Share this page
ga riga ga rigar nan Basmah na bala'in san ta " Kina nufin da gangan kenan tayi"Daddy ya faɗa " Eh mana wallahi da sanenta tayi wannan aikin Saboda ta 'bata mata rai to kin k'one Hankalinki ya kwanta ko" ta faɗa tare da kallan Alesha dake rabon ido muryarta na rawa tace "Wallahi Mommy bansan yayi zafi ba dan Allah kiyi hak'uri" Taya ko zaki sani bak'ar munafuka algunguma kema sai naki sun k'one " Mommy ta faɗa tare da ɗaukar dutsen guga ta manna mata shi wajen cinya wani irin ihu Alesha ta saki................. 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943* *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 4 Tuni hawaye suka wanke mata fuska, dutsen sai da ya taso ta kayanta gashi rigar dake jikinta kamar roba take shiyasa dutsen yayi saurin kama kayan banda kuka da yarfe hannuwa ba abunda take, Basmah tayi murmushin jin daɗi Uwani kam sai da ta zubar mata da k'allah, Daddy na tsaye bai ce komai ba "Gobe ma ki sake wallahi wanda yafi wannan zan miki kuma karb'i ki gyara sa ki goge kayan nan yanzu " Kukan da take ya ɗan tsagaita sai shesshek'ar kukan da take, tasa hannu ta kar'ba, Daddy yace " Yaran nan basa jin magana" Ai haka nake so nice daidai da ita zan gyara mata zamanta " Mommy ta faɗa tana jin kamar ta kifa ma Alesha mari Basmah tayi wajen Mommy tace" Yi hak'uri tun da kinga kema na rama miki" taja ta suka bar wajen Daddy shima ya wuce, Uwani ta matso wajenta ta dafa kafad'arta tace " Hajiya ƙarama Sannu ki ci gaba da hak'uri wata rana sai dai labari" Zauna na duba miki wajen na gani idan bai yi komai ba Zama tayi wajen ta janye rigarta Uwani ta duba mata wajen dukka fata bata tashi ba amman yayi jaaa sosai " Uwani samomin ruwa na zuba a wajen ko zai rage min zafi" Aah Hajiya ƙarama idan kika sa ruwa fatar wajen zata taso ne bara ina zuwa akwai zumar da innata ta bani wacce nake shan magani da ita sai a shafa a wajen " Ta faɗa tare da miƙewa Alesha ta gyad'a mata kai, Uwani taje ta ɗauko honey 🍯 ta shafa mata taji zafi sosai bayan an gama shafawa amman daga baya ta daina jin zafin, Uwani ta gyara dutsen ta ida goge mata kayan ta kwashe takai ɗakin basmah Washe gari ƙarfe goma sha biyu na rana Ummie suka fita tare da k'awayenta da mota Sune nan sune can hanyarsu ta komawa gida suka yi kaura da wata mota gaba ɗayan su suka fito, Ɗaya daga cikin su tace " Mun shiga uku kunga yadda motar nan tayi idan yace sai mun biyasa tamu ta ƙare dan wallahi kuɗin motar nan zata siye wannan sau uku " ta nuna motar su, sauran duk suka kallo ta Ummie ta buɗe baki da niyar magana ganin an buɗe murfin motar yasa ta dakata, fitowa yayi ya duba gaban motarsa ya watsa musu wani ɗan banzan kallo ko a jikinsu duk sun kafesa da ido ko motsin kirki basa yi ba ƙaramin kwarjini ya musu ba in fact tun da suke basu taɓa ganin Saurayin da ya musu kwarjini da kyau kamar shi ba duk abunda ake nema a tare da namiji wannan ya haɗa komai har ya juya ya koma motarsa ya shiga ya fito da hannunsa waje ya miƙe yatsunsa biyu ya musu alama da su kwace masa, kamar waɗan da basa cikin hayyacin su suka mammanne ma mota yaja motarsa ya fece ya barsu nan sai k'amshin turarensa da ya mamaye