Share this page
"kayi ka gama indai shan K'amshi ne naga Son ban tsorata" namma dariya aka saka Siddiqa hadda mishi galo, shi kuma Hararanta yayi tare da alaman zakizo hannu. Sai dare suka koma gida bayan Dady ya dawo shima anyi dashi. _Happy family_ iiooii "". "". Haj, Bara ce zaune tana kallon NTA harta zata tashi sai taga ana cigiyar iyayen wata yarinya, "subhanallah" itace Kalmar da ta fito bakinta jin anyi mentioned sunan 'yarta tilo data cire rai da sake ganinta, ga photonta an nuno, badan ita mahaifiyarta bace to da tabbas ba zata ganeta ba, tayi baki ta rame kaman kwarangal (dama ya lafiyar kuwa balle tayi zawo) lolzz. i Da kuma ta shiga part d'in Momy tayi sa'a ta samu Dady nanan shima, tashi sukayi a tare suna tambyanta lafia meya faru take kuka? Baki na rawa ta shiga nuna musu TV da hannunta tace "yan...zu aka ..yi..cigiyar iyayen Fauziya a NTA, wallahi na ganta da idona.." Ta fad'a tana rushewa daioo kuka. Cikin sa'a kuwa Momy na kamo tashar sai gashi ana cigiyar. ioooiiii A ranar Dady ya sama musu flight sukabi zuwa Abuja, shida momy da Mami daooi malam Haruna, dan duk dashi ake nemanta dayin addu'a Allah ya bayyana ta. Ba Wanda bai zubario mata da hawaye, ganin halinda take ciki ko magana dakyar takeyi i tanayi tari na sarketa, gafararsu take nema tare da nuna tsantsar nadamarta, amma sam basajin me take fad'a, rungume ta Haj, Bara tayi tana mai suspending kanta akan cutar da 'yarta, hospital suka kaita aka bata first aid, ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba jin ciwon da take tare dashi wato cancer ta private part, gurin duk ya lalace ta bud'e ko had'a kafafu bata iyayi, abin kam ba kyan gani gwanin tausayi, haka akadan bata magunguna zasu rage mata rad'ad'in ciwo. Washe gari suka biyo flight suka dawo, tun suna flight take tambayan Siddiqa da Haiydar so kawai take ta gansu ta nemi yafiyarsu, suna isowa Momy ta kira Haiydar tace yazo shida matarshi yanzu tana nemansu. Tafe suke gabansu na darr saboda basusan dalilin kiran ba. Suna shiga a parlour suka taradda Dady, Momy, Mami, Mal Haruna, Hanan sai wata mai jinya wacce basu nan kowa cece ba, fuskar kowa suka kallah ba walwala, cikin alaman tambaya ya bud'e zaiyi magana...yaji mai ciwon tace. "Ya Haiydar baka ganeni ba ko?" Tuni idon Siddiqa ya kawo k'walla saboda girmama Allah da tsoron duniya, tuni ta gane muryan, lallai duniya abin tsoro ce, shi kan shi jin muryan yasa ya kalleta da kyau tabbas itace, "tome ya sameta haka" ya d'auka a zuci ya fad'a, jin tace. "Sakayya ce Yaya tun a duniya, bayan ka jefomu waye" nan ta gayamusu shawarar da Halidubu ta bata da yadda ta kira Mami ta zugota, taci gaba da cewa. "Mun sauka a birnin London lafia, inda muka bud'e sabon shafin shakatawa muda turawa, rayuwace ta 'yanci a namu gani, ba ruwan kowa da abinda kake yi, hakan yasa duniya tayi mana dad'i bama tunanin komai ga kudi mun Tara, aha muka yanke shawarar auren jinsi inda turawa masu jida dollars suka auremu, dama ibada ko anan saitayimin dad'i nakeyi, balle kuma gamu a k'asar yahudu, nama manta da musulunci rayuwa kawai akeyi ba alkibla. " kwatsam bayan shekaru sun tafi mun saba dasu, suma sun saba damu, sai ciwo ya kamani, koda akaje asibiti INA d'auke da cancer ta private part, kuma ta zama chronic, har ranar mutuwa