Share this page
mubar garin, amma yanda kika gani?" "Na Amince k'awata matsala d'aya ce ya zanyi da Mami?" "Kada ki damu da wannan kawo kunnenki kiji" matsowa tayi kusa da ita, (ni Maryama duk k'wak'wana dason d'auko muku rahoto basu barni naji komai ba), sai shewa naga sunyi suka tafa (nace Ashe bugun *gadanga k'usar yaki* bai horaku ba, to Allah ya shiryamu daku baki daya). Daganan na kwasa a guje zuwa gidan Dady dan ganin wace wainar ake toyawa. Lolz Suna isa gidan direct part d'in Momy suka wuce, a parlour suka sameta tare da Hanan da Zubaida suna kallon Africa TV 3, bayan sun gaisane Momy tace "kai na ganku haka wani iri?" Ta fad'a ganin yanayin fuskarsa da kuma ganin Siddiqa bayansa tayi fuskar tausayi. "Magana ce tafe dani, Dady na nan kuwa?" Eh" kawai ta fad'a sannan haura sama domin kira musu shi. Zama yayi sannan yace dasu Hanan su shiga ciki ganin ba wasa a fuskarsa ya sakata bin bayan Zubaida suka shiga d'aki. Bayan Dady ya sauko sun gaisa ne yace " Son Momynku tace kunzo da magana, meke tafe daku?" Ya tambaya yana kallonsa. "Am Dady dama ba wani Abu bane face...." Nan ya gayama su Dady duk abinda ya faru. Mamaki ne ya kamasu Momy sai salallami take yi, yayin da Dady yace. "Ai kaga irin abinda nake gujemaka tun farko, shiyasa na haneka Auren ta amma kak'i ji, duk da bansan shed'ancinta yakai haka ba" haka yaita yarfa masa fad'a har saida ya sauke aya sannan Siddiqa tayi magana cikin siririyar muryarta tace. "Dady ba laifinsa bane..daganan itama ta gaya musu abinda ta sani game da asirinda akayi zuwa hanyar da tabi ta warwaresa. Ba k'aramin mamaki sukayi ba sannan suka jinjina na mata da irin k'ok'arin da tayi, Momy tace " yata Allah yayi miki Albarka lallai *Had'uwarmu dake* wani haske, kai kuma Son inason ko gaba ka kiyaye Addu'a domin garkuwar musulmi CE, Allah yayi muku Albarka." "Ameen " sukace baki d'aya. Shima dad'i Albarka ya sanya musu sannan yace da Haiydar "to yanzu ina Fauziyar?" "Dady tunda na fitar dasu gidan bansan inda ta nufa ba." "To Allah ya kyauta, duk laifin Sambo da Bara'atu ne su suka kashe rayuwar 'yarsu, sannan yace kai kuma Son ka dena yin saki ukku Kai tsaye ka kiyaye." Itama Momy tace "tabbas Allah ma bayason hakan saika kiyaye." Ya ansa da "inshaa Allah zan kiyaye, sannan yace Dady ina Neman alfarmar ka barni na dawo nan gidan da zama kafin na gina wani gidan, dan wallahi wancen ya ficemin arai gaba d'aya." "Ba matsala ai naka ne Son, ka dawo kayi zamanka" daga nan aka rufe taro da Addu'a kowa zuciyarsa cike da jimami. Siddiqa tsohon part d'in su taje ta k'ara kakkab'ewa tare da taimakon Zubaida da Hanan, duk da ba wani datti dan Momy na kula dashi akai-akai, nan taje guri yad'au kyelli da k'amshi, dake dama basu d'auki komai ba zuwa wancen gidan komai sabbi aka zuba, sai bayan la'asar suka kammala salla tayi sannan ta d'auko phone d'inta ta kira haniniyarta wato Shamcy. Tana d'aga wa ta bata labarin abinda ya faru sannan ta k'ara da yi mata godia akan sata a hanya da tayi tace *Had'uwata dake* besty Alkhairi ne ke k'awace ta gari da duk Wanda ya sameki to za'a tayashi murna dan ya samu *Babban rabo*(cweetjidda) ina alfahari dake Besty." "Kai besty kinfi k'arfin haka gurina, kuma