Share this page
wayanta ta Kira number Aysha taji ko sun wuce,kashe taji wayan Alaman suna bisa iska. Lolz Wayan Aunty ta Kira ta tmbyeta su ya Ansa sun wuce? Ta gayamata tun 9:00am aka kaisu air port.Sallama sukayi snn ta hang up. Siririn tsaki tayi Wanda yaja hnkalin Shamcy tace mata "ke km me akayi miki na tsaki??" "Hmmm! Ki barta kawai nida Ya Jameela ce...wai zata har sun wuce kota Dan Kira ta fadamin" "Hhhhhhhh! Haba dai en Mata kefa kikace tayi ta tafi ki huta,shine km tun yanxu har kin Fara missing Nata tun kan aje ko ina?" Shamcy ta fada tana daria "Ke! Yimin shiru anan damma kin samu na kulata" ta fada tana wani cin magani snn ta mike na shige toilet. "Kyayi kya gama gulman naki ki dawo hanya"Shamcy ta fada. ** ** ** Basu suka bar hostel din ba sai 11:30,yau dimma akon swiss sukayi baki anyi mishi Ado da fulawoyi milk,hijab ta saka milk da plat shoes milk sai post itama milk batayi wani kwalliya ba Amma tayi kyau mashaa Allah. Tsiraran mutane ne a farfarjiyar skul din kowa sai harkar gabansa yakeyi a haka suka wuce sai kallonsu akeyi SBD sun burge mutane ba karya,Bakin titi suka isa snn suka tari napep zukace ya kaimu gesse gidan Amarya kenan. Umar kam ganin yayi dare yayi tsawo da yawa matsuwa yayi safia ta waye yaje ya samu Ana's yai masa hanyar *haduwa da ita* Koda suka hadu gurin breakfast sai wani sauri yakeyi,Har saida mom tayi magana "Umar wannan saurin fah haka? Ko kanada wani uzuri ne?" Cewa yai "Momy kinsan bikin Ana's nefah! Yau zamuyi wunin Ango" Haiydar kam cewa yayi" Anya! Kuwa bros,kodai...."kodai me? Ka fada mana cewar dady. Uhum!kodai ya samo mana Aunty nida my Hanan ya fada yana kollon Hanan, Turo baki tayi tace "ni kadaina cemin Ur's kaje can nemo matanka"ta karasa fada tana murguda mishi baki,Kama bakin ya matse ai ko nan take tai kara. Momy ce ta balla mai harara "Allah son ka fita hanya baby kana matsa Mata da yawa fah!" Ta fada tana jawo Hanan zuwa jikinta,ita km ta wani lahe wa a jikin Momyn. Haiydar xai kara mgana...Dady yai gyaran murya snn yace ko da gaske mganan Haiydar son? Ya fada yana kollon Umar. Itama momy kallon sa takeyi tana jiran mezaice,sunkuyarda kansa yayi yana mai shafo kansa snn yace "Kila dai na dubata a yau dinnan a cikin kawayen Amarya" Aiko Hanan najin haka sai cewa " yawwa bros,nima ka samomin aunty kaman irin Wanda yayan Amal ta sit Dina ya samomata kullum sai ta gayamin wai tana sonta sosai,nima ka samomin kaji yaya" ta fada tana kallonsa. Cewa yayi "To my little Angel Zan samo miki,snn yace Bari na tashi kada Ana's ya nemeni"ya fada yana gayama iyayen NASA zai fita. Addu'a sukayi kamar kullum snn dady ya haye samansa,Umar da Haiydar tare suka fita suma,mommy da Hanan kadai aka Bari a falon,yayin maid dinsu ta kwashe flasks din takai cikin ta wanke. 