lafewa kawai yai jikin momy.
Bangarensu Siddiqa kuwa suna fita sch din,napep suka Tara ta kaisu Tasha,Shamcy sai meta takeyi mata wai ta Hana azo daukansu SBD wata akidarta can ta banza..
Murmushi kawai tayi,koda suka karasa Tasha baya Shamcy ta Kama musu SBD Siddiqa ta dake akan ba zasu dauki shata ba,A haka suka karasa Arg shamcy sai surutu take Mata ,Ita km tai Mata banxa karshenta ma air pie tasa ta Dade kunnenta tana saurarn kira'ar *Maheer Al-mu'akkill* dole itama tai shiru da taga ta maida ita mahaukaciya.
_wannan kenan_
π ~meryerm Abdool~ π
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *HADUWATA DAKE* ππ»ππππ
ππππ
( _Base on love story_ )
Written by :- π meryerm Abdoolπ
Edited by :-
*Maman ussey* & *AAJ*
_I DEDICATE DIS PAGE 2 ENTIRE FAMILY OF LATE,DR ABDULKADIR GULMA.MAY ALLAH BLESS B WIT U MY FAMILY AMEEN_ πππππ
*Page* 13&14
Sanda suka isa Argungu aka aje mutun biyun a babbar Tasha,Fita sukayi sunayima su Siddiqa godia biya musu kudin motar da sukayi.
Cewa tayi "Laa ai ba komai" fuskarta kunshe da murmushi,Haka mutanen suka tafi suna girmama karamci irin na Siddiqa.
A haka driver ya karasa dasu gidan sarki,yana mamakin saukin Kai irin nasu kaman ba 'ya'yan sarki ba,Sam basu dauki Kansu can da nisa ba..
Suna fita dogarai suka Fara russunawa suna kwasar gaisu sai ji kake suna fadin " Takawarki lfy er toron giwa er sarki jikar sarki,Gaba salamun baya salamun"
Gaishesu ta farayi cikin jin kunya SBD ita kunya takeji in suna russuna mata sbd a haife sun haifeta,Tasha gayamusu su daina amma Sam basu daina ba..
Ita kam Shamcy sai wani dadi takeji a ranta gashi anata basu girma.
Suna shiga cikin gidan da jakadiya Fara haduwa,Aiko tana ganinsu ta Fara "lale maraba da uwargida" tare da fadada murmushin fuskarta (dama haka take kiranta) karasowa tayi gurinta itama murmushin takeyi tana fadin "sannu Inna ya gida ?
"Lfy wlh sai Alkhairi, yanzu kuke tafe da ranar nan? Ashe tare kuke da Shamciya gsky km kin kyauta! Cewar jakadiya
"Eh wlh inna gatanan sai yau ta Kara zuwa km KO yanzun ma dalilin bikin Aunty Aysha ne (dama har iyayensu sunan da kawancen su koda yanxu da zasu taho saida ta Kira ta gayamusu har sukace mom dinta tace zatazo itama Ana gobe aure,Dan zuwanta ne suka shaku da Aunty Aysha)
Harararta Shamcy tayi snn tace " Banason sharri besty"
Gwalo tai mata kana tace "ai gaskia na fada"
Murmushi kawai jakadiya tayi saboda yaran suna burgeta snn tace "Ku karasa ciki na tsaida Ku da surutu daga zuwanku"
"Laa ba komai Inna" ta fada snn suka karasa Main part din iyayensu mata......
A corridor suka hadu da Rufaida aiko da gudu ta makale Siddiqa tana fadin oyoyo Aunty..
Jin oyoyon Rufaida ne ya fito da sauran mutan gidan.
Cewa take "My Rufee me mama ke baki kikai lukuta haka dake.....
Fitowan su Aunty ne yasa ta sauke Rufaida ta karawa inda Aunty dake ta dokin ganin er tata tana fadin "maraba da er lelen Aunty"
Rungumeta tayi itama tana fadin "Nayi missing dinki Auntynah da muryar shagwaba"
Aysha kam gurin shamcy taje mutuniyarta tana Mata sannu da zuwa snn tace " kinga Aunty ta erta kawai takeyi zo muje kanwata" ta fada tana musu hararar wasa!
