Share this page
** Siddiqa ce zaune a falo tare da Aunty wacce bata Dade da isowa ba, su Rufee da Jabir sai surutu suke cikata dashi na abinda akayi da batanan, Aunty ce tace "ke Rufaida kuje inda jakadiya naji tana nemanku" aiko da gudu suka tashi saboda sunsan neman jakadiya akwaita da labarun ban daria. Tace " Baby sai kuma mukaji anyo mana suruki a birnin kebbi" Zaro ido tayi sannan tace "lah ya Anas gayamuku yayi kenan" Aunty tace "ko daya Mubarak dai ya kira ya fada masa shi kuma ya fada mana, ke har mai martaba saida ya fada masa" dafe kai tayi tace "na shigesu da bakin ya Mubarak yanxu hadda mai martaba ya gaya ma?" "To meye abin damuwa Siddiqa bayan Anas yace yaron baida matsala shima Umar yace adan zamanta sukayi lokacin bikin su Aisha baiga illarsa ba, indai kina sonsa aiba matsala" Rufe fuskarta tayi da hannayenta sannan ta kwasa da gudu tayi d'aki, Aunty tace "ja'ira kina sonsa kenan" ta fada tana murmushi. Tana shiga d'akin kiran Umar na shigowa saida ya kusa tsinkewa sannan ta daga nan yake gayamata zasuzo da familynsa zuwa weekend, tace "da sauri haka Ya Umar " "Naki wasa nifa tunda kika amince da soyayyata gani nike kaman kin zama tawa" Cewa tayi "ai dama ni takace" yace "Allah" tace "sosai kuwa" haka sukayi wayansu cikin nishadi. Shima ya Mubarak ya kirata yace zaizo weekend saboda su tattauna maganar. Sannan sukayi waya da Aunty Jameela da Ramlah harda Shamcy kuma duk akan maganar ne kowa na goyon bayan abin. Istikhara ta karayi dama tunda yace yana sonta take tayin istikhara kuma taji ta natsu sosai da abin. _kuyi manage da wannan friend naji zazzabn nason dawomin_ ๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ช. โœ๐Ÿป ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„ [5/20, 6:22 PM] ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ( _Base on love story_ ) *Written* *By* ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„ ( _Siddiqa_ ) ยฉ *PERFECT WRITERS FORUM* *P.W.F* *Page* 30&31 Duk yanda Haiydar yaso ya zillewa tafia zuwa Argungu ya kasa samun daman yin hakan saboda Dady yace ba excuse kowa sai yaje, dolensa ya hak'ura. Siddiqa nauyin fad'an zuwan su Umar tayi saida Umar d'in ya kira Anas ya gayamai shi kuma ya fad'ama Ramlah ita kuma ta kira Aunty ta gayamata (ni kuma nace ina ruwan a aiki kare, kare ya aiki wutsiya). Itakam Aunty daria ma abin ya bata ta kira Siddiqa tace "ke Baby abu sai kace Budurwar k'auye, ai kin kinajin kunyar mai martaba da mamansu Aysha ai kya gayamin ko? Ko nima kunyar tawa kikeji ne?" Boye fuskarta tayi da tafukan hannunta sannan ta kwasa aguje tayi d'akinta. Daria kawai Aunty tayi sannan tayi bangaren mama ta gayamata zuwan surukan nasu, murmushi mama tayi tace "wannan zumudin haka kodai dama keda 'yar taki kun matsu ne?" daria Aunty tayi sannan tace "Aa ai zumudin na suriki nane shine ya sakota a gaba" "to Allah ya sanya Alkhairi sai a gayama mai martaba aji ta bakinsa" cewar mama. "Ameen maman yara, hakan za'ayi sai da anjima idan ya shigo sai a fada masa" hakadai sukata firansu cikin nishadi kaman ba kishiyoyi ba sam ba kyashi a tsakaninsu zamansu gwanin birgewa. Bayan mai martaba ya shigo da aka gaya masa cewa yayi da