suka shiga Mommy tayi musu sannu da zuwa uwar ta ansa ba yabo ba fallasa, sannan suka zauna maid ta d'auki kayansu takai d'aki.
Gaisuwa sukayi sannan uwar tace "Ashe Umar an cimma sa'i muna shirin zuwa biki sai kuma mukaji wannan mummunan sakon"
Murmushi k'arfin hali Mommy tayi tace " hakane Bara lokaci yayi ba wata magana kuma".
Itama diyar gaisuwa tayi masu sannan Mommy ta nuna masu familynsu Siddiqa itama ta gabatarda ita garesu yayin da Siddiqa ke rakub'e gefe tana jan carbi hawaye wani nabin wani, gaisawa sukayima juna sannan suka zauna, Zarah na gefe itama tana rungume da Hanan data k'i cin abinci sai aikin kuka da takeyi wai ita akaita inda ya Umar, itama Zarah kukan takeyi saidai hawaye kawai abin gwanin tausayi.
Ranar da akayi Addu'an uku su Siddiqa suka wuce bayan Mai matarba sun tattauna da Dady game da wasiyyan marigayi.
Mutane sun watse saboda Dady yace ba wani zaman gaisuwa da za'ayi ya yafe, shi ka Umar Allah yayi masa rahama (zaman gulma ne kawai dacin abinci).
Ya rage saura su inna da kuma su goggo Bara, tarasu Dady yayi dan yi musu bayani gameda shawarar da suka yanke shida mai martaba.
Yace" kaman yadda kuka sani marigayi yabar wasiyyan ahad'a Haiydar da Siddiqa, to mun zauna dashi Alh,Muhammadu mun ga dacewar hakan, dan haka mun yanke za'a had'a hadda nasu Zarah wani wata mai kamawa inshaa Allah ".
" Wayyo Allah" sukaji anyi ihu sannan tace " wallahi nikeson ya Haiydar, kuma wallahi ni zai Aura ba ita ba" ta fad'a.
Dago ido Haiydar yayi Wanda tunda aka fara maganar kansa na k'asa saboda tunda akayi rasuwar ya bala'in canjawa ya zama so silent dak'ar yace magana, gashi ana maganan Aurensa da Siddiqa hankalinsa ya tashi sannan ita kuma wannan fitsararriyar tace waishi takeso.
Dady yace" ke fauziya nutsu anan, me kike fad'a haka? Ko bakiji mena fad'a bane iye?" Ya tambayeta.
Maminta tace " to ai Yaya abin Alkhairi ne ta fad'a kuma ma banda abinka Yaya gida bai koshi ba ai ba'aba daji ba"
"Wallahi kedai Bara'atu bansan yaushe zakiyi hankali ba yanzu saboda son zuciyarki saina bata Aure kenan ayi da 'yarki to ahir d'in ki Aure ba fashi" ya fad'a sannan ya tashi ya fita.
Momy ce tace "Alhaji adaibi komai a sannu " harara Bara ta kwad'a mata sannan taja 'yarta suka fita daga falon tana fad'i a ranta " zakuci ubanku ne Ku duka dani kuke zancen"
Haiydar ya rakasu da harara saboda ya tsani goggon tasa da 'yarta.
Su inna kuwa sukace Allah ya sawwak'a.
*waima shin wacece fauziya Wanda akafi Sani Fuu fashion??*
Ku biyoni a sannu dan jin cikaken bayani.
_kuyi manage da wannan nad'an shiga busy ne_ love u guys ๐
โ๐ป
๐Meryerm Abdool๐
[5/20, 6:22 PM] ๐Meryerm Abdool๐: ๐๐๐๐
๐๐๐๐ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐๐ป๐๐๐๐
๐๐๐๐
( _Based on love story_ )
```Written```
```By```
๐ *Meryerm Abdool* ๐
ยฎ ```PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S```
( *P.M.L* )
_Kuna raina akowane lokaci, u guys ur grateful pples, love u 4rm d button of my k'albiโค, Member of pure moment of life writer's_ love u all ๐๐
*Page* 40&41
*FAUZIYA*
'Ya d'aya tilo ga Alhaji Sambo Wamakko, wanda aka fi sani da Sambo kwangila, Wanda yayi fice da gurin yiwa gwannatin sakkwato a baya daga haka arziki ya hab'aka, ya kowa kasuwancin k'asa da k'asa, ya had'u da Hajia Bara'atu wani zuwa da tayi sakkwato gurin kanwar babansu dake iyayensu sun rasu tun suna yara, wacce ta kasance k'anwa ga Alh,Muktar Sadauki kuma k'aramar kanwarsu, kudi shine abin da yaja ra'ayin Bara'atu ga Auren Alh, Sambo dan Bara akwai son k'arya da nuna isa duk da yake iyayensu sun bar musu tarin Arziki amma hakan bai hanata Auren kudi ba, yayinda shi kuma Kyawunta ya fisgeshi.