"Au Ashe tare kuke da Shamcy babyn Aunty nifa Sam bamma ganta" Aunty ta fada tana kallon Shamcy.
"Ina kuwa zaki ganta Aunty bayan bakya ta kawo saita Siddi mummu" Aysha ta fada tana dariyar Siddiqa (SBD haka take ce mata idan taso tsokana)
"Bata rai tayi snn tace Aunty kinga zata Fara ko?
"Haba Aisha daga zuwanta"cewar Aunty
"Ayi hkr Aunty" cewar Aysha
Dariya sukayi gaba daya snn suka gaggaisa kana Aysha taja Shamcy sukayi bangarensu.
Itama km Siddiqa sukayi bangaren Aunty dama can ne gurin zamanta.
Rufaida kuwa na makale da ita. Tana shiga dakin Aunty Ramla kan gado ta sameta sai bacci take.
Murmushi tayi snn tace "lallai Amaren nan sai hutawa kukeyi kuna wani shahararen kyau kome su mama ke Baku oho...da sauri rufaida tace 'aah kullum sai sunje part jakadiya da safe da marece ankawo wata Mata tana musu gyaran jiki"
"Kai Rufee kin cika surutu jeki Inna shirya Zan nemeki" snn ta debo chocolate masu yawa ta bata aiko da gudu ta tafi.
Itama fita tayi taje Nata dakin aiko ta sameshi a gyare sai kamshi ke fta tasan aikin Aunty ramla ne, cire tufafin tayi ta fada toilet......
**
**
**
Haydar kuwa bayan sun dawo daga masjed car dinshi ya dauka sai gidansu Saleem.
Koda yaje KO ya sameshi dai2 shima ya dawo daga masallacin gaisawa sukayi snn suka karasa dakinshi.
"Amma fa dazun ka bani tsoro sosai D one! Cewar Saleem
"Hmmm! Kabari kawai Leem Am not in d mode dazun raina ya Riga ya baci ne sosai.
"Ai kuwa nine sheda! Amma meye ainihin abunda ya faru ne ??
Anan gayamai Abinda ya faru snn ya Kara da cewa "Saina yi Mata abinda harta mutu ba zata mantani ba snn kuma abinda zaisa ta tsani kanta da kanta,tayi danasanin *HADUWATA DA ITA*
.......
"A gaskiya kam ta kira ruwa amma D one daka kyalet...........
Da sauri yace "what!!!! In kyaleta.....
_Sorry friends pls kuyi manage da wannan wlh a gajiye Nike yay_
Love u Allπππ
πmeryerm Abdoolπ
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *HADUWATA DAKE* ππ»ππππ
ππππ
( _Base on love story_ )
Written by:-
πmeryerm Abdoolπ
Edited by :-
*Maman ussey* & *AAJ*
Dedicated 2 all members of *MATAN KIRKI MASU NAGARTA GROUP* love u wit all myπππ
*page* 15&16
"Came down! D one bawai ina nufin ka kyaleta kada ka mata komai bane, Aa nifa nufina kada ka illata Mata rayuwa!! Kaga kanada kanwa km aure zakayi kaga bazakaso ayima daya daga cikinsu illa ba"Saleem ya fada da muryan lallashi
Binsa yai da mugun kallo snn yace" ga Dan iska kenan! Amma Kafi kowa sanin iskanci baya gabana,Da ina bukatarsa da tuni nayi SBD akwai masu request dayawa rejecting dinsu nakeyi (subhanallah wai mace ke tallan jikinta ga namijnda ba Nata ba Allah ya karemana imaninmu ameen).
"Haba D one kada ka dauka da zafi nifa ba haka nake nufi ba"
Daga kafada yayi snn ya tabe baki yace "koma me kake nufi kaita shafa,Amma abinda nai iyyar yi Mata ba fashi" yana gama fada ya bude kofar dakin ya fita da karfi ya rufeta ji kake dunm...
