Share this page
ba, sannan ta mik'awa Dady yaron ya ganshi tare da saka mishi albarka. Tuni asibiti ta cika da 'yana uwa da abokan arziki, su Shamcy, Aunty Ramlah, mutanen Argungu da sauran jama'a sai santin yaron suke wannan ya d'auka yaba wannan, ganin asibitin ta cika yasa Haiydar sake jiki yayi gida don ramuwar bacci... Bayan an sallamo su, su aunty sukace zasu wuce da ita, Momy ta roki arzikin a bari har bayan biki sannan su wuce sa ita, hakan kuwa akayi, d'akin kusa da Momy tasa aka gyara Mata, Haiydar yana jiran adawo su tafi sasan su, sai ganin yayi sun tare part d'in Momy, fushi yayi ganin ba Wanda ya kulashi yasa ya tataro ya dawo dfad'aashi ake zaman jego ba kunya, sai bacci ke maidashi part d'insu, ga wani extra care da mai jego da baby ke samu daga Momy abin sai sam barka. Anyi shagalin biki sosai, an rak'ashe an cashe naira tayi ihu, su Shamcy Aunty Ramlah sune k'irjin biki, su Aunty Aysha ma sunzo,Zaran ya Mubee ma tazo da 'yarta mai sunan Mama suna kiranta da Ameera, kowa yayi iya k'ok'arinsa mai jego da baby Umar wanda zasu kira da *Little* sai shiga wannan su fita wannan suke, kaya kuwa kaman masu shirin bud'e boutique, dagin kudi kuwa tuni yaro ya zama millonia, anyi taro an watse lafiya sai fatan Allah ya raya baby kan sunnah. Biki da sati Aunty tazo wucewa da Siddiqa, Haiydar kuwa yace Sam besan zancen ba, saida Momy ta nuna mishi bacin ranta sannan ya amince badon yaso ba, yanaji yana gani aka wuce dasu, ji yayi kaman ya koka saboda yasan zaiyi missing d'insu ba kadan ba. Ba k'aramin gyara takesha ba daga Aunty da jakadiya, tuni ta d'auki sheki kamar sabuwar amarya, ga wani cikowa da haske data k'ara, oga D one, duk k'arshen sati yana Argungu ganin baby love, da little Bros, d'insa, duk yazo da rigima suke rabuwa, duk kuwa da sai ya bita ya mammatse ya lalub'eta amma hakan bai masa shidai ta yadda ta bada kai bori ya hau, ita kuwa tace nahi (Aa).., wani sa'in har tausayi yake bata saidai tana tsoron yin ciki, don Aunty ta tsorata da cewa muddin ta yadda ta bata kai ba tare data koma ba to ciki zatayi, itakam bata sake ciki da wuri haka (WO Siddi tsoro) lolz. Wata biyu sukayi Mai martaba yace su tattara su koma, Aunty tace ai kam tun kan wannan surukin nawa yai mana bore dariya akayi gaba daya Siddiqa kam sunne kai tayi a cinya tana dariya, ranar da zasu koma sukayi waya da safe yace cewa bazaizo wannan week ba tunda ko ya taho tayar masa da hankali kawai take ta barshi da yin azumi, dariya kawai tayi, shi kuma yayi fushi yace baxai k'ara zuwa ba in taga dama ta dawo intaso ta tabbata can ya kashe wayarsa...(zuciyar maza ta kono)lol. Kamar yadda ya saba idan ya dawo zai shiga part d'in Momy kafin ya wuce nasu, yana shiga idonsa yai tozali da abar kaunarsa sanye cikin code lace pink and gold color an mata gown, murza idonsa yayi yaga dai gaske itace, fuskewa yayi waishi fushi yake, gun little kawai yaje dake hannun Hanan tana mishi wasa sai bangalar baki yake yana dariya yayi girma abinda kamar ba d'an 2months ba, yana sanye cikin Riga red da Jean black, shoe din ma red sai k'amshi yake zubawa. Ansarsa yayi yana mishi wasa sai dariya yakeyi ya kalli Momy yace "Momy kinga yanda Umarinki yayi girma da wayo?" "Na Gandhi mana, gashinan sai dalalan yawu, niba tashi nake ba ta 'yata Nike." Siddiqa sai dariya tace musu, tana gaidashi yayi mata kamar baiji ba, saida Momy tace "bakaji ana gaida kai bane Son, ko sannu da hanya baka mata ba, sai ta d'anka kake." "Oh to sannu anzo lafia" kawai ya fad'a fita da little a hannu. "Oh Son rigima, kina fama 'yata." "Hmm ki barshi Momy fushi yake saboda, ban gayamasa zamu dawo ba" ta fad'a tana murmushi sannan taja su Zubaida zuwa part d'in ta........ *9:30.......* Tana tsaye gaban mirror tana Shafa turare alaman da wanka ta fito, ya turo kofa ya shigo, wajen bed din little yaje ya ganshi sai bacci yake an shiryashi cikin sleeping dress d'insa, kiss yayi masa tare da Shafa kansa yayi mishi addu'a. Gurinta ya k'arasa ya kama k'ugunta da hannayensa ya d'ora kansa a kafard'arta yasa baki ya cije mata kunne, k'ara tace "kai piyaa ka cika mugunta mena mama?" Ta fad'a tana turo lip. Juyowa yayi da ita gabansa ya kama lip d'in da nashi lips, yana tsotsa, saida yayi mai isarshi sannan ya barta yace "waike ana fushi dake amma ko'a jikinki ko? Tau zakiyi bayani gani gaki" yana gama fad'a haka ya sunkuceta sai kan bed ya direta ya cire towel din ya 'yar. Deep and hot kiss yake bata ta ko'ina tuni itama ta fara mayar danata sokk'onin, sun d'auki lokaci a cikin yanayin kafin daga karshe Haiydar ya turning light up, ganin za'a shiga duniyar nishad'i yasa ni (Meryerm Abdool na tattaro nawa da nawa zan bar d'akin kar naga abinda yafi K'arfina, bar kawo kofa naji sanbatun Haiydar). "Ahhhhhh wasshhhhh, baby love yane...ya haka.... Wayoo....baby.... Kai....ashhhhhh....woooo.." _a 170 nabar d'akin_ πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸƒπŸ½β€β™€πŸ™ŠπŸ™ˆ. πŸ‘‰πŸ»πŸ˜œ. ✍🏻 πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:22 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HAD'UWATA DAKE_*πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _based on love story_ ) ```Written``` ```By``` πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER_* *P.M.L* ```MANZON ALLAH (S.A.W) YANA CEWA:-``` _Kashe dinku da zato, domin shine mafi k'aryan zancen._ Sannan yana cewa:- _Kashe dinku da hasada, domin tana cinye kyakkyawan aiki, kamar yadda wuta kecin itace._ *sisi, zato zunubi ne koda ya zama gaskia, mu daure mu rik'a yiwa kowa kyakkyawan zato, koda kuwa an cutar da mune, ladar na gurin rabbil izzatih.* *sisi meya jaki yiwa wani ko wata hasada akan ni'imar da Allah yayi masa? Hasada na nufin jin zafi, k'uncin zuciya, nuna bakinciki akan ni'imar da Allah yayi ma wanninki, hasada mugun ciwo ne, saimun dage da Neman tsari daga gareshi.* Allah yasa mudace πŸ‘πŸ» *Page* 68&69 Cikin takun k'asaita irin bata tace saukowa daga stairs d'in, sanye take da top ash and pink mai bud'ad'en wuya, da mini skirt black, tayi parking kanta a tsakiya, sai k'alli yake, ya sauko zuwa wuyanta, tasha makeup, chewing gum takeyi in personality da d'an bakinta da yasa lipstick pink. Tunda ta fara saukowa ya kafeta da ido ko kiftawa bayayi, shima yayi gayunshi cikin shirt white and black da jean blue, sai farin glass na gayu daya laka a idonsa, ya d'ora kafa d'aya kan d'aya, yayi tagumi sai aikin kallonta yake. Tana k'arasowa hure mishi ido tayi tare da janye hannayen daga fuskarsa tace "kallon fa?" Smiling tare da janyosa da k'arfi ta fad'a jikinsa, d'an k'ara tayi tare