shi kuma yana Shafa sumar kanta da take fidda wani sihirtaccen k'amshi, kallo suke cikin tashar zee TV wani series waishi *jamai raja* da yake itace mai kallon don Siddiqa akwai son India, shikam hankalin na kanta gaba d'aya.
Jan hancinta yayi saida tayi 'yar kara ta turo baki tace "Ya Haiydar wannan muguntan fa so kake ka ida cire gutun hancin ka huta ko?" Ta fad'a tana mishi hararan wasa.
"Aa to nake dai na k'ara mishi tsayi, yawwa bana ce miki banason ya Haiydar ?"
"Oh to shikenan zance dear" tab'e baki yayi yace "nop banason dear ai kowa ma za'a iya kiransa dear, someone special nakeso."
Daga kai tayi alaman tunani sannan tace cikin siririyar muryarta "piyaa."
"Wow! What romantic Indian name, me yake nufi baby love?"
Cikin rad'a tace "masoyi" tare da b'oye fuskarta cikin k'irjinsa, kara rungume ta yayi shima cikin rad'a yace.
"Ina matukar kaunarki Maryam, ina sonki! Hmm no word can express how much I adore u, Allah ya barmu tare cikin Aminci, ya azurtamu da 'ya'ya na gari, ka kauce musibu da shaidan a cikin Auren mu, ya kuma bamu hak'uri da juna" tare suka ansa "ameen."
Haka couple d'in sukaci gaba da gudanarda soyayyar su cikin tsabtacciyar kauna, kowa k'ok'arin yayi abinda ran d'an uwansa zaiyi farinciki yake, notification letter ya rubutu ya dauki hutun one month dan angwancewa, Saleem kuwa hada kiransa danyi masa tsiya yace.
"D one matar tushe ta rikita ka kenan" tsaki yayi yace "waya gayama matar cushe ce dan sa eyes, matar so zakace" dariya yayi, yace" kai nagode wa Allah daya nunamin wannan ranar ban mutu ba, dama ai na gayamaka".
"Hhhhhhh! Dama aini ma ina sane nakeyi" nan da yaita yi masa tsiya Shiko yana bashi ansa dai-dai shi.
Haka itama Shamcy ta kira tayi mata tata tsiyar, su Siddiqa kam ba bakin magana wai barawo a hannun mata, sai cewa tayi "ni kizo don Allah besty inason ganinki fa" tace "wah! Ba yanzu ba sai anyi dashe tukun" tace.
"Aa ba dashe za'ayi ba girbewane za'ayi" daria tasa mata ita kuma ta kulu ta kashe wayar....
*A week later....*
Sai ga sammaci daga koto anyi kasan Dady da Haiydar, Abu kamar wasa sai gasu a kotu, wai tana karansu akan, sakin izgili da duka, sai kazafi da akayima mata, shiyasa ta gudu.
Chakwakiya akayi sosai kafin akawo ladidi da gateman, da kuma video da Haiydar ya dauka itama Siddiqa ta fad'i abinda ta sani, akai.
Daganan Alkali yayi watsi da k'arar sannan ace ta bi yasu kudi akan banna musu lokaci da tayi, kai tsaye sukace sun yafe, amma still saida kotu ta cita tarar 1m, sannan suka bata shawarar nemawa 'yarta shiriya...
Bakinciki ya taru yayima Haj, Bara yawa, ga ba 'yarta, ga asiri ya kara tonuwa Wanda bai Sani ba ya Sani yanzu, ga rashin samun nasara, mutane kuwa sai Allah wadai sukeyi da halinta, haka ta shiga malaman tsibbo, da bokaye, duk dan ta gano inda 'yarta take, su kuwa sun samu banza sai tatsarta suke kaman ATM card, duk ta yamutse ta jeme, ka kowa ya rabu da ita, ga miji baya k'asa be masan wainar da ake toyawa ba.....
Haiydar ne kwance a parlor yana kallon American film, yaji kamar alaman kakarin amai a kitchen, taji yayi da sauri yaje kitchen d'in.
Siddiqa ya samu duke gurin sink sai kwarara amai take rike da cikinta, kamata yayi saida ya tabbatar ta gama sannan ya wanke mata baki ya gyara gurin, d'aukarta yayi kamar baby yai sama da ita wanka yayi mata sannan ya nad'ota a towel, kan bed ya dorata, lafewa tayi tana maida numfashi.