saida likitan ya gayamusu, jin haka yasa d'auki Halidubu suka kaita itama ita kuma itama d same ciwon saidai ita nata hadda breast cancer, jin haka yasa suka tattarimu sai airport daga mu sai kayan jkinmu aka maidamu Nigeria, gamu a airport ba Wanda ya kula mu, har aka watse saimu kad'ai, ma'aikatan airport suka d'auke mu suka zubar a tasha, cikin dare Halihudu ta mutu saboda wahala da tsananin ciwo, gani rungume da gawa bamai kulani haka akazo sharan tasha aka wuce da gawarta bola, dan duk daukarsu mu arnane saboda yanayin shigarmu, haka naci gaba da rayuwa a tasha ina bara ina samu cin abinci, watarana idan ban samu ba haka bake kwana, tsawon wata na d'auka ina a tasha naga rayuwa nayi kuka nayi nadama, nasan menene duniya, anan Allah ya kawomin bawan Allah daya taimakamin yakaini NTA aka saka cigiyata bayan yaji labarin rayuwata ya girgiza da yaji, ya nunamin kuskure tare da nunamin har yanzu inada damar tuba ya runga koyamin kara2n musulunci da rayuwa na tsawon sati 1, daganan ya fad'a min zai wuce garinsu dama dan ci rani ne, kwana biyu tsakani sai kikazo" . Koda takai nan ta tsaya tace "to kunji abinda ya faru dani amma nayi mamaki ganin Mami anan gidan, ina Abbana? Meya faru?" Hawaye ke fita idon matan yayin da mazn zukatansu suka karye. Dak'ar Mami tace "dota komai ya faru dake nice sila saboda ban baki tarbiyarda ta dace da islama ba na nuna miki so na hauka Wanda a yanzu *nayi nadama* (Ayshat garkuwa) nima na tafka kuskure bayan tafiyarki a dalilinki" nan ta gayamata komai daya faru. Tana kuka tace "Abbana ya rasu ba tare da mun gana ba, bare na na nemi yafiyarsu, Allah ya jikan Abbana" ameen sukace, sannan Mami tace "air shima yana bukatar yafiyarki dan ya bada nashi gudummuwa gurin tashin lokacinki da bare ya baki tarbiya". " Bara'atu ayi hakuri a manta baya wannan lamarin kaddarace wacce ta riga fata, ayi afuwa a manta baya tunda Allah ya kaddari kun gane gaskia, shi kad'ai wata ni'imace a garemu, so bygone by bygone, Haiydar, Maryam a yafi juna kowa ya manta da baya" Dady ya fad'a. Nan dai akayiwa juna yafiya, tare da fatar samun lafiyar Fauziya, Hanan CE taje ta taho da 'yan makaranta, Fauziya tayi mamakin ganin 'ya'yansu gwqnin sha'awa kamar abata, tace a cikin ranta imana aure tayi da yanzu tanada mai mata addu'a, tayi turr da hali irin nata da nasu irin sa( Allah ya kiyashemu). Suma yaran sai tambayan wacece suke akace wata mamansu ce diyar kaka CE, Humaira tace "wannan ce diyar kaka, saidai mamarta" ganin tanda tadawo tsohuwa, Siddiqa zata daketa tace. "Aa ai da gaskiyarta" abin sai tausayi (hmm such is life). Koda sukaje gida cike da jimami Siddiqa tayi wani sukuku da ita, haka suka kwwntar da yaransu suka shafesu da addu'a sannan suka ja musu d'aki. Kwance take ta lafe a katifa, ya shigo cikin sleeping dress White, yace "common baby love, wai meye haka ne?" "Piyaa wallahi jikina yayi sanyi da yawa naji tsoron duniya". Murmushi yayi yace" hakane matata duniya abin tsoro ce, kinga dan ban *had'u dake* ba, da ban san halinda zan shiga ba" ya fad'a yana kashe mata ido. Dukan k'irjinsa tayi cikin shagwab'a tace "uh um be serious mana" mammata yayi a k'irjinsa yace. "Am serious" yace sannan ya rad'a mata a kunne "gara ma ki ware dan yau zan bama Salmana kani". Zaro ido tayi tace" piyaa