Share this page
Yi shurun ki kawai Ummie ko ni da nake haka ace baban ku ya rasu ba wanda zai yi min irin auren nan bare ke da k'uruciyar ki yarinya mai jini a jika kyakkyawa san kowa k'in wanda ya rasa a ce za'a miki irin auren nan inaa lahlahh lahhlahh bana ni ba" Wannan ma ai abun kunya ne kamar ni ace anyi min irin wannan auren ai sai duniya ta min dariya level ɗina ya zube ga k'awaye ni wallahi ba wanda zai min irin auren nan koda bana da masoyi bare kuma ina da wanda zuciyata ke k'auna had'ad'd'en gaye san kowa k'in wanda ya rasa ga kuɗi ga kyau ga izzah ga isa " Ta faɗa cikin shauk'i, Mommy sai murmushi take yi Daddy kam imani yawa ya masa ya kasa ce da su komai ya zubama sarautar Allah ido yana kallo " Jeki ki ci gaba da abunda kike yi, basmah ta tashi?" Ban sani ba " Okay je ki abun ki" ta wuce ƙuma ƙuma tayi ɗaki, Daddy yayi shuru yana kallan Mommy bai taɓa sanin rashin mutuncinta ya kai haka ba sai yau! Bai taɓa sanin gur'batacciyar tarbiya ta bama yaransa ba sai yau! Yar'sa zata tsaya a kansa tana gaya masa magana san ranta ko nauyinsa bata ji lallai ya ƙara tabbarda maganar da ake cewa idan zaka auri mata ka lura da tarbiyarta da tarbiyar gidan su wacce kake da tabbacin zata yi ma yaran ku tarbiya mai kyau, numfasawa yayi ya ce " Yanzu hajiya abunda kika yi kinga ya dace kenan? " Dallah dakata Alhaji " Mommy ta faɗa tare da ɗaga hannu" Akan me ina ji ina gani zan bari a cutar min da y'a koba komai kai da kunnen ka kaji tace akwai wanda take so dan haka wallahi bazan yarda kayi mata auren dole ba saboda da wanda zuciyarta ke so " Hajiya ƙaramin mutum kike san ku mayar da ni ko me bayan na riga da na sanar masa zan bama ɗansa auren yar'ta" Wannan kuma kai ka jiyo matsalar ka ce da kake wannan zance yar' ai ba ita kaɗai gareka ba koda ba kai ka haifeta ba ai yar'ka ce tunda yar' yayanka ce kana da ikon zartar da duk hukuncin da kake so a kanta ba wanda zai tambeka dalili gashi ta isa aure dan kaff unguwar nan ba ɗan sa'arta duk ƙasanta suke gashi ba masoya gareta ba bare ace tana da wanda take so dan haka kaje ka sameta ku k'ark'are zancen ni kaga tafiya ta " Ta faɗa tare da tashi ta wuce............................ 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943* *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 7 Daddy yayi shuru yana tunanin maganar da Mommy ta faɗa kafin ta tashi, ya rasa abunda zai yi har ga Allah bazai iya kiran Dad ya sanar masa ya janye maganar auren ba gashi wacce ya ce zai basu aurenta taƙi amincewa yanzu ya zai yi basmah dai bata isa aure ba koda ma ta isa tana ganin yadda yayarta tayi ita ma ai bazata amince ba, ya jima zaune a falo shi kaɗai jikinsa duk yayi sanyi ya rasa abun yi haka ya miƙe zai je d'aki, dai-dai ya kawo ɗakin Alesha ya ja ya tsaya ya kalli k'ofar d'akin zuciyarsa ta fara sak'a masa da, me zai hana yaje ya masu Alesha ya tabbata zata amince ko dan ta faranta masa "Anya kuwa zata amince?" Ya faɗa a fili tare da girgiza kai ya kama hanya zai wuce har yayi tako biyu zuwa uku sai ya juyo yace " Bara kawai na gwada" ya faɗa tare da juyawa ya tsaya bakin k'ofar ya k'wank'wasa k'ofar, Alesha na zaune saman sallaya tana karatun Alkur'ani mai girma taji