Shima toilet ya koma yayi wanka sannan ya dawo ya shirya, bacci takeyi hani'an, tsayawa yayi ya kalleta sosai na 'yan mintuna ganin nayi yayi murmushi, da yake yayi diploma akan psychology (human learning) tuni ya gano yaron ciki tattare babyn tashi, amma yafi so suke hospital su tabbatar.
Jin an tsaya akanta ne yasa ta bud'e idon ta fes ta sauke su akansa, tashi tayi cikin jin kunya ta gyara towel d'in, sannan ta taje ta shirya, kaman ba ita ba.
Bayan ta ya dora kanshi yace "baby love when last kikayi period?"
Zame kanshi tayi ta kalleshi tace "me kake nufi piyaa? Nifa ba ciki bane bane, ko amai da nayi dazu, ninaja saboda Abu ta tsaya min a mak'oshi shine nasa yatsa, ya sakani amai" ta fad'a tana turo baki.
"To naji zazzabin dare fa na meye" ya fad'a yana murmushi.
Cikin kulewa tace "yanayin gari mana" dariya yayi yace "sai yanayin gari kam, to naji shirya muje hospital".
Ta gama k'ulewa akan dariyar yake mata tace " bazanje ba" tare da haye bed abinta........
_Hhhhhh, nima dai dariyar nayi, woo Siddiqa rigama_ πππ.
βπ»
πMeryerm Abdoolπ
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *_HAD'UWATA DAKE_*
ππ»ππππ
ππππ
( _Based on love story_ )
*Written*
*By*
πMeryerm Abdoolπ
Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*P.M.L*
```Manzon (S.A.W) yana cewa:-```
_Duk Wanda yayi da Allah da ranar k'arshe, toya fad'i alkhairi ko yayi shiru, duk Wanda yayi imani da Allah da ranar k'arshe, to ya kyautatawa bak'onsa, Wanda yayi imani da Allah da ranar k'arshe, kada ya cutar da makwabcinsa_.
*sisto nida ke, dasu, muna aikata karantarwar manzonmu kuwa? Hmm Allah ya bamu ikon gyarawa ameen.* ππ»
*Page* 64&65
Ganin tayi fushi ne ya sakashi danne dariyar ya bita gadon yana lallabata da bata hak'uri akan suje hospital a duba lafiyarta, cewa tayi "waini piyaa meka d'auki ciki ne, duka yaushe ne...? Ta fad'a tare da rufe idonta.
Smiling yana hango wauta irin tata, yace " to naji amma dai kinsan koba komai munje a duba lafiyarki?" Cewa tayi "nifa qlau nike" ganin ta k'asa ganewa yasa ya canja maganar da cewa.
"Kin k'arasa girkin ne?"
"Aa, ya kusa dai, na rage gas d'in, barin duba, in yayi" ta fad'a tare da ficewa.
Binta yayi da kallo yace "Maryam Rigima, ko idan cikin ya bayyana ya zatayi oho!" Tab'e baki yayi sannan shima ya sauko k'asa.
Tun daga ranar, kullum sai abu ya tsaya mata a wuya, data saka yatsa sai amai, ga wani manne masa da takeyi, kullum cikin b'ukatarsa take, ba dare ba rana, har mamakin kanta take, abun har kunya yake bata, shikam gogan naka, sai wani k'iba yake da haske ya samu kaza daga sama gasasshiya.
Yanzu ma zaune suke parlour, suna kallo kwance take kan k'irjinsa, tana bacci cikin bacci abin ya tono ta, farkawa tayi, ta fara b'alle masa mab'allen rigarsa tana Shafa k'irjinsa, kallon yayi yace.
"Baby love, kin tashi?'
Daga masa Kai kawai tayi tanaci gaba da Shafa k'irjinsa, cewa yayi "menene?" Ido ta zuba mishi cikin kasalalliyar murya tace "muje d'aki" tana boye fuskarta a k'irjinsa.
Daria yayi yace "nifa na gaji" turo baki tayi tana dukan k'irjinsa tana fad'in "uhmmm banaso" tasan tsokanarta yake haka take masa da.