wajen, kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya " Allah ya taimake mu ko magana bai muna ba amman fa wallahi gayen nan ya haɗu over" Ummie ta 'balla mata harara kana tace " Cikin ku akwai wacce ta san shi ko ta taɓa ganinsa a wani waje?" Duk suka ce basu taɓa ganin sa ba sai yau Mota suka shiga taja suka wuce bayan ta koma gida banda tunanin sa ba abunda take ta ɗaukar ma kanta alƙawarin sai ta nemosa a duk inda yake sai sun yi soyayya cikin dare har mafarkinsa sai da tayi 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Ammie tana fara masa maganar Aliya ya nuna baya buƙata ranta ya 'baci sosai ganin duk matar da suka nema masa yace baya so kuma shi yaƙi ya nemi mata da kansa tun da mahaifiyar Noor ta rasu, Ammie ta sanar ma dad yadda suka yi dashi yace "Ta barsa da shi kawai yasan abunda zai yi" Ƙarfe huɗu yana kwance a ɗaki gaba ɗaya ya rasa abunda ke masa daɗi Rukayya ƙanwarsa ta k'wank'wasa ɗakin sai da ta kusa minti biyu tsaye sannan ya bata izinin shigowa tace "Yaya an ce ka sauko za'a ci abinci" Da hannu ya mata alama da taje ya ji sai tace " Baka jin yunwa?" Ya d'ago ya 'balla mata uwar harara da gudu tabar ɗakin, miƙe wa yayi ya shiga toilet ya fito ya zura takalmi ya fito koda ya isa kowa ya hallara, Dad sai Ammie da Husnah da rukayya Noor kuma na zaune saman ƙafafun Rukayya, yaja ɗaya kujerar ya zauna ya gaida iyayensa, husnah ta gaidasa Noor tace "Papah" Ya kalleta ya ɗauke kai husna ta miƙe ta zuba ma kowa abinci suka fara ci Noor tace " Aunt rukk" Na'am Noor " Dad yace Mommy na ta kusa dawowa" ta faɗa cikin farin ciki, Azaad da ya kai loma sai da abincin ya tashi kamasa ya ɗauki ruwa ya sha, ya kalli Noor ya 'balla mata harara, dad da Ammie duk suna kallansa dad yayi murmushi irin nasu na manya yaci gaba da cin abincinsa Noor tayi shuru Bayan sun gama cin abinci ya miƙe zai wuce dad ya dakatar da shi yace "Zauna jira ni zamuyi magana" Jin haka yasa sai da gabansa ya faɗi ya koma ya zauna Su rukayya daman sun wuce sun koma falo Ammie ta tattara kayan da suka gama cin abinci ta kira mai aiki ta miƙa mata ita ma ta koma falo ta basu guri, Dad yace "Azaad Maganar gaskiya zan faɗa maka na gaji nagaji da wannan abun da kake yi da kunyar da kake bama mahaifiyarka" Dad kunyar me?" Ya faɗa dan shi baya tunanin akwai abuda yayi wanda zai ba mahaifiyarsa kunya"Mata nawa tana nema maka har Yaran aminan ta amman kake bata kunya to nagaji da wannan kai na rasa wane irin mutum ne ko tausayin yarinyar nan Aminatu baka yi koda yaushe cikin kiran take a kaita wajen Mommynta yaushe Mommynta zata zo ko wannan bai isa yasa kayi aure ba ko dan yarinyar nan amman kai na fuskanci ba ruwanka to wallahi ba zaka tsufarmin a gida ba dan haka na baka nan da ƙarshen wannan watan da muke ciki ka fito da matar da zaka aura idan har watan nan ya ƙare baka fito da ita ba ni zan zaɓa ma duk wacce na so tashi kaban wajen " Azaad zuciyarsa kamar zata fito saboda 'bacin rai shi bai ga abun damuwa ba saboda yaƙi yin aure shi dai ke zama da mata ba su ba to yace bayaso baza a k'yale shi ba Yana kawowa falo sai ga yaya Aminu, yayansa sun shigo tare da yaransa su biyu duka maza Noor ta miƙe da sauri ta kama hannun baffa wanda shi ne ƙarami kuma shi ne sa'ar ta tace "Baffa nima Mommy na ta kusa zuwa" Baffa ya kama mata murna shima Ahmad yazo suka riƙe hannun juna suna ta tsalle suna murna Azaad baƙin ciki kamar ya kashe sa ya wuce yayi ɗaki ko tsayawa gaisawa da yayansa bai yi ba................ 