bangama hutawa ba" cikin muryan tausayi. Ciccib'arta yayi kamar baby yace " tau bari kofa" wutsil wutsil ta kamayi da kafafunta, shi Kuma yana mata dariya, har suka shige d'akin sa....... _Allah yasa asamo mai sunan Dady_ 😁😝 ✍🏻 πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:35 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HADU'WATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Based on love story_ ) *Written* *By* πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* *P.M.L* ```Zanyi amfani da wannan damar wurin rokon gafarar duk Wanda na batawa Wanda na Sani da Wanda bansani ba, ina Neman afuwa, nidai Meryerm Abdool na yafewa kowa, Allah ya taramu a ladan watan Ramadan mai alfarma ameen``` πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ» πŸŒ™ _Allahumma baliklanah fi Sha'aban, waa balliglanah fi Ramadam, bi rahmatikah ya arhamar rahimeen_ πŸ‘πŸ» πŸ”š *Page* 74&75 A gurguje haka rayuwa tayi ta tafia yau farinciki gobe tsabanin haka, dama zaman duniya haka ya gada, abubuwa da dama sun faru. Rasuwar Fauziya bayan tsananin jinya da tasha, dan kuwa gaban ya k'ara lalacewa idan za'ayi mata har makota sai anjiyo ta saboda tsananin azabar da takeji a gurin, saidai kuma ta rasu tana mai mik'a wuya ga umarnin Allah dabin sunnar manzonsa, inda ake mata kyakkyawan zato. An sanya ranar auren Hanan da k'anin Siddiqa Abdullahi, dana Rufaida da Yayan Hanan Abubakar, dana Abdulrahman da K'anwar Shamcy Sa'adiya, dangin uku sun sarke sun koma 'yan uwa juna bana wasa ba, sai jiran lokacin biki. Jabir autan Aunty kuma ana turkey, birnin Istanbul inda yake karatun mass com, su Hanan suke nan Federal university Kalgo ita da Rufaida suna k'ara tun nursing, tana zaune gidan Dady. Amincin Siddiqa da Shamcy sai abin da yayi gaba, abin sai Sam barka, yanzu yaran Shamcy 3 da cikin na 4, ina Aunty Ramlah keda 4, Aunty Ayshat 3, zarah nada 2 da cikin 3, Siddiqa uwar a kwashe keda 4 da cikin na 5, dan oga D one ya cika aikinsa. Lolz Arzikin Haiydar ya fad'ad'a kamfaninsu yayi suna Sosai a kebbi, Saleem an tamfatsa gida inda suka tare da iya tsohuwa mai ran k'arfe. Haiydar yace Siddiqa ba zatayi aiki ba, haka ma Shamcy ya hana, amma sun basu jari mai kwari inda suka had'a da Aunty Ramlah suke kawo kaya daga Dubai. Yau tun yana office ya kirata yace ta shirya itada yaransa zasuje unguwa, hakan yasa suka shirya zaf gwanin sha'awa ita da yaranta, yana zuwa lunch kawai sukayi suka kama hanya, tafia ce mai dan nisa da yaran sukaga an kama hanyar Argungu sai murna suke suna fad'in zasuga mai martaba dasu Aunty da Mama, can guraren *Adamu Augie collage of education, permanent site* suka tsaya. Bakin wani gidan gona suka tsaya Wanda aka rubuta *Haiysid and their kids farm* kallon gurin Siddiqa tayi sannan ta kalleshi, zadaden murmushin nan nasa yayi mata yace. "Shine babban burinki, ni kuma banda abin roro sai farincikinki". " ya akayi ka sani Papan Huda?". "Nasan abinda yafi haka game dake, Momman Humaira". Tsananin farinciki baya misaltuwa saida yaran suka fita sannan ta rungume shi a k'irjinta tana cewa " ka cika min duniya mijina komai na rayuwa kayimin abinda na fad'a dama Wanda ban fad'a, mezanyi maka na nuna godia ta?" "Kinyimin komai a rayuwa Maryama, kinban yara kyawawa masu tarbiya kin soni, pls