aikinki yayi yadda akeso, sauran ki d'ayan, shima nasan zaki zomin da excellent" ta fad'a tana daria. Itama dariyar tayi sannan sukayi sallama. Haiydar kuwa yana barin gidan direct hospital ya wuce, saida aka tabbatar masa da lafiyarsa sannan ya wuce gidansa ya d'aukar musu important thing nasu, ya kulle ciki sannan ya gayama mai gadi zai koma tsohon gidansu, yaci gaba kula da gidan kafin ya samu mai sayenshi, sannan ya wuce, mai gadi kam kan shine ya k'ara kullewa gashi ba daman ya tambaya. *9:00pm* Siddiqa ce tsaye gaban mirror d'aure da towel tana shafe jikinta da soft perfume masu wani sihirtaccen k'amshi,kofa akayi aka shigo tare da sallama ansawa tayi ba tare data d'ago ba. Haiydar dake tsaye bakin k'ofa ji yayi wata kasala saukar masa ganin Siddiqa a haka da kuma jin daddad'an k'amshi dake tashi. Jan kafa yayi ya k'arasa inda take yasa hannyensa biyu ya kama k'ugunta sannan ya d'ora kansa ga kafard'arta yace " *ina sonki* Siddiqa yau kam bakina bazai iya boye Kalmar sonki ba." D'ago wa tayi cikin mamaki ta kalleshi daga mata gira yayi yace " yes I mean it" shiru tayi batace komai ba. "Kije kiyi alwala kizo muyi sallah" cewa tayi ainayi lsha'i yace "wannan sallar godia ga Allah CE zamu yi." "OK to ai inada alwala" to dakko dadduma ko" d'auko wa tayi ta daura zani ta saka hijab sannan ya jasu sallah, Addu'a sosai ya kwararo musu daga yayi mata tambayoyi ta ansa mishi yadda ya kamata. Dauko plate da cups yayi juye kaza da hollandia, bismilla yayi mata ganin tak'i cine yasa ya janyo ta jikinsa ya ringa bata har saida ya tabbatar ta k'oshi sannan yaci bashi, bayan ya gamane ya fita da plate d'in. Koda ya dawo d'akin harta haye bed, light up yayi sannan ya bita gadon, ( ni maryama) ganin za'ayi Abu yafi k'arfin idona yasa na tattara nawa da nawa nabar d'akin. _gudnyt Mrs, Sadauki, fatar za'a Samar mana baby_ 😳😜 ✍🏻 πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Based on love story_ ) ```Written``` ```By``` πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* *P.M.L* ```ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA YANA CEWA:-``` *Dukkan ninku masu kiwo ne kuma zamuyi tambaya ga yadda kuka gudanarda kiwonku* *Ma'ana kiwon 'ya'yanmu, 'ya'ya ni'ima ne wani b'angaren kuma musiba ne, ya danganta da yadda muka basu tarbiya, Allah yasa mu dace Ameen* πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ» *Page* 60&61 _Duk saurin da nake gari ya waye naje na dauko muku rahoto, amma sai bacci ya zolayeni ya d'auke ni, bani na tashi ba sai 9, baki kawai na wanke na isa gidan, amma kash a parlor na samesuπŸ˜’πŸ˜±πŸ˜¨_ Rungume yake da ita bata tea a baki, sai wani k'ara narkewa take a jikinsa, juya kai tayi alaman ta k'oshi, kallonta yayi da murmushi kana ganinsa kaga sabon Ango goshinsa sai kyalli yake, kallo daya zakayi masa ka tabbatar yana cikin farinciki, yace. "Sowie baby nah daure ki shanye zakiji k'arfi a jikinki kinji 'yar Albarka" turo baki tayi tace "uh um nidai ya isa haka." "OK" kawai ya fad'a sannan ya mik'e ya dauki cup da plate d'in wainar kwai don kai kitchen, binshi tayi da kallo har yaje ya dawo, hure mata ido yayi yace. "Kallon fa?" Sauke numfashi tayi tace "hmmm dama ashe haka kake?" Smiling yayi