ana k'wank'wasa mata ƙofa tama yi tunanin ko Uwani mai aiki ce saboda ita kaɗai ce idan zata shigo take k'wank'wasa mata ƙofa amman idan ba ita ba sai dai kawai taga mutum a kanta, tana kai aya ta tsaya ta miƙe fuskarta da murmushi tana buɗe k'ofar ganin Daddy yasa sai da gabanta ya faɗi ba shiri taja baya da sauri k'irjinta na dukan uku uku kanta a ƙasa ta durk'usa muryarta na rawa tace " Dadd....dy ina.....wuni" Kai tsaye yace "Zan iya shigowa?" Da sauri ta gyad'a masa kai tare da faɗin " Eh" Shigowa yayi ya barta nan durk'ushe a wajen yana kallan d'akin tsaftsaf duk da ba wasu kaya masu kyau ne da yawa a ciki ba dan daga wardrobe sai gado da mirror amman d'akin ya burgesa ya kalli gefen gado inda ta shimfid'a sallaya yayi murmushi, juyowa yayi ya ganta durk'ushe a wajen yace " Ta so mana daughter" Alesha ta ɗago kanta ta kallesa cikin mamaki na kiranta daughter da yayi saboda rabon da taji ya kirata da wannan sunan tun lokacin iyayenta na raye, Tashi tayi duk da har yanzu hankalin ta bai kwanta ba, Daddy ya yi mata nuni da alamun ta zauna, Ta zauna gefen gado, ya mayar da dubansa gareta yace "Daughter na zo neman wata alfarma ce a wajen ki ban sani ba ko zan samu?" Tayi shuru ta kallesa tayi ƙasa da kanta tana tunanin wace irin alfarma ce Daddy zai zo nema a wajenta " Kinyi shuru baki ce komai ba ko kema zaki watsa min ƙasa a ido ne kamar yadda Ummie da mahaifiyarta suka yi min?" Muryarta na ɗan rawa tace " Ka faɗi abun da ka ke so Daddy muddin bai sa'bama addinin Musulunci ba zan maka shi da yardar Allah " Da ta faɗi haka Daddy sai da yaji wani bala'in daɗi a zuciyarsa, bai 'boye mata komai ba ya zayyano mata duk abunda ya faru tun daga zuwan Dad har maganar da sukayi da Ummie, Alesha wallahi gaba ɗaya taji duniya ta tsaya mata, Allah ya gani tana bala'in ganin girman Daddy haka take kallansa tamkar mahaifinta duk da shima ɗin mahaifinta ne domin k'anen Abbanta ne, Kamar yadda idan mahaifinta ya nemi abu a wajenta ba zata iya bijiremasa ba haka shi ma Daddy ba zata iya tsallake maganarsa ba, ta rasa amsar da zata basa Daddy ya zauna kusa gareta yace "Daughter dan girman Allah ki taimaka ki rufamin asiri mutumen nan yana ganin girmana nima ina ganin nasa yanzu idan na kira sa na ce na janye maganar wallahi mutumci na da k'imata duka zasu zube a wajen sa zai ɗauke ni mutumen banza mai baki biyu nasan wannan ba abu mai sauk'i ba ne saboda rayuwar ki ce duk da haka idan kinji baza ki iya ba wallahi ba wani abun ba ne ki sanar min kawai domin ko yar' da na haifa da cikina ta kalli cikin idanuwa na ta sanar min bazata taɓa aurensa ba" Ya ƙarashe faɗa cikin tausayi " Daddy kai mahaifina ne nasan ba zaka taɓa yin abunda zai cutar da ni ba na amince Allah yasa hakan shi ne mafi alheri " Kin amince? " Daddy ya faɗa yana kallanta ta gyad'a masa kai hawaye masu zafi suka zubo mata, wani irin hugging Daddy ya mata cikin tsantsan farin ciki yace " Ubangiji Allah ya miki albarka Allah yasa ki gama da duniyar nan lafiya Allah yasa wannan auren ya zame muna alheri mu duka Allah ya gafarta ma su yaya Allah ya gafarta musu! Allah ya gafarta musu Nagode daughter nagode da kika fitar da ni wannan matsalar " Ya dade yana yi mata