Share this page
duk da bata san silar kukan ba , Ummie sai da taci kukanta sosai sannan ta juyo kalli Alesha dake tsaye a kanta ita ma har ta fara hawaye, Ummie ta buge hannunta dake jikinta tare da wurga mata harara ta miƙe kamar zata tureta ta nufi akwatinta ta buɗe ta ɗauko duk abunda yake nata ta saka ta rufe akwatin ta ɗauki mayafinta ta saka ta wuce wajen da wayarta ke zube a ƙasa ta ɗauka ta ja akwatin ta zata fita Alesha tayi saurin shan gabanta tace "Ummie lafiya ? Meya faru ina zaki je?" Gidan ubana zan je Alesha "Saboda me? Laifin me aka miki dan Allah Ummie ki sanar min me yake faruwa ko wani ne baya da lafiya a gida?" Alesha kowa lafiyarsa k'alau ki jaye min na wuce kawai na gaji da zama a gidan nan ne gidan mu zan je ki bani hanya" Ummie bazan baki hanya ba sai kin faɗa min dalilin da yasa zaki tafi sannan me aka miki ki ke kuka?" Hmmmmmmm Alesha wallahi tallahi idan baki bani hanya ba zan turaki baya" sai dai ki tura ni Ummie bazan jaye ba "Ohh haka ki ka ce" Ummie ta faɗa tare da sakin akwatin da niyar tura Alesha baya ganin haka yasa Alesha ta bata hanya taja tsaki tare da jan akwatin ta fice zata bi ta Noor ta fashe da kuka sosai dan ta tsorata dole Alesha ta fasa ta zo ta ɗauki Noor tana rarrashinta............ 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Alƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 32 Tafiya take ko ganin gabanta bata yi sauran kaɗan ta buge da bangon ƙofa ta tsaya ta share hawaye ta buɗe ƙofar ta fice Tana fitowa mai gadi ya rugo a guje ya nufo fa yana faɗin "Gimbiya fita za'a yi da kayan ne ai da kin kira ni nazo na ɗaukar miki kin san bana son naga kin wahala"Wata uwar harara Ummie ta watsa masa sai da ya tsorata saboda idanunta sun yi ja sosai amman duk da haka sai yayi murmushi ya kai hannu zai kar'bi akwatin tare da faɗin "Allah ya huci zuciyarki gimbiyar mata"Tak'i miƙa masa akwatin ya sake kai hannu zai kar'ba ta daka masa tsawa tare da faɗin " Shin na ce bana so ko ana dole ne? Musa ka fita idona na rufe wallahi kaji na rantse wallahi! Wallahi na rantse da wanda ya busa min rayuwa idan ka sake min magana sai na shararamaka mari ai ka ji ni dai banza kawai saboda tsabagen rainin wayo ni sa'ar ka ce ko tsararka ce iskancin banza kawai mtssssssssssssssssssasa" ta faɗa tare da jan akwatin ta tayi gaba da sauri mai gadi ya biyo bayan ta yace" Hajiya gimbiya kiyi hak'uri abun bai..................... " Ai ko ida faɗa bai yi ba Ummie ta juyo da ɗauke shi da wani gigitaccen mari sai da ya ja baya tare da dafe kuncensa saboda iya ƙarfin ta haɗi da ɓacin ran da take ciki ta sauke masa a fuska tare da yi masa warning da hannu ta juya taci gaba da tafiya ta buɗe ƙofar gate ta fita mai gadi bai daddara ya sake biyota yana" Hajiya dan Allah kar ki tafi ki barni ki tausaya min" Ummie cike da mamaki ta juyo ta kallesa duk marin da ta masa amman sai da ya sake biyota ganin yana neman cimmata yasa ta riƙa sauri sai ga taxi ta biyo ta tare tayi sauri ta shige suka wuce Mai gadi kamar wani ƙaramin yaro ya fashe da kuka yana kiran sunan ta ya juya ya koma ciki yayi zaune kuka kawai yake yi a haka Azaad ya dawo ya tarar da shi bayan ya buɗe masa gate ya shigo yayi parking ya kirasa ganin yana kuka a tunanin sa ko Rashi aka masa Azaad yace "Musa lafiya meya faru?da girmanka kana