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943* *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 5 Yaya Aminu ya saki baki yana kallansa ya kalli Ammie yace " Topah Ammie wa ya taɓa ɗan lelen ki naga ya ƙara haɗe rai" Ammie tayi murmushi tace "Shi da Mahaifin ku ne " Da alama an masa abunda ya taɓa zuciyarsa " Maganar dai ɗaya ce wacce ka sani" Aure?" Yaya Aminu ya faɗa, Ammie ta gyad'a masa kai"Allah ya shiryesa bara naje mu gaida da Dad " Okay" ya nufi dining wajen da Dad yake zaune yana ɗan wani aiki cikin wayarsa Yaran suka dawo wajen Ammie, Azaad yana isa ɗaki banda zarya a ɗakin ba abunda yake yi kamar zai tashi sama zuciyarsa sai tafasa take akan 'bacin rai, yadda yake ji shi wallahi bazai iya tsayawa da wata mata ba da sunan soyayya bare kuma har ta kai su ga Aure bama soyayya ba ko tsayuwa da mace baya san yi, Amman shi ne Dad zai yanke wannan hukunci shi gaskiya bazai yi aure ba Noor kuma dan tana faɗin a kaita wajen Mommynta ba ga su Rukayya nan da husnah ba ai sun isheta d'ebe kewar mahaifiyarta, ya numfasa a zahiri yace " Zamuyi magana da Ammie nasan zata fahimce ni ita, toilet ya wuce ya sake wanka ya sauya kaya sai k'amshi yake zubawa kamar wanda a ka yima ɓarin turare a jikinsa Koda ya sauko ƙasa ba kowa duk suna sama sai mai aikin su da ta fito daga kitchen wucewa yayi ya fice ya shiga motarsa ya bar gidan Dad zaune a office ɗin sa sai faman aikin cike wasu takardu yake saboda yau za'a zo amsar su baya so azo amsa ba tare da ya kammala aikin ba knocked ƙofar aka yi yaɗan jima sannan ya bada izinin shigowa Daddy ne ya shigo hannunsa riƙe da wasu fayil yace "Sir angama aikin" Okay " Ya karɓi fayil ɗin ya duba yace " You can go " Thank you sir " Daddy ya juya har ya kai bakin ƙofa Dad ya kirasa ya dawo yace"Please sit " daddy ya zauna Dad ya dakatar da aikin da yake yi ya mayar da hankalinsa ga daddy yace " Two days bamu gaisa ba to ya gida ya iyalai" Daddy yayi murmushi yace " Wallahi alhamdulillah duk suna lafiya ya wajen ku?" Alhamdulillah " sai kuma duk suka yi shuru can Dad yace" Kana da 'yar mace Babba? " Daddy ya washe baki yace "Eh ina da dan a ƙallah tana da 20 years a duniya" Ahh ma sha Allah ya sunan ta ne?" Sunan mahaifiyata ne amman muna kiranta da Ummie" Allah sarki Allah ya albarkaci rayuwarta " Amin Sir " Bara na ci gaba da aikin nan kafin su iso " Okay Sir" Daddy ya miƙe Dad yace "Ohh na manta Please sanar da PK ya sanar after prayer akwai meeting so su ɗan jira kafin su je lunch break " Okay " daddy ya wuce ya fita Dad kuma yaci gaba da aikinsa Bayan sun tashi daga aiki Daddy sai da ya koma gida ya riƙa tunanin tambayar da Shugabansu ya masa, bai dai sanar da kowa ba Mommy zaune a falo tare da basmah Ummie ta yi wajen party tare da k'awayenta Alesha kuma na ɗaki, Sallamar da ake tayi ne yasa Mommy taja tsaki ba tare da ta amsa ba tace " Wai waye ne? " Duk da ta gane muryar