11:30 Umar ya isa gidan Ana's yana cikin yadi milk yayi kyau sosai. Kiransa yayi a waya yana dagawa ya fara fadin "Ango kasha kamshi km Baban yaya" Dariya Ana's yayi snn yace " ka fadi haka mana tunda kanwata ta rikita ka" "Kaman kana a gurin kuwa,gani fa kofan gidanka fah"Umar ya fada. "Aiko gashi bana gidan kasan suna yini yau,Ina gidanmu yanzu haka"cewr Ana's. Nisawa Umar yayi Snn yace "to ganinan xuwa" Yana yima motarsa key,napep na aje su Sddq,zama yai cikin car din yana kare Mata kallo sai yaga ta kara msa kyau,su km Sam basu ma Ganshi ba,da yake yana dan nesa da gidan ne,Biyan me napep sukayi suka shige ciki. Saida suka wuce snn yaja motarsa zuwa family house din su Nas,A tsohon dakinsa ya sameshi kwance yana kallon pics din bikin cikin system. Gaisawa sukayi snn ya zauna yana tayashi kallon pix din.kamin yake cewa. "Nas wai ya za'ayi ne akan kanwar nan tamu?nifa na rasa ta Ina Zan Fara" "Haba Abokina kada ka zama matsoraci mana" Ana's ya fada "Hmm Abokina ba tsoro bane kawai ganin nakeyi kaman Inna tunkareta kai tsaye za'a samu matsala" UmR ya fada. Cewa Ana's yayi "toka Bari zanyi mgn da ita" "Yawwa Abokina ko kaifa!"Umar ya fada yana murmushi snn yace" yanxu kuwa naga sunzo gidan tare da wnn kawar tata" "Tau shikenan Bari zuwa bayan zuhr zanje gidan nai magana da ita,SBD nasan halinta sarai tana iya kin kara komawa gidannan da wuri tace skul ne ba interval din yawo,haka takeyi idan tazo gidannan saita hada wata bata kara zuwa ba,ba yadda mami batai da ita ta zauna nan ba,amma sai cewa tayi wai Aa tafison hostel SBD zatafi kr2 acan din SBD idan tana gida ba zatayi kr2 sosai haka dai taita kawo hujjarta dole mami ta kyaleta" Murmushi Umar yayi snn yace "aifa daga ganinta akwai ra'ayi Kai,Amma fah nikam tana burgeni sosai" Haka dai sukayi ta tattauna a tsakaninsu. Bangaren su Sddq kuwa suna shiga gidan tap suka isko falon da mutane hadda En Argungu sun iso ,Aiko nan suka Fara Mata tsiya wai tana gari amma suda ba en gari ba sun rigata zuwa. Ramla kuwa juyamata baya tayi Alaman tayi fushi,Gabanta taje ta rage tsawonta snn ts Dora hannayenta akan cinyan Ramlan tace. "Haba sisi kada ki bari ayi mana dariya,mun tsaya kankamta dakinmu ne snn km wlh bacci ne yai gaba damu yau,but pls sowie My Sweat Aunty"ta fada tana kwaba fuska Alaman zatayi kuka. Daria suka kwashe da ita suna masu fadin yaufa zamuga Yaya da kanwa a Rana. Ramlah kam dagata tayi snn tsce "kyalesu babyn Aunty na hkr ya wuce,naso dai ace kin Riga kowa zuwa gidannan,Amma nasan zaki ringa zuwa min end of week ko?" "Yee! Nagode sis,Inshaa Allah zanyi kokari na ringa zuwar miki sisina" ta fada tana yi musu gwalo. Haka dai sukayita fira basu tashi ba har saida aka Kira zuhr snn suka je domin gabarda ita. Umar kuwa suna tare da Ana's tare sukayi sallah snn ya wuce gida da sunan saiya ji yanda sukayi. Anas na isa gidan falonsa ya tsaya na washe snn ya kira Ramla yace ta hado masa Abincinsa taba Sddq ta kawo mai. Da sallama ta shiga falon snn ta aje tray akan center table,ta juya zata tafi ya kirata yace ta zauna mgn zasuji,dawowa tayi ta Zauna snn da ta sunkuyar kanta tana kallon carpet. Gyaran murya yayi snn yace" Sddq inaso ki nutsu sasai ki saurareni,snn yaci gaba da cewa,Kin gane Wanda nace yai dropping dinku jia?? Girgiza Kai tayi tace "Aa" "To Abokinane sosai yama wuce Frnd yakai Dan uwa,nasan Sadauki