Galala Saleem yasaki baki yana kallon kofar kafin ya sauke numfashi yace "D one rigima Allah ya sawwaka"
Siddiqa kuwa bayan ta fito daga wanka turare kawai ta Shafa snn ta zira wata gown ta material tabi lfyar gado.....
Ba ita ta farka ba sai 4:pm tana tashi toilet ta fada tayi Alwala..
Bayan ta idar da sallah,tana azkar Nata ne Ramla ta shigo dakin.
"Sis, kin tashi kenan!na shigo dazu bayan na tashi Aunty ke gayamin kun iso na samu kin kwanta,shine naga anyi sallah na dauka baki tashi ba"cewar Ramlah.
"Wlh kin ganni kuwa sai yanzu na tashi,Da bacci nazo tab idona kinsan no place like home!" Ta fada tana kollonta da murmushi.
Darawa Ramlah tayi snn tace " Hakane! tau inkin gama muna main parlor dasu Aysha da Bestinki" ta fada tare da juyawa.
Bayan ta idar direct main parlor ta wuce wanda ya kasance tsakanin part din mama da Aunty,Babbane sosai set 4 cikinsa.
Da sallama a bakinta ta shiga cike yake da kawayensu Anty Aysha,Shamcy ma na cikinsu sai fira ake sosai da yake kai waye ce,ansa sallamanta sukayi kana suka gaisa,Sun baje a falon sunata tsara yadda bikin zai kasance.
Zama tayi snn tace,"Ya Ramla wai duka event din nan yinsu zakuyi gaba daya?
"Tab! Tome za'a fara a ciki" fadar Aysha
Shamcy ko cewa" tayi dole mu rakashe bikinsu Aunty's ai dole mu dibi shoki" ta fada tana daria
"Kyace haka mana er bidi'a kawai "ta fada tana hararar Shamcy
Snn tace "Aunty jameela a maida wukar ciki km aini Aunty Ramla na tmby bace ba" ta fada tana turo baki.
Rungumeta Ramla tayi snn tace "kyaleta sisi,amma kiyi hkr kinga an riga an tsara abin haka km shine bikin farko a gidannan, gara adan burge ko??
"Nifa ba ruwana kuyi abinku kada wadannan su cinye ni" ta fada tana nuna su Shamcy
Darawa gaba daya akayi snn wata cikin kawayensu race "kai Siddiqa ke kam ta daban kike kin huta"
"Mu km daba na daban ba fah khairat" fadar Ayshat
"Kai jameela wlh kin cika kishi" cewar Ramla
Ayshat zatayi mgn kenan Aunty ta shigo rike da karamin tray a hannunta tana fadin "Baby kina nan da rashin cin abinci kinnan matsa karbi nan kici tun dazu kowa yaci kina bacci amma kin tashi koki nemishi" ta fada tana mika mata tray.
"Lah! Aunty yanzu nake shirin tashi in debo"ta fada tana ansar tray.
"Hmm ba wani tashi da zakiyi,nidai matsa kicinye shi tas" waro ido tayi "duka fah Aunty"
"Sosai kuwa" Aunty ta fada tana mai ficewa.
Fried rice ce da akayi da koda taji kayan lambu sai pepper chicken da zobo da yasa hadi.
Ci take tana wani yamutsa fuska,sai tsokananta sukeyi Ramla na shige mata.
Basu suka tashi ba saida sukaji kiran magrib snn suka mike suka gabatar kana kawyensu suka wuce da bayan sun gama tsara yadda kamu zai kasance gobe a *grand fishing*
Siddiqa dai jinsu kawai tace don kuwa ba zuwa zatayi ba.
Sai bayan isha snn ta samu zuwa gurin mai mai martaba don su gaisa sbd koda suka iso yana fadarsa.dama sai magrib ake tashi aje masjid shi km baya shigowa ciki sai bayan isha.
Tare da Shamcy sukaje koda suka shiga yana kishingide kam tum2 yana jan carbi,Da sallama suka shiga Ansamusu yai ya dago kansa yana fadin.
" Uwata saukar yaushe?
"Dazun muka zo"
"Madalla ku karaso" Shigowa sukayi suka zauna kasan capet suna kwasar gaisuwa.