addu'a Alesha ta lafe a jikinsa duk da tashin hankalin da take ciki amman hakan bai hanata jin daɗi yadda suka kasance yanzu tare da Daddy ba sai yanzu ta ji a she tana da mahaifi har yanzu musamman addu'oin da ya yi mata, Sai da aka fara sallah sannan ya bar d'akin zuciyarsa cike da farin ciki Dad daga wajen Daddy kai tsaye gida ya nufa tun kafin ya isa ya kira Yan uwansa ya shaida musu yana san ganin su, bayan ya isa Ammie kawai ya sanar ma da zancen auren yace kar ta sanar ma kowa sai an d'aura, bayan yan uwansa sun zo ya sanar mu duk abunda ya faru suma sun goyi bayan sa ɗari bisa ɗari akan hukuncin da ya yanke Alesha cikin dare kasa bacci tayi sai juyi take zuciyarta gaba ɗaya ba daɗi ta miƙe taje tayi alwala ta shimfid'a sallaya tana nafila, a ƙarshen raka'a da tayi sujjada ta fashe da kuka tana kai ma Ubangiji kukanta ta jima kafin ta ɗago ta sallame Washe gari, ƙarfe biyu aka d'aura aure, Mommy da tayi zaton maganar ta wuce sai kawai ganin tayi Daddy ya shigo ɗauke da goro tare da wani ɗan uwansa shi kuma yana riƙe da kuɗi masu yawa, dan a k'allah zasu kai one million, ai ba shiri Mommy ta miƙe Daddy ya aje goron hannunsa wanda suke tare ya ɗaura kuɗin saman goro ya kalli Mommy yace "To Hajiya Ubangiji Allah ya sanya alheri Allah yasa can ne gidan ta" Mommy ta masa kallo me kake nufi, yayi ma Daddy sallama ya wuce Mommy ta kalli Daddy tace " Wannan na miye?" Sadakin Alesha ne yanzu ma haka har an d'aura aure yar' albarka " ya faɗa tare da duk'awa zai ɗauke kayan sai ga Mamma ta shigo, Daddy ne ya kirata ya sanar mata yayi mata bayanin komai bata ji daɗi ba gaskiya dan bata so a ce auren Alesha ya kasance a haka ba duk da tana san taga tayi aure amman bata so ya zo ta haka ba Sallama tayi ta ƙara so cikin falon "Ma sha Allah! Ma sha Allah wannan ne sadakin barakallah" Ta faɗa Daddy yace "Shi ne million ɗaya"Mamma ta zaro ido Mommy kuma sai da cikinta ya yi ƙara jin ance million ɗaya sadakin Alesha "Ma sha Allah Ubangiji Allah ya sanya albarka a cikin wannan lamari " Mamma ta faɗa "Amin ya rabbi " Daddy ya mik'a mata kuɗin yace"Taje da su ta nuna ma Alesha " ta kar'ba ta wuce tayi d'akin Alesha Wane ne Daddy da Mamma a wajen Alesha! Daddy dai k'anen Abbanta ne mahaifin ta ya saki nono shi ya kama Abbanta su uku ne a wajen iyayen su Maza biyu mace ɗaya mace Allah ya mata rasuwa, Abbanta mutum ne mai jama'a mai taimakon al'umma bayansan yaga mutum cikin damuwa kuma Allah ya basa tarin dukiya bai taɓa yin faɗa ko gaba da shi da wani ba, Duk sati ranar Friday gidansa haka zaka tarar da mutane kamar gidan biki an cika yasa an dafa abinci mai rai da lafiya a bama mutane da drinks sannan idan ka gama cin abinci zaka wuce ga takeaway ɗin ka da doughnut da cake 🍰 a ciki, Alesha su biyu ne a wajen iyayen su daga ita sai k'anenta, iyayensu na mugun son su domin duk abunda suke so ana musu, Mommy idan kaga kulawar da take yi ma Alesha wanda bai sani ba zai ɗauka ita ce ta haifeta duk da ba gida ɗaya suke ba idan ta siyama su Basmah wani abu to tare da Alesha haka suma iyayen Alesha muddin wata ya kai ƙarshe haka za'a kira a turo su Basmah su je ayo musu shopping sai abunda suke so shi zasu za'ba..................... 