Ba'a wani d'auki lokaci na akayi bikinsu, duk da saida aka akai ruwa rana da 'yan uwanta akan auren ta nace tace sai shi, haka suka hak'ura aka aura mata shi, anci amarci son rai, kafin daga baya su fara fuskantan matsala saboda shi Sambo irin mutanen masu I don't care with family daga yau yana wannan k'asar sai gobe yana can, zaman shi kad'an ne a Naija, shiyasa yaita Auri saki saboda matan basa iya jurewa, amma fa awadace suke da komai na more rayuwa saidai kam miji sai dai inkin ganshi.
A haka aka haifi Fauziya wadda Bara ta d'auki son duniya ta d'ora mata ba kwab'a ba tsangwama komai takeso shi takeyi dama to uba baya kusa sai tarbiyarta kacokam ta koma gun uwarta, shiyasa ta tashi a sangarce, sam batayi kara2n Islam ba saboda tace ba taso haka uwar ta kyaleta saboda batason bacin ranta ( ni kuma nace wannan ba shine so ba, kaso naka duniya ta k'ishi, ka k'ishi duniya ta soshi. Atoh ).
Haka ta kammala primary a ragaice sam batada respect ga wulak'anci batasan girman d'an Adam ba ko kad'an, ba Wanda ya isa yayi magana akan tarbiyarta yanzu uwarta tace bakin ciki ake mata akan 'yarta kwaya d'aya tal, dole 'yan uwanta dana babanta da makwabta suka kama bakinsu dan idan suka matsa saita zage taci mutuncin mutum akan 'yarta,Dady ne kawai ke taka mata burki saboda tana d'an shakkarsa, saidai ta tsani Mommy sam bata kaunarta ko kad'an haka in taje zata ringa yad'a mata bak'ak'en maganganu son ranta, saidai Mommy tayi murmushi kawai, shi kuma Haiydar dalilin da yasa ya tsaneta kenan, ita kuma 'yarta saboda rashin tarbiyarta.
Zuwanta secondary shine mafarin k'ara lalacewarta saboda bording tace tanaso amma fa ta kudi inda ba'a wahala saboda duka k'awayenta can sukace zasu itama tace sai can, duk da uwar bataso ba saboda bata 'yar tata tayi mata nisa amma dole ta hak'ura saboda cikar farincikin 'yarta, zuwanta ba dad'ewa seniors suka fara rububin ta da sunan Mommy and daughter da haka aka lalata da lesbianism ta kware a hanyar da Mommys d'inta suka k'are ta koma yi da wasu suma ta koya musu, haka tabi ta lalata yara da dama duk taga an kawo new comer tofa saita kalallameta da sunan Darling ko Daughter ta lalata ta.( mu kula sosai 'yan uwa masu bording schools da irin wannan shirmen na Mommy&daughter ko Darling bance duka ba amma wallahi mafi yawa abin suke aikatawa kenan kuma wallahi illar lesbian ba kad'an bace kuma is hard mutum ya fara ya kuma daina, Allah ya kiyashemu ameen).
