Share this page
ne gida 5 designers, haka Ramla taita tagawa tana sanya Albarka, haka suka wuni a gidan Ramla na kara bata shawarwari ba ita tabar gidan ba sai bayan magrib Anas ya sauketa har bakin hostel ya kaita,tai masa godia sannan ta shige ciki. Sanda ta shiga ta isko Shamcy tayi dai2 kan bed handout hannunta tana karantawa da sallama ta shiga, ansawa Shamcy tayi mata sannu da dawowa tare da tambyan Aunty Ramlah , ta gayamata suna lafia sannan ta tambayi bangarensu kawunta da taje gurinsu . Cewa Shamcy tayi " ki bari k'awai besty kawu Rigima yakeji wai na koma gidansa da zama saboda yanaso mu saba da Bilya d'ansa wai aimana Auren zumunci kiji fah" Daria Siddiqa tayi saboda tasan halin kawun na Shamcy sarai mugun kwadayi ne dashi Shima ya hanama Shamcy zama gurinsa,tace "tome kika masa?" kwafa Shamcy tayi snn tace " ki bari harki gama daria mana" "Ohh! Sowie besty " Siddiqa ta fada,Snn Shamcy tace "aini da imani yaimin yawa cewa kawai nayi to ai kawu basai na dawo nan ba indan wannan ne, shime fah ya ringa fada inda yake shiga banan yace fita ba, hadda cewa wai duk momy ce ta dauremin nake musu rashin kunya, nidai hankuri kawai na bashi na dawowata" Daria sosai Siddiqa take mata snn ta kama hsnyar toilet tana fadin "aiko besty da kin bari munsha biki" dake dsma ta tube shigewa toilet tayi. Shamcy cewa tayi "ai dole kyace haka saboda kinji keta, ke ki soshi mana in gaske ne (da yake yaron Sam bai natsu ba) Siddiqa bayan ta fito daga wanka ta shirya kan bed ta haye kusa da Shamcy ta zauna tace. " Besty nimafa kinsan da naje gidan ya Ralmah meya faru, ina wannan gayen daya kawomu ranar da aka kawo Amarya..." Nan dai ta bata labarin komai. Cewa Shamcy tayi" haba gaske yai ta kallonki rnarda ya kawomu ashe ya saka S da O,Amma fa gayen ya hadu besty, kuma kince ya Anas yace baida matsala, sai dai kama kince yayan D one saiya kenan" Smiling tayi kana yace "kodan na maidashi hankali zanso yayansa" _tofah_ πŸ€” ✍🏻 πŸ’„ ~Meryerm Abdool~ πŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Base on love story_ ) *Written* *by* πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *P.W.F* *R.I.P. ABDUL-KADIR MAHMUD D/DAJI, WE LOVE U FRIEND/DADY BUT ALLAH LOVE D MOST, MAY ALLAH (S.W.T) MAKE JANNAH UR FINAL HOME. MISS U PAPA😭😭😭😭😭😭😭😭😭* *Page* 25&26 'Murmushi Shamcy tayi tace" Hmmm! Besty nifa gani nake keda D one akwai wata a kasa. Bude baki tayi za'ayi magana....sai k'aramar wayanta ta fara tsuwwan neman agaji, d'auka tayi ta duba mai k'iran nata murmushi k'awai tai bata d'aga ba har ta tsink'e, wani kiran ne ya sake shigowa saida ya tsink'ewa sannan ta d'aga, " _Amincin Allah ya tabbata a gareki sarauniyar mata Maryama_ Fuskarta d'auke da murmushi ta ansa da cewa " _kaima Aminci ya tabbata gareka, tare da d'aukacin musulmi"_ Wani irin shock yaji, sosai muryarta ta ratsasa, cewa yayi " _ina fatar kin wuni lfy, kuma kina cikin nishad'i tare da tunanina kaman yadda nake naki"_ "lfy qlau" ta fada a tak'aice. Dama yasan ansan ba zata wuce hakan ba, a haka yaita zanta da hira tana ansawa da um aa sannan ya ringa gayamata