da dukan k'irjinsa tana turo lip. Capke lip d'in yayi tare da matseta a k'irjinsa yaci gaba da bata light kiss, lumshe ido tayi tare da zagaye hannayenta a wuyansa tana tayashi jin dadin, ita kanta tasan tayi missing gwarzon mijin nata sosai, tsawon 10mnt suka d'auka sannan ta fara janye bakinta ta lume a k'irjinsa tana maida numfashi. Rad'a mata yayi a kunne, cikin muryan shaukin so " baby love kin canzamin da yawa, kin rikitani, kinsa na manta kaina, dama haka mata ke zama idan suka haihu? Gayamin mesu Mama suke baki meye sirrin?" Smiling tare da mik'ewa taja hannunsa zuwa dinning area, tana fad'in "sirrinmu ne piyaa basai ka Sani" tare da kashe mishi ido d'aya..... Tsawon sati d'aya ana murza love, little kan da anyi wanka su Hanan zasu d'aukesa zuwa part d'in Momy, can yake wuni sai kuma idan yaji yunwa, sam baida tsanani, kowa tara ya samu.... "Baby love! Baby love!!" "Yes piyaa" ta fad'a tana fitowa da kitchen, k'arasawa tayi tare da hug nashi tayi pecking nashi, tare da tambayanshi aiki, shima peck ya bata a goshi sannan ya ansa da lafia, tare da tambanyan gida da prince d'in sa, ansan briefcase tayi tare da jan hannunsa takaishi d'aki tare da taimakonta yayi wanka ya shirya sannan suka sauko k'asa sukayi lunch. Bayan sun gama sun baje a parlour suna hutawa, cewa yayi " oh kinga zan manta ko? Ina zuwa" ya fad'a tare da mik'ewa. "Mene piyaa?" "Hold on! Am coming dear" ya fad'a tare da hayewa stairs d'in, dawowa yayi tare da wani envelope a hannunsa yace "oya baby close ur eyes and give me ur hand." Ba tare da musu ba ta rufe tare da bashi hannu, Abubuwa ya d'ora a hannun yace "surprise" yana dariya. Bud'e idonta tayi tozali da surprise kuwa, visa ne da passport, sai key na motar, kallonsa tayi cikin mamaki dason k'arin bayani, smiling mai tsada yayi mata yace. "Visa ne na honeymoon ne da zamuje very soon, so saiki zaba mana countries d'inda kikeso muje, key kuma na motarki ne, wannan duk tukuici ne akan faricikin da kike bani a rayuwa, kinyi min komai Maryama, ba abinda zance dake sai nagode wa Allah daya bani ke a matsayin haske mai haskaka rayuwata". Rungumesa tayi tana jin kaunarsa na k'ara ratsata, tace " thanks so much my dearies sweatable husby, ur d best in besties, my star dat shine in d night, my noorul hayatih thanks more and much abban Yayana" ta fad'a har da 'yar k'wallarta ta farinciki. K'ara rungume ta yayi yace "u deserve more than dis baby, u are my would world, so no thanks" ya fad'a ya mik'ar da ita tsaye yace. "Muje kiga car d'in taki" a tare suka fita, mota ce, matrix new version fara mai kyau, shiga tayi ta zauna, wow readers nasan kun hango Siddiqa a mota. Lolz. Part d'in Momy suka shiga ya gayamata isowar motar da maganar tafiyarsu, da yake tasan da zancen, albarka ta sanya tare da nuna farincikinta, daga nan suka d'auki su Hanan da Prince d'insu akaje tasting. Sati d'aya yayi yana koyamata hannunta ya fad'a, don Siddiqa bata tab'a kaud'in koyon mota ba, wannan abar su Aunty Ramlah tuni aka k'ware. *A week later....* A yau ne flight d'insu Mr&mrs D one ya daga bayan sunyi decided zuwa kasashe biyar *Turkey, India, south Africa, Dubai and Saudi Arabia* sunyi bankwana da 'yan uwa da abokan arziki, kowa na musu fatan alkhairi. _safe journey Mrs Sadaukis_ ✈ *************"***"** *Wai ina labarin Haj, Bara shin anga Fuu kuwa ko Yaya?