Sunan fuu fashion ya samo asaline daga k'awayenta saboda yawan kwalliyarta da daukan wanka amma fa na fitsara, bayan kammala kara2nta na secondary haka ta dawo cikin gari taci gaba da bad'alarta kuma tayi sa'a da garin da yayi k'aurin suna a aikata wannan d'abi'a(sorry mutanen sakkwoto banyi don cin zarafi ba saidai fad'akarwa) haka taci gaba da inda ta tsaya, ta debo yara ta kawosu gida su shige d'aki suyi iskanci ba tare da uwar ta fahimci komai ba (iyaye ya kamata Musa ido sosai ga shige da ficen 'ya'yanmu, Musan k'awayensu da tarbiyarsu saboda tab'arb'arewar wannan zamanin da muke ciki da musibu sukayi yawa, 'ya'ya amanace wadda abin tambayne ranar gobe k'iyama yadda muka rikesu, Allah ya bamu ikon tarbiyar 'ya'yanmu kan sunnah Ameen).
Haka rayuwar tayita tafia a baud'e uban saidai in sun ganshi, yanzu haka tana Udus sokoto tana BMS a fannin computer tana shekarar k'arshe, tana 26 years, 1year Haiydar ya bata, iskanci kuma sai abinda yayi gaba hadda matan manya yanzu take mu'amala amma har yau uwarta bata san tanayi ba ana tsoron a fad'a mata ta karyata da kuma ci zarafin mutum a banza.
Maza sam basa gabanta saboda bata d'aukesu komai ba sai fanko gashi shekaru nata tafia tun in anyi ma uwarta magana tana fad'a har itama abin ya fara damunta, data tuntub'eta tace ita bata samo Wanda takeso bane dole ta kyaleta, dama tun can Haiydar yana burgeta saboda kyansa da gayunsa shiyasa yanzu data ganshi taga ya k'ara had'ewa ta yanke shawarar aurensa saboda ta rufe bakin mutane kada kowa ya gama ganota, ita kuma uwar ba k'aramin dad'i taji ba da zancen 'yar tata duk da batason Haiydar saboda rashin kunya da yake mata amma dole tayi amfani da damarta taga 'yarta ta samu *muradin ranta* (mm ussey ) koda halin k'ak'a..
_wannan kenan_
** ** **
*Back 2 story.....*
Ranar Hajia Bara ta tattara ta koma da mugun k'udiri a ranta.
Bayan fitarsu daga falon shima Haiydar haka ya tashi jiki sabule yabar parlon ya nufi part d'in sa, a parlor ya yada zango yai masauki kan kujera three seat, shiga duniyar tunani lokaci kad'an komai ya rikice mishi, ga rashin d'an uwansa rabin jikinsa ga auren yarinyar da ya tsana yasan kuma halin Dady sarai baya magana biyu, kuma koba komai zai so ya cikama d'an uwansa burinsa na k'arshe a rayuwa to amma kuma ya zaiyi da tsanar da yayi mata? Ga kuma wannan 'yar iskan da yafi tsana a rayuwarsa wai itama shi takeso duk da ya d'auki lamarinta a matsayin shirme, to amma meyasa shi baza'a barshi ya zabi wacce yakeso ba..........
Dafa shinda akayi ne ya dawo dashi daga tunanin da yake, d'ago kai yayi ya kalli Wanda ya dafashi da idanunsa da suka yi dan ja saboda tension.
Saleem ne tsaye gabansa yace "haba D one take things easy mana, tunda Yaya ya rasu ka d'auki damuwa ka daurama kanka, ka hana kanka sakat, Ya Umar ya Riga ya tafi Addu'a kawai yake nema yanzu daga gareka damusan ba taka bace saboda ba zata dawo da Ya Umar ba, pls b a man" ya fad'a yana bubbuga bayansa alaman rarrashi.
"Leem ba zaka gane matsala ta bane, bawai mutuwar bros tasani shiga damuwa har haka ba, yes inajin mutuwar sa amma kuma in baka manta kasan na fad'a maka bros yabar wasiyya akan ahad'amu da Siddiqa shine fa Dady ya taso maganar...." Nan dai ya gayamai yadda sukayi.
Murmushi Saleem yayi yace "to miye abin damuwa anan mutumina, ka manta da maganar waccen Fauziya tunda dama kace Dady ya kwab'esu, maganar Siddiqa kuwa dama can kunason junanku kawai Ku cika burinku Dana yaya" ya k'arasa fad'a yana daria.
Harara ya watsa masa yace "nine ke soyayya da wannan bak'auyiyar god forbid" ya fad'a yana tofar da yawu.