Tashi da ita yayi yana fad'in "muje na taimaka miki kada kimin kuka" dukan k'irjinsa taci gaba dayi tana mishi shagwab'a, shi kuma sai dariya yake mata.
Bayan sun fito da duniyar nishadi inji Haiydar, suna kwance suna suna hutawa, ji tayi abu ya tsaya mata a wuya, kin saka yatsa tayi saboda tasan mezai biyo baya.
Minti kad'an taji cikinta ya mugun juyawa sai amai shaaa, daga gadon har Haiydar da ita kanta saida ta batasu, kuma still yink'urin take, rungume ta yayi yana Shafa mata baya, tare da hura mata iska, yunk'urin take amma ba abinda ke fita, sai nishi take gwanin tausayi, dak'ar abin ya kwanta mata.
Dauk'arta yayi ya kaita toilet ya wanketa kamar baby yanayi yana mata sannu, itakam ta gama galabaita, ko ansawa bata iyayi, numfashi kawai take fitarwa, wata gown ya saka mata sannan ya kaita d'akin shi, dawowa yayi ya yaye zanin yaje ya wanke sannan ya goge katifar da k'asa, wanka yayi, sannan yayi part d'in Mommy cikin damuwa.
Bai samu Momy a parlour ba sai Hanan da Zubaida dake kallo, gaidashi sukayi ya tambayesu Momy, suka gayamai tana d'aki, haurawa yayi sama zaune ya sameta tana lazumi, jin shigowar sa ya sakata dakowa ta kalleshi, bayan ta ansa sallamarsa tace.
"Son yadai na ganka haka meke faruwa?"
Zama yayi kan sofa yace "Mom Siddiqa ce ba lafia" ya fad'a cikin damuwa.
"Subhanallah meke damunta? Kunje hospital ne?"
Nan ya fad'a mata rikicin da sukayi akan zuwa asibiti, amma bai gayamata maganan ciki ba.
"Haba gaske nake ganin ta kwananin tana rama ashe ba lafia, amma kuma Son banda shashanci saika biye mata, kasan Mara lafia ba kasafai yake asibiti ba, yanzu tana ina?"
"Tana dakina tayi bacci".
" OK bari in kira Doctor Fatyy(family doctor su)" ring 2 ta d'auka Momy ta gayamata bukatar ta, ta bata tabbacin zuwanta nan da minti 15, tayi tace suje ta ganta.
Tana kwance kan bed fuskar fayau, sai haske data k'ara, ga rama kaman tayi ciwon shekara, sai bacci take kwasa.
Haiydar zuwa yayi bakin gadon ba yaje ba kunya, ya kama hannunta da d'ayan hannun shi d'ayan kuwa yana shafa kanta dashi.
Mumy kuwa cewa tayi "Allah sarki 'yata ashe haka taji jiki" cikin ranta kuwa murna fal, ganin yanzu sun dawo normal, kallo d'aya tayi ma surukar tata ta hango alamun juna biyu tattare da ita, ta matsu Dr, ta iso ta tabbatar musu da hakan.
Kiran Momy Dr, Fatyy tayi tace ta iso, Momy ce ta fito tayi mata jagora zuwa d'akin, cikin wasa tace da Haiydar " d'an Momy wannan rikicewa haka, Abu kaman ba jarumi ba" ta fad'a tare da dafa goshin Siddiqa, zafi rau, koma tayi ta zauna tace "Jikinta da zafi, amma kuma naso idonta 2 nayimata 'yan tambayoyi".
Hura mata iska Haiydar ya farayi, Dr Fatyy ce tace " kada ka tasheta mana" amma ina aikin gama ya gama don kuwa ta tashi, ba tare data bud'e ido ba, ta k'ara jan hannunsa ta rungume a k'irjinta.
Momy tace "sannu 'yata" unexpected taji muryan Momy, ware ido tayi taga shin gaske ne, aiko nan idonta yayi mata tozali da Momy da wasu mata biyu alaman baki ne, kunya ce ta lullub'eta da sauri ta maida idon ta rufe, tare da jan blanket.
Murmushi irin na manya Momy, sannan Dr Fatyy tace "haba kanwata tashi mana, zan tambayeki kinji" ta fad'a tana murmushi.