tun kuruciya har yau,iya sanina dashi bayada matsala,yanada kirki sosai,ya ganki km ya yaba dake shine yai min mgn a maimakon ya tareki Kai tsaye baisan ya zaki dauki abun ba shiysa yaga ya ksmata ki faraji daga gareni me kikace?" Tunda ya fara bayani taji kirjinta na bugawa,itadai baxatace tana far in ciki da zancen ba ba kima zatace tana bakin ciki ba,cewa tayi. "Yaya zanyi shawara" "OK to ba komai,Amma dai zai ya ganinki kuyi mgn ko?"ya tmbyeta "Eh"shine Amsarta. "Ok tashi ki tafi kawai. Hska ta tashi jiki a sabule ta wuce.... _wannan kenan_ πŸ’„ ~meryem Abdool~ πŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *HADUWATA DAKE* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Base on love story_ ) ```Writing``` ```By``` πŸ’„meryerm AbdoolπŸ’„ ~Dis page 4 whose who been happy wit returning of Mrs,president~ *Muhammadu bukhari* Love u all❀❀ *Page* 21&22 'Har ta fice daga parlon ya Dan daga murya ya kirata,SBD wani tunani da yayi a ransa! Dawowa tayi ta zauna inda ta tashi. Cewa yayi "Dama Zan tmbyeki ne koda wani Wanda kikeso daban,duk da cewa Ramlah ta gayamin bakya kula kowa amma gara naji a bakinki,feel free kada kiji komai" "Niko nakeda Wanda nake matukar so! Saidai......... Katse mata maganan zucin da takeyi Ana's yayi ta hanyar cewa "kinyi shiru kanwata bakice komai ba" "Uh um! Yaya ba Wanda nace inaso" ta fada tana wasa da yatsunta. "OK shikenan" Bayan ta fice ne daga parlor'n cikin gida ta shige ta iskosu sunyi group Ana cin abinci,itama kitchen ta wuce ta wanko hannunta tazo tai joining nasu,sakin ranta tai ba Wanda ya fahimci komai,Bayan sun kammala suka kwashe plates din suka wanke suka gyara gidan tsaf,snn suka dasa sabuwar hira. Sai bayan la'asar En Argungu suka wuce,suma su Sddqr zuwa 6:00 suka wuce da sunan zasu ringa zuwa akai2,kayan makeup da perfume Ramla ta hada musu,godia sukayi mata inda ta rakasu tana Kara jaddadama musu su ringa jewayowa kada su manta da ita sukace Tasha kuruminta zata gansu,ta koma ciki su km suka tari Napep suka wuce. Ana's kuwa tana ficewa ya daga waya ya Kira Umar ring 2 ya daga yana fadin. "Ya akayine mutumina" Gaya masa yadda sukayi da Sddq yayi snn ya Kara da cewa "saika dage kaga ka samu shiga,in Ku kasa wasa kada ka kara tuntuba" ya karasa fada yana daria. "Kada ka damu mutumina,komai zai tafi yanda ya kamata,Yanzu yaushe zamu hadu da ita??"Umar ya tmby. "To sai yadda ka tsara"Ana's ya bashi amsa. "Ah! Nikam ai ko yanxu a shirye Nike saina zo"Umar yace. Daria Ana's yayi snn yace "lallai Abokina kayi nutso a ciki,wai kaman ba Sadaukin da na Sani bane,any way ka Bari harta Kara zuwa sai kazo nan gida kuyi mgn" "Hmmm! Ka jika Nas da wani zance ai luv ne,Amma ka fini sani kome akeji aciki,saidai tazo din saika sanarda ni" "Hhhhhhh! Hakane kam Sadauki,gashi yanzu har ta zama tawa gaba ni kadai,Ana's ya fada yanajin kaunar matar tasa har cikin bargo. "Muma! Muna hanya inshaa Allah.Umar ya fada. "Allah yasa ayi nasara ya km sa Ayi damu"cewar Anas,snn yai mishi sallama. ** ** ** *Monday* Haydar ne zaune kan motarsa yana research din wasu