matar "Amina ce"Matar ta faɗa Mommy tace "Basmah je ki buɗe ƙofa" Bubbuga ƙafa tayi tace " Ni Allah mommy bazan iya ba ina zaune ina kallo zaki wani ce naje na buɗe ƙofa ke ki tashi kije da kanki ki buɗe" Haba mai da wuk'ar yi hak'uri Alesha! Alesha!" Na'am" Alesha ta fito mommy tace taje ta buɗe ƙofa ta wuce taje ta buɗe matar da ta gani ne tsaye yasa ta saki murmushi tace "Mamma" ta faɗa jikinta ta rungumeta Mamma ta ɗago ta tana murmushi tace mu shiga daga ciki ta riƙe hannunta suka shiga sai tsakiyar falo ta saki hannunta ta samu waje ta zauna Alesha ta zauna ƙasa gefen ƙafafunta tana jin wani irin farin ciki na ganinta Gaisawa suka yi da Mommy, mommy sai wani shan k'amshi take yi Mamma ta jima zaune a falon kiran sallah da aka fara yasa tace ma Alesha ta taso suje ɗakin ta tayi sallah Sai da suka yi sallah, bayan sun gama Alesha ta fito ta je kitchen ta ɗauki filet ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa da lemo guda biyu ta fito tana fitowa sai ga mommy ta bita da wani mugun kallo Alesha ta sunna kanta ƙasa mommy tace " Duk wannan abun da kika ɗauko ubanwa zaki kai ma? Wallahi idan baki koma kika rage su ba zan wanka miki fari shashashar banza kawai" Mommy ta juya ta wuce Alesha ta koma ta mayar da lemo guda ta kaima Mamma Tayi kwance saman jikin mamma tace " Mamma nayi kewarki sosai kullum ina san naje wajen ki" Ba wani nan ai baki yi kewana ba da kin isko ni, ni da na damu ai kinga na kawo ƙafafuna rabon da na ganki tun sallah fa da kika je idan na kira waya kuma ina san magana dake ba'a ɗaga wa wai meya samu wayan ki? " Ta lalace" Kuma ba'a gyara miki ba ko a siya miki wata ba?" Alesha tayi shuru dan abunda bazai yiwu ba ne Mamma ke faɗa "Yanzu bama wannan ba me yake hanaki zuwa waje na " Mommy bata bari na ina zuwa ko ina daga makaranta sai gida sai kuma idan zanje cefa ne" Cefa ne fa?" Eh" Ke ke zuwa yin cefa ne ina ita mai aikin ku " Tare muke zuwa" Okay har yanzu kina karantarwar kenan?" Eh" Allah ya taimaka " Amin" Alesha " Na'am" ta amsa muryarta da alamun bacci take ji " Idan na tambeki zaki faɗa min gaskiya" Eh " Me yake damunki ?" Ba abunda ke damuna Mamma me kika gani ?" Alesha ni zaki ce ma ba abunda ke damunki ni fa mahaifiyar ki ce kuma ba haka na sanki ba duk wanda ya sanki yasan ba haka kike ba duba kiga yadda kika rame" Alesha ta kalli jikinta tace " Ni ba abunda ke damuna" Ki dai ce ba zaki sanar min ba Alesha kin sauya sosai ban san ki da zurfin ciki ba Aleshar da na sani da bata 'boye min komai amman yanzu" Mamma ta faɗa tare da yin shuru idanun alesha sun ciko da ƙwallah tace " Ni ba abunda nake 'boyewa" ta faɗa muryar ta kamar zata yi kuka " Idan bakya 'boye komai ai da kin sanar min" Ko ida rufe baki bata yi ba Alesha ta fashe da kuka ta k'ank'ameta tana kuka mai ban tausayi, Mamma ta shiga rarrashinta tana Bubbuga bayanta har tayi shuru ta lumshe idanunta daga haka bacci yayi awon gaba da ita saman jikin mamma, Mamma ta gyara mata kwanciyarta tana shafa kanta ita ma baccin ya ɗan ɗauke ta huɗu da minti goma Mamma ta farka ta zabura Alesha baccinta take hankali kwance, Mamma ta shafi fuskarta tare da kiran sunanta a hankali ta buɗe idanunta da suka yi