kuka haka kamar yaro" Mai gadi ya ƙara fashewa da kuka yace "Ta tafi yalla'bai ta tafi ta barni"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un musa hak'uri zaka yi duk mai rai baya wuce lokacin sa Ubangiji Allah ya gafarta mata Allah ya raya abun da ta bari " Azaad ya faɗa a tunaninsa matarsa ce ta rasu musamman da yaji yace ta tafi ta barsa" Mai gadi ya ɗago ya kallesa jin yana faɗin Allah ya gafarta mata yace "Yalla'bai ba rasuwa aka min ba"Ikon Allah to meya faru?" Hajiya ce ta tafi" Hajiya ta tafi?" Ya faɗa cike da mamaki yace" Wace hajiyar?" Hajiya Ummie yanzun nan ta wuce ba yadda ban yi ba dan ta tsaya kar ta tafi amman sai da ta tafiyarta " ya faɗa wani sabon kuka na taso masa Azaad ya gyara tsayuwarsa yana kallan mai gadi cike da mamakinsa saboda Ummie ta tafi shi ne yake wannan kukan kamar wanda aka aiko ma uwarsa ko matarsa ta rasu yace "Musa saboda Ummie ta tafi ka ke wannan kukan? To miye matsalarka da tafiyarta ne?" Wallahi yalla'bai bazan 'boye maka ba ina mutuwar bala'in son hajiya Ummie idan ban sameta ba zan iya rasa rayuwata dan Allah yalla'bai ka taimaka min na aureta "ya faɗa tare da gurfanawa ya haɗe hannayesa yana rok'on sa Azaad rasa abunda zai ce masa yayi can yace ya taso ya miƙe tsaye Azaad yace "Ya aka yi haka?" Wallahi ban sani ba lokaci ɗaya Allah ya ɗora min son ta" Shikenan nan ka daina kuka zamuyi magana "To yalla'bai zaka mata magana ne ta aure ni"Azaad yayi murmushi yace "Kai dai kawai zamu yi magana"To yalla'bai Nagode sosai "Yanzu ka daina kukan nan ka je kaci gaba da aikin ka"To " ya faɗa tare da goge fuskarsa Azaad ya wuce Koda ya shiga cikin gida ya tarar da Alesha goye da Noor tayi bacci tana tsaye yayi sallama kusan sau uku amman hankalin ta baya nan tana can duniyar tunani sai da ya taɓata ta firgita ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya yace "Tunanin me kike haka?" Yaya Ummie ta tafi " Okay wani abu ne ya faru?" Aah " ta faɗa tare da girgiza masa kai"Okay sauketa " Bacci take yi" Ki kwantar da ita mana ta fa wuce goyo ki daina goyonta " Yaya yarinya ce fa"Yarinya ce amman ta wuce goyo ta girma"Ni gaskiya bana ganin girmanta bata wuce goyo a guna ba" To shikenan zamu gani idan cikin ci ya girma zaki goya ta " Ciki! Wane ciki?" Wanda na baki ajiya jiya " Ya faɗa tare da ɗaga mata gira ta turo baki tace "Ni ba abunda ka bani" To shikenan idan ma ban baki jiya ba yau zan tabbatar na baki " Ni dai wallahi bana so" ta faɗa tare da wucewa tayi ɗaki ya biyo bayanta Ta shimfid'e Noor zata wuce ya janyota ya mannata da bango hannunsa kawai taji ya damk'i na shanunta yana matsa zata yi magana ya haɗe bakin su waje ɗaya duk ya kashe mata jiki ƙafafunta suna neman gagarar ɗaukar ta bakin su na haɗe ya ɗauke ta suka fito ɗakin suka yi nasa ɗakin ya kwantar da ita saman gado abubuwan da yake mata yasa jikinta ya mutu tana son ta hanasa amman ta kasa tana ji tana gani ya raba ta da kayan jikinta bata fargaba sai da taji wani azababben zafi ya kai mata ta fashe da kuka tare da sa hannu ta turasa bata san ta makaro ba don ko gezo bai yi ba, taci kuka sosai kamar me kiran sallah da ake ne ya faɗo kunnen sa da sauri ya sauka a kanta ya ɗauke ta suka yi toilet ya haɗa mata ruwan zafi ya sakata ta wahala sosai taci kuka, bayan sun yi wanka harda na tsarki tare da dauro