lecture nasu da yace next week zasu Fara exam,sanye yake da jeans baki da shirt maroon color wacce akayima rubutu gabanta da white pent,shoes dinsa ma maroon ne,sai glass daya saka baki,suman nan ta kwanta luf sai sheki take. Saleem ne ya karaso yana cewa "D one ka ganni sai yanzu wlh sai yanzu na samu tashi kasan jiya na shawu sosai(da yake jia sunje club bankwana akan sai after Exam zasu koma SBD duk iskancin Haiydar to baya wasa da time din Exam SBD tsaro! Shine Saleem ya yaita banbamama cikinsa kwaya,Haydar kam sigarinsa yasha danan abinda ba'a rasa ba). "Ai saida na gayama kasha kadan Kai km kana wai na bankwana ne,injin dai iya ta ganeka (cewa da kakarsa)"ya fada ba tare daya dago kansa ba. "Inah! Ai cemata nayi zaxxabine ya rufeni shi yasa ban fito da wuri,shinefa duk ta rude hadda cewa naje hospital"Saleem ya fada yana daria. Smiling Haydar yayi yana cewa "zata Kama kane watarana" Dirowa yayi daga kam motar snn ya bude booth din motar ya Ciro musu carpet suka shimfida suka zauna,yana yima Saleem bayanin abinda bai fahimta ba. Su Sddq ne tafe sun fito daga office din wani lec,nasu da yayi test da basunan sukaje rokonsa yayi musu,yace suje zaiyi musu kafin Exam sai laka musu notice, godia sukayi masa snn suka fito. Tundaga nesa ta hangeshi,A ranta tace dama wannan yana kr2,Dan ta dauka iskanci kawai ke kawoshi skul,dauke kanta tayi tare da tabe baki. Shamcy na kalle da ita amma sai tayi kaman bata ga me tayi ba tace "Besty gafa mutumin naki can,ta fada tana kallon inda suke. Cewa tayi "kefa er air ce,to me ruwana dashi"ta fada tana shan toka. Daria kawai Shamcy tayi,sunzo dap dasu Saleem ya hangosu,cewa yayi. "D one kafa fight partner ka nan" Yana dago kansa sukayi 4 eyes,harara ta balla mishi,Shi km murmushi yayi Mata Wanda shikadai yasan ma'narsa. Kauda kanta tayi tana mai Jan siririn tsaki snn tace "kaji dashi koma me kake nufi Ina ankare dakai" Murmushi shamcy tayi tana cewa "Hmm kwaji dashi dai Ku duka. Tajita amma tai kaman bataji ba,A haka zuka karasa lab,dinsu.... Haydar kam cema Saleem kawai yayi "banda lokacinta yanzu"ya fada bayan ya maida hnkalinsa ga tab dinsa ya gudure a ransa zai kyaleta har sai ta Saki jiki snn ya Mata yai Mata rashin mutunci,A haka sukaci gaba da research din yana yima Saleem bayanin inda bai gane ba. 'Siddiqa kuwa ba ita ta samu daman zuwa gidan Ramlah ba sai ranar Friday shima SBD ta dameta da kirane wai tana nimanta,tasan kiran bazai wuce sbd wannan abokin ya Ana's ba. Taso suje tare da Shamcy,Amma tace wai zataje gidan kawunta ya kirata yana nemanta,dole ta hakura ta shirya taje bayan an dawo jumu'at. Tana ta shiga gidan ta isko Ramla a falo tana kallon wani series a zee TV wato *doli armano ki* zama tayi kusa da itah tana gaisheta snn "tace Kai amma nayi missing last last episode wlh ban samu na kallaba sbd kr2,Ashe wannan simran din haka ya hasowa urmi wuta,gsky yasakata gaba"ta fada tana mai Kara maida hnkalinta ga TV. Itama Ramlah cewa tayi "Ina kuwa zai kyaleta tunda bayaso taji dadi a rayuwarta,yafiso ya ganta a kunci,haka dai zukaci