irin sonda yake mata, haka dai sukayi hiran har ta d'an d'au lokaci kafin yai mata sallama. Tana gama wayan ta juwo ga Shamcy ta maida hank'alinta kan handout d'inta tace" Besty me ma kikace d'azun"? "Uhum ya wuce kuma ai " Shamcy ta fad'a ba tare da ta d'ago ba. Tab'e baki tayi sannan tace " kyaji dashi, na wani zo na biye miki kina jacking ni kuma ko oho!" Ta fad'a tana janyo bag d'inta ta ciro handout. Daria ma taba Shamcy, darawa tayi tace "lallai besty kinje kina shan love sannan kice wai kin biyemin, sannan kuma wake gasan k'arafe irinki" kwantawa k'awai tayi ta juya mata baya..... ** *** ** *On monday*........ Siddiqa da Shamcy ne tsaye bakin hall fitowarsu kenan daga exam, Sanye take da Arabian gown black tayi rolling da kashka White book ne rungume a k'irjinta, da Alama exam din tayi sweet dan sai smiling takeyi suna d'an hira da Shamcy, phone d'inta ne tayi ring cirowa tayi daga post d'inta ta daga da sallama, Umar ne yayi mata barka da fitowa daga exam, en kwana kinnan kullum yakan kirata kusan sau hudu a rana sannan ga dinbin text na love da best wishes na exams, yanzu kam ta saki jiki sukanyi fira sosai kaman dama can sun saba, saidai har yanxu bata bashi amsarshi ba tana jan class, Amma ta riga ta gama yadda da sonsa saboda koba komai yana da kulawa sosai kuma ga sauk'in kai a gaskia yanada saurin shiga rai. Bayan ta gama wayar tace ma Shamcy "Besty me mukema tsayi anan? Nifa tsayuwan ya isheni" ta fada tana da nuna kosawa. Cewa Shamcy tayi " kinga Ameera tak'i ta fito na amshi wannan handout d'in da zamuyi anjima, ta ansa wai zatayi copy, amma mu k'arasa can gun kafin ta fito" ta fada tana nuna gurin wasu bench dake cikin wasu Shadow. K'arasawa sukayi suka zauna kan bench d'in, zaman su ba d'adewa Haiydar ya wuce ta gabansu da motansa Wanda Sam shi bai gansu ba, Shamcy ce ta fara ganinsa tace " gafa lil dinku nan ya wuce besty" ta fada tana k'unshe daria. "Imma kin fad'a da gatse ne kike wani k'unshe baki ke kika sani, amma abinda kika fad'a hakan yake" Siddiqa ta fada tana kallon cikin idonta. Murmushi kawai Shamcy tayi ba tare da tace komai ba..... 3 days later........ Siddiqa ce kwance kan bed tana waya da Umar da yake sai marece zasuyi exam nasu shiyasa bata fita ba, suna wayanne yake gayamata yau zasuje ma Teema don a yau suke graduation, zasuje gurin prize and giving day nasu, tace "kace dai zarah yau gata ga mommy, gaskia nayi murna Allah ya dawo daku lafia, ina tayata murna ka gayamata pls?" "Uhum kindai k'i gayamin matsayina a zucianki, kinga da kin amince da yanzu su mommy sunyi, amma dai ba komai zan gayamata" Umar ya fada, ya matsu ta gayamai wane hukunci ta yanke, saidai sam bayaso ya takurata ko yanzu ba baiso ya fad'a ba zucianshi ne ke azalzalanshi. Cewa tayi "kada ka damu ya Umar komai ya kusa zuwa k'arshe zakajini inshaa Allah" "Ba komai Siddiqa mai gaskia keep waiting till u prompt it love u d most" "nagode Ya Umar" ta fada sannan sukayi sallama.... Taron graduation din nasu Fateema yayi kyau sosai inda ta anshi gift masu dinbin yawa saboda ba laifi Zarah akwai kai, sunyi pics