alwala ya sake ɗauko ta suka fito ya ajeta gefen gado ya fita yaje ɗakin ta ya ɗauko mata wata riga da hijab ya saka mata ya zura mata hijab ya shimfid'a musu sallaya ya ja su sallah a zaune tayi tata sallah ko da ta gama sallah jikinta har ya fara zafi Azaad ya juyo yace" Sannu" ta ɗauke kanta wallahi Allah ya gani haushi take ji, ta tuna da Noor dake bacci gashi an yi sallah ta miƙe dakyar ta yi hanyar fita Azaad yace "Ina zaki je?" Ɗaki " ta faɗa ba tare da ta juyo ba ta wuce................. 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Alƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 33 Tana tura ƙofa sai ga Noor tsaye tana murza ido tace" Baby kin tashi?" Noor ta gyad'a mata kai tare da faɗin " Mommy zan yi fitsari" Okay mu je " ta faɗa tare da kama hannunta duk da saurin da take son tayi amman ta kasa a hankali take takawa har suka isa toilet ta saka ta fitsarin bayan ta gama tayi mata tsarki tasa tayi alwala suka fito ta bata hijab ta shimfid'a mata sallaya ta tace" Princess magrib raka'a nawa ce?" Uku " ta faɗa tare da nuna mata yatsunta uku tace" Yawwa good girl oya do it "Okay mommy " Alesha ta wuce ta kwanta Noor ta fara sallah, koda ya shigo ya ga Noor na sallah yayi murmushin jin daɗi as her age abu ne mai matuk'ar wahala a samu yaro ko yarinya iyayenta na saka ta yin sallah har ta san raka'oin da zata yi, wucewa yayi wajen Alesha dake kwance idanunta a rufe kamar mai bacci al halin kuma ba baccin take yi ba da ta ji k'amshin turarensa sai ta ƙara lafewa Zama yayi kusa gareta yace "Kin yi bacci ne?" Ya faɗa tare da kai hannu ya shafi fuskarta take yaji zafin jikinta yace "Subhanallah fevern ya dawo meyasa baki sanar min ba ko na kira likita ne?" A hankali ta buɗe idanunta har ta sauke su a kan sa ganin yadda ya riki ce yana ƙoƙarin kiran likita har ya lalubo number sa zai kira ta riƙo hannunsa ya juyo ya kalleta ya aje wayar gefe ya riƙo hannun cikin nasa har tafin hannun ta akwai zafi Yace "Mene ne?" Yaya ba sai ka kira likita ba da na sha magani zai sauka " Beb ki bari kawai na kira ta kinga ko ɗazu kinyi fama da zazzaɓin nan yanzu ma gashi ya sake dawowa" Yaya ko ɗazu da na sha magani ya tafi yanzun ma da ya dawo saboda k............."Sai tayi shuru ta ƙasa ƙarasawa yace"Ina jin ki saboda me?" Ta turo baki tace"Please ni dai ba sai ta zo ba da na sha magani zai tafi "Hakan ki ke so?" Ya tambeta ta gyad'a masa kai yace " Shikenan amman idan naga bai sauka ba zan kirata kin amince?" Eh" "Mommy! Mommy na miki addu'a"Noor ta faɗa tare da hawa gadon tayi wajen Mommynta Azaad yace "Ni kuma fa?" Mommy nayi ma "Ikon Allah gaskiya gidan nan ana nuna min son kai ba komai nima na kusa na rama wannan wulak'ancin da ake min da kin haihu" Alesha tayi dariya tare da faɗin "Yaya wulak'ancin me aka maka"Wa yasan iyaka idan nace miki abu sai ki ce y'ar ki ita kuma Mommynta komai Mommynta nima dai Allah ya nuna min kin haihu komai zamuyi daga ni sai ɗana don ma ku ji " Hhhhhh yi hak'uri"Ku zan bama hak'uri bama wannan ba me kika roƙa mata ne?" Wannan sirri ne fa tsakanin y'ar da uwa" Hmmmmmm sirri ba" ya faɗa tare da tashi yaje ya ɗauko mata magani ta sha cikin ikon Allah ba da jimawa ba maganin ya yi mata aiki zazzaɓin ya sauka Sha ɗaya da arba'in yana zaune a ɗaki yana ta dubin shigowarta amman shuru hakan