kuma jinin ya kusa harbawa zuwa kwakwalwarsa wanda bama fata, so yanzu ka saka hannu sai ayi masa aiki"ya fad'a yana mikowa dady paper. Saka hannu yayi sannan ya koma inda Umar, koda yaje nurses sun je da rigan shiga operation zasu saka masa, wayarsa ya ciro daga aljihunsa ya fara rubuta text kamar haka:- _"zan tafi na barki a dai-dai lokacin muke bukatar juna, pls kada kiyi kuka Addu'arki kawai nakeso sannan ina neman alfarmarki don Allah ki daure ki auri Haiydar, saboda *Haduwarmu dake* Alkhairi ne, ina muku fatan Alkhairi, ki yafemin laifukanda na miki_." Naki Umar Sadauki. Yana turawa aka canja masa kaya, Mom na rike da hannunsa tana masa Addu'a ya kalleta muryan na fita dakyar yace" Mommy kiyafemin laifunkanda nayi miki". Matse hannunsa tayi cikin nata hawaye na fita a idonta tace "Umar bakayimin komai ba kai d'ane da kowacce uwa zatayi alfari dashi, bakamin laifin komai ba, ciwo ba mutuwa bane inshaa Allah zaka warke kaji". Murmushi yayi sannan ya kalli Haiydar dake rike da dayan hannunsa yace " lil pls ka dena aikata abinda kakeyi da bashi da kyau sannan ina Neman alfarmar ka Auri Siddiqa ka maye mata gurbina zakayi alfahari da ita idan kika zauna tare, sannan ka yafemin laifinda nayi maka a zamanmu dakai" Shima hawayen ykeyi yace" zan daina inshaa Allah, pls ka dena fad'an haka radadin ciwo ne kawai zaka warke da yardar Allah, kuma bakayimin komai ba sai Alkhairi nima ka yafemin" ya k'arasa yana hawaye. Murmushi yayi sannan ya kalli Dady yace " Dady ka yafemin, kuma don Allah Ku k'arfafa zumunci Ku had'a Haiydar da Siddiqa ". Dady kam ya karaya da wasiyyan nan da d'an nasa keyi, yace"bakayimin komai ba son nayafemaka Allah ya baka lafeeya" Ya sake juyawa inda Mommy yace "Mommy ki rokamin Zarah da Hanan da inna kice nace zanyi missing nasu" Itama zuwa yanzu ta karaya "tace nafemaka Umar kuma inshaa Allah zakaji sauki kaje garesu" ta fad'a tana share hawaye. Daga nan aka tura gadan zuwa operation room, su kuma suka zauna reception. Siddiqa tunda ta shiga gida d'aki ta shige ta rufe taci kukanda batasan dalilin yinsa ba, daga baya bacci yadan d'auketa wadda yake cike da mafarkai Mara ma'ana, tshinta yayi dai-dai da shigowa text d'in. Tana karantawa hankalin yai bala'in tashi, wayar ta kira ta jita kashe, dirowa tayi daga bed ta fita d'akin a rikice. 1hour later.... Dr, ya fito daga operation room duk yayi zufa, tare suka Mike suna tambayansa anyi nasara, yayin fuskarsa ce ya canja yace" mutuwa da rayuwa a hannun Allah suke, mu iyakacinmu muyi iya kokarinmu mu, sorry 2 say kun rasa shi". Shako wuyansa Haiydar yayi yace "what!!" Sannan ya tafi luuu zai fad'i, Dady ya tarosa ya some a jikinsa... _nima anan na some na yadda phone Dina_ ๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข *Innalillahi wa'innah ilaihirraji'un, ina mika ta'aziyyata ga daukacin musulmin duniya na wannan babban rashi da mukayi na shugaba,Malami,jagora a musulunci _Dr, Alhassan Sa'eed Jo's_ Allah yai masa rahama ya albarkaci zuriyarsa ya kyautata tamu bayan tashi.