wuri haka, akace iyayen yaron ne sukace ya kamata ka kulla zumunci tun yanzu, saboda Dady ya gayama Umar kada ya nuna ya sansu yafison yayi ma aminin nasa bazata, shiyasa ba'agaya musu ainihin dalilin zuwan ba, cewa sarki yayi to ai ba komai Allah ya kawosu lafia, ai duk wanda yaso abinka ya gama maka komai. Hakan kuwace ta kasance ahalin gidan Alh, Muktar Sadauki sun shirya tsaf sai tafia Argungu kowanne yayi gayu sosai, su Haiydar yau wankan shadda akayi da yace bai cika sakata ba daga juma'a sai sallah sai kuma daurin Aure, duk da haka ba karamin kyau yayi ba kalar brown ce shaddar amma light sai ya saka k'ube dark brown, shima kuma Umar milk color ya saka. Dady kuma hadda babbar riga, Zarah da Hanan anion material pink sukayi yayin da momy ta hade cikin swiss less, haka suka fito gwanin sha'awa da motan Dady suka fita bayan sunyi Addu'ar tafia, Haiydar ne yaja motar, suka wuce security da gate man suna musu Allah ya kiyaye hanya. Dady yace "gashi zamuyi tafian da ba'aso ta family gaba daya Allah dai ya kaimu lafeeya" kowa yace ameen. Bangaren gidan mai martaba suma shiri sukeyi sosai, Mama da Aunty da suka shiga kitchen sai wasu barori dake dan tayasu, Siddiqa kin fitowa shiga kitchen d'in tayi saboda kada su mama suka tayi Rashin kunya, d'akuna ta gaggara sannan tayi ma su Rufaida shirinsu su jakadiya ma ba'a barsu a baya ba, falon saukar bakin mai martaba aka gyara can ne za'a saukesu. Saida aka kammala komai aka gyara ko ina sannan suka shirya, atampa ce blue and yellow ta shirya cikinta batai wani kwallyaba amma tayi kyau sosai. 12:00pm suka iso, wangale masu get dogarai masu tsaron get sukayi sannan suka kwashi gaisuwa yayin dogaran fada suka k'arasa suka sanarda Sarki isowan bak'insa. Ya Mubarak ne ya taresu da murnarsa dake shima ya iso jia, bayan sunyi parking sun fito, russuna wa yayi ya gaida Dady da Mommy sukayi musabafa dasu Umar, shima Dady hannun ya basa saida yad'an duk'ar da kansa sannan ya bashi hannu Dady yace "akwai Alkhairi a cikinta d'ana ko bakaso na samu ne" murmushi kawai yayi sannan su Zarah suka gaidashi yayi musu iso zuwa falon bak'i. Waziri Mai martaba taba ya wak'ilta sannan ya shiga daga ciki dai2 suma sun fito saboda Umar ya gaya musu k'araso wan bak'in, shine kan gaba iyalansa na take masa baya. Da sallama a bakinsa ya shiga idonsa suka sauka kan aminin nasa, da mamaki bakinsa na rawa yace "Muktar.. Kai..Kaine ko mafarki nakeyi"? Tasowa Dady yayi yaja hannunsa zuwa kujeran kusa dashi, zama Mai martaba yayi sannan Dady yace "nine dai Muhammad bayan tsawon lokacin da muka dauka bamu hadu ba" Gyara zama Sarki yayi yace "kaddai kace d'ana Umar shine ya rikid'e ya dawo surukina?" "nima lokacin da Umar yazo min da zancen na girmama Allah garara misali wadda ya wuce misali cikin ikonsa yasa yara sun dawo mana da zumuncin mu wadda ya dad'e dayin rauni" ya k'ara da cewa "shiyasa nace kada Umar ya fad'a nine mahaifinsa har sai munzo na baka surprise"cewar Dady. " Aiko ka bani big surprise amma kuma fushi nike dakai ace tsawon lokacin nan..." Katseshi Dady yayi yace"let bygone by bygone a manta da baya saboda mu duka munyi wa juna laifi saidai nace muce Allah ya tsare