yi sallah tare bayan sun gama ta ɗauko mata jakarta suka fito falo, Ummie na kwance tana charting ta kalleta tace "Ummie lokacin sallah fa yayi"Ban tashi yi ba " ta faɗa ko ɗago kanta bata yi ba, bata sake cewa komai ba ta wuce dining ta zubama Noor abinci ta zaunar da ita ta bata, suna gamawa driver na isowa har harabar gida ta rako Noor sai da suka wuce ta tsaya tana kallon yadda gidan yake, tunda aka kawota tsawon wata huɗu yanzu ko bakin k'ofar falo ƙafar ta bata taɓa lek'awa ba sai yau da ta fito tayi tsaye tana kallan gidan da fulawowin da ke wajen
ta juya ta fara tafiya kenan aka buɗe masa gate, tun da ya danno motorsa ciki idanunsa suka sauka a kanta ta juya tana tafiya, wani abu yaji ya tsaya masa a mak'ogaro yana tunanin meya fito da ita wajen nan, koda ya isa parking space yayi parking ya fito har ta shige ciki, ran nan nasa a ɓace ya wuce ciki
Koda ya shiga bai ganta ba tayi kitchen, Ummie da ta lula duniyar charting tana kwance bata tashi taje tayi sallah ba k'amshin turarensa ya ziyarci hancinta ta ɗago da sauri ta zuba masa na mujiya ta tashi zaune Azaad ko kallan wajen da take baiyi ba tace "Sannu da zuwa yaya Azaad"Sannu "ya faɗa tare da ƙara haɗe fuska, ta miƙe tsaye ta nufi wajen da yake tace"Yaya Azaad tun d'azu nake ta zaman jiran ka kasan fa zamu yi magana amman shi ne kaje kayi zamanka " Okay kar na je gun aiki kenan ko?" Ni ba haka nake nufi ba " Mtwwssssssssssssss dallah matsa min can" ya faɗa tare da ra'bawa gefen ta ya wuce ya zauna cikin falo
Ta zo gabansa ta durk'usa ta marairaice fuska ta kallesa tace "Yaya Azaad dan Allah ka bani lokaci muyi magana wallahi maganar nada matuƙar muhimmanci idan ban sanar maka ba zan iya cutar da rayuwata ka taimakeni ni ko ma nan ne ba matsala sai muyi magana indai zaka saurare ni wallahi ba matsala " Ko da ta ƙarashe faɗa gaba ɗaya hankalin sa baya nan yana kan Alesha wacce ta fito daga d'aki tana tafe tana shan ice cream cikin kwanciyar hankali a natse, Ummie ganin hankalinsa baya kanta yasa ta ɗago ita ma tana kallan sashen da yake kallo, bata san lokacin da taja tsaki ba tana mai kawar da kanta, tsakin da ta yi ne yasa ya juyo ya kalleta
Alesha turuss ta ja ta tsaya lokacin da ta iso cikin falon ganin Ummie durk'ushe a gaban Azaad sai kawai ta yi murmushi ta ƙara so tace "Sannu da zuwa yaya"Yawwa sannu ya kike ya kaɗai ci dan nasan by this time yar' ki ta tafi school " Ai kuwa bata jima da tafiya ba"Okay bara na je na samu na watsa ruwa " ya faɗa tare da miƙewa Ummie ta rafka uban tagumi, Azaad har yayi nisa ya juya ya kalli Alesha yace "Ki dafa min tea ki kawo min"Okay "Kiyi min irin haɗin da kika min jiya" An gama " ya wuce yayi d'aki, ita kuma sai da ta ida shanye ice cream ɗin da take sha sannan ta miƙe ta shiga kitchen
Ummie kamar ta ɗora hannu a kai tace wayyooo Allah tama kasa fahimtar komai tana mamakin yadda aka yi har yanzu bata janyo hankalin Azaad gareta ba duk wannan uban wankan da matsu da rangwad'ar da take masa sai taga duk abunda take yi ma a banza, tana nan zaune a wajen har Alesha ta gama dafa tea ta fito da shi ta nufi d'akin Azaad da ido kawai ta bi bayanta da kallo