* ๐Ÿ’„ Meryerm Abdool ๐Ÿ’„ [5/20, 6:22 PM] ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ( _Based on love story_ ) *Written* *By* ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„ ยฉ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_* ( *P.M.L* ) ~Mutuwa aya ce ga al'umma, amma mutuwar malamai musiba ce ga Al'ummah. Allah (S.W.T) yana cewa:- idan zamani ya rikice zunubai suka yawaita sai mu dauke ilimi mubarku da jahilcinku. Ta hanyar malamai ne muke samun ilimi, idan aka dauke su Al'ummah sun shiga musiba, Allah ka jikan malam Dr, Alhassan Sa'eed Jos, kasa mutuwa ta zamo Hutu, ka bashi magaji daga cikin iyalansa ameen.~ ๐Ÿ‘๐Ÿป *page* 38&39 Dady na rungume da Haiydar ba abinda yake fad'i sai, "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allhumma ajirni fii musibatii" abin yake maimaitawa kenan. Mommy kuma rasa natsuwarta tayi nad'an lokaci harta dora hannu aka zatayi ihu, sai kuma natsuwa ta dawo mata, zamewa tayi k'asa tana fad'in " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" tana maimaitawa itama sannu a hankali taji hawaye na silalo mata. Nurses ne suka iso da bed d'in d'aukar Mara lafiya suka d'auki Haiydar, ganin za'a wuce dashi yasa Mummy mik'ewa tabi bayansu tana share hawaye. Dr, ya dafa Dady yace "Alhaji sai hakuri duk rai bata wuce lokacin ta, yanzu Addu'o'inku kawai yake nema" ya fad'a yana kokarin wucewa. Share gumi yayi yace "hakane Dr, zan iya zuwa gareshi yanzu?" Ya fada yana kallonsa da idanunsa da suka kad'a sukayi ja. Girgiza masa kai yayi sannan yayi gaba Dady yabi bayansa, kwance yace kan bed a rufe da blanket daga kafa har kai, yaye zanin Dady yayi saida gabansa ya fad'i, wai Umar d'insa ne kwance kaman yace ya tashi, amma kuma ba daman hakan. Yayi wani irin haske fuskarsa d'auke da murmushi kaman kayi masa magana ya ansa, ji yayi kwalla ta zubo masa, gogewa yayi sannan yaba Dr, Umarnin a cika file d'in karbar gawa zasu wuce dashi. Mommy na zaune hannunta cikin na Haiydar tana tofa masa Addu'a ga k'arin ruwa da aka masa, tunani take lokaci d'aya farincikin da suke ciki ya juye zuwa kishiyarsa, sun rasa Umar har abada ga kuma Haiydar a kwance wannan duniyar fa gashi cikin awowi kad'an komai ya canja masu.....Dady ne ya katseta ta hanyar sallamar da yayi ya shigo d'akin. K'arasawa yayi bakin gadon wanda yayi dai-dai da farfad'owar Haiydar jin hannunsa cikin hannun mutum ne yasa shi cewa" nasan ba zaka tafi ka barmu ba Bros, nasan ba zakayi nisa damu ba nasan ......." Mommy ta katseshi ta hanyar girgiza shi tace "ka dawo hayyacinka son nice fa momynka" ware idonsa yayi ganin hannunsa cikin na Mommy ya sakashi tashi zaune yace. "Na ganki Mommy amma don Allah kada kice min abinda Dr, ya fad'a gaske ne" ya fad'a yana hada hannyensa guri d'aya. Sosai iyayen suka tausaya masa saboda sun san irin shak'uwar da ke tsakaninsu, dole ya baka tausayi saidai ubangiji ya fisu sonsa ya kuma karb'i abinsa. Lallashinsa iyayen suka shiga yi da nuna masa karb'ar k'addara, jinsu kawai yakeyi amma shi sam ya kasa yadda da cewa d'an uwan nasa ya rasu...har saida yaga gawarsa tukun.. A firgice ta shigo ta falon inda k'awayenta suke, ganin yanayinta yasa suka shiga ta tambayan ta meya faru, bata bi ta Kansu su ba ta fice, k'aramin falon Mama ta samu Aunty da Mama suna tattaunawa gane da bikin, fad'awa jikin Aunty tayi ta saki kuka tace. "Aunty kiga text d'inda ya Umar ya turomin" ta fad'a tare da mika mata wayar. Ansa tayi ta karanta, itama adan firgice tace "ba yanzu yabar nan ba? Tome wannan text d'in ke nufi me kama da wasiyya?" Ta fad'a tana mik'awa Mama. Karantawa tayi duk da hankalin