Share this page
gabanta ya faɗi dan tayi zaton laifi tayi Haka ta daure ta fara kiransa kusan kira uku sannan ya ɗaga tayi sallama tace "Yaya ina wuni?" Aikin me ki ke yi yanzu?" Ya faɗa"Ba komai " Okay ki shirya ki zo nan yanzu"To "ta faɗa a sanyaye "Ba fa to ba ki shirya ki zo kiyi sauri bata jin daɗi "yana gama faɗin haka ya kashe wayar Tashi tayi ta je ta sanar ma Ammie ta dawo ta shirya ta gama shiryawa kenan sai ga Noor ta shigo tana kuka Rukayya ta tambeta waya taɓeta tace"Gun mommyna zan je" Noor manya yanzu gudun mu ma ake yi saboda kin ga Mommynki ko? zo na shirya ki muje " ta shiryata suka wuce Azaad ko da ya koma d'akinta ya tarar da ta tashi ta goge jinin da ya zuba ƙasa ta cire zanen gado ta ɗauko wani sabo tana tsaye tana tunanin yadda zata shimfid'a zanen gadon da mamaki yake kallanta yace "Wa ya saki duk wannan aikin? Baki ga ciwon da yake jikin ki ba ne?" Alesha bata ce da shi komai ba sai ma zama da tayi saman drawer gadon sakamakon kanta da ya sara mata ganin yadda ta riƙe kai yasa ya isa wajen da take ya dafa ta yace "Ciwo yake miki ne?" Tana jin sa tayi banza da shi ya ƙara maimaitawa zai sake magana wayarsa tayi ƙara ya ciro ya duba yaga Rukayya ce ya ɗaga wayar ya kai kunnensa ba tare da yayi magana ba ya janye wayar ya juyo ya fito ya nufi k'ofa ya buɗe, Noor da ta matsu ta ga Mommynta tana ganin an buɗe ta shigo a guje tana faɗin "Mommy! Mommy! Mommy na dawo where are u " Noor ganin bata ganta ba yasa ta juya ta kalli Papah tace" Papah ina mommyna " D'akinta" ta juya tana murna tayi d'akin A guje ta isa wajenta tana murna suka rungume juna suna farin cikin ganin juna, ta ɗauketa ta aza saman cinyoyinta tace "Wa ya kawo ki?" Aunty " Tare da aunty ki ke?" Ta gyad'a mata kai, "Mommy miye wannan?" Noor ta faɗa tare da nuna kad'ar da ke hannun Alesha"Na ji ciwo ne a hannu " Aww sorry Mommy"ta faɗa tare da yin wani abu da baki, Rukayya ta shigo ta gaidata tare da yi mata ya jiki, kasancewar Azaad ya faɗa mata abunda zata yi yasa ta wuce kitchen ta ɗora girki ganin marece yayi yasa ta dafa taliya ta gama ta je d'akin sa d'akin a gyare yake glass ɗin da ya fashe kawai ta tattara ta kwashe ta goge jinin da ya zuba ta dawo d'akin Alesha ta zauna suka fara fira sama sama har aka yi kiran magrib Rukayya ta fara zuwa tayi alwala sannan Alesha ta tashi Noor ta bi ta suka yi alwala suka fito a zaune tayi sallah, Bayan ta sallame ta ɗauko Alkur'ani mai girma tana biya ma Noor tana amsawa Rukayya ta sa su gaba kamar mai kallan tv sunanan suna karatu har aka ta da isha'i sannan suka yi sallah suka fito falo gaba ɗaya Suna zama Azaad na shigowa ɗauke da ledodi bai tsaya ko ina ba sai gaban Alesha ya aje ledodin Noor da Rukayya suka yi masa sannu da zuwa, Alesha idanunta na kan tv tayi kamar bata san da tsayuwar mutum a wajen ba, ya kalli Rukayya yace "Kin kammala girkin?" Eh " Okay je ki kawo muna"To " Ta faɗa tare da miƙewa Noor ta taso ta faɗa jikin Alesha kanta ya bugi hannunta mai ciwo tace "Washhhhhhhhhhh"Ta faɗa tare da runtse ido "Sorry mommy yana miki zafi?" Eh "Sorryyy" ta faɗa kamar zata yi kuka tace "Papah ka ba Mommy magani hannunta na zafi"Ga maganin nan na siyo mata " To Mommy zaki sha?" Alesha ta gyad'a mata kai Noor ta sake cewa "Ba zaki yi kuka ba ko?" Wallahi sai