Share this page
ta tashi taje ta buɗe, Ihu tayi na murna tare da faɗawa jikinta "Mammaaaa" ta faɗa cike da tsantsan farin ciki suka yo cikin falo nan take ta cika mata gabanta da kayan ciye ciye tama rasa inda zata sakata saboda farin ciki Mamma sai kallan take yi taga duk ta sauya jikinta yayi kyau alamun hutu ya zaunu "Mamma ki ci" To ni nama rasa wanne zan ci " Duka zaki ci" Haba Alesha duk ina kike san nakai waɗan nan abubuwan ?" Cikin ciki " Mamma tayi murmushi tace " Ba kowa ne a gidan ke kaɗai ce?" Eh Noor taje school yaya kuma na wajen aiki " Allah Ubangiji ya taimaka " Mamma ni dai ki fara ci na gani " Kar'bi dai wannan kije ki kai bedroom ki aje " Mamma ta faɗa tare da miƙa mata wata leda ta kar'ba taje ta kai ta dawo ta takura ta dole sai ta ci gaba Mamma ba yadda ta iya dole ta fara ci ta k'oshi amman Alesha sai da ta d'ura mata shi ta gama suka fara fira Alesha na kwance saman jikin Mamma Azaad ya shigo ɗaukar wasu takardun da ya bari Gaisawa sukayi da Mamma cikin mutantawa har ƙasa ya ke Alesha na kwance jikinta taƙi tashi bayan ya miƙe ya kalleta yace "Ki tasar mata saman ƙafafu mana" Ƙafad'a ta mak'e kamar ƙaramar yarinya ta turo baki tace "To ai mamana ce" Uhmm tun da ke kaɗai ta haifa ko?" Mamma ni ki faɗa masa kar ya takura min" Ai gaskiya my son ya faɗa son ki kai ki ida ƙafafun ne ?" Jin haka yasa ta tashi ta koma gefe ta turo baki wai tayi fushi "Haba ko ke fa yanzu ma ai harda iska sai ta ji amman kin zo kin maheta" Mamma dariya take Alesha ta juya fuska ta ma daina kallon wajen da suke "Mama bara naje na ɗauko wasu takardu da zan kai office"To Shikenan " ya wuce yayi d'aki Mamma ta kalli Alesha tace" Ki tashi ki je ki taya sa duba takardun" ta miƙe ta nufi d'akin ta ja tayi tsaye ya kalleta yace "Baki sanar min zamuyi baƙi ba" Nima bansan zata zo ba "Okay" Ya d'auko suka fito ya wuce Yana fita Ummie na shigowa ta kalli Mamma tace"Ina wuni "Lafiya kalau ya gida" Lafiya "ta faɗa tare da wucewa bedroom Mamma ta bita da kallo ta juyo ta kalli Alesha tace"Kar dai ki ce min Ummie gidan nan ta dawo?" Wai tazo hutu ne"Hutu? Tun yaushe tazo?" Zata yi kusan wata" Uhmmmmmm Alesha kina ganin zamanta a nan ba wata matsala " Eh in sha Allah mamma ba wata matsala"To Shikenan Allah yasa " Amin" Mamma ta ƙara yi mata nasiha sosai, Azaad ya dawo ɗauke da manyan ledodi guda biyu ya bama Alesha yace ta ba Mamma ya juya ya koma, Alesha taji daɗi sosai Da mamma ta tashi ta bata tayi ta masa godiya tare da yi masa addu'a Ummie tana shiga d'aki ta wuce toilet tayi wanka ta fito ta kwanta zuciyarta cike da farin ciki na ganin burinta ya kusa cika bacci ya ɗauke ta Tsawon kwana uku tun da suka dawo wajen malamin da suka je har yanzu bata samu damar ai watar da shirinta ba saboda malamin yace idan zata yi amfani da shi ya kasance daga ita sai shi ne kuma sharad'in sai ta fita daga gidan sai tayi amfani da kwallin ta shigo da zarar sun yi 4eyes da shi Shikenan an gama zai ji duk duniya ba wacce yake so sai ita sai ɗaurin magani wanda zata zuba masa a abinci shi kuma da ya ci duk abunda tace haka za'a yi bazai sake jin maganar kowa ba sai tata Alesha tayi aiki ta gaji, duk abunda yake gidan nan wanda ake gogewa sai da ta goge ko'ina sannan ta share tayi mopping har cikin dakunan su ta wanke toilet toilet ta