* Abubuwa da dama na jarabawa suka had'ewa Haj, Bara, bokayenta na tsaka da tatsarta suna shirya mata k'arya, sako ya samesu na rasuwar Alh, Sambo kwangila asanadin crash da flight d'insu ya samu ya k'one k'urmus, bone yoyo, ga tashin miji ga b'atan 'ya, kuma wata ta b'ullo Alh, Sambo yaci bashin banki na billiyoyin kudi asanadin 'yan 419 daya had'u suka damfaresa kud'i sosai, ba tare da yayi shawara da kowa ba yaci bashin banki, banki kowa yasan basusan hasara ba ko rashi haka aka sayarda gidajensa da sauran kadarori har gidan da suke ciki, ba'a barsu dashi ba, lokaci daya komai ya k'are, har takai 1k sha'awa take bata, duk k'awaye da masoyan da take tak'ama dasu suka gujeta, gashi tayima masu sonta da gaskia rashin mutunci( dama haka rayuwa take baka gane me k'aunarka da gaske saika shi ga musiba). Saiga Haj, bara ta koma 'yar wanke-wanke a gurin wata mai saida abinci a bakin hanya, gaka masifaffiya komai nata masifa haka zata saka Bara gaba in tayi mata kuskure, ita kuma sai lallab'a da bada hak'uri gudun kada ta rasa hanyar cinta, inka ganta ba zaka ganeta ba, duk ta fita hayyacinta, ta lalace, ga sanyin ta dawo calm and cool, kullum cikin kukan nadama takeyi, ta yadda cewa duniya tafi bagaruwa iya jima(Wanda ya taka ta sannu bata barshi ba, balle kayi mata garaje, duniya ba tabbas). Kwatsam Dady yaji labarin halinda take ciki, ya shiga tashin hankali jin halinda gudar jininsa take ciki, duk kuwa da irin rabuwarda sukayi, bai warganta ba ya tafi gurin tare da rakiyar Momy, saida ya zubar da kwalla ta yaga inda 'yar uwarsa ke rayuwa, ita kam mamaki tayi sosai dan batayi tunanin yayanta zai k'ara waiwayar lamarinta ba, saboda irin abinda tayi mishi, lalai naka sai nqka. Cikin kuka sosai ta durkusa gabansa tace "Yaya don Allah kayi hak'uri ka yafemin, kaga abinda nake girba ko, ko yanzu ubangiji ya nunamin girmansa Yaya na tub'a" ta fad'a tana k'ara fashewq da kuka. D'agota yayi yace "Bara ke jinina ce kinga kuwa hannunka baya rub'ewa ka yanke ka yar, kuma ni ban kullaceki da komai nasan by time going zaki gane in masoyinki ne, kuma na godewa Allah dayasa kina cikin masu rabo, da har ya jarabceki da nuna miki duniya ba komai bace, yanzu kin koyi rayuwa kuma kin gane kuskurenki alhamdulillah Allah abin godia". " hakane Yaya nagane na tafka kuskure mai girma a rayuwa ta komai Fauziya tayi nice sila, saboda Nina b'atata aganina gata nake mata Ashe halaka nake sakata ciki, sai daga baya k'awayenta sukazo suka gaywmin duk abinda suke aikatawa da yake su sun samu shiriya (cewa dasu Lady) nan dai akaita maida zancen ta nemi yafiyarsu, sukace komai ya wuce. Alheri mai yawa Dady yayima ma mai abinci, taji mamaki da kunya data gane wacece Haj, Bara, hak'uri ta bata, tace ba komai ai rayuwa ce, haka suka wuce gwandu ta nemi yafiyarsu kawu da sauran 'yan uwa, sannan suka dawo Bk, zama suke na gaskia da amana kowa yana K'ok'arin farantawa d'an uwansa..... B'angarensu Siddiqa kuwa suna can sai shakatawa suke, suna waya akai akai gida suji lafiyar juna, sun ziyarci countries 3 suna India Wanda daga nan sai Saudi Arabia, one month sukayi a kowace k'asa. Haiydar ne zaune cikin wani lambu a cikin gidanda suka kama gurin ya had'e kunsan India da tsara