ja alamun bacci Mamma ta sakar mata murmushi tace " Tashi muyi sallah" ta turo baki ta miƙe Mamma ta shiga tayo alwala itama taje tayi suna gamawa Mamma ta shirya zata wuce Alesha ta sa mata kuka Mamma bata tsaya biye mata ba dan tasa idan ta biye mata zata kai kusan magrib kuɗi ta ciro dubu goma ta miƙa mata tace ta siye wani abu, Alesha na kuka ta fito yi mata rakiya Mommy na zaune a falo tana cin abinci ta ɗago tace " A she kina nan nazata kin wuce tun ɗazu" Aah yanzu zan wuce "Yayi kyau Allah yasa an tsuka abun kirki" Mamma tayi murmushi tace "Sai anjima"Mu jima da yawa " Mamma ta wuce Kusan wata ɗaya da sati biyu da maganar Dad da Azaad amman ba wani bayani a wajen Azaad, Dad ya zuba masa ido ne kawai shi kaɗai yasan abunda yake shiryawa........... 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943* *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 6 Misalin sha biyu na rana Daddy zaune a falo tare da Mommy kasan cewar yau weekend ce ba aiki, mai gadi yayi sallama cikin falon ya shaidama Daddy yayi bak'o yana waje yana jiran sa, Daddy ya taso ran sa a ɗan ɓace saboda ya tsani sai yana zaune yana hutawa a tadasa gashi kuma shi baiyi da kowa zai zo wajen sa ba ya fito har harabar gidan baiga kowa ba ya kira mai gadi ya taimbesa "Ina baƙon?" Yana waje cikin motarsa Alhaji "Mai gadin ya faɗa cikin ladabi"Okay buɗe musu geta su shigo " Da sauri mai gadi ya wuce ya buɗe gate Wata k'erarrar mota ce mai masifar kyau da ɗaukar ido tsaye gaban geta ɗin, Driver dake cikinta ganin an buɗe gate yasa ya kunno kan motar ciki ya nemi waje yayi parking da sauri ya fito ya buɗe mazaunin baya wanda mai gidansa ke zaune, Daddy ya saki baki da hanci dan san ganin ko waye a ciki, baki ya buɗe irin na mamakin nan ganin Dad ne yazo gidan sa abun ya basa mamaki ta yadda aka yi yasan gidan sa nufi wajen sa yayi fuskarsa ɗauke da murmushi shima Dad haka ya basa hannu suka gaisa Daddy yace " Rankaidad'e ka ne a gida na ? Bisimillah mu shiga daga ciki" No basai mun shiga ba a nan ma kawai yayi" Haba dan Allah mu shiga daga ciki ba girman ka ba ne tsayuwa a nan"Kar ka damu nan ɗin yayi "To haka za'a yi?" Bakomai "okay bara na samo muna abun zama" Daddy ya faɗa tare da kiran mai gadi yaje ya ɗauko musu kujerun roba masu tsayi ya aza musu cikin harabar motoci suka zauna suka ƙara gaisawa Dad yayi shuru ya rasa ta yadda zai fara magana Daddy ganin shurun yayi yawa yasa yace "Sir kayi shuru baka ce komai ba" Dad ya ɗan murmusa yayi gyaran murya ya ƙara gyara zamansa ya kalli Daddy zaaa kyau yace " Dole ne kaga nayi shuru saboda bansa yadda zan fara yi ma bayani ba" Subhanallah Allah yasa dai lafiya?" Daddy ya faɗa" To lafiya ba lafiya ba Alhaji wata matsala ce da ta jima tana damuna na rasa wanda zai min maganin ta shi ne na ce bara na zo wajen ka ko Allah zai sa na samu magani " Matsala fa ka ce Alhaji kuma ba mai ma maganinta sai ni?" Dad ya gyad'a masa kai Daddy yace "To ina jinka wace irin matsala ce Allah yasa zan iya yi ma maganin ta " Nasan kasan ɗana Azaad?" Eh nasan sa sosai "Ma sha Allah Tunda Allah yayi ma matarsa rasuwa wajen haihuwa yanzu kusan shekara ta shidda muke ciki amman yaƙi ya ƙara aure duk matar