wanke ƙananun kayan su tayi girki tagama ta bad'e gidan da k'amshi duk aikin da take yi Ummie na zaune tana kallanta sai da ta kammala komai ta faɗa toilet dan yin wanka Ummie ta fito falo tana ganin Azaad da sauri ta koma d'aki ta ɗauko kwallin ta ɗauki mayafi, Noor na zaune tana game da wayar Mommynta ta fito ta fita gidan gaba ɗaya ta tsaya gefen gate ɗin ta shafa kwallin ta janyo mayafinta ta ɗora har saman kai ta rufe fuskarta kamar sabuwar amarya ta tura k'ofar gate ta shiga mai gadi shi dai na zaune, tafiya take bata ko kallan gabanta mai gadi daga can ganin zata take wani k'adangare wanda tun d'azu yake wajen da alama bai da lafiya yasa ya ce " Kai kai kai gaban ki" A yadda yayi maganar sai da ta tsorata saboda da ƙarfi yayi aiko ba shiri ta yaye gyalen ta kalli gabanta bata ga komai ba k'adangaren ya gudu ta juyo ta kalli mai gadi ido huɗu suka yi da shi ta wurga masa harara tace "Lafiya?" Murmushi ya sakar mata........................ 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Alƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 24&25 Ta sake 'balla masa harara har ta juya ta tuna da ta yaye mayafin kuma sun haɗa ido da mai gadi, wani uban ihu tayi tare da juyowa ta kalli mai gadi wanda ya ɗan matso kusa gareta tace "Wallahi ka cuceni ka cuce ni Allah ya isar min ban yafe ba" ta faɗa cikin kuka " Wallahi bazan yafe ma ba duk wannan baƙar wahalar da na sha Shikenan ta tafi a banza ka rusa min komai ina farin ciki komai yazo ƙarshe yanzu gashi............." Bata samu damar ƙara sawa ba saboda kukan da yazo mata ga wani baƙin ciki da haushin mai gadi da ya tsaya mata wallahi a yadda take ji kamar ta samesa tayi ta duka Ta kama hanya tana tafiya tana kuka, Mai gadi ya biyo bayanta yana faɗin" Dan Allah ki daina kuka ki tsaya ki faɗa min me aka miki ki daina kuka wallahi jin nake nima kamar na kama miki kukan dan Allah ki daina kinji gimbiya " Ummie ko jinsa bata yi tasa gaba sai kuka take a haka har ta shige ciki mai gadi ya ja yayi tsaye yana faɗin"Gimbiya! Gimbiya! Gimbiyata ki tsaya" ya faɗa sai ga hawaye shi ma ya nemi waje ya zauna bakin k'ofa Alesha tana fitowa wanka ta ja Noor ita ma tayi mata wanka ta shiryata cikin ƙananun kaya riga da wando ta bata waya ta ci gaba da game ita ma ta shirya ta haɗe cikin ƙananun kaya riga da wando ta saka hula kalar wando basu wani kama jikinta sosai ba duk da haka sun fito mata da surar jikinta, kayan sun ɗebota sosai sun mata kyau, sai k'amshi suke zubawa ita da Noor kamar inda aka yi ɓarin turare a jikinsu, Ta wuce ta ɗauki Noor tace "Washhhhhhhhhhhhhhhhh"Noor ta kalleta tace "Mommy kin gaji?" Alesha ta gyad'a kai tare da yatsina fuska tace " I'm very tired baby" Sorry Mommy I'll tell Daddy to buy you some sweets, you're tired. Okay " ta faɗa tare da gyad'a kai Alesha tace"Really, my dear ? " Noor ta gyad'a kai ""Alright, let's go to the living room before dad returns."Okay mommy" Suka nufi falo sai ga Ummie tafe tana kuka "Subhanallah Ummie meya faru? Me aka miki ki ke kuka?" Alesha ta faɗa lokacin da Ummie ta ƙara so wajen su amman ko tsayawa bata yi ba ta wuce bedroom, hankalin Alesha ya tashi ganin yar' uwarta na kuka ta aje Noor tace ta jirata ta zo ita kuma ta bi Ummie a d'aki Tsaye ta tarar da ita tana kuka sosai irin na ban tausayin