gaba" Kowa ya Ansa da Amin sannan aka gaggaisawa da tambayan bayan rabuwa, suma su mama zama sukayi kusa da kujeran Momy yayin yaran suka zauna kasa maza suka zauna tare suma matan suka had'e su Hanan da Rufee kuwa tuni aka sark'e kaman sunan juna dama can (ni kuma nace parrot an had'u da parrot) hadda Jabir ba'a barshi baya ba. Aunty ce tace "nifa 'ya'yan nawa sun rikitani waye Umar a ciki duk sun girma abinsu, ko shine mai kukan A bashi su tafi da ita lokacin da kukazo nadin mai martaba" (lokacin Siddiqa zama tace da sukazo Haiydar ya ganta ya riketa gam yace mommy ta samu baby da zasu tafi hadda kuka saida akai mishi dubara sannan suka wuce). Mommy da itama ta tuna da lokacin tace "Aa wannan Haiydar ne babban ne Umar ta nuna musu shi" Aunty tace "to Aleeyu still gashi Siddiqa zata zama taku" kowa saida dara a falon banda Haiydar smiling kawai yayi. Itama Siddiqa dukar da kanta tayi tana daria kasa2 tana dago kanta Sukayi 4 eyes da Haiydar harara ya balla mata ita kuma ta d'age kanta tana tabe baki tace a ranta "Ashe yana saka manyan kaya, dalla jishi kaman na kirki a ido amma sai iskanci...." Mamace tace "ya kama kuci abinci an zauna anata fira gashi kunsha hanya" "gaskia kam ya kamata ke Siddiqa ke zuzzuba abincin" cewar Aunty. Mommy tace "to ai gwanda a sako gaba daya dan kuma da alama bakuci ba, kema Zarah tashi ki tayata" Dady yace "hakane, ni kuma a had'ani da aminina yau zamuyi tuna baya" daria sukayi gaba daya sannan Sarki yace "lallai kam aminina ya kamata a tuna baya Allah yayima 'yaran nan Albarka gaskiya *had'uwarsu* ta zamo Alkhairi"suka ansa da ameen. Katuwar dadduma aka shimfid'a tsakiyar falo sukayi saving iyayensu, su kuma su ya Umar sukayi part d'in ya Mubarak ya Zarah ce ta kai masu abincin(wacce na kula suna Satan kallo itada Mubarak). Bayan ta fitane ya Mubarak yace " Umar wannan kanwar tamu tanada kirki, ko zaku bani itane?" Murmushi yayi yace mai zai hana indai tanaso" Haiydar kuma kama hab'a yayi yace" aini ina ankare dasu tun dazu sai satan kallon juna sukeyi" daria Mubee yayi yace "kai maza ashe ka saka mana eyes" Umar yace "lil yaushe ka koyi saka eyes ban sani ba?" Murmushi yayi yace "basar kawai bros, na fad'ane kawai ashe gaske ne" haka dai sukayi ta chapter daya baya suka ci abinci. Kiran sallah ya tada su maza sukayi masjeed matan kuma suka shiga cikin gida. Bayan sun dawone Umar ya kira Siddiqa yace "na fahimci yau sam bakya yayina su mommy kawai kike tattali ga kuma lil na kawo miki Ku gaisa amma kinci fitowa" cewa tayi "Laa.. Ya Umar nina isa kawai dai kada su mommy suga nayi rashin kunya" yace"hakane shy girl amma fah kinyi kyau kin ganki kuwa" "Kai ya Umar ai kama fini kyau" Yace" rufamin asiri kada masu jan rigannan su kamani" Daria tayi "sun isa su kama yarima" "Yarima fah" eh mana ko baka yadda bane" "Yadda dole gimbiya tayi magana, yanzu dai kizo Ku gaisa da lil sannan Zarah ta rakoki" "Ok" ta fada a tak'aice, dan tasan inta biye ta Umar ba yanzu zasu aje wayan ba. Hang up! Sannan tace "hmmm ya Umar badai ba baekwanci ba" Zarah tace nidai ya Umar ne ai bikiga komai, Ya Haiydar ne dai miskili" Tace "ai naga alama, muje wai ki rakani zan gaisa da Haiydar