yasa ya tashi ya zura takalminsa ya fito ya nufi ɗakin ta ya tura ya shiga, ɗakin ba haske ya laluba ya kunna glub kwance ya hango su suna baccin su hankali kwance " Matar nan me take nufi ne?" Ya faɗa tare da nufar gadon yayi tsaye addu'a ya yi ya tofa ma Noor yasa hannuwa kawai ya tallabo Alesha ta buɗe idanunta da sauri ta fara mutsuniya tana zillo tana son ta sauka ya fito da ita yayi ɗakin sa suna shiga ya sauke ta saman gado "Yaya dan Allah ka barni na kwana a can"Saboda me?" Yaya ita kaɗai ce fa dan Allah ka barni na kwana tare da ita" Saboda Ita kaɗai ce me zai cita ba inda zaki je a nan zaki kwana " ya faɗa tare da cire jallabiyarsa tayi saurin ɗauke idanunta daga shi sai gajeren wando ya wuce ya kashe wuta Ya hayo gado ya kwanta taji gabanta ya bada ɗasssss, ganin yayi kwancinsa yasa ta gyara ta kwanta tana kwanciya ya matso kusa gareta ya janyota jikinsa "D......dan Allah y......a.....ya ky......... Kayi hak'uri" Ta faɗa bakinta na rawa"Mu yi bacci " ya faɗa ita dai duk a tsorace take da shi sai da taji numfashin sa ya sauya alamun yayi bacci sannan ta sauke ajiyar zuciya ta rufe idanunta da tunanin Noor bacci yayi awon gaba da ita Ummie tun da ta koma ta shige ɗaki banda kuka ba abunda take yi mommy ta kasa gane kanta tambayar duniya ta yi mata amman taƙi faɗa mata abunda ke damunta, washe gari rufi ta zo ta kawo mata maganin da malamin ya bayar wanda zasu karya sihirin tana kawo mata tayi hayak'in ta kira sunan musa mai gadi sau uku tare da faɗin "Na sake ka na sake ka na sake ka " Tsawon wata biyu Ummie duk ta rame tayi baƙi har da abincin kirki bata ci tunanin Azaad ya addabi ruhi da gangar jikinta tana gida ko ina bata zuwa mommy tun tana tambayarta har ta zuba mata ido 'bangeren su Alesha kuwa soyayyar su suke sha bilhak'k'i Azaad na nuna mata tsantsar soyayya da kulawa abun sai wanda ya gani............ 🌸🌸 AZAAD 🌸🌸 Mallakar Zainab Dodo ✍️( Sarauniyar Taskira 👑👑👑) *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} *https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531&mibextid=ZbWKwL* _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari._ *Alƙalaminmu ƴancinmu💪* Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇 09046495943 Chart only 👂 *Bismillahi Rahmanin Rahim* page 34&35 Mommy zata wuce ta gaban ɗakin su Ummie taji wani irin numfashi da Ummie ke yi kamar shed'arta zata fita da sauri Mommy tayi cikin d'akin, koda ta shiga ta hangota ƙasa ta faɗo tana shure shure da ƙafa kanta yayi baya numfashinta kamar zai bar gangar jikinta a ruɗe mommy tayi wajenta tana jijjigata tana kiran sunanta, Ummie ko jinta bata yi " Mansur! Alhaji Alhaji? Mansur wayyooooooooooo Allah na shiga uku Ummie kada ki tafi ki barni dan Allah kar ki mutu" ta faɗa tare da miƙewa ta fito fuskarta duk hawaye ne tana kai falo sai ga Mansur ya shigo tace "Mansur zo" Mommy lafiya meya faru?" Ganin tashin hankali a kan fuskar mahaifiyarsa ga kuma hawaye tace" Ummie ce Ummie ce muje " Meya sameta Mommy?" Mu je Mansur " ta faɗa tare da juyawa tayi gaba Mansur na biye da ita suka yi d'akin Turusssss ta ja ta tsaya ganin Ummie ta daina motsi Mansur ya nufi Ummie ya durk'usa yana jijjigata tare da kiran sunanta shima ya ruɗe ya ɗago ya kalli Mommy yace "Mommy bata motsi bata numfashi meya sameta?" Mommy tace " Aah aah