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943* *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 8 & 9 Kwatsam wata rana ya haɗu da wani mutume har suka fara hurd'a sosai abban Alesha ya aminta da mutumen sosai, mutumen yazo musu da wata hanya yadda zasu samu kuɗi sosai cikin k'ank'anin lokaci abban Alesha ya aminta da zancen sa hakan yasa ya basa rabin dukiyarsa ya basa rabi da sunan zasu yi kasuwanci, tun da mutumen ya tafi shuru kake ji har aka share watanni abban Alesha tun yana samunsa a waya har ya daina samunsa aka share watanni ba shi ba labarinsa abun ya damesa sosai, abu kamar wasa har aka yi shekara ɗaya mutumen bai dawo ba gashi Allah ya kawo ma abban Alesha wata jarabawa, ma'aikatarsa ta kama cikin shekara ɗaya arzikinsa ya ragu sosai har ya kai ga abincin da ake dafa ma mutane duk sati baya da wannan ƙarfin yanzu hakan yasa duk wani alkhairin da mutane suke yi masa suka daina saboda daman ba domin Allah suke yi ba Wata safiyar juma'a da safe sun aje Alesha a makaranta za suyi final exam ta kammala SS 3 su kuma zusu wuce suje ƙauye dan ya ga gonarsa da ake masa noma har sunje sun dawo a hanyarsu ta dawowa suka samu accident gaba ɗaya motar ba wanda aka samu a raye su duka Ko da Alesha ta dawo gida cike da farin ciki saboda exam ta musu daɗi sosai tun daga bakin gate taga mutane an taru wasu na alwala wasu kuma na zaune saman shimfid'a, gabanta ya faɗi sai da ta shiga ciki ta ƙara tsinkewa mutane sun cika sosai a harabar gidan su sai kallanta ake yi dauriya kawai tayi ta ƙara sa ciki turuss ta ja ta tsaya ganin mutum uku kwance ko motsi basa yi an lullu'be su da farin k'yalle ga jini ga mutane na kuka, yayar mahaifiyarta ce ta taso Mamma ita ma idanuwanta sun yi ja sosai alamun taci kuka ta riƙo Alesha tace " Kun ta so?" Alesha ta kalleta maimakon ta bata amsar tambayar da tayi mata sai tace " Mamma su waye waɗan nan? " Mamma tayi shuru ta kasa ce da ita komai Alesha tace " Ina mama na da abba Aminr! Aminr! " Ta riƙa kiran sunan k'anenta " Mamma ko basu dawo daga inda suka ce zasu je ne ba?" Duk dauriyar Mama akan kar tayi kuka ta kasa sai da ta fashe da kuka ta rungume Alesha tace" Kiyi hak'uri Alesha kiyi hak'uri " ta ja hannunta suka yi d'aki ta zaunar da ita sai da tayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta sanar mata abunda ke faruwa, Alesha tayi shuru Mamma ta ɗauko mata doguwar riga ta miƙa mata tace ta cire uniform ɗin ta tasaka rigar su fito falo, an shiryasu ana san a kai su makwancin su, tashi tayi ta sauya kayan suka fito falo ta tsaya wajen kanun su Daddy ya shigo tare da wasu yan uwansu aka ɗauki gawawwakin su Alesha ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi mai taɓa zuciya Mamma ta riƙo ta " Shikenan yanzu bana da kowa Mommy ta tafi ta barni abba ma haka yanzu babu wanda zamu riƙa faɗa da shi Amir ya tafiyarsa" Wallahi sai da ta ba ma duk mutanen da ke cikin falon tausayi " Shikenan bana da kowa" ta rushe da kuka mamma ta janyota jikinta tana bubbuga bayanta alamun rarrashi saboda ta kasa magana ita ma kukan na san cin k'arfinta Koda akayi kwana uku da rasuwarsu Alesha ta rame sosai cikin yan kwanakin nan ko abinci bata ci sai aikin kuka, sati