Mik'ar da ita zaune yayi, da sauri ta janye jikinta ta zauna gefen gado kanta na k'asa, ganin haka yasa Momy ta mik'e tare da cewa "zataje ta dawo" ta fice.
Tambayoyi Dr tayi mata sannan daga k'arshe ta bata wata kwalba tace ta kawo mata fitsarinta, bayan ta kawo taba nurse tace tayi gwaji da yake sun taho da kayansu, gwajin farko saiga positive, rubutu tayi ta kawoma Dr, tana dubawa murmushi tayi sannan tayi rubuce can ta.
Haiydar ta mik'awa paper tare da cewa "congrat Mr, Haiydar ur wife is 1 month pregnant" wayyo dad'i kashe zanso kuga yanayin da gogan ya shiga, fad'a bazai yuwu ba (ku misalta farincikinsa abokai)lolz
Shawarwari ta basu sannan tayi musu sallama, Haiydar kuwa sai wani lallab'ata yake kaman kwai, ita kanta tayi farinciki da cikin komai itama zatakai ga d'an kanta, duk kuwa da taso sai ta gama sch tukun, to amma Allah ya Riga yayi nasa ikon, sai fatan rabuwa lafia.
Momy murna kawai tace zataga d'an Son, wai murna kaman me tuni ta fesawa su Aunty, Dady ma na dawowa maganar da aka tarbesa da ita kenan, shima yayi murna tare da Sanya Alkhairi...
*******************
Hohoho su Siddi an zama single, laulayi take zubawa bana wasa ba, Sam batason warin gas, shiyasa tuni Haiydar ya koma cim abinci inda Momy, itama komai taci saita amayar, hollandia kawai take sha ta zauna mata, ga Haiydar tuni ya koma bakin aiki saidai kam yana can zuciyarsa na gunta, bini- Bini ya kirata yaji lafiyarta data babynsa, daya dawo gida kuma yana nanike da ita, datayi motsi me kikeso? Ina ke miki ciwo? Hakane kullum har tausayi yake bata yadda ya damu sosai.
Su aunty Ramlah da Shamcy sune 'yan jinya, sai tsiya Shamcy ke zuba mata wai daga nuna mata hanya sai shige da wuri haka, itama da cikinta daya fara fitowa, skull anyi resuming amma kam Siddiqa bata koma ba sai application ta rubuta a bata excuse kafin ta k'ara jin sauk'i.
Saida cikinta yayi 3 months sannan ta d'an samu sassauci, sai kuma dan bazan kwadayi daya biyo baya, itace awara, fara, danyen mangwaro, k'anzo da salat, b'ula( for 'yan kebbi) haka aunty ke aiko mata ita duk sati cike da long bucket, Haiydar kuwa ya kulla abota da masu salat kullum suna hanyar saye, har shima ya koyi ci tare suke kwadayin komai taci da nashi a ciki.
Time goes on, cikin Siddiqa yakai wata 7, yayinda Shamcy ta haihu, su Siddiqa amara k'irjin biki kullum ana gidan ana barar da kwad'ayi, inka ganta bazakace tana da juna biyu saboda a k'irji da hip ya shige, ranar suna yarinya taci sunan iya tsohuwa, Rabi'a zasu kirata da Mimi, anyi suna an watse lafia sai fatan Allah ya raya Mimi kan sunnah manzo (S.A.W).
*2 month later...*
Siddiqa ce zaune k'asa tayi d'ai d'ai zaman masu ciki ga bowl d'in k'anzo gabanta tana aikama cikinta, Haiydar yayi sallama, ansawa tayi tare da yi mishi sannu da zuwa daganan zaune.
Aje Briefcase d'insa yayi kan seated sannan yasa hannunsa kan k'ugunsa ya rike yana irin tafiyar masu ciki, bata fuska tayi tace " piyaa zaka fara ko? Ai nadai kusa saukewa na huta, nima na fara maka yanga ehe."
Daria yayi ya k'arasa gabanta yana fad'in "mai ciki wata hidima akeyi haka bako tayi" ya fad'a tare da tsoma hannunsa.