da aka kawo masa sai yace baya san ta bama wannan ba yarinyar da aka haifa masa kullum cikin faɗin take a kaita wajen Mommynta gashi shi uban nata ko maganar aure babu a tare da shi shiyasa nake san ayita ta ƙare kwana ki muka yi magana da shi akan na basa wata ɗaya ya kawo matar da zai aura da zarar watan nan ya wuce ni zan zaba masa duk matar da nake so in tak'aicema zance yanzu wata ɗaya har da kwana goma sha shidda ba wani bayani shiyasa nake san a d'aura masa aure ba tare da shi kansa ya ma sani ba sai dai kawai yaji labari Alhaji saboda haka ne yasa na zo wajen ka ina san mu ƙulla alaqa a tsakanin mu dan girman Allah ka taimaka ka bama ɗana Azaad auren yar'ka dan Allah Alhaji ka dubi maraicin yarinyar nan ka tausaya mata" Dad ya faɗa tare da haɗe hannayensa waje ɗaya yana neman amincewar daddy Daddy yayi shuru yana kallan Dad yana matuƙar ganin girman Dad koda ba a matsayin sa na shugabansa ba yana ganin mutumcin Dad sosai saboda taimakonsa da riƙon amana da gaskiya baya san ayi zalumci kuma baya mu'amala da masu irin wannan rayuwar ya riƙe gaskiya komai zak'inta kuma komai d'acinta Daddy ya kusa minti uku ba tare da yace komai ba zuwa can ya numfasa yace " Rankaidad'e hak'ik'a naji daɗi k'warai da gaske a matsayin ka na babban mutum a ƙasar nan tamu wanda yake ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a ƙasar nan kayo tattako tunda gidanka ka zo har gida na wanda ko aikowa kayi kace kanasan gani na da gudu zan je amman duk da haka ka zo da kan ka sannan naji daɗi na jin wannan maganar taka tunda har ka yaba da tarbiyar gidana ka zo nema ma yaronka auren yar'ta wannan kaɗai abun alfahari ne a wajena kuma ina mai shaida maka ni MUSA na bama yaronka auren yar'ta idan ma kun shirya ko yanzu kuke so sai a d'aura auren " Wani irin farin ciki ne ya lullu'be Dad wanda da ka kallesa zaga gane yana cikin farin ciki tsantsa har sauka yayi saman kujerar da yake yace " Nagode! Nagode! Ubangiji Allah ya saka da alkhairi Allah yasa wannan haɗin da zamu musu yasa a ce gwanda da ankayi Allah ya kalli zuciyoyin mu "Amin Ya Allahu" Suka ci gaba da magana Daddy yace idan yana so yanzun nan sai suje masallaci a tara mutane a d'aura auren " Dad yace" Da zan fi kowa farin ciki amman mu bari mu fara sanar da iyalanmu musamman ma kai a sanar ma yarinyar kar ayi mata girshi saboda bazata bata da daɗi idan yaso zuwa gobe sai a d'aura auren saboda ni bana ma san yaron ya sani har sai an d'aura aure " Daddy yace"To Shikenan Ubangiji Allah ya shige muna gaba " Amin, ba'a ɗau wani lokaci ba Dad ya wuce da farin ciki Daddy ya shiga gida bai sanar ma Mommy ba sai da yaje masallaci ya dawo ya sanar mata abunda ke faruwa, Mommy ta wurga masa wani kallo na bakasan abunda kake yi ba Daddy ganin bai samu goyon baya ba a kan hukuncin da ya yanke wajen Mommy yaaa ya kira Ummie ya sanar mata yayi mata miji, wani wulak'antaccen kallo ummie ta riƙa yima mahaifinta ta tun da ya fara magana har ya gama ta miƙe tsaye tare da riƙe k'ugu cikin tsiwa ta kalli mahaifinta tace " Wallahi banga uban da zai min irin wannan Auren ba haba dan Allah Mommy kina ji fa" ta faɗa tare da kallan mahaifiyar ta Mommy tace "

Chapter 2 of 13