d'in" ta fada tana sanya hijab nata itama Zarah mikewa tayi ta saka nata suka fice dan tana miradin 'kara kallon fuskar man d'in nata. Dake mai martaba yana suna falo shida Dady, su mommy kuwa suna part d'in mama. Suna shiga sai Umar ya cewa Mubee "to gatanan taji daga bakinka" itakam Zarah dad'i ne ya rufeta wadda taeso shima yana sonta amma saita basar tana taja class, gefe suka kama banajin me suke fad'a. Siddiqa data fahimci bai gayama Umar abinda ke tsakaninsu sai itama ta basar tace "yau dai gani ga lil d'in mu da nake tashan labarinsa, koda yake nama sanka saidai bamu tab'a magana ba" Murmushi zamu hadu yai mata dan ya fahimci ta raina mishi wayo sannan yace " hakane Aunty mu nima ina ganin fuskarki a sch ashe kace aunty tamu" haka suka gaisa kaman da gaske amma idan suka kiyaye idon Umar sai sakon harara suke aikawa juna (ni kuma nace to yaufa akeyita kenan) Umar sai d'adi yakeji Lil da Siddiqarsa suna fira kaman Susan juna hada cewa sai su rika zumunci a skull ya kular masa da ita, itama ta kular masa dashi. Su Dady kuwa tattauna sukayi akan yadda abin zai kasance suka yanke zuwa k'arshe wata zai turo 'yan uwansa Neman Auren saboda ayi komai cikin lokaci in yaso ta k'arasa kara2n a gidanta. Suma su mama sai hira suke kaman dama can sun saba tuni suka shaku kaman kada su rabu, su Rufee kam sai kirinya suke an hadu da an dace. Lolz Sai bayan la'asar suka wuce cike da farinciki da tsaraba da suka sha. _wannan kenan_ โœ๐Ÿป ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„ [5/20, 6:22 PM] ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ( _Base on love story_ ) ```Written``` ```By``` ๐Ÿ’„ *Meryerm Abdool* ๐Ÿ’„ ยฉ *PERFECT WRITERS FORUM* *P.W.F* ```Ina neman afuwanku friend da jina shiru da kukayi, na shiga busy ne, shiyasa nai maku page 2 na toshe mouth ``` ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ *Page* 32&33 *3days later....* Wayar Zarah ce tayi ring..tafi tayi ta fice daga falon, Mommy ta bita da kallo tace" nifa bangane miki ba Zarah kwana biyun nan sai wani muku2 kikeyi da yawan zaman d'aki. Umar ne yace "Hmmm ki bari kawai Mommy, inaga itama 'yar gida za'ayi ita da Mubarak" Sai lokacin Dady dake karanta magazine yayi magana yace "son da gaske kakeyi ko kuwa wasa kake"? Haiydar dake sana'ar tasa ta danna tab, yace" da gaske ne Dady, nikadai suka bari ina garari bamai sona" ya fada ba tare daya dago ba. Daria sukayi dady yace "Hanan d'in fah" "ohh! Dady rabani da rigiman Hanan tace naje can na nemi matata" cewar Haiydar. Mommy tace "yata kam kayi mata tsufa akai kasuwa son" Turo baki yayi yace "Mommy hadda ke" ya fada kaman yaro. Ya Umar yace "yau dai zamuga mommy da son d'inta a rana" ya fada yana daria "gani kuma na nawa" cewar Dady. "Aa son baza'a gammu a rana ba, ai kai matarka mak'erinta bai ma gama k'erata ba" ta fad'a tana daria. Zaiyi magana kenan Zarah ta shigo,saida ta zauna sannan Momy tace "su Zarah an girma" bata fahimci inda Mommy ta dosa ba tace"Mommy girma kuma? kara girma nayi hala?" Daria suka saka mata,kwab'a fuska tayi tana shirin kuka ita batasan me suke ma daria ba, Dady yace "ki barsu Autah, ku kuma ku daina kusan daria cin rai gareta" gum