"Lfy lau mamata ya mkrnta da kara2 fatar kuna himma ko? " eh Babanmu"
"Tau Allah ya taimaka yasa ku kare lfy" Ameen suka fada A tare snn ya Tmbyi Shamcy bangaren iyayenta ta ansa da suna lfy.
Nasiha ya musu kamar kullum sai sukai mishi sallama yana mai sanya musu Albarka.
Koda suka koma part dinsu mama da ya mubarak suka fara haduwa, Anata murnar dawowar su mama daga dubai ita da kanwar babansu(sunje siyen kayan Amare)
" Aa lovely sis.saukar yaushe fadar Mubarak"
"Dazun mukazo"
Gaidashi Shamcy tayi snn ya tmbyesu skul din suka ansa da lfy lau,Snn su mama suka shigo Rufee na makale jikin mama.
Da murmushi suka karaso goggo Ma'U na fadin "Ashe uwar mayya an karaso " eh goggo" ta fada tana karbar mata bag dinta itama Shamcy kabar ta mama tayi tana musu sannu da zuwa,Karaswa sukayi cikin suma su Aunty duk suka fito Ana musu barka da dawowa.kowa sai murna akeyi bayan an gaisa aka snn suka shiga ciki don yin wanka da salloli.
**
**
**
*10:00 am*
Haydar ne cikin skul duk inda yasan zaiga Siddiqa ya duba bai ganta km harda kawarta bai gani.dakyar ya tmby wata er course nan take gayamai sunje Argungu biki.
Ohhh! Shaf ya manta da bikin sbd barinsa na son daukar fansa.
"Damn u " ya fada yana furxarda iska a bakinsa.Snn ya shige motarshi ya bar skul din,Ko Saleem bai nema ba sbd har yanxu haushinsa yakeji.
Su Anas kuwa ayau suka sauka A Argungu domin fara event dasu dama ita Aysha mijinta dan Argungu ne amma Abuja zasu zauna sbd can yake aiki.
Dama ita kayanta suna isowa aka kai mata na gidanta anan Abuja Snn na Ramla aka wuce dasu bk kayane designers aka debo musu an gyarama kowacce gidanta masha Allah.lol
Da za'aje kamu ba yadda Ramla da Aunty basuyi da Siddiqa akan taje fafur taki dama inta kafe tofa bai mai canjata mama kam cewa twi" su kyaleta ita ta sani " hakan kuwa ta kasance taki zuwa,su Shamcy kam ana kan gaba,guri yayi kyau sosai anyi barin nera.
Bayan sun dawo Shamcy ta kawoma Sddiqa video ta gani ko lallonta batayi ba.haka aka gudanarda sauran event din irin *culture day* wanda akayi al-adun kabawa sosai kamar wasan gargajia ds snn akyi su *Dinner* kusan kala uku a *grnd fishing* gidan ya cika sosai har saida aka kai sauran bakin guess house din sarki,Tofa Aure na fari da aka farayi a gidan ga sarki da mutane sosai sbd Karamcinsa,Snn ga km en uwan mama dana Aunty.
Ranar daurin Auren da sassafe,Siddiqa taje kaiga mama bata sameta daki ba sai a kitchen ta iskota,bayan sun gaisane mama tace "yawwa Siddiqa tunda kinyi wanka dan mika su Anasa karinsu na rasa wanda zai kai musu,maza dakko hijab ki kai musu keda su jabir da rufaida"
"To mama" ta fada tana komawa ta dakko hijab dinta,tana sanye da shadda pink tayi gown sai hijab milk da plate shoes suka pink,plask ta dauka da tray yayinda Rufee ta dauki bread jabir ya dauki wani food plask.
"Ina sukene mama"
"Suna part dinsu mubarak" cewar mama.
Da sallama ta shiga part din,sun kai su goma suna zaune suna taba hira,Aje musu sukayi snn suka gaisa ta fice.
Bayan fitarta ne,Umar yace " Nas wannan fah itama kanwarsu Ramla ce naga tunda mukazo ban taba ganinta ba"
"Tofa! Sadauki(haka frnd dinsa ke kiransa family name nasu ne)kodai ka kamu ne?cewar Anas.
