Share this page
mai kama da an daurawa muciya Zane ta fiki, saidai ma ke ki fita, tome yasa yake sonta amma ke baya sonki? Kiyi tunani sosai sannan kiyi amfani da damarki ki kwatarwa kanki 'yanci, idan kuwa kika tsaya kallon ruwa sai kwado yayi maki kafa, so kawata think deeply an find d best solution 4 ur self ur female." Nutsuwa tayi sosai tanajin shawarar da aminiyar tata ke bata, kuma da dukkan alamu abin na shigarta yadda ya kamata, haka Shamcy taci gaba da bata shawarwari har time d'in lectures d'insu yayi suka shiga hall. Sai 2 suka fito, napep suka Tara saida ya fara sauketa Shamcy na kara jaddada mata tayi iya k'ok'arin ta sai ta jita sannan sukayi sallama (k'awar kirki kenan mai doraka a hanya idan ka baud'e, Allah ka datar damu da k'ayawen Arziki ameen). Haiydar kuwa bashi ya tashi ba sai 7:50am, cikin sauri yayi shirinsa cikin suite brown, da niyyan zuwa office dan tunda aka bude company ninsa bai k'ara zuwa ba, sai yau da yakeda niyyan zuwa, parlour ya fito ganin ba kowa yasakashi sanya mai aiki (wacce Mami ta samoma Fuu), kawo masa ruwan zafi duk kuwa da breakfast da yaga ta jera, amma baijin zai iya cinsa, coffee kawai yasha sannan ya d'an zauna jiran Siddiqa ta fito ya sauketa skull. Jin shiru bata fito ba gashi time na tafia ya saka shi shiga d'akinta ya duba ko shiri takeyi, wayam ya gani ba kowa har toilet alaman ta fita kenan, kwafa yayi yace "wato yarinyar nan ta riga ta gama renani shine zata fita ba tare dana Sani ba, hmm! zamu gauraya ne" ya fad'a yana ficewa daga d'akin. Direct parking space ya nufa domin wucewa office, dai-dai nan motar Fuu ta shigo tsayawa yayi saida ta k'araso sannan ya isa inda tace da murmushi dauke a fuskarsa. Itama murmushi take tace "Baby ina zuwa da sassafen nan?" "Office zanje my love" ya fad'a a tak'aice. "OK, ka ganni sai yanzu ko, wallahi wata kawatace tazo garin nan naje don na daukota, shine na samu ta sauka a hotel, naje mukayi ta hira koda na ankare 1 tayi shine kawai na kwana acan, saboda gudun bata gari." "Ba komai my love, hakan da kikayi yayi dai2" dan shi Sam baya ganin laifinta ko kadan komai tayi dai2 ne muddin suna tare. Peck ta bashi a kumatu sannan tace "saika dawo" ta wuce ciki shima yaja mota yabar gidan. Tana shiga breakfast kwai ta narka sannan ta shige d'aki ta fad'a kan bed sai bacci, tun jiya har yau suna Abu daya ai dole ayi baccin hasara, Allah ya shirya. Zaune yake a office ya had'a kai da desk ga aiki birjik gabansa amma ya kasa komai. Turo kofa akayi aka shigo d'agowa yayi ganin Saleem ne(dayake nan yake aiki shima a matsayin manager) yasa ya d'an saki fuska, k'araso yayi yana fad'in. "Kaga babban yaro D one in d city, angon Maryama da Fauziya yaro da kudi abokin tafiyar manya, manya masu duniya." Wani malalacin murmushi ya saki sannan ya bashi hannu suka gaisa yace "Leem yane, ya Madam?" "Qlau Madam yanzu ma na sauketa skull, tana can tare da Uwargidanka." "OK" kawai yace. Saleem yace "Dude meye Damunka wai kaida kake angon biyu amma banga kana shining ba, what is going on?" Tsaki yaja yace "lahe kawai abokina wadannan duk shirme ne, basa iya kula dani?" Smiling Saleem yayi yace "hadda mintin zuciyarka?" "Hmm! Ai itace kan gaba, bata iya komai bafa common dafa ruwan zafi wahala yake