Dariya sosai Saleem yayi kafin yace "ai nasan ba zaka tab'a yadda ba, amma muna nan dakai gaskia zatayi halinta, any way koma bakwa soyayya idan kun shige daga ciki zakuyi ne"
Mugun kallo ya jefeshi dashi sannan yace "dawa?" Daria Saleem ya karayi yace.
"Ka fini sani" ya fad'a yana kashe ido daya, duka ya kwada masa abaya yana fad'in.
"Yaron nan kafa lalace Iya tayi maka Aure kawai, danna fahimci shi nakeso"
"Da kuwa zatayi min data taimakeni " Saleem ya fad'a, haka sukayi ta zolayar juna..
Bayan sun koma gida bak'i 'yan biki wasu duk sun kuma da jimamin mutuwar, har k'awayen Siddiqa na garuru duk sun koma banda Shamcy ita kad'ai ta rage.
Mai martaba yasa aka kira masa Siddiqa bayan ya k'ara mata gaisuwa yayi mata naseeha kamar kullum sannan yace " Uwata kinji abinda muka yanke nida Dadynku game da wasiyyan marigayi" nan ya fad'a mata yadda sukayi sannan ya Tambayi meye ra'ayinta.
Tace "Babanmu komai kuka yanke ba nida jayayya dashi, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi" ta fad'a hawaye na zubo mata tana tuna Ya Umar, da kuma k'iyayyanta da Haiydar.
Yaji dad'i sosai da maganar ta, sannan yayi mata Addu'a yace " inshaa Allah sai sunyi alfahari da *had'uwarsu* a zamansu, sannan yace ta shiga ciki.
Zaune suke ita da Shamcy tana gayamata yadda sukayi da Mai martaba ita kuma tana bata baki...wayan tace tayi ringing tana dubawa taga sabuwan no. Sanda ta kusa katsewa sannan ta d'aga da sallama a bakinta.
Sosai muryanta ta daki kunnensa, saidai yaja lokaci sannan ya ansa sallamar cikin isa.
Sarai ta gane shi amma sai tayi shiru danjin dame yazo, saida ya kara jan lokaci sannan yayi magana cikin muryan nan tasa dake saka 'yan mata ladabi, kaman bayason yi yace.
"Nasan kin gane mai magana, idan ma baki gane ba to keta Shafa, ina gargadinki daki je ki gayama su Abba bakyasona, if not hmmm! Ki shirya zaman prison a gidana"
Maganar ta b'ata mata rai, amma saita dake ta bashi ansa.
"Naji k'aramar barazanarka saidai inaso kasan wqni abu, kai in banda k'addara data gitta ta rabani da masoyi na me zanyi dakai k'aramin yaro, sannan da kake cewa naje na gayama su Abba cewa bana sonka to bazanje ba saboda ni nasan girmansu , gidanka kuma daxai zamo prison to fursunan zasu kasance biyu ne wato nida kai" tana kai nan bata jira ya fad'i komai ba tai hang up.
Sororo ya ringa bin wayar da kallo yadda ta sakar masa maganganu cikin kwanciyar mind, sosai maganganun suka daki zuciyarsa kwafa yayi yace "dani kike zancen".
Tana aje wayar ta kalli Shamcy tace" kiji me yace fad'a besty, a hakane zakice zamuyi zaman lafeeya?" Siddiqa ta fad'a ranta na suya .
Smiling Shamcy tayi tace " besty kenan! Wannan ai duk love fight ne kukeyi, kuma son juna amma kun kasa yadda da hakan".
Harara ta watsa mata sannan ta mike ta shige toilet.
_wannan kenan_
โ๐ป
๐ ~Meryerm Abdool~ ๐
[5/20, 6:22 PM] ๐Meryerm Abdool๐: ๐๐๐๐
๐๐๐๐ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐๐ป๐๐๐๐
๐๐๐๐
( _Based on love story_ )
```Written```
```By```
๐ *Meryerm Abdool* ๐
ยฎ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_*
( *P.M.L* )
*hakkokin musulmi ga dan uwansa musulmi guda shida ne:- 1,kayi masa sallama idan ka iskeshi, 2. Idan ya rokeka ka bashi idan kanada, 3. Idan ya nemi taimakonka ka taimaka masa, 4. Idan yai atshawa ya godewa Allah ka masa Addu'a, 5. Idan bashida lafia kaje ka duba shi, 5. Idan ya mutu kaje masa mak'abarta ga maza.*
Allah yasa mudace.๐๐ป
*Page* 42&43
Da alwala ta fito dake lokacin zuhr yayi, kallonta Shamcy tayi ta bushe da daria, banza tayi da ita ta tada sallar ta, saida ta kammala tayi Addu'a sannan ta kalli Shamcy tace.