guri, yana kwance bisa resting chair yana danna tab, Siddiqa ce tafe sanye da sari ya ansheta sosai kaman amrita road(lolz) kwantawa tayi a jikinsa tace "piyaa wai me kake dubawa a tab d'innan ne kullum cikin latsata kake, shine kawai abinda baka daina ba a cikin halayenka dana sanka dasu a skull." Smiling yayi yace " kinga abinda nake dubawa" ya tura mata tab d'in, folder ce ba abinda ke ciki face hotunanta, wadanda batasan dasu ba, harna rwnar da ta fara skull akwai, mamaki ya kamata, tace . "Ya akayi ka d'aukesu?" Smiling ya k'ara yi yace" basar kawai 'yan matana, wayo ake maki baki Sani ba" ya kashe mata ido. Dukan wasa tayi mishi tace " amma shine kake wani sham K'amshi idan ka ganni." "Ai kedin CE saida taku" dariya sukayi gaba d'aya.... Daga India suka dira saudiya inda suka zage damtse sukayi bauta sosai, da yin ibada!!.. Yau flight d'insu ya tashi zuwa gida naija bayan tsawon hutunda suka sha, cike da tsaraba. _sauka lafia matafiya_ βœˆπŸ‘†πŸΏ *Fateema (Mrs bello) gaisuwa gareki* πŸ‘πŸ». ✍🏻 πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„ [5/20, 6:35 PM] πŸ’„Meryerm AbdoolπŸ’„: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *_HADU'WATA DAKE_* πŸ‘‰πŸ»πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ( _Based on love story_ ) *Written* *By* πŸ’„ Meryerm AbdoolπŸ’„ Β© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* *P.M.L* πŸ’“ _K'aunarku a raina ta daban ce kaman yadda kuma kuke na daban, kun wuce abokai kun wuce aminai kun wace 'yan uwa kun wuce...... Bansan me zance ba, all what I known u r so special 2 meπŸ’— *Maryam dakingari, Maryam warah, Maleeka Autah, Hadiza garba*, and rest kuna raina a ko yaushe, Meryerm Abdool takuceπŸ’ž Allah ya bar k'auna_ AmeenπŸ‘πŸ» *Page* 72&73 *_AFTER EIGHT YEARS_* _tunda muka sha sunan Arjun muka rak'ashe muka bararraje, na cikawa buje na iska, nayi balaguro sai yau na dawo, nace bari na garzayo naga wace wainar ake toyawa_ 😜 Motar ce bak'a kirar Highlander 2016 sai kyalli tace naga tayi parking, a parking space kafin ma ya matukin ya kashe motar naga wata yarinya ta fito sanye da uniform, gown ce iya gwiwa da mini hijab sai sock fari da shoes bak'ak'e, zatayi kimanin 3 year, kallon fuskarta nayi da naka tana kama da Siddiqa saidai fatar irin ta Haiydar ce, da gudu ta kwasa tayi cikin main parlour tana fad'in "Momma am back" Siddiqa na gani zaune a parlour zaune tana kallon zee TV, cikin shigar alfarma ta kara wani fresh alaman hutu ya zauna, jin kuwwar Salma ne ya sanar da ita dawowarsu murmushi tayi tana fad'in "kai Huda na hankali" sannan ta canja tasha zuwa Africa TV 3. Sallama tayi tare da fad'awa jikin Mamanta tace "Momma am back." "Ur a welcome my preety, how was skull?" ta fad'a tana cire mata hijab, tace "oya jeki gun Habiba(sabowar maid d'insu da yake anyi ma Zubaida aure kwanaki, sun taka rawar gani sosai sunyi mata komai da iyaye kema 'yarsu) ta cire miki uniform ayi wanka, kinji 'yar albarka). Time d'in sauran suka doka sallama, namiji biyu da mace d'aya sanye da uniform suma irin na Salma, mazan sun sha zanzaro, Kansu d'aya saidai d'aya yafi daya jiki kad'an d'aya kuma yafi fari, a ido zakace sunyi ten years, kallonsu nayi da kyau, yadda day'an ke tafiya cikin tak'ama da izza yana wani basarwa da kaman da yake yi da Haiydar