da friend d'inta da family nasu sosai, haka taron ya tashi kowa ya kama gabansa cike da k'ewar juna. 4:30pm Haiydar ya dawo daga skull fitowansa kenan daga exam, part d'insa ya wuce yayi fresh up sannan yaje part d'in momy. Da sallama ya shiga, duk suna falo sai fira akeyi an saka Zarah tsakiya sai labarin Skull take basu, Dady ne kawai bayanan dake yayi tafia. Shigewa yayi yana fad'in "oyoyo my Zarah welcome home my cute Zarah" ya fad'a yana zama kusa da Zaran, turo baki tayi tana juya masa baya . Juyowa da ita yayi gabansa yace " Haba cutie kema kinsan bazank'i zuwa graduation naki haka kawai ba exam ce ta hanani kiyi hakuri kinji" kara tura bakin tayi aiko me Hanan za'ayi inba daria ba sannan tace " Aunty Zarah keda ya Haiydar Allah Sam bakwa girma" ta k'arashe tana daria. Harara Zarah ta balla mata, Shi kuma Haiydar yace k' yale wancen mai kama da tsofin, duba kiga gifts d'inda na kawo maki" ya fada yana dakko wani set na jewelries masu shegen kyau ya saka mata a cinya, aiko nan take tai tsalle ta rungume shi, momy kam sai daria take musu, godia tayi masa sannan ta nuna masa phone d'in da Ya Umar ya bata a matsayin gift nashi iPhone5 mai kyau da ita. Haka suka hadu akai ta fira kowa sai nishadi yake..... _Ni kuma nice happy family_ ☺ ✍🏻 πŸ’„ ~Meryerm Abdool~ πŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD,UWATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Base on love story_ ) *Written* *by* πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *P.W.F* *Page* 26&27 'A haka su Siddiqa sukayi ta zana exam nasu cikin kwanciyar hankali, a gefe d'aya kuma shak'uwace sosai ta shiga tsakaninta da Umar, wanda zuwa yanzu ta yardarma kanta Umar shine masoyi na gaskia gareta jira kawai take su k'arasa exam ta gayamin ta amince da soyayyarsa, a d'an zamanda tayi dashi ta fahimci mutun ne mai hak'uri ga tausayi da nuna tsantsar kulawa ga abinda ya keso ga uwa uba Addini to me ake nema ga miji bayansu? ( nace babu). *A week later....* 'Cike da farinciki suke saukowa daga step d'in hall d'inta suka rubuta exam d'insu ta k'arshe, Siddiqa ce ta ciro wayanta a bag nata nata tana kunnata text ne ya fara shigowa cikin wayanta daga Umar yana tayata murnan k'are exam nata lafia sannan yana matan fatan cinyesu gaba daya, murmushi kawai takeyi saboda taji dad'in text d'in. Shamcy tace" Ya Umar d'innan yana bala'in sonki besty, ya kamata kibashi ansa hakanan inba so kike ruwansa yahau ba, kuma kema basarwa kawai kikeyi amma da alama kin kamu" ta fada da zolaya. Bugu takai mata tai saurin gocewa tana daria cewa Siddiqa tayi "Allah besty zan kama kine kema" ta fad'a tana yi gaba, hostel sukaje already tun jiya sukayi parking da niyyan zasuje gidan Aunty Ramlah su kwana, gobe kowa ta kama garinta. Hostel sukaje da niyyan sai sunyi azhar zasuje gesse, suna zaune sunadan taba hiran exam d'inda sukayi ta k'arshe, wayan Shamcia ce tayi ringing tana dubawa taga number Dadyn ta dagawa tayi da sallama yake gayamata gashi ya shigo Bk ya fito daga Sokoto, dake ta gayamai yau zasu k'are exam shine ya biyo dan ya wuce da ita, baso