sukayi da bakinsu sannan Dady ya k'ara cewa. "Autah shin gaske ne abin naji daga bakin yayyinki wai keda d'ana Mubarak...." ai kafin ya k'arasa fada ta ruga da gudu tabar falon, daria kawai yayi. Mommy tace "yaran zamani sai abarsu, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi suka ansa da ameen. Hanan ce ta shigo falon da gudu tana fadin "Am back Mommy..." Harara Mommy ta balla mata, da sauri ta fita tayi sallama sannan ta shigo a nutse ta gaida Dady da Mommy dasu Umar sannan taje jikin Mommy tace "am back momy" tace "ur welcome angle, ko kefa Hanan yanzu kije ciki ki cire uniform dije ta miki wanka muyi lunch kinji" d'aga kai tayi zata wuce Haiydar yace. "Matar yau me aka karanto mana?" turo baki kawai tayi ta fice....... ** ** ** Siddiqa ce ke waya da Shamcy ta gaya mata komai game da zuwansu da dangartakar da ke tsakaninsu dasu Haiydar, shamcy tace. "Ashe kenan yanzu ba sauran 'yar zama a tsakaninku saidai zaman Aunty da lil d'inta" ta k'arasa fad'a tana daria. Itama dariyan tayi tace "ina kuwa bakima San wani renin hankali da yamin ba, nuna yayi sam bai sanni sai cewa yayi kaman yana ganin face d'ina skull d'in, Allah gayen dan duniya ne na kwarai" Daria Shamcy ta k'ara yi tace "ai kema 'yar duniya ce shine ya nuna miki ya fiki iya duniyanci" "Bakima san wani abu ba, gaisawa mukayi a mutunce hadda tab'a hira saidai sakon harara da muke aikawa juna idan mun kiyaye idon ya Umar" Daria sosai Shamcy tayi tace "lallai besty lamarinku sai a barshi kawai" tace ai ki bari akwai chakwakiya idan bazai bari nina ba bari zan ba" Tace "Allah ya kyauta sannan tace to yaushe ne aka saka ranan" "To uwar zumudi ai ba'a saka ranan ba, nifa naso ace sai na gama amma naji su mai martaba na fad'in wai gara ayi a gama in yaso na ida kara2n acan, shima ya Umar haka yace" "Ai gaskia suka fad'a" cewar Shamcy. Tace "kince haka mana tunda bake ce ba" Sake cewa Shamcy "Aini ma Dady yace gara na fitar da miji dan bazai bari har na k'are ba, shekara uku fa besty kinga ai dole su damu muyi aure saboda gudun lalacewar zamani, yin Auren shine kwanciyar hankalin su" Tace" haka ne kam Allah ya kara tsaremu da mutuncin mu dan mulkinsa" ameen" tace. Sannan Siddiqa tace "um besty ki gaida hajia time 4 kitchen aunty tayi kira" daria tace "lallai kam su Aunty su matsa kiyi masters inya Umar yaci sai kunne ya mik'e" "Kyaji dashi" ta fada daria kawai Shamcy tayi sukayi sallama Siddiqa ta wuce zuwa kitchen... Mubarak yayi sallama d'akin Mama zaune ya sameta kan dadduma tana lazumi shima zama kan sofa saida ta k'are ta juyo tace" yadai Mubarak bakinka da magana" Dayake dama Mubarak direct 2 d point ne baya boye2 kuma Mama abokiyar maganarsa ce, gayamata abin da ke tsakaninsa da Zarah yayi yace yanaso a hada dana su Siddiqa" Murmushi Mama tayi tace "mashaa Allahu amma kuwa nayi murna, Allah ya sanya Alkhairi, amma meyasa kak'i fad'a tun lokacin da zuka zo, sai a tsaida maganan gaba daya" Cewa yayi "to ai banji daga bakin ta ba kuma kinsan halin 'yan matan nan da jan aji, shiyasa ban fad'a ba saida ta amince don gudun matsala" Tace " kayi kyau kai hakan da kayi, kuma inshaa Allah idan mai martaba yazo za'a gaya masa sai yayi