nan wallahi ta bama Alesha tausayi sosai duk da bata san dalilin kukan nata ba, ta dafa kafad'ar Ummie cikin sanyayar murya ta kira sunan ta tare da faɗin "Ummie dan Allah ki daina kukan nan kinji ki faɗa min meya faru" Ta faɗa cikin raunanniyar murya, Ummie ta juyo ta kalleta da idanunta da suka yi ja saboda kuka ta wurga mata harara tare da ture hannunta daga saman jikinta cikin kuka tace "Ba ruwanki da abunda yake damuna ki je kawai kiyi sha'anin gabanki" Haba ke kuwa Ummie kar ki faɗi haka mana please ki faɗa min meya faru "Idan na faɗa miki abunda yake damuna zaki min magani ne? Eh " Wallahi muddin ina da maganin damuwarki Ummie zan baki idan kuma banada zan roƙi Allah da ya yaye miki dukkan abinda yake damunki ya kawo miki mafita "Alesha na roke ki dan girman Allah ki fita wallahi bana ko san jin muryar ki bare kuma na ganki" Alesha tayi shuru tana kallanta idanunta sun ciko da k'wallah zuciyarta tayi rauni sosai Hawaye suka zubo mata ta goge ta kai hannu zata dafa Ummie, Ummie ta wani ja baya da sauri tare da ɗaga hannu tace "Banaso! Banaso! Ki barni Alesha " Ta faɗa da ƙarfi, Alesha ta wani marairaice fuska Ummie ta janye daga nan ta koma wani gefe ta barta nan tsaye, Ta share hawaye ta juya ta fito ta ɗauki Noor tana tafiya tana tuna abunda Ummie ta gaya mata yanzu har ta iso falo "Papah" Noor ta faɗa Alesha ta ɗaga kai ta gansa kwance shima ita yake kallo tun da yaji alamun tafiyarta ya mayar da dubansa wajen har suka ƙara so ga k'amshin su da ya mamaye falon kallanta yake tun daga sama har ƙasa ba ƙaramin kyau tayi masa ba sai dai fuskarta babu alamun annuri a tare da ita, Sauke Noor tayi hawaye suka zubo mata tayi saurin sa hannu ta ɗauke su Azaad na kalle da ita Ta juya da sauri ta nufi kitchen saka makon wani kuka da yazo mata Noor ta wuce wajen daddynta ta na masa surutu Azaad wani abu yaji ya tsaya masa a zuci wannan damuwar da ya gani a tattare da Alesha yasan ba zata wuce silar Ummie ba ce yana jin ta lokacin da ta shigo tana kuka amman ko kallanta bai yi ba, ya tashi zaune ya miƙe tsaye ya kalli Noor yace " Zauna nan ina zuwa kinji?" Ta gyad'a masa kai ya bi bayan Alesha Kuka take sosai ya ja yayi tsaye bakin k'ofa yana kallanta sai da taci kukanta ta buɗe pampo ta wanke fuskarta ta juyo suka haɗa ido tayi ƙasa da kanta, takowa yayi yazo gabanta ya tsaya yasa hannu ya ɗago ha'barta idanunta a lumshe yace " Look at me " A hankali ta buɗe idanunta ta kallesa ta kuma janye idanun " Mene ne? Tell me " girgiza masa kai tayi yace "Ba komai ki ke kuka?" Wani sabon kuka yazo mata Azaad ya janyota jikinsa ya rungume, Alesha ta rungumesa sosai tana kuka ya shiga bubbuga bayanta cikin kuka take faɗin "Yaya meyasa su Ummie basa so na Mansur baya so na basmah bata so na Ummie bata so na Mommy bata so na ba wanda yake so na daddy ma...,................. Ta rushe da kuka Azaad na bubbuga bayanta alamun rarrashi kukan ya lafa ta ɗago tace "A rayuwata ban taɓa sanin na aikata musu wani laifi ba amman tunda iyayena suka rasu lokaci ɗaya duk suka juya min baya duk suka tsane ni bansan me na musu ba " Wallahi ta ba Azaad tausayi tace"Yaya ina jin zafi a nan" ta faɗa tare da nuna k'irjinta Azaad ya buɗe fridge ya ɗauko mata ruwa ya kawo ya buɗe ya kafa mata robar ruwan a baki ta buɗe baki ta fara sha tana