biyu da rasuwar su masu bin abba bashi suka zo aka biya su Mamma gidan ta tare da zama saboda ita ma shekara ɗaya da rasuwar mijinta yaranta maza ne kuma manya ne sauran sunyi aure biyu kuma karatu suke yi basa ma k'asar bayan wata ɗaya Mamma ta samu Daddy ta nemi alfarmar tana san ta ɗauki Alesha ta kasance a wajen ta Daddy yace bai san zancen ba shi zai riƙe ta a hannunsa Mommy ta taji shi zai riƙe Alesha baƙin ciki kamar ya kashe ta ganin ba wani abu kirki aka samu ga gadonta ba kuma zai d'auko musu wani nauyi ya ƙara musu Mamma ganin kamar Mommy bata san zama da Alesha yasa ta ƙara nacewa akan ita zata ɗauke ta ba yadda bata yi ba akan ya bata Alesha amman yaƙi amincewa dole ta hak'ura Tun daga lokacin ta koma hannun Daddy gidan su aka rufesa, Bayan exam ɗin su ta fito Daddy ya kai ta University tana University Ummie na SS 1 seconday school, Ganin irin kulawar da Daddy yake yi mata yasa Mommy da yaranta suka fara kishi da Alesha, suka fara kai ma Daddy sukarta tun baya biye musu har ya fara biye musu, bai taɓa dukanta ba amman faɗa kam tana shan sa har sai tayi kuka, Mommy kuwa kamata take yi tayi ta jibga kamar Allah ya iko ta sannan muddin tana gida to duk wani aiki ita zata yi shi koda mai aiki su na nan kuwa, Wannan kenan Ammie taci kwalliya ta haɗe cikin wani leshi mai masifar kyau ta zuba wata kafurar sarka mai tsada ta yafa babban mayafinta fuskarta ɗauke da murmushi tana sauko wa su Rukayya dake zaune a falo suna d'aurin takeaway da Ammie ta sa ka su husnah ta ɗago tana kallan Ammie dake saukowa har ta iso wajen su " Wai har yanzu baku ida ba?" Saura kaɗan ammie " Rukayya ta faɗa"Okay kuyi maza " To Ammie wai na miye wa ake haɗa ma wannan! ?" Na baƙi ne ku kama jiki sun kusa fara zuwa " Baƙi za muyi? " Yau ake auren yayan ku koma na ce an ɗaura " Rukayya da husnah suka kalli juna cikin mamaki da jin furucin ammie Rukayya zata yi magana Dad ya shigo ya ja wankan farar shadda kamar shi ne angon, su husnah suka gaishe shi yace ma Ammie " Tare muke da yan d'aurin aure suna waje yanzu zanje na du'be musu ƙofar baya dan Allah ayi k'ok'ari a aiko musu abun taɓawa " In Sha Allah yanzu kuwa" Daddy ya wuce ammie ta kama hanya zata yi kitchen Rukayya tace " Ammie wai wa ne yayan na mu yayi aure ba mu sani ba?" AZAAD " Ta faɗa tare da shigewa kitchen Rukayya da husnah suka buɗe baki suna kallan juna Mamma ta ɗauki sadakin tayi ɗakin Alesha koda ta sameta idanunta sun yi jajirrr alamun taci kuka har ta k'oshi tana ganin Mamma ta fashe da wani sabon kuka, Mamma ta zauna saman gado kusa gareta ta janyota tana bubbuga bayanta tace " Mammaaa" Naam " Kai na ciwo yake min" Alesha ba dole kan ki yayi ciwo ba kin yi zaune sai kuka kike kinga yadda idanunki suka yi kuwa Please ki daina kukan nan kinji ya isa haka kinji! baban ku ya min bayanin komai nayi farin ciki sosai duk da ba ta haka naso auren ki ya kasance ba amman ba yadda zamuyi saboda Ubangiji ya riga da ya tsara lamarinsa ba wanda ya isa ya sauya sa Wallahi tayi farin ciki sosai da Ubangiji ya nuna min auren ki Alesha na jima ina san naga kinyi aure ke ma kin kama naki gida ki duba kiga duk fa yan sa'an ki sunyi aure harda yara idan ina miki magana sai ki mayar da