Cunno baki tayi tare d'auke kai, murmushi yayi ya jawota jikinsa yana fad'in "haba baby love ai kinsan nida kene masu cikin tare muke renin cikin mu" haka yaita janta har ware sukaci da hira...
Guraren 12am na dare, cikin bacci taji kamar tanaso ta zaga nayi, janye jikinta tayi daga nashi taje toilet, saidai me tana zuwa taji cikinta ya wani juyawa, mararta ta d'aure, bayanta ya rike, wani irin azababen ciwo taji yana ratsata, dafe sink tayi da hannayenta sai nishi tace, ganin ba sarki sai Allah yasa ta fara kirqnsa cikin wahalalliyar murya.
"Piyaa! Piyaa!! Piyaa!!."
Cikin bacci yaji kiran hannu yasa ya Shafa gefenta baiji komai ba, hakan ya saka shi mik'ewa cikin sauri ya fad'a toilet inda yake jiyo muryan ta.
Duk'e ya ganta, sai zufa ke karyo mata, k'arasa wa yayi inda tace cikin rud'u ya rungume ta yace.
"Menene baby love?"
Nishi kawai tace ko magana ta kasa yi, ganin haka yasa ya sungumeta a rud'e ganin wasu ruwa nabin kafafunta yasahi kara rikice wa, motar ya sakata, sannan ya koma ya zura jallabiya a baibai ya tada motarsa, horn yakewa gateman ba k'ak'auntawa, shima gigice ya tashi ya bud'e gate, a 160 yajata yabar gidan ya nufi F.M.C hospital..........
βπ»
πMeryerm Abdoolπ
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *_HADU'WATA DAKE_* ππ»ππππ
ππππ
( _Based on love story_ )
*Written*
*By*
πMeryerm Abdoolπ
Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*P.M.L*
π _what a such kind human being u are? Aunty Ummi A'isha (Ruwan kashe gobara) ked'in ta daban ce, komai naki ya banbanta dana saura, ina matukar kaunarki, 2 d high rank of my β€_ ππ
*Page*66&67
Ba gateman kad'ai ba har security sunyi mamakin meya fitar dashi a wannan daren haka cikin firgici, ba ansa, sai fatan Allah yasa lafia sukayi masa.
Tafe yake hankalinsa ya kasu gida biyu rabi nakan driving, rabi nakanta ganin matsanancin halinda take ciki, sai sannu take kwararo mata, ji yake kaman ya maida ciwon a jikinsa, saboda yanda yaga tana wahala, ya k'ara jinjina ma Momy ashe haka mata ke wahala, gaskiya wanda bai girmama iyayensa ba yayi hasara(wallahi harara babba kuwa, Allah yasaka ma iyayenmu da alkhairi ameen).
Suna isa bai tsaya wata2 ba sungumarta kawai yayi, yai ciki da ita, yana shiga kuwa nurses suka kawo gadon mara sukayi ciki da ita biye yake dasu, saida suka isa labour room sannan sukace ya dakata, badon yaso ba haka ya tsaya sai safa da marwa yake yana mata Addu'ar samun sauki, haka likita tazo ta shige ciki, ki yayi kaman ya bita yaga halinda baby love dinsa take ciki.
Tsawon awa biyu, shiru ba Wanda ya fito, gashi baizo da waya ba balle yace zai Kira Momy ya gayamata, kuma bazai iya tafia yabarta ba, haka dai yaita kai da komo addu'a k'unshe a bakinsa.
Abu kamar wasa ba ita ta haihu ba, sai 3:30am bayan taci bakar wuya, dan kuwa tunda ta fara nak'uda bata samu sassauci kona second ba, sai yanzu data haihu ji tayi kaman an zare mata k'aya.
Kukan baby ya sanar dashi isowarsa, nan take murna ta lullub'esa anan gurin yayi sujudus shukur, yana mik'ewa saiga wata nurse ta tunkaro shi bakinta a washe tace.
"Congrat Sir, matarka ta haifi baby boy, kyakyawa, daga yaron har uwar suna cikin k'oshin lafia"
Bakin D one kamar ya yage, don murna yake "kai mashaa Allah, zan iya ganinsu kuwa?"
"Aa ana kimtsa su ne, yanzu dai kawomana kayansu".