da ta sa Alesha dariya hatta Azaad sai da ya murmusa, tace"Princess bazan yi ba " Okay mommy " Rukayya ta kawo abincin nan tsakar falo ta zubama Azaad nasa ta aje gabansa ta kalli Alesha tace"Aunty na haɗe muna waje ɗaya?" Eh" ta saka musu waje ɗaya su duka, Azaad yace ta duba cikin ledodin nan akwai nama ta miƙa ma kowa ta duba ta miƙa ma kowa gasasshen nama ne kowa da nasa ɗauri ta zauna suka fara cin abinci, Alesha bata ci naman ba Noor da Rukayya ɗauri ɗaya suka buɗe suna ci Azaad kam ya tashi da filet ɗin taliyar duniya taliya tana cikin favorite food nasa yana mutuwar son ta shi ma bai wani ci naman sosai ba ya tashi ya miƙa mata magani ya ce ma rukayya" ga fruit nan ta yanka saura kuma tasa a fridge" ya wuce d'akinsa Bayan sun gama cin abinci ta sha magani Rukayya kuwa ta wuce kitchen da kayan ta ɗibi waɗan da zata yanka saura kuma tasa a fridge............... 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 18 Kwanan Rukayya huɗu a gidan, Alesha ta sake mata fuska sosai su zauna suyi fira su yi wasa da dariya idan ka tarar suna fira kamar yaya da ƙanwa, Ƙafarta kuwa sauran kaɗan wajen ya haɗe yanzu tana iya takawa ko ina hannu tuni ya warke daman ba sosai ta ji ciwo a hannun ba, tsakanin ta da Azaad kuwa wata maganar kirki ma ba haɗa su take yi ba amman idan Rukayya ko Noor na wajen yayi mata magana lafiya lau take amsawa idan kuma daga ita sai shi ne yayi mata magana ciki ciki take basa amsa abun har mamaki yake basa Yau ta kama Saturday tun da tayi sallahr asuba bacci ya ƙaurace ma idanunta ta kalli Rukayya da Noor sai baccin su suke yi miƙewa tayi ta fito dan shirya musu breakfast, har zata shiga kitchen ta hango Azaad kwance saman kujera wuyansa ya ɗan juye ta nufi wajensa tayi tsaye ta turo baki tare da faɗin "Mutum da girmansa yana irin wannan kwanciyar" ta faɗa tare da sa hannunta biyu ta tallafo kansa ta gyara ta juya zata wuce ba zato ba tsammani kawai taji ya janyota ta faɗa jikinsa ta wani zaro ido, daman ba bacci yake yi ba ya rufe idanunsa ne kawai ya wani rirrik'eta yana kallan ta, hannuwanta na saman k'irjinsa, ta ɗago ta kallesa tayi ƙasa da idanunta "Ina girman yake?" Ta ji ya faɗa, a zuci tace "Ohhh daman ba bacci yake yi ba" kiciniyar k'watar kanta take amman ta kasa shi kuwa ya zuba mata ido yaga yadda zata karb'i kanta "Zaki wahal da kan ki ne kawai"Kitchen zan shiga "Ba ƙarfi gareki ba?" Ya faɗa Alesha ta gyad'a masa kai alamun eh yace "Good k'waci kan ki to" ta ci gaba da kiciniyar k'watar kanta ganin ta kasa kuma wallahi duk da gaji ta kwantar da kanta a k'irjinsa tace "Yaya please ka caka ni ka ji" Har kin saduda ke fa mai ƙarfi ce bai dace ki saduda tun yanzu ba " Ya faɗa tare da sakinta ta miƙe kamar wacce tayi dambe sai haki ta ke, tayi tsaye tana gyara rigarta tace"Ai saboda ka ga ban shirya ba ne shiyasa amman ni mai ƙarfi ce " Hannu ya kai zai janyota tayi saurin ja da baya tayi masa gwallo"Ni ko?" Ya faɗa, Ta ɗaga masa gira tana murmushi dimple ɗinta sai lutsawa suke yi, tayi hanyar kitchen "Zan kama ki ne" ya faɗa yana dariya yana jin wani farin ciki a ƙasan zuciyarsa Kitchen ɗin ta shiga tayi tsaye tana tunanin abunda zata shirya mu su kawai ta yanke shawarar yin YAMARITA ta fitar da duk abubuwan da zata yi amfani da su, cikin k'ank'anin lokaci