hakan ba Amma ba yanda zatayi saboda zama da Siddiqa da tayi ta koyi halayenta taso sai goben tabi ta kasuwa. Haka suka kwaso kayanta a bakin hostel suka ganshi k'arasawa sukayi suka gaisa sannan suka saka kayan a booth, yace da Siddiqa ta kwaso nata kayan sai suyi dropping d'inta a gidan Ramlah cewa tayi su wuce kawai suda suka kan hanya kuma tafian da d'an nisa kada su maida Kansu baya ya Anas zaizo ya dauketa bayan Azhar, haka su Shamcy suka wuce suna ma juna hannu lallai zasuyi missing din juna. Kaman yadda ta fada kuwa haka akayi bayan sallan zuhr Ya Anas yazo ya d'auketa ya kaita gidanshi. Bayan sallah magrib ne Umar ya kirata yace mata ya iso dake dama tasan da zuwan already ta shirya hijab kawai ta saka tayima Aunty Ramlah sallama ta wuce, a harabar gida ta ganshi jingine a motan sa ya dora hannayensa a k'irjinsa, da sallama a bakinta ta isa, Ansawa yayi sannan yace. "Barka da fitowa Maryama sarauniyar mata" Murmushi tayi sannan ta gaidashi tace ya k'araso daga ciki, yace " Aa bafa dad'ewa zanyi ba dama Nazo ne naji yaushe zaki wuce goben saboda nazo na kaiki" Cewa tayi "Aa wlh kabarshi kawai zanbi motar haya" yayi2 da ita akan ta bari ya kaita ta dage akan zatabi ta haya dole ya barta yace amma shi zai kaita tasha goben, haka ta amince kada yaga ta cika ra'ayi da yawa, kiraye2 sallar isha aka fara yace zai wuce sai goben in yazo, sannan ya ciro wani dan k'aramin box ya bata, k'in karba tayi. Yace " gifts dinki ne fa na k'are exam kuma na gayamiki bana kyauta a mayar min so better take it, ko kinaso naji ba d'adi a raina"? Girgiza kai tayi sannan ta karba tayi mai godia, yaji d'adi a ransa saboda kowa nason idan yayi kyauta a nuna anji d'adi da kyautan, sallama sukayi ya wuce itama ta shiga daga ciki, Isko Ya Ramlah tayi tana gyara teburin cin abinci da abincin dare, tayata tayi suka k'arasa sannan ta nuna mata box d'inda ya bata rings d'in gold ne d'an karami mai shegen kyau baida wani ado a jikinsa amma kam ya hadu sosai sakawa tayi a yatsanta na tsakiya ya zauna daram kaman an auna, sai murmushi takeyi saboda zoben ya mata kyau. Ramlah ce tace "wannan fara'a haka babyn Aunty, Ashe dai Ya Umar ya iya zabe kenan" murmushi ta katayi sannan tace " kai Aunty Ramlah" itama Ramlah murmushin tayi sannan tace suje suyi isha kafin Ya Anas ya dawo suyi dinner, sallah sukayi suka zauna falo suna tab'a hira har Siddiqa tace gayamata Ya Umar yace shi zaiyi kaita tasha gobe in zata wuce. Ramlah cewa tayi "wannam sauri haka Siddiqa aina d'auka zaki zaunamin kona sati 2 ne kafin ki wuce" Cewa tayi" tab nikam tafia zanyi bakiji yadda nayi missing d'insu ba especially kiriniyar Rufee da Jabir" "Ko kin koma sune kadai abokan naki yanzu ba gashi bani ba Jameela suma su Abdul basu, ya Mubarak ma ya wuce Kd" cewar Ramlah. "Haka Aunty Aysha itama tace wai naxo Abuja na mata sati biyu kona koma gida baxanji dad'i ba duk gida ba kowa wai saisu Jabir, nace mata naji d'in Amma ba India zanje kuma ai Aunty nanan " Siddiqa ta fada. "Ai shikenan tunda kin dage sai kin je Allah ya kiyaye" Ramla tace, haka sukayi ta fira har