kici gaba da sona har karshen rayuwarki" ya fad'a yana k'ara matseta a k'irjinsa. "Inshaa Allah zan soka har numfashi na, na k'arshe, nima kayimin alfarma, koda ka kawomin abokiyar zama pls kada ka walaka'ntani" ta k'ara lumewa a k'irjinsa tanajin rad'ad'in kishinsa tun kafin ayi kishiyar. "Wayace maki zan k'ara aure baby love, idan kikaga nayi aure to kaddara tace haka, amma nikam banda wannan intention ke kad'anki kin wadaceni" sauke numfashi tayi. Sannan suka shiga ciki, Wanda tuni yaran sunga abin burgewa sunyi ciki sosai, part by part ne, tun daga poultry section, livestock section, fishery section, orchard section, guri ne mai girma, ciki ake hatching d'in fish ake ga incubator da ake harvesting chick, ga bee hive ana rearing bee, kai babban gidan gona ne babba, ga ma'aika ko'ina sai aiki suke, gurin yayi mata sosai sai gaisawa suke da ita suna sannu madam daya ke ya gayamusu zuwan mai gurin. Sai la'asar suka bar wurin suka isa Argungu nan sukayi Sallah aka gaggaisa sannan ta gayamusu abin alkhairi daya sameta, sunyi farinciki sosai tare da sanya alkhairi.. Su Dady ma sunyi farinciki dajin haka, Wanda zuwa yanzu yake a matsayin Senator, na kebbi South, likkafa taci gaba. Siddiqa ce ta shigo cikin d'akin sa, cikin wata half gown light purple mai igiyoyi a gaban ta tasha make up kamar wacce zata gasar kyau, ga d'an cikinta daya turo gwanin sha'awa, ta bayansa taje ta rungume sa tare da shafa kirjinsa da hannayenta yana tsaye gaban mirror yana Shafa turare. Turning d'inta gaban sa yayi tare da cewa "komai naki na daban ne, kyawunki daban ne, k'amshinki daban ne, *Had'uwata dake* ta daban ce" French kiss ta farayi masa cikin salo mai rikitarwa, ganin tsayi zai gagaresu yasa ya jata zuwa be tare da janye igiyoyin.........πŸ™ˆπŸ™‰πŸ™Š Pen up✏ *_TAMMAT BI HAMDILLAH_* _INA MIK'A GODIYATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA MAI KOWA MAI KOMAI DAYA NUNA KAMMALA WANNAN DA LITTAFIN NAWA MAI SUNA *HADU'WATA DAKE* INA ROKON ALLAH YASA INYI HUJJAH DA WANNAN LITTAFI KADA YAYI HUJJAH DANI, KUSKURE ALLAH YA YAFE, YA TARA A LADA DANI DAKU BAKI D'AYA._ *Allah ya dad'a tsira da amince ga Annabinmu, shugabanmu Muhammad (S.A.W) tare da sahabbansa da iyalansa da dukkan wadanda sukabi tafarkinsa har i zuwa ranar k'arshe.* TUKUICI GAREKU Iyalan gidan Dr late Abdulkadir gulma, family ba abin kaunata, kune farincikina, nice farincikinku, Allah yabar zumunci. JINJINA GAREKU Matan kirki masu masu nagartaπŸ’•group Ameenan juna group Maman ussey novels Jannart lameedo Sumyn bash novels Pure moment friend novels. Kuna daban ne gaiswarku daban ce, ameenan arziki kuna raina a kullum, Allah ya barmu tare, cikin k'auna, ya k'ara d'aukakamu mufi haka ameen. Pure moment of life writers. My mentors kun taka rawar gani a gareni. Maman ussey Abdul AAJ Fatyy Azland Ummi A'isha. Anan nace cewa saduwar alkhairi ina alfahari da duk wani ko wata masoyan *Had'uwata dake* ina sonku a duk inda kukeπŸ’˜ Ina muna fadan ganin Ramadan lafeeya da dacewa da ni'imar da ke cikinsa sa albatkarsa ameen. ~Taku har abada~ πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:35 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HADU'WATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Based on love story_ ) *Written* *By* πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* *P.M.L* ```2MORROW LEADERS, 2MORROW ELDERS πŸ’ž``` *Abdulmajid, Ramlah, Rufaida, Baffa, Kausar, Affan, Hanan, Amima, Yusuf, sultan, ihsan, iman, ilham, yusrah, khadija, Nana, Abdallah, Habiba, Ammar, Ameerah, Rahmah, Zainab, Ayshat, Ameer, Haleefa, Nusee, Twins, Salma and rest.