ta kammala ta dafa Black tea, Ga yadda ake haɗa YAMARITA Ingredients yam -4 eggs -1 cup flour -2 tbsp corn flour -1 seasoning cube -1 tsp dry celery -½ tsp tumeric -1 tsp curry -salt -oil for drying METHOD Peel and cut yams into rectangular shapes *wash and add them into a pot,sprinkles some salt and add water *place the pot on a stove and cook the yam under medium heat till soft *drain in a colander and allow it to cool *in a plate, combine flour, corn flour, dry celery and turmeric, mix well *crack in the eggs in a bowl,add seasoning cube and curry ,whisk well *dip each yam in the beaten eggs then coat with flour mixture Black Tea -ginger -Lipton -cloves -cinnamon -sugar *method*; *place ginger,cloves,cinnamon in a pot of water and bring to boil *strain,add sugar and Lipton. Azaad ya shigo kitchen ɗin yayi tsaye bakin k'ofa ya lumshe ido yana shaƙar daddad'an k'amshin da ya kewaye ilahirin gidan ya buɗe idon sa yace"Me ake dafa muna ne haka k'amshi duk ya dame ni a falo"ya faɗa yana murmushi Alesha ta juyo ta kallesa ita ma fuskarta ɗauke da murmushi tace "Delicious breakfast ne "Uhmmm let me take shower 🚿 sai na zo naga wannan Delicious food ɗin da ya cika hancina da k'amshi "Okay a fito lafiya" Ya wuce yayi d'akin sa, ta haɗa komai ta kawo dining table kayan da ta ɓata ta wanke ta dawo falo gyara falon kawai tayi ta goge kaya saboda bai yi datti ba ta saka turare ta wuce bedroom ɗin ta Ta kalli agogo taga ƙarfe tara har da minti uku duk basu tashi ba suna nan suna bacci, ta gyara d'akin ta share ta goge ya rage sauran gado ta wuce toilet ta wanke daga nan tayi wanka ta fito ta ɗauki Noor dake bacci tayi toilet da ita suna shiga ta aje ta tsaye ta ɗibi ruwa ta shafa mata a fuska, Noor ta ɓata fuska tace "Mommy bacci zan yi"Okay bara a yi wanka sai ki ci gaba da baccin "Uhmmm"Ta cire mata kaya tayi mata brush sannan ta sata cikin ruwa Noor tace "Mommy"Na'am"cikin bacci naga kin haifo two baby's masu kyau " ta faɗa tana murmushi Alesha ta zaro ido tace"Mafarki ba gaske ba ne kinji" Eh"tayi mata wanka suka fito ta tada Rukayya su kuma suka shirya, koda Rukayya ta fito har sun shirya sun yi kyau abun su ita ma ta shirya a gurguje suka fito Suna isowa falo Alesha ta hango Azaad zaune saman dining ya zuba ma kansa abinci yana ci ta saki baki tana kallansa da mamaki Noor ta ruga a guje wajensa tace "Good morning Papah"Morning how was your night?🌃 "Fine Papah "Good " ya faɗa but ko kallanta bai yi ba breakfast ɗin sa kawai yake yi ba ƙaramin daɗi YAMARITAN nan yayi masa ba Rukayya ta gaidasa Alesha ta kallesa tace "Ina kwana" Ya ɗago ya kalle ta, kayan da ta sa sun mata kyau sosai kamar ba zai yi magana ba can dai sai ya ce "Ban gan sa ba ke kin gansa ne?" Ya faɗa tare da tsureta da ido Rukayya ta kumshe dariyarta Alesha ta turo baki tace "Uhm antashi lafiya?" Alhamdulillah" ya buɗe baki zai yi magana ko me ya tuna oho naga yayi shuru ya ɗauki tea ya kai baki Alesha ta zuba musu abincin su ta ja kujera zata zauna suka ji ana k'wank'wasa k'ofar falo abun duk ya basu mamaki saboda basa expecting zuwan kowa by this time " Bara na duba waye" Ta faɗa tare da wucewa tayi bakin k'ofar tana zuwa ta ce "Waye?" Muryar da taji ne abun ya bata mamaki ta kai hannu ta buɗe k'ofar bata gazgataba sai da ta ganta, People Ummie ce janye da k'atuwar akwatin ta..................... 