bata, ita kuma waccen matar cushen Sam bana ganemata yanzu zata maka abin kirki anjima ta juye Dana rashin arziki haka take kamar hawainiya, nidai ganinan kawai sunan nayi Aure." "Kai abokina yanzu kenan ya kakeyi?" "Ya kuwa zanyi kasan dai da kunya naje gun Momy da sunan cin abinci, sai tace meye amfanin matana, ni kuma ba iya cin abincin 'yan aiki nikeyi ba, gani nan dai daga coffee sai tea sai snack kamar dan wahala." "Dude kamata yayi ka lallab'a ita Bestynmu tunda ta iya kana danci gurinta." Tab'e baki yayi yace "tab wancen 'yar kunamar nasan ba yadda zatayi ba, tunda tayi mana na satin Aure ta tattara ta aje saidai tayi na dai bakinta, gashi ta bala'in renani." Daria Saleem yayi yace "lallai kana tare da mata, amma da zakaji shawara..." Daganan ya fara bahi shawarwari yanda zai b'ullo musu. Siddiqa tana isa Jakarta kawai ta aje sannan ta wuce kitchen ta fara aiki, abinci mai rai da motsi tayi tare da taimakon Zubaida da Hanan dake tazo gidan. Tuwon semo tayi da miyar kibewa danya wacce taji naman rago, sai ferfesun chicken, sannan ta had'a zobo, suka jera a dinning, gyara parlon tayi sosai ta goge ta baza turare sai k'amshi ke tashi. Sannan taje d'aki ta tsala wanka ta shirya cikin wata gown ta material peach color, sannan ta feshe jikinta da perfumes masu sanyin k'amshi, fitowa parlour tayi ta zauna zaman jiran isowar oga D one........... _pls kuyi manage da wannan nepa ne sukayi Lalata_ πŸ˜”πŸ™Š ✍🏻 πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Based on love story_ ) *Written* *By* πŸ’„ ~Meryerm Abdool~ πŸ’„ ```Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa :-``` _Duniya wani d'an jin dad'i ne, mafi jin dad'in ta Wanda ya dace da mace ta gari._ *ina kuke sister's, muyi k'ok'ari mu kasance ababen jin dad'i ga mazajenmu ba fitina ba, Allah yasa mudace* *Page* 56&57 Fuu wacce tunda ta kwanta, bata tashi ba sai bayan la'asar, ba maganan sallah wanka kawai tayi ta saka best da bomb Short, ta fito main parlour dan Samar wa cikinta abinda zataci. Da kallo tabi parlon ganin komai neat ga daddad'an k'amshi dake tashi ko'ina, abin ya burgeta (k'azanta batada amfani ko kai k'amine kana son kaga anyi tsabta, kowa nason kallo tsabta aikatawar ne dai sai Mara kyuya). Ganin Siddiqa yasa tace "sisto ashe kin dawo da skull?" "Eh na dawo ya gidan?" Fad'a ba tare data kalleta ba. Itakam Fuu ji take kaman taje ta rungume Siddiqa saboda wani feeling da takeji akanta, ganin inta dad'e a parlon za'a iya samun matsala yasa tace ladi mai akinta ta kawo mata abinci tana jiranta parlon ta, wucewa tayi tana sak'a yadda za'ayi ta d'and'ani Siddiqa dan kuwa abin ya fara damunta, gashi ko gaisuwar kirki basayi (aiko kyayi kya gama, gani nan bari nan dukiyar uban wani). Da kallo Siddiqa ta bita sai wani karkad'a jiki take, amma ina ba abinda ke motsi komai a shafe kamar sanda. Lolz "Allah ya kyauta" Siddiqa ta fada sannan ta maida hankalin ta ga kallon da take. Haiydar kuwa sai 4 yabar office saboda ayyukan da suka sakashi gaba, gidan Momy ya wuce bayan sun gaisa ya dan zauna yanaso ya tambayi abinci yana kuma jin nauyin hakan, daga k'arshe dai tambayan Hanan yayi yace yaji gidan shiru, nan ta gayamai tana gidanshi da Zubaida tazo tabita. Harya tashi zai wuce Momy ta