sannan ya janyo ta zuwa jikinsa yace "Mugu ko" girgiza kai tayi alaman eh. Rad'a mata a kunne yayi "indai akan sonki ne bakiga komai ba, a mugunta na. Cewa tayi " amma dai Ya Haiydar wannan son da kaketa fad'a tsakanin jiya zuwa yau ne ya fara ko?" K'ara matseta yayi a k'irjinsa tare da lumshe ido yace "Aa ya fara ne tun farkon *Had'uwata dake*." Zamewa tayi daga rik'on da yayi mata tace ta kalleshi cikin mamaki tace "kana nufin ranar da ka watsa mana tab'o?" Girgiza kai yayi yace "Aa ranar da na fara ganinki a skull, a ranar na fara sonki! Love at first seen, amma nabar abin a zuciyata, saboda banaso na gayamiki, ki renani" kallon yadda ta lafe a jikinsa tana sauraronsa yayi sannan yaci gaba da cewa. "Ana haka ne kuma sai muka shiga 'yar tsama dake, hakan yasa nace zan cire sonki a raina na gyara miki tunani, amma ina kullum farashin sonki kara hau hawa yake a birnin zuciyata, na shiga rudu sosai lokacin da ya Umar ya nunamin ke a matsayin wacce yakeso, saboda na yadda na rasaki, ina son Yayana shima yana matukar sona....." Katse shi tayi ta hanyar cewa. "Ni kaina nasan yana sonka matuka dan magana d'aya zuwa biyu saiya ce Lil." A tare sukace "Allah yayi maka rahama ya Umar." Kallon juna sukayi suka ansa da "ameen" sannan yaci gaba da cewa "nasan da Bros yasan ina sonki to tabbas zai barmin ke saboda nasan zai yimin abinda yafi haka, to saidai nima ina matukar son ganin farincikinsa kuma na fahimci kece farincikinsa, shiyasa nabi dare ina rokon Allah ya yayemin sonki, amma kash hakan bata samu ba, wayyo har kishin bros nayi akanki dan muddin naga yana waya yana daria ko murmushi raina kece kawai yake bani, naji kaman na shakesa, Saleem shine mutum na farko daya fahimci ina sonki amma kuma nayi fuska nace Sam ba haka ba." "Rasuwar Bros ta girgiza ni wuce tunanin ki, sai daga baya na gane akwai abinda ubangiji ya gani, yasa ya d'auke minshi, nafi kowa farinciki a ranar da kika zama mata a gareni amma kuma na kasa nuna hakan saboda tsoron kada renani kuma kik'i amincewa dani." Saketa yayi ya zame k'asa kan gwiwarsa ya d'ora hannyensa kan cinyarsa yace "gani gaban ki Maryam Siddiqa, nasan ni mai laifi ne a gareki, amma inaso kiyi hak'uri ki yafemin, ki d'aure ki samamin gurbi a zuciyarki, badon halina ba sai don Allah, pls Siddiqa 4 d sake of my brother's love" ya fad'a yana D'ora kanshi a cinyarta. Hannunta ta nutsa a cikin sumarsa tana shafawa sannan tace "waya gayama bana sonka Ya Haiydar? To Bari kaji ban tab'a son wani namiji ba bayan kai, kuma bana tunanin zanso wani bayan kai, so daya ne tak kuma kai nakema shi." Cikin mamaki ya dago tare da zare ido da bude baki alaman mamaki k'arara ya bayyana a fuskarsa. Sannan yace "kina nufin har Yaya Umar d'ina?" Smiling mai rikitashi tayi tace "kamar yadda na fad'a maka to hakane, saidai Ya Umar yanada matukar kima da girma a idona, na yadda sane saboda yana sona kuma ya had'a komai da ake nema ga mijin kirki, kuma nayi niyyan Auren sa da zuciya daya na zauna dashi na bashi cikakkiyar kulawa kamar yadda addini ya tsara, amma da yake, Allah baya d'ora ma baya abinda bazai iya ba, sai yayi nashi iko." Jinjina kai yayi alaman gamsuwa sannan yace "to idan na fahimceki dai2 kenan kema