Sai da ta k'wank'wasa k'ofar ya bata izinin shigowa ta turo k'ofa ta shiga turuss ta ja ta tsaya ganin sa ɗaure da towel a k'ugu tayi ƙasa da kanta ta cikin mirror yake kallanta "Ƙara so mana" ya faɗa duk da yana shafa mai a jikinsa but still ita yake kallo ta cikin mirror, taka wa tayi a hankali kamar wacce k'wai ya fashema a ciki, wani had'ad'd'en table ta nufa ta daura cup ɗin tea a kai ta janyo table ɗin ta kawo bakin gado ta aje wajen da ta tabbatar da nan zai zauna ta juya zata fita ta tsinkayo muryarsa yana faɗin" Jira ni na gama" Ta wani marairaice fuska ta juyo kallo ɗaya tayi masa tayi saurin yi ƙasa da idanunta saboda ya juyo ya kafeta da ido gashi ba kaya a jikinsa, Alesha jin take kamar ƙasa ta buɗe ta shige wani irin nauyinsa take ji wallahi
'Bangaren Azaad kuwa ya ce ta jira sa ne kawai ba tare da wani dalili ba haka kawai ya tsinci kansa da son ganinta kusa da shi
" Ki zauna mana ko tsayuwa zakiyi kamar wata soja " Yaya dan Allah ka bari na je na dawo" Ina kenan? " Ya faɗa tare da ƙara so wa wajen ta "Akwai abunda zan yi ne" Me za kiyi?" Shi ma ya tambaya" ta wani bubbuga ƙafa a ƙasa tana turo baki "Ina jinki" Uhmmmmm uhmm daman...........uhm daman....hmm." Wallahi duk ta dabulce ta rasa me zata ce, can dai sai tace " Zan je na duba na gani idan lokacin dawowar Noor yayi " ta faɗa ne kawai saboda tana san ya barta ta fita
"Ta da kanki ki duba ga clock nan " ta ɗago kanta ta kalli agogon " Lokacin yayi?" Ya faɗa yana kallanta ta girgiza masa kai, ganin kawai tayi ya ƙara shigowa jikinta kafin tayi wani yunk'uri ta ji ya ɗaga ta sama kamar wata baby ta fara zillo amman ina ya riƙe ta sosai, sai tsakiyar gado ya aje ta
Ummie mafisa kawai take ita kaɗai a falo ganin daga kao tea Alesha ta lak'e, da wani irin sauri ta juyo da taji alamun buɗe ƙofa ta juya ta ga ba ita ba ce, a she k'ofar falo ce ta motsa ta wani ja dogon tsaki kamar bakinta zai fita " Wannan wace irin masifa ce mata daga kai tea sai ki samu guri ki yi zaman ki baya son ki bakya son sa to ba zaku rabu ba kowa ya huta wannan bala'in har ina to wallahi ni dai kam na gaji yau za'a yi ta ta ƙare ki fita ki bar min miji na.....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 21
Ido cikin ido suke kallan juna ya ɗaga mata gira ta ji kunya ta rufe idanunta, la'b'bansa kawai taji saman nata ta yunk'ura zata tashi ya mayar da ita ya riƙe ta sosai, ya haɗe bakinsu tana kutta kutta amman ina sai da ya tsotse bakin tasss kamar bata shafa lipgloss ba
Yana sakinta tayi saurin basa baya ta kifa kanta a katifa tana jin mugun kunyarsa, Azaad kuwa ganin yadda tayi sai abun ma ya basa dariya ya sauka saman gadon yana mai jin wani irin farin ciki na shigarsa, bayan ya sauka tsaye yayi yana kallanta, juyawa yayi da sauri ya kalli k'ofa jin yadda aka buga k'ofar da ƙarfi can kuma aka ci gaba da bugawa da ƙarfi har Alesha sai da ta ɗago ta kalli k'ofar, ran Azaad ya 'baci gashi har yanzu ba'a daina buga k'ofar fa "Bara na duba ko waye" Alesha ta faɗa tana ƙoƙarin sauka saman gado Azaad yace "No! stay here bara na duba wane mahaukacin ne haka " ya faɗa tare da wucewa wajen door Alesha tabi bayansa da kallo