jin sanyin ruwan na ratsa zuciyarta taasha ruwan sosai sannan ya janye mata ya aje ya riƙo hannayenta ya kalleta yace "Wa ya gaya miki ba wanda yake son ki Yar' ki Noor tana son ki su Rukayya na son ki Mamma na son ki Ammie na son ki Daddy na son ki nima ina son ki"Ta ɗago ta kallesa yace "yes Alesha nima ina son ki so let they lose you if they think you're not enough if they don't see your value let them walk, people make time for who they care about and if they're not making time for you then believe them when they say they're too busy don't force it, if they wanted to be with you they would be if they choose something or someone else over you let them it hurts but you can't make someone feel what they don't you shouldn't have to beg for someone to care, to love you, to put in the effort, if they're okay with going weeks without talking to you or never seeing you, let them go focus on those who see your worth without you having to prove it, I always say one thing that I have stopped worrying about the thing's that I have lost , the people that I have lost, Things and people who are want to be with me are with me, So stop worry about mutanen da basu damu da ke ba basa son ki Okay we love you so much " Alesha ta faɗa jikinsa ta rungumesa tana jin wani irin sanyi da farin ciki yana ratsa gangar jikinta shima ya rungumeta sun kusa minti uku a haka sannan ta ɗago Ya d'aura hannunsa saman fuskarta ya shafi gefen kumatun ta yace "Ki daina sama kan ki damuwa akan wannan abun ba'a san damuwa saboda ba ƙaramin illah takewa mutum ba ki daina kinji" ta gyad'a masa kai yace" Idan Allah ya kai mu gobe ku shirya zamu fita " Toh" ya ɗago ha'barta bakinsa kawai taji a nata ya shiga kissing bakin "Papah! Papah!" Suka jiyo Noor na faɗi a bayan su Alesha tayi saurin ƙwace kanta daga gare shi tayi wajen Noor " Sweet mene ne?" Ana kiran Papah " ta faɗa tare da nuna mata waya Azaad ya zo ya karb'i wayar Alesha taja hannun Noor tace "Mu je" ya bi bayanta da kallo har suka fice ya sauke ajiyar zuciya wani kiran ya sake shigowa ya ɗaga shima ya nufi falon ya yi tsaye yana gama wayar ya aje zai zauna a ka k'wank'wasa k'ofa Alesha ta miƙa da zumma taje ta buɗe ya kalleta yace "A haka zaki je ki buɗe k'ofar idan masu aikin gidan nan suka zo wucewa suka ganki fa?" Ta koma ta zauna ya wuce yaje ya buɗe ƙofar Mai gadi ya gani tsaye ya kallesa yace"Lafiya dai?" Uhmmm yalla'bai Alhaji uhmm daman naga hajiya ta shiga ne tana kuka wallahi duk na damu " Azaad kallansa yayi da mamaki to ina ruwansa ko me yaga tana yi harda su faɗin ya damu ko yayi tunanin wani abu ne ya faru, ya faɗa a zuci sai yace masa"Kar ka da mu ba wata matsala ba ce " To Shikenan " Azaad ya juya zai wuce" Dan Allah kace ina gaidata " mai gadi ya faɗa Azaad Ya juyo ya tsaya sai kuma ya juya ya rufe kofar ya koma falo................ 