kirashi, dawowa yayi ya zauna, tace "Son meke damunka ne naga ka fad'a ka wani hargitsewa, meye matsalarka?" Shafo k'eyarsa yayi sannan ya yanko mata 'yar banzar, yace " Momy nad'anyi zazzabi ne 2 days d'in nan, sannan kuma ga pressure office kinsan ban saba ba" ya fad'a yana kwabe fuska. Cikin d'an tashin hankali da nuna kulawa tace " Subhanallah son kaje hospital kuwa?" Girgiza kai yayi yace "kada ki damu Momy nasha magani kuma na samu sauk'i." "To Allah ya kara sauk'i, office kuma da sannu zaka saba kaji" girgiza kai yayi alaman gamsuwa sannan yayi mata sallama ya wuce. Tafe yake yana sak'a da warwara, tabbas idan yayi wasa yunwa illa zatayi mishi, k'arshe dai da yaga no way 2 go, ya yanke shawarar kin na maid hakanan toya zaiyi. Tun farfajiyar parlour k'amshi ya fara tarbonsa, da mamaki ya shiga gidan yasan tunda Siddiqa ta daina gyarawa saidai mai aiki da Zubaida suyi, shima d'in ba wani mai kyau ba. Mamaki bai gama cikashi ba saida ya shiga ciki, yana sallama Siddiqa ya gani a parlon tasha kwalliya, ansa sallamar tayi sannan ta tashi taje ta hugging d'insa tayi sannan tayi mishi sannu da zuwa cikin sakin fuska ta ansa briefcase d'insa hannunta cikin nashi ta jashi zuwa d'akin sa. Binta yayi kaman rakumi da akala, ko magana ya kasa yi, cikin ransa kuma fad'i yake "to yau kuma da wacce tazo" haka ta kaishi d'aki, toilet ta shiga ta had'a mishi ruwan wanka sannan ta fito tana fad'in. "Ga ruwan can kayi wanka, idan ka fito ur food is ready" sannan ta fice tana murmushi ba tare data jira ansar sa ba. D'an tab'e baki yayi sannan ya fad'a toilet yayi wanka, shiryawa yayi cikin jeans baki da shirt peach color dark, sumannan tasha gyara sai k'amshi yake zubawa, yadai fito D one sak. Cin abinci yake cikin kwanciyar mind, duk da bai nuna zalamarsa ba, amma saida Siddiqa ta fahimci yana tare da yunwa, har ta fara zargin kanta na rashin kula dashi, sosai yasan yayi missing girkinta sai wata nutsuwa ke shigarsa kuma gashi tayi favourite d'insa, saida ya cinye Wanda ta zuba masa sannan yasa sob'o, duk wannan bidirin da ake fuu batada labari batama San ya shigo ba. Fitowa tayi dan d'auke ruwa saboda na fridge d'inta sun k'are, sai ganin shi tayi yana goge bakinsa da tissue alaman yanzu ya k'are cin abinci, ta d'anyi mamakin ganinsu tare saidai bataji komai ba( son na karya ne, sha'awa ce kawai). Cikin karairaya da yanga ta isa gurinsa, dafa shi tayi sannan tace "Baby Ashe ka dawo ban Sani ba." Lokaci d'aya ya tattara duka hankalin sa gurinta, ya canja daga D one zuwa soko, yace "um...ai yanzun na shigo my love, yanzu ma shirin zuwa gurin ki nakeyi sai kika fito, hope dai kina lafia ba wata matsala?" Cikin jin dad'i tace "lafia lau baby, ya office d'in?" Ita kam Siddiqa ganin an manta da ita yasa ta sulale ba tare da sun Sani ba, tana mamakin wannan irin so da Haiydar ke yima Fauziya abin ya wuce hankali, amma ta k'udiri kwatarwa kanta 'yanci cikin sauki. Yanzu kam Haiydar baida matsala ta gefen abinci Siddiqa ta kiyaye masa cikinsa, ta b'angaren sha'awa ma ba laifi yana rage zafi da Fuu. Fauziya kuwa zuwa yanzu ta samo 'yan uwanta anan Bk ta wad'anda dama can sun iya da kuma wad'anda take koyawa, har gida take kawosu suyi iya shegensu, Haiydar ba magana yake ba, ba ruwan sa