kin dad'e da fara sona?" "Yes of course! Na fara sonka a lokacin da na fara ganinka my first in d skull shine farkon *Had'uwata dakai* d same 2 u love at first seen!, saidai kuma ganin halinka yayi opposite da nawa yasa na gudurce a raina ko sonka zai zamo ajalina to lallai bazan aureka ba, na amince da ya Umar ne saboda sonda nake maka, ko ba komai ina tare da jininka, sai daga baya nakeji a gun ya Umar Ashe Sam yadda na d'aukeka ba haka abin yake ba, kamar kai nima besty ce mutum ta farko taga gane ina sonka, kaima kana sona abinda nika k'asa ganewa sai ita hadda jaddamin duk ranar da gaskia tayi halin ta saita cini tara." Kan seat ya zauna ya janzota kuwa jikinsa sannan yace "wannan Bestyn tamu da mijinta sun sa mana eyes da yawa" lumuwa tayi jikinsa tace "sosai kuwa." Haka dai suka lalace anan suna tuna asirin zukatansu, tare da tuna abubuwan da suka faru baya wani abin dariya wani na ban haushi, saida aka fara kiran sallah sannan ya mik'e yana fad'in. "Kinganki ashe haka kike da fira? Amma idan aka ganki ki ringa cin magani." Smiling tayi tace "ai kaima baka magana sai jin feeling kana magana kaman mai ciwon baki" dungure mata kai yayi yace "naji dai a komai nayi *kece sila* (suhana) hannu ta mik'a masa alaman ya d'auke ta. Mak'e kafad'a yayi yace " naki wayon" cewa "Allah bazan iya tashi ba." "Hmmm! Yarinya gwanda ma ki ware, dan ko yau inaso na kashe arna koda dubu ne." Zare ido tayi tace "me!" Daria yakeyi bil hakk'i, hadda kama ciki ganin yadda ta tsure, ita kuma shagala tayi da kallonsa sai taga yayi mata kyau sosai, saboda bata tab'a ganinsa yana daria ba. Ganin ya tsaya ne yasa sakata kwab'a fuska tare da fara dukan kujera, tana fad'in "wallahi ya Haiydar ban warke ba, Allah sai in kanaso ka k'arasa nine"ta fad'a tana dame fuska. Daf da fuskarta yaje yace" yaushe na tashi daga Lil, na koma ya Haiydar? Ko daga jia zuwa yau ne?" Ya fad'a yana kashe ido d'aya. Cikin shagab'a tace "ai dama nasan kai ba little bane, ko da can tsokana ce tasa nake cewa." D'aukarta yayi kamar wata baby yana haurawa sama yana fad'in "bari inje in k'ara gasaki, saboda naji dad'in kashe arena, yau kuma za'a kiramin? Tunda an kiramin Aunty da Mama, da Mai martaba" ya fad'a yana daria. Dukan k'irjinshi ta ringa yi tana fad'in "Allah banaso" shi kuma yace "Toni inaso mana...." ****************** *12:00pm.....* Fauziya ce na hango ta dame cikin jean& shirt irin crazy nan, tayi rolling d'in gyale sannan ta mamma no respect, Halidubu na gefenta itama ta dame cikin tata irin shigar, suna zaune a reception suna jiran flight dinsu dazai tashi zuwa one. Kallonta Halidubu tayi tace "beb ya kamata ki kira Mami." "OK" kawai tace sannan ta danna kira. Ring 2 ta d'aga tace "hello dota" cikin muryan kuka tace "Mami." Rud'ewa haj. Bara tayi jin tilon 'yarta na kuka, cikin damuwa, tace "dota menene?" "Mami ya Haiydar ya sakeni, bayan yayimin tsinannen duka saida kamannina suka canja." Cikin Rud'u tace "what! Kutumar ubancan, yama isa dan Uwarsa, yanzu kina ina kuma saki nawa yayi miki, sannan ya akayi haka ta faru ko maganin ya karye ne?" Ta jera mata tambayoyin. "Bansan ya akayi ba kawai zuwa yayi ya sameni yaita dukana har saida yaga bana numfashi sannan