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 19 Murmushi Ummie ta sakar mata,ita ma ta mayar mata ta bata hanya ta shigo, Alesha ta shigo da akwatin Ummie na gaba Alesha na biye da ita a baya janye da akwati, Alesha tace "Mamma ce ta aiko ki?" Aah sai ta aiko ni zan zo gidan nan ne "Na ganki da akwati ne"Yes kaya na ne nazo nayi hutu a nan ne "Alesha bata sake cewa komai ba har suka ƙara so cikin falo"Ku ce ina da sa'a kenan yanzu ku ke breakfast gani komai banci ba na fito " ta faɗa Azaad har ya kai cup bakin sa zai sha tea yaji muryarta ta doki kunnensa ya juya ya kalli inda yaji sautin muryar, idan mutum na dining duk abunda yake cikin falo zai iya ganin sa Kallanta yayi tun daga sama har ƙasa sannan ya kalli Alesha ya ganta riƙe da akwati ɗauke kansa kawai yayi yaci gaba da abun da yake yi Rukayya ta juyo ta kalleta, Ummie kuwa kallan Azaad take kamar zata haɗiye sa kwana biyu da bata gansa ba sai ta ga ya ƙara yi mata wani kyau, takawa ta fara yi tana rangwad'a ta nufi dining table ɗin, Alesha ta ja akwatin ta nufi d'aki da ita Ummie Zagayawa tayi ta nufi Kujerar da ke gefen hannun hagunsa ta ja tare da zama, Rukayya tace " Baiwar Allah ba ko sallama zaki zo ki zauna" Ohhh very sorry i forget wallahi sorry fa ya kike but ban sanki ba?" Uhmm nima ban sanki ba"Rukayya ta faɗa tare da yi mata wani kallo, Ummie tayi murmushi tace " A gidan nan nake kuwa?" Gidan nan bangane ba?" I mean Ni ƙanwar matar gidan ce "Oh really "Rukayya ta faɗa saboda ko kaɗan bata ga wata kamar su da Alesha ba Ummie tace "Yeah nd u?" Ni kuma ƙanwarsa ce " Ta faɗa tare da nuna Azaad wanda ko jin su baya yi yasa headphone 🎧 a kunne "Ki ce ƙanwar boss ce "Ai kuwa "Rukayya ta faɗa tare da ci gaba da yin break ɗin ta Ummie ta janyo plate ɗin Alesha da ko ci bata fara ba ita kam ta fara cin abinta Rukayya ta kalleta haka kawai taji Ummie bata yi mata lokaci ɗaya "Aunty ina mommyna"Noor ta faɗa "I'm here baby what happen "Alesha ta faɗa tare da ƙarasowa tana kallan Noor wacce ta haɗe fuska"Come here baby "Noor ta tashi ta je wajenta Alesha ta ja kujera ta zauna ta ɗauketa ta ɗora saman ƙafafunta tace"What happen?" Mai makon tayi magana sai kawai ta lafe a jikinta Alesha tace"Kin k'oshi?" Ta girgiza kai"Okay na baki " Ta gyad'a mata kai, "Rukayya Please bani plate ɗin nan " Rukayya tace" Wallahi Aunty ke ce ke sangarta yarinyar nan sai ta riƙa yi ma mutane taɓara kala kala shiyasa ma yanzu bata zaunuwa ko ina saboda tasan ba wanda zai ɗaukar mata wannan taɓarar sai ke yarinya na cin abincinta ta tashi tace sai dai ki bata "Rukayya sa ido kika koma? " Alesha ta faɗa tana kallan Rukayya "Ki ce sa ido kike muna miya shigo da ke tsakanin yar' da uwa eh fisabilillah yarinya jaririya idan ban mata abunda take so ba wa zan ma? " Wannan ce jaririyar? Allah sai ma ki sa na kai mata duka"Duka fa ? Rukayya so dai ki ke mu ɓata wannan jaririyar zaki daka aah gaskiya bazan ɗauka ba duk wanda ya taɓa min yarinya zamu 'bata ko Sweet?" Ta faɗa tare da kallan Noor, Noor ta gyad'a mata kai Alesha ta ƙara gyara mata zamanta "Mu dai muna ganin abubuwa akan yarinyar nan"Rukayya ta faɗa tana dariya Alesha tace "Yanzu ma zaku fara gani" ta faɗa ita ma tana dariya