Ya buɗe k'ofar kenan tana ɗaga hannu zata sake bugawa, kamar wata zautacciya ta saki baki tana kallansa ko k'yaftawa bata yi sanda tayi tozali da faffad'an k'irjinsa sai da ta haɗiyi wasu yawu, ganin irin kallan da take yi masa yasa ya dubi jikinsa gaba ɗaya ya manta abunda ke jikinsa ya ja dogon tsaki tare da rufe k'ofar ya koma ciki ya wuce wajen wardrobe ɗin sa ya buɗe ya kai hannu ya jayo wata babbar riga ya saka ya juyo Alesha ta kallesa tare da faɗin "Waye?" Yarinyar nan ce " ya wuce ya buɗe ƙofa tana tsaye a wajen, Fuskarsa kamar wanda bai taɓa sanin dariya ba a rayuwarsa ba wallahi sai da Ummie ta tsorata da shi ya kalleta cikin kaurarriyar murya yace"Lafiya? Me ya faru? " Ganin yadda ya mata magana babu alamun wasa a tattare da shi yasa muryarta ta fara rawa alamun kuka tace " Yaya Azaad naga kun shige d'aki kun barni ni kaɗai a falo kuma ina jin tsoro shi ne na biyo ku " A yadda tayi magana bai ga alamun wasa a tare da ita ba hakan yasa ya ɗan sauko yace" Tsoro ki ke ji?" Eh wallahi idan ina zaune ni kaɗai tsoro na ke ji "Okay to yanzu zauna nan ki jiramu mu fito" Ko dai na shigo ciki " A ina?" Cikin d'akin " Aah ki jira nan" Tom " ta faɗa kamar wata ta Allah ya koma ciki
"Wayyooooooooooo Allahnaaaaaa" Ummie ta faɗa tare da fashewa da kuka ta ɗora hannu a kai tayi bedroom ɗin Alesha ta shiga tayi tsaye tace" D'azu fa da towel ya fito ɗaure a k'ugu to me suke yi a cikin d'akin ne ? " Zuciyarta ta fara sak'a mata wani abu tace"Ina wallahi ƙarya ne bama zai yiwu ba kaiiiiiii impossible " ta juyo ta fito tayi cikin falo kamar wacce sabuwar hauka ta kama ta cire ɗankwalin kanta tayi wurgi da shi ta ɗauki filon kujera tayi wurgi da shi ta ɗora hannayenta saman baki ta yi ihu ta koma ta zube saman kujera tana mayar da numfashi kamar wacce tayi wani aikin wahala hawaye masu zafi suka gangaro mata tasa hannu ta goge tace" Allah sarki Daddy da ace tun farko nayi ma ka biyayya da duk ban shiga cikin wannan matsalar ba amman gashi nan ga abunda na ja ma kai na nan da yanzu ni ce a gidan nan wallahi"ta faɗa tare da fashewa da kuka tace "Wallahi duk laifinki ne Mommy duk ke ce laifin ki ne wallahi"ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya
Tana kwance a wajen sai ga Alesha ta fito a guje Azaad na binta a baya Ummie ta tsura masa ido ya shirya cikin wani yadi baƙi an yi ma yadin aiki kamar shadda yadin ya masa kyau sosai ga hular nan da ya kafa mai ratsin baƙi da fari gemunsa ya sha gyara gashin ya miƙe jikinsa sai k'amshi yake yi, suka riƙa zagayen falon Azaad na son ya kama ta amman tana 'bod'asa Allah ya basa Sa'a ta juya zata gudu ya kamata "Wa na kama yanzu? Wa na kama? " Ya faɗa yana yi mata cakulkula dariya ta hana tayi magana, faɗawa jikinsa tayi dan ya daina yi mata cakulkula ta k'ank'amesa still tana dariya shima dariyar yake yi hannunsa zagaye da k'ugunta
Zuciyar Ummie kamar zata fasa k'irjinta ta fito fili, ta wani zabura ta miƙe tace "Wannan wane irin abu ne dan Allah zaku shigoma mutane kuna wannan abun" Azaad da Alesha duk suka juyo suka kalleta dan basu ma lura da mutum a wajen ba sai da suka jiyo muryarta, Alesha ta janye jikinta daga garesa tace" A she kina falo?" Ummie ta banka mata harara wani irin haushin Alesha take ji ba kaɗan ba tace "Aah bana nan kurwata ce a nan" Allah ya huci zuciyarki daga tambaya "Kema haka daga ba yar da amsa" ta faɗa tare da harararta, Alesha bata sake kula ta ba ta nemi waje ta zauna Azaad kuwa tuni ya wuce yayi d'aki dan ɗauko shayin da ta kai masa