magana da abokin nasa, yanzu dai bari na gayama Aunty ku " Mama ta fada ta mikewa... Aunty kam cewa "shikenan za'ayi tuwona maina, bani in baka kenan, Allah ya sanya Alkhairi, ya kuma nuna mana lokacin biki" Mama tace "ameen" Mai martaba da aka gayamasa yayi murna sosai dajin labarin kuma anan take ya kira dady ya labarta masa. Dady yace "nima dazu na tsinci maganan cikin gida ina niyyan kiranka sai gashi ka kirani, kaga ikon Allah ko lallai ba wani sarki sai Allah" "Ikon gagara misali kenan, dole mu godemasa da wannan ni'imar da yayi mana" sannan ya kare da cewa "kuma idan ba damuwa munaso a hada danasu Umar"cewar mai martaba. Dady yace" haba meye abin damuwa a ciki kawai a hada idan ya amince taci gaba a gidansa shikenan" Sarki yace "zatayi kara2 inshaa Allah, yanzu ya abin zai kasance kenan?" "Kaman yadda muka tsara tun farko hakan za'ayi zan gaya musu inyaso in suka nema suma sai nema a gurinsu saboda a cika al'ada" Dady ya fada yana daria.. Shima mai martaba dariyar yayi yace "aikam cika al'ada kam" sukayi sallama kowanne su cike da farinciki... Kaman yadda aka akawari hakan ce ta kasance kanin Dady sunzo gurin kannin mai martaba inda akayi komai yadda ya dace sannan akayi komai da al'ada ta tanadar aka tsaida Aure watanni 5 masu zuwa dai-dai su Siddiqa sunyi hutun second semester. _toh Allah ya kaimu misha buki_ ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ โœ๐Ÿป๐Ÿ‘‰๐Ÿป ๐Ÿ’„ ~Meryerm Abdool~ ๐Ÿ’„ [5/20, 6:22 PM] ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* ๐Ÿ‘‰๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ ( _Base on love story_ ) ```Written ``` ```By``` ๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„ ยฎ *_PURE MOMENTS OF LIFE WRITERS_* *P.M.L* ~Wannan shafin nakune Ameenan juna group๐Ÿ‘ฉโ€โคโ€๐Ÿ‘ฉ. Kuna kaunar novel d'in nan, nima ina kaunarku~ ๐Ÿ˜˜ *Page*34&35 Ana gayama Umar an tsaida rana, farinciki ya lullub'esa yasan yanzu kam baida sauran fargaba, sai jiran lokaci, Haiydar ya kira yana fada masa an saka rana dake baya gida shi kuma ya kasa hak'urin harya dawo, aiko yana gayamasa ji Haiydar yayi kaman an gaya masa ranar mutuwarsa saboda yanda ya tsani siddiqa (a cewarsa nikam nace Kodai... Um bari dai nayi shiru). Daurewa yayi ya nuna farincikinsa ya kuma sanya Albarka. Kallon Saleem yayi yana yamutsa fuska dama yaje gurinsa ne don tunda suka gama exam basu cika haduwa ba yana bashi labarin zuwan da sukayi gidansu siddiqa ne ya Umar ya kirasa, yace. "Kaji wai har an tsaida rana, nina rasa me bro ya gani a tattare da yarinyar nan ya mato akan ta haka, gashi suma su Dady sai zumudi sukeyi wai a sanadin hakan zumunci ya dawo sai kace in basu hadu ba zumuncin bazai dawo ba" ya fada yana jan siririn tsaki. Smiling Saleem yayi sannan ya dafasa yace" c'om D one ni banga abun damuwa anan ba saina farinciki, indan abinda ya shiga tsakaninku ne aiya wuce ka manta kawai kuci gaba da zumunci Ku ina zaifi" "What! In manta pa kace? Are u in sense kasan me kake fad'a kuwa"? Ya fad'a da k'arfi. Wani murmushin Saleem ya k'arayi yasan meke damun abokin nasa amma yasan koya fad'a ba yadda zaiyi ba,yace " yi hakuri kada ka d'auka da zafi, to yanzu me kakeso kayi ne?" Ya