"To b'ulalliya zoki fidda min dariyan da kikemin a jikina" ta fad'a tana tsuke fuska.
Darawa Shamcy ta k'arayi sannan tace " dad'inta dai kema kina b'ulewar, sannan kuma ai dole in dara saboda taku salon soyayya daban ce wato madness and blindness love kenan" ta k'arasa fad'a tana ci gaba da daria.
Ta k'ulu iya cikin bacin rai tace "kefa wani lokacin matsala ne dake, kina jin meyake fad'a amma kin nace akan wai soyayya muke, a ina kikaga anaso haka?"
Still dariya take tace "gashi na gani gunku, yarinya gwanda ki yadda dan na ganoku tsaf".
Ganin idan ta biyeta ranta ne zaici gaba da b'aci a banza yasa ta kyaleta, kwantawa kan bed ta lumshe ido kaman mai bacci, ganin haka yasa Shamcy mik'ewa tana fad'in " love bird an shiga duniyar kenan" sannan ta shige toilet don yin wanka.
**************
Zaune yake yana buga k'asa yana wani rubutu wanda baida kan gado, sanye yake da malun-malun yasha rawani k'ara buga k'asa yayi sannan ya kalli gefen hagunsa, Hajia Bara zaune kaman mai neman gafara, yace.
"Hajia na duba dakyau naga akwai aure a tsakaninsu amma fa..." Da sauri ta katse shi da cewa "Ala gafarta malam da wata matsala ne?"
"Eh to...amma bari nayi istikhara na gani"
Wata sharb'eb'iyar tasbaha ya janyo wacce tsayinta zaiyi na yaro d'an shekara 5, ta katako, haka ya fara janta yana fad'in " Allahu, Muhammadu,fir'auna, shedan" haka ya ringa yi har yakai kan liman ya fad'a ga Fir'auna.
Dagowa yayi ya kalleta yace "har yanzu Abu daya yake bani, wato indai aure to za'ayi amma kuma duhu ne zagaye da ita".
Zaro ido tayi ta d'ora hannu aka tace " na shige su ni Bara, duhu malam tona meye?"
"Kada ki damu zamuyi maganin abin komai zai wuce zatayi aure kuma zata mallaki miji sai yadda tayi dashi, ga wannan duk yadda za'ayi ya tsallakashi" ya fad'a yana mik'a mata kullin magani.
Karb'a tayi ta saka a jaka tace "nagode malam Allah ya biyaka da aljanna, malam nawane kudin aiki?"
Murmushi yayi yana hango wauta irin tata cikin ransa yana fad'in mahaukaciyar banza malamin Allah ne zai tsaya anan, sannan yace a fili "ba komai Hajia ayi ki bada au sadaka ce ba zabi" hannu ta saka a jaka ta ciro bandir na 'yan 1000 guda uku kenan sun kama 300k ta aje mishi.
Da murmushi yace "to Allah ya karb'a" tace "ameen malam ta rataya jakanta ta mik'e ta tayi masa sallama, da dariyar zuci ya bita yana tsine mata (haba 'yar uwa da boka da malamin duba duka matsayin su d'aya a gurin Allah su duka mushikaine, duk Wanda yace yasan gaibu to lallai yayi fito na fito da Allah saboda sanin gaibu sai lillahi, duk Wanda yaje gurin boka kuma ya gurin boka kuma ya yadda da zancen sa to hak'ik'a ya kafirta, kuma istikhara ba'ayima mutum saidai yayi abinshi yadda musulunci ya tanadar Allah yasa mudace yasa mifi k'arfin zukatan mu ya karema imaninmu ameen).