ya bani saki uku" ta fad'a tana rushewa da kuka. "Uku fa." "Eh Mami, shiyasa na yanke shawarar bin duniya kawai kiyafemin Mami bazan iya zama ayita yimin gori ba kema a batamiki, bazan jure ba" kit ta kashe wayar. Sannan tayi saurin kashe wayar ta cire sim ta yar. Juyawa tayi ta kalli Halidubu tana smiling, hannu ta daga mata tace "Weldon excellent job" sannan ta cilla wayar a jaka...... Haj, Bara tana fad'in "kada kiyi min haka dota kece farinciki na kada ki tafi ki barni...." Taji kittt alaman an katse wayar. Bin kiran tayi amma ina is switch up! Haka tayi ta kira Abu daya ake gayamata. Zaman dirshim tayi sai zufa ke keto mata ta ko'ina, duk kuwa da Ac dake aiki, jitayi kaman ta d'ora hannu aka tayi ihu, ta rasa wane irin tunani zatayi k'wak'walwar ta cushe baki d'aya... Tayi tsayin hour gurin, kafin daga baya ta mik'e ta dauki jaka da mayafi, ta kira driver ta tace ya fitar da kota zasuje birnin kebbi.. *Around 2:30pm...* Siddiqa ce Zaune a parlour tana kallo, pop corn gabanta tanci, jin tayi kaman hayaniya cikin gidan, remote ta d'auka ta rage murya, tabbas hayaniyace akeyi. Kira ta kwalama Haiydar dake kitchen yana kiciniyar sama musu abinda zasuyi tayi. "Ya Haiydar" Daga can ya ansa "yes Baby menene?" "Zo kaji" fitowa yayi yana fad'in "what happened?" "Kaman hayaniya nakeyi cikin gida." "OK Bari, in duba" komawa kitchen yayi ya juyo indomie a plate, aje mata sannan ya fita don ganin meke faruwa.....! _pls manage am in little busy_ πŸ˜‰πŸ˜‚ ✍🏻 πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Based on love story_ ) *Written* *By* πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* *P.M.L* _This Page goes 2 my charming, adorable parents ever have in d would world, Late, Dr,Abdulkadir A. Gulma and Haj. Salma Sani, ILYπŸ’‹_ *Page*62&63 Yana fita direct part d'in Momy ya wuce, saboda can yake jiyo hayaniyar, da shigarsa da Gaggonsa Bara ya fara cin karo dake tsaye tsakiyar falon tana surfa bala'i kaman ta ari baki sai cewa take. "Kyace nayi hak'uri abi abin a hankali mana, tunda naki d'a na hannunki, niko tawa 'yar, ko oho! To wallahi bazai sab'u ba wai bindiga a ruwa, ehe" ta fad'a tana girgiza jiki. Da kallon rainin wayo ya bita kafin yake shigowa cikin parlour gaba daya, Momyn sa ya kalla dake zaune tana ba Haj. Bara baki. Yace "Momy wai duk wannan hayaniyar ta mecece?" Kafin ta bude baki tayi magana tuni Bara ta cafke tace. "Ta ubanka ce nace d'an iskan yaro, ka had'a rigima dan ka kai tsinanne sannan kazo kana tambaya, to bari kaji wallahi kaji na rantse, duk inda kasan ka kaimin 'ya kaje ka dawo da abita, idan kuwa ba haka ba hmmm!." Da kallon baki isa ba ya bita, ya bud'e baki zaiyi magana...Momy ta katse shi da cewa " kada ka sake kayi mana rashin kunya anan Son" ta fad'a cikin tsauri, kama bakinsa yayi amma zuciyarsa sai k'una take, saboda yadda maganan ta Sosa ransa. "Bayan kin riga kin gama b'ata yara da bakin halinki da kikayi gado, sannan yanzu kizo kina gyaran munafunci..." Katseta yayi ta hanyar cewa. "Dakata Gaggo..." Itama Momy katseshi tayi tace cikin tsawa " ba nace ka kamamin bakinka ba....." Ana haka Dady yayi sallama Wanda dadowarsa kenan daga taron da mai girma governor ya kirasu, ansa