K'wank'wasa k'ofar falo aka yi Alesha taje ta buɗe Noor ce ta dawo ta ɗauke ta suka yo falo ta zauna ta rungumata "So nake ma mu je saloon a miki kitso ni kuma a min gyaran gashi kina so ayi kitso ko?" Noor ta girgiza kai alamun aah" Sweet bakya san kitso? " Ta gyad'a kai tace" Mommy bacci zan yi " Bacci yanzu? To bara na cire miki uniform sai na goya ki" Noor ta mak'e ƙafad'a bata san a cire uniform, Alesha ta miƙe ta ɗorata a baya ta cire ɗankwalinta ta goyata da shi, Ummie ta kalle su ta taɓe baki a zuci tace "Wahalalliya kawai" Azaad koda ya fito ya tarar da Alesha goye da Noor har tayi bacci wallahi yana mugun jin daɗin ganin yadda Alesha ke son Noor da yadda take bata kula da tarbiya kamar ita ta haifeta duk da baya nuna mata amman yana jin daɗi
Ƙarasowa yayi falon yace " Yan makaranta har an dawo ke bakya jin nauyinta ne ki ke goyonta" Yaya bata da fa nauyi kuma ai bata wuce goyo ba " Gareki ba"Hhhhhhh "Ni zan fita zan tsaya masallaci idan akayi sallah na wuce gida"Okay Ubangiji Allah ya tsare Ya kai lafiya "Amin ya rabbi" ya juya ta tashi tayi masa rakiya ta juyo kenan taga Ummie a bayanta bata ce da ita komai ba ta yi wuce warta ita kuma Ummie ta buɗe ƙofa ta fita Azaad har ya kusa isa wajen motarsa yaji yo Ummie na k'allah masa kira ya tsaya ta ƙara so da ɗan gudunta
Ta sakar masa murmushi "Me ne ne?" Ya faɗa tace "Yaya Azaad kan maganar da zamu yi ne"Okay kinga yanzu ina sauri lokacin magrib na ƙaratowa "Yaya Azaad dan Allah ka bani five minutes kaɗai sun isa sun ma yi yawa"Okay ina jinki kiyi sauri"Yaya Azaad ina son ka " Da wani mahaukacin sauri ya ɗago ya kalle ta cike da mamaki da al'ajabi irin nata
"Yaya Azaad wallahi ina bala'in son ka ina son ka idan baka amince min ba wallahi zan iya rasa rayuwa ta ka taimaka min"Ta faɗa tare da rushewa da wani irin kuka ta zube ƙasa ga gwuiwoyin ta....................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 22
Ta ɗago ta kallesa shi ma ita ɗin yake kallo ta share hawayenta tace" Yaya Azaad ka temakeni zan iya rasa rayuwata wallahi inaa maka son da ba ko wace yar' mace ke maka ba dan Allah ka saki aunty Alesha ka aure ni wallahi zan share maka hawayenka zan so ka na kula da kai nayi ma ka biyayya fiye da yadda baka tunani nasan bakwa son juna kai da Alesha haɗa ku ne kawai a ka yi zaman biyayya ne ku ke yi kuma na tabbata babu wani abu da ya taɓa shiga a tsakanin ku na zamantakewar ma'aurata saboda a d'aki ɗaya muke bacci da ita kullum wanda na tabbata da akwai abunda ke shiga tsakanin ku da sai dai ta riƙa kwanciya a d'akin ka, kaga hankali kwance cikin ruwan sanyi kawai sai ka sake ta tun da ba abunda ke shiga tsakanin ku bare a ce ko ta samu ciki idan ka saketa nan da sati ɗaya sai ayi auren mu na tabbata kowa zai yi farin ciki saboda muna son junan mu " Har ta kai ƙarshe Azaad banda kallanta ba abunda yake yana sauraran haukar da take faɗi
Da hannu ya nuna ta fuskarsa babu alamun wasa yace" Ya ma sunan ki? Miƙe" ta miƙe tana murmushi yace "Na miki kama da kalar yan iskan mazan nan da zaki tsayar da su kina faɗar abunda ranki ke so? Eh" ya faɗa da mugun tsawa har maigadi da ke bakin gate sai da ya juyo ya kallesu