"OK" ya fad'a da yake dama ya saka jakar kayan a mota tuni yace kar aje haihuwa tazo a rud'e a manta, aiko gashi anyi hakan, da an manta.
Kayan ya mik'a mata tare da bata bandir d'in 'yan 500, yake tukuicinta ne, washe da baki ta ansa tana zuba godia dan tasan ta haye sannan ta shige ciki, minti kad'an ta fito da jaririn an shiryashi cikin kayan sanyi farare masu laushi, an kannnad'eshi a towel bai laushi shima.
Mik'a mishi shi tayi tana fad'in " yallabai ga babyn, subhanallah saida gaban Haiydar ya fad'i ganin babyn dan kuwa kaman Ya Umar yayi kaki ba inda ya baroshi sak kamar shi.
Rungume yaron yayi a k'irjinsa sai hawaye sharrr, dan ya ganin yaron gani yayi kaman Bros d'in nashi ne ya dawo gareshi, nurse dake tsaye ganin yana kuka tace.
"Yallab'ai duk farincikine haka, murmushi yayi yace " dole nayi kukan farinciki Bros ya dawo gareni" itakam da bata fahimci inda ya dosa ba cewa kawai tayi "bari naje za'akai Madam dakin hutu, inta huta saika ganta."
"Ok" kawai ya fad'a duk da yana muradin ganin babyn tasa, amma ganin babyn ya tafi dashi, kiran sallah yayima yaron sannan yayi mai huduba da sunan Ya Umar, dama burinsu kenan idan suka haifi namiji su maida sunan sa, sai kuwa gashi yazo harda kamanninsa, ikon Allah kenan.
Shiga yayi d'akin rungume da d'ansa dake faman tsutsan yatsu, kwance take tayi fayau da ita sanye da Arabian gown red, gashinta ya bazu a filo sai bacci take cikin kwanciyar mind, kamar ba ita ta haihu ba.
Gaban gadon ya tsaya yana kallonta cike da kauna, ko kiftawa bayayi kaman yau ya fara ganinta, aje babyn yayi gefenta, shi kuma ya sarke hannunsa a k'irji yaci gaba da kallonta, shurinta babyn ya farayi, yana kuka tare da tsota hannu, hmm daga gani za'ayi zarumi anan.
Jin ana shurinta da kukan jaririnda taji yasa ta bude ido ta sauke ga Haiydar dake tsaye yana mata murmushi, ganin tanaso ta tashi ya sakashi kamata ya had'a ha k'irjinsa, sannan ya d'auko babyn ya d'ora a cinyarta, kallon babyn tayi tare da kallonsa alaman mamaki, murmushi yayi yace.
"Baby kinga ikon Allah ko? Ya Umar ya dawo garemu" jinjina kai tace "Allah abin godia.
K'ara matseta yayi a k'irjinsa yace" nagode Maryama ba abinda zance dake sai Allah yayi miki albarka, ya kuma sakaki farinciki kaman yadda kika Sakani, ba abinda zan kira *Had'awata dake* face had'uwar alkhairi wacce nake alfahari da ita, Allah ya barmu tare har mutuwa".
"Ameen" ta fad'a cikin siririyar muryarta, tare da rungume babyn a k'irjinta tanajin kaunarsa na ratsata irin ta d'a da uwa (haihuwa kenan ni'imace).
Kuka yaron ya farayi alaman yanayin yunwa, kallonsa tayi sannan ta kalli Haiydar sai kuma ta d'ora yaron a kafad'arta alaman rarrashinsa zatayi.
Girgiza mata kai Haiydar yayi sannan yace "no baby love, ki bashi abincinsa mana tunda yazo duniya baici komai ba sai tsotson hannu yake."
Batace komai ba, kuma batada niyyan yin abinda yace, sai jijjiga yaron tace shi kuma yaki yin shiru, suna hakane Dr, ta shigo d'auke da cup a hannunta mai d'auke da tick tea, murmushi tayima Siddiqa tare da tambayanta yanayin yadda takejin jikinta, ta amsa da normal sannan ta mik'a mata cup d'in tare da ansan babyn dake kuka tace da Haiydar, cikin raha.
"Baban baby ka kasa ka tsare, kaki matsawa"murmushi yayi sannan yace.