Anas ya shigo sukayi dinner sannan suka dan zauna kallo zuwa 9:00 tai musu saida safe ta shige ciki. Kam kago ta kwanta ta kunna data ta fara chat nan take gayama Shamcy kyautar da Umar ya mata cewa Shamcy tayi " wannan ya Umar fah ya hado da yawa, wai sai yaushe zaki gayamasa kin Amince dashi nifa na karaga kaman nice shi ta sender mata da jar fuska" daria ta tura mata hadda hawaye sannan tace " aina fahimci kimma fushi matsuwa, to kwantar da hankalinki inshaa Allah gobe zanyi masa text bayan na shiga motan zuwa Argungu" "Yawwa kokefa er gari ysnxu naji zance" Shamcy ta turo mata, haka sukaci gaba da chat d'insu, Umar ma ya hau online ta kara yimin godia sannan ta nuna mai zoben ya mata kyau sosai, yace ba komai tunda zoben ya mata hakan ma ya isheshi jin dad'i, sai zuwa ten sannan sukayi sallama ta kashe data tai Addu'ar bacci sannan ta kira safeya. ** ** ** Ba ita tabar gidan Ramlah ba sai 3 shima saida tayi da gaske, so tayita riketa zuwa gobe, dakyar ta samu ta barta ta wuce, koda suka isa tasa motan saura mutum biyu ta cika biyan kudin yayi aka bata gaba ita kuma ta biyama na baya kaman yadda ta saba, saida motarsu ta tashi sannan ya wuce gida. Suna fita daga birnin kebbi ta janyo wayanta ta fara rubuta masa text kaman yadda tai Alk'awari. _"Assalamu Alaikum, Amince Allah ya tabbata a gareka ya ma'aboci hak'uri da mutumci, Ya Umar a yau nake sanarda kai na amince da kai a matsayin masoyi na gaskia saboda ka cancanci hakan, ka ha'da komai da ake nema ga d'a namiji kai abinso ne ka kowacce ya mace, a yau na baka makullin zuciya, na aminta dakai a matsayin zabin raina_" Yana kwance bisa kujera ya lumshe ido sai tunaninta yakeyi ysji karan jigowan text yana dubawa yaga nata ne da sauri ya bude,kusan suman fariciki yayi da yaga abinda ta rubuta a ciki. Kiranta yayi tana dagawa yace " dole nayi marking wannan ranar a matsayin ta na babbar rana agareni ranar da *sanyin idaniyata*ta amince da soyayyata nagode sosai Maryama Allah ya bani ikon rik'eko amana, zan kiraki anjima barin jema lil da daddad'an Albishir shine zai fara ji" kit ya kashe wayan. Murmushi tace aranta "lallai Haiydar nada matsayi sosai ga yayan nan nashi da wuya suyi magana mai tsawo bai sako lil ba, Amma kam wannan karon zakaje masa da Albishir d'inda zai rikitasa, kila ya gayamasa Abokiyar fadansa ce a skull, Oh! Idan Umar ya gano ta masa karya ya zatayi? Ba ansa, um komai da meye yaukam za'ayi ta k'are" duk cikin ranta take xancen. Da smiling ya shiga part d'in Haiydar zaune ya sameshi kan seeter ya jingina bayansa ga saman seat din ear piece,rungemeshi saboda murna yana cewa " lil am d winner " ware manyan idonsa yai akansa sannan ya cire ear piece d'in ya kalli yayan nasa yana smiling shima. K'ara cewa Umar yayi " I win d heart of d gal lil, yau ta amince da soyayyata ta amince na zamo masoyi agareta" Haiydar duk da baisan wacece ba Amma yaji tama gama rena musu wayo sai yanzu ta amince data amince da soyyyar yayansa, Amma daya fahimci yayan nasa na matuk'ar k'aunarta sai yayi cooling yana smiling yace. "Am so happy bros 2 hear, ina tayaka