sallamar Momy tayi ta mik'e tare da anso kayan hannunsa, cikin girmama. Tsayawa yayi ganin kanwarsa tsaye sai jijjiga jiki tace kuma ta kasa koda ansa sallamarsa, ga d'ansa gefe zaune a carpet, shima da alama ransa a bace yake ganin yanayin fuskarsa ya nuna. Cewa yayi da kanwarsa, "ke kuma daga ina haka, kuma meya faru na ganki haka?" Kallon shi tayi tace. "Haba Yaya yama Za'ayi kace bakasan meke faruwa a gidankan ka ba, kace ba kasan me D'anka yayi ba, ai wannan bama zai yuyu ba" ta fad'a tana ki gaba da girgiza jiki. D'an murmushi yayi ya zauna kan seat sannan ya nuna mata d'aya yace "zauna" saida ta turo baki tana k'una k'uni sannan ta zauna Wanda yayi dai2 da saukowar Momy daga sama zama tayi itama. Sannan Dady yace "Bara'atu, kinsan abinda 'yarki take aikatawa?kin binciketa metayi? Kafin kizo nan da bala'i." "Haba Yaya metayi ita, bayan ita aka cuta" ta fad'a tana harare harare. Murmushi ya k'ara yi sannan yace "to bari kiji abind ya faru kafin ki yanke hukunci" daga nan ya gayamata abin da ya faru. Tashi tayi tsaye sannan tace "ai dole yarinya tace zata gudu, wato banda saki, duka, Ashe hadda sharri aka bita dashi, to wallahi ba zata sab'u ba wai bindiga a ruwa, dole na bima 'yata hakk'inta, kuma itama munafukar matar taka da tace taji da kai duk kotu ce zata rabamu daku, azzalumai kawai" ta fad'a tana nuna Haiydar. Haiydar dake zaune jin ta kira Siddiqarsa da munafuka ji yayi kaman ya tashi ya sharara mata mari, amma ba daman haka. Dady kuwa tsawa ya daga mata yace "ke Bara'atu kada kiga ina sassauta murya ki d'auka tsoronki nake, Aa nayi hakane danki fahimci me nakeso ki gane, amma tunda abin naki rashin mutunci ne, kije kiyi duk abinda kikeso" yana kai nan ya mik'e ya haye sama ya barsu anan. Itama fita tayi tanada surutai Mara dad'i tare da cin alwashi alkaline zai rabasu...... Dady kuwa bayan ya hau sama kiran kawunsu yayi tare da sauran 'yan uwansu ya shaida musu abinda ake ciki kada sai Abu yayi nisa ba tare da sun sani ba. Sun dad'in gayamusu da yayi sukace yayi kyau kai, kiranta sukayi suka bata baki amma sai cewa tayi "dan ba 'yayansu akayima bane,shi yasa suke cewa tayi hak'uri, dan haka ba ruwan su, su barta taji da abinda ya isheta" ba k'aramin baci ransu yayi ba, sannan kawu ya kira ya gayama Dady. Dady yace "kawu meyasa kuka kirata, da nasan zakΓ  kirata dana haneka don nasan a yadda hankalin Bara'atu ya bar jikinta komai zata iyayi, amma kuyi hak'uri kawo ku barta duniya ce tafi bagaruwa iya jima." "Ba komai Muktar, Allah ya sawwaka" kawu ya fada sannan sukayi sallama. ******************* Rai a bace Haiydar ya shiga part d'insa amma tozali da yayi da abar kaunarsa kwance kan 3seat tana bacci cikin kwanciyar hankali, ganinta kawai da yayi sai yaji 90% na fushinsa ya tafi, plate d'inda ya aje mata ya bud'e, ganinsa yayi yanda ya ajeshi ba tare data ciba, rufewa yayi sannan ya koma inda take ya duka dai2 fuskarta, shafawa yayi sannan ya kai mata Peck a kumatu. Sannu a hankali ta fara bude idonta ta sauke su akansa, k'ok'arin tashi takeyi, smiling yayi mata sannan ya jayota zuwa jikinsa bayan ya zauna shima. Yace "baby love meyasa baciki abincin ba, gashi har ya fara hucewa" turo baki tayi tace. "Ba kaine