"Pls be serious mana Nas"cewar umar
"Ai nayi sbd ban tabajin mgar mace a bakinka ba,Siddiqa sunanta itama kanwarsu Ramla ce,Abinda yasa baka ganta ba kuwa a evens dinda akayi sbd tace wai bidi'a ne "
Sosai yaji ta kara burgeshi
"Gsky Nas ta kwanta min inasonta idan ba matsala??
_Tofah kunji frnd_
πmeryerm Abdoolπ
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *HADUWATA DAKE* ππ»ππππ
ππππ
( _Base on love story_ )
Written by:-
πmeryerm Abdoolπ
Edited by:-
*Maman ussey* & *AAJ*
*Page* 17&18
"Mashaa Allah nayi farinciki jin hakan daga bakinka Sadauki,km nasan inshaa Allah baza'a samu matsala ba sbd macen zata ki ka Abokina"cewar Anas.
"Hmmmm! Kada kafa zirani da yawa mutumina,Amma naga kaman Zan sha wuya kafin na samo kan yarinan?
Darawa Ana's yayi snn ya gyara zama yana fuskantarshi yace "Haba Sadauki Kada ka bada maza! Mana,Tun bakuyi magana ba harka Fara da raki??
Snn ya Kara da cewa "km ai Siddiqa Sam batada matsala saidai.....?
Da sauri Umar yace "saidai me?"
"Hhhhhh! Lallai Abokina ka kamu da yawa wannan sauri haka kamar nace baza'a baka ita ba.
"Haba Nas pls joke apart muyi serious issue! Bakaji yadda zuciya take bugawa bane" Umar ya fada yana Dora hannunsa dai2 heart dinsa.
Murmushi Ana's yayi "Wato Sadauki,Siddiqa tanada wani ra'ayi na daban Wanda ta banbanta da sauran en gidannan dashi,Sam a rayuwarta bata damu da kudi KO mulkin gidansu ba tana rayuwane kamar cikin sauki,komai tanayine irin na ordinary people, saidai fah idan ta kafe akan Abu tofa anzo gun dan ba zata lankwasu ba,Snn ta tsani renin wayo da km wulakanci kowa yai mata zata rama.
Sosai yaji ta Kara shiga ransa koba komai tsarin rayuwarta ya burgeshi,ji yake kaman ta zama tasa tun yanzu,sai hango zamanda zasuyi da ita yakeyi.......
"Bakace komai ba kayi shiru sai smiling kakeyi"Anas ya fada yana fadashi.
"Ka bari kawai nawa wlh sonta ne keta bin jini da jijiyoyin jikina shiyasa kaji na kasa magana"Umar ya fada yana mai lumshe idanunsa.....
"Tofa! Abu ya kawo ga ma'iya wai kukan Aure da salollani! Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki?? Cewar Anas yana rike baki.
"Uhum! Nidai ya za'ayi ne,nifa bamma San mezan gayamata bane idan mun hadu?snn wai yama za'ayi na ganta mutumina??
"Kaika Sani! Ana's ya fada yana Mai kokarin tashi..
Rike mishi hannu Umar yayi snn yace "Aiba haka za'ayi ba Nas solution zaka sama mini"ya fada yana zuba mishi idanu.
Dayaga Alaman iyakan gskyarsa yace managan sai yace mishi"Tau naji! Yanzu dai muje mudan karya snn mu shirya kaga time na tafia kada mu bata lokaci" Ana's ya fada yana mai mamakin canjawar frnd din nashi lokaci daya,Wanda Sam Mata basa gabansa Amma yau daya er kanwarsa ta rikita masu shi( ni km nace na love oo )
Karasawa sukayi gurin frnds dinsu dake karyawa..akan carpet.
'Siddiqa kuwa tana shiga cikin part dinsu dakin Asyha ta wuce dan ganin KO sun tashi,bude kofan tayi sallama dauke a bakinta,Aysha na kwance a bed ta rungume fito phone dinta a kunnenta tana mgn kaman Mai rada,sai wasu frnd Nata su biyu 2 dake bacci,dai2 time din Shamcy ta fito daga toilet tana Mai Ansa sallamanta.