yasa na gane Arjun, shi kuma d'ayan little ne dan kamaninsa sun k'ara fitowa Sak irin na Ya Umar, macen kuma itama kamar Arjun saidai farace tas ita, itama sai feeling take(nace tofa sai haihuwa D one kam) lolz. Da sauri little ya isa inda Siddiqa ya rungume ta yace " oyoyo Momma missing u" itama rungume tayi tace " oyoyo da Yayana yau Kaine a gidan?". "Eh dama na gayama Momy kada aje d'aukana zanbiyo Papa nazo na ganku" Smiling tayi tare da Shafa kansa tace "Good boy kayi tunani nima ina missing naka". " Momma am back." "Mommah am back" Arjun da Humaira(Ayshat) suka fad'a a tare. Rungume su left and right side sannan ta Shafa musu kai tace "welcome swerrys, how was ur studies?". " fyn oo Momma" suka fad'a, sannan tace " Bros, Arjun go and fresh up than come and having lunch". "OK Momma" suka fad'a tare da wucewa d'akin su. Sannan ta kalli Humaira tace "my Humee ja hannun uktih d'inki kuje gurin Habiba ta muku wanka, kuzo muyi lunch" turo maki Humaira tayi tace " Momma ni danyi da kaina, saidai tama Hudah". "OK kiyi dakyau kinji babynah" gyada kai tayi taja hannun Hudan suka shiga ciki, sauke numfashi tayi tare da cewa "nawa woo" gyaran murya taji anyi, tayi saurin duba gurin ta duba, Haiydar ta gani jingine da k'ofa ya rungume hannayensa a k'irji yana jifanta da murmushi, jima dai bai canja ba yana nan yanda yake, saidai ya k'ara fresh hadda wani dan tumbi daya aje alaman kudi da huta sun zauna, sanye cikin suit bak'a yace. "Inkin gama da pretty, swerrys, Yaya, sai azo aji da babban baby". Cikin takunta ta isa gareshi tare da hugging nashi tayi pecking nashi tace " ai dama Kaine babban baby kuma naka ne farillah, nasu nafila ne" ta fad'a tana mishi fari da ido. K'ara rungume ta yayi tare da mata light kiss a lips, yace "yawwa matata, shiyasa farashin sonki ke k'ara hauhawa a kullum cikin zuciyata, amma kinsan me?" "Aa saika fad'a." "Uhum! Yau na hango wata......katseshi tayi ta hanyar dukan k'irjinsa tana bubbuga k'afa, sannan ta turbune fuska da shirin kuka, sannan ta janye jikinta zata tafi. Rik'eta yayi yana dariya yana fad'in " haba murucin zuciyata wasa nake fa" k'ok'arin janye hannunta take, ya rike gam tare da fizgota ta fad'a k'irjinsa, zata ci gaba da dukanshi ya rad'a mata a kunne "a parlour idan yaranki suka fito suka gammu kece da kunya" tonu haka yasa ta jashi zuwa ciki, tana hararanshi shi kuma yana mata dariya, saida suka gama rigimarsu sannan ta taimakamai ya wanka ya shirya. Koda suka fito tuni yaransu sun hallara a dinning su kawai suke jira, little da Arjun kaya iri d'aya suka saka but different color, itama Humaira da Huda nasu iri d'aya an kama kowacce kanta da kalan kayanta, gashi sai reto yake a bayansu. Kujera yaja ya zauna ita kuma tayi saving d'insu tare da basu umarnin yin basmala, cin abinci suke cikin nutsuwa har suka kammala ba Wanda ke magana, hamdala sukayi, aka tattara kwanukan akai kitchen sannan suka zube a parlour. Inda suke kallon dandalin yara manyan gobe, remote Arjun ya dauka ya canja tasha zuwa peace TV, inda Dr, Zakir Naik gabatar da shirinsu na *similarities b/w Islam religious and Hindustan* Humaira ta baki tace "papa kaga Arjun Ahih ya canja mana tasha, kuma manyan gobe akeyi" ta fad'a kamar tayi kuka saboda son shirin da takeyi. "Arjun meyasa ka canja