komai tayi dai2 ne. Tsakaninsa da Siddiqa kuwa ba laifi zasu gaisa har su d'an tab'a hira sometimes, don tana mishi hidima. Siddiqa kam abin yanzu har tsoro yake bata irin yadda Haiydar ke rawar jiki gaban Fauziya abin ya wuce so saidai tsoro, bakace Haiydar ne D one in city ba, abin gwanin tausayi idan ka gani, sannan ga kawo mata barkatai da takeyi na yau daban na gobe daban, ita kam abin na d'aure mata kai. ********************* Wata rana ta fito zataje kitchen don dora girki sai taji Fauziya da k'awayen sai shewa suke suna zugata wata daga cikinsu ce tace "wallahi k'awata kina abinda kikeso, ga mijinki sai yanda kikayi dashi, kina juyashi son ranki, k'awata kina buro'uba fa." Wani shu'umin murmushi tayi tace "kibar d'an iska, aiba a banza na barshi ba, da haka kawai ne ko kallo ban isheshi ba, ya tsaneni sosai, shiyasa nayi maganinsa na auresa nake juya shi yadda nakeso" ta fad'a tana daga musu gira. Shewa sukayi suna fad'in "kinyi dai2, saidai kam ki fad'i sannu kada munafukai suji fa." "Hmm! Kada Ku damu yau mune da gidan muyi abinda mukeso" ta fad'a tana daria, dan batasan Siddiqa ta dawo ba. Siddiqa kam da tayi niyyan fita taji hirarsu ta tsaya dask'arewa gurin tayi saboda mamaki, komawa d'aki tayi cike da mamaki tace "Kai duniya mutum mugun icce, kai mutane bakyau" sannan ta kira Shamcy ta bata labari abinda taji da yake duk abinda ke gudana tana gayamata. Shamcy batayi wani mamaki ba ga yadda take ganin take-taken Fuu da kuma yadda take bata labari tasan zata iya aikata haka, shawara ta bata akan tayi k'ok'ari ta karya sihirin in yaso daga baya suga me zasuyi, ta ansa mata da yanzu kuwa zata kira liman, sannan sukayi sallama. Limamin Masarautarsu ta kira bayan sun gaisa yace " 'yata Maryama meya farune?" Da yake dama duk Abu ya shige mata duhu shi take tuntub'a ya warware mata, bayani komai tayi mai. Yace" to tad'an bashi lokaci kad'an ya k'ara bincikawa" godia tayi masa sannan sukayi sallama. *One hour later...* Ya kirata ya fara mata bayani kamar haka tana rubutawa :- "Da farko zaki zamo ganyen magarya guda 7 sannan ki samo duwatsu guda 2 masu dan girma, saiki nik'a ganyen magaryar akan duwatsun, sannan ki samo ruwa roba ki juye ganyen magaryar kiyi alwala mai kyau ki zauna ki nutsu, kiyi bismillah ki karanta fatiha kafa 7 kowacce 1 kin kika k'arshe ki tofa a ruwan. sannan ki karanta aya ta (225) cikin suratul bak'ara sau 7 ki tofa, sannan aya ta (117) zuwa (122) na suratul a'araf sau 7 ki tofa, sai aya ta (79) zuwa (82) cikin yunus, sai aya ta (65-70) Dhaha sau 7, kafirun x7, ikhlas x7, falak' x7, nas x7 duk a tofa a ruwan, sai asha ayi wanka na tsawon kwana 7, sannan a samo dabino ajwad guda 7 a kowacce rana da safe, da yardar ubangiji za'a samu waraka." Godia sosai tayi masa yace ba komai ai yiwa kaine, sannan sukayi sallama. Ta kira ta gayama Shamcy, ta kuwa k'arfafa mata gwiwa sosai. Tasa an samo mata duk abinda ya dake ta kuma fara aiki, sai fatan samun nasara, cikin dubara irin ta mata ta saka shi yake shan ruwan dacin dabinon. Fauziya ce zaune cikin d'akin ta, yau k'awayenta ba Wanda yazo gashi wani irin feeling takeji, tana cikin hakane ladidi mai aikin ta ta shigo ta kawomata lunch, har ta juya zata wuce zata wuce Fuu tace "ke zonan" zuwa tayi