gaba da hiransu game da series din. Ana's kuwa Ana tashi daga jumu'at ya Kira Umar yace su hadu gidansa Sddq zatazo,da yace Ramlah ta fada masa zuwanta SBD ya gayamata komai,km tayi fariciki SBD tasan Umar mutumin kirki ne sosai. Cikin farinciki yace "yanxu kuwa zaka ganni,ko gida bazan je ba.am on my way" Darawa Ana's yayi snn yace " aifa ba'ayi ba sai bana" "Koma dai me zakace nadaiji din"ya fada snn suka aje wayar,juya akalar car dinshi yayi zuwa titin unguwarsu Ana's yana driving yana murmushi. Yana isa gidan a bude yaga gate din shima ya soka tashi car din snn gateman ya kulle gate din,Ana's na fitowa daga motarshi Umar na Parke tasa,jiransa yayi ya fito snn ya bashi hannu suka gaisa. Ana's ne ke cewa "kagafa mai nema ido rufe"ya fada yana daria. Shima Umar dariar yayi yana fadin " naka wasane,kasan da zafi2 akan daki karfe" haka dai Ana's yaita zolayarsa,shi km yana bashi Amsa,bude masa falonsa yayi ta kofar waje ya shiga,snn ya yace yadan jira kadan yanxu zaiga gimbiyar tasa,ya karasa yana daria ya snn ya fits... Cikin gidan Ana's ya shiga da sallama ansawa sukayi snn Ramlah ta tashi ta tarbeshi tana mishi sannu da zuwa snn ta anshi daddumar hannunsa. Itama Siddiqa sannu da zuwa tai masa snn suka gaisa,ya tmbeta skul din ta ansa da lfy qlau' snn ya gayamata isowar bakonta,sunkuyarda kai tayi cikin kunya,murmushi yayi ya wuce ciki. Wani medium tray Ramlah ta bata tace maza taje garesa kada yaga an shanyashi ansa tayi snn ta wuce,itama Ramlah wucewa tayi dakin Ana's. Da sallama ta shiga falon yana zaune kan 3 seated idon akan kofar aiko tayi masa kyau sosai, tana sanye da atamfa light purple mai ratsin pink,hijab dinta ma pink ne,karasawa tayi ta Dora tray kan center table,sannu yayi Mata ta ansa a kunyace snn ta zauna kasa kan carpet..tana mai gaidashi. Ansawa yayi snn yace "ta zauna a kujera mana" Girgixa Kai tayi snn tace" nan dinma ya isa " Jiyayi ta kara burgesa sosai. _tau nima ta burgeni kufa frnds??_ πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *HADUWATA DAKE* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Base on love story_ ) Written by:- πŸ’„meryerm AbdoolπŸ’„ Edited by:- *AAJ* & *MAMAN USSEY* Β© Perfects Writer's Forum P.W.F ~Dis page goes 2 u, my charming, lovable, adorable, gorgeous, dearest Aunty Fatyy Azland 😘😘 4 ur encourage and support. Love u 2 d high rank of ma~❀❀❀ *Page* 23&24 'Gyara zama Umar yayi sannan yace " Maryama Siddiqa nasan Anas ya gayamiki meke tafe dani, to amma wak'a a bakin mai ita tafi d'adi". K'ara gyara zama yayi yana facing d'inta, ita kuma k'anta na kasa tana wasa da yatsunta na hannu, sannan yace. "Ina matukar k'aunarki Siddiqa, ban taba soyayya ba sai a k'anki, ranarda na dora idona ak'anki naji ba wacce nakeso sai ke" had'e hannuwansa biyu yayi alaman begin yace " pls ki taimakeni ki soni ko d'an kadan ne " ya k'arisa yana k'allonta. Dagowa tayi suka hada ido, wani shock!! taji da sauri ta maida id'onta kasa, tasan ba yaune rana ta farko da namiji ya fara cewa ya sonta ba, amma wannan kam yazo mata a bazata, tun farkon ganinta