* May Allah (S.W.T) Bless continue be wit u my kids, ILYMAM πŸ’˜ *Page* 70&71 Cikin yardar Allah sun sauka lafeeya kuma sun samu mutanen gida lafia sai murnan dawowan su akeyi, ganin Hajia Bara'atu ya basu mamaki, saida aka nutsu sannan akai musu bayanin abinda ya faru, sannan ta nemi yafiyarsu, sosai Siddiqa ta tausaya mata harda k'wallarta, sabanin Haiydar da bata wani bashi tausayi ba, yadai ansa daya yafe a tak'aice. Haj, Bara kuwa ganin Little lokaci d'aya ya shige rayuwarta taji tana matukar k'aunarsa, yayi girma abinsa tafia ko'ina zuwa yake idan ka ganshi zakace yayi 1β…› year, yanzu ko yake 9month. Sunje Argungu sun gaidasu da Kai musu tsarabarsu su Mama kuwa sai tsiya sukema Little wai broiler girman yayi yawa, Haiydar kuwa hadda tare mishi ba kunya. Shamcy tazo musu sannu da zuwa tana ganin Siddiqa ta hau mata tsiya, wai wannan fresh haka, kodai anyo tsaraban baby ne, tace tufemin yawunnan naki, yaushe na fito da labour room, dariya sukayi baki daya. Haiydar yanzu ya sake da Gwaggon tasa ganin yanda take nan yadda take kulawa da prince d'insa, dan inkanason ganin farinciki Haiydar to kaso little, yana matukar k'aunar d'ansa, ko Siddiqa tayi mishi abu tofa ya isheshi banbami da mita. Tunda suka dawo Siddiqa ke fama da zazzabin dare, idan dare yayi jikinta zafi yake sosai, ga yawan bacci da kyuya( kasala) da Haiydar yayi mata magana taje hospital sai cewa tayi canjin weather, zata ware, murmushi kawai yayi tare da cewa to. Yau kam zazzabin ya isheta ga tashin zuciya, saukinta ma little bamai damuwa bane saiya yini baisha Mama ba, komai ci yake, kuma yini yake part d'in Momy. Bayan sun gama breakfast Haiydar ya mik'e zai wuce, sai ganinta yayi sanye da hijab da jaka yace, "yau da wuri haka zaki fita?" Da yake suna services ne, da Edo state aka kaita Shamcy kuma Bayelsa, abin masu mulki cikin sauki aka mayarda su bk, inda suke gudanar da abinsu cikin kwanciyar mind. "Aa hospital zaka ajeni, zanga Dr ne" ta fad'a tare da kallon cikin idonsa. Dariya ce ta kono shi amma gudun yayi ya tono rigima yace "oh sowie baby kinga ina urgent ne, meeting zamuyi by 8, kije da car d'inki kawai, wai meyasa bakyason fita da ita?" "Uhum ni driving ne banaso ni kad'ai" ta fad'a cikin shagwab'a. "To yi hakuri kije yanzu kinji baby love" girgiza kai tayi cikin shagwab'a alaman ta amince, peck yayi mata sannan ya shiga motarsa ya wuce, yana sakawa a ransa yau za'a kwanto masa kura. Lolz Saida ta nemi rakiyar su Hanan, hadda little akaje, a mota ta barsu ta shiga ciki, gwajin farko aja gano ciki na wata 2, wowo Siddiqa kamar tasa ihu taji, Dr ganin yanayin ta ya canja ne tace "k'anwata ko bakya farinciki da cikin ne" murmushi yake ta mata tace "Aa ina dai mamakine naga shayarwa nake". " ayya ai faruwar hakan shi yafi komai sauk'i ma, ki kira Haiydar d'in sai a baku shawarar yanda kula da Born and unborn babyn naku gaba d'aya." "OK" tace a tak'aice sannan ta shiga kiransa da niyyan yazo a