murna Allah yasa matarka ce" "Ameen lil, Damaa nace Kaine mutum na farko dazan fara fad'ama kuma zan fara nunawa pic nata" ya fad'a ya mika masa wayansa. Dask'arewa yayi saboda tozali da yayi da fuskar Siddiqa tana murmushi, Umar na gayamishi sunanta da course nata Amma ina Sam baiji ba, har seda ya tab'oshi sannan ya firgigit yai saurin saisaita ksnsa kada ya ganoshi. Duk da haka yaso ya ganosa amma saiya basar yace " koka Santa ne "?. Cewa yayi " no just I seem like na taba gsninta a skull"k'irk'iro murmushi yayi yace" ina tayaka murna kyakyawa da ita" Shima Umar d'in murmushi yayi "yace nagode, sannan yace kaga kuwa munyi sa'a Dady na gida tashi zakaji muje ai masu bayani don nikam so nake ayi komai cikin lokaci nima dai na shiga daka ciki hakanan" Ji yayi kaman yayi ihu amma saiya danne yace " let me fresh up, vcos dawowa na kenan daga skull" Haiydar ya fada yana mik'ewa. "OK" Umar ya fada yana janyo wayarsa domin kiran gimbiyar tasa.... Duk jikonsa ya mutu a sukwane yaja k'afarsa ya fara taka stairs d'in.... _kuyi manage da wannan fans yau da mura da ciwon kai na wuni_ 😀😫😰 ✍🏻 πŸ’„ Meryerm Abdool πŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Base on love story_ ) *Written* *by* πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *PERFECT WRITERS FORUM* ~Nagode sosai da Addu'o'inku, am getting better now😊😊 love u friends~ ❀❀ *Page* 28&29 Bayan shigarsa d'akin zaune yayi kan bed ya dafe kansa da duka hannayensa saboda wani irin sara yake masa, sai kuma ya mike zunbur kaman wanda aka tsikara ya ringa safa da marwa a d'akin, hannunsa ya dunk'ule ya nushi iska yace. "Damn u! Siddiqa meyasa kika shigo rayuwan yayana? meyasa kikeso zama d'aya daga cikin familyna? meyasa kika batamin plan dina akanki"? sai sambatu yake shi kad'ai ba Wanda zai ansa masa tambayoyinsa. Ganin ba ansa yasakashi shigewa toilet yana mai addu'ar Allah yasa kar Dady ya amince da Auren saboda yasan da Dady yace Aa to dole Ya Umar ya hak'ura da ita. Da sauri2 ya shirya saboda gani yace kaman ma Dady yace bai amince, haka imagination d'insa ya basa, hadda wani murmusawa, saukowa yayi ya samu Umar sannan suka dunguma zuwa part d'in iyayen nasu. Koda suka shiga falon Hanan ta baje kan carpet tana Homework yayin Zarah ke kwance kan kujera tana chat, dagowa tayi ta gaidasu bayan ta ansa sallamarsu, Hanan kam tuni taje ta mak'ale ya Umar tana zuba masa surutu shi kuma yana biye mata, zama sukayi sannan Umar yace "Dady da Mommy fah?" "Yanzun Mommy ta shiga kitchen Dady kuma yana Samansa" Cewar Zarah. Harara Haiydar ya zabga mata yace " Kina kwance sai aikin chat amma kinbar Mommy da shiga kitchen.... Katseshi tayi tace " Aa wlh Ya Haiydar nima yanxun na fito da ciki taje ta dubane" Shiru yayi ya kyaleta yayin da Umar yace "jeki duba Dady kice gamu falo" mik'ewa tayi ta haye sama. Dama sun saba hakan, idan sukaje falon basu samu iyayensu ba, zasu iskosu har d'aki suce sunzo ayi fira, kusan tare suka shigo falon Mommy da Dady da Zarah sukayi aka dasa fira kaman yadda suka saba kiran la'asar ya tadasu sukaje suka gabatar. Bayan sun dawone