dashi yake mata kwarjini sannan tana ganin k'imarsa sosai duk da cewa bawai tanajin sonsa bane a ranta, soyayya kam mutum d'aya tak! take ma ita..... Gyaran muryan da yayi ne ya dawo da ita, sannan yace "kinyi shiru bakice k'omai ba" "Uhum" kawai ta fada wani irin k'unyarsa data lullubeta. Yace " bazakice k'omai ba, kada ki sak'a jikina sanyi k'ice wani abu mana Siddiqatah" yayi maganan k'aman mai shirin yin kuka. Sosai maganarsa ta bata k'unya saboda yanayin yanda yayi k'aman wani yaro, wai kuma ita yake yima, smiling k'awai tayi. Shima daria yayi yace "na baki kunya koh? to yi hakuri na cik'aki da surutu tunda dazu gashi ko banko gabatar mik'i da k'aina ba, duk soyayya kice da rudar da dani, amma yanzu zan gabatar miki da k'aina saboda nifa da gask'e maganan Aure ce ta kawoni gunk'i" ya fada yana kallonta. Sai lokacin tai magana cikin siririyar muryarta tace " lah ba k'omai " Ta fada amma still kanta na kasa. "Da farko Sunana Umar Muktar Sadauki, mu en asalin gwandu ne amma anan Bk muke zama, momy nah er Dakingari ce, mu uku ne gun iyayenmu nine first born, sai Haiyar snn Auta zarah sai Hanan da momy ta dakko er k'anwarta ce itace Autarmu, nayi kr2 bangaren engineering wadda a yanzu har na fara aiki inada shekaru 30 fatar banyi miki tsufa ba?" Ya fada yana mai mata kallon tambaya da yake tunda ya fara magana da Dan dako kanta. "Aa" kawai tace Sannan yaci gaba da cewa " Momy ta D'ade tana son nayi Aure ita Dady da kuma Haiday ke harma Hanan tanason na kawo mata Aunty, Amma da yak'e komai na Allah ne sai yanzu Allah ya *hadani dake* ina fatar samun k'arbuwa gareki in hakan ta zanyi farinciki kuma idan sabanin haka ta faru shima bazanga laifinki ba saboda komai nufin Allah (Abin wasu suka kasa ganewa kenan). Yaci gaba da cewa "Anas ya gayamin komai game dake sannan kuma nima naga wasu saboda nasan gidanku hasalima a can na gank'i, nasan gidane na k'aramci, nasan km kema kinsan kanena saboda skul daya kuke kuma a yanda yayi suna nasan ba zaki rasa saninsa ba, mema suke k'iranda...yauwa D one" Da sauri ta d'ago k'anta a d'an razane, murmushi yayi yace " nasan zakisan lil saboda rigimarsa" "Haba gaske dai k'irjinta ya buga ya buga ta taji ya k'ira sunansa, koda yake normally in aka kira suna irin nasa haka takeyi saboda sam batason taji abunda ya shafesa, sannan ashe dan uwansa ne shiyasa taji muryansa tayi mata familiar a ranar da suka fara *haduwa* ta kasa tuna inda tasan muryan sai yanzu ta gane, d'uk da sam basa k'ama saidai ta jini amma kam voice nasu iri dayane saidai wannan yana d'an saurin bak'i, yayinda Haydar ke magana kamar a d'ole....... " Kuma gashi da nuna isa da izza" maganansa ce ta d'awo da ita daga zancen zucin da tak'eyi tace. "Nakan Ganshi a skull kuma inajin labarinsa" haka k'awai taji ba zata fad'a masa er tsamarda suke ba . "Lil kenan! Rigima, yanzu dai Malamata kinji Anfara kira sallah nizan tafi, sai naji daga gareki, nan zuwa yaushe zan jiraki, kiyi tunani sosai sannan kiyi shawara da wad'anda kika yarda dasu" Umar ya fada yana Dan smile. Jitayi ya burgeta daga