"Uhum! Kinga manyan en bidi'a fah wato sai yanxu aka samu tashi Allah dai yasa anyi sallah" Sddq ta fada tana Mai kallon Shamcy.
"Kai Besty karki hada da sharri fah mezai hanamu yin sallah"Shamcy ta fada tana karasawa gaban mirrow.
Aysha ce tace "ke kada ki matsa ma mutane fa,meye naki a ciki tunda bakiyi ai kya Bari masu yi suyi abinsu" ta fada tana wurga Mata harara,gama wayanta kenan.
"Tau jarababbiya nadai kusa na huta da jarabanki saidai kiyima Ya Sulaiman" ta fada sannu2.
"Me kika ce?
Turo baki tayi "snn tace nifa bance komai ba"snn Ta juwa tana kallon Shamcy tace "besty in kin gama ki sameni daki mu karya Karin time din waleemar yayi" ta fada tana mai ficewa daga room din.
Kwafa Aysha tayi snn ta mike ta fada toilet.
Shiri sosai sukayi na zuwa waleema Wanda za'a gabatar karfe 10:00am a farfajiyar gidan,Atampa ce super England brown ce Mai ratsin yellow,Anko sukayi itada Shamcy Anyi musu Riga da siket dinkin ya zauna a jikinsu,simple make up tai amma tayi kyau sosai..kaman a sake a gudu.
Shamcy kam masu yima Amare kwalliya sukayi Mata itama tayi kyau mashaa Allah..
An gyara gurin sosai inda aka kafa runfuna da aka jera kujeri gwanin sha'awa..
Malam malamai Aka gayyato irin su *Shaik,Kabeer gombe,Shaik giro Argungu,Mal.Abbas jega,Mal.Ladda Bunza da Alarammominsu*.
Amare kam ba'a cewa komai sai mashaa Allah sunyi kyau sosai.
Wa'azi sosai malaman sukayi inda suka bama Amaren shawarwari game da zamantakewar Aure,da koya masu dabarun zama da mazajensu inda A karshe sukayi Addu'o'i sosai na samun zama lfy da mazajensu,snn sukayi Addu'a na samu zaman lfy a kasarmu mai Albarka Nigeria.
** **
**
Karfe 1:00pm dai2 aka tashi da waleema bayan An raba kayayyaki sosai a gurin duk Wanda yazo,tofa ya samu kayan rabo masu dimbin yawa,Abin sai Wanda ya gani.
Amare kuwa kuka sukayi sosai SBD naseehar ta ratsa su,sauran mutane kuwa jikinsu yayi sanyi SBD anyi naseeha mai kashe jiki,haka dai aka watse kuwa na farincki da sanya Albarka.
Bayan an sauko daga jumu'a ne akayi sanarwar Auren nasu inda aka daura Auren *Sulaiman Basheer dobi* & *Aisha jamila Muhammad lll* Dana *Ana's Ahmad zogirma* & *Ramlah Muhammad lll* kan sadaki dubu #50,000 sai fatar samun zama lfy.
Bayan daurin Auren bakin Angwayen kamar ya yage sbd murna sai gaisawa suke da mutane,Daganan suka wuce inda mai maitaba ya hada musu liyafa suda Abokansu, Aka kashi gara. Lol
*Haiydar* ya halarci Auren kaman yadda yai Alkawari amma Ana karewa ya juya a cewar wai uzuri yakeda KO ruwa garin bai sha ba ya wuce,amma duk da haka Ana's yaji dadin zuwansa.
Bangaren Amare kuwa anyi wankin amare a gidan kakansu tsohon sarki mai rasuwa,Inda za'a wuce da Ramla bayan la'asar,Aysha kuwa sai gobe zasubi jirgi da sassafe.
Lokacinda za'a wuce da Ramlah kuka sosai takeyi inda suka rungume juna ita da Aysha Suna kukan rabuwa,Sddq itama ta rumgumesu gaba dayansu tana kuka itama ,Bayan an kaiku gurin Mai martaba yayi musu naseeha sosai haka iyayensu mata sunyi nasu.