maganata banza yanzu gashi nan da Allah ya tashi yin lamarinsa lokaci ɗaya ya kawo miki miji har gida Allah abun godiya ne sannan gidan miji sun ce basa buk'atar komai har kayan ɗakin ki duk su zasu yi komai nan da zuwa sati uku sai ki tare a gidan ki naji babanku ya ce ya taɓa aure matarsa ta rasu ta bar yarinya Alesha ina san ki natsu ki kwantar da hankalin ki kin dai ga yadda auren ki ya kasance ba sanin juna kuka yi ba keda shi bare ace har kun shak'u kin san abunda yake so da wanda baya so dan haka dole sai kinyi hak'uri kin jire kin kai zuciyarki nesa aure ma ana son ka ya aka ƙarasa bare kuma wannan nasan ki da hak'uri da juriya to ki ƙara akan wanda na sanki da shi kin san abunda yasa ake yawan gayama ma'aurata su yi hak'uri?" Alesha ta girgiza mata kai" Saboda hak'urin cikinsa yafi yawa akan jin daɗin da ke cikin sa Alesha zan iya ce wa duk matar duniya ba za'a rasa wata damuwa a tare da ita ba dangance da zamantakewarta da mijinta ba hak'urin nan da kika sani shi ne take yi dan haka Alesha ki kasance mai hak'uri da kau da kai ki gani kiyi kamar baki gani ba ki ji kiyi kamar baki ji ba kiyi masa biyyayya gwargwadon iyawarki ki kula da yarsa tamkar ke kika haifeta hakan ma zai sa ya ƙara ganin kimar ki da girmanki Ina san ki zamo gimbiya a gidan auren ki da wajen mijin ki in Sha Allah tunda har yanzu akwai sauran lokaci zan zaunar da ke na koya miki abubuwa sosai ta yadda zaki saye zuciyar mijin ki cikin ruwan sanyi, an gyara wayar ki? " Aah" ta faɗa tare da girgiza mata kai "Okay kar ki damu shekaran jiya yayan ki ya kira yace idan ya kira layin ki baya samu na sanar masa wayar ta lalace shi ne ya turo kuɗi yace a siya miki sabuwa yanzu ma haka na bayar a siyo ina tsammanin anjima ko gobe za'a kawo min wayar sai na kawo miki " Nagode sosai Ubangiji Allah ya saka masa da alkhairi Allah ya basa sa'ar karatun sa"Amin " Mamma ta ɗaura mata sadakin a hannunta tace " Ga sadakin ki" Alesha ta kalli kuɗin tayi shuru can tace "Ni bana so ba abunda zan yi da su"Alesha kin taɓa jin an ce babu abunda za'a yi da kuɗi? Ki kar'ba ki aje zanyi tunanin abunda za'a yi da su "To Mamma amman ki aje a wajen ki zai fi"Shikenan " Azaad tun da ya shigo abun ke basa mamaki duk da wannan ba abun mamaki bane a wajen sa dan inda sabo kusan haka gidan su yake al'umma na taruwa sosai musamman idan Dad na gari amman yanzu abunda ya fara basa mamaki na murnar da mutane ke masa suna faɗin Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya kansa duk ya d'aure ya kasa fahimtar abunda ke faruwa............... 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *GA MAI BUƘATAR A TALLATA MATA SANA'AR TA KO GROUP ƊIN TA NA KASUWANCI YOU CAN CHAT ME ON 09046495943* *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 10 Koda ya shiga cikin falo ya tarar da mata sai surutu suke yi wasu na cin abinci ya kaɗa kai ya wuce yayi sama bakin sa ɗauke da tambayoyi shi dai ban san da wani biki a gidan su ba da wannan tunanin ya wuce ɗakin Ammie Sallama yayi ya tura ƙofar ya shiga aunty suwaiba matar yayansa da su Rukayya sune a cikin ɗakin ya haɗe fuska ya dudduba bai ga Ammie a ɗakin ba ya juya zai fita sai gata ta shigo "Son kai

Chapter 3 of 13