wallahi! Wallahi Ummie baza ki mutu ba lokacin ki bai yi ba bazaki mutu ki barni ba wallahi"ta ƙarashe faɗa tare da fashewa da kuka tana jijjiga Ummie " Mu je asibiti" Mansur ya faɗa tare da miƙewa tsaye Mommy ta taimaka masa ya ɗora ta saman kafad'arsa suka fito suka nufi mota ya buɗe mazaunin baya ya sakata Mommy ta zagaya zata shiga Mansur yace "Mommy mayafin ki fa" Yi sauri je ka ɗauko min " ya wuce yaje ya ɗauko mata mayafinta suka wuce Wata babbar asibiti suka tsaya suna shiga aka karɓe su aka yi emergency da ita Mommy ta kar'bi wayar Mansur ta kira Daddy ta shaida masa abunda yake faruwa ta sanar masa da asibitin da suke Alesha kwance ita kaɗai a falo Noor bata nan an kai ta gidan Ammie Azaad kuma ya fita, ga ciwon kan da yake damunta kusan kwana uku take fama da ciwon kai, yau ma kwance take ciwon kan ya dameta Azaad ya shigo ya tarar da ita kwancen yace " Ba dai ciwon kan ne ba?" Ta ɗago ta kallesa tare da ƙoƙarin tashi yace "No yi kwancin ki kawai" ta koma ta kwanta tare da faɗin "Sannu da zuwa"Yawwa wai ko zamu je asibiti ne dear? Wannan ciwon kan yayi yawa " Yaya ban jima da shan magani ba" Amman ya kamata mu je a duba wannan yawan ciwon kan na mene ne " To Shikenan amman yaya mu bari zuwa anjima idan muka dawo sai mu biya mu ɗauko Noor "Okay" ya faɗa tare da zama ya ɗaura kanta saman cinyoyinsa ta ɗago ta kallesa shi ma kuma ita yake kallo tayi murmushi ta ƙara shigewa jikinsa ya tura hannunsa cikin rigarta yana matsa................... Alesha ta lumshe idanunta tana jin wani irin mugun daɗin abunda yake mata ita yanzu har mamakin kanta take duk yadda ya taɓa ta mugun daɗi take ji har Allah Allah take ya kai hannu a jikinta Asibiti kuwa dak'yar suka samu numfashinta ya dawo suka bata taimakon gaggawa tare da binciken abunda yake damunta, Mommy sun kusa kai awa ɗaya tsaye hankalin su a tashe musamman Mommy, fitowa aka yi da ita kwance saman gado tana bacci sakamakon alluran da suka yi mata da sauri duk suka nufo ta Mommy tana kallan yar' ta ta cike da tausayi duk ta rame tayi baƙi wani ɗaki aka kai ta aka sa mata ruwa likita ya juyo ya kalli su Daddy yace "Please ku ɗan fita tana buƙatar hutu a halin yanzu " duk suka fito waje Bayan doctor ya fito ya kalli Daddy yace"Kai ne mahaifita ko?" Eh ni ne" Daddy ya faɗa tare da gyad'a kai " Okay muje office ina san ganin ka" Okay " Ko na zo mu je ne" Mommy ta faɗa Daddy yace " Aah ki tsaya a nan kawai kar ki damu in sha Allah zata samu lafiya " Ya faɗa suka wuce office ɗin likitan Bayan sun shiga suka zauna likitan ya kalli Daddy yace" Yalla'bai wane irin sakaci ne haka kuka bar yar' ku da damuwa har tayi mata yawa irin haka " Wallahi likita ni bansan tana da wata damuwa ba idan ba kwanaki ba da mahaifiyarta take sanar min cewar bata da lafiya aka je aka siyo mata maganukka wallahi ban sani ba "To a gaskiya bazan ɓoye muku ba kun yi sakaci sosai saboda yar' ku tana cikin damuwa matuƙa akwai abunda take ɓoye muku wanda bata sanar muku ba ban sani ba ko bata so ku sani ne wanda sana diyar haka ya haifar mata da ciwon zuciya" Ciwon zuciya?" Daddy ya faɗa tare da miƙewa tsaye ya dafe k'irji " Kwantar da hankalinka yalla'bai "Likita taya hankalina zai kwanta kana sanar min yar'ta ta kamu da ciwon zuciya " Hak'uri zaku yi sannan muddin aka bi matakan da zamu ɗora ta a kai in