zubar da cikin bawai abasu shawara ba, dan Sam bata yadda da wata shawara ba, ganin tace d'anta mutuwa kawai zaiyi idan yasha ciki, 2 miss call tayi mishi bai daga ba. "Inaga basu fito da meeting d'in ba" ta fad'a ma Dr, d'in tare da mik'ewa tace "barin tafi inyaso saimu dawo anjima" tayi mata sallama ta fice. Ikon Allah ne kawai ya mai dasu gida dan gaba d'aya bata cikin hayyacinta, hankalinta ya Riga ya gama tashi, suna isa direct part d'insu ta wuce ta zube a parlour kaman kayan wanki tana neman possible solution, little kuwa sai wani mak'ale mata yakeyi yaki yadda yabi su Hanan part d'in Momy. Yana kallon call d'inta yak'i dagawa yafiso komai zai faru saiya dawo ya lallashi abarsa a d'aki, dama ba wani meeting da zasuyi ya fad'ane kawai dan zillewa zuwa hospital. Da sallama ya shiga ganinta yayi zaune cikin seat tayi tagumi, little kuwa tuni yaje da gudunsa gurin abbansa, dagashi yayi tare da mishi wasa, sannan ya iso inda take, wacce sallamar kawai ta ansa can ciki mak'oshi dan haushi yake bata. Yace" baby yadai ko jikin ne?" Ya fad'a wai shi wayayye. Paper ta mik'a mishi yana ganin abinda ta k'unsa, cikin murmushi ya aje little ya dagata sama yana zagaye parlour da ita yace" kai am so much happy baby zan k'ara zama Dady iyyeni, little zai zama Yaya" ya fad'a yana kallon little dake mishi daria duk da baisan me ake cewa ba. Itakam kallon tace cikin mamaki tace " I seen like murna kakeyi piyaa?" "Yes of course dear abin farinciki ne yasamemu let join happiness 2gether" ya fad'a yana kama hannunta irin baima fahimci halinda take ciki ba. Fizge hannunta tayi tace "me kake nufi, ya kakeso muyi da little?" Cikin ko in kula yace "kici gaba da feeding d'insa mana, zuwa haihuwa sai a yayesa." "What! So kake ya mutu, kana mu kashe rayayye mu jira Wanda baizo duniya ba?" Ta fad'a cikin b'acin rai. Dama yasan za'ayi haka, ganin ranta ya b'aci yasa yaja hannunta suka zauna, sassauta murya yayi cikin lallashi da lallama yake bata hak'uri, akan ta hak'ura, suje hospital zai a basu shawara yadda zasuyi, Sam taki yadda da haka, yanata rarrashi ita kuma ta kafe akan ba haka ba, ( dama Siddiqa da ra'ayi) ganin abin nata yayi yawa sai rarrashi yake tana bultsemishi yasa ranshi ya fara b'aci yace "to fad'amin ya kikeso ayi?" "A zubar da shi kawai" "What! Ashe ke shashace ban Sani ba, Ashe bakya sona, gudan jinin nawa kike cewa na zubar? D'an Sunna bana haram ba, dama son iya baki ya tsaya baikai zuci ba?" Ya fad'a cikin bacin rai har idonsa ya kad'a. Little ganin iyayensa suna hayaniya yasa ya fashe da kuka tare da zuwa kan cinyar Siddiqa yana laluba rigarta alaman zaisha mama, hawaye kawai kebin fuskarta ganin an doketa an hsnata kuka hadda cewa wai bata sonsa, d'an ture little tayi alaman bazaisha ba. " kada ki sake ki sakamin yaro a shirmenki, Malama ki bashi abinshi yasha." "Me wallahi bazan bayar ba, Salon ya mutu, koda zaisha nonon sai bayan na cire cikin, kima yau dinne basai gobe ba" ta fad'a cikin tsiwa, da Bacin rai. Daga hannu yayi zai mareta, kome ya tuna ya sauke hannun tare da nunata da yatsa yace "kee ki kiyaye, kije kiyi duk abinda zakiyi kiyi, amma ki Sani kome yasamu cikina zanyi mummunan sab'a miki, idan haihuwa da nine bakyaso ki bari ki haifemin cikin in yaso kije a cire mahaifarki gaba d'aya, ni