Bayan ta koma gida a parlor ta samu Fauziya tare da k'awayenta Lady, da Shakira kowacce tayi d'ai-d'ai akan seat cikin shigar banza music na tashi a falon sai dum kakeji ko sallamanta basu ji ba, ganin ta kawai sukayi a tsakiyan falon.
Kallonsu tayi da murmushi tace " 'ya'yan Mami sai hutawa kukeyi" kallonta sukayi sukace eh sannan kowa sukaci gaba da abinda sukeyi ba niyyan gaisuwa balle sannu da hanya.
Har ta kama hanyar bedroom sanin ba biyota Fauziya zatayi ba yasa ta kiranta ta d'auki lokaci sannan tazo tana turo baki alaman an katse mata jindad'i zama tayi gefenta ta dora kanta bisa wuyanta tace "Mami meye hala" ta fad'a cikin shagwab'a.
Zafo kanta tayi sannan tace "Dota burinki ya kusa cika zaki mallaki Haiydar ki juyasa kamar waina, sai yadda kikayi dashi" wani irin tsalle tayi ta rungume uwar ta bata peck tace.
"Wow! Mami I so much love u u'r d best mother in d world" itama rungume ta tayi tace "any thing u wish dota u most 2 get it at any circumstances".
Sannan ta d'agota tace " saidai hanzari ba gudu ya zakiyi da matarsa dan Malam yace dole zasuyi aure".
"Manta da wannan maganin ta zanyi" amma cikin ranta fad'i tace ai duka zan had'a na Aure su dan tayimin babyn...
Mami ta dawo da ita ta hanyar cewa zaki iya kuwa Dota?"
Murmushi tayi tace zan iya Mami, am barin je gurinsu Lady kada su k'osa da jirana" ta fice ba tare da jiran ansa ba.
Girgiza kai kawai tayi tana murmushi tabi 'yar da kallo.
Koda ta fita basa parlon dak'inta ta samesu suna romancing juna tsaki ta daka Wanda ya dawo dasu tace "matsiyata kawai jarababbu daga fita har kun wani zuwa nan saboda rashin hak'uri".
Hak'uri suka fara bata don kada ta korasu ba tare data basu wani abun ba, cewa tayi " is ok! Just guest what?"
Kallonta sukayi da sauri sukace menene??
Tace "Aure zanyi very soon".
Zaro ido sukayi a tare sukace Aure!!.
" yes of course"
"Shikenan kinbar harkar kenan" cewar Lady.
Wata shu'umar dariya tayi tace "ko ance miki kogi yayi gobara kya yadda, zanyi kawai saboda tsaro" ta fad'a tana kashe ido.
Sukace yanzu mukaji zance daga nan suka fad'a tafkin masha'arsu, Allah ya kiyashemu ameen.
Biki sai matsuwa yake anata shirye-shirye, Mommy ce ta kira Haiydar tace "Son banji me kuke tsarawa bane kaida taka matar, gasu Zarah shiri kawai suke"
Sosa kai yayi yace "Mommy ba wani abune za'ayi ba kawai waleema ce zasuyi ta mata sai dinner dasu Saleem suka had'a bayan kawo amarya" Sam bayason Mommy ta fahimci wani Abu shiyasa yace mata hanya2 amma ba wani shiri dayakeyi hasalima Saleem ne keyin komai tare da sauran friends d'insu.
Itama Siddiqa tana b'angaren Shamcy ce keyin komai dake tun zuwanda tayi bata koma ba dan da iyayen ta sukazo gaisuwa cewa sukayi ta zauna tana d'ebema Siddiqa k'ewa, shine da aka saka bikin kusa sukace ta zauna har ayi bikin, wasu k'awayenta na nesa duk sun k'ara dawo wa, haka 'yan uwa da abokan Arziki suma duk sun sake dawowa.
Su Aunty da Mama dasu Aunty Jameela da Ramlah sun dage sai shiri ake hadda su Rufee da Jabir ba'a barsu baya ba, jakadiya ma an sake sabon shiri anata gyara Amarya ciki da waje, daurewa take sosai gurin boye rashin son Auren Shamcy ce da Auntys d'inta sukasan matsalarta suma sun daukeshi a matsayin soyayyar boye sukeyi ba tare da sun sani musamman da yake sun San labarin yadda ya faro.