"Wallahi wannan ne farko kuma na ƙarshe da zaki sake tsayar da ni kina faɗa min irin wannan banzar magana shashashar yarinya kawai ubanwa zai aure ki da na aure ki gwanda na mutu banyi aure ba ke harma kin isa ki zo gabana ki tun kareni da irin wannan maganar wallahi al'barkacinta kika ci kuma ko yanzu albarkacin ta zaki ci na k'yale ki tsabagen iskanci harda faɗin zaki iya mutuwa to ki mutu mana ina ruwana waya damu duk wanda ki ka ga ya mutu lokacin sa ne yayi banza mai mugun hali maci amana mtssssssssssssssssssssssssssssssssssss" ya faɗa tare da juyawa ya barta nan tsaye, ya shiga mota ya yi baya da gudu ta matsa ya figi motor ya fice
Ummie na tsaye jikinta duk yayi sanyi bata taɓa expecting zai iya yi mata cin fuska irin haka ba sai ga shi
Ta jima wajen a tsaye dan har sai da aka tayar da sallah ta juya ta yi cikin gida, kallo ɗaya Alesha tayi mata ta ɗauke kai, bedroom ta wuce ta ɗauki wayarta ta kira ƙawarta Rufi kiran na fara shiga ta ɗaga " Amaryar Azaad ya ne ya ake ci meke going ?" Rufi ba lafiya wallahi zuciyata ta kusa bugawa" Subhanallah Me ya faru ne?" Miye ma bai faru ba Rufi wallahi komai ya faru" To kimin bayani yadda zan fahimta " Uhmmmm Rufi..........................." Ta shiga zayyano mata duk abunda ya faru har ƙarshe
"Ummie a she akwai babban aiki a gaban mu na yi zaton cikin ruwan sanyi zaki karɓe sa a hannun ki ashe abun ba haka ba ne but don't worry akwai mafita " Wace irin mafita ce Rufi?" Akwai wani malami da na taɓa ji kuma nasan wajen da yake an ce aikinsa kamar yanzan wuk'a ne yana yi aiki zai kankama " To Rufi yaushe zamu je?" Duk lokacin da kika shirya "Mu je gobe mana"To Shikenan " Yawwa sai ki biyo ta nan ki ɗauke ni saboda ba da mota nazo ba" Okay bai da matsala amman bazan shigo ba waje zan tsaya da kinga kira na sai ki fito " Hakan ma yayi" Cike da farin ciki ta aje wayar har ta k'osa taga safiya tayi
Azaad yana fita bai ko tsaya yin Sallah a masallacin ba ya wuce gidan su masallacin gidan su yayi Sallah sannan ya shiga cikin gida har ƙarfe tara yana gidan sannan ya musu sallama ya wuce bai koma gida ba sai goma da rabi
Alesha ta kawo masa abinci yaci ya k'oshi ya wuce d'aki yayi wanka ya sanya gajeren wando da vest,
Noor har tayi bacci Ummie kuma baccin nason ɗauke ta Alesha kuma ta kwanta kenan wayarta ta fara ringing ta kai hannu ta janyo wayar number Azaad ta gani ta ɗaga kiran tare da kafa wayar a kunne, ban ji abunda ya faɗa mata ba kawai naji tace "Tom" ta aje wayar ta sauka ta ɗauko hijab ɗinta ta saka ta buɗe ƙofa ta fita
Ummie dake kallanta ta taɓe baki tace " An dai kusa tattarawa a barmin gida na sha iska a je can a ƙara ta na matsu gobe tayi Azaad ka kusa shigowa hannu sai yadda nayi" ta faɗa tare da yin wata shu'umar dariya
Alesha tana fita ta wuce d'akin Azaad zaune ta tarar da shi da system a gabansa da alama aiki yake yi ga wasu takardu a gaban sa tayi sallama ya amsa ba tare da ya ɗago ya kalleta ba, ta ƙara so tace "Sannu da aiki"Yawwa "Me za'a kawo ma?" Babu ba abunda nake buƙata " Okay" Ta kusa minti uku tsaye kuma shi bai ce ta zauna ba ga shi tana jin bacci tace "Yaya zan je na kwanta"Okay " ta juya ta kama hanya zata fita ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta yace"Ina zaki je?" D'aki" Okay nan ba d'aki ba ne kenan "Ba nufi na ba kenan" Koma mene ne daga yau a d'akin nan zaki riƙa kwana.................