kana tace "Ni dai miƙo min"To ya na iya ai dole "Ta miƙo mata plate ɗin Azaad sai kallan Alesha yake yi ita ko hankalin ta na kan Noor da take ciyar da ita, Ummie kuwa idanunta na kansa ganin hankalinsa ya karkata ga Alesha ta ji wani baƙin ciki, daga ƙarshe ma miƙewa yayi ya koma falo Sai da Noor ta k'oshi sannan ta ci Ummie ta riga su gamawa ta miƙe ita ma ta koma falon bayan sun gama Rukayya ta gyara wajen suka dawo falo Azaad ya so zama falon amman ganin Ummie ta saka sa gaba yaji kawai ya tsalgu ya tashi, yayi hanyar fita Alesha ta miƙe da sauri ta bi bayansa har ya buɗe ƙofa ta kirasa ya tsaya tare da juyowa ta ƙaraso ta fara wasa da yatsunta tace "Uhmm yaya daman" Sai kuma tayi shuru, ya gyara tsayuwarsa tare da riƙe k'ofar yace "Continue " Daman...um...mie ta zo ne tayi hutu a nan " Ta faɗa kanta a ƙasa"Da kyau " ya faɗa tare da ɗaga ƙafad'a"Ni zan fita "Allah ya kai lafiya ya tsare"Amin akwai abunda kuke so ne?" Alesha taji bala'in mugun jin daɗin wannan tambayar da ya yi mata duk da babu abunda suke buƙata tace " Aah babu" ta faɗa tare da girgiza masa kai "Okay "ya juya ya wuce Tayi tsaye tana kallansa yadda yake tako cikin izzah, tafiya a hankali kai wallahi tafiyarsa kawai abun kallo ce, sai da yayi mata nisa sannan ta juyo ta dawo falo tana murmushi, karaf suka haɗa ido da Ummie wacce duk abunda suke yi ga idanunta abunda suke faɗi ne kawai bata ji, ta wani haɗe fuska kamar anyima zawo yayyafi🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Washe gari Rukayya ta wuce duk da ba ranar ta so tafiya ba taso sai Friday da an fito masallaci sai ta wuce amman ganin tasu bata haɗu da Ummie ba yasa ta wuce saboda idan tace zata zauna to wata rana za'a tarar da suna dambe domin kuwa Rukayya bata ɗaukar raini bata san shisshigi Ummie kuwa abunda tasa gaba kenan, Ummie taji daɗin tafiyar Rukayya sosai dan tana ganin ta tare mata yin abunda take so ko da taso yin wani abu sai Rukayya ta abunda zai sa ta fasa Yau Tuesday an kai Noor school Azaad kuma bai fita ba yana zaune a falo yana kallo Alesha na kitchen tana haɗa lunch Ummie ta fito tana tafe tana rangwad'a tana murmushi direct wajen Azaad ta nufa, jin an masa tsaye a kai yasa ya ɗago ya kalle ta ya tashi daga kwancen da yake yace "Me haka?" Yaya Azaad magana nake so muyi da kai mai matuƙar muhimmanci amman naga duk lokacin da na raɓeka sai naga kana wani kakkauce min "Faɗi ina jin ki" Yaya Azaad dan Allah baka fahimci komai a tare da ni ba "Ban fahimta ba faɗi maganar ki ina san na wuce wajen aiki yanzu"Gaskiya maganar ba zata yiwu a nan ba muje d'akin ka ko mu fita waje " Azaad da mamaki yake kallanta, ya miƙe kawai zai wuce ta yi saurin shan gabansa dai dai nan Alesha na fitowa daga kitchen hannunta riƙe da kula kallan su kawai tayi ta wuce dining, jin motsinta yasa Azaad ya juyo da sauri ya kalli inda take ganin ba su take kallo ba ya sauke ajiyar zuciya ya juya yabi ta ɗaya hanyar yayi d'akin sa Hawaye suka zuboma Ummie tasa hannu ta goge ta nemi waje ta zauna ita kaɗai tasan yadda take son wannan bawan Allah, a yadda take jin son sa zata iya aikata komai indai har zata samesa tashi tayi ta koma d'aki Azaad abunda zai ɗauka ya ɗauko ya fito ya lek'a kitchen wajen Alesha k'amshin miyarta duk ya baibaye falon wato Allah ya bata