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Alƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 26&27 "Hello rufi" Na'am ya ake ciki ne naji muryarki wani iri lafiya dai ko?" Rufi Komai ya lalace Shikenan tawa ta ƙare komai ya rushe" ta faɗa tare da fashewa da kuka Rufi tace "Ummie ki tsaya ki min bayanin abunda ke faruwa ban fahimci komai ba meya lalace? Dan Allah ki tsayar da kukan nan kimin bayani yadda zan fahimta" "Rufi maganin da muka kar'bo ne yau da na samesa shi kaɗai a falo sai na fita waje ina murna dan aiwatar da shirin....................................." Nan ta zayyano ma Rufi duk abunda ya faru" Amman mai gadin nan anyi ɗan kutumar uba wallahi shege yanzu Shikenan ya rusa muna shirin mu Allah dai ya ci ubansa ni wallahi kaina ma ya kulle na rasa me zan ce ya riga ya cuce mu Yanzu kinsan me za'a yi?" Sai kin faɗa" Idan Allah ya kai mu gobe zamu koma wajen malamin muyi masa bayanin abunda ya faru ko za'a samu mafita " To Shikenan Rufi nagode" Karki damu Ummie in sha Allah sai kin auri Azaad ki kwantar da hankalin ki kar ki sa damuwa a ranki " Rufi idan na ce bazan sa damuwa a rai na ba wallahi ƙarya na miki ni kaɗai nasan yadda nake ji wallahi rayuwata ban taɓa son wani ɗah namiji sosai ba kamar yadda nake son yaya Azaad ba " Ummie na sani hak'uri zaki yi zuwa gobe na tabbata zamu samu mafita" Allah yasa zuciyata kamar zata buga nake ji " Ki daina faɗin haka Ummie" Rufi ta rarrasheta tare da sanyaya mata zuciya da kalamai masu daɗi waɗan da take son ji sannan suka yi sallama Washe gari, Alesha tun da tayi sallar asuba bata koma bacci ba sanin Azaad ya sanar mata zasu fita duk da bata san inda zasu je ba ta kammala duk aikin da zata yi ta yi ma Noor wanka ta shiryata ita ma tayi wanka ta fito ta tayar da Ummie dake bacci ta tashi zaune ta kalleta tace "Lafiya?" Ki tashi ki shirya zamu fita " Mtsssssssssssssssssssssss saboda wannan dalilin zaki tayar da ni to ni ba inda zan je sai kun dawo" jin tace ba inda zata je yasa Alesha ta wuce dan shiryawa Ta shirya ta haɗe cikin wata had'ad'd'iyar atamfa orange color mai manyan zane ga ɗinkin atamfar riga da zane an mata ɗinkin mai kyau da ɗaukar ido atamfar tayi kyau sosai kuma ta mata kyau, ta kawo wata siririyar sark'arta mai haɗe da yan kunne da abun hannu ta saka ta d'aura agogo a ɗaya hannu ta ɗauko gyale da takalmi da jaka kala ɗaya kuma kalar da zata shiga da atamfar ta saka ta yafa mayafi ba wani makeup sosai a fuskarta amman wallahi tayi bala'in kyau kamar ita tayi kanta ta ɗauki turare ta feshe jikinta ta kira Noor ta ƙara fesa mata ta aje ta riƙo Noor kamar wata ƙaramar yarinya tace " Sweet nayi kyau kuwa?" Mommy sosai sosai " Dagaske?" Eh kuma ki tambayi Daddy zai faɗa miki "No ai tunda princess tace nayi kyau Shikenan"Iyyeeee ammata" Noor ta faɗa Alesha ta tuntsire da dariya "Wannan wane irin wulak'anci ne mutum na bacci ba zaku barsa yayi ba" Ummie ta faɗa tare da ɗagowa ta kalle su sanda tayi arba da Alesha sai da cikinta ya murd'a ta miƙe zaune da sauri tana ƙare mata kallo, wallahi ita kanta tasan Alesha ta fita da komai duk namijin da ya samu Alesha matsayin matar aure abu ne mai matuƙar wahala ace yana tsaya kula wasu matan bare kuma irin su Ummie sai dai idan ƙaddararsa ce a haka amman ita son sa ya rufe mata ido ta kasa ganin haka bare ta fahimta Dogon tsaki kawai ta ja ta koma ta kwanta taja bargo la lullu'be jikinta Alesha ta ja hannun Noor suka fito, falo suka nufa Noor tace "Mommy yau bazan je school ba?" Eh Princess Papah yace zamu fita yau va zaki samu zuwa ba sai gobe "Okay mommy" suna zama Azaad na fitowa shima yayi kyau ya haɗe cikin manyan kaya sai k'amshi yake zubawa, tun kafin ya ƙara so ya kafe Alesha da ido wajen kallanta har tashi faɗuwa