" yawwa Dr, za'a iya bashi nono kuwa? Gashi sai kuka yake, sannan kuma idan ba matsala a sallamemu kawai mu wuce."
Murmushi tayi tace "why not idan ya kawo abashi abinshi don yafi komai mihimmamci ga jariri, maganan sallama kuwa ba yanzu ba, ka'ida ne duk aka haihu koba matsala sai anyi 12hour, so kaje gida kawai ka samomata abinci mai nauyi taci." Tana kai nan tayi musu sallama ta fice.
Matsowa yayi ya rike mata cup d'in yana bata yace "baby love yi kisha, ki bashi shima yasha".
Kollon kasan ido ta mishi tace " piyaa kaje gida ka huta mana, idan na k'are zanji dashi, daganan saika gayama su Momy ko?"
"Uh um baby love nina fiso yasha agabana inga yadda ake feeding" smiling kawai tayi cikin jin kunya ta fidda nonon ta bashi, aiko caraf ya kama da k'arfi, k'ara tayi tare da yarfe hannu saboda zafi daya kama tayi saurin janye mamanta, aiko yaro ya challara ihu shima.
Kallon yadda ta b'ata fuska tayi yace "yadai" tace "zafi" cikin rarrashi da dabara ya samu ta yadda ta bashi nonon, tana bashi tana yarfe hannu, shi kuma sai kallonsu yake abin ya birgesa sosai, ga Brest d'in tsaye gwanin sha'awa, tab d'insa ya d'auko ya wacce yayi ma pics dasu, selfie ya d'auke su bayan ya rumgumosu gaba daya.
Saida babyn ya k'oshi sannan ya ya Karbesa, yanaci gaba da kallonsa sai bacci yake dake cikinsa ya dauka, itama kwantawa tayi, aje babyn yayi gefenta, peck ya bata a goshi tare da Shafa kanta yace.
"Baby love naso ace sunyi discharge dinmu a bawa su Momy surprise, well bari naje gida na gayamusu, sai a sama maki Abu mai nauyi, what do u want?"
"Any thing, no choice piyaa" ta fad'a idonta rufe.
"OK" ya fad'a sannan ya wuce.
******************
Yana kai unguwar yaji ana kiran assalatu, tsayawa yayi yai sallah sannan ya shiga ciki, zaune ya samu Momy tana lazumi, kallonsa tayi bayan sun gaisa tace "yadai Son wannan sammakon lafia? Gashi na ganka cikin annuri".
" ummm Momy ya Umar d'inki ne ya iso" da yake tasan da zancen sunan tace "mashaa Allah, 'yata ta samu saikin k'afa, ta haihu gida abinta, amma shine kika zauna harta haihu kak'i kirana" ta fad'a tana mik'ewa tare da fad'in "bari in d'auke reza inje in gyarasu."
"Murmushi yayi yace" Momy tana asibiti fa can ta haihu" nan ya fad'a mata yadda akayi, fad'a sosai tayi masa, tace aibai kamata ya kaita shi kad'ai ba, ya kiyaye irin haka ko gaba, to yace sannan ya wuce sannansu danyin wanka kafin Momy ta shirya.
Tuwon semo da miyar kubewa bushashiya sai farfesun kifi da da kunu data had'a mata, sannan taje tayiwa Dady albishir,aiko taci goro babba.
Haiydar bayan yayi wanka kiran mutane yayi tayi yana gayamusu haihuwa, harsu aunty saidai ya gayamusu sunyi sabon ango, murna sukayi sosai sannan kukace suna hanyar zuwa, su Hanan ma da Momy ta gayamusu sai tuma suke suna Aunty ta samo musu baby.
Sai 7am sukaje sun samu tashin ta kenan, tana ganin Momy ta Dukar da Kanta cike da kunya ta gaidasu, amsawa tare dayi mata sannu da jiki, Haiydar ba kunya ya d'auki babyn ya d'ora a cinyar Momy yace "yace Momy kinga mai kama da Bros, ko?"
Saida kirjinta ya buga ganin yaririn sak kaman lokacinda ta haifi Umar da girman da komai, kwalla ce ta taru a idonta saboda tuna mata da Umar dinta da yayi saurin mayarwa tayi ba tare data bari sun sauka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 16