kusa da ita a lababce, "cire tufafinki" ta fad'a cikin d'aure fuska. Zaro ido ladidi tayi sannan ta toshe bakinta, "ke kiyi abinda nace, ko yanzu nayi K'asa-k'asa dake anan" cikin kyarma ta shiga tub'ewa. Janyo ta tayi zuwa kan bed ta fara shafata da lalubaeta, itakam ba abinda take sai kyarma, takai hancinta wurin wuyanta taji doyi turata tayi saida ta fad'i k'asa tace. "Wa wuya wacce bata Wanda wanka dalla ficemin daga d'aki" a firgice ta mik'e ta kwashi kayanta zata fice. Dakatar da ita tayi ta hanyar cewa " ke tsaya nan ki saka kayanki, kuma duk kika yadda naji maganar nan wje saina kasheki" ta fad'a da tsawa sannan ta mik'e ta saka wata gown da yalolon gyale ta fice daga d'akin. Ladidi kuwa tana saka kayanta bata zarce ko'ina ba sai part d'in Siddiqa da yake sun d'an saba kuma irin yarannan ne masu shegen surutu, tana zuwa ta hau gayama Siddiqa abinda ya faru, saurin kwabaeta Siddiqa tayi tace kuma kada ta k'ara kawomata labarin wani kuma kada ta yadda ta gayama wani. Sai bayan ta fita Siddiqa ta tace "kai jama'a wannan duniya! Gaske ake tara mana mata a gida Ashe da walaki, Allah ya shirya." *2days later...* Yayi dai2 da kwana 7 da fara aikin Siddiqa, Haiydar zaune office duk kwankinan jin shi yake wani iri kamar ana sauke mana wasu kaya bisa kanshi, yau kam ji yayi fayau dashi uwa an sauke masa guduma aka, ga wani tsanan Fauziya dake mamaye ranshi harma yafi Nada, ganin kamar mafarki yakeyi tun daga son Fauziya, Auren ta zuwa yanzu, jin yai kawai yaje gida ya duba shin hakan ya faru da gaske. Fita yayi ya gayama sakatariyarsa zaije gida ya dawo, sannan yadau motarsa ya wuce..... *muje zuwa friends yanzu akeyinta* πŸ€” ✍🏻 πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD'UWATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Based on love story_ ) *Written* *By* πŸ’„Meryerm Abdool πŸ’„ Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* ( *P.M.L* ) ```An karb'o daga baban Abdurrahman, Abdullahi bin Masa'ud (Rd) yace: naji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:-``` *Ana tattara halittar d'an Adam a cikin uwarsa, tsawon kwana arba'in yana maniyi, sannan ya koma jini kwatankwacin haka, sannan ya koma tsoka kwatankwacin haka, sannan a aiko masa mala'ika ya busa masa rai, ya kuma umarceshi da kalmomi guda hud'u, littafin arzikinsa, ajalinsa, aikin sa, shiryayye ko fitsararre, ya kara da cewa na rantse da wanda raina yake a hannunsa, d'ayan ku zai kasance yana aikata aiki irin na 'yan Aljanna har sai abinda ya rage tsakaninsa da ita kwatankwacin kwayar azarra sai littafinsa ya rinjayesa ya aikata aiki irin na 'yan wuta kuma ya shige ta, haka kuma d'ayan ku zai kasance yana aikata aiki irin na 'yan wuta har sai abinda ya rage tsakaninsa da ita kwatankwacin kwayar zarra sai littafinsa ya rinjayesa ya aikata aiki irin na 'yan Aljanna kuma ya shige ta.