🌸🌸 AZAAD 🌸🌸
Mallakar
Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑)
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
*https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL*
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._
*Alƙalaminmu ƴancinmu💪*
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
*Bismillahi Rahmanin Rahim*
page 23
Baki ta saki tana kallansa jin yazo mata da wani sabon salo tayi tsayinta a wajen taƙi ko motsawa ya ɗago ya kalleta yace "Shawara ki ke yi?" Baki ta turo gaba tare da faɗin "Yaya Noor fa?" Meya faru da ita?" Tana d'aki" Ita kaɗai ce a d'akin? Ko cinyeta za'a yi da ba zaki iya bacci ba sai tare da ita " Yaya amma.........................."kallan da yayi mata yasa ta kasa ƙarasa abunda take san faɗa, bai sake ce da ita komai ba yaci gaba da aikin sa ita ma bata sake cewa komai ba tana tsaye har ya gama ya tattara ya kai ya aje ya shiga toilet ya fito ya kalleta bai ce komai ba ya zagaya ya haye gado ya kwanta
Har ya kwanta ya ɗago ya kalleta yace "Umurni na baki ba shawara ba ki zo ki kwanta idan kuma bazaki bi umurni na ba fine ki buɗe kawai ki fita ban riƙe ki ba hanya buɗe take" ya faɗa tare da komawa ya kwanta
Jin abunda yace yasa jikinta yayi sanyi, a hankali ta fara takawa ta nufi gadon ta isa ta kalli gadon ta wuce ɗaya gefe kamar mai tsoro tsoro ko wacce za'a kama haka ta zauna saman gadon ta kusa minti biyar zaune ganin kamar yayi bacci ta cire hijab ɗinta ta nad'e ta aje a gefe ta kwanta can ƙarshen gado wallahi in dai tayi k'wak'k'waran motsi ne to zata iya faɗowa ƙasa amman haka ta kwanta, ganin tayi kawai ya kai hannu ya rage hasken d'akin a zuci tace " A she bai yi bacci ba" can Noor ta faɗo mata a rai tasan muddin ta farka bata ganta ba kuka zata yi da tunanin Noor bacci yayi awon gaba da ita
'Bangaren Ummie kuwa tana farke tana jiran taji shigowar Alesha amman shuru tun tana duba agogo har ta daina dubawa bacci 'barawo yayi awon gaba da ita
Washe gari Azaad na wucewa masallaci ta baro d'akin tayi nata
Tana shiga suka haɗa ido da Ummie wacce tashin ta kenan, wani kallo ta riƙa yi mata irin kallan nan na tuhuma, Alesha ta ɗan ji nauyin Ummie na ganin ta barsu ta tafi d'akin sa, wucewa kawai tayi bayi Ummie ta raka ta da harara " Bak'ar munafuka wai ita ta fito wajen miji hmmmmmmmmm wato saboda nace ba'a d'akin sa take kwana ba shi ne ya kirata taje ta kwana a can uhmm ayi dai mu gani sauran kwana nawa kwana nawa ya rage muku Hhhhhhh" ta faɗa tare da fashewa da shu'umar dariya
Har Alesha ta fito tana dariyar ta shimfid'a sallaya ta yi sallah ta sallame ta kalli Ummie dake kwancen ta kuma idon ta biyu tace "Ummie bakya sallah ne? Kina ji fa har an kusa gama sallah a masallatayya" Ina yi ban tashi yi ba sai na huta " ko uffan Alesha bata sake cewa ba ta miƙe ta nad'e sallaya ta aje ta fito ta shiga kitchen
Azaad ko da ya dawo masallaci bai ganta ba daman yasan da wuya ya tarar da ita sai gashi kuwa ya haye gado
Shaɗaya da yan mintuna Rufi ta iso ta kira Ummie ta fito suka wuce, Alesha na zaune a falo taji ana k'wank'wasa k'ofa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 13