Haiydar ke cewa "Dady magana muzo da ita fah!" Cewa Dady yayi " Aa to shine kukak'i fada tun tazun, naga alamun magana a bakinku kyaleku kawai nayi" ya k'arasa maganan da murmushi. Saida yayi Addu'ar Allah yasa Dady yaki amincewa sannan yadan shafo k'eyarsa yace" um dama bros ne ya samu matar da yakeso kuma har ta amince masa" "Kai mashaa Allahu" Dady ya fada. Itama mommy cewa "madallah da wannan zancen er inace halan?" Itama Zarah tsalle ta daka sai gaban Umar tace" Da gaske Yaya" Hanan kuwa cewa tayi " yee! nima zan samu aunty" sai rawa tace kwasa haka falon ya rude da hayaniyar su. Dady ne yayi gyaran murya sannan yace" ina jinka Haiydar " gyara zama Haiydar yayi yace" kanwar matar Ya Anas ce Abokin Bros" "Toh madallah, amma ai bansan Anas din waya aura ba kasan ban samu halartar Auren ba ranar munyi meeting da governor" Dady ya fad'a yana kallonsu. K'ara sunkuyarda kai Umar yayi yace " um eh Dady 'yar gidan sarkin kabin Argungu ce" Tashi tsaye Dady yayi yace "Allahu akbar! Allah mai iko dama shi Anas 'yar muhammadu ya aura, lallai mun watsar da zumuncin mu, gashi Allah cikin ikonsa yara zasu dawo mana dashi" ya fad'a yana fad'ad'a murmushin fuskarsa. Kallonsa sukayi su duka da alaman tambaya a fuskokinsu banda Mommy da itama murmushin ne a fuskarta. Zama yayi sannan yace " Sarki Muhammad abokina ne tare mukayi secondary school a *Nagari collage* sannan muka wuce ABU Zaria tare, Abotarmu ta wuce abota har takai aminta har mukayi Aure muna zumuncinmu nakan kai mommy ku Argungu gidansa shima yana kawo nashi iyalan gurinmu zuwanmu na k'arshe gidansa, lokacin da akayi masa nadin sarauta ya zama sarki mukaje tayashi murna lokacin Umar na 9 Haiydar kuma yana biyar ita kuma Zarah ba'a haifeta ba, shine zuwana na k'arshe gidansa muka wuce malesia inda nayi Masters dina da PHD". Ya kara da cewa " mukanyi waya dashi time 2 time da muke can bayan dawowarmu yazo ya yimin murnar dawowa, nace masa zanzo inshaa Allah to bansamu zuwa ba gaskia daga haka zumuncin namu yaita ja da baya tun muna waya har muka rasa number juna, ni banjeba shima baizo ba gashi dama matan namu basu saba da juna ba, sai gashi Allah ya dawo mana da zumuncinmu ta wannan hanya" Dady ya fada fuskarsa tab da farinciki. "Ai Dady Anas d'an kanwar sarkin ne" Umar ya fada. "Tabbas anyi haka Umar ya taba gayamin akwai kanwarsa dake aure a garinnan amma kuma sai ban k'arfafa na Santa ba, Ashe sai duk ana tare ba'a Sani ba" cewar dady. Momy ce tace" haka fah almura ke tafia cikin ikon Allah, ka duba kaga Alhaji lokacin da aka manta da wani zumunci lokacin Allah ya dawo mana dashi ai yanzu kam dole mu rika da gaske. Haiydar kam Sam labarin baiyi masa dad'i ba saboda ba haka yaso ba amma kuma ba yadda zaiyi dole yabi da murmushin yak'e. Cewa Dady yayi " yanzu tafia dole ta kamamu zuwa Argungu sai a shirya zuwa weekend muje, nasan zuwa lokacin kun gama exam" ya fada yana kallon Haiydar. "Eh" ya fada a tak'aice. Haka dady yaci gaba da basu labarin zamansu da Babansu Siddiqa abin gwanin sha'awa sai daria sukeyi, su Zarah hadda tuntsirawa. ** **

Chapter 5 of 16