* Bukhari da Muslim suka ruwaito (arba'una hadith). _'yar uwa idan kikaga mutum na wani aiki wanda bai dace ba, idan bazaki nema mishi shiriya ba, to ki kama bakinki, dan bakisan meke tsakaninsa da Ubangijin shiba_. Allah yasa mudace duniya da lahiraπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ» *Page* 58&59 Tafe yake cikin mota kanshi gaba d'aya ya d'aure, tunani kawai yakeyi to wai ya akayi har ya Auri Fauziya, yarinyar da yafi tsana a duniya, wai itace matarsa har yayi tarayya da ita, tome ya sameshi har take juyawa kaman waina bugun sitiyari yayi da k'arfi yace "no it can't happen" sannan ya k'ara gudun motarsa dan ya isa ya ganema idonsa gaske ne ko mafarki. Horn yakeyi ba k'ak'auntawa, da sauri gateman ya bud'e masa get, ko parking space bai isa ba ya tsayar da car d'in ya fito, kai tsaye cikin gidan ya nufa cikin sauri. Gateman kam mamaki ne da tsoro ya kamashi ganin yanayin da mai gidan nasa ya shigo fuskarsa ba sauki duk da kuwa dama can bai cika fara'a ba, amma na yau yafi na kullum dan ko gaisuwarsa bai ansa ba, sannan kuma meya dawo dashi a wannan lokacin da bai saba dawowa ba tunda ya fara zuwa aiki? Ganin ba ansa ne yace "Allah yasa lafia" sannan ya koma gurin zaman sa. Yana shiga parlon direct part d'inta ya nufa, ganin ba kowa a parlon ne yasa kashi shigewa d'akin..... Lokaci daya jininsa ya daskare, idonsa suka firfito, hankalin sa ya tashi saboda abinda idonsa yayi tozali dashi, ba komai bane face Fuu ce da wata mata haihuwar uwarsu kan bed, sunyi nisa cikin masha'a hankalin su yabar jikinsu. Dak'ar yaja k'afarsa zuwa parlour ganin sam basu san shigowar sa ba, kan 1 seat ya zauna ya dafe kansa dake barazanar rabewa gida biyu saboda tsananin tashin hankali, shidai yasan tunda uwarsa ta haifesa be tab'a ganin bala'i irin wannan ba duk kuwa zuwa club d'inda yakeyi, kuma wai cikin gidansa. Tashi yayi zunbur kamar wanda aka tsikara ya zare belt d'in suit d'insa, ya koma d'akin, abin tak'aici still suna manne da juna suna Lalata(Sadnaf), cikin fushi ya rik'e belt d'in da kyau sannan ya fara aika musu sak'on tsumagiya, bayan ya kulle k'ofar da key. Fauziya da abokiyar wartsewarta, ba zato sukaji saukar bulala, Wanda shiya dawo dasu hayyacinsu, ganin Wanda ke dukansu yasa ta zare ido cikin kuka take mishi magiya akan yayi hak'uri, ganin sam bayajin magiyarta ne yasa ta shige jikinsa, ta rungume sa da dukka hannayenta tana fad'in. "Pls baby kayi min rai wallahi yau d'aine kuma shima sharrin shaidan ne" tana yi tana shafa bayansa cikin salon iskanci, ta d'auka da ne da yake mata biyayya. Hankad'a ta yayi har saida kanta ya had'u da gado, sannan ya jayo k'awarta data kai bakin k'ofa da niyyan fecewa ta murd'a tajita kulle, had'e su guri d'aya yayi yaita jibgar kayan banza har saida ya tabbatar yayi musu lilis sannan ya barsu. Main parlour ya koma ya dauko biro da takadda ya rubuta mata saki uku tsaf, sannan ya koma d'akin, suna nan inda ya bar su, sai maida numfashi suke, tsawa ya daka musu yace. "Shegu 'yan iska, Ku tashi maza Ku shirya na baku ko yanzu na k'ara muku wani dukan" aiko jiki na rawa suka daddafa gina suka mik'e sai ko tsayin kirki basu iyawa saboda jikin da sukaji. Da mugun kallo ya bisu sannan yace"na Baku 2mnt ku shirya, inba haka ba hmm" sannan ya fice parlour. Aiko a daddafe kowaccen su ta zura rigarta bamai taimaka d'aya, ko magana basa iyawa, koda ya dawo sun saka riguna sun zube k'asa kaman kayan banza, paper ya jefa mata sannan yace "to ibilishiya magajiyar 'yan iska, duk da bansan ya akayi na Aureki ba, kuma kike juyani yadda kikeso, koma dai meye yau dubunki ta cika, Allah ya tono minke inda kika binne kanki, sannan