ta iya girki sosai wallahi "Madam sannu da aiki"Ta juyo ta kallesa tace "Yawwa sannu"Idan kin kammala kin huta ki ɗan shiga ki gyara min d'aki "Tun lokacin da abun nan ya faru bata ƙara shiga d'akin sa ba, Alesha tayi shuru tana kallansa, abunda ya faru ranar ya faɗo mata "Zan sa Ummie t..........." Hannun da ya ɗaga mata hakan yasa tayi shuru yace " A kan wane dalili zata shigar min d'aki? Ke da nake da aiko a kan ki na saka ki baki yi ba Shikenan amman kar ki kuskura ki tura min wata d'akina" ya faɗa tare da juyawa ya fice Ta bi hanyar da kallo ta juya taci gaba da aikinta Bayan ta gama tana tsaye tana shawarar taje ta gyara masa ko ta kyalesa kawai daga ƙarshe dai ta yanke shawarar shiga ta gyara ko ina ta share ta goge haka ma toilet ta haɗa ƙananun kayansa ta wanke ta sakar ma d'akin k'amshi ta kunna AC ta fito Tana fitowa Noor na dawowa daga school tayi mata wanka ta bata abinci ta kwantar da ita tayi bacci saboda uku 3 na yi zata wuce islamiyya sai da tayi bacci sannan ita kuma ta tashi ta faɗa toilet tayi wanka tare da ɗauro alwala................ 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Alƙalaminmu ƴancinmu💪* *Amincin Allah ya ƙara tabbata a gare ku yan uwa masu k'amshin tuffa tare da fatan an yi sallah lafiya ina rokon Ubangiji Allah mai girma da ɗaukaka da ya sake nuna muna wata shekarar cikin k'oshin lafiya, Barkar mu da sallah sai na zo karɓar barka da sallah na 😀😀😀* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 20 Ta zauna gaban mirror ta shafa mai ta buɗe humra ta mulke jikinta da ita ta shafa powder ta gyara girarta ta ɗauki lip liner pencil brown ta ja ta kawo lipgloss ta shafa ta miƙe ta ɗauki tufafin da ta fitar ta saka ta kawo daurin nan na zarah buhari ta yi ta koma wajen mirror ta ja kujerar mirron ta zauna ta buɗe drawer ta ɗauko wata ƙaramar akwatin ƙarfe inda sark'ok'inta suke ta ciro wata had'ad'd'iyar sark'a ta saka tare da yan kunne da abun hannu ta mayar ta kalli kanta ta cikin madubi, ita kanta sai da tayi murmushi ganin irin kyawon da tayi, atamfar tayi mata kyau ga ɗinkin da aka yi mata wanda ya ƙara fito da ita ta miƙe ta ɗauki turare ta ƙara feshe jikinta ta ɗauki wayarta ta koma gefen gado ta zauna ta lalubo number Mamma ta fara kira Wayar bata jima da fara ringing ba Mamma ta ɗaga suka gaisa, Tana cikin wayar Ummie ta shigo da fara'arta idanunta suka sauka kan Alesha sai da cikinta ya murd'a ganin irin kyawon da Alesha tayi ta yi cass abunta kamar wacce zata je wani Babban taro na manyan mutane nan take ta haɗe fuska wallahi Alesha tafi Ummie da komai nesa ba kusa ba domin duk wanda yake da mata irin Alesha aka ce zai tsaya kula irin Ummie to ko kai kanka abun zai baka mamaki amman saboda So da ya rufe mata ido yasa ita bata ganin haka sai take ganin ta fita Kasa zama d'akin ma tayi saboda har wani abu take jin yana taso mata ta fito ta dawo falo Sun jima suna waya da Mamma sannan suka yi sallama tana kashewa kiran Yaya Imran na shigowa ( Ɗan Mamma wanda ya siya mata waya) Murmushi ɗauke a kan fuskarta ta ɗauki wayar suka gaisa shi ma sun ɗan taɓa fira sannan suka yi sallama ta tada Noor ganin lokaci ya ƙarato ta kaita bayi ta wanke mata baki, ta sa tayi alwala suka fito ta saka mata uniform ɗin islamiyya tasa hijab suka

Chapter 6 of 13