tambeyesa. "Kawai banason ganinta da Yayana ne kurum, baxanyi mata komai ba saboda zumunci dake tsakaninmu kuma bros na matukar sonta saidai nikam banasonta da Yaya na". "To dawa kake sonta" Saleem ya tambayesa. Lumshe ido yayi sannan ya waresu yace "koma waye" Daria yaba Saleem amma saiya danne yace "mutumina just forgot d past focus on present it's better!" Cewa yayi "bazaka gane bane Leem, na tsani yarinyar fiye da tunaninka, koda yake manta kawai fad'in ba wani amfani ni zan buda sai mu sake had'ewa" ya fad'a yana dirowa daga kan motan dake waye Saleem ya sameshi. "OK ba matsala barin shiga ciki nadan k'arasa wani, watakil na bullo zuwa anjima" Saleem ya fad'a. Umar kuwa yana k'are waya da Haiydar, Siddiqa ya kira tana d'agawa yace " Amincin Allah ya tabbata gareki sanyin idaniyata". Murmushi tayi itama tace" tare dakai makullin zuciyata, fatar kana cikin koshin lafia?" Wani irin dad'i ne ya rufesa kaunarta na kara ratsashi "ina lafeeya mamata uwar 'ya'yana fatar kema kina lafia?" "Kai ya Umar har na zama matar kenan" "Uhum tome ya rage bayan shafa fatiha, ranar kuwa kinsan meye?" Murmushi tayi tace" Aa saika fada" "Daga zan zama bawanki sai yanda kikayi dani" Kama baki tayi kaman yana gun tace "dena fad'a hakan kada aji ace zaka zama mijin tace" Yace " aini mijin kafin tace zanma zama, Allah dai ya nuna mana lokacin kiga abinda zai faru" daria tayi tace "ameen" suka d'an tab'a hira kana sukayi sallama. Aunty ta kirata sai tsaiya take mata, tace su siddi single wato jira kawai kika mu daga kema ki daga amma shine kikayi ma Abbas tsiya kikace ba yanzu zakiyi Aure ba(Abbas d'an waziri ne tun tana secondary yace yana sonta tace ba yanzu zatayi Aure ba har yayi Aure tuni). "Kai Aunty Jameela Allah ki daina maida hannun agogo baya Abbas d'in da yama manta da zancen amma ke baki manta ba, kuma ai ko yanzu saina kammala za'ayi" "Makira idan aka d'aura sai kice a kwance" Aysha ta fad'a. Daria tayi tace "Allah nayi missing rigimarki Aunty Jameela" "Kyaji dashi ki gaidamin dasu Aunty" "Zasuji ki gaida Yaya Sulaiman" Aunty Ramlah ma ta kira, harda su Abdool sun kirata sun nuna farincikin su. ** ** ** Hutun su ya kare dama bamai yawa bane amma sun tsara da Shamcy akan sai wani week zasu koma. Ramlah ta kira Aunty akan akawo mata wacce zata ringa yin mata aiki saboda lauyayin da takeyi sam batason warin gas, da Aunty ta gayama Mama mezai hana Siddiqa taje ta kawai tunda dama hutunsu ya kare, hakan kuwa akayi ta tattara ta wuce saboda naka sai naka. Sai daga baya ta fad'ama Shamcy, tace ba komai ai lalura ne Allah ya bata lafia itama tana zuwa wani sati. Ramlah duk ta rame kaman wadda ta shekara tana jiyya, Siddiqa tace "Aunty Ramlah kinga yadda kika dawo kuwa? Tab gaskia nikam zan fasa Aure, wannan irin wahala haka" ta fada har ranta dan itakam abun ya bata tsoro. Murmushi Ramlah tayi tace "hoo! Babyn Aunty kenan a gaida iyayenmu da suka ita haifarmu,ai dole mu jinjina musu, Allah dai ya saka masu da gidan aljanna, da kike kin fasa aure ai kinyi karya dolenki kiyi don shine mutuncinki" "Wallahi kam Aunty Ramlah sunyi kokari Allah ya biyasa musu bukatunsu na Alkhairi" ta fad'a amma kam

Chapter 6 of 16