ba zanyi miki Allah ya isa ba, na barki da halin ki." Sannan ya kalli k'awarta yace "kema matsiyaciya 'yar uwarta ko haka na barki na fanshe ladan iskancin da kuka yimin a gida sannan ya jasu kiii kaman kayan wanki ya kaisu waje ya zubar sannan ya koma ya kwaso musu wayoyinsu da mayafansu cike dayi musu kashe din ya basu nan da 5mnt subar unguwar ko yayi k'asa-k'asa dawo sannan ya koma ciki. Duk abinda akeyi gateman dan kallo ya koma, yanaso yayi magana yana tsoron mai gidan nasa ganin yanayinsa ba rahama sak *Haiydar*. *********************** Su Fauziya kuma ganin ba sarki sai Allah kuma idan sukaci gaba da zama gurin ya fito ya samesu sun san sauran, yasa k'awar tata daurewa ta kira wani dak'ar ta iya magana ta gayamai yazo ya d'aukesu gidan Fuu, minti kad'an sai gashi ganin su cikin wani yanayi yasa shi tambayan ta " lafia kuwa" tace "ba lokacin magana bane fara kaimu gida tukun" taimaka musu yayi suka shiga sannan yaja ya wuce. *3:00pm....* Siddiqa ta shigo gidan ganin Haiydar baije d'aukar taba yasa ta shigo napep da sallama ta shiga parlon. Haiydar dake zauna parlon tunda ya koma ciki bai fitoba ko sallar zuhr anan yayita, yana zaune dafe da kansa dake sara mishi, a haka ya ansa sallamar ba tare daya d'ago ba, k'arasowa tayi kusa dashi ta dafashi tace. "Ya Haiydar menene na ganka wani iri meya sameka?" Ta shera mishi tambayoyin cikin rud'u, ganin yadda idonsa ya kada yayi ja. Cewa yayi "ba komai! Ki shiga ciki ki shirya kizo muje gidansu Momy" badan ta gamsu ba, mik'ewa tayi jiki ba kwari taje d'aki ta watsa ruwa sannan ta sake kaya, ta sameshi parlor, tashi yayi yai gaba ita kuma ta bishi baya da tunani barkatai a ranta, suka shiga mota suka wuce. Su Fuu bayan driver k'awarta mai ansa sunan Halima wacce suke kira Halidubu ya kaisu gida ya taimaka musu suka shiga ciki mamakin abin ya samu Uwargijiyar tashi a gidan k'awarta ita da k'awar tata. Maikin ta tasa had'a musu ruwan zafi, suka gasa jikinsu sannan ta kira doctor ya dubasu ya basu magani, sai lokacin suka samu damar magana Halidubu tace. "Fuu dama haka mijinki yake da muguwar zuciya Mara imani, tabbas zai iya kisa." "Hmmm ki bari kawai k'awata ni kaina bansan haka yake ba,although nasan yanada zuciya but tunda mukayi Aure ban tab'a ganin shi cikin yanayi irin na yau ba, bana raba daya biyu nasan magani ne ya karye." "Kai dear har yanzu kinada saura bakisan namiji ba, hmmm Namiji kanen ajali(Fareedat Musa) shiyasa kikaga tuni na balle nawa Auren nake zamana cikin kwanciyar mind, shiyasa na fada miki ki kashe Auren kawai kafin maganin ya karye ya walakantaki kika k'iji to yanzu wa gari ya waya?" "To aini dama nayi Auren saboda gujewa sa'idon mutane, sai kuma dan Mami na ta samu nutsuwa, kada itama ta fahimci halin da nake ciki, amma bayan haka meye acikin aure banda takura( a naki tunanin ba)." Sannan ta k'ara da cewa "dear menene mafita yanzu?" Nisawa Halidubu tayi tace "bakida matsala k'awata dama na gayamiki akwai turawan da suka gayyaceni dana koma can su k'asarsu ba ruwan kowa da sha'anin kowa akwai freedom sosai, ke in tak'aice maki har Auren jinsi anayi yana cikin constitution d'in k'asar, inkin yadda zaki bini duk yadda za'ayi yau zan sama mana visa gobe mubi flight d'in safe

Chapter 11 of 16