sha Allah za'a ga haske " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Daddy ya faɗa tare da komawa ya zauna, likita ya basa shawara akan su lalla'bata ta sanar musu abunda yake damunta idan kuma taƙi faɗa yayi masa bayanin yadda za'a riƙa kula da ita da bata kulawa sannan a riƙa zama kusa da ita da hana mata tunanin komai ta hanyar bata labarai masu daɗi har Allah yasa ta mance da damuwar da ke damunta, Daddy yayi masa godiya sosai likitan ya rubuta maganin da za'a siyo wanda zata riƙa sha kafin su sallameta aka kuma maganin da za'a bata, Daddy ya fito ya sanar ma Mommy duk abunda suka tattauna da likita Ƙarfe huɗu ta farka ta buɗe idanunta tana kallan d'akin, Mommy ta lek'o kenan taga ta farka ta shiga da sauri ta yi wajenta tana faɗin " Ummie sannu kin farka sannu! Sannu mamana" ta faɗa tare da zama gefen gadon ta riƙo ɗaya hannun ta Ummie tace " Mommy ki kira min aunty" Ummie wace aunty?" Aunty Alesha dan Allah ki kira min ita" Me zata miki ke da ki ke cikin wannan condition " Mommy ki kira ta ki kirata" Ta faɗa numfashinta yana wani iri ganin haka yasa Mommy tace "Shikenan! Shikenan kwantar da hankalin ki zan kira ta Shikenan" Ki ce ta zo yanzu" To bara na kar'bo wayar Mansur " ta faɗa tare da tashi ta fita tayi tsaye tana dubin inda zata gansa saboda sun yi masallaci hanyar masallacin ta nufa sai gasu shi da Daddy tace " Kana da number Alesha ne?" Mansur yayi shuru can yace "Eh ina da" Okay kira min ita ka bani " To" ya faɗa tare da ciro wayar daga aljihu ya binciko number ya fara dialing number Alesha sun gama sallah kenan tana kwance saman jikin Azaad wayarta ta fara ringing, Azaad yace bara na ɗauko miki ya mayar da ita gefe ya tashi yaje ya ɗauko mata wayar ya kawo da mugun sauri ta tashi zaune sunan da taga yana yawo akan screen ɗin ne yasa gabanta ya faɗi saboda tun da take maganar kirki ma ba haɗa su take yi ba bare har ya kira ta sai dai idan wani abu ne ya faru ganin yadda tayi Azaad yace "Lafiya kuwa" Yaya Mansur ne ke kira na anya lafiya kuwa " Mansur wane Mansur?" Yaya Mansur dai " Ohh Mansur yayan Ummie?" Eh shi " Shi ma sai da yayi shuru can yace"To ki ɗaga ki ji Allah yasa lafiya " Amin" ta faɗa tare da ɗaukar kiran da ya sake shigowa a karo na uku Tayi sallama da siririyar muryarta, muryar Mommy taji ta amsa sallamar, Mommy tace " Alesha ce?" Eh ni ce Mommy " Okay Alesha muna asibiti Ummie ba lafiya"Subhanallah Mommy meya ke damunta " Uhm Alesha bari kawai yanzun ma ta farka ne take ta kiran sunan ki tace na kira ki dan Allah ki zo" In sha Allah Mommy gani nan tafe Allah ya bata lafiya kuna wace asibitin?" Mommy ta sanar mata asibitin ta kashe wayar "Yaya Ummie ce ba lafiya suna asibiti ta farka yanzu tana son gani na" Allah sarki Allah ya bata lafiya "Amin" Zaki iya zuwa yanzu ne?" Eh" Okay shirya sai na kai ki " ta tashi ta sauya tufafi saboda kayan da ke jikinta ba na fita ba ne Azaad kuma jallabiya ya zuba Alesha ta zura hijab ɗin ta har ƙasa suka fito, Saman hanya suka sayi Fruit ya'yan itãcen marmari Tare suka shigo asibitin suna isa ta kira Mansur shi yazo ya kai su wajen da suke Azaad suka tsaya shi da Daddy suna gaisawa ita kuma tana gaidasa ta wuce cikin d'akin, Mommy na zaune kusa gareta basmah Kuma na gefe zaune saman kujerar dake d'akin Koda abun ya faru bata nan

Chapter 10 of 13