ganinsa zaiyi sauki kai, jinjina kai tayi sannan tace " inna gama zakaji" Yace "Ok! Zan iya samun digit naki " ya fada yana mika mata hannunsa, karamar wayarta ta mika masa ya saka number sa ya kira sannan ya dauko wata er karamar Leda gefensa mai kyalli ya hada da wayanta ya mika mata. Wayar kawai ta karba snn tace "Aa pls ka barshi k'awai" Cewa yayi " ni kuma kinga bana kyauta a maidamin, ya za'ayi kenan?" Shiru tai masa,ganin tayi shiru ne yasa yace "any way nizan wuce kuma bazan koma dasu ba" yana gama fadi ya mike, itama mikewa tayi ta rakashi suna fita falon suka had'u da Anas ya fito da shima, komawa tayi falon a kunyace yayin da Anas ya fara mishi tsiya yana fadin. "Tsuntsun luv aina dauka a ciki zakayi Sallan" Umar yace" Aa kwana dai zanyi ba sallah ba" Haka dai Anas yayi ta masa tsiya shi kuma yana ramawa, nan sukayi Alwala suka wuce masjeed.. Siddiqa kuwa tana komawa ta zauna duk k'unya ta rufeta ganin da Anas yai musu,zama tayi saida ta tabbatar sun wuce sannan ta dauki tray d'inta ta aje mishi daya danci snacks din kadan sannan ta dauki ledar ta wuce cikin gida.. ** ** ** Haiydar kuwa sallama sukayi da Saleem bayan ya saukesa gida, shima gida ya wuce saboda gajiye yake, bude masa get mai gadi yayi suka gaisa dashi da sauran securities dake duty sannan ya wuce parking space, har ya fito zai wuce part dinsa yaga motan yayan nasa ta danno, tsayawa yayi harya k'araso ya fito musabaha sukayi sannan Haiydar yace" daga ina haka bros" "Tadi" Umar ya bashi Amsa a tak'aice. Daria sosai Haiydar yakeyi (ni kuma nace dama yana daria kenan) Sannan yace" Kaine zakayi tadi Yaya?" Smile Umar yayi yace "am serious lil joke a part" Zaro ido! yayi snn yace "wace mai sa'arce? A ina take? Yace yana jiran amsa. " Wannan saurin haka lil,to ai bata ansa tana sona ba ka bari harta yadda sannan na hadaku abinda k'awai zan gayamaka shine a skull dinku take" Umar yace . "Hmmm! Yaya ba macen da ta isa ta k'ika, meye sunanta zan nemota dolenta ta soka tunda kana sonta" "Aa lil! Ba haka ake soyayya ba, shifa so nemansa akeyi da lalama bada k'arfi ba saboda haka ka bari nizan lallaba da kaina har nayi nasara" Daga kafada Haiydar yayi yana tabe baki yace" well wish oll d best, nixan shige saboda a gajiye Nike wlh" Sallama sukayi sannan kowa ya shige part dinsa, Haiydar kam mamaki yakeyi wai a lallaba shikam ina bazai iya ba (ni kuma nace Aa fah gadanga banda cika mouth) lolx Siddiqa kuwa bayan ta shiga cikin gidan daki ta wuce ta isko Ramla na sallah,dake ita batayi kwanciya tayi kan gado ta shiga tunani game da Umar. Tasan dai bawai tanajin sonsa bane a ranta amma kama zataso akan dalilai uku, na farko ya hada abubuwanda za'aso mutum dominsu, yanada k'irki, Addini, abin hannunsa, kyau, na biyu kuma kodan tayi maganin Haiydar zata soshi, na uku kuma ta barma kanta sani, haka dai tayi ta tunaninta har Ramlah ta sallame tace mata "kindawo Babyn Aunty" Kaita girgiza mata, sake cewa Ramlah tayi "toya kukayine" gayamata yadda sukayi tayi sannan ta bata ledan da ya bata, budewa Ramlah tayi perfumes

Chapter 4 of 16