Tasha?" Yamutsa fuska Yayi yace "inaso na kalla ne Papa" Murmushi Siddiqa tayi ganin iko irin na Arjun tace "to sannu second D one, inso kake ka kalla ka koma d'akin Ku mana" ta fad'a tare da d'aure fuska. Hararanta Haiydar yayi, shi kuma Arjun ya m'ike yana yamutsa fuska yabar parlon, murmushi tayi dan tasan dalilin hararan. Jin anfara kiran sallah ne Haiydar yace da little "Prince kira Arjun muje masjed" mik'ewa yayi ya tafi. "Yawwa Papa kace yau tunda ba islamiyya& tahfiz jamuje gidan su Dady!" Cewar Huda. Shafa kanta yayi yace "kai Salmana naga Yayan nan yazo ba". " Aa papa muje zanga cu Momy da kaka da Aunty Hanan". "To my Mamah barin dawo da Sallah sai muje ko" saboda yanda yake son yarinyar sbd kaman da takeyi da Siddiqa. "Baby love sai ku zama cikin shiri" kwalalo ido Huda tayi tace "papa wai sai kata kiran momma baby, bayan ita babba CE" baka baki yayi yana jinjina wayo Huda, lallai dole yazo ya daina cewa haka gaban su. Siddiqa dariya tayi dama ta gayamai ya dena fad'a a gaban su, dai2 nan su Arjun suka fito yaja hannunsu suka wuce, itama taja matan suka shiga ciki sukayi tasu... ******************* Da gudunta ta shigo parlour bayan tayi sallama tare da ta haye kan cinyar Hanan wacce zuwa yanzu ta zama Budurwa sosai kyanta ya k'ara fita yanzu suna level one university tare da Rufaida(kanwar Siddiqa) tace "Aa Mamana kece a gidan? Keda waye?". " nida cu Momma ta Papa dacu uktih da ahih" da fad'a tana dariya, sannan ta kalli Momy da Haj, Bara(wacce ta Auri gateman gidan daya nuna yana ra'ayinta tayi na'am da yake mutun ne mai kirki mal, Haruna kuma matarshi ta rasu, shine Dady ya basu part d'aya daga cikin gidan sa suke zaune lafia, inda yanzu baya gadi, shago Dady ya bude mishi a sabuwar kasuwa yake business d'insa acan). "Momy, kaka cannunku" cewa su kayi "bazamu ansa ba sai yanzu kikayi lokacin mu" dariya tasa tare da hayewa cinyan Momy dai nan sauran suka shigo. Bayan an gaggaisa Little yaje kusa da Momy tare da d'ora kan shi, a cinyarta tace 'Umari na iyakar weekend d'in kenan?" Smiling mai k'ayatarwa yayi mata yace "kinsan bana iya zama banganki ba, kinsan me?" "Aa saika fad'a " "Yau a skull an tambayemu our ambition". " iyye Umarina mekakeso ka zama hala" " I said I am Umar Aleeyu Sadauki, 4rm primary 5, 9 by age, I want 2 b an engineer, kinga saina k'era miki gidan k'arfe" ya fad'a yana dariya. Itama dai dariyar k'arfin hali tayi cikin ranta kuwa d'anta ya tuno mata dashi komai irin nasa yake, oh Allah kenan ya dawo mata da Umar d'inta, gashi yau ya zabi irin course din baban nasa, ba ita kad'ai ba duk wani babba dake parlour saida little ya tuno masa da Ya Umar, addu'arda suka saba masa idan suka tuna shi ita sukayi, duk kuwa da kullum cikin yimasa sukayi, saboda bazasu iya mantawa dashi ba, although ma ga copy nashi ya ishesu debar kewa. Kakace tace "to kaifa miskili nawa ni kad'ai meka zaba mana?" Cewa da Arjun, Wanda tunda suka shigo ya kame gefe sai feeling yake. Yatsina fuska yayi saida ya gama tanbad'arsa sannan yace "I am Abdulmajid Aleeyu Sadauki, 4rm primary 5, 8 by age I want be a medical doctor, so I will inject u when u r sick" ya fad'a cikin d'aure fuska irin yama zama likitan o. Kowa saida ya dara a parlon banda shi, daii smiling kawai yayi, Momy tace

Chapter 14 of 16