Dakar aka rabasu snn aka wuce ta ida mota Ina Sddq ke gefenta sai kanwar babansu Shamcy ta kame gaba dake suma yau zasu koma Skul din SBD Ana shirin Fara exam ne.......
Gidane mai kyau sosai ya hadu mashaa Allah.
Saida aka Fara biyawa ta ita gidan gwagwon tasu ta tarbesu sosai snn ta Dora dayi musu naseeha.daga karshe tai fatan samun zama lfy mai dorewa.
Bayan en kai Amarya sun watse aka barta daga it's saisu Sddq Dan har wayenta ba ba wacce ta tsaya,Suma Sddq wucewa zasuji skul Dan Sam ba zasu kwana anan ba.
Bayan An kawo ango abokai sunyi Addu'a aka danyi siyan baki sai Shamcy ke mgn,Sddq kam shiru tai musu har suka gama Dan ta matsu su tafi.
Umar kuwa tunda suka shiga dakin Sddiqa kawai yake kallo amma in style Anas kawai ya ganeni SBD yasan za'a rina.
Da zasu tafi ne Anas ke cewa.
"Sadauki pls ga kannaina kayi min drop nasu A FUK tace ba zasu kwana b" ya fada yana kashe mai ido daya.
"Lah! Ya Anas daka barshi wlh zamu hau napep" cewar Sddq.
"Aa ki Bari kawai na ajeku ba komai"Umar ya fada
Taso yin gaddama shamcy ta girgiza Mata kai,
Cewa tayi "Tau Aunty Nah sai mun shigo gobe" ta fada tana mai kwace jikinta da sauri tabar dakin don kada Ramla ta riketa,tana fadin "tau Ya Ana's a kulamin da yayata sosai"
"Inshaa Allah " ya fada.
Har bakin hostel ya kaisu godia sukayi mashi,cewa kawai yai ba komai snn ya wuce,sai taji muryansa its familiar sharewa kawai tayi suka shige ciki.
Tafe yake yana driving cikin nutsuwa,nishadi kawai yakeyi bini2 yayi smiling alaman yana cikin farinciki.......
``` love u oll frnds```
π ~meryerm Abdool~ π
[5/20, 6:22 PM] πMeryerm Abdoolπ: ππππ
ππππ *HADUWATA DAKE* ππ»ππππ
ππππ
( _Base on love story_ )
*Page* 19&20
'Karfe 9:30pm,ya isa gida yana parking car dinshi direct part dinsa ya wuce,wanka yai ya sauya kaya zuwa na bacci bayan ya gama feshe jikinsa da turare,yaso yaje ya gayama mom dinsa sun dawo dakai angon sai km yaga dare yayi wata kila sunyi bacci (bayan gama liyafar ango suka dawo bk tare da wasu frnds dinsu aka bar sauran Dan daukan Amarya,gd ya wuce direct saida aka tashi kai angone yaje gidan).
Kwantawa yayi kan bed tare da janyo filo ya rungume ya lumshe ido kaman mai bacci,fuskarta kawai yake hangowa da Dan lip dinta mai daukar hnkali sai tattausar muryarta mai Kama da busar sarewa lokacinda take masa godia yake tunawa,murmushi ya ringa yi shi kadai (ni km nace tofah! Umar an shiga system din kenan π).
Wayar shi ya janyo da niyya kiran Ana's sai km ya tuna Angone fah,aje wayan yai bedside drawer,yana fadin.
"Dole na nemaka gobe Nas...Sam na rasa ta ina Zan Fara tunkararta wlh"
Haka dai yaita sakawa da warware har bacci yai gaba dashi......
....Washe gari sai gurin karfe 9:00am su Sddq suka farka bayan sunyi sallah fajr suka koma duk da kuwa ba Al'adanta bane komawa bacci,Amma SBD gajiyan biki dole tadan runtse tayi baccin SBD har sarawa kanta ke mata,da yake weekend ba skul wanka tayi snn ta hada musu breakfast dai2 itama Shamcy ta fito daga wankan,karyawa sukayi Snn suka gyara dakin nasu sosai da yake jira sharewa kawai sukayi.
Bayan sun gamane ta dauko
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 16