yayi ya tsaya ya ɗan daidaita ya isa wajen su suka yi masa ina kwana suka wuce dining har suka zauna suka fara cin abinci idanun Azaad na kanta tun bata lura ba har jikinta ya bata da kallanta yake yi ta ɗago suka haɗa ido ya sakar mata murmushi tayi masa nuni da ido akan yaci abinci ya ɗauki spoon ya fara ci Bayan sun gama ta kashe kayakkin falo ta wuce bedroom ta sanar ma Ummie sun tafi ta dawo suka wuce ta buɗe ma Noor gidan baya ita kuma ta shiga gaba Azaad ya shiga yaja motar suka wuce Tafiya suke ba mai magana a cikin su har suka isa gidan su Azaad yayi parking suka fito suka nufi cikin gidan, Ammie da Dad ne kawai a gidan, cikin girmamawa Alesha ta gaidasu Noor na mak'ale da ita tama k'i yadda ta tafi wajen Ammie Dad wannan ne farkon ganin da yayi ma Alesha ya yaba da ita sosai ya ga alamun hankali da natsu a tare da ita, basu wani jima sosai a gidan ba suka wuce Wani had'ad'd'en saloon ya tsaya ya nemi waje yayi parking ya ɗauki wayarsa ya fara kiran Rukayya tana shiga a ka ɗaga yasa wayar a speaker yace "Fito gamu mun iso" Okay gani nan tafe " k'ittttt ya kashe wayar Ya juyo ya kalli Alesha ya juya ya kalli Noor yaga hankalin ta na kan game ɗin da take yi ya juya ya riƙo hannun Alesha wani irin taushi yaji a tafin hannun ta ya riƙe hannun sosai yana murza tafin hannun yace "Rukayya zata zo ta shiga da ku idan aka gama sai ki kira ni nazo na ɗauke ku idan dare bai yi ba wata k'ila mu biya ta wajen Mamma " Jin abun da yace yasa Alesha tayi murmushin jin daɗi har fararen hak'oranta suka bayyana tace"Okay " K'wank'wasa glass ɗin motar aka yi ta gefen Alesha ya saukar da glass ɗin Rukayya ce ta gaidasu Alesha ta fito ta buɗe ma Noor ita ma ta fito suka wuce Suna shiga aka tarbeta aka bata wajen zama ta zauna, sanin abunda ya kawo ta yasa basu tsaya wani ɓata lokaci ba aka ɗauko mata wani babban littafi wanda suke da design duk style ɗin kitso da lalle da gyara gashi duk wanda mutum yake so sai ya za'ba, gefen gyaran gashi ta duba saboda bata son kitso ta zaɓi wanda take so ta nuna sannan ta zaɓarma Noor kitson da za'a mata ta koma gefen lalle nan ma ta za'bi wanda za'a musu ta gama za'bawa kenan wayarta ta fara ringing Noor ta miƙa mata wayar Azaad ne ta ɗaga tare da kafa wayar a kunne yace " An fara?" Aah yanzu dai za'a fara "Okay kuna buƙatar wani abu na kawo muku?" Aah no bama buƙatar komai " To Shikenan sai munyi magana anjima"Okay " ya kashe wayar, aka fara Koda ƙarfe uku tayi an gama komai ta kirasa ya zo ya ɗauke su, Azaad banda kallan Alesha ba abunda yake yi kamar zai haɗiyeta, ita ta masa kwatancen gidan Mamma har suka isa, Mamma taji daɗin zuwan su sosai wallahi duk da basu wani jima ba suka wuce a hanyar su ta komawa suka tsaya supermarket suka shiga yace kowa ya ɗauki abunda yake so, basu ma wani ɗauki kayakki da yawa ba duk shi yayi ta kwasar musu suka fito suka wuce gida yana aje su bai tsaya ba ya fita Bayan sun shiga ciki ta duba Ummie bata nan ta kira wayarta gata tana ringing amman ba'a ɗaga ba har ta gaji ta aje ta wuce ta je ta aje ledodin da suka shigo da su abubuwan da tasan kuma zasu iya lalacewa ta saka a fridge Misalin ƙarfe tara na dare Ummie ta dawo bata cema kowa uffan ba har Azaad ta wuce warta bedroom ta faɗa toilet tayi wanka Misalin goma saura Noor

Chapter 8 of 13