Yakan kirata a waya su dank'arawa juna bak'ak'en maganganu son ransu.
_to fa koya za'ayi wannan Auren oho!_ nima ban Sani ba ๐ค
_pls kuyi manage da wannan munata bukukuwa daga wannan sai wannan_ love u fans ๐๐
โ๐ป
๐ Meryerm Abdool ๐
[5/20, 6:22 PM] ๐Meryerm Abdool๐: ๐๐๐๐
๐๐๐๐ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐๐ป๐๐๐๐
๐๐๐๐
( _Based on love story_ )
*Written*
*By*
๐Meryerm Abdool๐
ยฉ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_*
( *P.M.L* )
```ALLAH MADAUKAKIN SARKI YANA CEWA:- (FASBIR SABRAN JAMIL, KUMA YANA CEWA:- INNALAHAA MA'ASSABIRIN) da dai gurare da dama da yayi magana akan *HAK'URI* Allah yabamu hak'uri mai amfani ameen```
*Page* 46&47
Saida ta tabbatar ya fice sannan ta mik'e ta shiga toilet tayi brush don da gaske bacci take zuwan sa ne ya tasheta, ledar ta d'akko ta bud'e kaji ne da suka sha kayan lambu sai tashin k'amshi suke tuni suka tono mata yunwa don rabonta da Aminci tun Karin safe.
Plate ta d'auko da cup wad'anda ke saman k'aramin fridge dake cikin d'akin, juyewa tayi sannan ta hau ci, ko rabin d'aya bataci taji ta k'oshi, Hollandia ta tsiyaya a cup tasha sannan ta saka saura a fridge, ta shiga toilet ta sake brush sannan ta sake Addu'a bacci tabi gadonta.
Kwance yake kan gado, surar ta kawai ke masa yawo a kwakwalwa duk da rufe take da blanket kanta ne kawai waje, amma yanayin yadda kananun kitson ta suka rufe gefen fuskarta ya bashi sha'awa duk da gashin bamai tsawo bane can ba dan iyakarshi wuyanta, amma kam bakine sosai ga santsi dan har farkon ya fara warwarewa, sai gaban kan daya kwanta luf, ga wani saje a gefen fuskarta.
Tsaki yaja sannan yace "ina bata time dina gurin tunanin wannan abar ( ni kuma nace kodai-kodai....ganin yanaso yajiyoni yasa na kama bakina don ci gaba da d'auko muku rahoto) lol.
Wayansa ya dauko ya danna kira ring 2 aka d'aga " Ya Haiydar yadai?" Saida ya karak'e yangarsa sannan yace " bakiyi bacci ba?".
Nisawa Fuu fashion tayi sannan tace "tunaninka ne ya hanani bacci, gobe sammako zanyo na dawo Bk don na ganka" dake da ita akaje kai Zarah.
"Ki ganni na miki me? Nifa rawar kannan naki ne banaso, nadai gayamiki ki bari sai nan gaba za'ayi maganar, so keep d secret" sannan ya tsinke wayar.
Wani shu'umin murmushi Fuu tayi sannan tace " Hmm Haiydar ka gama jiji da kanka kazo hannu, billahillazi saika rena kanka muje zuwa dai" ta fad'a tana ci gaba da les chat nata da abokan yinta nan dai bacci yayi gaba da ita ba maganan Addu'a.
Da asbah yana tashi saida yayi wanka sannan yayi alwala, kwankasa mata kofa yayi sannan ya wuce, dama ta tashi dake ta Saba tun gida, tab'e baki tayi sannan tace " Ashe yana sallah a jam'i" ta mik'e ta fad'a toilet.
Saida ta gama Azkar tana da karatun qur-an kaman yadda ta saba sannan ta fito taga tsarin gidan da kyau, tsarin ya burgeta sosai sai sakama iyayen ta Albarka take dan gaskia sunyi k'ok'ari ba kad'an ba, daga k'arshe ta dire kitchen.
Ruwan zafi ta tafasa wadda sukaji ginger da glove sai k'amshi ke tashi sannan ta fere Irish ta soya ta kuma soya kwai ta juye a k'ara min plastic takai dinning table ta jera.
D'aki ta koma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 16