bakazo ka bani ba" murmushi yayi yace " kai baby love shagwab'a, dama haka kike Ashe zansha fama dake kenan." K'ara cunno baki tayi ba tare da tayi magana, dariya ta bashi kaman wata yarinya, sungumarta yayi ya kaima toilet d'in d'akin k'asa ta wanke bakinta, sannan suka dawo parlon sukaci noddle d'insu yana bata tana bashi cikin sigar love, bayan sun kammala ne sunyi hamdala yakai plate da cup d'in ciki ya dawo ya zauna kusa da ita. Cewa tayi " ya Haiydar." "Na'am baby love" ya fad'a yana kallon ta. "Meya faru hala dazu, naga ka dad'e da kaje duba meke faruwa?" Yatsina fuska yayi yace "is not a big deal, dama Goggo Bara ce tazo tana da masifa, kinsan halinta dama bataso a zauna lafia, so shine kawai yanzu naji tana fad'in karana zatayi ko meye oho, can mata dai" ya fad'a yana tab'e baki. Sosai yayi mata kama da time d'inda suke fad'a, anan ta gane halin nanan dai kenan, dan zaro ido tayi tace "k'ara fa Ya Haiydar kana nufin koto zaku shiga kenan?" "Yes hakan take nufi, kuma ni a shirye nake da ita, kada ki tada hankali ba abin damuwa bane kinji." Girgiza Kai tayi tace "Allah ya sawwaka" yace ameen." Saida yayi 3 days yana jinyarta duk kuwa data ji sauk'i tun ranar amma tak'i nuna masa gudun kar ya k'ara yi mata baranbarama, dan taga take taken sa zaiyi Rigima, daya shiga gurin Momy saida ta banyesa 'yarta lafia take jia da yau bata shigo ba, sai cewa yayi tayi dan zzabine shine bata samu ta shigo ba, cewa tayi "Ayya, Allah ya bata lafia ka gaida min ita kafin nazo. Yana shiga kuwa ya gayamata sakon Momy, zaro ido tayi tace "na shigesu bari in tashi inje kafin tazo naji kunya" haka kuwa ta mik'e ta zura hijabinta tana, shidai kallon ikon god kawai yakeyi, saida tazo ficewa ne yace. "Baby love" juyowa tayi ta kalleshi ba tare da tayi magana ba. "Dama kinji sauki ko?" Sai lokacin ta tuna tab'argazar da tayi, saita koma d'ingisawa ita a dole ciwo takeji, dariya ma ta bashi yace. "Hmm! Yarinya gwanda ma kiyi tafiyarki dan yau ba d'ingishi kike ba, ko rarrafe kike saikin biyani wahalar da kika sakani na d'aukarki" wani marairaice fuska tayi cikin sanyi tace. "Wayyo Ya Haiydar pls yi hak'uri wallahi da saurana fa" darawa yayi yace "to jeki naji" haka ta fita jiki sanyi qlau dan tasan yau tata ta sameta. Aiko kaman yadda ya fad'a hakan ce ta faru, don kuwa taci kud'arta, ta murzu iya murza, dan saida yaga da gaske numfashinta na zuwa da dawowa sannan ya sarara mata. Kwance suke bayan sun tsarkake jikinsu suna hutawa kan bed, dan ba ita kad'ai taji jiki ba, shima yaji. Idonta lumshe kamar me bacci tana kan k'irjinsa yace" baby love." "Na'am Ya Haiydar" ta fad'a ba tare data bud'e idon ba. "Yawwa banason Ya Haiydar d'in nan, ki canja min suna." Still idonta rufe tace " wanne suna kakeso to." Zaune ya tada ita yace "bud'e idonki mana, yanda zaki zabo mai kyau." "Uh um ya Haiydar bacci nakeji" ta fad'a tana k'ara narkewa a k'irjinsa, "OK, tom bari muyi baccin" gyara mata kwanciya yayi sannan ya kwanta shima daga nan wani bacci mai dad'i yayi gaba dasu............. *2morrow morning...* Bayan sunyi kari sun shirya cikin k'ananun kaya sai zuba kamshi suke, a parlour suka yada zango kamar kullum tana kwance bisa k'irjinsa,

Chapter 12 of 16