ta ya tashi amma danta kwantar mata da hankali yasa tace "Ku kwanta hankalinku wata kila yana mata wasa ne". " Allah ba wasa bane Mama, inaji a jikina wani abu na shirin faruwa da ya Umar, kuma maganganunsa na yau suna kama dana ban kwana" Siddiqa ta fad'a cikin kuka. Aunty tace" kwanta da hankalin ki baby ba abinda zai same shi ki kirasa yanzu kinji". "Na kira bata shiga ba harta Zarah tana ring ba'a daga ba" ta fad'a. Mama ta daga wayanta ta kira Mommy amma shiru ba'a dauka ba'a daga ba, nan hankalinsu ya kara tashi, ga kuma kuka da Siddiqa ta sakasu gaba tana musu. Anyi duk abinda ya dace a asibitin an basu gawar yayin Haiydar ya koma kurma ba magana, police ma sun kawo motar Umar amma abin takaici an dauka kudaden da dayan wayarsa sauran abubuwa duk a sunan anje ceto ( hattara da ci da ceto wai kaga mutum ya samo accident amma sai aje da sunan ceto ayi sata, wannan wace irin musiba ce Allah ya kiyashemu ameen). Text Dady ya tura ga duka contact nashi ya sanarda rasuwar, sannan aka tura ga ma ta wayar marigayin. Hankalin Mai martaba ya daga sosai ganin sakon aminin nasa na rasuwar surukinsa, ya girmama Allah mai kashewa da rayawa sannan ya fad'a a fada akan ayi shiri zuwa jana'izar ya shiga ciki sanarda iyalansa. Had'uwa sukayi da Mubarak da shima yaga text d'in, a rude yace "ranka shi dade kaga text d'inda aka turomin" ya fad'a yana k'ok'arin nuna masa, dakatar ta shi yayi ta hanyar cewa "Alh Muktar ya turomin nima, ba Wanda ke wuce lokacinsa Allah yai masa rahama, ka shiga ciki ka gaya musu su shirya zamu wuce can d'in gaba daya" yana kare fad'i ya shige ciki". Koda Mubarak ya shiga ya isko su sunata jimamin abin yayin da Siddiqa keta rusar kuka su Mama na rarrashinta saboda abin akwai tausayi da tashin hankali mutuwar miji satin Aure, shima ta bashi tausayi sosai yasan tayi babban rashi dan yasan Umar mutumin kirki ne ma saukin kai da sanyin hali, ya fad'a musu sak'on Mai martaba. ** ** ** Lokaci daya gidanjen biyu masu cike da farinciki, farincikin ya koma makoki, ikon Allah kenan mai yi inda yaso lokacin da yaso gun Wanda yaso bamaice masa meyasa? Sarkin sarakuna Allahu, Allahu Akbar!!. Motoci kusan 8 sukaje dasu, sun samu anyi masa wanka anyi sutura, anan suka had'u akayi masa sallah aka mik'a shi gidansa na gaskia. Matan suka shiga ciki, fad'in irin taron da akayi gurin jana'izar sai iya cinye mana page ba tare da mun gama ba, Umar mutumin mutane ne abokin kowa ba abinda kakeji ana fad'i sai kyawawan halayensa ana masa fatan alkhairi, da dacewa da kyakyawan makoma. Yayi mutane iya mutane harma wadanda basu samun daman ganin kushewarsa ba( Annabi Muhammad (S.A.W) yace idan gawar mutum ta samu mutum mumunai arba'in suka sallacesa ana masa kyakyawan fata, Allah yasa mudace ameen). Kashe gari... Motace siyana 2016 latest, ta parker bakin gidan wata matace ta fito wacce kallo daya zakayi mata ka gane kamarda sukeyi da Dady, sai wata matashiya wacce itace ke jan motar siririya,dogowa sosai ta tafi sanbal one take, farace fuskarta ba laifi kyakyawace tana yanayi da Zarah, saidai ta fita katon mouth, sanye take da Jean pencil sai top iya guiwa da dan siririn gyale da tayi rolling. Gaisawa sukayi dasu Dady dake waye sannan suka shiga daga ciki, sam yarinya bataji kunyar shigar da tayi ba, hakama, uwar tata. Ciki

Chapter 7 of 16