kuma na nemi maison haihuwa na aura saboda inason yara" yana Kai nan ya d'auki d'ansa dake kuka ya fice daga part d'in cikin K'una rai, dan yasan idan yaci gaba da tsayuwa ana iya yin banna.... ********************** Durk'ushewa tayi a gurin tana ruzgar kuka, ganin ba mafita ne ya sakata daga waya ta kira Aunty Ramlah, tana d'agawa ta fashe mata da kuka tana fad'amata abinda ya faru. "Haba Siddiqa da halinki da wqyonki kika yi wannan danyen aikin, aida kin gayamin dana hanaki aikata haka, haba ai 'ya'ya rahama ne, gaskia kin kwab'e lamari, wannan abin yafi k'arfina su Mama zan kira" tana gama fad'a ta kashe wayarta, k'ara rushewa da kuka tayi, tana jiran sammaci daga su Mama. Ai Ramlah na gayamusu ran Mama ya b'aci bata jira cewar aunty ba ta kira Siddiqa. Ganin wayar Mama saida cikinta ya kad'a tace "na banu" d'auka tayi cikin sanyi, dagacan Mama tace" ke wace irin sakarya ce shin ma kinsan yana haifeku ne? To bari kiji tun daga Mubarak har Abdallah ba Wanda baisha ciki daga cikinku ba, amma gakunan a raye ba Wanda ya mutu, ke inba abinki kimma samu mjinki bai nuna miki tsana ba yace yanason abin sa sai kece zakice bakiso, to kin Dade baki zubar ba" haka Mama ta balbalete tsab. Aunty kuma nasiha tayi mata da ban baki, tare da lallashi, tuni nadama ta rufeta ta gane bata kyauta ba. Haiydar part d'in Momy ya wuce yaje ya zai yana mata abinda ya faru, taga wautar Siddiqa saidai shima tayi mai fad'a akan lallabata ya kamata yayi ba fad'a ba, sannan sukaje part d'in tare da Momy da Gwaggo, fad'a sosai sukayi mata tare da nasiha da rarrashi, sannan Momy tace. "Indai Umar dama nawane, kuma yanacin komai Ku had'o kayanshi kawai ya koma hannuna" kaysnshi ta had'a ta basu suka wuce, shima gidan ya bari gaba d'aya saboda yanda yakeji har yanzu, su aunty ma ta kirashi sun bashi hak'uri tare da cewq shirme da k'uruciya. *10:00pm....* Haiydar ne zaune kan gado yana aiki a cikin system turo kofa akayi, sanin wacece yasa ya ansa sallama ba tare daya d'ago ba, jin anki magana yasa shi d'agowa, "subhanakallahumma ahsanul kalikeen" shine abinda ya fad'a, ganin Siddiqa cikin wata fitinanniyar night gown pink, komai nata ya bayyana tana mishi shu'umin murmushi. Mantawa yayi da fushi ya ture system gefe ya ware hanayensa alaman tazo, zuwa tayi cikin takun k'asaita, ta fad'a k'irjinsa cikin sanyin murya tace. "Piyaa i apologize..... Katseta da yayi da cewa. " Apologize accepted" tare da had'e bakinsu guri daya cikin rud'ewa........ Tun daga ranar sukaci gaba da bawa juna kulawa ta musamman suka shiga laulayi sai dai wannan da sauki, har cikin ya isa haihuwa. Wannan karon ma namiji ta k'ara sunb'ulowa mai kama da Haiydar Sak. Momy tace 'yata kin haifumin Umar da Son yanzu saurah Zarah da auta na Hanan, dariya akayi gaba d'aya banda ita data soke kai cikin kunya tana murmushi. Cikin sabon gidansu da Haiydar ya tsara musu dake legislative quarters, anan akasha suna tsarin mai kyau irin na India. Lols Zanso kuga oga D one rawar Kai kaman yau akafa yimai haihuwa, su Shamcy da zarah su auntys Ramlah an rakashe an chase, inda yaro yaci sunan *Abdulmajid*(my next novel inshaa Allah) zasu kirasa da *Arjun*. _Allah raya Arjun akan sunnah_ πŸ‘πŸ»πŸ˜‚ ✍🏻 πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta

Chapter 15 of 16